Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Shima da ya gaji fita kawai yayi daga dakin. Likita yazo ya sake duba Asmau ya tabbatar musu cewa zasu iya tafiya da ita gida. A haka suka tafi ko da suka iso gate din gidansu Abubakar da yake shine a farko kafin nasu wani kukan ta sake fashewa dashi. Mutanen da suka zo daurin aure sun koma zaman makoki. Duk a nan suka sauka suka shiga gidan. Gaban Asmau sai faduwa yake balle da taji ana cewa ga amaryar nan ta shigo. Mutane da dama suka taso ana kallonta. Kowa na fadin albarkacin bakinsa na dangane da tausayawa gareta. Bayan sun shiga gidan dakin Mama aka wuce da ita. Ko zama batayi ba Umma tace mata taje tayi alwala saboda batayi azahar da la'asar ba. Jiki kamar wadda bata da laka haka ta shiga bandakin jiri na dibarta ta dauro alwala tazo ta biya sallolin dake kanta. Tana sallar tana zubar da hawaye. Bayan ta idar ta dade tana kuka da addu'a. Sadiya ta hado mata tea mai zafi ta mika mata. Kai ta girgiza alamun bazata ta karba ba. Kusa da ita Sadiyan ta zauna " ki daure ki sha ko yaya ne sai kici abinci. Kowa da kika gani dauriya kawai yake yi Asmau." Nata hawayen ta share sannan ta dubi Shema'u tace "Anti Shema'u kisa baki ta sha ko kadan ne". Taruwa akayi ana lallabata tasha tea din amma taki har Umma da Mama suka dawo daga waje inda suka karbi gaisuwar wasu maza 'yan unguwar. Suma suka saka baki har Asmau ta karbi tea din. Bai fi rabin kofi tasha ba ta fara kwara amai saboda tun jiya rabonta da abinci. Haka ta rinka amai ta baki ta hanci abin tausayi. Ta galabaita sosai. Bayan ta gama aman Nasiba ta dagata zata shiga da ita bandaki ta gyara jikinta ta fadi kasa a sume. Nan da nan aka taru a kanta ana mata fifita. Aka shafa mata ruwa a fuska tare da sauke mata zip din rigarta don tasha iska amma duk da haka bata tashi ba. Mama tace aje a kirawo mata Baba a waje. Ita Umma gefe kawai ta koma tana kuka. Gani take yi kamar Asmaun ma ta cika. Shi da wasu suka shigo suka ga halin da Asmau ke ciki. Jafar aka kira da Abdulhalim suka sakata a mota aka kaita wani asibitin mafi kusa dasu. Su Mama suka biyosu a wata motar kowa bakinsa da addu'a. Bayan an bata gado wata likita da nurse suka zo suka tsaya a kanta ana ta kokarin ceto rayuwarta. Allurai kala kala kam tasha su. Likitar tace jininta ne ya hau ga kuma rashin kuzari a tare da ita. Gwajin jini ta umarci ayi mata don su gani ko akwai wani ciwon a tare da ita. Har wani likitan ne yazo suka taru ana ta abu daya sannan suka samu ta farfado. Su Umma sai godiya suke ga Allah. Mama na zaune a kusa da Asmau tana sake bata baki akan tayi hakuri kuma duk da ana mata karin ruwa ta daure taci abinci sai ga nurse din ta shigo. Shema'u ta tashi da kyar Anti Bintu tace " kema kina bukatar hutu tun dazu baki zauna ba. Kada kafarki ta kumbura". Murmushi Shema'u tayi sannan ta tambayi nurse din tana fata babu wata matsala a tare da Asmau. Nurse Ngozi ta washe baki cikin hausarta irin da inyamuran da suka zauna a Kano tace "babu wani masala sai abin murna...." ta