Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 11
suka karasa tal'udu ya shiga gidan ya fito hannunsa rike da manyan ledoji ya saka a bayan motar yadawo mazaunin driver ya zauna yana aika mata da wani kallo, ahanya ya tsaya yai mata siyayya sosai kama da kayan kwalam da gashashshiyar kaza sai wajan mangariba suka koma gida wannan karon a kofar gidansu ya ajje ta kaina yai gaba ya wuce gidan su dake ɗan gaban nasu Salima sosai, da sallama Salima ta shiga gidan tai tozali da Mama daake alwalar sallar mangariba ta washe baki "Sannu da zuwa Mama bayan na fita kika dawo" "E! dana dawo Marwa ke gayan kin fita ɗazu ina kikaje" Salima ta ajje mata ledojin hannunta a kusa da ita ta ce "Amir ɗan gidan Alhaji Baffah muka fita tare da shi shine yamin wannan siyayyar" Mama ta dafe kirji idanunta akan Salima ta ce "Salima fita kuma kuka je ina ya ce dake mai" "Mama bafa wani abu bane kawai rakiya na masa ya karmowa hajiyarsu kayan ankon bikin yayansa da za'ayi da mukaje ma ko gidan ban shiga ba wallahi mama da muka tawo a hanya yake gaya min sona yake aure na zaiyi" "Salima ashe daman bakida hankali kin taɓa ganin jirgi yabi hanyar mota ina haɗi keda Ɗan Alhaji Baffah Yarima duk faɗin unguwar nan wane kamarsa ke Salima fita a idanuna ki tsaya iya matsayinki karki ɗorawa kanki abinda zai zo yadame mu" Salima ta zunɓuri baki tai fuu ta wuce ciki tana magana kasa kasa Mama ta harareta bata kalli inda Salima ta ajje ledojin ba tai shigewarta ɗaki ta tada sallah, Marwa ta kalli Salima dake ƴan kananun maganganu tai murmushi ta ce "Yaya nifa banga laifin Mama ba maganar gaskiyya ta gaya maki kirma ki biye masa wallahi ba auranki zai ba Amir bama kalarki bane, ni Yaya magana ma nakeso muyi zaman nan ya isheni haka tunda nai candy ina zaune a gida ba cas ba as shine da nace kodai aikin company zan fara na rinka samun ɗan na kashewa ina biyawa kaina ƴar bukata ta da bata fi karfina ba saika yini baka da ko sisi" Salima taiwa Marwa wani kallo na kaskanci kafin ta ce "Aikin Company kuma kina mace haba dan Allah" "Yaya ba haramun bane ai da zaman nan danake na banza ai gara na yi aikin" Mama data idar da sallah ta juyo ta kalli Marwa ta ce "Marwa ki je ki nemi aikin inkin samu kiyi abinki Allah ya taimaka zaman haka ba daɗi" Marwa taji daɗi sosai bayan ta idar da sallah ta tafi gidansu kawarta Hannatu da itace tai mata tayin fara aikin companyn tunda itama acan take aiki ta gaya mata gobe in zata tafi ta biyo mata su tafi tare Allah yasa a ɗauketa, ai kuwa washe gari kafin bakwai na safe ta gama shirinta bakwai saura kwata Hannatu tazo suka tafi bayan ta amince da dokokin companyn ta amsa tambayoyi take anan ta fara aiki kullum ɗari biyar in kanaso za'a baka kullum ko bayan kwana goma ko na wata guda itadai wata ta cw zata rinka karɓa tana ganin kamar saiya fi mata auki lokacin data fara aikin goma ga wata ne hakan yasa kuɗin da zata ɗauka dubu goma kenan. 