Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kunnenta ne. Umma tace "ke lafiyarki kuwa?" Tayi saurin daidaita kanta. Yanzu fa ta gama cewa babu zancen aure a sauran rayuwarta. Me yasa take jin wani daban idan al'amarin ya shafi Jikamshi. ***** Col. Ishaq yana zaune ya saka abinci a gaba bai ci ba ya soma wayar. Dariyar da yake yiwa Asmau ce tasa Hajiya kallonsa. "Yaya dai kake dariya kai kadai? Kwana biyu na fuskanci wani nishadi kake ji." "Hajiyata babu komai" abincin yaci dan kadan ya sa Bilkisu ta kwashe kwanukan. Wai shine tunanin mace ya mayar haka. Abin da mamaki, duk dakiya irin ta soja yanzu baya jimawa sai Asmau ta fado masa. ****** Da wuri suka tashi aka karasa shiri saboda Yassar yana son dawowa a ranar. Kafin karfe goma na safe sun hau hanya bayan sun biya gidan Mama sunyi mata sallama. Aina'u tana gaba Asmau na zaune a baya da baby Husna da Amatullah. Sunyi nisa Qasim ya kirata. Har kunya taji saboda yace ta kirashi kafin su fito taki kira, a cewarta kada ta sa masa rai yayi zaton zata amince nan gaba. Adduar neman tsari yayi musu sannan ya gaisa da Amatullah. Ba dadewa kuma Col. Ishaq yayi mata text. Lokacin bai dade da shiga office dinsa ba. _Zan kira ki yanzu ki fara dauka kafin ki hadani da princess dina._ Ya zata yi ne da Jikamshi. Duk irin wannan abubuwan da yake yi mata kara kashe mata jiki yake yi. A daya bangaren kuma tana ganin gangancinta da har ta bari yake tasiri a zuciyarta haka. Idan har aure ya zama dole a kanta ma bashi ya kamata ta aura ba. Qasim yafi kusanci da ita, yafi sanin dukkan matsalarta. Amma Jikamshi shine a ranki zuciyarta ta tuna mata kafin wayar ta fara ringing. A kasalance ta daga wayar ta kara a kunnenta kamar tana jin tsoron amsawa. Shi kadai ya sauke ajiyar zuciya da yaji ta dauka. "Just wanted to let you know how much I miss you." Muryarsa da komai nasa daban take jinsa. Ga wani girmansa da take gani a kullum. Lumshe ido tayi batare da tayi koda gyaran murya ba. "Idan kin janye yajin aikin yi min magana ki fada min zan zo na ganki. Ina Princess dina?" Mika mata wayar tayi ta fara bashi labarin tun dazu suke cikin mota suna ta tafiya. Ina zasu je da safen nan ya tambayi kansa. Sai kuma ya tambayeta waye yake tuka motar tace Uncle Yassay ne. Yana son jin inda zasu je amma kuma baya son tilasta Asmau tayi masa magana. Karshe yace tace masa ya kirashu idan sun tsaya. Bata ajiye wayar ba ta fadi sakon. Yassar yasa Ainau ta danna speaker a wayar. Gaisawa suka yi ya fada masa inda zasu je. Col. Ishaq yace to a kula masa da 'yarsa. Sai da ya ajiye wayar ya hau tunanin ko kwana nawa zasuyi. Kwana biyun da baiji murya ko yaga Asmau ba baya jindadi. ***** A gidan Anti Bintu yau tun safe suke kitchen ita da 'ya'yanta. Yadda kasan bata ga Asmau ba bayan dawowarta haka take ji. Maman mijinta Kawu Yuduf tana gidan ana gyara a nata gidan. Tun da taga suna aikin nam take tabe baki tana kananan surutai. Bata tashi yin magana sosai ba sai da taji tsayuwar mota taga duk sun fita tarbarsu Asmau. Suna shigowa ta ganeta don