Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 11
binsa da kallo jin a karo na farko na rayuwata da yayi min magana da tsawa "Yayana gaba ɗaya yau ka canza min kamar ba kai ba ai ba yau nafara shiga ɗakin naka ba baka taɓa min magana na daina ba ɗazu kamin tsawa yanzu kamin magana da ihu shikenan Yayana na lura ka daina kaunata zan canza yaya" na mike zan fita ya ruko hannuna ya dawo dani kusa da shi ya zaunar yana leka fuskata ya ce "Ko kaɗan ban daina kaunarki ba Rubie ina nan a yayanki mai sonki har gobe" "To mai yasa ka canza Yaya Meer yaufa ba gidan wacce mukaje daga masjid ka dawo damu gida kuma kazo ka rufe kanka a ɗaki ko abinci baka ci ba" "Naci abinci wajan Hajiyarmu ɗazu dana dawo daga sallar la'asar, da dare ki dafamin abinci zanci bayan sallan insha" "To mai zakaci?" na tambayesa ina turo baki "Yaya Meer baida wani zaɓi duk abinda hannun Rubina ya dafa zaici koda kuwa maɗaci ne to zaiji daɗin sa kamar sweet" Nai murmushi ina kallonsa na mike zan tafi na sunkuyar da kaina dai dai kumatunsa na sumbata nace "Yayana Ilove you da yawa da yawa gaba ɗaya cikin yayuna ba kamar kai da yaya Amjad" "Amjad amjad kuma nidai bana so a kuma haɗani da kowa a cikin yayun nan na zama nine na gaba gaba kuma ɗan gaban goshi" nai dariya na mike na fita ina masa bye, Uwair ya maida kansa jikin kujera ya kwantar yana sakin ajjiyar zuciya ya mike ya koma ɗakinsa ya ɗauki diary ɗinsa ya maida cikin jaka ya fito da choculate da yawa daga cikin jakarsa ya ajje a gefan gado ya maida jakarsa ma ajjiyarta kana ya zuba choculate ɗin a wata leda ya fito daga part ɗin nasu, kai tsaye ya wuce part ɗin Ummi ya tarar Rubina bata nan ya bawa Ummi ledan choculate ɗin ya ce ta ajjewa Rubina, Ummi tai godiya ya fita a gidan cikin motarsa Rubina saida nai sallar insha sannan na shiga kichin nama rasa mai zan dafawa Yayana Uwaimeer ina cikin kicin ɗin Yaya Aliyu ya shigo kamar mai neman wani abun naga yana ƴan dube dube a kichin ɗin ni kuma ina tsaye ina tunani har ya karaso inda nake "Rubina mai za'a dafa mana da daran nan" "Yah Aliyu nima kaina ya kulle na rasa mai zan dafawa Yay Uwaimeer" annurin fuskar Yah Aliyu ya ɓace lokacin dana ambaci Uwaimeer, yaja tsaki tareda duba agogo ya fice daga kichin ɗin, banji komai a zuciyata ba na ɗakko indomie guda biyu na ɓare ta na zuba mai a prying pan mai yawa na soya indomie min na tsane ta a colander sannan nai gretting attaruhu da albasa a gretter na zuba su a gefe kana na fasa kwai na zuba specias kaɗan a ciki na ɗebi albasa da attaruhu danai gretting na zuba a ciki na soya kwai guda bakwai, na dafa carrot da pies sannan na soya attaruhun danai gretting na tsaida ruwa bayan ya tafasa na kawo green beans da pies da cartot na zuba a ciki na ɗan lokaci sannan na zuba indomie da specias ɗin cikin indomie ɗin na dafata na ƴan mintina sannan na juyeta a plat na kawo wainan kwain na ɗora akai na fito da shi daga kichin ɗin na kawo danning na ajje na ɗau wayata na kira lamban Uwaimeer "Sorry gani nan a hanyar part ɗin ku" yana gama faɗin haka ya katse kiran minti biyu tsakani ya shigo da sallama, bayan