Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwadayi. A gidan Babana ma sai tace naci. Mu a gidan Zinayu koko da kosai muke ci, ko byodi da tea, ko tuwon safe ko Ummi" Kasa cin abincin Asmau tayi ta fashe da kuka. Sunga rayuwa ita da Amatullah. Dan kudin da take samu a kudin makaranta yake tafiya. Abinci kuwa sai dai aci garau garau. Su Umma suma kukan suke tayata. Abinda tafi karfi a da shine yanzu yafi karfinta. Anti Bintu tazo ta rungumeta "komai ya wuce Asmau. Kuka bazai dauke shekarun baya ba sai dai ya tuna miki da bacin rai." Hajjo tace "haka ne ki dena kukan haka. Rayuwace kowa da irin tasa duk da dai komai yana da sanadi. Naji dadi da kika koyawa yarinyar nan tarbiya mai kyau." A haka suka ci abincin ana taba 'yar hira har Asmau ta sake. Kafin su tashi Amatullah ta sake cewa "Ummi daga yau a nan zamu zauna ne?" "Eh mana ai kun dawo gida kenan" inji Shemau Tare duk suka tashi aka kwashe kwanukan suka fara layin wanka. Wurin shadayan safe Asmau na saka kaya don kuwa Mama Yalwa tace yau a gidanta zasu yini taji wayarta na ringing. Ko da ta dauka bakuwar number ta gani har tayi zaton ko Zulaiha ce tace "tuba nake maman 'yan biyu ban samu na kiraki ba" Shiru taji daga daya bangaren tace "Zulaiha ko kinyi fushi ne. Ni da ke fa ba'a ji kanmu ba" "Ashe kin iya hira Idon kuka" ji tayi gabanta ya fadi. Muryar da ko cikin bacci yanzu tasan zata gane taji. Kamar yana gabanta ta dan russuna a kunyace ta gaishe shi. "Har kin gane mai magana, ko kuwa dai wayancewa kika yi?" Tana murmushi tace "Na gane" Col. Ishaq ya gyara kwanciyarsa. Shi bai ma san dalilin da yasa yayi mata waya da safe haka ba. "To waye?" "Baban Amatullah" "Uhmm uhmm, a wurinta kadai nake baba. It seems ko sunana baki sani ba. Shiyasa jiya kika kasa fadawa yayanki" Asmau taji muryarsa kamar baiji dadin hakan ba tace "na sani kuma na fada masa ma" Magana yake kamar maganar aiki ce mai zaman kanta yace "me kika ce masa? I am sure ba Baban Safina kika ce ba". Ita fa kunyarsa take ji. Ganinsa take yi babban mutum mai matukar kwarjini da cika ido shiyasa bata tsawaita hira dashi. Sake maimaita tambayar yayi tace "Col I. M Jikamshi" Wani iri yaji yadda ta fadi sunan a hankali kamar bata so yaji. "I. M Jikamshi yana rokon alfarmar ayi saving din numbarsa saboda kada ki sake kirana Zulaiha. By the way ina princess dina? "Ana yi mata wanka" "To zan sake kira anjima ki hadani da ita. Ina fata kinji request dina. Idan kika sake kirana da sunan mata zamu kulleki ni da Safina. Ki gaida da Umma." Amsa masa tayi da to...tana 'yar dariya ta ajiye wayar. Mimi babbar 'yar Shemau ce ta shigo tana kiranta Umma tace tazo falo. Hijab ta saka ta fito daidai lokacin da Qasim ya dago kansa. Suna hada ido nata ya ciko da hawaye shi kuma nasa suka yi ja sosai. Ya kura mata ido yana kallonta "Asmau ke ce?" Ta fashe da kuka tana kallonsa tana tuna wasu lokuta a da. Yayi dan jiki kamar bashi ba. A da Abubakar ya fushi kumari. Gashi duk ya canja alamun yana da sukuni. Kusa da Umma ta zauna a kasa ta gaishe shi tana dan