dama ta santa. Yar tsohuwa tace "Yanzu duk wannan doki da murnar na ganin shegiya ne da uwarta, banda lalacecar zamani yaushe 'ya zatayi zina sannan a rinka rawar jiki don ta dawo kamar wadda tayi wani abin arziki" Anti Bintu ta rasa me zata ce don tsabar kunya. Asmau kuwa tuni ta soma zubar da hawaye. Babbar 'yar Anti Bintu da ake shirin aurarwa bata rai tace "haba Gwaggo" "Wane irin haba, barni nayi magana son raina. Ba 'yar zinar bace ko kuwa uwarta bata bar mata abin kunya ba na 'ya'ya da jikoki?" Ba Asmau ba hatta Aina'u sai da tayi kuka. Allah Ya rufa musu asiri ma Kawu Yusuf yana gidan ya fito daidai sanda babarsa ke yabawa Asmau maganganu. "Gwaggo me ya kawo wannan maganar kuma. Kaddara ce wacce bata wuce kan kowa" "A'a wallahi irin wannan kaddarar sai 'ya'yan da basu da tsayayye a kansu. Nawa jikokin Allah Ya tsare min su. Kowacce zata kai budurcinta gidan miji" Kuka wiwi Asmau take yi. Kukan nata ba don abinda Gwaggo ta fada bane ai duk abinda tace gaskiya ne. Gaskiya kuwa akwaita da daci. Lallai sun tafka babban kuskure a rayuwarsu kuma muddin tana numfashi tasan wannan abu bazai taba gogewa daga zukatan mutane ba. Mutumci madara ne idan ya zube ba'a taba iya kwashe shi gabadaya. Anti Bintu ta kaisu dakinta tana ta rarrashi da bata baki. Yassar ya kasa zama ya fice ya koma mota rai a bace. Allah Kadai muke yiwa laifi yafe mana baki daya amma indai dan adam ne to a kowane lokaci ya sami dama sai ya tuna mana da laifinmu ko da bisa kuskure ne. Hakika shaidan dole yayi murna idan yaci galaba ya sanya mutane suka aikata zina domin tabonta baya taba kankaruwa a duniyar mutane dai. Yassar na zaune ransa sai suya yake. Ko kadan abinda aka fadawa yayarsa baiyi masa dadi ba. Mutane basu san laifi indai Allah akayiwa kuma aka tuba Shi mai yawan gafara ne da jinkai. Yamadidi da mai laifi bashi daga cikin kyawawan halayen musulmi. Tsaki yayi ya dauki wayarsa ya kira Col. Ishaq dama ya karbi numbar a wurin Asmau. Ya sanar dashi sun iso lafiya sai dai tuni ya gano akwai abinda yake damun Yassar din. Yayi ta tambayarsa me ya faru ya dage babu komai. Hankalinsa ne ya tashi ya kira Asmau. A lokacin Anti Bintu har da mijinta sun gama bata baki sun fita akan sai tayi hakuri domin zata yi ta cin karo da irin haka. Tana ganin wayar batayi tunani komai ba ta dauka. Wannan muryar mai dadi taji yace "Ummin Safina" Fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya wanda ya sashi saurin tashi daga zaman da yayi. "Asmau me ya ya sameki?" Shasshekar kukanta ya cigaba da ji ya sake kiran sunanta har lokacin bata amsa ba. Hankalinsa a tashe yace "Asmau please ki amsa mana" "Naam" ta fada cikin muryar kuka. To me aka yi mata haka?duk yadda akayi abin ya shafi 'yan uwanta tunda yaji Yassar ma ransa a bace. "Kina son ganin Jikamshin ki?" Ya fada cikin wata irin murya. "Naam" ta sake fada da alamar tambaya duk da kukan da take yi. "Kinji me nace fa ni bana son gulma. In zo ki ganni ki fada min damuwarki?" Sake kankame wayar tayi tana jindadin maganarsa harda dan murmushi. "Kinyi