sun gaisa da Ummi dake zaune a falo tana kallo ya hawo step inda danning yake yaja kujera ya zauna yana kallona, na tura masa plat ɗin indomie ɗin gabansa ya buɗe idanu ya ce "Wow dilicious gaba ɗaya kin tada min yunwa" nai murmushi tareda dafe fuskata da hannu biyu ina kallonsa yanda yafara kai indomie ɗin bakinsa yana gyaɗa kai "Rubie yanzu inna tashi fita na tafi ɗakina ta ina zanbi?" fashewa nayi da dariyar data saka Ummi kwala min kira, na mike na tafi har sannan ina dariyar tambayar da Yaya Meer yamin, wani kallo Ummi tamin kallo na ki shiga tai tayinki ina dariya nace "Afuwa Ummina bazan sake wannan dariyan ba Yay Meer nefa ya fara santin abinci" tai murmushi tana gyaɗa kai tareda maida hankalinta ga kallon da take tamin alamar na koma, na ɗakkowa Yay Meer lemun gora da ruwan Gora na ajje masa a gabansa dana tarar har yaci rabin indomien "Watonko maganar gaskiyya Rubie girkin nan yai bala'in daɗi gaskiyya mijinki yai dace da wacce ta iya sarrafa tukunya" "Kai dai yay Meer kaci indomie kawai maiye wani kawo maganar aure ana zaune kalau kama daina maganar nan kar Baffah yaji bana son yamin maganar aure harga Allah karatu nakeso ina fata da burin na zama babbar likitar mata" "To Allah ya ida nufi amma dai ban gani anayi ba a gidan nan karatun ƴa mace" "Za'a fara daga kaina ni zan kafa wannan tarihin insha Allah zan zama likitar mata a cikin gidan nan gaban Ummina da Baffana gefe ga Yayana Uwaimeer" shidai baice komai ba harya gama cin indomie ɗin ya sha ruwa da lemu muka ɗan taɓa hira kafin muka mike muka nufi part ɗin Baffa, atare muka shiga wajan Baffah yana zaune kan carfet ya kishingiɗa a jikin tum tum yana lazami gefansa ga Hajiya Zainab data gama jera masa kalolin kulolin abinci ga bwols da plat plat a ajje kusa da shi, Baffa yana fara'a sosai ya amsa mana sallamar mu yana aika mana da murmushi "Maraba lale da zara da wata" Yaya Uwaimeer ya zube a gaban Baffa ya ruko hannunsa kafin yai masa wata runguma sai hawaye "Lala mai zan gani Uwaimeer hawaye kuma duk na daɗin gani na ne" "Baffah baffana nai misssing naka da yawa sati kusan takwas ban saka ka a idanuna ba" "Kai Uwaimeer bana son sharri ko shekaran jiya ai munyi vidio call dakai kaifa ka zaɓi tafiya ka barmu kai ka zaɓi wannan aikin mai tsanani" "Baffa Aikin nan taimako ne wa kasa fa" "To masha Allah ubangiji ya taimaka Uwaimeir yakare ka" "Amin" muka faɗa lokaci ɗaya nida Yay Meer kamar waɗanda suka haɗa baki, Baffah yabimu da kallo kana yai murmushi ya ce "Ɗazu mun tafi masallaci Mahmud ke gayan wani labari mai daɗi masha Allah nida na zaci tanan zanji wannan labarin mai daɗi kuma sai na jisa ta wani waje daban to nayi farin ciki da hakan Allah yasa ayi damu" Uwaimeer yai kasa da kansa yana murmushi a zuciyarsa kuma yana nanata maganar Abba yana son gano mai yake nufi, duk da bansan maine ake addu'a akai ba amma ni na amsa Amin ɗin Baffah kafin yaci gaba da faɗin "Jibi lahdi nida Mahmud da abokina Alhaji Sada zamuje in mukaje mai gaba ɗaya zamuyi da kuɗi da sadaki zamu saka wata biyu zan maka lefe sai akai daga baya sannan ka karasa ginin ko?" kai