Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 11
ta kwashe a wajan ƴan sandan sunki bata belinsa dole ta dawo gida cikin damuwa suke tattauna maganar da Marwa da Mamansu, "Mama ni gaba ɗaya zaman nan haka yadaman kullum bakada kuɗi a hannunka kana kallo mutane kowa na kashe kuɗi musamman a break na makaranta yanzu fa takai matakin bana ma iya fitowa cikin makaranta sanda aka fito break sai kawaye na su rinka min dariya suna nuna ni wai na cika mammako da son kuɗi" Marwa ta faɗa tana share hawayan idanunta, Mama ta mike ta shiga ɗaki tana goge hawaye ta ari wayar Salima tasa wata lamba bugu ɗaya ana biyu aka ɗaga kiran "Assalamu alaikum" "Wai kece a daran nan ko dai zaki zone mu kwana yau zan baki ko nawa kike so" "Ba wannan ba Sammani an kama ɗana Sani Salima yau taje wajansa amma a police stesion amma sunki bata balinsa haka ta dawo nace bari na kiraka ko zaka taimakan" "Kinsan wannan ba wata matsala bace Abu kawai dai dole ayi abin nan da hausawa ke kira ban gishiri na baka manda gobe zanje inda yake zan kawo maki shi har gida da dare ke kuma kizo mu kwana tare kuma dole zaki bani dama naji zumarki ba kamar da ba" Mama tai shuru ta kasa cewa komai tana tunanin shin ta amince masa ko kuma? to inta ki yarda tayaya zata fito da Sani daga wajan ƴan sanda "Ya kikai shuru ko na baki lokaci kiyi tunani nan da goben" "A'a shikenan Sammani na amince inya fito ɗin zan zo inda muka saba haɗuwa" Alhaji Sammani ya gintse wayar ya kece da dariya harda kwanciyya a kan gadon dayake zaune ya kalli yarinyar dake ta barci kan gadon yana jin wani shauki na daban da burin ganin safiya tayi yaje ga ƴan sanda ko nawa zai bayar a saki yaron indai zai sami cikar burinsa akan Abu matar da suka haɗu watanni huɗu da suka wuce da farko sun haɗu a facebook ta fara da turo masa sassan jikinta a hoto yana biyanta har takai ga sun fara haɗuwa yana rage zafi da ita yana biyanta a cewarta inya biyata yaranta take saiwa abinci duk yanda yakai ga son ya shige ta taki basa dama sai dai kawai su haɗu a ragewa juna zafi ya biyata su rabu, sai gashi a ɓagas gobe zai sami cikar burinsa, a ɓangaran Mama ma shiru tayi tana tunani a zuciyarta ita kaɗai "Na shiga uku ni Abu mai nake shirin aikatawa ne haka, ina zan kai gingimeman zunubin nan da aure na, kawai kima daina wani tunani ki amince kawai baga shiba ga kowa ma indai zaki sami abinda zaki rufawa ƴaƴanki asiri" taji ɗaya ɓangaran na zuciyarta ya bata amsar datafi aminta da ita hakan yasa ta mike ta fita ta bawa Salima wayarta ta kalli Marwa dake rungume da Ameerah datai barci tausayin yaran ya kamata ta koma ɗaki ta zauna can dai ta fito ta kwankwasa ɗakin Babansu Salima ta shiga da sallama "To Abu da kika shigo min ɗaki da daran nan mai zan maki?" "To Yanzu Baban Salimah bazan shigo ɗakin ba sai zan maka wani abu?" "To ai tambayya nayi mai zakimin ke fa duk wata ɗawainiyya da hakkin miji dake kan matarsa ba wanda kike min" "Kai wanne kake min abinci kake bani ko sutura kake min, ɗan hakkin nan na kwanciya ma yaushe rabon daka sauke inda nake godewa Allah ma dayasa gidan nan namu ne da kila haya ma saina biya" "Gidanmu