shiru ko ba kya son gani na?" "Eh" sai tayi saurin cewa "a'a" tun kafin ya sake magana. "Ban san abinda ya saka min ke kuka ba amma ki rinka jira sai ina wuri kiyi kuka don na rarrasheki. I will see you soon in sha Allah" Bai jira tayi magana ba ya katse wayar ya tashi ya tafi office din abokinsa. SADAUKARWA GAREKU *MATAN KWARAI NA SAMI SAKON GAISUWA *UMMUL DIHYAH, HASSANA, USAINA, AMINA DA RUQAYYA. SAURA MASU GAISUWA DUK BAN MANTA DAKU BA. NAGODE ABINDA AKE GUDU🙆🏽38 Batul Mamman💖 Har karfe tara na dare ta wuce Col. Ishaq bashi da niyar tafiya. Hira suke yi da Anti Bintu da Kawu Yusuf kamar sun dade da sani juna. Sai ko Amatullah da ta tare a falon tana jikinsa tun bayan tashinta daga bacci. Hatta masallaci da ita suka je da Yassar. Maman Kawu Yusuf kuwa tana daga daki tuni tayi bacci bata san wainar da ake toyawa ba. Asmau tana tare da 'yan uwanta suna tasu hirar amma tana tunanin yaushe Jikamshi zai tafi ne. Gashi a dalilin zuwansa Yassar yayi biris da zancen komawa Kano. Ainau ta dauki waya zata kira babbar Yaya wato Shemau ta tsegumta mata abinda ke faruwa a Zaria Asmau ta hanata. "Naga alama sai da ya tofeku tas ya shigo gidan nan. Kowa sai wani kokarin kyautata masa yakeyi" Ainau tayi dariya "ki ce hakan baya miki dadi duk sai mu daure fuska" "Yaya Asmau mu dai kada ki cucemu ki hanamu zuwa bikin sojoji. Kinsan babu abinda ke bani sha'awa kamar su hada takubba amarya da ango su wuce ta tsakiya." Dijah ta fada tana hango ranar bikin. Daga nan suka shiga tsara biki harda irin kayan da zasu saka. Tun Asmau na hanasu har ta koma sakin baki tana jin yadda suke bayani kamar gobe ne daurin aure. Da ta gaji tace "to amarori sai kuyi hakuri zan bata muku show amma ni bani da niyar aure, dadin abin ma ba cewa yayi yana sona ba kuke ta rawar kai" Ainau tace "jiran *I love you*kike sai kace wata matar da. Yanzu ai alama kawai ta isheki. Dazu fa da na fito falo ba karamar kunya naji ba yadda yake yi miki ga Anti Bintu a wurin." Bata da abin cewa da zai hanasu abinda suke yi sai kawai ta kyalesu. ***** A falon Col. Ishaq yace zai nemi wurin kwana gobe da sassafe ya kama hanyar Kano don ba da niyar kwana yazo ba. Yassar yaso binsa masaukin da zai nema sai dai yadda Anti Bintu ke kallonsa ya gane rashin dacewar hakan ko don kada ya dora masa nauyi. Tace ya daure ya biyo ta gidan yayi breakfast sannan ya wuce. Ya tashi yana yi musu godiyar irin karramawar da suka yi masa, suma suna masa godiyar ziyarar da ya kawo musu. A waje ya tsaya da Amatullah wurin motarsa ya tura Yassar ya kirawo masa Asmau. Daga shiga sallar magriba bata sake fitowa ba. Gabadaya kewarta ta dameshi. Don kada aga rashin kunyarsa tayi yawa ne da tuni ya nemeta saboda ziyarar ma don ita yayi. Tasha tsokana a dakin kafin ta fito. Yassar ne mai yi musu jan ido su dena damun matar ubangidansa. Yana fadin haka ta dage ta kai masa dundu a baya tana cewa duk sun raina ta amma zatayi maganinsu. Tana sakkowa daga matattakalar kofar wajen yana ta kallonta har sai da ta kusa faduwa saboda yadda kafarta