kurun Uweir ya gyaɗa alamar e batare dayace komai ba na kalli Yay Meer daketa doka murmushi yanzu na fuskanci inda maganar tasu ta dosa waton dai auran Uweimeer da Raihana za'a tsayar take naji wani kunci da bansan na maine ba ya mamaye zuciyata na fara kokarin mikewa zan bar wajan Uweimeer ya dafe min hannuna ya hanani ta shi "Baffah ka manta da yaran nan kaci abincinka" Hajiya Zainab ta faɗa tana wani haɗe rai tareda aika min harara a fakaice "Rubinan Baffah kinci abinci? in bakici ba zonan muci tare wanko hannunki" na ɗago zanyi magana karaf idanuna cikin na Hajiya Zainab aiko ta aika min sakon harara da kallon gargaɗi nai kasa da kaina ina murmushi nace "Baffah munci abinci da Ummina ɗazu" "Masha Allah, to zuba min" nakai hannuna saman kula zan buɗe Hajiya Zainab ta warce sarving spoon ɗin dake hannuna zatai magana Baffa yai saurin katse ta da "Shikenan Hajiya Zainab ya isa basai kince mata komai ba, Rubina kuje Allah yamaku albarka" muka mike nida Uwaimeer muka fito har sannan hannunsa na cikin nawa mun baro part ɗin Baffah kenan muka hango Hajiya Umma na tahowa da sauri Uwaimeer ya saki hannuna yai saurin wucewa gaba kamar ba tare muke ba wani kallo tabimu da shi tun daga nesa ina hango kallon datake aiko min ta cikin hasken daya hasga gidan "Uwaimeer baka jin magana maina gaya maka ɗazu? Hajiya Umma ta tambayesa bayan ta tsare sa da idanunta yai kasa da kansa, na tsaya kusa da shi nima nayi kamar yanda yai "Muna fuka ɓace min daga nan kuma wannan yazama karo na karshe da zan sake ganinki da ɗana, mayya kawai" gaba nai sau biyu ina juyowa ina kallon Uwaimeer dake yiwa Umma magana harna shige part ɗinmu suna nan tsaye suna magana, a karshe a fusace tai baya ta fasa shiga part ɗin Baffa, ina shiga ɗakina wayata tai kara alamar shigowar sako saida nai shirin barci nasa kayan sanyi riga da wando naja bargo na lulluɓa sannan na ɗauki wayata na duba messages ɗin daga Yay Meir _Kiyi hakuri Rubie ki yafewa Hajiya muna nan kalaman datake binki da su insha Allah wataran zata gane gaskiyya nidake jini ɗaya ne ba abinda zai rabamu ina tare dake zan zame maki bango majinginarki a ko yaushe_ nai murmushi ɗan wannan kalaman ya wanke min duka kuncin dake zuciya ta najima na yafewa Umma hajiya, nai addu'a na maida kaina na kwanta Hajiya Zainab data fito daga part ɗin Baffa a maimakon ta nufi wajan ta saita nufi part ɗin Umma Hajiya ta sameta zaune nan falonta tana duba littafin muwadɗa malik kallo ɗaya Umma Hajiya tayiwa Hajiya Zainab ta maida hankalinta ga karatun da take "Hajiya kina kallon abinda ke faruwa a cikin gidan nan kin zuba idanu ko to ki kuka da kanki randa wani abin kin ya fito daga wajan wannan shegiyar yarinyar Rubina da ɗanki Uwaimeer" Hajiya Umma ta mike a fusace ta karasa gaban Hajiya Zainab tana huci ta dafa kafaɗar hajiya Zainab ta ce.......... 07039793439 [7/27, 4:58 PM] maman sauban: 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode four4️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* "Mugun nufinki yabiki Zainab mummunan zaton da kikewa Uwaimeer a gidan nan ki gansa a kan ƴaƴanki" "Banzo