Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Asmau yayi tunda ta zauna. Itama yayi mata kyau sosai domin kuwa korayen kayan sojoji ne irin wanda suke sawa lokutan taro a jikinsa. Sai yau ta kara jin soja yayi. Fuskar nan tasa ya gyara saje ya kara haske da kyau. Ji yayi inama daga wurin dinner sai gidansu. Ya mika hannu mai sanye da farar safar hannu mai santsi zai riko nata da yasha lalle suka ji kukan Amatullah. Kuka harda ajiyar zuciya wai Umminta da Babanta zasu tafi su barta. Ana ta rarrashinta akan suma can zasu je yarinya taki amincewa. Col. Ishaq yace a miko masa ita. A tsakiyarsu ta zauna ta hana ruwa gudu don har suka isa wurin surutu kawai take yi. Gata a tsakiyar iyayenta duniya tayi mata dadi. Da suka je wurin ya fara cika. Duk masu cewa zasu sword crossing dinnan kowacce ta je. Gashi dai card admit ne amma haka wurin ya cika sai san barka. Iyaye ma ba'a barsu a baya ba. Hajjo da Yaya tagwai ma duk tsufansu sunce basu taba ganin bikin sojoji ba dole ne ayi dasu. Tare da sauran yara aka hada Amatullah sannan MC ya sanar kowa ya zauna ango da amarya zasu shigo. Yace a zauna ne saboda a tsaye dogaye zasu karewa marasa tsaho. Duk sojojin wurin cikin uniform din occassion suke. Dole su burge mutane. Sannan babu hargitsi don biki ne na manyan kasa da kowa baya son tsokano su. Layi ne sojoji suka yi hagu da dama mutum goma goma. Kowanne ya rike hularsa a hannu daya sannan suka hada takubbansu ta sama inda amarya da angi zasu wuce. Kida ne mai taushi yake tashi aka umarci amarya da ango da su taho su wuce. Babu masu daukar hoto ta waya don ance kowa ya zauna. Masu daukar hoto biyu ne kawai wadanda aka hayo su suke binsu. Sun zo inda zasu shiga karkashin takubban hularsa na makale a hannunsa ya lankwasa hannun damansa yayi mata alama da ta rike. Duk da tana jin kunya haka ta zura hannunta ta cikin nasa suka fara tafiya. Jama'a kuwa sai tafi har suka wuce suka zauna. Duk taron da akayi da tsari dole ya bada sha'awa. Irin wannan taron akayi a bikin Ishaq da Asmau. Tana daga mazauninta ta hango Qasim table dinsu daya da Ma'u suna ta hira. Ta nunawa Jikamshinta yayi murmushi "Allah Yasa shima tashi Asmaun mace ce tagari kamar tawa" "Amin" ta amsa tana 'yar dariya masu hoto suka sami na yi. Yaya Tagwai tace da Hajjo "wai ku a bikin Kano tsufaffi basa takawa ne? Tunda muka zo kidin yara ake sakawa suna ta rawa." Hajjo tayi dariya sosai sannan ta yafito Yassar da hannu tace aje a saka wakar da zasu iya takawa kuma a fada filin nasu ne tsufaffi. Ango da amarya dole su sauko. Yassar ya rinka dariya yaje ya fadi sako amma don shakiyanci wakar da yace a saka bata dace da Yaya Tagwai da Hajjo ba da sauran irinsu masu kashin kafa yayi laushi. Sai da suka fito tsakiyar fili ga ango da amarya kawai aka soma wakar Uban Duma ta Ali Dawayya. Hajjo ta karkace itama Yaya Tagwai ta gotar da kafa daya zasu fara taku suka ji sautin yafi karfinsu. Kunnen Yassar ta jawo yace "wallahi Hajjo tsohuwar waka nace ya saka kuma ita ya saka." 