ke hardewa. Yayi saurin zuwa inda take yana mata sannu ta dan daure fuska. Yayi murmushi "ashe dai kema kina jin yadda nake ji Asmau." "Nake jin me?" "Dazu garin kallona kika kusa bugewa da bango, yanzu kuma gashi kina neman faduwa" yayi mata murmushi "idan muka yi aure anya zaki bari na rinka zuwa aiki?" Tafa hannu tayi tana girgiza kai sannan tace "ni bansan me zan ce maka ba ma." "Babu abin fada ne tunda kinsan gaskiya" Ya bawa Amatullah ledar alawa yace ta shiga ciki yana zuwa. Sai da ta nunawa Asmau tayi masa godiya sannan ta shiga ciki. Yace "gara ta koma cikin gida kada ki koya mata soyayya tun yanzu" Dan cije lebenta tayi tana murmushi. Har kasan zuciyarta ta amince tana son Col. Ishaq. Bata san lokacin da ta kira sunansa ba a can ciki tana mai jan sunan. _Jikamshi_" Wani irin sonta yaji yana kara shigarsa. Bai taba damuwa da sunan garinsu ba amma saboda dashi Asmau take kiransa har wani dadi yake ji na daban. "Yes dear" Ta sunkuyar da kanta kasa "wai so...so" "Ki fadi abinda zaki fada bana son jan rai. Ko don kinga ina son muryarki. Hmmm? Sai ki rinka kara hargitsani da ita." Murmushi ta sake yi shima yayi. Yana jindadi idan yaga ta saki jikinta tana fara'a kamar kowa. Tace "Wai soyayya muke yi"? "A'a a filin yakin duniya na uku muke" ya bata amsa yana daga gira. "Kina so nayi miki gwari gwari ne sai ki fi fahimta?" Ta kawar da kanta gefe cike da kunya da fargaba. Muryarsa taji yace "Ina sonki Asmau Ummin Safina. Babban burina yanzu bai wuce na aurenki ba da kasancewa tare daku har karshen rayuwata. Kuma zuciyata tana bani kema abinda ke taki zuciyar kenan. Right?" Hawaye taji sun taho mata. Wannan mutumi da ya santa cikin kankanin lokaci kuma yasan sirri mafi muni a rayuwarta shine yake fada mata kalaman so har yake batun aure. Dole taji sonsa yana kara shigarta sai dai kuma bata manta alkawarin da tayiwa kanta ba. Duk irin son da take yiwa Jikamshi bazata iya aurensa ko waninsa ba. Tana kuka tace "Nagode Jikamshi, kaine mutum na farko da ya fara sona da gaskiya tun bayan kaddarar da ta sameni. Ka kyautata min kuma ka kyautatawa Amatullah. Allah Ya saka maka da alkhairi. Amma kayi hakuri da maganar aure. Kasan komai game da rayuwata me zai sa ka...." Bai nuna damuwa ba ba fuskarsa sai ma murmushi da yake yi mata a yayin da take zubar da hawaye. "Asmau, Asma'u na. Kina ganin idan nace na janye zaki ji dadi?" Sai da taji faduwar gaba sannan ta gyada masa kai. "Hmmm kamar gaske. Ina so kisan cewa bazan taba janyewa ba. Ni ba karamin yaro bane. At the age of 42 nasan meye so ko kishiyarsa. Kuma a naki idon so nake gani....infact kamar ki hadiye ni" "Lahhhhh" ta iya fada hawaye na sintiri a idonta. Wallahi tana son Col I.M Jikamshi amma dole ta hakura indai ba so take ta daukarwa kanta dala ba gammo ba. Tana da yakinin ko Hajiyarsa bazata lamunce danta ya aureta ba. "Rufe bakin mana" Ta kuwa hade bakinta kamar yadda yace. Dan kara matsowa yayi amma da sauran tazara a tsakaninsu. "Kafin haduwarmu na ajiye batun aure a gefe tun bayan rabuwarmu da