murmushi ga hawaye "Yaya Qasim ai bazan ganeka ba" Yau da Asmau namiji ce babu abinda zai hanashi rungumeta don ya nuna mata tsantsar farincikinsa da ya ganta. Jiya da ta tsaya a Shanono su Inna suka ce dare yayi ya bari gari ya waye ya karaso Kano ji yayi inama bai biya ya sanar dasu ba. Yau dai burinsa ya cika Asmy din Abubakar ta dawo gaban iyayenta. Amatullah ce ta shigo falon tana kira Asmau. Duk da ta sake da mutanen gidan amma haka halinta yake da an dan jima sai ta nemi Umminta. Tana ganinta kuwa zata kama wata sabgar. Gaban Qasim har faduwa yayi da ya ganta. Baya bukatar wani karin bayani ya tabbatar wannan 'yarsu ce wadda rabon haihuwarta ya jefa iyayenta da su kansu cikin rudani. Tashi yayi ya durkusa a gabanta yana shafa fuskarta, muryarsa na dan rawa yace "yaya sunanki"? Tayi masa murmushi irin wanda yake tunawa Asmau da Abubakar idan tayi shi "Safinatu Amatullah Abubakay" Rungumeta yayi kawai hawayen farinciki na fito masa. Muddin yana raye yayi alkawarin kula da ita har karshen rayuwarta. Yana shafa kanta yace "Safinatu nine babanki" Ta dago kanta tana kallon Asmau "Ummi ni babana biyu ne"? ABINDA AKE GUDU🙆🏽37 Batul Mamman💖 Tana gama wayar Ainau ta tambayeta ko waye tace baban Amatullah ne. Ainau ta kurawa 'yar uwarta ido "Yaya Asmau zaki iya yin sati a garin nan kuwa ko kawai mu bi Yaya Yassar mu koma Kano" "Kada ki damu Ainau, irin wannan abubuwan nasan ban fara ganin komai ba ma. Idan ya faru ne yake taba min zuciya na dan lokaci har nayi kuka. Dama abinda ake gudu kenan, ba wai yin a lokaci daya ba, abinda zai je ya dawo bayan kayi. Kinga rana daya a rayuwata ta canja akalar komai nawa." Kuka suke yi duk su biyun Ainau tana bata hakuri "Ku zan bawa hakuri ma da na janyo ake yiwa tarbiyar da Umma ta bamu kallon gazawa. Don Allah kada ku bari taji wannan labarin. Shima Yassar din zanyi masa magana" Anti Bintu tana bakin kofar tana jinsu. Tausayin Asmau ta kara ji ta koma wurin maigidanta. Alfarmar kada su fadawa Yayarta tazo nema sai gashi Asmau tayi wannan tunanin. Sun dauki lokaci a dakin suna magana kafin su dawo falo bisa umarnin Kawu Yusuf. Rokonsu yayi da suyi hakuri da halin tsufa irin na mahaifiyarsa kuma yana fata zasu sake a gidan bazasu takura kansu a daki ba. Sai da suka yi sallah aka zauna cin abinci. Babu wata hirar kirki sai hayaniyar Amatullah. Kowa jikinsa a sanyaye yake. Ganin haka Asmau ta rinka dauko hira duk don ta nuna musu bata tare da damuwa. Su Yassar sun dawo daga masallaci inda suka yi sallar la'asar yace zai kama hanyar komawa. Anti Bintu ta tsayar dashi ya jira a kawo sako da take son ya tafiwa da Umma dashi. Yana zaune a falon Col. Ishaq yayi masa waya yana tambayarsa kwatancen gidan da suke zai zo ganin Amatullah. Yassar ya tashi tsaye cike da mamaki, sannan ya kwatanta masa inda zaije ya jirashi sai yazo ya kawo shi gidan. Anti Bintu ta tambayeshi ko lafiya ya sanar da ita bakon da zasuyi. Murmushi tayi "anya 'yar yazo gani ko uwar 'yar" "Nima tunanin da nake yi kenan Anti. Mutumin ba karamin burgeni yake yi ba. Idan