Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 11
faɗi ya buɗe, ware idanuna nayi da sauri ganin zanen hoto na ya zagaye sa da zanan hart na dafe kirji, ya wani aika min da banzan kallo ganin yanda na dafe kirji ina ganin bugun zuciyarsa ya kara karfi har ina iya juyo bugun fat fat da sauri sauri irin dai ya kaɗu ɗin nan, na sauke ajjiyar zuciya bance komai ba saidai a zuciyata girma da kimar Uwair ta karu sosai "Yayana wai ashe har haka kake ga kaunar ƴar kanwar nan taka?" baice min komai ba har ya gama ɗaukar abubuwan mihimmai ya tisa keyata muka fita ya ce naje nai sallah na rakasa yaci abinci yunwa yake ji bai karya ba, ya wuce masallaci ni kuma na koma part ɗin mu, bayan nai sallah nai wanka na fito rikeda wayata danake duba sakon da bakon masoyi ya turon sarkin naci _INA KANO_ Iya abinda ya rubuta kenan alamun yazo kano kenan ban masa reply ba na fita waje inda Yay Meer ya sanar min yana bayan gidanmu yana jirana bayason Hajiya taga fitarmu tare shi yasa, na zauna cikin motar ya mata key yana kallona na mika masa wayata tareda masa bayanin sakon da ake turo min da wata lambar daban da ba tada dayai bloking ba, ya taɓe baki tareda maido min wayar kan cinyata yaci gaba da tukinsa "Ki basa dama yazo mana koba ce maki yai zai zo ba bayan kin rigada kin karya alkawarinmu kallonki fa kawai nake da baki gayan kin fara soyayya da Nura ba na sani tun ina Calabar aka sanar min tunda shi kika zaɓa Allah ya sanya alkhairi" "Nifa wallahi yaya ba....bame ba Rubina?" yakatse ni da saurinsa "Cewa zaki bakya son sa to yaudarar sa kike kenan toya zakiyi da Baffah dake shirin kiranki a yau ya tambaye ki kina son Nura" na zaro idanu adai dai sanda wayarsa tayi kara Amir dake zaune kofar gidansu Salima suna hira akan idanunsa Uwair suka wuce shida Rubina a mota ba shiri yaiwa Salima sallama ya koma gida ya shiga yana kwaɗawa Hajiyarsu kira ya isketa can bedroom ɗinta "Kina nan Umma kina shirin aurawa Raihana Uwair ga can ya na yawo a gari da Rubina ya ɗauketa sun fita ko ina suka tafi bakiga wankan da sukai ba nifa na fara zargin Uwair laluɓe yarinyar nan yake ke kuma kin kasa fahimta" "Kai Ubanka Amir Allah ya tsare can dai kan ƴaƴan wasu amma badai Uwair ba mutumin banza matsa ka ban waje ɗan iska kawai" Amir da zuciyarsa ke tafarfasa ya juya ya fita yana jin badaɗi shiga harga Allah zuciyarsa ta biya da Rubina ɗakinsa ya faɗa ya kunna sigari ya fara zuba ba kakkautawa Har kiran da takewa Uwair ya katse bai ɗaga ba ta sake maida masa wani kiran wannan karon bugun farko ya ɗaga "Assalamu alaikum hajiya bar...bar gaisuwarka duk inda kake maza maza zo ina son ganinka yanzu yanzu" "To" Uwair ya faɗa cikin ladabi ya ajje wayar ganin kiran ya katse yai kwana suka koma ɗaya hannun da zai maidasu gida "Ki dafa min abu mai sauki Rubie hajiya ke kirana" kaina kurum na ɗaga masa alamar to muka shiga gidan kai tsaye ya wuce ɓangaran Hajiya ya sameta tsaye a bedroom ɗinta tana zagaye a zafafe tayo kansa kamar zata kai masa duka ta ce "Uwaimir na gaji da zagaye zagayan nan na ka