'Yan taro suna ta dariya Yaya Tagwai ta gwangwaje abinta. Ango ma sai gashi yana juyi da abokai. Asmau dai kunya ta hanata rawa sai dariyar tsufaffi dake cikinta. Iyaye ma sunyi tasu da amarya da ango asa ta turanci asa ta hausa. Da taro yazo karewa su Hajjo sunyi hanyar fita aka saka Mata ku dau turame. Dafa juna sukayi ita da Yaya Tagwai suka koma fili suka sha rawa. Su Ainau sun sha dariya kamar cikinsu zai kulle. Hajjo tace ita ba don amarya tayi ba. Dole ta taka idan aka ambaci sarki. Sai wuraren shadaya da rabi wurin yayi saukin mutane anata tafiya gida. Col. Ishaq ya dubi Asmau wadda duk ta gama gajiya. Ga tsinin takalmi. Drebansa yace ya bashi key din mota ya bi wasu ya tafi gida. Abokinsa da suka zo tare yana wurin yace "ango duk tsiyarka fa tare zamu tafi. Naga kana sallamar dreba nasan ni zan biyo baya. Kasan Mami...." "Mamo ba Mami ba. Ka fita idona Captain. Wai Baraka ba tazo ba. Don Allah ka dauketa ku tafi dare yayi" Saluting dinsa yayi yana kyakyata dariya. "Na barku lafiya angon Asmau." A can gefe daya kuma su Mami ke neman Bilkisu a tafi gida an rasa inda tayi. Tana can ita da Yassar a wurin wasu kujeru. Abinci yake ci yunwa ta dame shi yaji sallamarta. Har kusan kwarewa yayi don baiyi zaton ganinta ba. Tayi murmushi ta zauna a kujerar dake kallon tasa. Yassar ya ajiye cokalin yana kallonta. Tace "ci abincinka mana" "Bazan iya ba. Ni bana iya cin abinci a gaban mutane shiyasa ma kika ganni a nan yanzu" "Ni kuma kaga so nake kullum ka rinka ci a gabana" Sauran abincin bakinsa ne yasa shi kwarewar da yake gudu da yaji abinda tace. Tayi masa sannu amma tarin yaki tsayawa. Da tayi magana sai ya sake yin tari. Bilkisu ta dan harare shi "dama saboda ni kake tarin? To aiki ya sameka don bazan dena yi maka magana ba" Yassar ya rasa me zai ce mata. Haka yake da kunyar mata tuntuni. Babu wanda zaice ga budurwarsa. Ta dan sassauta kallonsa tace "ni na gaji da kallon kallo da muke yi fa, sai yaushe zaka ce kana sona?" Wannan karon da ya fara tari har sai da ya sauko daga kan kujera. Yana dafe da kirji tana yi masa sannu yace "ke haka danginku suke ne, basa jin kunyar magana" Turo masa baki tayi "to ba wani bane a cikin 'yan biki yace yana sona ba. Kuma har cewa yayi zaiyiwa Uncle magana shima soja ne a karkashinsa yake" Yassar ya ware ya koma ya zauna yana kallonta babu zancen wasa "don Allah kada ki amsa masa. Nima zanyi sojan nan har Yaya Ishaq ya karbo min takarda zanyi short service" "Uncle Ishaq nake ce masa fa" tana magana kamar zata yi masa kuka Duk ya rude da tayi zancen wani soja yace "to nima Uncle Ishaq kinji" Ta juya masa ido "to kana sona kenan na sallami wancan" Kai ya sunkuyar kasa da gaske kunyarta yake ji ya gyada kai a hankali. "Ni da baki zaka fada" "Kiyi hakuri zanyi miki text ko na kiraki" Shan kunu tayi "zan cewa wancan ya turo kawai" Yassar ya sake rudewa "me yayi zafi kiyi hakuri. Ina sonki mana ai ko ban fada ba kin sani" Sai yanzu yaga alamu taji kunya ta rufe kuskarta da mayafi ta tashi "bari naje nasan ana jirana. Don Allah ka kirani fa" Yayi murmushi "in sha Allah ina zuwa gida zaki ji wayata" Sai da ta soma tafiya ta dan daga murya yadda zaiji tace "Yassar" Ya juyo yana kallonta "dama karya nake yi, so nake kawai kace kana sona" daga haka