yace yana son Yaya Asmau ai ya gama min komai. Wallahi binsa zan rinka yi sau da kafa". "To sarkin zumudi, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki" Anti Bintu ta fada amma itama tana fatan hakan ya tabbata. Dan ganin da tayi masa ranar da suka dawo da Asmau ta yaba dashi. "Bari kiga naje bakin layin kada yazo yayi ta jirana" "Ita yayar taku tasan da zuwansa?" "Kai bana jin ta sani, kyaleta kawai Anti kada ta bata lamarin. Ba karamin aikinta bane ta tura masa Amatullah taki zuwa su gaisa. Kuma ai kinga bai dace ba mutum yayi tafiya irin wannan saboda danka" Wannan karon dariya sosai ya bawa Anti Bintu. Lallai Yassar da yana da iko tuni zai bawa sojan nan auren yayarsa. Yana fita ta shiga ciki suna daki ana ta wanka saboda zafin gari. Ta tarar Asmau ta shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi shudiya ta yafa karamin mayafi fari a kanta. Anti Bintu tace ta taso ta tayata hadawa bako abinci don duk 'yan matan gidan suna Islamiyya. Tashi tayi tabi bayanta ta bar Ainau da yaran. Da yake akwai sauran abincin rana salad kawai ta sake hadawa ita kuma Anti Bintu ta hada zobo mai sanyi. Tray din abincin ta dauka ta shiga falo, ko tsakiyarsa bata kai ba taji sallamar Yassar da ta Jikamshi. Sai dai murya ta biyun ce tafi daukar hankalinta har ta daga kai suka hada ido. Sanye yake cikin kayan aikinsa da hularsa rike a hannu. Yayi kyau sosai. _Innalillahi wa inna ilaihi rajiun_ ta fada saboda tsabar kaduwar da tayi hannuwanta suna rawa tana neman sakin tray din a kasa. Wani irin kallo ya bita dashi yana wani kashe ido. Sai kuma ya karasa gabanta ya karbi tray din da yake tangal- tangal ta kasa rike shi da kyau. Sai da ya ajiye shi a kan centre table din falon ya sake dagowa yana kallonta kamar wadda aka kafe a wurin yace "Duk murnar ganina ce haka tasa kika kasa motsi?" Juyawa tayi bayanta taga Anti Bintu tana murmushi,daga bakin kofa kuwa Yassar ne bakinsa ya kusa zuwa keya don dadi. Ji tayi kamar ta make shi. Mamakin ganinsa ta yi sosai har ta kasa hada wata kalma a bakinta. Shi kuwa ba karamin dadi yaji ba da ya ganta. "Kinyi tunanin wasa nake yi da nace zan zo? Gashi ko wurin zama baki bani ba sai aikin daukar miki tray daga shigowata" Da sauri Yassar ya nuna masa kujera. Anti Bintu ta karaso ta zauna suka gaisa amma har lokacin idonsa na kan Asmau da ta tsaya kawai tana kallonsa. Bata taba kawowa da gaske zai zo ba kamar yadda ya fada a wayar. Ji tayi ya sake shiga ranta har abin yana bata tsoro. "Yaya hanya? Yassar na shirin tafiya yace ka shigo gari" Sai sannan ya maida hankalinsa ga Anti Bintu yana magana da alamar damuwa a fuskarsa "Waya muka yi da Ummin Safina sai naji kamar tana kuka kuma taki fada min abinda ya sameta. Shine kawai nayi deciding na taho don ko na zauna bazan iya aikin ba" _Subhanallah_ ta fada a zuci. Shi kuwa me yasa yake haka ne. Baya jin komai idan ya fadi magana a gaban mutane. Kallonta Anti Bintu tayi sai taji kunya. Kada tayi tunanin ko ta fada masa abinda ya faru ne. In'inar karfi da yaji ce ta kamata "Uhmmm...dama...da.....lokacin...kai" ta rasa karyar da zata yi ma. Shi kuwa ya zuba mata ido kamar bai san da mutane a wurin ba. Anti Bintu tayi gyaran murya don ta kula hankalinsa yayi gaba. Hasashensu ita da Yassar ya tabbata. Wannan kallo da yake yiwa Asmau indai ba na soyayya bane to bata san dame zata kwatanta shi ba. A iya saninta dai yasan komai game da Asmau shiyasa ta fada masa magana ce surikarta ta fada da batayi mata dadi ba shine dalilin kukan. Bata so aka fada masa ba tana tsaye a inda take tun dazu ta soma hawayen da ta rasa dalilinsu. Karshe ciki ta shige kawai ta koma daki. Sai da yaga shigewarta yace "ita Asmau haka take ne da saurin kuka? Na zata a yadda taga rayuwa by now ta zama jaruma wadda zata iya daukar duk abinda yazo mata" Yassar ya bi bayanta zai lallabata ta dawo wurin bakonsu don maganar komawarsa Kano yanzu kuma tabi iska. Anti Bintu tace "tun da can Asmau mace ce mai raunin zuciya. Faruwar wadannan al'amuran sun sa ta kara samun rauni dole ne sai muna binta a hankali har Allah Yasa ta iya sakin jikinta kamar da. Dazu munyi mata nasiha sosai akan toshe kunnuwanta game da irin wadannan maganganun da zasuyi ta tasowa" "Allah Ya kara rufa asiri. Kiyi hakuri I just can't help myself when it comes to Asmau" Tayi dariya "babu komai, mu hakan muke so ma. Allah Ya tabbatar mana da alkhairi" Da yake yasan bazata girmeshi sosai ba sai yayi murmushi "ko Yayata? Kada kice kin gano ni " "Na nawa kuma" tayi dariya. Sai ya rufe fuskarsa da hularsa "amma kuwa har naji kunya." Anti Bintu me zatayi banda dariya ta tashi "haka kake da abin dariya" Dan dakewa yayi shi a dole babu wasa "don dai kawai a gaban in-law nake. Amma ni serious mutum ne. Soja ai baya abin dariya" "Uhmmm naga alama, sai dai ban rike sunan wannan sojan ba" "Call me Ishaq" "To Ishaq kanina Allah Ya bada sa'a. Bari na turo maka ita. Ga abinci nan don Allah ka ci" Daga shi har ita dariya suke yiwa juna sannan yayi mata godiya ta tafi. Da taje dakin Yassar ta gani yana faman bawa Asmau dake kuka hakuri tana yi masa fadan me yasa ya kawo shi gidan. Ta shiga dakin ta zauna a gefen gado "bana son shirme Asmau, meye abin kukan ma. Idan mutum ya nuna kina da mahimmanci a rayuwarsa bai cancanci wulakanci daga gareki ba. Dan gyara fuskarki kije ku gaisa." Ta tashi zata shiga bandaki ta wanke fuskar Yassar yace "Antinmu kema kinyi mubaya'a ne. Naga kin shigo kina dariya" Ta kalli Asmau da ta juyo tana kallonsu " ina wasa da kai ne. Tashi ka bani wuri kazo ka zauna a cikin mata" fita yayi yana dariya kawai. Asmau ta wanko fuskarta ta fito "mubaya'ar me Yassar yake tambayarki?" Ainau da tun dazu bata saka musu baki ba tace "nima abinda zan tambaya kenan" "Ku kyale shi shashancia ne kawai" ta bagarar da zancen ta fita. Ainau tace "ko dai baban Amatullah yana ciki ne" "Kinga ki kiyayeni. Ya isheku daga ke har Yassar" Tana jiyo dariyar Ainau har ta kai karshen korido din da zai kaita falon. A zaune ta same shi yana waya ta zauna a wata kujerar daga can gefe. Yassar yana daga kusa dashi. Sai da ya gama