matata ta shekara kusan shadaya. Yanzu da na hadu dake sai nake jin rayuwata bazata kara min dadi ba idan babu ku. Ki manta da komai na bacin rai ki rungumi mai sonki. Ni fa nake nufi" Murmushi ne yazo mata babu shiri. Sannan tace "Kasan dalilina na gudun aure. Gori nake gudu ko a ni ko Amatullah. Sannan kaima duk inda kaje za'a nuna ka" Hamma yayi alamun baya son maganar "duk kin tsareni da zance kin hanani na tafi na kwanta." "Maganar fa tana da mahimmanci" "Bacci na ma yana da mahimmanci. Ina fatan haduwa da Asmau ne muyi hirar arziki batare da tayi min kuka ba." Jikinta ya kula yayi sanyi. Duk abinda take gudu ya riga ya hangosu amma ko da aure ko babu abinda ya faru ya riga ya faru a baya. Wucewarsa sai a hankali idan Allah Yaso. Indai ya sami amincewar Hajiya wanda baya tunanin zata ki to duk abinda mutane zasu fada sun dade basu fada ba. "Zan baki lokaci daga nan har ki gama zamanki. Yassar ya fada min zaku je Niger so duk zan baki damar yin tunani kiji ko zaki iya zama batare da kina ganina ba. Ranar da kika dawo a ranar zanzo naji amsarki. Kada kiyi tunanin gujemin Asmau." Kanta a kasa har ya shiga mota yana tausaya mata. Ba don kaddara ba ace tana son abu amma wani kuskure da ya riga ya wuce yasa tana gudunsa. Bata dago kanta ba har ya saita motar zai tafi sannan suka hada ido. A hankali ta karanta lebensa ta gane abinda ya fada wanda ba'a ji sai motsin bakinsa kawai. _Love you_ ****** Bayan tafiyarsa gida ta shiga tana ta juyayin zancensa. Dakin Anti Bintu ta nufa tayi sa'a bata dade da fitowa daga wanka ba. Cike da damuwa ta zayyana mata yadda suka yi da Jikamshi. "Ko baki fada ba Asmau idanuwanmu sun gane mana. Ki godewa Allah da Ya dubeki da rahma Ya kawo miki mai share miki hawaye" "Anti ba kya ganin rashin dacewarmu. Karshenta danginsa bazasu amince ba. Kuma ina tsoron wulakanci da gori nan gaba duk da ni na janyowa kaina." Ta fashe da kuka "Haba Asmau. Har yaushe za'ayi ta maimaita abu daya. To bari kiji in fada miki. Indai bakiyi aure ba wallahi sa ido sai yafi a kanki. Ko takalmi kika canza sai an sami masu yi miki muguwar fassara. Gara kiyi aure ki samu garkuwa da rufin asirin da kowace mace take nema." Tasan gaskiya ake fada mata amma gaba take ji. Ranar da miji zai goranta mata. Ranar da zai nuna mata alfarma yayi mata da ya aureta. Anti Bintu tana ta nuna mata ta karbi kyautar Allah hannu bibbiyu ta fada mata yadda suka yi da Qasim. "Ikon Allah, wannan yanke shawara ba zai yiwu da gaggawa ba. Duk mun shaida irin neman da Qasim ya rinka yi miki. Amma banyi zaton abin zai kare a soyayya ba. Ga kuma Ishaq da kuka hadu lokaci guda ya kamu da sonki da na Amatulllah. Kuma kema nasan shi din kike so. Ki bari ku koma Kano nima sai nazo ayi magana da su Hajjo da Yaya Abu. A yanzu dai ki dage da neman zabin Allah. Amma ki sani aure shine gatanki. Kada na kara jin kince bazaki yi ba" ***** Sati dayan da suka yi sunji dadin zaman garin idan ka cire maman kawu Yusuf. Soyayyar Jikamshi kuwa kullum karuwa takeyi a ranta. Duk da basa waya don yace zai bata lokaci tayi tunani batare da ya dagula mata lissafi ba. Ga Qasim kullum yana waya amma baya mata zancen soyayya. Shima yace sai ta dawo zasuyi shawara. Al'amura duk sun cakude mata. Ranar da suka cika sati Umma, Yassar da Jafar suka iso harda Sabira. Mota biyu suka yi. A ranar suka wuce Wushishi. 