Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bane to a wurina sun wuce komai. Iyalin dana ne. Dana Shu'aibu wanda kake bi ba. Kuma ka sani daga tafiyar nan in Allah Ya yarda zamu tashi mu basu gidansu. Ka fara nema mana gida kafin mu dawo". Daga haka ta fita Garzali yana take mata baya. Aka Rabe da shiga tashin hankali. Kafin goma na safe sun gama shiri aka kama hanyar Azare. Mota biyu suka yi, daya Abdulhalim ne da Umma, Mama da Hajjo. Dayar kuma ta Qasim tare suke da Jafar , Kawu Garzali da Zubaida wadda jikinta yayi sanyi. Tsoronta bai wuce kada suje su barta a wurin Mamanta ba. Ita ta rinka yi musu kwatance har suka isa gidan. Addua suke yi Allah Yasa su dace a sameta. Zubaida suka saka a gaba sai dai Umma ta kula yarinyar da gaske bata kaunar shiga gidan. Hajjo tace su bata hanya. Ta shiga da sallama sauran na bayanta. Ai tunda matan gidan suka ga bakin dake shigowa tare da Zubaida kallo ya dawo garesu. Na cikin daki ma fitowa suke yi. Qasim ne karshen shigowa kafin kace meye wannan mata marasa suturar arziki sai gudu suke yi suna rufe kofa. Dan sanda a gidansu a irin wannan lokacin ba abin arziki bane. Gashi ya hade rai, kyakkyawar fuskarsa kamar bashi bane Qasim mai barkwanci da yawan wasa. Wata ta tsegumtawa Uwargida zuwansu Zubaida sai gata ta fito da daurin kirji kanta babu dankwali. Da dan sauri ta taho inda Zubaida ke rabe a gefen Umma. "Zuby ina kika shiga tun jiya ake nemanki. Ziza tace min ta ganki da jaka." Ta bi su Umma da kallo "wadan nan fa?" Mama ce ta bata amsa "mu iyayen Asmau ne. Yarinyar da tazo gidan nan da ciki. Ki fada mana inda take".. Uwargida tayi dariya "amma Zuby baki da hankali. Yarinya ta fito yawon bariki shine kika je har gidansu. To nima nan bansan inda take ba. Munyi da ita zata zubar da cikin ta fara sana'a sai kuma ta bar gidan. Ai da 'Yar Dabas na gidan nan ba karamin kudi zata kawo ba". Tassss taji saukar wani wawan mari da ya gigita ta har bakinta ya fashe. Idonsa a rufe da bacin rai Qasim yace 'Yar Dabas din uwarki. Kin tara 'ya'yan mutane kina bata musu rayuwa. Wallahi idan baki fito da Asmau ba kulleki zanyi sai naga wanda ya tsaya miki." Umma, Mama har ma da Hajjo sai kuka Kawu Garzali na basu hakuri. Abdulhalim ya rike hannun Qasim da yake shirin sake sauke shi a jikin Uwargida. Ransa ya gama baci. Ina zai ga Asmau shine tambayar da yake yiwa kansa. Zuciyarsa ta gama bashi lallai akwai hannunsa a lalacewar rayuwarta da ta amininsa. Ya zama dole a gareshi ya nemota ya aureta. Umma na kuka tana rokon Uwargida ta taimaka ta fada musu inda Asmau taje. Uwargida ta rike kumatunta da yau zafi ga yaran gidanta suna kallo "tunda kika bari danki ya mareni bana fatan ku ganta. Indai karuwanci kuke tsoro ina nan ko da boka ko dan bori sai 'yarku ta zama magajiya...." Wannan karon shaketa Qasim yayi har sai da Zubaida tayi kansu duk yadda ta tsani mamanta kuwa. Su Mama suka ce ya saketa yaki. Kawu Garzali da Abdulhalim sunyi iya kokarinsu yaki sakinta. Da taji shaka ne ta nuna dakin da kayan Asmau suke. Da gudu Umma ta shiga dakin. Zuciyarta ta kara tsinkewa da taga jakar Asmau. Ga kayanta a ciki sai wari sukeyi saboda datti da dadewa. Haka Umma ta rungumi kayan tana kuka. Jafar ne ya shigo da sauri yace a cikin mutanen da ya tsaya nunawa hoton Asmau yana cigiya wani yace ya santa tana sayar da magani a kemis. Basu tsaya wata wata ba suka yi hanyar fita harda Zubaida. Uwargida tace "Zuby idan kika sake kika fita daga gidan nan kada ki sake dawowa. Ki nemi wata uwar ba dai ni ba. Ke a haka kina tunanin akwai namijin da zai aureki idan aka ji wacece ta haifeki." Turus Zubaida ta tsaya tana hawaye. Tana tsoron fita tunda bata san matsayinta a wurinsu Umma ba. Dukkansu tsayawa suka yi Hajjo ta koma ta kamo hannun Zubaida tana murmushi hakoranta da suka rine da goro suka fito. "Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma kinyi kin gama da yardar Allah." Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta." Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki. Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti. Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida tayi iyaye da miji in ce dai shikenan." Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar kyautatawa Asmau. ***** Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan Sada. Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama. Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa. "Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya da gaskiya kun hau kun zauna." Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...." Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba. Wayyo Allah na" Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda ya janyo shigowar sauran mazan. Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?" Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau. Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace "amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba." Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini tsufa" Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora bazasu fi goma ba" Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da tsufansu suke fadan shekaru. Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace ya ganta?" Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare har zuwa Jos ne. ABINDA AKE GUDU🙆🏽26 Batul Mamman💖 Da asuba Zulaiha ta tashi ta dama koko sannan dora ruwan wanka cikin tukunya. Dakin da Asmau take ta shiga ta gani ko ta farka ta tarar da ita a zaune rungume da 'yarta. Zulaiha tayi dan murmushi "Wannan yarinya kamar za'a kwace miki ita. Ke ko dan kunyar nan ta dan fari bazaki yi ba". Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi suka gaisa. Allah kadai Yasan irin son da take yiwa yarinyar nan. Yanzu bata da burin da ya wuce yadda zata yi ta inganta mata rayuwa. "Wane suna zaki saka mata?" Tambayar Zulaiha ce ta katse mata tunani. "Sunanta Safinatu, sunan kakarta ne". Zulaiha ta karbeta tana kallo "Allah Ya rayaki Safina. Tubarakallah ba dai hanci da idanu ba. Ina tsammanin nan gaba kadan sai an cike takarda zan bari a ganta. Zaki boye mata suna ne?" "Zan kirata Amatullah, baiwar Allah. Burin babanta kenan mu sakawa yaranmu sunan iyayenmu." Muhsin ne ya shigo dakin a guje kamar an biyo shi. "Umma gudu bandaki ki rufe kofa ga Abba nan da wayar radiyo yana nemanki". Kusan faduwa Zulaiha tayi garin sauri ta mikawa Asmau jaririyarta ta fita a guje. A tsorace Asmau ta tashi tana kokarin buya a bayan labule don duk ta kidime da taji muryarsa. "Ke Zulaiha fito nan barauniya. Na ajiye dubu biyar a aljihun wando yanzu na duba babu". Inuwar mutum ya gani a bayan labulen ya daga wayar zai saukewa Asmau a jiki yaji kukan baby. Sai a lokacin ya dan nutsu yana kallonta. Ita ma idonta a kansa ta zaro su a tsorace. Yayi saurin gyara tsayuwarsa. "Ashe bakuwa mukayi a gidan. Sannu da zuwa. Ya mutan gida?" Sai a lokacin Zulaiha ta shigo muryarta na rawa tace "Gidado ashe ka tashi. Bakuwa mukayi jiya zata kama hayar daki a nan. Mijinta ne tafiya ta kama shi." Hankalin Gidado duk yana kan Asmau yace "babu komai, ai kin kyauta da kika bata wurin zama. Dama kudin kosai zan tambayeki na nawa za'a siyo?" Yana magana yana bin jikinsa da susa. Zulaiha tace masa ta bayar da kudin yace to idan ta shigo daki sai ya bata. Kana ganinsa kasan karya yake yi ko kuma bai saba bada kudin komai a gidan ba. Fitowar da yayi da niyyar dukanta dama salon ta tsorata ne ta bashi kudi. Har ya fita motsi kadan