🔯🔯🔯🔯🔯 Nuraddeen yai shuru yana kallon number Uwaimir daya ke shirin kira, gabansa yai wata irin bugawa da karfi tuna wayar daya taɓa ji uwair ɗin nayi da Rubina, ya sauke ajjiyar zuciya jikinsa sanyaye yama fasa kiran lambar Uwair ɗin yabari akan inta dawo kawai sayi magana tunda dai har ya samu Baffah yabasa dama to yana ganin yayi maganin rabin matsalar ya shiga ɗakinsa yai shirin barci zuciyarsa fal da tunanin Rubina *LONDON* Randa Uwair yabaro kasar ranar Baffah ya sauka nai tsalle nai murna da zuwan Baffah duk kewa da ɗacin ran danake na tafiyar Uwair gaba ɗaya ta tafi sabida murnar ganin Baffah na, ya saka ni jikinsa yakai hannu ya zagaye ni da shi ya ɗago kaina yana kallo hawaye suka zubo daga cikin idanunsa nakai hannu na share masa hawayan dake zuba daga cikin idanunsa "Allah maki albarka Rubina kici gaba da hakuri haka rayuwa take tana zuwarwa da mutane kaddara ta ko'ina ubangiji ya jarabaka danya ga imaninka kici gaba da hakuri Asma'u wataran sai labari kinji Allah yabaki lafiya yadawo maki da ganin ki" "Amin Baffah ko iya haka gani na ya tsaya ina gidewa Allah bazan manta da karamcin yaya Uwaimir a gareni ba hakika shi ɗin ɗan uwana ne na musamman mai maganin duk wasu matsolina" "Allah maku albarka gaba ɗaya ya haɗe min kanku" "Amin Baffana" Ummi dake tsaye kan step tana kallon Baffah da Rubina murmushi shimfiɗe a fuskarta ta ce "Rubie sake sa mana ya zauna ya huta ko ruwa ba'a kawo masa ba kin wani eukunkume sa kamar zai gudu ya barki" Nai dariya tareda barin jikin Baffah na koma gwfe na zauna ina dariya "Ranka yadaɗe barka da zuwa, zuwa ba sanarwa" "To hankali yayo nan ba Rubina ba Umminta gida duk ba daɗi" Ummi ta taɓe baki tana aikawa da Baffah ƴar harara, Rubina ta haye sama tana dariya kai tsaye ɗakin da Uwair ya zauna ta shiga har sannan kamshin sa na nan daram a cikin ɗakin, ta faɗa gado tareda rungume lallausan bargon da har sannan ke fitar da sassanyan kamshin turaran Uwair daya gama bin jikinsa "Hummm Ina missing naka Yayna ko ka sauka yanzu Allah ya tsare min kai aboki" na faɗa ina sake kai bargo kan hancina na lumshe idanu a zuciyata ina ayyano suffofin Yayana Uwair a fili na firta "Anty Raiha kinyi da dacw da samun mijin kware mai sanyi hali sassanyar zuciya kyau da ilimi Allah ka dube ni nima ka bani miji mai kalar halin yayna Uwair ina sonki fiyeda duka sauran yayuna ɗan uwa" Baffah tsaye gaban madubi futowarsa daga wanka kenan yana tsane kansa da karamin tuwel ɗin dake hannunsa Ummi na gefansa tana ƴar dariya kasa kasa da alama tare sukai wankan "Allah fa da gaske nake Fatima shekaran jiyan nan yazo ya samw ni na eiga na gaya masa wace Rubina a wajanmu kuma ya yarda ya amince zai aureta a haka ki gayawa yarki zai kira lambarki anjima ɗazu da mukai waya da shi na basa lambar wai ta Uwair dana fara basa bata shiga" "Cab ai wallahi gara da baima samu uwair ba da kai tsaye zai katse sa randa na sauka kasar nan ya kalli idanuna ya bayyana min alamun na yana son Rubina" Baffah ya juyo da sauri yana kallonta "Da gaske kike uwair ɗin, to mai yasa ni yakasa faɗi min" "Ni abinda nake tunani kamar yana jin tsoron mahaifiyarsa ne kuma nima bana goyon bayan auransa da Rubina hajiya bazata taɓa batinsu suji daɗin rayuwa ba shi