mayar da kallonta ga Asmau "...congratulations ashe ciki ne yana baka wahala." Dummmmmm haka dakin ya koma babu wani abu da yake motsi na wani dan lokaci har maganar nurse Ngozi ta gama shiga kwakwalwarsu. ABINDA AKE GUDU ๐Ÿ™†๐Ÿฝ4 Batul Mamman๐Ÿ’– Kallon kallo suka fara yiwa juna. A wannan lokacin da za'a sake auna jinin Asma'u ba karamin hawa ya sake yi ba saboda tsananin firgicin da ta tsinci kanta a ciki. Mama ce tayi karfin halin kallon Ngozi tace" 'yar jakar uba bakinki ne cikin ai, dama Hausa bata gama zama ba dole kiyi shirme. Bari likitan tazo da kanta muji daga bakinta. Kila ma ciwon ciki kike son cewa kika ce ciki zaki karasa tsorata mu." Nurse Ngozi tace "Madam ina jin Hausa sosai fa. Yarinyarki is pregnant zata haihu shine abinda nake nufi." Takardar hannunta Umma ta fizga tana karantawa jikinta ya hau rawa. Shema'u ta karbi takardar suka hada kai ita da Nasiba da Anti Bintu suka karanta. Gabadayansu Asmau suka zubawa ido da tsantsar mamaki a fuskokinsu. Mama dake tsaye a gefe ta zaro ido tana tambayarsu me suka gani a takardar. Jafar ko kallon takardar baiyi ba ya fita wurin likitan inda Abdulhalim yake tsaye tana masa bayanin magungunan da aka rubutawa Asmau. Kamar wanda aka jeho haka ya shiga office din ransa ya gama baci. Abdulhalim ya tambaye shi ko jikin Asma'un ne. Jafar yace "ai gara ace jikinta ne da abinda mahaukaciyar nurse dinnan ta rubuta. Wai ciki? Asma'u ke da ciki kamar a tatsuniya...." likitar ya kalla "...ki taso muje ki sake gwadata don kada ku karasa gawar da ba taku ba." A tare suka koma dakin wanda yayi shiru kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa. Karar fanka kawai ake ji sai jefi jefi wannan ya kalli wannan. Suna shigowa likitan ta karbi report din daga hannun Nasiba ta karanta. Ita ma abin ya bata mamaki domin kuwa Abdulhalim yayi mata bayanin dalilin suman Asmau. Ta bukaci kowa ya fita suka fice babu musu. Sirinji ta dauko daga aljihun rigar asibitinta ta sake daukar jinin Asmau. Bayan ta gama tace "Asmau yaushe ne lokaci na karshe da kika ga al'adarki?" Tun dazu kwakwalwarta ta kulle babu wani tunani da take iya yi sai yanzu ta dawo hayyacinta da taji wannan tambayar. Hankali a tashi tace " biyu ga watan da ya wuce na gama". "Yanzu kuma gashi ana karshen wata na gabansa. Yau kinga ashirin da takwas ga wata." Likitan ta fada tana rubutu a wata takarda. Fuskarta na kan takardar tace " ki fada min gaskiya kin taba tarayya da namiji?" Kasa bada amsa tayi sai jikinta da ya kara mugun yin sanyi. Fatan mutuwa kawai take yi akan bala'in da yake tunkaro ta. Da taki magana likitan ta fita su Umma suka dawo har yanzu babu mai cewa uffan kowa zuciyarsa na sake-sake. A haka likitar ta dawo kana ganin fuskarta kasan labarin da ta kawo bashi da dadi. Ita kanta ta tausayawa mutanen ta dan sunkuyar da kai "a bisa binciken da nayi da kuma amsar da Asmau ta bani ya nuna tana da CIKI na kusan wata biyu." La haula wala quwwata illa billah....a rana daya duk wani farincikin gidajen biyu ya koma