sai ya juyo ya kalli inda Asmau ke tsaye. Da yasan da bakuwa bazai yarda ya kunyata kansa haka ba. Banda abin namiji yaushe mutum zaiyi tafiya ya bar mace kamarta a gida. A tsorace ta samu wuri ta zauna tana tunanin kyau irin na mijin Zulaiha. Duk da kana ganinsa kaga mai shaye shaye amma hakan bazai hana mace ganin kyansa ba. Duk da taga kyan 'ya'yansa amma babu wanda ya kama kafarsa. Zulaiha tayi dan yake "kinga irin tawa kaddarar ko? Kiyi hakuri nayi karya nace haya zakiyi. Da ban fada masa kina da aure ba babu abinda zai hana shi nemanki." Asmau ta sake zaro ido tana dafe kirji "duk da kinsan hakan shine kike zaune dashi"? "Hmmm ke dai indai _abinda ake gudu_ ya riga ya faru to sai dai hakuri." Darajar Asmau yau Gidado ya bayar da kudi banda kosan da Zulaiha ta siyo an karo bredi. Zinaru babar Gidado ko abinci bata ci ba ta dauki kayan miyarta da kayan kadi da take siyarwa ta fice daga gidan. Sai da suka ci abinci kowa yayi wanka sannan Zulaiha ta zauna bawa Asmau nata labarin. "Kamar yadda kika ji sunana Zulaiha. Iyayena duka yan Yobe ne zama ya kawosu nan. Ina da yayye maza uku ni kadai ce mace kuma auta. Babanmu yana zuwa saro kaya daga Kano da Lagos shiyasa duk wani abu na yayi ko kayan burgewa to zaki gani a jikina domin ba karamin gata suke nuna min ba shi da Inna. Nayi makaranta har na kai aji biyar a sakandire sannan na hadu da Gidado. Na tabbata da kika ganshi dazu kin fahimci mutum ne shi da Allah Yayiwa baiwar kyau. Haduwarmu ta farko Allah Ya dora min masifar sonsa. A lokacin Zinaru mahaifiyarsa tana dillancin kaya. Da zarar Baba ya dawo daga saro kaya zata zo ta diba ta sayar. A hankali aka fahimci ni da Gidado mun fara soyayya. Duk wani dan kudi da abu mai kyau idan Baba ya bani sai na bashi ya sayar saboda tausayinsa da nake ji. Shiyasa ya like min yake nuna min soyayya ni kuma duk na makance da irin halayyarsa ta shaye shaye da neman mata wanda mutanen unguwa da yawa suka sani. Ita kuma Zinaru babu wanda yasan mijinta ko danginta. Kawai ganinta akayi da danta. Baba yayi min fadan ya dokeni duk a banza. Ya dena bawa Zinaru kaya ya hana Gidado zuwa gidanmu. Amma daga makaranta sai na gudu na tafi gidansu. Idan naje nice wanki, wanke wanke, shara da duk wani aikin wahala nashi da nata. Idan zan tafi na kawo kudi na bata. Itama baki ga yadda take sona ba." Zulaiha ta share hawaye "A lokacin gani nake babu abinda zai nema banyi masa ba saboda so, bana taba ganin laifinsu. Aka hanani zuwa makaranta, karshe ma wan Baba ya kawo dansa don ayi min aure su huta. A ranar auren na gudu muka je gidan mai unguwa ni da Gidado muka kai karar iyayena. Mai unguwa ya aika aka kirasu ya bawa Baba shawarar ya barni na auri wanda nake so Baba yaki amincewa. Guguwar so na dibana nace idan ban auri Gidado ba zan shiga duniya." A nan ma Zulaiha sai da ta tsaya tayi kuka sosai "Baba yana kuka yace ya amince ayi auren. A nan aka daura sai dai gidan su Gidado ciki da falo daya ne suke haya. Haka iyayena suka rufe ido suka yi min kayan daki sannan Baba ya bani wannan gidan da kike gani amma ya gargadeni duk ranar da na tako zuwa gidansa tsinuwace zata biyo baya. Wannan dalilin yasa nake ta shaye duk wani bakincikin da na fara gani tun kafin na cika sati a gidan. Kaf kayan dakina sun sayar sannan babu abinci. Matar da ta ranta min kudi jiya makociyarmu ce tasha zuwa cetona idan yana dukana. Zinaru kuwa ta tsaneni ta tsani yarana. Burinta danta ya auri wata mai arzikin ya rabu dani. Bata taba masa fada akan abinda yake yi. Tun kafin na haihu nayi yaji sai dai daga bakin kofa Abba ya koroni. Ina cigaba da hakuri ne kawai saboda idan auren ya mutu ba karamar kunya zanji ba sannan gidanmu basa sona. Babu wani dangina da ya taba zuwa gidan nan." Asmau taji tausayin