nan danna gaya maki magana mara daɗi ba kawai nazo na nuna maki abinda tunaninki baikai nan ba amma tunda haka kika ce shikenan" ta juya ta fice faga ɗakin ta koma part ɗinta tana mita "Umma ni kinzo sai mita kike min waya kaiki wajanta bayan kinrigada kinsan halin Hajiya bata ragawa kowa a gidan nan ba" "Rahama daga zuwa gaya mata gaskiyya sai abin ya zama da gayar magana to na zuba idanu kamar yanda ta zuba nata in wani abin yafaru mu ƴan dariya ne" "Allah ya kyauta" Rahma tace ta mike tabar falon ta koma ɗakinta Kwana biyun da Yay Meer yamana a kano jinsa nayi kamar wanda mukai wata biyu sabida washe gari wajan goma na safe muka fita nida shi gidansa dayake ginawa dake unguwar bechi sabuwar unguwace hakan yasa gina ginen ma ɗai ɗaiku ne muka shiga gidan da har an rufasa anma yiwa wani wajan plastar dan kasan ma an gama plaster ko ina saura kaɗan ya kammala muka gama leka ɗakunan kasan muka fara hawa step ɗin da zamu hau saman benan "Wato a rayuwa ina kaunar saman bene, Yay Meer nifa zan iya rayuwata a sama bazan sakko ba inba wani waje zani ba" yai murmushi ya jingina ta bango ya tsaya daga tafiyar da yake yana kallona da murmushi a fuskarsa ya ce "Kawai kice inna tashi samar maki miji cikin abokai na na samo maki wanda gidansa bene ne" nai dariya ina cigaba da hawa step ɗin muka karasa saman "Hmmm wayyo rayuwa Yay Meer nan ace ni za'a kawo ko to ina jin da kaina zanzo na tsara komai yanda falona da sauran rooms zasu kasance" yai murmushi batare daya ce komai ba muka gama kallon gidan muka fito yana lissafa min abinda yarage za'ayi a gidan, har muka karasa gidan Anty Sanah hirar gidan yake bamu jima sosai a gidan ba dan yau ziyara zamuyi saida mukaje duka gidan yayunmu mata waɗanda suke aure anan garin kano sai ƴamma muka koma gida bayan mun biya ta shoprite ya min uban siyayya haka muka koma gida da niki nikin siyayya a hannu na washe garin da zai koma calaber nayi kuka sosai har muka rakasa filin jirgin saman malam Aminu kano yatashi ina kuka sosai kamar wanda akace min yatafi kenan, Muna tafe a mota sanda muke hanyar komawa gida Yaya Amjad sai faɗa yake min "Kin wani cikan mota da ihun kuka kamar wanda aka ce maki yatafi kenan karyar banza nan da gobe ma kila kin manta da shi" shiru nayi ban tanka masa ba yinin ranar sam gidan bai min daɗi hakan yasa na tattara na tafi gidan Yaya Aliyu kamar yanda na saba nakanje wani bin nai sati guda na dawo Allah yahaɗa jini na da Anty Hannah matar Yaya Aliyu, Fauzan da Ni'ima mai sunan Ummi su nake wasa da su suka ɗebe min kewar Yay Meer har zuwa sanda Yaya Aliyu yadawo daga office shima yai murna sosai da zuwan nawa bayan yai wanka ya huta daga gajiyar aiki bayan sallar mangariba yace muzo mu fita shopping nida shi da Fauzan muka fita cikin nishaɗi sai bayan sallar insha muka dawo gida Anty Hannah na tsokanarmu ina nata siyayyan, nai dariya kawai batare dana ce mata komai ba na nufi ɗakin Fauzan, washe gari dazan tafi scool tare muka tafi da yaya Aliyu da Fauzan kasancewar Fauzan schools ɗinsu bata kai tamu nisa ba yasa shi aka fara ajjiyewa kafin ya ɗauki hanyar school