kishiyarsa. Umma tayi kan Asmau wadda dama tasan haka zata faru. "Asmau me nayi miki zaki yi min muguwar sakayya irin wannan? Uban waye yayi miki ciki? Har kinsan ki kebe da namiji ba tare da aure ba a tsakaninku?" Tana magana tana dukan Asmau ko ta ina. Su Anti Bintu ne suka yi kokarin riketa tana fada tana kuka. Shema'u ma gefe ta koma tana nata kukan. Wane irin abin kunya ne wannan Asmau ta janyo musu a wannan halin da suke ciki? Umma na dukanta duk da rashin lafiyar da take ciki amma ta kasa yin kuka. Biyewa son zuciya na 'yan mintuna ya wargaza dukkan wani farinciki da ta taba sani a rayuwarta. Irin ABINDA AKE GUDU kenan. Yau asirinta ya gama tonuwa. Sirrin boye ya fito fili bata da abinyi sai yadda Allah Yayi da ita. Mama ta rike hannun Umma da take shirin sake dukan Asmau "ba da duka zamu tambayeta ba Bara'atu. Kada ki bari bacin rai yasa kiyi aikin dana sani." Muryar Umma har ta dashe tace "akwai wani dana sani daya wuce haihuwar wannan yarinyar? Fyade aka yi miki ko kwaya kika sha da har zaki yarda da namijin da ba naki ba?" A hankali Asmau ta sakko daga kan gadon har allurar da ake yi mata karin ruwa ta fita daga hannunta bata sani ba jini ya rinka zuba daga hannun. Ranar wanka ba'a boyon cibi. Sai a lokacin ta soma kuka ta durkusa akan gwiwoyinta a gabansu Umma. "Tsautayi ne da sharrin shaidan. Don girman Allah ku yafe mana. Wallahi sau daya ne kawai. Idan har ina da ciki na Abubakar ne". Cikin tsawa Mama tace "kin ma isa ki dora masa. Wallahi nasan karya kike yi saboda kinga kasa ta rufe masa ido shine zakiyi masa irin wannan mummunan kazafi?" Magana take tana haki saboda bacin rai, sai kuma hawaye. "Yanzu kinyi masa adalci kenan? Ko kwana baiyi a kabarinsa ba kike binsa da mummunar shaida bayan kinsan mala'iku suna tsayawa karbar shaida akan mamaci. Allah Ya isa tsakanina dake. Har yaushe kika ga Abubakar din ma? Mutumin da sau biyu yake zuwa Kano a wata. A can makarantarku dai kika hadu da wanda yayi miki" Anti Bintu ta kama hannun Asmau ta tayar da ita tsaye cikin jin haushin maganar Mama gashi Umma taki cewa komai "wannan magana bata asibiti bace. Mu bari idan an sallameta sai ayi a gida. Amma kowa yasan bata da wani saurayi bayan Abubakar." "Babu wata magana da zamuyi a gida. Kai, ku wuce mu tafi." ta fadawa Abdulhalim da Nasiba. Dukkaninsu an rasa mai bakin magana. Tabbas Abubakar ne kadai saurayin Asmau. To amma kowa yayi shaidarsa wurin kyaun hali. Mutum ne mai kawaici da kunya. Ita kanta Asma'un ba don a gabansu aka yi komai ba sai su karyata saboda itama ko 'yan unguwa zasu shaideta da kyaun hali. Abdulhalim yaso ya tsaya domin a kare maganar a nan Mama ta daka masa tsawa dole yabi bayanta suka fita tana ta bambami. Bude kofar dakin kenan suka hadu da mata sun kai shabiyar daga gidan rasuwar suke sun taho jin halin da Asmau take ciki. Kana ganinsu kasan duk abinda ake yi a cikin dakin sun gama ji. Mama ko kallo basu isheta ba tayi gaba su Nasiba na bin bayanta. Matan dai tunda har an gansu dakin suka shiga suna tambayar ya