yasa ma ban wani ɗau maganar da mihimmanci ba koma dai maine ni nayi farin ciki da zuwan Nuran nan daman ina tsoron Aliyu" Ummi ta karasa faɗa damuwa bayyane a fuskarta "Mai yasa bakya son Aliyu ya auri Rubina?" Ummi taiwa Baffah wani kallo kafin ta ce "Dalili ɗaya ne banda shi da zanyi farin ciki da auranta da Aliyu sosai, na farko Hannah matarsa ƴar kanwata ce uba ɗaya idan na ɗau Rubina na basa mai nayi kenan sannan ni bana so Rubina tasan ita wace" "Koba daɗe ba ba jima dole wataran Rubina zatasan ko ita wace ni ina fata na sanar mata da bakina da nata, akwai company na na sharaɗa nai aniyar barmata shi gaba ɗaya Rubina ko yau na mutu batada gado na nayi magana da Amjad zasu zauna da lauyoyi na zan saka hannu bansan ranar mutuwata ba Fatima bana son na mutu na bar Rubina a tagayare nayi iya bakin kokari na in nemo iyayanta na kasa na gaza mata ta wannan ɓangaran shi yasa nakeson bar mata wani ɓangare na dukiyata da zata tsira da shi ko bana raye" "Amma dai kasan hakan da zakai zai iya jawo cece kuce Hajiya tayita korafi gefe ga Dada ni ban son kananun maganganu" "Dukiya dai tawa ce ko? ba uban dayake tayani nema sanda nasha faɗi tashi na harna tara ta waya sani" "A'a fa arinka dai tunawa Hajiya dai da ita akaita faɗi tashin nan" Baffah yai murmushi yana faɗin "Nawa ta zuba a cikin dukiyar, mubar ma maganar nan nifa wallahi a yunwa ce nake" Ummi tai dariya irinta basawa tana zura bakar abaya ta ce "Mu sauka kasa to a sama maka abinci" Baffah yakaraso kusa da ita ya tsaya yana kallonta yasa hannu ya ɗago fuskarta "Kinsan yunwar ai kema Fatima, na rasa gane wannan sirrin naki kullum bakya tsufa kina nan a yanda kike bayan tarin jikokin da kika ajje" Ummi ta rungomo Baffah tana dariya taja sa suka faɗa saman gado Uwair bakwai na dare ya sauka garin abuja wani jirgin yahau zuwa calabar sanda ya isa cikin gidansa yai hamdala yana godiya ga Allah yai sallar insha kana yai shirin kwanciya barci dan gobe ya sani fitar sassafe ce, shi gaba ɗaya ma wallahi sai yanzu aikin nan daya zaɓarwa kansa yadamesa gaba ɗaya ba sakewa idan da ba soja ne shi ba ba abinda zai baro sa da Rubina take kewar Rubina ta mamayesa yaji kwalla na zubowa daga cikin idanunsa ya rasa wanne irin so zuciyarsa kewa Rubina da kullum burin zuciyarsa shine su kasance tare a ko yaushe har barci yafara ɗaukarsa yaji wayarsa na ring ganin lamabar kasar waje yasa yai saurin ɗaga kiran "Yay meer" yaji sassanyar muryar Rubina ta daki dodon kun nan sa "Uhmm Rubie yane" "Yay Meer yaka sauka gida fatan kana lafiya gaba ɗaya ma sai naji nan ɗin ba daɗi nima Allah dawowa zanyi" "Kizo kiyi mai anan ki zamanki kawai Baffah ya ce bazaku wuce sati ba zaku tawo tare sabida bikin.."sai yai shuru ya kasa karasawa Rubina tai dariya "To karasa mana bikinka nima daman ai shi nake tunani amma tunda haka ne nayi farin ciki Allah yasani akai bikin abokina yayana bana kasa ba'a kyauta min ba nima fa biki zanyi sosai kama ware min kuɗin party ɗina daban saina gayyato duka kawaye na da muka gama schools tare, nima nayi shiga irinta amare" ba karamar dariya