kuma, gidana dai" "Kai kace haka Baban Salimah ta ina ya zama gidanka inace filin nan gadarsa nayi daga mahaifina a ginin ma nawa na saka kiwo na gaba ɗaya na kauyanmu saida na saida su ni naci karfin ginin nan kai karashe kawai kayi, ai nayi kokari ma danace gidanmu" "To rashin kunya zaki min Abu ko zagina zaki kimin gori fito ki gayawa duniya cewa bana baki komai ko kice bani na gida gidan nan ba" hayaniya suka fara kamar Baban Salima ya kai mata duka "Mama, mama dan Allah ki fito" Mama taji Muryan Marwa na faɗa daga bakin kofar ɗakin Baban nasu, Maka taja tsaki ta fito daga ɗakin tana mita, "Mama dan Allah ki daina biyewa Baba kuna hayaniyar nan" "Marwa barni barni na rinka maida masa da martani auran mutumin nan banga abinda ya tsinana min ba banda masifa haba duk hakurin danake baya gani Allah yana kallo duk halin dana faɗa Babanku shine sila" "Yi shuru mama karya jiyo yazo yaci gaba da sababi" 07039793439 [7/28, 9:39 AM] maman sauban: 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode five5️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* Rubina na kwanta kan gado na rungume wayata bayan nai kissing ɗin wayar karfi da yaji na zama masoyiya na kamu da zazzafar kaunar wanda ban sani ba, ban taɓa ganinsa ba sai dai shi da alama ba karamin sani yamin ba ƙaran danaji wayana yayi alamar shigowar sako yasa na zabura da sauri nakai hannu na ɗau wayan kamar zata zame daga hannuna sabida karkarwar da hannun nawa keyi kamar yanda na zata reply ne daga masoyina wanda nakewa lakabi da bakon masoyi _"Da gaske? kin tabbata kin shirya gani na?"_ da sauri na maida masa amsa da _Tabbas na shirya kuma na tabbatar zuciyata na bege da shaukin son ganin bakon Masoyinta_ _Bako a zuciyarki kuma Ruby haba na wuce bako Ruby ni ɗan gidane a zuciyarki na riga nasan yanda nake jinki a zuciyata kema haka kike jina na baki assament kiyi tunani a duk cikin maza waye zuciyarki tafi so da kauna ki kwatanta ni da shi_ na karanta reply ɗin daya dawo min da shi nai saurin typer masa _Yay Meir shine na farko a zuciyata ina matukar sonsa matsayinsa na yayana kuma jigona_ saurin kwantawa yayi a gado bugun zuciyarsa na karuwa sanda ya karanta wannan sakon nata yai saurin kashe wayan gaba ɗaya ya janyo wata dake ajje kusa da shi ya kira wata lamba Sanda naji ring na wayana har zabura nai dan sai zuciyata ta bani bakon masoyi ne ya kirani abinda bai taɓa yi ba kenan saidai sakon messages ko chat ta whatsapp, ganin Yay Meeer ke kirana ya sanyaya min jiki nai picking call da sassanyan murya "Assalamu alaikum Yay Uwaimeer barka da dare" "Barka dai Rubina ya kike ya gida ya su Ummi Baffah dasu Khalipha" "Kowa lafiya duk da dai ni bana gida ma" "Kina ina?" ya tambayya yana haɗe rai kamar yana gabanta "Gidan Yaya Aliyu" na basa amsa a zafafe ya fara magana cikin hargagi kamar yana magana da sa'ansa "To zaman me kike a gidan wani? ke ina gidanku maine amfanin naku gidan salon kizo kina yiwa wata can bautar yara na baki nan da gobe ki koma gida malama" yana gama faɗan ya katse kiran nai shuru tareda zubawa wayata idanu kamar ina ganin Yay Meer a cikinta "Mai yake