'Yan uwa da abokan arziki sunyi musu tarba mai kyau. A gidan Kawun su Umma aka yi musu masauki. Mutane suna ta zuwa ganin Asmau da 'yarta. Kowa da abinda zai fada. Wasu su fadi mai dadi wasu kuma sai dai a kawar da kai idan sunyi magana. A nan ma sati guda sukayi suna zaga dangi sannan suka kamo hanyar Kano. Tun a hanya Qasim ya sanar da ita zai zo washegari da daddare idan sun huta saboda jin amsarta. To kawai tace tana tunanin abinda zata fada masa. Gashi Umma tace sai sun dawo Kano zasuyi maganar sosai don duk su biyun babu na yarwa amma dai zukatansu sunfi karkata ga Qasim da suka sani tuntuni. ***** Kamar yadda yayi alkawari a gidan Isha tayi masa ma. Bayan sun gaisa da Umma suka fito waje da Asmau suka zauna kan wasu kujeru daga gefe. Bayan fitarsu Col. Ishaq ya rinka kiran wayarta. Yasan jiya tace zasu dawo saboda haka lokacin jin amsarta yayi. Da yaji shiru saboda tun kafin magariba ta jona chaji ta barta a daki sai kawai ya shirya ya taho. ****** Suna zama Qasim yace "Ya naga kamar kin rame ne? Ko duk rashin hutu ne kuna ta ziyara." "Kai kuma kayi kiba Yaya Qasim kamar ba dansanda ba. Anya zaka iya bin barawo da gudu kuwa yanzu?" Tare suka soma dariya yana kallonta yana jindadi. A daidai wannan lokacin Col. Ishaq ya shigo gidan da motarsa. Bisa rashin sani ya haskosu suna dariya ransa yayi matukar baci saboda kishi. ABINDA AKE GUDU🙆🏽39 Batul Mamman💖 Tsabar bacin rai yasa yayi wani irin cin taya sannan yayi parking din motar. Duk jikinsa tsuma yake yi, zai iya rantsewa bai taba jin kishi makamancin wannan ba duk tsahon rayuwarsa. Asmau ma tuni ta hadiye dariyarta gabanta na faduwa. Duk da bata ganshi ba amma ta gane motar. Sai taji ta tsani kanta da har tayi abinda zai bata masa rai. Amma laifinsa ne don ranar da suka dawo yace zai zo shiyasa yau ta fito wurin Qasim da kwarin gwiwarta. So take yi ta fara sallamarsa sannan shima wanda yayi nasarar samun soyayyar tata ta nemi su rabu. Duk iya tunaninta karatu ne kawai mafita garesu ita da Amatullah. Qasim bawan Allah ya kula da yadda ta canja lokaci guda har ya fara tunanin waye a motar. Motar ya rinka kallo da Asmau. ****** Kamar ya juya haka ya rinka ji sai dai kuma hakan ba girmansa bane tunda har ya shigo gidan. A zuci ya karanta *Hasbunallahu wa ni'imal wakeel*har yaji bacin ran ya ragu sannan ya fito yana zuba _kamshi_. Taku yake daidai har ya iso kusa dasu. Kamshin turarensa da yake sanya Asmau nishadi ne ya fara ziyartar ta. Taji bugun zuciyarta ya tsananta. A iya saninta da Jikamshi baya boye magana ko gaban waye. Bata san me zai ce a gaban Qasim ba, mutumin da bai cancanci wulakanci ko kadan ba daga gareta. Yana karasowa ya saki fuska duk da ta ciki na ciki ya mikawa Qasim hannu yayi masa