ta tafi. Ya zauna yana sosa keya. Yana tunanin ko dai soyayya a jinin dangin Jikamshi take. Tasha fada kuwa a wurin Mami. To bukatarta ta biya ko kadan ranta bai baci ba. ****** 'Yan uwan Asmau sunyi gaba da harda yi mata tayin ko zata bi motar Umar tunda Ainau ce kawai a ciki. Col. Ishaq ya jefi Shemau da kallo harda harara ta kwashe da dariya. Dama tsokanarsa tazo yi. Sai da yayi sallama da abokansa sannan yazo ya sameta a inda yace ta jira shi. Jikinta yayi sanyi tunda taga ya sallami 'yan motar tasu. Har wani dan tsoronsa take ji. Ya kula da canjin yanayinta a ransa yace baki ga komai ba. Hannunta ya kama ya tayar da ita suka nufi wurin motar yaki sakin hannun. Wani iri take ji daban don bata saba ba. Idan ba bisa lalura ba tana iya rantsuwa banda Abubakar babu wani namiji da ba muharraminta ba da ya taba mata hannu. Shima jin hakan yake har ransa. Ya dade yana jiran ranar da Asmau zata halatta gareshi ya tabata batare da tsoron zunubi ba. Sai ma lada da zai biyo baya. Gaba ya bude mata ta zauna sannan ya zagayo ya zauna wurin dreba. Ya tayar da motar sannan ya kamo hannunta ya dora akan giyar. A haka ya saka giyar ya soma tuki cikin nutsuwa. Zuciyar Asmau ta kusa ballo kirjinta don tsoro. "Tunanin me kike yi ne" Ta dan rufe idonta ta bude "babu komai" muryar nan a salihance take fita. "Are you sure, har tunanin abinda zan iya yi miki daga nan zuwa na kaiki gida bai zo kanki ba?" Ta shiga kifta idanu kamar mara gaskiya. Saboda dare ne kuma titin babu motoci sai tsiraru shiyasa yake iya kallon bangaren da take. "Kinyi shiru, bari na fada miki abinda naji zuciyarki tana cewa" Kallonsa tayi tana jiran taji abinda zai ce. Shima sai da ya dan juyo sannan ya mayar da ido sa ga titi. "Zuciyarki tace yau dai gani ga Jikamshina a matsayin maya da miji. Daga nan zuwa ya kaini gida zanyi kokari ko kiss ne nayi masa" "La'ila ha ilallahu, ni banyi wannan tunanin ba..." Asmau ta fada tare da cukwikuye kanta cikin mayafinta. Kunya taji har bazata iya misalta ta ba. Shi kuwa dariya yake mata. Yana son wannan kunya ta Asmau. " ko kwana daya bamuyi da aure ba har kin fara karyata ni?" Ta dan dago kanta daga kan cinyarta da ta rufe "ba haka nace ba fa" Nishadi kawai yake ji gashi ga Asmai a matsayin maaurata. Ya daga gira daya "to yaya, kin amince kinyi wannan tunanin?" Ta soma girgiza kai sai taga ya bata fuska. Tayi saurin cewa "Allah Sarki banyi ba amma dai naji nayi tunda haka kake so nace" "Good girl, that means I will get one kafin mu rabu yau." Ta turo baki don ta san idan ta sake magana wani abin zai kuma fada. A hakan ma bata tsira ba ya kalli dan bakin ya sha janbaki "Mayar da lips din mana, ai ba yanzu za'ayi ba sai mun isa gida. Naga alama kin fini zumudi". Kwafa tayi tana tunanin me zatayi masa, tukinsa yake hankali kwance. Tace "Jikamshina" "Yes sweetheart. Kinsan fa yanzu duk wani suna da ake kiran masoyi a duniya zan kiraki dashi" "Zan rama ne." Yayi dariya "dama haka nake so. In ce wani abu ki rama yanzu?" Ta gyada kai "I want to hug you" Ta bata fuska a shagwabe "wallahi zan maka kuka" Ya sami abinda yake so. Tana jinsa yana dariya ta ja mayafi