mai jiki. Anti Bintu tace da sauki suka tashi ko minti daya cikakke basu yi ba suka fice ana ta mayar da zance. Bayan fitarsu Anti Bintu tace "Yaya Bara baki ce komai ba kina jin abinda Maman Abubakar take fada." "Me zance Bintu? Kin taba ganin cikin shege yayi uba kai tsaye a kasar musulmi? Duk abinda Mama Yalwa ta fada tayi min daidai. Nima da namijin ne nawa bazan yarda a kakaba masa cikin shege ba." Hada ido suka yi da Asmau Umma ta sakar mata wani mugun kallo. Abinda yafi wannan ma tasan zata gani tunda haka ta faru. Kusa da Umman ta dawo ta sake durkusawa a kasa ga wani irin jiri da take ji, kirjinta kuma kamar ana hura wuta. "Umma ki yafe min. Wallahi sharrin shaidan ne kuma muna ta istigifari kullum. Wallahi bazan kara ba wannan ma kaddara ce. Umma...." Ture ta Umma tayi ta dubi inda Shema'u da Jafar suke tsaye suna hawaye "Jafar fita ka samar mana abin hawa mu koma gida." "Asma'un fa?" Anti Bintu ta tambaya. Tamkar da dutse tayi maganar haka Umma ta shareta. Bayan Jafar ya dawo Umma ta rike hannun Shema'u saboda kafarta data rike suka yi hanyar fita. Asmau na ganin haka ta tashi tabi bayansu Anti Bintu na kiranta bata tsaya ba. Haka suka fice daga asibitin ga dare suka shiga tasi din da Jafar ya tsayar. Har suka isa gida babu mai magana a cikinsu. Abin mamaki nasu gidan a cike suka same shi bayan tunda aka yi rasuwar aka koma gidansu Abubakar. Bacin ran Umma ya sake karuwa don tasan labari ya riga ya iske duka umguwar. Sai cewa akeyi ya jikin Asmau. Aka rasa me amsa musu tunda sun san ainihin abinda ya kawo su. A cikin falo Umma zata wuce dakinta taji ance "Ke Bara'atu dakata." Ta gane muryar mai maganar ta san ba karamin rashin mutumci yazo yi mata ba. Alh Rabe ne kanin marigayi. Kin tsayawa tayi sai da taji muryar Hajjo mahaifiyar maigidanta sannan ta juyo. Kuka ne ya kwace mata yadda taga duk 'yan uwan mijinta a wurin mazansu da matansu ga kuma mahaifiyarsu. Allah Yasa itama akwai nata 'yan uwan wadanda suka zo biki daga Wushishi ta jihar Niger. Dangin mijinta basu taba kaunarta ba gashi Asmau ta sake shafa mata kashin kaza. Jafar ya juya ya matan dake binsu kamar jela yace duk su fita. Surutai da gunaguni suka rinka yi har suka watse. Aina'u da Yasar ma yace duk su tashi. Yasar baiso hakan ba a ganinsa shima ya girma ransa a bace ya tura Aina'u suka shige ciki. Kowa a zaune banda Asmau dake rakube a jikin kofa. Alh Rabe ya zare mata ido "munafuka algumguma ai sai kizo ki zauna kin wani tsaya mana a ka kamar sa'anninki." Da sauri ta zube a wurin da take tsaye ta dukar da kanta hawaye na kwarara a kumatunta. Hajjo ta furzar da goron bakinta a kan kafet tace "hankalinki ya kwanta ko Bara'atu? 