Zulaiha sosai. "Lallai kema kinga rayuwa wadda ta zama izina ga sauran mata. Soyayya da kiyayya duk idan suka yi yawa halaka ne. Allah Ya karemu daga sharrin son zuciya" "Amin" Zulaiha ta amsa tana tashi "kinga aikin da nake yi dashi nake ciyar da gidan nan kuma nasa su Humaira a makaranta. In dai zaki iya zaman amana damu sai mu zauna tare mu rufawa juna asiri". Asmau tayi mata godiya sosai. Zata zauna a gidan amma dole ta nemi aiki saboda kula da Amatullah da kuma abinda zasu ci don bazata zamewa Zulaiha karin nauyi ba. ***** Daga masallci Qasim ya taho Kano. Ya hade cikin kayansa na 'yan sanda kana ganinsa kasan babu wasa. Da ace da wuri ya sami labarin wadda taga Asmau tun a jiyan zai taho. Hajjo da Garzali su ma da sassafe suka shirya zasu fita. Alh Rabe ya tambaya ina zasu je ne, jiya har ya dawo basa nan. Hajjo tace "tafiya ce ta kama mu zuwa Azare, an sami wadda ta ga jikata Asmau." Karara fuskarsa ta nuna bacin rai ya juya ga kaninsa "yanzu kai Garzali idan Hajjo ta makance da son wadanda basu damu da ita ba sai ka biye mata? Bara'atu da iyalinta har wata tsiya ne da za'a damu dasu. Wane irin raini ne bata kawo miki ba Hajjo?" "Wai Alhaji menene matsalarka dasu? Ni tunda nake ban taba ganin abin batanci da sukayi mana ba sai ma wanda muka yi musu" cewar Garzali yana kara karya hularsa. Cikin kuka Hajjo tace "ba laifinka bane Rabe. Ni na bada kofa har ka sami damar takasu ina kallo ban hana ba. Kuma da kake cewa su ba wata tsiya bane to a wurina sun wuce komai. Iyalin dana ne. Dana Shu'aibu wanda kake bi ba. Kuma ka sani daga tafiyar nan in Allah Ya yarda zamu tashi mu basu gidansu. Ka fara nema mana gida kafin mu dawo". Daga haka ta fita Garzali yana take mata baya. Aka Rabe da shiga tashin hankali. Kafin goma na safe sun gama shiri aka kama hanyar Azare. Mota biyu suka yi, daya Abdulhalim ne da Umma, Mama da Hajjo. Dayar kuma ta Qasim tare suke da Jafar , Kawu Garzali da Zubaida wadda jikinta yayi sanyi. Tsoronta bai wuce kada suje su barta a wurin Mamanta ba. Ita ta rinka yi musu kwatance har suka isa gidan. Addua suke yi Allah Yasa su dace a sameta. Zubaida suka saka a gaba sai dai Umma ta kula yarinyar da gaske bata kaunar shiga gidan. Hajjo tace su bata hanya. Ta shiga da sallama sauran na bayanta. Ai tunda matan gidan suka ga bakin dake shigowa tare da Zubaida kallo ya dawo garesu. Na cikin daki ma fitowa suke yi. Qasim ne karshen shigowa kafin kace meye wannan mata marasa suturar arziki sai gudu suke yi suna rufe kofa. Dan sanda a gidansu a irin wannan lokacin ba abin arziki bane. Gashi ya hade rai, kyakkyawar fuskarsa kamar bashi bane Qasim mai barkwanci da yawan wasa. Wata ta tsegumtawa Uwargida zuwansu Zubaida sai gata ta fito da daurin kirji kanta babu dankwali. Da dan sauri ta taho inda Zubaida ke rabe a gefen Umma. "Zuby ina kika shiga tun jiya ake nemanki. Ziza tace min ta ganki da jaka." Ta bi su Umma da kallo "wadan nan fa?" Mama ce ta bata amsa "mu iyayen Asmau ne. Yarinyar da tazo gidan nan da ciki. Ki fada mana inda take".. Uwargida tayi dariya "amma Zuby baki da hankali. Yarinya ta fito yawon bariki shine kika je har gidansu. To nima nan bansan inda take ba. Munyi da ita zata zubar da cikin ta fara sana'a sai kuma ta bar gidan. Ai da 'Yar Dabas na gidan nan ba karamin kudi zata kawo ba". Tassss taji saukar wani wawan mari da ya gigita ta har bakinta ya fashe. Idonsa a rufe da bacin rai Qasim yace 'Yar Dabas din uwarki. Kin tara 'ya'yan mutane kina bata musu rayuwa. Wallahi idan baki fito da Asmau ba kulleki zanyi sai naga wanda ya tsaya miki." Umma, Mama har ma da Hajjo sai kuka Kawu Garzali na basu hakuri. Abdulhalim ya rike hannun Qasim da yake shirin sake sauke shi a jikin Uwargida. Ransa ya gama baci. Ina zai ga Asmau