yace "Yassar dan bamu wuri ina son siye zuciyar yayarka" Ya tashi yana dariyar da ta soma bawa Asmau haushi ita kuwa ta bata rai. Ya dan mike kafafunsa "yunwa nake ji" Fuskarta babu wata fara'ar kirki tace "ba ga abinci nan a gabanka ba" "Kince naci ne?" "Au sai nace?" Ya gyada kai yana murmushi wanda yasa ta dan saki fuska. "To ga abinci nan kaci" "Nagode" ruwa ya fara sha sannan ya bude plate din da aka hada masa abincin zai ci. Asmau ta tashi "bari na baka wuri kaci abincin" "No yi zamanki please" Kasa kallonsa tayi yana cin abincin. Shima kadan yaci ya rufe plate din. Haka yake abinci bai dame shi ba. "Asmau kalleni nan" Dan kadan ta iya daga kanta ta dube shi "Ina so ki zama jaruma mai hakuri da dukkan abinda zata ji ko ta gani a wurin mutane. Babu wani abu da bazai wuce ba a duniya saboda haka yawan zubar da hawaye akan magana ba naki bane. Ke uwa ce dole ki jajirce wurin zama macen da ba raguwa ba ko don kada 'yarki tayi koyi da hakan" Yana magana ta soma hawaye har ya kai karshe. Girgiza kansa kawai yayi "Don nace ki rinka barin kukanki kiyi a gabana shine zaki yi kuma. To share hawayen ko na share miki da kaina" Habar mayafinta tasa ta goge hawayen da sauri "Ko ke fa...yanzu ace nazo tun daga Kano amma fuskarki duk a kode" Ta dan turo baki "don zaka zo sai nayi kwalliya?" "Sosai ma kuwa, ko ba kya so ki kara samun karbuwa ne. Yanzu haka zan kama hanya har na koma gida kodaddiyar fuskar nan zanyi ta gani. Da na sani driver nasa ya kawoni" Asmau tace "nifa..." "Ke fa me? Kinga mu bar wannan zancen sai kin koma gida. Wai ina princess dina ne banganta ba" "Sai yanzu ka tuna da ita? Tayi bacci" Ya kwantar da kansa a saman kujera "duk laifinki ne. Kin wani kasheni da ido kinsa bana tunanin komai sai naki. Kije ki tasheta magriba ta kusa kada ki koya mata baccin yamman nan" Asmau ta tashi tana tafiya tana waigensa. Duk juyawa sai yayi mata murmushi sai ta kawai da kai. A na ukun ta kusa karo da bango ya soma dariya "yi a hankali ba yanzu zan tafi ba sai kin koreni da kanki" A kunyace ta shige tana mamakin yadda ya gama da zuciyarta cikin dan kankanin lokaci. ****** Bayan tahowarsu Mama Yalwa taje gidan Umma. Suna zaune harda Hajjo take fada musu yadda suka yi da Qasim a daren jiya kafin ya tafi da kuma amsar da Asmau ta bashi. Hajjo tace "ki ji min yarinyar nan fa. Ita banda abinta ai ba saka mata ido zamuyi ba. Kuma yaron nan Qasimu ya cancanci yabo wallahi. Bari ta dawo muyi magana amma aure ai shine rufin asirinta." Umma tace "nima na yaba da halayensa sosai. Nasan duk abubuwan da take tunani har yasa take tsoron yin aure. Amma ko kadan ba hujja bace. In sha Allah zamuyi mata magana. Ni kaina ban hango mata rufin asiri ba kamar a gidan Qasim. Allah Yayi masa albarka". "Amin" Mama ta amsa. "Kar kiso kiga yadda naji dadin labarim nan. Yarinya ce mai biyayya nasan bazata watsa mana kasa a ido ba. ***** Da yamma ne bayan tafiyar Mama Anti Bintu ta kira Umma tana bata labarin zuwan Col. Ishaq da hirar da suka yi. Cike da murna tace "Yaya Bara wallahi na yaba da