'Yarki ta janyo mana abin kunya ta bata mana suna a gari. Tun rasuwar Shu'aibu babu yadda bamuyi dake ba akan ki bari 'yan uwansa su raba 'ya'yan a tsakaninsu kika ki amincewa. Yau wa gari ya waya uhmm? Dama tarbiyar mace mai zaman kanta har wata tarbiya ce." Hanci ta tsaya fyacewa tana kukan Bara'atu ta cuce ta. Umma tayi shiru kawai, tun dazu da aka aika musu da rasuwar Abubakar babu wanda yazo cikinsu. Yinin bikin ma cewa suka yi tayi a gidanta suma zasuyi nasu ko babu amarya. Sai yanzu da wannan abu ya faru shine duk suka taho. Harda Yaya Abu da babu abinda ta halarta na bikin wai tana ciwon wuya. Alh Rabe ya doka tsaki "dama me kike tsammani daga mace irin wannan Hajjo? Saboda na taimaki rayuwar 'ya'yan dan uwana fa har shahada nayi nace zan aureta duk da yadda nake kyamar mayu 'yan garinsu amma taki. Yanzu ta fada muku shegen da ya dirka mata cikin ko kuwa saboda samarin sunyi mata yawa bata san waye uban ba?" A kufale Jafar yace "Kawu nayi tunanin zama akayi na maslaha akan matsalar nan ba bakaken maganganu ba." Umma ta watsa masa harara don yayi shiru amma duk da haka sai da Yaya Abu ta hado masa ashar ta kunduma masa. Sannan ta dubi Asmau "to karuwar cikin gida wadda ake nuna mana kunfi kowa tarbiya. Cikin na waye don ko ni ban yarda na yaron nan bane Abubakar bawan Allah. Gara da Yalwa taki karba zaku gurbata musu asali." Jin batayi magana ba har Hajjo ma ta sake tambaya yasa Kawu Rabe yayi kanta yana haurinta da kafa. Tun tana zaune har sai da tayi kasa yana tattaka ta. 'Yan uwan Umma suka tashi aka rike shi sannan suka janyeta. Umma dai sai kukan zuci. Duk abinda aka yi musu a yau Asmau ce ta janyo mata saboda haka bata da bakin magana. Kallonsu take yi suka ci gaba da caba musu bakaken maganganu 'yan uwanta suna karewa sannan suka tashi. Hajjo tace "ki shirya sati mai zuwa ki turo min Yasar da Aina'u gara nasa su a gabana don bazan bari zuri'ar Shu'aibu ta gama lalacewa ba ina raye. Ranar gidan Umma ansha kuka kala kala. Shema'u duk yadda suke da kanwarta ko inda take taki kallo. Asmau ta bata kunya sosai. Anyi ta tambayarta kuma taki magana tunda sunki yarda cikin Abubakar ne. Abu dai har tsakar dare suna dakin Umma ana ta magana daya. Asma'u kuwa babu wanda ya shigo dakinta. Kawayenta da suke gidan gabadayansu bata san inda suke ba har da aminiyarta Walida wadda take ganin kamar bazata gujeta ba a wannan yanayin. ABINDA AKE GUDU ๐Ÿ™†๐Ÿฝ5 Batul Mamman๐Ÿ’– Zaune take kan abin sallah tana addu'a tana zubar da hawaye. Bata taba tsammanin ganin rana makamanciyar wannan ba a rayuwarta. Babu Abubakar ga cikinsa a jikinta batare da aure ba. Yau da cikin aure ne bata san irin soyayya da gatan da Umma da Mama Yalwa zasu nuna mata ba. Ashe haka ake ganin bambancin rayuwar wadda aka shafa fatiha akanta da wadda ba'a shafa ba? Gashi dai duk abu daya suka yi, amma mai aure sai ta zama tauraruwa har idan batayi ciki ba ayi ta korafi ko aji tausayinta. Ita gashi kuskure sau daya tak, tayi cikin da bata bukata gashi hatta mahaifiyarta tana nuna mata kyama. Aure ibada ne, zina kazanta ce. Wani kukan ne yazo mata da taji cikinta na kukan yunwa. Yanzu idan taci abinci abinda ke cikinta ma zai samu? A hankali ta shafi cikin zuciyarta na kuna. "Wayyo Allah, Ya Allah Ka jikan Abubakar Ka karbi tubanmu" abinda ta fada kenan cikin raunanniyar muryar da ta gama dashewa don kuka. Akan abin