sallama. Qasim ya karbi hannun shima cikin fara'a ya tashi suka gaisa. Sai kuma suka kalli Asmau suna jira ta gabatar dasu. Tsuru tayi da ido kamar wadda tayiwa sarki karya. Da kyar ta saita kanta tace "Yaya Qasim ga baban Amatullah da nake fada maka. Col. I M Jikamshi." Sake kama hannunsa Qasim yayi yana murmushi "naso ace har gida nazo na sameka domin kara mika godiya bisa taimakon da kayi mana. Allah Ya saka da alkhairi Ya bada lada. Ashe manyanmu ne masu tsaron kasa. Bari na baka girmanka yallabai." Gyara tsayuwa Qasim yayi ya daidaita kafafunsa sannan yayi saluting Jikamshi. Shima murmushi yayi ya tsaya a attention ya mayar masa da salute din duk suka yi dariya banda Asmau. Col. Ishaq yace "ka kirani Ishaq kawai. Asmau bata iya kiran sunana kai tsaye ne shiyasa kaji tana maka kwana kwana ko" ya fada yana mata kallon da ke kara kashe mata zuciya. Ta sunkuyar da kanta kawai. Abinda take gudu kenan ya bata kunya a gaban Qasim. Ta daure tace "ga Yaya Qasim shi dan sanda ne" "Allah Sarki, its a pleasure meeting you. Ai ta bani labarinka. Kune manyan ai muna bayanku. Baka ji ana cewa abokin kowa dan sanda" Col Ishaq ya fada yana kara kallonsa zuciyarsa fal kishi yana ta kokarin dannewa. "Nima ta fada min yadda ta hadu daku. Muna kara godiya." "Kada ka damu ai yiwa kai ne. Amma me kuke yi a waje haka ga kura? Ina tsammanin damuna ta kusa tsayawa dai" yadda yayi maganar Asmau ce ta fahimci da biyu yake yi. Shi kuwa Qasim ya dan sosa kai yana dariya. Ko babu komai Jikamshi ya girme shi "Yallabai kenan. A tayamu addua dai muna nema ne" Wani abu ne ya tokarewa Col Ishaq makoshi yaki sauka kasa. Wai ya taya shi addua. A zuciyarsa yace (Allah Yasa kada ta taba yi maka soyayya irin ta mace da namiji.). Abu daya ke yi masa yawo a ka shine kada Asmau ta juya masa baya. Wannan Qasim din wani sanyi ne gareshi mai sa mutum yaji dadin mu'amala dashi. A fili kuwa murmushin yake yayi "ah to bari naje naga Amatullah sai na tafi. Dama ita nazo gani kewarta ta isheni" daga nan gefe ya matsa ya kira Yassar. Bai dade ba ya fito ya shigar dashi ciki. Ransa a bace da ya hango Asmau da Qasim yana taya Jikamshi kishi. Bayan sun shiga ciki Qasim yayi ta yabon saukin kai irin na Col. Ishaq "kamar ba babban soja ba, ji yadda yake jana kamar ya dade da sanina" "Uhmm" kawai Asmau tace a sanyaye. "Asmau wace shawara kika yanke mana?" Ta dago kai a hankali "Yaya Qasim ni dai da mun bar maganar nan" "Kinga Asmau duk abinda kike gudu baki da tabbas a kansa. Yana iya faruwa ko kuma kiga bai faru ba. Haka nan ma masu aure na fuskantar matsaloli musamman mata daga dangin miji. Bance komai zai tafi mana daidai ba amma nayi alkawarin tsaya miki har karshen rayuwata" Tausayinsa ta kara ji. Banda tsoronta na aure ko kadan bata jin son Qasim sai tausayinsa saboda yadda yake mata. "Ka dan kara min lokaci, ban samu nayi maganar da Umma ba" "To babu komai, shi garaje ai bashi da alkhairi. Duk yadda kuka yi ki sanar dani. Sannan zan kiraki idan na koma gida in sha Allah. Akwai keke da na siyowa Amatullah bari