ka fito fili ka gaya min maike tsakaninka da shegiyar yar nan Rubina" Uwair yai kasa da kansa kafin a hankali ya aro jarumta ya furta "Hajiya sonta nake so na aure" afusace Hajiya ta fitar da hannu ta kwaɗa masa mari a fuskarsa tana huci kamar zakanya ta ce "Ni zaka kalli tsabar idanuna ka gayan kana son wannan bara gurbin ashe gaskiyya Amir ya gayan akwai wata kullalliya a tsakaninku da yarinyar to inaso ka buɗe kunne kaji da kyau ko bayan raina ni Bintu ban amince maka ka auri wannan bara gurbin ba idan kuma kai gangancin auranta ko bayan raina Allah ya isa tsakani na dakai ban yafe maka nono na daka sha ba Uwaimir" da sauri Uwair ya zube kan gwiwowin sa hawaye suka fara zuba daga cikin idanunsa "Kiyi hakuri Hajiya duk abin bai kai haka ba ki yafe min dan Allah karki fushi danina shiga masifa dan Allah hajiya" "Tashi ka bani wuri" ba musu ya fito daga ɗakin nata kai tsaye ya faɗa na Amir yana shiga warin sigari ya cika masa hanci da sauri Amir yai wulli da karan sigarin dake hannunsa ya makale jikin bango ya ɗaga hannayansa alamar sallamawa Uwair da yake jin zuciyarsa na masa zafi ya shaki wuyan Amir ya dunkule hannu yakaiwa bakin Amir naushi take ya fashe ya fara zubar da jini idanunsa suka firfito waje, Uwaimir ya kwantar da shi saman gado har sannan hannunsa na kan wuyansa ya ɗora masa kafarsa ɗaya kan ruwan cikinsa yana huci kamar zaki ya ce "Ni sa'anka ne Amir da har zaka kawo gulmata ka haɗani da mahaifiyata bakasan daman haushinka nake ji ba kan abinda kukaiwa Rubina na kyale ka kawai ne sabida Hajiya kar ranta ya ɓaci shine zaka zo ka haɗani da ita yau zan nuna maka shekaru takwas ɗin dana baka a duniya ba a banza ba" Amir da jikinsa yai sanyi ganin yafara hango mutuwa kusa yasa ya haɗe hannuwansa waje ɗaya alamar roko Uwaimir ya sakesa ya fara tarin wahala, Uwaimir ya haɗa kan Amir da fuskan gadon yabuga Amir ya saki kara, har Uwaimir ya kai kofa zai fita yaji Amir na faɗin "Allah ya isana kuma wallahi saina rama akan Rubinan" Uwair yai wani miskilin murmushi ya haɗa hannuwansa guda biyu ya buga suka bada sauti ya nuna sa da ɗaya alamar gargaɗi ya fice daga ɗakin, rai ɓace ya shiga ɓangaransu ya faɗa ɗakinsa ya fara zagaye a ciki zuciyarsa ba daɗi kwakwalwarsa ba abinda dake amsa kuwa a ciki irin kalamin Ummansu "Ko bayan raina ka auri Rubina ban yafe maka nono na daka sha ba," "No" ya faɗa da karfi tareda kaiwa miror ɗin dakinsa hannu ya tarwatse a ɗakin tamkar wani mahaukaci haka yafara yin wurgi da duk abinda yazo hannunsa yana ihun "Karya ne" a haka na shigo ɗakin na same sa ya hargitsa ɗakin hannunsa na zubar da jini, da sauri na ajje Food flask ɗin hannu na na isa inda yake na rikesa lokacin dayake kokarin buga kofar toilet "Uwair yayana lafiya maiya sameka maine" naja sa na zaunar gedan gado ina kallo yana kallo na "Rubina akwai alkurar mutuwa yimin na mutu dan Allah kafin sonta yai ajalina, Rubina yau zan sanar dake wani sirri na zuciyata data ɗauki tsawon shekaru tana dakonsa, ki fahimce ni Rubina dan Allah ki fahimce nima vada son raina zan