sallar bacci ya saceta tana rungume da AlQur'ani. Gari na wayewa ta rinka jin muryarsu Umma a kitchen ana dafa abincin da ta fuskanci na sadaka ne da za'a kai gidan Kwamishina. Tana son fita amma tana tsoron abinda zai biyo baya. Duk wannan tashin hankalin wata muguwar yunwa take ji sai dai ko zata mutu bazata fita neman abinci ba. Sai wurin karfe goma taji gidan ya danyi shiru. Tana nan zaune Anti Bintu ta shigo dakin. Itama dai ba sakin fuska tayi ba, ta shigo dauke da plate din abinci da ledar pure water. A gaban Asmau ta ajiye ta juya ko gaisuwar da take mata bata amsa ba. Sai da ta fita ta fashe da kuka. Rana daya Asma'u ta zabge idanu sunyi ciki kamar ta shekara a kwance. Tana jin tausayinta sai dai dole a nuna mata kuskurenta. Abincin da ta kai mata ma babu wanda yasan ta kai. Kuka tayi sosai sannan tabi bayansu Umma da suka riga suka tafi gidan rasuwar. Su Umma zasu shiga gidan taji Mama Yalwa tana cewa alajirin da ya kawo abincin ya mayar musu da abincinsu bata so. Dama tasan tun faruwar al'amarin jiya dole Mama ta canja mata. Sai dai mutuwa ta kori komai shiyasa ta daure tazo. Sallama tayi suka shiga sai tayi kamar bata ji abinda Mama ke fada ba. Itama kunyar ganin Umman tayi sai ta bar gaban kulolin abincin. Haka suka gaisa kowa fuskarsa a cunkushe su Umma suka sami wuri suka zauna. Babu mai cewa komai dama gidan rasuwa ne. Mutane 'yan kallo suka taru suka zuba musu ido. Haka ce ta kasance kullum Umma zatayi abincin sadaka kuma su je gidan su zauna sai anyi la'asar su koma gida. Tsakaninsu da Asmau kuwa ko kallonta batayi duk da tana fitowa ta gaisheta. A rana ta shida ne da daddare wata dattijuwa cikin 'yan uwan Umma tace ya kamata su zauna suyi magana akan lamarin Asmau. Umma tace "kayya dai Gwaggo, me ya rage mana kuma banda zubewar mutumci." Gwaggo tayi dan murmushi "Bara'atu nayi tunanin ke mace ce mai hangen nesa da tawakkali. Me kike tsammani ga yarinyar da take cikin yanayi na Asmau ace kowa ya juya mata baya? Idan abin ya isheta dole tayi tunanin nemawa kanta mafita koda kuwa mafitar halaka ce fiye da halin da take ciki yanzu. A 'yan kwanakin nan duk wanda ya kalleta yasan tana cikin damuwa kuma muna fatan ta yi nadama. Kamata yayi a sake tambayarta lallai ta fadi gaskiya game da cikin sai a san matakin dauka." Kowa a dakin yayi na'am da shawarar. Shema'u dama mijinta yayi mata fada akan rashin kula Asmau da suke yi ba shine mafita ba. Umma tace aje a kirawo Asma'un. Gabanta na faduwa ta shiga dakin kowa ya zuba mata ido. A can gefe ta zauna idonta a kasa. Anti Bintu tace " Asmau ki dubi girman Allah da halin da kike ciki ki fada mana gaskiya game da cikin jikinki." Kai a sunkuye ta sake nanata musu cewa na Abubakar ne. Ran Umma a bace tace ta tashi ta fita. Ji take inama Asmau tace fin karfi aka yi mata. Da ta tausaya mata amma da jin bayaninta kasan abin ba haka bane. Shawara aka yanke jibi bayan anyi kwana bakwai da rasuwar suje su sanar da iyayen Abubakar. Haka kuwa akayi. Da yawan 'yan bikin sun koma Wushishi sai