damun yayana kwana biyu mai yasa yake shirin canza min daga yayana mai laushi da saukin kai yana son rikeɗewa ya zama zazzafa mai zafi a komai nasa karan shigowar sako yasa na buɗe sakon a wayata _"Kiyi hakuri Rubie na maki faɗa kawai bana son zamanki gidan Aliyu ne kin gane ki koma gida gobe sorry na maki faɗa bazan sake ba na kasa controll na zuciyata ne dake min wani tunani daban"_ Kashe wayar tawa nai gaba ɗaya na maidata kasan filo na kwanta bayan na tofawa Fauzan addu'a nima nayi na shafa na maida kaina kwanta Uweimeer haka nan yaji zuciyarsa bata kwanta da Aliyu ba ba rami mai ya kawo rami maine haɗinsa da Rubina da har zai zauna yana gaya mata mai akeji a soyayya tabbas yazama dole ya tsaurara akan Rubina kada shi yana nan azo a masa sakiyar bada ruwa, ya mike daga inda yake zaune ya fito harabar barreck ɗin nasu ya tsaya ya zubawa waje ɗaya idanu yana tunanin tayaya zai fara bayyana wannan kudirin nasa daya rayu dashi tsawon shekaru yana makale a xuciyarsa ta yaya zai fahimtar da Hajiyarsa ta yaya zai tunkari Baffah da wannan magana mai nauyi shin zai fahimce shi ko kuma zai ɗauke sa a wanda baiji maganar daya faɗa ba, yau shekaru sha biyar kenan to yaya ma zaiyi da Raihana kai ya Allah, ya jima anan yanata nazari a zuciyarsa kafin ya koma ciki yai shirin kwanciya tareda cin alwashin gobe in Allah yakaimu zai kira Daddy suyi magana Washe gari ina tashi daga barci na haɗa kayana na ajje su a gefe Allah yasa ranar bamuda school ana hutun sabuwar shekarar musulumchi ina yin breakfast nace tafiya zanyi duk yanda su Yaya Aliyu da Anty Hannah suka takuramin da tambayar mai yasa zan tafi bance masu komai ba kawai nai shuru "Rubina kodai wani laifin mukai maki batare da mun sani ba" "Anty baku min komai ba hasalima inajin daɗin zaman gidan nan fiye da gidanmu amma dai tafiya zan" "To indai kina jin daɗin zama da mu mai zai sa ki kafe sai kin tafi yanzu kila dai wani abun mukai maki batare da mun san mun makin ba ko kuma wata ta zugaki ki tafi cikin su Sanah" "Allah yaya Aliyu ba komai kawai inason ganin Ummina" Aliyu ya ɗaga kafaɗa tareda taɓe baki ya ce "Ai saiki tashi na maidake gidan daman ai ke kika kawo kanki" nai dariya kawai na fito da trolly ɗita Aliyu ya fita da ita Anty Hannah ta bani Humra masu kamshi da arebian oud na mata godiya ta rakoni har bakin motar Yaya Aliyu dayake ciki harya tashi motan yana jiran karasowata inako shiga na kulle motan yaja motan saida muka fara tafiya kana ya juyo ya kalle ni da murmushi a fuskarsa jefi jefi yakan juyo ya kalleni saida mukai nisa yai parking gefan titi ya kashe motan ya ɗora kansa kan sitiyarin motar yana kallona na ɗan lokaci kafin ya sauke numfashi ya buɗi baki zaiyi magana komai ya tina sai yai shuru yaiwa motar key muka ci gaba da tafiya bai sake kallon inda nake ba har muka karasa gida, Ummi tayi farin ciki da dawowata haka ma Baffah da muka tarar a gida bai fita kasuwa ba yau ya ce yana hutawa ban kira Yaya Uwair a waya ba kamar yanda shima bai kiranin ba kamar yanda muka saba nadai masa messages na gaya masa na koma gida banga reply ba na damu kamar na kirasa amma saina