Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 11
na zaune a dannin room ta gama haɗawa Rubina abinci ta bata tana ci ta ajje mata ruwa da magunguna a kusa da ita tabar Khalipha yana kula da Rubinar, tsai yayi bakin kofar shigowa falon yana bin Rubina da kallon mamaki ganin tana lalube da hannunta kan danning ɗin "Khalipha kai Khalipha ka miko min maganina nasha ba Ummi tace inna gama ka taimakan ba" jiki sanyaye ya karaso cikin room ɗin ya zauna kujerar dake kallon wacce Rubina ke zaune ya kafeta da idanu "Khalipha Yay Uwair ne yazo wajan nan kamshinsa nake ji?" jikin Uwair ne ya ɗauki wani irin mazari jin abinda zuciyarsa ke faɗa masa "Rubina kalle ni ki kalle ni sosai gani zaune a gabanki bakya gani na?" Rubina ta miko hannu tana laluban inda yake yai saurin kai hannunsa kan nata "Yayanmu a sakamakon dukan dasu Hajiya sukai mata jiya ta daina gani fa" wani dummm Uwaimir yaji a kunnuwansa sakamakon maganar zuciyarsa ta tsaya cak na ɗan mintina tunaninsa suke neman gushewa yafara zaton kodai mafarki yake "Khalipha sake faɗi dan Allah ka karyata min kace karya kake Rubinan mai Rubinan tai masu da zasuyi mata wannan illar, Rubina Rubina" kansa yadafe yama kasa cewa komai "Uwaimir yaushe kazo?" yaji muryar Ummi ta na tambayarsa, ɗago da kansa yayi yana bin Ummi da ido yakasa cewa komai, hayaniya da hargowar Hajiya Umma yasa suka ɗago kansu suna kallon juna "Ina kake munafuki waton ta kiraka ta guntsa maka karya da gaskiyya shine har kazo gidan ka kasa shigowa wajena kai tsaye ka tawo wajanta gata uwarka ko gata uwar data kawo ka duniya to zo ka wuce muje in kuma ita ta haifa min kai sai naji yau" Uwair bai motsa daga inda yake ba hakan yabawa Hajiya Umma damar karasowa inda suke, Ummi ta ɗaga ɗaya daga cikin kujerer danning ta bugawa Hajiya Umma a fuska nan take goshinta ya fashe yafara zubar da jini da sauri Uwair ya mike yasa hannu ya dafewa Hajiyar wajan raunin da hannunsa yana kokarin janta subar wajan taja ta tsaya tana aikawa da Ummi wani kallo "Ni kikayiwa Rauni Fatima" "Na maki naji maki raunin idan har baki fasa shigo min pary ba wataran saina ji maki mummunan ciwon dayafi wannan" Uwair yaja hannun Umma suka fita daga part ɗin tana aikawa da Ummi zagi itama bata kyale ba har bakin gate ta biyo su tana rama duk abinda Umman ke gaya mata, sanda ta dawo ɗakin ta tarar Rubina na kuka sosai "Ummi mai yasa mai yasa duk gidan nan ba wanda Hajiya Umma ta tsana sai ni maina mata Ummi zuciyata ta fara ayyana min maganganun Hajiya Umma gaskiyya ne niba ƴar gidan nan bace ina iyayena suke" sak Ummi tayi tana bin Rubina da kallo kafin kuma ta ce "Ok kin yarda da maganarta to naji nima ina tambayarki ina iyayan naki suke tunda nida Baffa ba mune iyayanki ba suna ina gaya min suna ina" Ummi ta karashe faɗa a tsawace tsawar da Rubina bata taɓa jin Ummi tai mata irinta ba, jikinta ya fara karkarwa ganin hakan yasa Ummi ta karasa wajan Rubinan ta rungumeta ta fashe da kuka, Rubina ma kukan ta kama tana bawa Ummi hakuri "Kiyi hakuri Ummi na tuba bazan sake ba bazan sake ce maki komai ba nima na sani kune iayaye na na sani Ummi kawai zuciyata ta tsinke harna fara