sanar dake haka da wuri ba nakasa jurewa idan naci gaba da rikon wannan sirrin a zuciyata to tabbas gaf nake da rasa raina ko kuma zuciyata ta buga na mutu lokaci ɗaya ko na zauce na rasa hankalina shikenan idan na haukace kowa saiya guje ni ko" na fashe da kuka tareda faɗawa jikinsa na rungumesa sosai ina shashshekar kuka shima kuka sosai yake bamuyi aune ba muna a wannan yanayin mukaji an buɗe kofa an shigo ɗakin na ɗago na kalli bakin kofar na mike da sauri jikina na mazari sabida tsoron abinda zai biyo baya...... 07039793439 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode 1️⃣4️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* "Uwaimir, ashe duk maganar da mukai a banza ta tashi kazo kasata a jikinka kila da bamuzo bama da tuni labari ya canza" Amina tayo kan Rubina dake tsaye jikinta na rawa sosai ta ɗaga hannu zata kai mata duka uwair ya tare ya shiga tsakaninsu yana aikawa da Amina wani kallo "Matsa ka bani waje na daki munafukar yarinyar nan so take yanda aka haifeta ta hanyar zina ta jajiba mana masifa muma mu sami mugun iri a dangi" "Anty ya isheki haka kisan mai bakinki zai faɗa akan Rubina karki jawo wa kanki masifar da bazaki iya maganinta ba" sak Amina tayi tana kallon Uwair da mamaki "Mai kake nufi?" "Abinda duk zuciyarki take nufi akan Rubina nima shi nake nufi a kanki Anty" Anty ta ciro takalmin dake kafarta ta nufi Rubina Uwair yai saurin saka Rubina a jikinsa bayan ya mata rumfa ta yanda duk dukan da za'a mata bazai sameta ba sai dai ya sauka akansa, Anty Amina ta juya tana kallon Hajiya dake tsaye saroro bakin kofa tana salati, "Lalle Uwair ka nuna min iyakata" Hajiya iya haka kawai ta faɗa ta fice daga ɗakin tana kuka, Anty Amina ta aikawa Uwair da wani kallo na gargaɗi ta fice daga ɗakin, nima ina ganin futarsu na fusge daga jikin Uwair na fice da gudu ina kukan bakin cikin maganganun su Anty a kaina, Ummi na zaune a falo taga shigowar Rubina da gudu ta wuce ɗakinta tana kuka, Ummi ta girgiza kanta tasan ba komai ke saka Rubina irin wannan kukan ba inba maganganun Hajiya Umma ba maimakon ta nufi wajan Rubina kai tsaye ta fice daga part ɗin ta nufi na Hajiya Umma, tana kokarin shiga Uwair ya tare ta da sauri yana rokonta da kyar ya samu ta hakura ta fasa shigan ta wuce sashin Baffah dake cikin gidan yau yana hutawa bai fita kasuwa ba, a yanayin yanda yaga ta shigo yasa ya mike zaune kan gadon daga kwancen da yake yana kallonta "Baffah na rantse da Allah idan ba'a bar ɓatawa Rubina rai a gidan nan ba zan bar maka shi" ya kalleta yana murmushi ya ce "Kullum idan kaga ɓacin ran Fatima to akan Rubina ne wane ya taɓa maki ƴar gaban goshin taki" ta zauna kan sofa tana maida numfashi ta dafe kanta tama kasa cewa komai "Kidai kara hakuri Fatima saura kiris Rubina tabar gidan nan na mika ta ga gidan mijinta dana biyewa ta Nura da tuni bikin nan na Uwair tare za'a haɗa da nasu, ki ɗan kara hakuri insha Allah bazata kara wata biyu a gidan nan ba ba wanda zai sake takurata ina kyautata zaton a gidan Nura zataji daɗi insha Allah" Ummi