daure naki kiran nasa, kamar wasa saiga shi mun shafe mako guda nida Uwaimir bamuyi waya ba abinda bai taɓa faruwa ba a tsakanin mu, dana gayawa Ummi sai take gayan suna daji ne inda yake ba network gaba ɗaya na damu kullum inata tunanin halin da yake ciki har muka fara jarabawar fita daga scoundry sati biyu cur mukai bamuyi waya da Uwaimeer ba sai yau dawowata daga school kenan yau acan muka wuni jarabawar tai zafi sosai hakan yasa na dawo kaina na ciwo sosai da kyar na iya cin abinci nasha paracetamol na shiga ɗakin Ummi zan kwanta saiga Usham da gudu da wayata a hannunsa "Yaya Rubina yaya Uwaimeer ke magana" ai kusan wuntsulowa nayi daga gadon sai gani baje kan center carfet ɗin dake gaban gadon hannuna har rawa yake wajan karɓar wayar ina jin muryan Uwaimeer na fashe masa da kuka "Yaya kadawo gida ba abinda ya sameka yaya mutum nawa aka kashe bakaji ciwo ba" "Mutum nawa aka kashe kuma Rubina kamar waɗanda suka tafi yaƙi kawai mun zauna a dajin ne ana zargin akwai ƴan ta adda a ciki shiyasa yau mun dawo gidajanmu ba wandai yai karamin rauni ma bare wani babban ciwo, ya kike ya jarabawa a lissafina kun fara tun wancan satin ko?" "E! mun fara" "Ina fatan dai baki sawa kanki damuwa ba ko kiyi karatu sosai ki fito da sakamako mai kyau Rubie" "Insha Allah" "Yawwa kyauta ta sabuwar waya dal a kwali randa kuka gama zan zo da wani soprise ɗin da zai bugi zuciyarki" "Yay Meer in zuciyata ta buga kuma na mutu fa" "A kekeke daina wannan maganan aiba wannan bugun zuciyar ba" nai dariya jin lokaci ɗaya ya rikece daga ambaton mutuwa" "An saka rana fa angon Raiha" "Kina farin ciki" "Sosai ma tun bikin yaya Aliyu fa bamu sake biki ba a gidan nan sai nakan nan da kowa ya tama masa su Anty Sanah har sun fara tsara event" "Wanne event kuma Rubina ni Allah yasa ma ina kasar lokacin ina ganin ina cikin waɗanda za'a zaɓa zuwa Americha" "Yay Meer tafiya kuma?" na tambayya murya a raunane kamar zanyi kuka "Tafiya ta tsawon wata shida ma Rubina ki tayani addu'a a tabbatar da sunana a ciki waɗanda sukai nasara tafiyar alheri ce Rubie idan har yakasance na dawo to mataki ne na nasara da karin girma dana albashi da zan samu" "Allah yazaɓa abinda yafi alkhairi" "Amin Rubina, agaida sauran mutan gidan banyi waya da kowa ba a gidan ke na fara kira bari na kira Hajiyata da Baffah" ya katse kiran nai shuru tare da zubawa wayata idanu, bilhakki na dage da addu'a ba dare ba rana akan Allah yasa Uwaimeer yasami damar tafiyar nan Americha kamar yanda ya ce kullum mukai waya yana daɗa nanata min hakan yasa na maida hankali sosai har tashin dare na linka gefe ma ina addu'ar sa'ar jarabawa ta har zuwa ranar da mukai pepar karshe munsha ihu tsalle da murnar kammala makaranta kamar yanda ƴan candy kanyi munyi hotuna sosai an karɓi adress na juna tareda musayar lambar waya ga ƴan aji gaba ɗaya sanda muka gama hidimar mu na fito daga school inda driver ke parking yana jiranmu nida Sulaiman naga wayam na koma cikin school ina neman Yaya Sulaiman amma baya nan dana tambayi mai gadin makarantarmu yasanar min yanzu suka tafi, na fara tafiya zuciyata na kuna yau dai kam saina tari