yadda ya damu da Asmau. In Allah Yaso shine zai share mata hawayen dukkan damuwarta." Umma bata iya bata amsar kirki ba saboda tunani da ta shiga yi akan maneman 'yarta. ABINDA AKE GUDU🙆🏽36 Batul Mamman💖 Ba karamin damunsa rashin daukar wayarsa da Asmau take yi yayi ba. Sai dai kuma ya kuduri niyyar bazai barta ba. Murmushi yayi....yana son mace mai jan aji, amma bazai bari ta ja masa aji da yawa ba saboda yadda yake ji da ita a zuciyarsa. Har mamakin kansa yake yi. Bai yarda sonta yake yi har haka ba sai bayan 'yar hirarsu ta dazu. Yana son muryarta, kunyarta, yanayinta....ya dan shafa kansa yana murmushi ya tura mata da text "Asmau Ummin Safina ki shirya, don Jikamshi da gaske yake. Kiran wayarki kuma yanzu na fara. Gudnyt" ***** Hannunta har rawa ya soma bayan ta karanta text din. Wani abu taji ya ratsa jikinta gabadaya don dadi. Bayan Abubakar bata taba tunanin sake jin wani abu makamancin wannan akan kowane da namiji ba sai akan Col I.M Jikamshi. Sai dai kuma wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa. Yaudarar kai ne ma ta yarda wani abu yayi nisa tsakaninsu. Tafi kowa sanin ko ita wacece, bata cikin mata da zasu sami rabon aure a wannan duniyar. Dadin dadawa Jikamshi ba karamin mutum bane. Yana da wata kima ta daban a idonta, sam bazata so suyi rabuwa mara dadi ba. Gara tun ba'a soma ba kada a fara. Tana wannan tunanin ne bacci ya kwasheta. Washegari Umma ke fada mata su fara shiri nan da kwana biyu zasu tafi Zaria da Aina'u. Sati daya zasu yi daga nan zata zo ta same su su wuce Wushishi. Jin zata je Zaria wurin Anti Bintu yasa ta farinciki har ta dan manta da tunanin da ta kwana ta tashi dashi. Shirye shirye suke yi daga ita har Aina'u sun hada kayansu da komai. Yassar ne zai kaisu ya dawo washegari. Da yamma ne ta tafi gidan Jafar saboda yace yana son ganinta tace ya bari zata zo da kanta. A gida ta bar Amatullah tana bacci. Sun dan taba hira da Sabira ta tashi ta basu wuri. Ba wani dogon abu bane maganar karatu yayi mata wanda yace sunyi shawara ne da Shemau zasu hada kudi su biya mata ta koma makaranta. Kuka take yi sosai kamar yasan abinda take son yi kenan. "Yaya Jafar Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai, nima abinda yake raina kenan don bana son nayi ta zaman haka." "Kada ki damu Asmau. Ina so ki manta da rayuwar baya kiyi kokarin gina rayuwa mai kyau daga yanzu. Kada ki manta ko ke wacece a duk inda kike. A yanzu da kika dawo gida inda mutane suka sanki suka san labarin rayuwarki ki zauna da shiri na fuskantar kalubale kala kala. Dole duk inda kika shiga kiji maganganu marasa dadi daga bakin mutane daban daban. Abinda nake bukata daga gareki bai wuce ki toshe kunnuwanki ba. Komai yayi farko yana da karshe. Ki mayarda dukkan lamarinki ga Allah sai kiga kinyi nasara." Tayi murmushin takaici "hakane, kuma nagode da shawararka. Dole ne nayi hakuri da dukkan abinda mutane zasu ce game dani da Amatullah. Irin labarinmu dai da wuya yake zama tarihi. Duk wanda ya sanmu duk sanda muka hadu sai sun tuna. Wannan kaddara har jikoki