ɗinmu a hanya yana tuki jefi jefi yana kallona da murmushi "Wai nikan Rubina samarinki nawa?" saurin kallon Yaya Aliyu nayi ganin mun haɗa ido sainai saurin saka hanuna na na rufe fuskata ina dariya "Au dariya ma na baki, tambayarki fa nayi ko bazasu lissafu ba?" kaina na girgiza ina murmushi kana na ce "Banda saurayi ko ɗaya Yay Meer yace min karna kula saurayi inna bawa wani saurayi damar zuwa gidanmu to Baffa zai fara min maganar aure ni kuma Allah ya gani karatu nakeson yi bana ra'ayin aure" Yaya Aliyu ya taɓe baki kana ya maida hankalinsa ga tukin motarsa can kuma ya ɗago ya kalle ni ya ce "Komai Yaya Uwaimeer komai Yay Meer to ya tsaya yana maki wayo shi yana can yana soyayya da budurwarsa ke kuma kin killace kanki kin hana kanki kula kowa ai soyayya bata hana karatu ko wanne zaman kansa yake, ki buɗe kunnaki da kyau ki jini haka ki buɗe idanunki daga rufe sun da Uwaimir yasa kikai kisani Rubina soyayya wata duniya ce mai zaman kanta soyayya nishaɗin rayuwa ce, musaman inkayi katari da wanda yake sonka kake sonshi, Rubinan Ummi ki buɗe zuciyarki kawai ki bawa masoyanki dama su fito su bayyana maki irin son da suke maki" bance masa komai ba nai shuru ina tunanin maganganunsa har muka karasa school ɗinmu sanda zan fita daga motan na juyo na kallesa na ce "Yaya Aliyu kace na bawa masoyana dama su bayyana min son da suke min to ai ni ba wanda yataɓa zuwa ya ce yana sona" "To dama wane xai zo yace yana sonki kin sa a ranki bazaki soyayya ba yanzu kiyi tunani mai kyau" na fita daga motar bayan munyi sallama ya bani 500 na break sabida ban tawo da abinci ba sai goran lemu dana ruwa kawai dana ɗakko, Uwaimeer tun a cikin jirgi yaji gaba ɗaya kewar Rubina ta kamasa har wani sanyi sanyi yakeji a jikinsa sanda ya sauka a airport na garin yai waya a barreck ɗinsu akazo aka ɗauke sa tunda ya shiga gida ya kasa nutsuwa, kewa tunanin Rubina gaba ɗaya sun addabi zuciyarsa ya kunna data ya hau online mirmushi yayi sanda yaga stetus ɗin Rubina na one hourse daya wuce hotansa ne da emojis na kuka a kasa tai rubutu _Safe trip my Lovely broth_ lallausan murmushi yayi kana yai mata reply shima da emojis na kuka ya kashe datan ya fita wajan barreck ɗin,Washe gari Monday sassafe yai shiri ya nufi office ɗin mejor Usman Karaye, Rubina sanda nadawo daga school gaba ɗaya maganganun da mukayi da yaya Aliyu ke min yawo aka da gaske ne abinda ya faɗa kodai shin tayaya zan tabbatar da gaske ne soyayya nasa nishaɗi yinin ranar nazarin maganan nake har sanda Yay Meer ya kirani muka gaisa kamar yanda muka saba mun gama hirar da muke duk dare akan karatuna yana shirin katse kiran na aka masa da tambayar abinda yake damun zuciyata tsawon yinin "Yay Meer wai da gaske soyayya nasa nishaɗi wai soyayya wata duniya ce mai zaman kanta?" da sauri Uwaimeer ya mike zaune daga kwancan da yake harda wani dafe kirji ya ce "Rubie waya faɗa maki wannan maganan?" "Yaya Aliyu ne fa ya gayan da safan nan da muka tafi school ni kuma na wuni maganan naci min rai na rasa wazanma wannan tambayan da a gida nake to tabbas Ummina zan tambaya kuma sai gaka ka kirani" wani