na dauko yana bayan mota" "Nagode" "Wai kin gode, mutum da 'yarsa? Shiga ciki bari na dauko" Da sauri sauri tayi shige. ***** Daga kallon kofa sai agogo Col. Ishaq yake yi tunda ya zauna hankalinsa baya tare dashi. Ji yake kamar ya koma wajen ya hana zancen. Hajjo ce take kokarin janshi da hira sai Amatullah tana bashi labarin Wushishi. Yassar kuwa kamar yaje ya dauko Asmau yake ji. Da ta shigo Jikamshi ya kafe ta yayi da ido ta kasa kallon inda yake kawai sai ta shige dakin Umma inda suke ta hada kaya ita da Ainau zata koma gidanta washegari. Qasim ya shigo da keke mai kyau na yara. Amatullah sai tsalle da murna. Tana ta cewa ta gode kamar yadda Umminta ta koya mata. Hajjo ta dubi Col Ishaq "da kai da Qasim kuna shagwaba yarinyar nan da yawa. To ni ina nawa keken?" Suna dariya Yassar yace "kada ki damu ni zan siyo miki irin mai katuwar tayar gaban nan na zamaninku" Umma ta fito tayi godiya sannan Qasim yayi musu sallama ya fita. Sai da suka ji tashin motarsa Col Ishaq shima ya tashi yace da Amatullah ta kira Umminta su gaisa. Umma ta jinjina kai tunda ya shigo dazu ta kula ransa a bace yake yana dannewa. Gaskiya akwai matsala nan gaba sai dai fatan Allah Ya zabawa Asmau mafi alkhairi cikinsu. ***** Tana kwance akan gado har wani zazzabi ke neman kamata saboda tunani Amatullah ta fada mata sakon babanta. Ta dan zaro ido "Baba Qasim ya tafi?" "Eh ya tafi kuma ya kawo min keke mai kyau" "Kinyi masa godiya ko" "Nayi masa Ummi" "Muje kiyi wasa kafin lokacin bacci yayi" ****** Baya falo da ta fito sai ta saka takalmi ta fita waje. Tsaye yake a jingine da motarsa yana danna waya ta hasko fuskarsa. Kamar mai taka kwai haka Asmau ta karasa gabansa. "Ina wuni" Muryarta tana masa dadi, wani irin sonta yake kara ji yana shigarsa. Sai dai kishi yasa ya kasa amsa gaisuwar. "Asmau wallahi ina da kishi sosai. Kada ki bari na kara ganinki a yanayi irin na yau. I can't take it" Ta kara sunkuyar da kai da jin furucinsa. "Kinga ki dago kanki ki kalleni magana zamuyi" Mayafinta tasa ta rufe fuskarta gabadaya. kunyarsa take ji. "Kina so na bude fuskar ne da kaina?" Ta girgiza kai da sauri "To ki bude da kanki kafin hakurina ya kare" Hannu tasa ta bude fuskar tare da dagowa a hankali. Fuskarshi ta bata tsoro saboda babu digon wasa "Jiranki da nayi a falo dazu yana cikin lokutan da bazan manta ba a rayuwata. Zuciyata bazata juri ki hadani da wani ba" "Don Allah kayi hakuri" tace idonta na kawo ruwa. "Ki fada min ni dashi waye ya fara nuna miki so" "Kai ne" ta amsa masa jiki a sanyaye. Bata son bata masa rai ko kadan saboda yadda take sonsa. "Alhamdulillah, da ya rigani zan ci girma na bar masa ke don bazan iya tarayya da wani akanki ba. Ina da kishi mai zafi wanda ban taba sanin kaina dashi ba sai yau. Amma tunda na riga shi sai dai shi ya hakura. Ina sonki kuma bana jin zan iya hakura dake." Shiru tayi tana kallon kasa. Tun bayan rasuwar Abubakar ta cire rai da sake samun soyayyar wani da namiji sai gashi yanzu har mutum biyu ne suke sonta. Mutum biyun da take

Chapter 14 of 23