tunanin gaibu" "Hajiya wai maine kike haka ne ki tsaya na gyara maki raunin nan dan Allah yayi zurfi ba ki bari na baki taimakon farko saimu tafi hospital" "Hospital ɗin ubanwa ajimin wannan raunin ka kira min hospital to wajan ƴan sanda zaka kaini na shugar da karata" Uwair yadafe kai ya ciro wayarsa daga aljihu yaiwa Daddy text messages akan yazo gida yanzu, mintina tsakani saiga Daddy a gidan shiya tilasta Umma sukaje hospita ya kuma gayawa Baffah abinda ya kuma faruwa a gidan yau, Baffah ba karamin ɓaci ransa ya kuma yi ba ya kira lambar Hajiya Umma kamar bazata ɗaga kiran ba sai kuma dai ta ɗaga ko amsa sallamar datai masa baiyi ba "Kashe di na dake na karshe idan har kika kuma tayar min da fitina a gidana nan da kwanakin da zan tawo to dai dai yake da kin datse duka igiyoyin aurena dake" yana gama faɗin haka ya katse kiran nasa, Hajiya Umma ta jima rikeda wayar a hannunta jikinta yai mata wani irin sanyi "Ashe dama har akwai wata rana da zata zo Baffah yai mata barazana da igiyoyin auransa dake kanta?" tambayar da zuciyarta keta mata kenan "Hmm" tayi kwafa tareda cin alwashi a xuciyarta Uwair zaune cikin ɗakinsa yau kwanansa Uku kenan a garin banda masallaci ba inda yake zuwa yana zaune gaban laptop ɗinsa yana bincike "Yawwa Alhamdulillah" yafaɗa tareda mikewa ya fita part ɗin Ummi yai sa'ar ganin Khalipha zaune kan farar kujera yana danna wayarsa ya zauna kusa da shi yana kallon yaron ya ce "Khalipha sirri nakeso muyi da kai banyi maganar nan da kowa ba sai kai, zan tafi da Rubina Londan dakai nan da kwana huɗu jirgin karfe huɗu na yamma zamu bi, ranar Juma'a bayan an sakko daga masallaci ka yi dabara ka fito min da Rubina zan parking motata acan bakin titi dan Allah Khalipha ka rike min amana karka fayawa kowa wannan maganar ko ita Rubinan karka gayawa zan sanarwa da Ummi muna tare bayan mun sauka a london" Khalipha ya washe baki jin zai bar kasa shi ko sau ɗaya ma bai taɓa zuwa wata kasa ba amma yau gashi zai keta hazo yayi doguwar tafiya har Turai "Ai wallahi Yaya ko aljani bazaiji wannan maganar ba bare mutum kuma zan fito da ita dazarar naga ka fitar da motarka daga gidan nan naji daɗi daya kasance zanje kasar turawa" "Idan har ka rike wannan sirrin to ni kuma nai maka alkawarin zan ɗauki nauyin karatunka a duk kasar da kake so nidai fatana kar wanda yaji wannan maganar" "Ai yaya karka wani damu nine fa cab ba wanda zaiji yasin" Uwair ya mike ya fita daga part ɗin ya koma ɗakinsa, yana zama wayarsa tai kara yai murmushi ganin Captein ke kiransa ya ɗaga da sauri ya mike tsaya ya sara ma mai magana ta cikin wayar "Morning sir" "Morning Uwaimir ka maza kazo nan hospital rukunin Captein Abbas ne suka sami hatsari sunji munanan ciwuka dole muna bukatar irinku a wajan" "Sorry sir bana garin fa nazo gida, munyi magana da Genarel na zaci ma ya sanar maka" "Bai gayamin ba amma gaskiyya ka maza ka dawo bakin aikinka" "Na gayawa Genaral matsalata yama karfi uzirina akalla zan kwashe kusan sati uku bana bakin aiki," "Ok" captein ya faɗa bayan ya katse kiran Uwair ya koma ya zauna shuru yana tunanin mafita ga soyayyar sa ga Rubina yana jin kamar ya hakura da