gwauran numfashi Uwaimeer yaja ya koma ya kwanta ya lumshe idonu yana murmushi "To yanzu mai kike so nace" "Ka gaya min gaskiyya ne ko karya, in gaskiyya ne to tabbas nima ina son tsaida saurayi" "To ba gani ba ki tsaida ni kawai" "Subhanallah Yay Uweir Rubina ce fa" "Au ai na zata da Assama'un Baffa nake magana" mukai dariya lokaci ɗaya kafin na katse kiran ganin Uweir na neman katse min tunani na danake son zurfafawa har nayi barci da tunanin araina washe gari bayan nayi sallah da asuba na kunna wayata sabida ka'idar Ummina ne kashe waya a duk dare nima abin saiya shiga jikina kullum karfe goma na dare nakan kashe wayata, ina kunna wayata sakone yafara shigowa na wata sabuwar lamba _"Barka da safiya tauraruwar mata abincin ruhina, zuciyata na rayuwa kullum da begenki da kauna kullum ina mafarki da burin ganin ranar da zan fallasa maki abinda ke raina ki bani dama na buɗe maki zuciyata tauraruwa ta"_ Na karanta messages ɗin yafi sau goma karo na farko na amsa tex messages daga masoyi duk da bansan daga waye ba amma lokaci ɗaya naji zuciyata ta kamu da son ganinsa banyi reply wa sakon ba amma kam matuka naji daɗin sakon, dan koda nadawo daga school kafin na tafi Islamiyya saida na kuma karanta messages ɗin wani ikon Allah da dare ma da zan kwanta saiga wani zazzafan massages ɗin nayita karantawa ina murmushi ni kaɗai, abu kamar wasa saiga shi kullum messages saiya shigo min sau ba adadi a rana na zafafan kalamai masu daɗin gaske da sanya zuciya a shauki Hajiya Umma zaune suke saman fararan kujerun dake ajje kasan bishiyar data yiwa gidan rumfa "Hajiya Haule na rasa yanda zanyi da yarinyar nan nifa kullum na buɗi idanu na ga yarinyar nan na tuna alakar ta da Uwaimir zuciyata bata min daɗi ina zargin da wani abin makale a zuciyar Uwaimeer amma kullum inna titsiye yaron nan ce min yake ba komai nidai ina jin tsoron faruwar wani abin, ita kuma shegiyar ga bakin jini har yau fa babu wanda yataɓa zuwa yace yana sonta koda wasa nifa da cewa nayi kodai gidan bokanya zamuje amin aiki akan Rubina a sami wani yazo ya aure ta ko zuciyata ta sami salama" Dariya Hajiya Laure tayi kana ta gyara zama ta ce "Ni daɗina dake wutar ciki ina ma haɗin Uwaimir da Rubina shegiyar da batada asali zaiyi gangancin aura idan yana son Rubina to ai bazai taɓa karɓar tayin auran Raihana ba duk da ina ganin gangancinki wallahi Hajiya Binta da har kikayiwa Uwaimir tayin auran Raihana har mai Rahina suke da shi aduk cikinmu kawaye kinsan itace koma baya a cikinmu itace mijinta baida karfi duk da mai kuɗi ne kinsan ai bai kai mazajanmu ba karma mijinki yaji labari mai makon ki shiga ki fita ki samo masa mata ƴar minista ko ƴar wani kusa a gwamnati kamar mu ko kuma cikin ƴaƴan manyan masu kuɗin kasar nan kika ɓige a gidan Rahina har mai suka mallaka da har zakiyi sha'awar haɗa zuri'a da su" "Hajiya Haule sam ni bana burin ɗana ya auri ƴar mai kuɗi wanda ubanta yafi ubansa arziki to idan kai haka mai kenan kace mata mai bare ma kinsan Uwaimir duk cikin yarana shine mai karamin karfi to mai zaisa na ɗakko ƴar da zata zo ta raina min shi koba komai na yaba