kadan suka rage saboda abinda ya faru. Babu wanda ya sake zuwa daga gidan Hajjo dama basu sa a ka ba. Umma da Anti Bintu suka je sai Gwaggonsu da Asmau. Mama na ganinsu ta hade rai Umma ta daure ta bukaci ganinsu ita da Alh Adamu. Harda Abdulhalim da Nasiba suka zauna a falon. Gwaggo ta gabatar musu da dalilin zuwansu. Alh Adamu yayi gyaran murya ya soma magana "duk wannan bayanin naji shi tun a ranar da Abubakar ya rasu. Ina sane nayi shiru har sai an share makoki. Bazan boye miki ba Haj Bara'atu wannan labari yayi matukar muni garemu baki daya. Sai dai kuma tsakani da Allah wanda ake abin a kansa yanzu baya raye. Maganar Asmau kadai bazata sa mu karbi cikin jikinta a matsayin nasa ba. Yau da yana nan ne sai ya karba ko ya kare kansa." Tunda ya fara magana Umma ta soma zubar da hawaye.. " Alhaji duk mun shaida Asmau babu wanda take sauraro sai Abubakar. Idan kuka gujemu a wannan lokacin bansan inda zanyi ba. Dangin babansu dama ba kaunar mu suke yi ba, kune dai a garin nan kuka tsaya mana tamkar 'yan uwa....." Mama ta katseta "maganar 'yan uwantaka da cikin shege fa bata taso ba. Kamar yadda Baba ya fada da Abubakar yana raye sai muji ta bakinsa. Amma babu yadda za'ayi mu karbi cikin nan kawai don Asmau tace nasa ne." "To a bari ta haihu mana sai a gwada a tabbatar da zancenta." Abdulhalim ya fada yana kallon Asmau. Shi tausayinta yake ji. Mama tace " zanci mutuncinka wallahi. Idan an bari ta haihu ya dace da dan uwanka zaka karba ka rike ne? Shashasha tashi ka fita." Baba yace "ina zaunen kike irin wannan abin Yalwa?..." ya juya ga su Umma "kiyi hakuri Haj Bara'atu amma babu yadda zamuyi saboda babu kwakkwarar shaida. Idan har kina bukatar taimako kinsan ni mai taimaka miki ne kodayaushe." Yana kaiwa nan ya tashi ya shige ciki Mama tabi bayansa. Nasiba ma ta tashi babu wata magana da suka ji mai dadi. Umma da Asmau sun sha kuka. Suka tashi suka tafi gida jiki babu kwari. Asmau tana tausayin halin da ta jefa mahaifiyarta. Suna zuwa gida hawan jinin Umma ya tashi aka kaita asibiti. Kuka dai yaki karewa a gidan. Kuma aka ki tafiya da Asma'un asibitin. Sai bayan isha suka dawo Yasar yazo dakinsu Asmau ya kirata fuskarsa babu walwala. Tana tashi yayi mata wani kallon banza " idan kika kashe mana Umma wallahi sai nayi miki abinda baki taba tsammani ba. " A razane ta kalli yaron da ta bawa shekara hudu wanda tsakaninta dashi kullum girmamawa ce. Indai Yasar zaiyi mata haka kowa ma dole ya tsaneta. A sanyaye tabi bayansa. Yanayin da taga Umma ya bata tausayi sosai tace "Umma yaya jikin?" Maimakon ta amsa sai tace "munyi magana da wata ma'aikaciyar asibiti tace gobe mu kaiki karfe goma na safe a cire cikin". A tsorace Asmau ta mike tsaye tana kuka "Umma kada zunubin yayi min yawa. Ga laifin ciki ga na kisa. Don Allah ki janye..." Saukar mari taji mai zafi a kumatunta daga Jafar, marin bai gama shigarta ba yace "banza ana son taimakonki zakiyi mana shirme. Waye zai sake kallonki idan aka bari kika haihu? Dubi yadda kika tarwatsa mana gida Asmau. Ki