idan da rabo nasan za'a goranta musu wata rana" ta kare maganar da kuka. Tausayin kanwarsa yaji sosai. Ya dade da sanin cewa illar zina tana bibiyar mutum duk inda yaje. Musamman idan akwai haihuwa tsakani. Fatanmu kawai Allah Ya tsare mana imaninmu Ya karemu daga fadawa sharrin shaidan da mukarrabansa. "Ki tsarkake zuciyarki Asmau, daga nan ki barwa Allah komai. Rayuwa ce kowa da irin tasa. Babban abin dubawa dama shine tuba da komawa ga Allah. Idan kika yi haka to babu ruwanki da zancen mutane. Duk wanda ya fiye bibiyar kuskuren dan uwansa don tonon asiri to Allah na kallonsa kuma Shine Yasan yadda zaiyi da bayinSa." Godiya ta sake yi masa har ta kira Shemau tace zata je har gida tayi mata godiya. Dan uwa rabin jiki inji bahaushe...banga mai kamarka ba. Abinda suka aikata ita da Abubakar ba su kadai yake bi ba domin kuwa tasan za'a nuna iyayensu da 'yan uwansu idan dalili ya kawo suma a goranta musu. Kai zina laifi ce mai muni, kazanta ce mai kaskantar da mai daraja. Ya Allah Kasa mufi karfin zukatanmu. Masu neman aure maza da mata Allah Ka basu abokan rayuwa nagari. Mu kuma Ka bamu zaman lafiya da wadanda Ka hadamu dasu. ***** ASP Qasim zaune gaban mahaifiyarsa ya gabatar mata da zancen Asmau wanda ta dade da sanin kudurinsa akai. "Baba ni bazan hanaka aurenta ba. Babanku ma yace ya amince da auren. Abu daya nake so da kai shine ka tuna dukkan abubuwan da suka faru. Naso kwarai kayi aure kafin yanzu ta yadda ko ka auri Asmaun zaka hadata da wata matar" "Inna kenan, kina gudun ita kadai ta kasance surika a gareki saboda tana da 'ya kafin tayi aure?" "Dan nan yau da gobe sai Allah. Mutane da bakinsu bazasu fasa surutu ba" "Amma Inna nasha fada miki ina gudun zamansu da kishiya yaki dadi saboda gori. Da bata dawo ba kamar yadda kika bukata a shekarar nan zan nemi aure. Ku cigaba da yi mana addua." Ta kada kai "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi. Haj Yalwa tace zata zo dasu su gaishe da Malam. Allah Ya kiyaye hanya" Qasim ya tashi ya leka dakin mahaifinsa har lokacin bacci yake yi. Shiryawa yayi cikin wani yadi mara nauyi ruwan toka yayi kyau sosai ya kama hanyar Kano daga Shanono. Ana magariba ya iso. Gidan Mama ya fara zuwa suka gaisa sannan ya kira Asmau ya fada mata zai zo idan an idar da sallar isha. Umma taje ta sanarwa. "Allah Sarki Qasim, gaskiya ya rike amana. Ji yadda yake kokarin kula daku duk da ba a garin nan yake aiki ba. Allah Ya biya shi da mafificin alkhairi." Asmau ta amsa da amin tana gyara goyon Husna da tayi. Suna cikin hira Qasim yayi sallama Umma tayi masa izini ya shigo. Cike da ladabi ya gaisheta ta amsa fuska a sake. Daga nan ta tashi ta bar falon ta koma dakin Hajjo. A nan ta sanar da Amatullah zuwan Qasim daya baban nata ta fito gaishe shi. Qasim ya ajiye kofin lemon dake hannunsa yana maida hankalinsa Asmau. "Asmau magana nazo muyi, ina fata zaki saurare kuma ki fahimceni." "Ina jinka Yaya Qasim" "Asmau kinsan irin shakuwa da abotar dake tsakanina da marigayi Abubakar" Ta gyada kai tana tuno masoyin da bazata