ta rufe fuska har suka isa gidan Jafar. Yaron makota da yake masa gadi ya bude ga motarsa nan alamun sun dawo. Ta kama kofa zata bude taji ta a rufe. Yace mata "Kiyi hakuri kiyi min magana please" Ta noke kafada, ya ce "to shikenan ina zuwa. Umarni na baki kada ki bude kofar nan" Itama nata salon ramawar kenan yau duk abinsa bazata yi masa magana ba har ya tafi. Tana kallo ya bude ya fita ya zagayo ta gefenta ya bude mata. Sai da ta ziro kafafunta waje kawai ya durkusa a gabanta ya kafa kafar ya cire mata takalma yana bin yatsun kafar yana matsawa. Kasa magana tayi saboda bata yi zaton abinda zaiyi mata ba kenan. Ga kunya kamar tayi ihu. Har fargaba take kada wani ya fito ya gansu. Ta dan ja kafar ya rike sosai ya cigaba da matsawa yana magana a hankali. "Tun dazu kike dingishi kina tunanin zan bari ki shiga ciki ne kice wata tayi miki tausa a kafa?" "Don Allah ka dena kada yaya Jafar ya fito" tana magana idonta na kan kofa. "Matsoraciya bari kiga wani abu" bata ankara ba taji yayi mata daukar jarirai. Abinka da dogon soja tashi yayi ya nufi hanyar kofar gidan da ita. Asmau ta gama tsurewa ga tsoro tasa hannuwanta biyu ta kankame masa wuya "Ji...Jikamshi don Allah ka saukeni" "Anki din, ki sassauta rikon nan kin shake ni" Ta dan marairaice "idan aka fito aka ganmu fa" "Zaki sa na shiga dake har dakin da kike kwana idan bakiyi shiru ba" Shirun tayi don kada ta kara tunzura shi. Kanta a wurin kafadarsa ya cigaba da tafiya ta lumshe idanu. Komai nasa daban yake mata. Aure dadi aure lada yau ba tsoron fada take yi ba idan da wani zai fito ya gansu. Ko waye sai dai taji kunyarsa sabanin da wani namijin ne kawai da babu aure a tsakaninsu. Taji tsoron a kamasu sannan ta hada da lodin zunubi. Allah Ya kara karemu daga soyayyar tabe tabe babu aure wadda wasu suke yiwa kallon burgewa. Tunaninta ya katse da taji ya ajiyeta a bakin kofa sannan ya bata takakmanta. Ya daidaita fuskarsa da tata ta hanyar rankwafowa ya rage tsaho suna jin numfashin juna. Idonta a rufe don fargaba. "Ina jin na cancanci wannan kiss din da kika yi tunani dazu" Bata bude idon ba taji ya hada bakinsa da nata. Alhamdulillah cikakken farinciki yana tare da aure. Da da yanzu ta kwatanta sai taji yanzu duk da tana jinta kamar akan kaya kada wani ya fito kuma shima tana jin kunyarsa amma yanzu ne hankalinta ya kwanta. Yanzu ne taji nutsuwar kasancewa da namiji-mijinta. Ya dan dago kansa yana karewa fuskarta kallo kamar kada ya barta yace "saura ladan nauyi da na sha" . Tar ta bude idon "gaskiya bani da nauyi" "Ba kiji yadda zuciyata ke bugu bane da na daukeki." Ya dora hannuta daidai kirjinsa ya sake kissing dinta. "Ke dai ba na nauyinki bane, tsabar dadin kasancewa dake ne. Ba don ina jin kunyar Umma ba sai dai a biyoki da kayanki gobe" Kunya tasa ta kasa kallonsa. Ya rungumeta sosai a kirjinsa zukatansu na kara son juna "yau zanyi bacci mai dadi Matar Jikamshi. Ina fata kema zakiyi. Sai gobe idan mun hadu a dakinki" a goshinta yayi mata wani kiss din ya tafi ya barta a tsaye tana numfashi da kyar.ABIN DA AKE GUDU Na Batul Mamman Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 23 of 23