zuciyarta tai sanyi da maganganun Baffah batace masa komai ba ta mike ta fita ta koma part ɗinta ta tarar tuni har Rubina tayi barci HAJIYA UMMA "Uwair karka sake kazo min nan inda nake ka tako nan saina masifar saɓa maka" ya tsaya daga bakin kofar yana kallon mahaifiyar tasa ya ce "Umma na rantse maki da Allah koda nace maki ina son Rubina kika hana ban kara tada zancan ba zuciyata tamin zafi akan abinda Amir yamin ina a cikin wannan yanayin Rubie ta shigo kawo min abinci ta ganni wajan kokarin ganin ta lallashe ni yasa ta rungumeni kin sani ita batasan wane ni a wajanta ba kallon wa take min a zaton ta hakan ba wata damuwa ba ce, kince baki amince min kan son danake mata ba na hakura nabarta bari na har abada koda son Rubie zaiyi ajali na bazan sake furta maki wannan maganar ba fatana ki yafe ni Umma" "Shikenan komai ya wuce kuma ka katse duk wata alaka dake tsakaninku da ita bana so" "Insha Allah Umma zanyi yanda kike so kiyi hakuri" ya juya ya fita daga part ɗin hajiyar ya wuce part ɗinsu ya shuga ɗakinsa ya kulle kansa kafin wani lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufe sa, Ummi tabi Rubina da kallon takaici ganin idanun Rubinan sun tasa sunyi ja sosai, ranta ya kara ɓaci zuciyarta ta dugun zuma ta karasa gaban Rubinan dake zaune saman danning tana cin abincin rananta da bata samu taci da ranar ba sai yanzu da ta tashi daga barci, na ɗago kaina ina kallon Ummi data tsaya a kaina tana kallona "Ina glass ɗinki" "Yafaɗi ɗazu a ɗakin Yay Uwair lokacin danakai masa cus cus ɗin dana dafa masa" "Maiya haɗoki da Mamansa" shar shar idanuna suka kawo ruwan hawaye na fara shashshkar kuka, Ummi ta daka min tsawa a fusace ta kama kunne na "Kina jina daga yau ban yafe maki ba idan idanunki suka sake zubar da hawaye sabida Hajiya Umma a gidan nan ko ƴaƴanta duk wanda ya taka ki kema ki taka sa wanda ya zage ki ki rama bance ki ragawa ɗaya cikinsu ba har ita Bintun idan sunyo kanki zasu dake ki karki tsaya ki gudu nan waje na na ɗau hutun aikina ina ma tunanin ajje sa gaba ɗaya ina nan gida tare da ke nidai nasan Rubina ta jaruma ce karki ragawa kowa a gidan nan duk wanda ya nuna maki yatsa ki karya ni zan tsaya maki" kaina na ɗaga alamar to ina jin huɗubar Ummi na shiga kwanya ta ina jin zuciyata kamar ana ingiza ni ko dama can niba raguwa bace ko a school bana barin kota kwana tarbiyar dana samu daga wajan Ummi ta girmama na gaba shi yasa nake ragawa kowa a gidan amma daga yau na daina barin kota kwana idan hajiya ta zagan bazan rama ba amma zan maida mata da bakar maganar da zata hanata barci "Gobe idan Allah yakaimu sai muje hosputal kiga Dr Sadik saimu siyo wani glass ɗin" "Ummi akwai wani fa ina ganin ma basai an kuma siyan glass ɗin ba yanzu ina gani sosai sosai ba kamar baya ba lokacin da muna london" "To masha Allah, Zan gayawa Uwair yaima magana Dr magana na can landon ɗin in sunce karmu siya saimu barsa" kaina kurum na ɗaga, bance mata komai ba Ummi ta dafa kaina "Kici abinci sosai kinji Mamata ki manta duk wata damuwarsu" "Ummi har Hajiya fa cewa