da tarbiyar Raihana tabbas Rihana tayi matukar kokari wajan bawa Raihana tarbiyar da ita ta jani" "Hmmm to faɗa mana mu ƴaƴanmu basu da tarbiyya" "Nifa bance ba ranki ya daɗe" Hajiya Bintu ta faɗa tana ƴar dariya "Kece da abin haushi ana nuna maki gabas kina yamma ai auran ƴar manya babban jari ne kina gani saida na shiga na fita wajan ganin Faisal ya auri ƴar gwamna sannan zuciyata ta sami salama, Hajiya Umma tai dariya tareda ɗaukar hand bag ɗinta sukai sallama Hajiya Haule ta mata rakiya har wajan motarta ta shiga ta tashi motan ta ɗau hanya 🔯🔯🔯🔯🔯 Mama oyoyo oyoyo mama abinda Marwa da Amira ke faɗa kenan suna tsallan murnan dawowar Mamansu da yau kwana huɗu kenan rabonsu da ita, Salima dake kwance a ɗaki tana chat ta fito da sauri jin ihun Marwa da Amira "Umma ina wayanki?" Salima ta aika mata da tambayya "To uwata na saida ita" Umma ta faɗa tana kokarin zama kan kujera ƴar tsugunno dake tsakar gidan taja Amira jikinta tana shafa kanta ta ce "Uwata nayi kewarki da yawa inata tunaninki" "Mama mu kuma bakya tunaninmu?" Marwa ta faɗa tana turo baki gaba "Marwa nayi mana ai gaba ɗaya nake tunaninku har wancan sakaran Sani baya ma gidan ko naji banji hayaniyarsa ba "Mama yau kwana biyu kenan bamu saka sani a idanunmu ba tun shekaran jiya da yazo bai sake dawowa ba yau da safe naiwa Baba maganar sai cewa yayi maiya dame sa ko ina yaje ai zai dawo ba yaro bane shi ai "Hmm lamarin Babanku saidai addu'a na rasa gane kan mutumin nan" Mama na rufe baki saiga Baban ya shigo yana masifa "Ke Gambo ina kike Gambo ko baki dawo daga yawon ta zubar ɗin naki ba ne? to inma bata dawo ba ke Salima zo kiji wai an kama Sani yana police stetion saiki shirya kije nidai bazanje ba bare sisina tai kuka" "Malam wai ko baka gani ne naga gani a gabanka amma kazo kana ta ɗaga murya" "Au ashe kin dawo to maza kije division na sharaɗa ɗanki na can" yana gama faɗar haka ya shige ɗakinsa bai sake kallon inda Mama take ba, Mama ta share hawayan da suka zubo daga cikin idanunta ta ce "Kai jama'a Sani so yake ya kashe ni da raina inba haka ba sau nawa ina gargaɗinsa yadaina abinda zai kaisa wajan ƴan sanda amma bayaji duka duka yau she aka karɓosa daga division na sheka Allah kana gani ka shirya min wannan yaron" "Mama duk ba wannan ba ayi kokari aje kafin a mika sa kotu azo ana kici kicin biyan kuɗin tara" "Salima toba magana bace ta kuɗi wallahi ko biyar ban sauka da ita ba a garin nan aikin girki mukaje kaduna fa gidan masu kuɗi sosai wallahi wayata na siyar nai kuɗin mota amma mutanan nan wai sai cewa sukai mu bada account number zasu turo mana kuɗaɗanmu nidai gani ma nake ba turo mana zasuyi ba," "Kema Mama nace maki ki daina yawon bin gidan bikin masu kuɗin nan kina masu girki kayi masu bauta amma su suna kyashin su bitaka hakkin ka kiga fa yanda kukai a gidan bikin Hajiya Maimuna haba Mama" "Salima kenan inna zauna mai zamuci ko zuba maku idanu zanyi, kinadai ganin halin da ake ciki kin rigada kin san halin babanki" Salima taja tsaki ta koma ɗaki tana mita, washe gari sassafe ta tafi stesion ɗin da akace Sani nacan yinin guda

Chapter 3 of 11