Rubina ta basa ba wai tayi shigar amare "To waye angon ko dai na tawo maki da wanda nakeson ki aura" "Nifa ka gama kashe min zuciyar nan Yayna va lissafin aure a cikinta karatu ne kawai" "Yawwa nai farin cikin jin haka yanzu dai barci nakeji kinga nan mu dare ne yanzu zan cigaba da barcina da safe zan kiraki muyi magana" Rubina bata sake cewa komai ba ta katse kiran harya mai da kai zai koma barci kawai ya tashi ya faɗa bayi ya ɗauro alwala ya tada sallar nafila Hajiya Umma tsaye sakeke tana kallon Amir ɗanta cikeda mamakin maganar da yake "Na rantse da Allah Umma da gaske nake maki da kunne na na jiyo Yaya Amjad da Barister Shitu suna maganar ni bakin cikina ma shine yanda na rinka lallaɓa Baffa a kaini companyn nan yaki wai dole sai dai na zauna a kasuwa amma yanzu zai ɗauki wannan companyn babba yaba wata can mara asali nidai Hajiya kiyi wani abu akai gaskiyya kafin munaji muna gani wanan matar Fatima ta mallake komai mu amu tashi a tukar babu" Hajiya Umma tsabar takaici tayi ahuru tama kasa cewa komai sai numfashi da take furzarwa, ta mike tana zagaye a ɗakin nata "Amir ban taɓa shiga malamai ba ama yazama dole a wannan gaɓar na shiga malamai nabi bokaye amin ɗayan biyu kodai a farraka tsakanin Rubina da Ummi rikon Rubina da iko da ita duka yadawo hannuna ko kuma a farraka min tsakaninta da Baffah ya koreta a gidan nan ko kuma a kashe min ita gaba ɗaya" "A'a Hajiya duk ba haka za'ayi ba inada tawa shawarar mai kyau" Hajiya Umma ta juya tana kallon kofa ta saki lallausan murmushi ganin mai maganat datake tsaye a bakin kofa ta fara takowa zuwa cikin falon na hajiya 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode 1️⃣3️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* Amina ce ƴa ta biyu ga Hajiya Umma wacce ke bin Mahmud, ta zauna a falon tana aikawa Amir da harara, Amina masifaffiya ce ajin farko ko cikin kannan nata suna matukar shakkarta Amir ya sami waje ya zauna ya nutsu sosai yana aika mata da gaisuwa dan shi harga Allah ko iyayan sa da suka kawo sa duniya baya tsoro kamar yanda yake jin tsoron masifar Anty Amina "To wai kana wajan nan zamuyi magana kana jinmu" Amir ya kalli Hajiya ya marairaice fuska, Hajiya ta dubi Amina "Kinga bari muyi magana yana zaune Amir na waje na ne banda abokin magana sama da shi wani bin shike sharan hawayan damuwata, Amina ta gyara zama ta ce "Hajiya ba kowa zaki kama ba illa ki kama Baffah ram a hannunki idan kika mallake Baffah yazama mulki da ikon gidan nan gaba ɗaya yana hannunki idan kuma company ya zama na Rubina toya zama dole a aurawa Amir Rubina mu samu company ya zama na Amir kinga mun karu" da sauri Hajiya ta mike tana zare idanu ta ce "Allah ya tsari gatari da saran shuga wanne Amir ɗin wannan amir ɗin Allah ya kiyaye Amir ɗin danakewa tanadin auran Nabiha ƴar dubuty Govenour ki wani haɗasa da bara gurbin yarinya Rubina ƴar da akai zina aka haifa zan haɗa da ɗan danafi so fiye da kowa" Amina tai dariya itama ta mike tsayan "To Umma wai kina zaton barta zamuyi ta zauna tare da shi daga zarar ya aure ta zamu aika da ita lahira a