shine tambayar da yake yiwa kansa. Zuciyarsa ta gama bashi lallai akwai hannunsa a lalacewar rayuwarta da ta amininsa. Ya zama dole a gareshi ya nemota ya aureta. Umma na kuka tana rokon Uwargida ta taimaka ta fada musu inda Asmau taje. Uwargida ta rike kumatunta da yau zafi ga yaran gidanta suna kallo "tunda kika bari danki ya mareni bana fatan ku ganta. Indai karuwanci kuke tsoro ina nan ko da boka ko dan bori sai 'yarku ta zama magajiya...." Wannan karon shaketa Qasim yayi har sai da Zubaida tayi kansu duk yadda ta tsani mamanta kuwa. Su Mama suka ce ya saketa yaki. Kawu Garzali da Abdulhalim sunyi iya kokarinsu yaki sakinta. Da taji shaka ne ta nuna dakin da kayan Asmau suke. Da gudu Umma ta shiga dakin. Zuciyarta ta kara tsinkewa da taga jakar Asmau. Ga kayanta a ciki sai wari sukeyi saboda datti da dadewa. Haka Umma ta rungumi kayan tana kuka. Jafar ne ya shigo da sauri yace a cikin mutanen da ya tsaya nunawa hoton Asmau yana cigiya wani yace ya santa tana sayar da magani a kemis. Basu tsaya wata wata ba suka yi hanyar fita harda Zubaida. Uwargida tace "Zuby idan kika sake kika fita daga gidan nan kada ki sake dawowa. Ki nemi wata uwar ba dai ni ba. Ke a haka kina tunanin akwai namijin da zai aureki idan aka ji wacece ta haifeki." Turus Zubaida ta tsaya tana hawaye. Tana tsoron fita tunda bata san matsayinta a wurinsu Umma ba. Dukkansu tsayawa suka yi Hajjo ta koma ta kamo hannun Zubaida tana murmushi hakoranta da suka rine da goro suka fito. "Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma kinyi kin gama da yardar Allah." Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta." Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki. Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti. Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida tayi iyaye da miji in ce dai shikenan." Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar kyautatawa Asmau. ***** Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan Sada. Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama. Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa. "Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya da gaskiya kun hau kun zauna." Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...." Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba. Wayyo Allah na" Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda ya janyo shigowar sauran mazan. Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?" Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau. Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace "amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba." Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini tsufa" Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora bazasu fi goma ba" Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da tsufansu suke fadan shekaru. Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace ya ganta?" Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare har zuwa Jos ne. ABINDA AKE GUDU🙆🏽27 Batul Mamman💖 Qasim yayi alkawarin zuwa neman Asmau daga kauyen farko har Jos din. A sanyaye suka koma gidan Sada wadanda suke ganin sun zame musu 'yan uwa sakamakon kyautatawar da suka yiwa Asmau. Duka kayanta Rashida ta hada musu harda na jariran. Umma dai tasha kuka har ta gode Allah. Su Anti Binta, Shema'u da 'ya'yan Mama su Suwaiba duk sunyi ta kira su ji yaya ake ciki. Da zasu tafi har bakin mota Rashida da Sada suka yi musu rakiya aka karbi numbar wayar juna. Qasim ya cika alkawari wurin binciken Asmau sai dai babu wani abin arziki da ya samu duk da haka bai hakura ba. Duk inda yaji alamar anga mace da ta bata sai ya duba ko za'a dace. ***** Humaira babbar 'yar Zulaiha ke zaune gaban Asmau tana jira ta