ita kuma a wani ɓangaran na zuciyarsa yana jin kamar bazai iya ba ya shiga tunani da neman mafita ya fito ya bayyanawa kowa asirin zuciyarsa ya fara da Hajiyarsa wacce yake ganin itace babbar matsalar sa, Ranar juma'a Khalipha da Uwaimir tare sukaje masallaci sanda suka dawo biyu da rabi, Uwair kasancewar yasan shirinsa ko gida bai shigar da motarsa ba yai parking ɗinta a wajan gidan lokacin tuni Khalipha ya shige gida a sace Khalipha ya faki idanun Ummi lokacin tana bedroom ɗinta ya ɗebarwa Rubina dogayan riguna guda uku shima bai wani ɗebi nasa da yawa ba ya haɗa a trolly ya fita da ita ya saka a motar Uwair yadawo cikin gidan yaci abincin rana ya iske Ummi a ɗaki itada Rubina "Yawwa Khalipha zan fita gida zan gano su Anty Yana ne zasu dawo kano akwai gidan da mijinta ya siya shekaran jiya zanje na gano ya zubin gidan yake misan mune muke bukata ba daɗewa zanyi ba dan Allah ka kular min da Rubina kamata duk abinda takeso amana" "A'ah Ummi ban karɓi amana ba amana fa wuya gareta zandai kula da ita ɗin" "Yawwa Baban Baffah karka matsa ko ina ka barta kaji" kai kurum ya girgiza ta rungumi Rubina ta fita suna mata Allah ya kiyaye, Khalipha na ganin fitar Ummi yai ajjiyar zuciya ya kalli agogo uku da mintina ya fito falo ya buɗe windo ya hangi fitar motar Ummi daga gidan ya koma ɗaki yabi Rubina da kallo ya ɗakko mata mayafin abayar dake jikinta ya naɗa mata yana dariya ya ce "Kinga yanda kikai kyau kiwa Rubie bari na maki hoto" tana ji ya mata hoton tana murmushi yai jim na ɗan lokaci yana tunanin yanda zaiyi su fita can ya nisa ya ce "Rubina kin kwana biyu baki fita kinsha iska ba ɗazu ma da kukaje ganin likita baki wani zaga kinga gari ba zo mu fita mu ɗan zaga muje titi mu dawo ko nacewa Yaya Uwaimir yakaimu musha ice_Cream" "E! muje Khalipha amma karmu daɗe kar Ummi tai faɗa" ya kama hannunta ta mike ya mika mata plat shoe tasa ya ruko hannunta suka jero suna tafiya a cikin gidan tana ce wa "Oh rayuwa kenan Khalipha wancan satin iyanzu ina ganin komai amma yanzu kaga ba abinda nake iya gani nan gidan mune inda na rayu tsawon shekaru amma bazan iya ganin komai ba duhu kawai nake gani ko zan warke ma" Khalipha jikinsa yai sanyi jin furucinta na karshe ya kada baki ya ce "Zaki warke Rubina insha Allah" tana ji suna ta tafiya har suka zo bakin titi inda taji Khalipha na faɗin "Yawwa ga Yaya Uwaimir ɗin can ma zo muyi sauri mu shiga motar" ta washe baki sanda suka karasa ya buɗe mata gaban motar ta ya taimaka mata ta shiga ya maida murfin motar ya rufe ya zagaya back seat ya shiga ya zauna, Uwaimir yakafe Rubina da idanu tsawon lokaci yana kallonta kafin kuma yabawa motar wuta suka nufi filin jirgin saman malam Aminu kano, tun a parking space na filin jirgin Uwaimir yabawa wani abokinsa key ɗin motar da dama sunyi da shi su haɗu a wajan, suka shiga ciki aka gama duk wasu bincikensu da duba duban da zasuyi sannan suka nufi wajan shiga jirgi, Rubina ta coge a step na farko ta tsaya tana murza hannun Uwair dake cikin nata "Yay kamar jirgi muke hawa ina zamu ina zaka kaini" "Mu shiga daga ciki Rubina zan maki bayani" batai masa musu ba suka shiga cikin jirgin ya