take wai da bata shigo ɗakin ba wayasan abinda zamu aikata, Ummi mai take nufi?" na tambayya da muryar kuka "Nace ki manta da su, abinda suke nufinki da shi zasu gani a kansu insha Allah" Kwana biyu nai bansan saka Uwair a idanuna ba gaba ɗaya na damu ko wayarsa na kira bana samun sa abunda ban sani ba ashe gaba ɗaya ya koma gidansa da zama ko sallama bamuyi ba daga ranar da abin yafaru ban sake saka Uwair cikin idanu na ba sai ranar alhamis ɗin data kama ranar su Anty Raiha zasuyi gaɗa a gidan makama, na gama shiri na tsab kasancewar har gida ta bada gate pass guda biyar aka kawo min na bawa Halisa ƴar yayar Ummi da suka dawo kano daga mai duguri guda ɗaya na gayyaci kawata ta school Nabiha sai ɗiyar kanwar Baffarmu Raudah da suka zo daga Adamawa, Ina sanye cikin shiga ta asalin hausawa riga da zani na yafa wani zanin akaina bayan na ɗaure kaina da ɗan kwali irin na kakanninmu na dauri haka saurama suna sanye da kalar shigar tawa sabida duka atamfan ta ankon gaɗan su Raihanan Ummi ta ɗinka mana jiya muka amso su daga wajan ɗinki, na fito compound ina neman Yaya Sulaiman da muka gama magana da shi da safe zai kaimu na hango yaya Uwair yai parking cikin parking space na gidanmu da sarsar fa na karasa wajansa bugun zuciyata na tsananta nai saurin buɗe masa murfin motar na ɓangaran driver ya sako kafafunsa waje yayin daya gyara zamansa cikin motar yana kallona, ramar dana hango kan fuskarsa ita tafi tada min hankali na rankwafa kamar zan shiga motar na ɗago fuskarsa da hannuna na ce "Yaya bakada lafiya ne naga ka rame sosai" har sannan baice min komai ba idanunsa na kaina "Kinyi kyau kamar a kauye" nai ƴar dariya tareda faɗin "Na gode ama baka bani amsa ba bakada lafiya" "Banda lafiya Rubie zuciyata ce ke ciwo Hajiya ta rabani da Husnah ta" dariya nayi sosai harda rike ciki na jingina da murfin motar inata dariya shi kuma ya kafe ni da idanunsa yana aika min da murmushi, ya katse min dariyar bayan ya aiko min da tambayya "Wannan dariyar ta maice ne?" "Ta murnar abinda Hajiya tayi mana bata taɓa burge ni kamar yau ba danaji wanan maganar banda ma rigima irin taka ina kai ina son wata bayan ga Anty Raiha nai farin cikin jin maganar nan" "Hmm Rubie kenan daga randa kika san wace Husnah a wajena zakiyi kukan dayafi dariyar nan yawa" yana gama faɗar haka ya wuce part ɗin Hajiyarsu ni kuma na wuce part ɗin su Yayan ina neman Yaya Salman ina kokarin shiga babban falon nasu naji kum na bige a goshina na dafe wajan ina ihun wayyo na fasa kai "Ke Rubina nutsu ina hankalinki yake ne kika kwara min wannan kan naki mai kama da alkaki" na wangale bakina ina kallon Yaya Aliyu da bansan maiya kawo sa nan ba "Kai Yayanmu kan nawa ne mai kama da alkaki kodai alkakin kake son ci na sato maka a ɗakin Ummi naga jiya an kawo mata su da uawa hatda dubulam" "Ina zaki kikai wanan shigar kamar a kauyan adamawa" "Wajan bikin Anty Raiha Salman nake nema ya kaimu lokaci na tafiya" "Muje na mika ku ama dai ni inada abin yi ba zaman jiran ku tashi zanyi ba" "A'a to mungode kawai a tashi mu