Yaya Sulaiman na karta masa rashin mutumci akan abin nan da yake min saina nuna masa bafa tsoransa nake ji ba, ina gudun ɓacin ran Baffah ne shi yasa nake raga masa 🔯🔯🔯🔯🔯 A shirye ya fito cikin dakakkiyar shadda marun colour ya kafa hular zanna bukar wanda ta makutar shiga da shaddan sai tashin kamshin turare yake, sanda ya karaso ɗan madaidaicin falon mahaifiyar tasa ganin bata nan kai tsaye ya shiga bedroom ɗinta inda yake zaton tana nan, tana zaune kan sallaya alamun tunda ta idar da sallar azahur bata tashi daga kan daddumar ba ya tsugunna a gabanta ya zuba mata idanu ganin tana jan carbi "Innata zan fita office ɗin Brister Zubeir munada shari'a gobe mai zafi shi yasa zamu tattauna kilama zamu kaiwa wanda muke karewa ziyara yana birsin" "Allah ya tsare min kai Nuraddeen ya maka albarka yabada sa'a ya kare min gabanka da bayanka" "Amin amin innata nagode" ya mike ya soma tafiya harya kai bakin kofar fita daga ɗakin ya juyo yadawo wajan da take zaune kan dadduma ya ce "Innata kin manta baki min ɗayar addu'ar ba" Innah tai murmushi haɗe da girgiza kanta kana ta ce "Allah yabaka mata tagari wacce zamu zauna lafiya a gidan nan ta kular min dakai bayan kasa ta rufe idanuna" "Innah kullum kina zancan matuwa ai ba'asan gawar fari ba kilama nine na farko da zanbi Babanmu" "Tashi tashi Nura maza jeka Allah ya maku albarka yadawo dakai lafiya yabaku mata tagari ya haɗa min kanku" "Amin" yafaɗa bayan ya mike ya fita yana murmushi, ya karasa fitowa ɗan madaidaicin driving space ɗin dake cikin gidan wanda ke ɗauke da motoci biyu, yai murmushi ganin motar kaninsa Lameen da alama yana ɗakinsa yana barci ya shiga motarsa bayan ya buɗe get ɗin gidan ya fitar da motar waje ya fito daga motar ya maida get ɗin ya kulle sannan ya shiga motar yaɗau hanyar office ɗin Barister Zubeir yahau babban titi yana tuki cikin nutsuwa kiran Barister Mu'az daya shigo wayarsa yasa yaɗan rage gudun dayake yaɗaga kiran suna magana baiyi aune ba yaga yarinya sanye da Uniform a gabansa yai saurin sakin wayar yafara kokarin taka burgi amma ina kafin ya ankare yaga yarinya tayi wani tsalle ta faɗi a kasa motar ta tsaya cak ya fito a ruɗe ya ɗora hannunsa aka sanda yaga an ɗago yarinyar bata alamar motsi Ayi hakuri yau ba yawa 07039793439 [7/30, 9:41 AM] maman sauban: 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode Six6️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* Hannu ya ɗora aka hankali tashe yabi matasan da suka cicciɓi yarinyar da kallo kafin kuma yaga ansakata a motarsa yai saurin shiga shida wani dattijo a wajan suka fara zuwa wajan ƴan sanda dake ɗan nesa da wajan da abin yafaru aka basu ɗan sanda sannan suka nufi hospital da yarinyar, kasancewar asibiti ne mai zaman kansa nan da nan aka yi emergency da yarinyar bayan awa guda likita ya fito bayansa gadone mai ɗauke da mara lafiyar Nurse na turawa suka nufi wani word ɗin da ita daban, Nuraddeen da gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake ya kasa zaune ya kasa tsaye yabi Dr ɗin zuwa office bayan sunyi musabaha Dr ya nuna masa abin zama ya zauna yana sauraron bayanin da Dr ke masa "To