gama sakawa Amatullah kaya a goya mata ita. Zulaiha tace "Asmau kada ki goya mata ita kin santa da rawar kai. Tsorona daya kada garin rashin nutsuwa su fadi shiyasa idan tace na goya mata nake hanawa". "Umma da gaske zan nutsu bazan yar da ita ba. Ni da har girki nake yi miki amma sai ki hana ni goyo". Asmau ta dauko zani cikin wanda Zulaiha ta bata "tashi kinji babbar Yaya na goya miki ita. Ai nasan ko bakin kofar gidan bazaki je ba a nan zaku zauna" Duk yadda Zulaiha taso hanawa haka akayi goyon Humaira ta fita tsakar gida tana murmushin jindadi. Asmau ta sauke ajiyar zuciya. Watansu uku a gidan nan lokaci yayi da ya kamata ta fara neman aikin yi ko don ta ragewa Zulaiha nauyi. Ga Zinaru kullum tayi zancen kudin haya sai Zulaiha tace mijin Asmau ne ba'a samunsa ko da a waya. Gori kala kala take sha akan abincin da suke bata wanda ba danta ke nema ba. Gyara zama tayi yadda zata rinka hango Humaira da kyau sannan tace da Zulaiha "Nasan kina kokari sosai tun zuwana Allah Kadai zai baki lada. Amma ya kamata na nemi aiki. Saboda Amatullah dai nasan babu gidan da zasu daukeni kuma gashi bani da wata takardar makaranta. Shine nayi tunanin ko zan sami irin naki sai nayi". Zulaiha ta katse ta "haba Asmau, yarinyar nan har nawa take da zaki fara neman aiki? Ki bari ta kara kwari. Ni zamanmu dake duk wahalar da zan sha ban dauketa komai ba. Na dade ina rayuwar kunci da rashin makusanci kafin zuwanki." "Duk da haka gara nayi aikin ko don na taimaka miki. Ki duba fa tunda nazo su Muhsin basu taba zuwa makaranta ba saboda rashin kudi." Zulaiha tasan gaskiya Asmau ke fada sai dai kuma tana tunanin kankantar Amatullah. Shawara suka yanke washegari da taje aiki ta sami makociyarsu wadda tayi mata hanya. Da taimakon matar nan Allah Yasa Asmau ta sami aikin itama. Yanayin aikin nasu da wuya suje tare. Juya musu akeyi idan wasu suka yi na safe wasu sai suyi da yamma. Hakan yayi musu dadi kodayaushe akwai mai zama da yaran a gida. Asmau sai ta goya Amatullah ta tafi aikinta tunda bata isa a fara barinta a gida ba. Da yake yarinyar akwai dariya ga dan jiki sai tayi saurin shiga ran sauran ma'aikatan. Idan Asmau zata wanke bandaki sai a rike mata ita taje tayi aikin. Tunda ita mace ce mai ilimi sai ya zamto tafi sauran mayar da hankali wurin tsaftace duk inda ta gyara. Albashinta na farko kaya ta siyawa Amatullah har kala biyar da Ali autan Zulaiha. Sauran kudin kuwa kayan abinci ta siyo musu. Zulaiha sai godiya take yi mata har tayi mamaki ita da ake ta dawainiya da ita. Zamansu haka yayi ta tafiya cikin lumana da taimakon juna. A hankali likitoci da dama suka san Asmau saboda tsaftarta zance har wajen Chief Medical Director (shugaban asibiti). Da yaji yadda ake yabonta da son cigabanta tunda har turanci ta iya sosai ya canja mata aiki daga shara zuwa bada kati. Ba karamar murna sukayi ba saboda albashi ya karu. Ko kadan babu hassada tsakaninta da Zulaiha. Karshe ma aka mayar da ita bangaren bada sakamako idan anyiwa mutum gwaji a asibitin. Dan ihsani kuwa daga nurses da likitoci tana samu sosai a dalilin Amatullah. Bata da wata matsala a lokacin sai Gidado da Zinaru. Daga ita har Zulaiha basa jindadin zama dasu. Kudin hayar daki kuwa taki bawa Zinaru a hannunta kamar yadda take ta naci. Su Humaira aka mayar makaranta. Shi kuma Gidado baya shakka ko a gaban Zulaiha baya iya boye son da yake yiwa Asmau. Ya sha nemanta sai dai taki bashi hadin kai kuma kullum haka ta faru sai ta fadawa Zulaiha don gudun matsala. Tayi ta yiwa Zulaiha nasihar rabuwa dashi sai dai tayi murmushi kawai. Wannan ya tabbatar mata da cewa har yanzu Zulaiha na son mijinta. Sai ta kyaleta suka cigaba da zamansu. ***** Annur yana kwance a daki bayan ya dawo daga makaranta yana dan

Chapter 10 of 23