rasa abin hawa ka bari yayan ya kaimu kawai", yaɗan ɓata rai yana harata na dafe bakina ina ƴar dariya nabi bayansa muka koma part ɗin Ummi, na ɗakko wayata naiwa Ummi sallama muka fito nida Yayanmu Aliyu, ina danna wayata bayan na shiga motan naga alamar an min sako na buɗe ina mamkin nacin bakon masoyi dabai gajiya da aiko min da sakonni kala kala a kowacce rana wasu su ɓata min rai wasu su sani dariya _"Kinyi Kyau sosai rayuwata, har abada bazan daina addu'ar Allah ya mallakamin ke ba"_ na goge text ɗin ina jiyo hirar rakin su Nabiha da Halisa a bayan motan, muka karasa naima Yaya Aliyu sallama muka shiga ciki, ba karya waje yayi waje kyau iya kyau amarya tayi munsha rawa da liki, ba kowa daga gidanmu nai zatonma zanga Hajiyarsu Uwair amma bataje ba sai mangariba aka tashi bayan min fito muka tsaya muna jiran abin hawa horn ɗin danaji daga cikin wata sabuwa dal ɗin mota yasa na nufi wajan da alama mai motar mu yake wa magana jikina yaban ɗaya daga cikin ƴan gidanmu ne duk da ban taɓa ganin motar a gidanmu ba, ina karasawa glass na motar yai kasa na zaro idanu ganin yah Meer cikin motar ahankali ya ce "Maza kice su Halisa su shigo bana son wasu su kula nine anan" na zagaya tareda masu alamar su tawo nan, na buɗe front seat na zauna ina kallonsa da mamaki "Sabuwar amaryar sabuwar mota sabuwar rayuwa" yai murmushi yana kallona "Wannan motarki ce Rubina ki daina laruwa da sai wani ya kaiki inda zaki very soon zaki fara zuwa school bana son kina bin driver ko kuma kiyita yawon neman yaya wane zoka kaini tun lokacin da su Amir suka dake ki kan kawai nace su baki key na motata tun sannan nasai mki ita bata karaso ba sai jiya da yamma ɗazu na ɗakkota a gidansu Abokina Naupal" yana maganar ne kasa kasa da wata murya daban dani bansan shi da ita ba, nidai kallonsa kawai nake da mamaki nama kasa cewa komai "Mota mota fa yayana" "Batai maki ba Matrix cefa motar mata, idan batai maki ba sainai masa magana a canzo maki" jikina ya kara sanyi na shiga tunahin shin wane irin kauna ce tsakani na da Uwair dayai min kyautar da ko waɗanda muka fito ciki ɗaya ba wanda yamin "Maganar nan karta fita Rubie shi yasa nake maki ita kasa kasa, na riga na gama magana da Baffah ya amince min tun tuni bayan shi ban gayawa kowa ba ki fahimtar da Ummi kuma ki sanar mata tabar maganar a iya mu hajiyarmu idan taji nasai maki mota zan shiga damuwa" "Ni Yayna nama kasa cewa komai gaba ɗaya ka gama ɗauran jjinin jikina ama zan iya maka tambayya bazakaji haushi ba" kai yaɗaga min yana kallona "Inata mamakin inda kake samun kuɗi haka ka fitar dani waje anmin aikin ido yanzu kuma kazo kasai min mota ga hidimar bikin ka ina kake samun waɗan nan kuɗaɗan" yai murmushin gefan baki kana ya ce "Ana biyana albashi mai tsoka a fannin aikina na soji, gefw guda kuma haka ana biyana albashi kasantuwata na Likitan sojoji, bayan kuɗaɗe sun fara shigo min na saka hannun jari da wani company dake Americha yanzu haka ina kokarin saka wani hannun jari a wani company dake Japan gaba kaɗan yayan nan naki zai zama jan