Alhamdulillah ba wata babbar matsala bace kawai karaya ne a hannun dama sai buguwa a kanta da rauni kaɗan munyi nasarar gyara karayan munyi dresing na wajan raunin goshinta insha Allah nan da ɗan lokaci zata farka lafiya kalau" "Ok nagode Dr" Nuraddeen ya faɗa yana kokarin mikewa zai bar office ɗin Dr ya mika masa takardar magunguna data kuɗin da zai biya ya karɓa ya fita, yana fitowa ya zauna a recepsion yai kokarin saita kansa ya kira kaninsa Lameen, cikin barci Lameen yafara jin ring na wayarsa ya buɗe idanunsa da suke cike fal da barci yakai ganinsa ga madubin wayar ganin sunan yayansa na yawo bisa yasa ya ɗaga kiran cikin muryar barci ya ce "Hello Yaya Nura" "Lameen kanata barci ba, maza dan Allah zo nan dangi ka ganni a hospital ɗin annury yanzu dana fito na haɗu da tsautsayi na bige wata yarinya dan Allah ka tawo min da Atm card a ɗakina cash ɗin jikina basuda yawa" "Subhanallah Yaya Nura yanzu ya ake ciki bata dai ji mummunan ciwo ba ko?" "E! karaya ne kawai kadai tawo yanzu ana son magani sannan dan Allah karka gayawa Innarmu tazo ta tashi hankalinta ka bari in anjima na koma gida saina gaya mata" "To to gani nan yanzu yanzu Yaya yanzu zanzo ko wanka ma bazan tsaya yi ba ni gaba ɗaya ma na ruɗe ko tuki bazan iya ba nape zan hawo" "To" kawai Nura yace ya katse kiran ya mike ya nufi pharmacy na cikin hospital ɗin, yasai magungunan ya shiga ɗakin da aka kwantar da budurwar yarinyar da duka duka bazata wuce shekaru sha bakwai ba, ya kalli Nurse ɗin dake kokarin jona mata drip ya ce "Dan Allah ko zaki laluba aljihunta koda waya a ciki a samu a sanar da gidansu" Nurse ta kalli ɗan sandan dake tsaya bakin kofa ya mata alama da tayi abinda Nuran ya ce ta laluba jikin Yarinyar ta fito da wayar da gaba ɗaya ta ragargaje koda aka dannata ma taki kawowa, Nura ya ciro simcard na wayar ya saka a wayansa ya fara bincika lambobin kan layin BAFFANA UMMINA MY Lovely brother sune kawai lambobin dake adane akan sim ɗin zuciyarsa tafi karkata akan ya kira wanda yagani an saka my lovely brother da alama yayanta ne Uwaimer sauri sauri yake komai nasa so yake ya kammala komai kafin karfe biyu na rana yabi jirgi zuwa kano so yake ya sauka kano kafin lokacin da Rubina zata dawo gida so yake yau ya fallasa mata asirin dake binne can kasan zuciyarsa na tsawon shekara da shekaru yau kan jinsa yake ya shirya fafatawa da kowa BAFFA HAJIYA UMMA DA UMMI tunda yasan faɗawa Rubina wannan asirin na zuciyarsa dai dai yake da fashewar wani sirri da zai iya tarwatsa farin cikin Rubina da Ummi gaba ɗaya amma ya shirya insha Allah zai zamewa Rubina bango kuma rumfa insha Allah zai share mata duk kanin wani hawayanta da zai zuba sanadin maganarsa, karfe ɗaya da rabi ya baro office bayan sunyi sallama da Cepatein ɗinsu ya biya ta kasuwar waya ya samowa Rubina savuwar waya dal a kwali Inpinix mai kyau da tsada ya dawo gida nan barreck bayan yayi wanka ya shirya ƴan tsirarun kayansa na ciki boxer da singlate a karamar jakar goyo ya saka wayan a jakan ya fito harabar barreck ɗin inda Samuel ke jiransa zai kaisa filin jirgin sama, Uwaimeer yahau bayan mashin ɗin Samuel ɗin