bari a cire indai ba kuma neman karasa zubar mana da kima kike son yi ba." Shema'u ta taso ta rike kafadar Asmau "cire cikin nan shi kadai ne maslaha garemu baki daya. Waye zai dauki dawainiyarki data abinda zaki haifa? Haba Asmau, ki bari muji da bakinciki daya mana." "Ku kyaleta ta nuna min iyakata. Asmau da kinsan irin radadin da nake ji a zuciyata da baki soma bude baki ba ma. Wallahi nayi nadamar haihuwarki, ina ma barinki nayi tun kafin ki zama mutum da dai naga irin wannan bakar ranar a dalilinki." Umma ta fada kuka mai sauti. Hankalin Asmau ya sake tashi sosai da jin abinda Umma dake matukar kaunar 'ya'yanta take fada yanzu. Durkusawa tayi a gabanta tana ta kuka da rokon ta yafe mata. Anti Bintu mai jin tausayinta tace ta fita ta basu wuri. Tana bakin kofar taji Jafar yana cewa ko ta karfin tsiya sai sun kaita asibitin ko a kira likitan har gida a cire. Umma dai bata sake magana ba amma sauran sun amince. Har Gwaggo na cewa akwai wasu saiwoyi da basu fada a asibitin ba sai tasa a kawo daga Wushishi a bata tasha cikin zai zube. Kasa tsayuwa tayi a bakin kofar ta koma daki. Ita da Abubakar sunyi kuskure babba amma tabbas zubar da cikin nan karin laifi ne. A yadda ta janyowa gidansu bacin suna a duniya bazata so ta zama silar karin zunubi a garesu ba a lahira. Da wannan tunanin ta janyo akwati daya cikin na lefenta ta hada 'yan kayayakinta ta zuba a ciki. Dan kudin da ta samu na biki da dan sauran kudinta ta saka a jakar hannu mai girma sannan ta ciro wasu sarka ,dankunne da awarwaron daga wata drawer duk ta saka a ciki tare da wasu kayan kala uku. Ko kadan bata runtsa ba a daren. Asubar fari Jafar da Yassar suka bude gate suka tafi masallaci. Suna fita Asmau ta lallaba ta fice daga gidan tayi hanyar titi. ABINDA AKE GUDU ๐Ÿ™†๐Ÿฝ6 Batul Mamman๐Ÿ’– Ta tsakanin gidaje ta rinka bi don kada ta hadu da idon sani idan an idar da sallar asuba sun fito daga masallaci. Ta jima tana tafiya zuciyarta cike da fargaba. Ba ita ta iso titi ba sai da hasken rana ya fara bayyana. Jefi-jefi ababen hawa suke wucewa don ma titin nasu na hotoro wurin wucewar matafiya ne. Kusa da wani kanti da yake rufe ta shimfida dankwalinta tayi sallah sannan ta koma titi ta tare dan sahu. Mutumin ya kare mata kallo sama da kasa sannan yayi magana "Hajiya ina zuwa?" "Tasha zaka kaini." Ta amsa masa tana kara rungume jakarta da akwati. "Garin Kano kuma mai tasha da yawa sai ki fadi wadda zaki je" Sai da ta danyi tunani ta tuno sunan tasha daya " kaini ta unguwa uku, nawa zan baka?" Yadda dreban dan sahun ya kula ta matsu ta shiga yace "kawo dari biyu tunda kinga yanzu safiya ce sosai" Babu musu ta zuba kayanta ta shige tana kare rufe fuskarta da hijabinta. Sai da ta sauka ta fara rarraba idanu domin ko kadan bata san inda zata je ba. Ummanta 'yar Niger state ce to amma tasan zuwa yanzu duk 'yan uwanta sun gama jin labarin komai, idan taje wurinsu ba ta tsira ba. Tana cikin wannan tunanin taji ana cewa, "Azare mutum daya Azare mutum daya" Ko dogon tunani

Chapter 2 of 23