wuya" "Masha Allah nai farin ciki Allah yakara arziki mai albarka, godiyan mota kuma baki bazai iya furtawa ba sai dai zuciya zata cigaba da maka addu'a ako yaushe" bai sake cewa komai ba har muka isa kofar gida yai parking zan shiga gida yaban makullin motar na karɓa na shiga ciki, da gudu na faɗa ɗakin Ummi na ɗane ta "Rubina karki karya ni" "Ummi mota mota Yayna Uwair yasai min" Ummi ta rike baki da mamaki sai kuma ta girgiza kai "Allah sanya alkhairi Uwata yasa rai akayiwa nai farin ciki" na bata key ɗin na sanat mata motan na waje ta bawa wani ya shigo da ita ciki, na tafi ɗakina nai wanka sabida munyi waya da Nura yace min bayan sallar insha zai zo Ina idar da sallah na saka doguwar rigar atamfa na shafa cream na murza hoda da kwalli nabi jikina nai masa ɓarin turare, takwas da kwata nuraddeen ya kirani yace gashi ya iso na fito daga ɗakina naiwa Ummi sallama na fita nida Halisa data biyo ni zasu gaisa ina gafda fita daga part ɗin mu na karasa compound na gidan Uwair ya dakatar dani da faɗin "Rubie ina zaki kika fesa wanan turaran mai kamshin gaske haka Rubina kina da hankali kuwa, maza koma ki wuce ciki" nai sak ina kallonsa na ce "Nurie ne yazo fa sine zanje" "Ki koma nace bazakije ba" na ɗago kai na kallesa ganin lokaci ɗaya ya daka min tsawar da bai taɓa min irinta tsawon rayuwarmu "Amma Yayna inna koma ciki ai ban....kika sake magana anan Rubina saina kwaɗa mako marin da sai jinki ya ɗauke na wuce gadi wuce ciki!!!" na ɗago na zabga masa harara nai kamar na koma ciki sai kuma kawai na juya zanci gaba da tafiya ta.... 07039793439 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode 1️⃣5️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* Ya ruko hannu na ya marairaice fuska yai wani kalar tausayi, sai kuma yaja hannu na a fusace zuwa cikin part ɗin mu, Ummi dake zaune kan seater tana danna laptop ta ɗago tana kallon mu "Lafiya Uwair kake janta haka ko wani abun ta maka" tsabar takaici yakasa cewa komai sai zama da yayi shima kan seater ya dafe kansa yana girgiza sa "Rubina wuce ki tafi Nuradeen na jiranki dare na daɗa yi" na juya na futa ina waigen Uwair dabai ɗago ya kalle ni ba, Ummi ta maida hankalinta ga Uwaimir da har sanan yake rike da kansa "Ama mai yasa Uwaimir kana son Rubina ka kasa sanarwa da Baffanku mai yasa kuma ka je kake kokarin auran wata" yaɗago ya kalli Ummi da idanunsa da sukai ja sosai "Ummi tsoro ne ya hanani cika burina, Rubina itace muradin zuciyar Uwaimir nayi zaton zan iya sjanye sonta ya tsaya iya zuciyata banyi zaton zata fara soyayya da wani ba" ya sakko daga kan kujera ya motso ya kama kafafun Ummi "Dan Allah Ummi kisa baki Baffah yabani Rubina na aura dan Allah ya haɗa ɗaurin auren duka jibi" Ummi tai wani miskilin murmushi kafin ta ce "Ka makaro Uwaimir baka kyautawa zuviyarka ba da tai ta dakon son Rubina tsawon shekaru ama ka kasa gayawa Baffanku duk da tuni ni da shi mun riga mun ranfo ka amma rashin furtawarka taja komai, Baffah yariga da ya bawa Nuraddeen auran Rubina manya sun shiga magana

Chapter 10 of 11