yaja suka fita suna tafe suna hira hirar da rabinta kan yanayin aikin sune har suka karasa aiport ya sauka a mashin ɗin sukai sallama ya nufi ciki, awa guda cikin jirgi ta kawo su garin kano bayan ya fito daga cikin airport ya shiga da zai kaisa unguwarsu wayarsa tayi kara ganin sunan Rubina yasa yai murmushi ya ɗaga kiran da ƴar dariyarsa "Ƴammatan Candy nayi diley ko afuwan sister laifin Captein ne" "Assalamu alaikum" ras gaban Uwaimeer ya faɗi jin muryar namiji jikinsa yai sanyi sosai bugun zuciyarsa ya karu yana fita fat fat jin abinda ake faɗa masa ta wayan "Yanzu kuna wanne hospital to?" "Nan Annury hospital" "Gani nan" Uwaimeer yai magana da mai nape ɗin ya gaya masa inda zai kaisa yanzun kana ya kira BAFFA yasanar masa hankali tashe Baffa dake zaune a kasuwa yasa Amjad suka nufo hospital ɗin Uweir hankali tashe ya shiga hospital ɗin ya kira lamban Rubina Nureed deen ya ɗaga ya fito ya masa jagora ɗakin da Rubina ke kwance mintina kaɗan Baffah da Amjad suka iso, ganin a halin da Rubina take ba karamin tashi hankali Uwair yayi ba, ganinta kwance vata ko motsi, Uwaimer ya sake dubata sosai kasancewarsa na likita ya tabbatar tana nan lafiya barci kawai take "Amjad ka kai Uwaimeer gida ya samu ya cire wannan kakin ya huta gajiyar hanya ka tawo da Fatima Ummi" "Baffah dan Allah basai na tafi ba ka barni anan da dare bayan ta farka saina koma gidan" "Kariga ka sani bana magana biyu," Baffah ya maida hankalinsa ga Nura da Lameen dake rakuɓe waje ɗaya kallo ɗaya zaka masu kasan suna cikin tashin hankali, ya yafito Nura da hannu alamar yazo, Nura yakaraso gaban Baffa ya tsugunna har kasa "Kaima ka tafi gida ka huta kaji ɗan samari mun rigada mun san kaddara koda mutuwa Rubina tayi lokacinta ne yayi to alhamdylillah tana ma raye, Amjad a sallami police ɗin nan shima yatafi bakin aikinsa" "Tam Baffah" Amjad ya amsa yana kokarin zaro kuɗi daga aljuhun sa na wando, Lameen ya kama Nuraddeen suka futa bayan sunyi sallama dasu Uwair da ɗan sandan dake lasar leɓe ganin Amjad ya fito da sababbin kuɗi yana ƙirgawa Ummi tsaye a compound na gidan BAFFA sai faɗi in faɗa suke da Hajiya Zainab mahaifiyar Sulaiman da take karewa Sulaiman faɗan da Ummi ke masa "Zainab na rantse da Allah ki fita cikin magan nan inba haka ba zan matukar saɓa maki wallahi zan nuna maki ni ɗin jinin kanuri ce zan nuna maki bansan tsoro ba banda rashin mutumchi motar danshi kaɗai aka siya ko danshi kawai aka ajje driver yarinka kai sa makaranta kunbi kun tsamgwami yarinya itada gidan ubanta" "Ahayye nanaye cass gidan ubanwa nace gidan ubanwa nan ne gidan Uban Rubinan can dai adaije can anema mata wani uban amma ba dai Baffah Yarima ba wallahi, kuma sulaiman abinda kayi kamin dai dai Allah ma yataimaka da yau kun gama school ɗin dana gaya maka daga yau karka kuma sakewa ka zauna mota ɗaya da wannan shegiyar ƴar wama ya sani kilama ungulu ce ta koma gidanta na tsamiya, kuma idan baki nuna min ke jinin kanuri bace ba yau baki haifu cikin Yagana ba" Ummi ta fusata sosai jinta take iya wuya zaryar ta biyu a motarta zuwa makarantar su Rubina amma ba ita ba dalilinta

Chapter 4 of 11