dabarance bayan nan kinga batada kowa komai zai zama na Amir" "Ke nidai mubar maganar nan da ina murna kinzo da sabuwar dabara amma kinzo kin kauce hanya bari nayi magana da hajiya laurah maji mai zataje" Amir ya gyara zama zuciyarsa na ayyono masa da kyakkyawar surar Rubina ya ce "Ai hajiya kawai ayi yanda Anty tace inaga kawai hakan zaifi mana sauki wajan ganin an kawo kashen munafuka Rubinan nan nima na tsaneta wallahi gaba ɗaya Baffa yafi sonta fiye da kowa a gidan nan nida kafin ki gaya min wace ita bakiga kishinta da nake ba amma sanda nasan ita ɗin ba jininmu bace sai naji salama" "Kai Amir kiyaye ni har abada bazan taɓa bari jini na ya haɗu da Rubina ba ku tashi kuban waje" Amina ta taɓe baki tareda gyara zamanta a falon taɗau wayarta tana dannawa Amir ya shige ɗakinsa Hajiya tai samanta a fusace ta dannawa Hajiya Laurah kira RUBINA Kwanan Baffah shida a Londan muka juyo nageria bayan likitoci sun bani magani zamu koma karshan wata bayan bikin uwair, lafiya kalau muka sauka kano da sanyin asuba Yaya Amjad yaje ya ɗakko mu muna shiga gida na wuce ɗakina nayi sallar asuba sannan na kwanta barcin gajiya ban tashi ba sai goman safe, nai wanka sannan na ciro wayata daga handbag ɗita system ɗina na wajan Khalipha ina kunna wayar sakon Bakon masoyi yafara shigowa wayata _"Wellcome back masoyiya, nayi farin cikin dawowarki da murnar samun lafiyar idanunki a shirye nake yanzu da ki bani dama na fallasa maki sirrin zuciyata ki bani dama na bayyana gareki masoyiya"_ dariya nayi bayan na gama karanta sakon kiran Yayna ya shigo na ɗaga bamu jima muna waya ba yagayan zai shiga office inya dawo zamuyi waya wai na kwanta nayi barci sosai na huta sanan kar nayi wasa da abinci na rinka ci har rabonsa, nai dariya kurum bayan na katse kiran, da yammacin ranar sai ga bakon lamari Ummi ta shaida min ina da bako a waje na tsaya ina kallonta da mamaki ta haɗe rai tana faɗin "Ko bazakije ba" bance komai ba na saka mayafin abayar dake jikina saman kaina na gyara zaman glass ɗin idanu na nakai kofa zan fita daga falo ummi ta kira sunana a sanyaye "Rubina Ki tsaya kiyi tunani kan abinda bakon ya gaya maki karki yanke hukunci da garaje" tana gama faɗar haka ta mike ta shiga ɗakinta, jiki sanyaye zuciya fal zulumi haka na karaso farfajiyar gidan namu can karkashin wajan hutawarmu dake kusa da garden na hango mutum zaune kan farar kujera yai kasa da kansa yana danna waya, na karasa wajan idanuna a kansa na ja ɗaya daga cikin kujerun dake ajje a wajan na zauna, sai sannan ya ɗago mukai ido biyu, na wangale ɗan bakina ina dariya "Kai amma dai har naji faɗuwar gaba walahi da Ummi tace min wai nayi bako ashe kaine" yai murmushi idanunsa a kaina ya ce "Kin zaci saurayinki ne" "Saurayi kuma kai Allah na tuba ina ni ina wani saurayi ƴar karamar nan dani karatu fa zanyi" "Aure bai hana karatu Husnah, kamar yanda kika sani Sunana Nuraddeen Kamal mahaifina haifaffan garin gaya ne mun taso acan munyi karatun pramary da sakandiri duka acan kafin muka dawo cikin garin kano da zama inda naci gaba da karatu na karanta low a