taba mantawa ba a tarihin rayuwarta. "Duk abinda ya gudana a rayuwarku na sani na kuma san nima akwai sa hannuna a ciki. Bazan gaji da rokon gafararki ba saboda ance karfe daya baya amo. Kamar yadda kawa ta ribaceki haka nima nayiwa Abubakar, ga kuma sakamakon hakan duniya ta gani. Asmau tun kafin ki dawo na yanke shawarar aurenki ko a wane yanayi na sameki. Cikin ikon Allah yanzu na tsinci kaina da tsananin kaunarki" A razane ta dago kai ta kalleshi ta mayar da kanta kasa. Yayi sassanyar dariya "Nasan dole kiyi mamaki sai dai kuma ki sani burina ba wai na maye gurbin Abubakar bane. Ina so ki bani dama a matsayin masoyi na sami kaunarki na kuma zama uba ga 'yata Amatullah." Wannan shine ana wata ga wata. Ita fa ko kadan bata son maganar aure ma yanzu. Qasim wani babban jigo ne a rayuwarta saboda yadda ya damu da lamarinta da na Amatullah. Ya rike amanar Abubakar ba da wasa ba. "Yaya Qasim bani da abinda zance maka sai godiya da fatan alkhairi amma don Allah ka janye maganar aure a tsakaninmu. Maganar aure ba ta mace irina bace. Duk yadda zan so bani da wani mutumci da kima da zan kai gidan aure. Amatullah ko naki ko naso 'yarka ce amma don Allah mu bar maganar aure." Dama yasan da wuya ta amince kai tsaye. "Ba cewa nayi ki bani amsa yanzun nan ba. Zan baki lokaci kiyi tunani. Amma ki sani kamar yadda aure yake zama garkuwa ga kowace mace kema shine mutumcinki. Zamanki a haka shine zai janyo miki duk abinda kike gudu wato surutun mutane." "Ni dai....." Hannu ya daga mata alamun tayi shiru ya tashi tsaye "kiyi tunani nace kuma kiyi shawara da duk wanda kika san zai baki shawara tagari" Rasa abin fada tayi kawai ta sanar dashi batun tafiyarsu a washegari yayi mata addua sannan yace zai zo idan ta dawo yasan lokacin tayi duk wani tunani da zata yi. Bayan tafiyarsa Asmau ta shiga tashin hankali. Ko zata yi aure ba dai da Qasim ba. Idan ta amince tamkar taci amanar Abubakar ne. Kana ganinta kasan tana cikin damuwa ta tafi daki da niyar kwanciya wayarta ta soma kara. Sai da gabanta ya fadi da taga sunan mai kiran. Kwana biyu tun ranar da taki amsa wayarsa bai kara kiranta ba sai yau. Zuciyarta ce ta rinka bugu da sauri da sauri amma ta kasa amsa kiran. Text taga ya turo mata _Idan Safina batayi bacci ba ki hadani da ita. Taki muryar ma ina son ji amma ba a waya ba, so wayar ba taki bace._ Wani dan murmushi ne ya subuce mata. Sai kuma ta dan dake tana yiwa zuciyarta tuni da cewar ta manta da maganar aure. Babu wani namiji da zai aureta a yanayin da take ciki komai tsahon lokaci ace wata rana bai goranta mata irin rayuwar da tayi a baya ba. Dakin Umma taje ta bawa Amatullah dake aikin wasa da Husna wayar da ya sake kira. Kusan minti ashirin tana ta yi masa hira sannan mikawa Asmau. Da ta karba sakawa tayi a kunnenta tayi shiru tana so taji ko ya ajiye. Yanayin yadda take saukar da numfashi ne ya tabbatar masa ta karbi wayar. Murmushi yayi kamar tana kallonsa yace "Ana so ana kaiwa kasuwa" Da sauri Asmau ta kashe wayar tana dariya. Me ya kaita saka wayar a

Chapter 13 of 23