bayaro university mahaifina ba wani mai kuɗi bane yanada rufin asiri yana da gidan kansa inda muke rayuwa da mahaifiyarmu Innah mu uku ta haifa nine babba sannan kanina Lameen da kanwarmu Sakina dake aure yanzu a katsina mahaifinmu ya rasu shekaru goma da suka wuce lokacin na gama jami'a na tafi low school yanzu haka muna zaune da Innarmu a gidanmu dake gandu ni lauya ne mai zaman kansa kanina Lameen yaci gaba da kula da shagon mahaifinmu dake ƴan kaba ni kuma nakan ɗan taɓa kasuwancin zamani" nabi Nuraddeen da kallon tausayi hakanan nake jin tausayin wanda duk ya rasa ɗaya daga cikin iyayansa nakan hango kaina randa zan wayi gari na rasa Ummi ko Baffah na aduk ranar danai wannan tunanin wuni nake bana iya cin abinci tausayin Nura ya mamaye ilahirin zuciyata "Allah yajikan Baba, yakarawa Innah lafiya" "Amin na gode Husnah, bazan ɓoye maki ba Rubina na kamu da sonki watanni da suka shuɗe bazance ga rana ba amma dai nasan kawai ina sonki Husnah nai magana da Baffah ya ce nazo na nemi soyayyarki inkin amince ya bani ke na fito ayi mana aure" dam gaban Rubina ya faɗi a fakaice take ɗan karewa Nuraddeen kallo ba laifi kyakkyawa ne to amma inta amince da shi kuma ya zatayi da karatunta kuma mai zatacewa Yay Uwair daya ce karta kula kowa zaiyi magana da Baffah taci gaba da karatu to ga kuma Baffah ya turo mata da saurayi, data tuna dokar Baffah sai jikinta ya kuma yin sanyi, "Kinyi shuru Husnah inban maki ba ki faɗa min saina nemi wata" "A'ah ni bance maka ba ama dai ka bani lokaci nayi tunani" "Zan iya kuwa Husnah na faɗo sosai fa to amma dai na baki nan da dare dan Allah" kaina na ɗaga alamar to ya mika min wayarsa ya ce samin lambarki na karɓa nasa masa na mika masa ya kafe ni da idanunsa ya ce "Yimin save" ban musa masa ba sabida sabo nane na riga na saba da Yayana Uwair bama musu komai yace to nake cewa nai masa na mika masa ya ɗago ya kalleni bayan yaga sunan da nasa "Haba Rubina kuma bari kiga" bayan ƴan dane danne dayai a wayar ya ɗago min ita ya nuno min "Love" na faɗa ina zaro idanu ya karɓi wayata yasa min lambarsa yai save ya nuno min screen na wayar na zaro idanu tareda dafa hannu a kirji nace "Na shiga uku My one ya zaka sakan wannan sunan Yayna zaiyi faɗa fa" annurin fuskar Nuraddeen lokaci ɗaya ya ɗauke ya mike yamin sallama nima na mike harya fara tafiya sai naji ba daɗi na ce "Kayi hakuri" ya juyo yadawo kusa da ni ya tsaya yana kallona nai kasa da kaina "Mai akayi na bani hakuri kin rigada kin gaya min ne kina da wani" "Wani kuma wallahi banda saurayi Yayna fa Uwair aika san sa" na faɗa ina zaro idanu "To saime dan yaga wannan sunan basai ki gaya masa ba saurayi kikai karki sake ki canzan suna" kaina kurum na ɗaga alamar to yai gaba ina kallonsa ina nan tsaye wayata tai kara alamar shigowar sako _Jiki da zuciya sun shaida min yau abar kaunata tayi bako sai dai ki sanar da shi ke tawa ce a duniya insha Allah baki da miji inba ni ba_ bakon masoyi na faɗa a fili ban masa reply ba nai gaba abina bayan naga fitar Nuraddeen daga gidan namu Kamar da wasa saiga soyayyar Nura da nake kira da Nuri ta mamaye duka zuciyata ashe da gaske Yaya Aliyu yake dayace soyayya nasa nishaɗi lokaci ɗaya na rikiɗe na zama masoyiya kusan kullum muna kan network nida Nuri muna musayar kalaman soyayya Khalipha yayi ta min dariya wai Allah shima soyayyar nan zai fara yagan ni bini bini ina kasa kasa da murya kamar muna fuka, shirye shiryan bikin Uwair muke gadan gadan Baffah yasa aka kawo mana kayan fitar biki da zamuyi daga shagonsa na kwari lace biyu atamfofi bibbiyu takalmini jaka da mayafi duka iri ɗaya dubu ɗari biyu Yay meer yasa min a account waina kwalliya sannan na karo abinda nakeso in kuɗin bai ishe ni ba na kira sa, ni mamakinsa nake ga hidamar biki gata gini danma ya gama kasan gaba ɗaya saman ne ya kulle wai ba yanzu zai gyara ba Raiha ta zauna a kasan, nidai nasan tabbas da biyu yai haka yana nufin saman na budurwar sa ne Husnah kamar yanda yataɓa faɗan saura kwana goma bikin ya dira garin kano ba zama kusan tare muke yawon rabon aibi da shi duk kayan fitar bikinsa duka yana waje na yau saura mako guda bikin gida yaɗau saiti Baffah yai gyara a gidan an canza duka kujerun gidan an suba sababbi a ko wanne part, ƴan uwanmu na adamawa sun fara zuwa ina zaune kamar wacce aka tsikara na tafi wajan Uwair ganin har sha biyu saura bai shigo part ɗin mu ba harna tura kofar ɗakinsa zan shuga sai kuma nai saurin maida kofar na rufe na fara kwankwasa kofar "Wane a shigo" Yaya Uwair yafaɗa lokaci guda na shiga da sallama yana tsaye yana saka kayansa cikin babbar jaka ɗakin duk a hargitse "Yayana yanaga haka kamar mai shirin tashi?" na faɗa bayan na zauna akan gadon, ya kalleni murnushi shimfiɗe kan fuskarsa na rasa kalar wanan kallo na Uwair dayake yimin shi a ko yaushe, "Tashin zanyi ma ai Rubina gidan nan yafara tara baki bana son hayaniya kin sani, ga gobe ƴan uwan Hajiyarmu zasu zo azo ayita surutun ƴanzu wane ga yar wance kaki aura ka zaɓo bare kindai sansu da surutun tsiya gidana zan koma kawai na rinka leko ku" take naji zuciyata tai rauni na kifa kaina jikin hannu na na fara kuka ina ce wa "Yanzu shikenan inka tafi na daina ganinka, saidai kazo mana na yan mintina kilama sai kayi sati baka leko mu ba shikenan in kazo kano ba anan zaka rinka sauka ba gidanka zaka wuce" Uwair yai dariya yana cigaba da saka kayansa cikin jakar yana kallon yanda take kuka "Yawwa cigaba da kukan inda ma nake godewa Allah kuka kyau yake kara maki ba muni ba" Ai inajin yafaɗi haka saina fara share hawayan fuskar tawa na kakalo murmushi nayi ina sauke ajjiyar zuciya "Kiyi hakuri Rubina nima ba da son raina zan barki ba akwai lokaci, lokaci na nan zai zo da zamu rayu a waje ɗaya" na wangale bakina kamar kofar gari na mike nai tsallan murna ni a zato da fassarar da zuciyata taiwa maganar tashi yana nufin zan koma gidansa da zama ne, sai naji daɗi na zanzare muka cigaba da haɗa kayan ya gama haɗa jakar ya jawo bedsite drower ya fara haɗo takardunsa yana saka su a wata karamar jaka nakai hannuna kan diary ɗinsa cikin zafin nama yakai hanunsa kan nawa ya fisge da sauri garin saurin ya saka a jaka ya

Chapter 9 of 11