zaunar da ita kana ya zauna kusa da ita ya ce "Landon zamu tafi Rubina zan nema maki magani acan na rigada na gama magana har hospital ɗin da zasu maki aiki na gama da su su zasuzo su ɗauki ma a filin jirgi inmun sauka acan" "Waka gayawa da sanin wa muka tawo" "Ba wanda ya sani amma yanzu zan mana hoto na turawa Ummi sa biyo mu daga baya" ya saita camera ta wayarsa yai masu hoto shida ita sannan ya bawa Khalipha wayarsa shima yai hoto daga inda yake ya haɗa duka ya turawa Ummi ta whatsapp yaga kusan awarta guda ma da sauka a ajje mata hoto da rubutun ban hakuri yasa wayar tasa a airplanemode ya maidata aljihu, Rubina ta kwantar da kanta a kafaɗar Uwair kafin wani lokaci barci yai gaba da ita 🔯🔯🔯🔯🔯 Sanda Mama ta koma gida karfe goma na safiya ta tarar gidan sai Amira da Marwa Salima ta fita "Mama oyoyo" Marwa ta faɗa tana dariya "Yawwa Oyoyo Marwanatu ina Saliman taje?" "Yanzu ta fita wai taje gidansu Ayyah kawarta wai yau batada kuɗi ta je ta bata rancan 500" "Aishikenan ke zokije bakin titi kiyo mana cefane nasan bakuci komai ba" "A'a munci saurar shinkafar Sani muka ɗimama bai kwana a gidan nan ba har yanzu ma bai dawo ba" "Oh jama'a ni Zainabu Abu Sani a wace masifa yakeson sani ne wai? waton dana sa kafa nabar gidan shima saiya bar gidan Allah ya shirya min ku" mama ta zaro kuɗin da Alhaji Sammani ya bata, Marwa ta zaro idanu tana kallon uban kuɗin da Mama ta fito da su ta ce "Mama ina kika sami kuɗin haka?" dam gaban Mama yafaɗi tai saurin basarwa ta ce "Kuɗin aikina ne danayi na wancan satin dana shekaran jiya da mukaje kaduna aka ban duka na ciro su yanzu" "Kai Mama gasu da yawa kuwa, anya nima ba fara binki zanyi ba muna aikin tare nima inaso naga na dogara da kaina" "Zaki dogara da kanki Salima amma bata irin wannan harkar ba kinji Allah yamaku tsari, yanzu ungo dubu goman nan siyo mana taliya guda biyar da shinkafa kwano ɗaya sai ki siyo mai rabin kwalba ai inaga zai isha kuɗin ko" "E! zai isa mama mungode Allah ya kare ki mamanmu yakawo irin wananan aikin kiyita samun kuɗi" murmushin yake tayi tana bin Marwa da kallo harta fita daga ɗaki, Salima da sallama ta shiga gidansu kawarta Ayyah, Ayya dake duke tana wanki ta ɗago kao ta kelleta tana mata dariya "Daman nagaji wallahi da wankin nan sai gaki maza zoki tayani" "Cab na tayaki me wanki ai sam ba wata alaka nida shi ta kusa kota nesa zuwa nai ni ki ranta min ɗari biyar na samu musha ko garin kwaki ne" "Kema Salima kina bani mamaki yanzu fa zamani ya canza ba'a zama haka sai abinda iyaye suka kawo suka baka kaima mikewa kake ka nemi na rufawa kanka asiri" "To Ayyah mai zanyi dan Allah, komai nai tunanin nayi sai naga ana saida shi a unguwar nan" "Ji banza waya gaya maki irin wannan sana'ar, ke yanzu fa kan mage ya waye bare ma ke ɗin nan ai kina shigowa harkarmu walahi ba kananun kuɗi zaki rinka samu ba ina gaya maki" 'Wacce harka ce gaya min da sauri naji dan Allah" Ayyah ta tsame hannunta daga cikin bokatin wanki taja hannun Salima suka shiga cikin ɗaki 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode Ten1️⃣0️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* "Gidan wata hajiya ne ake zuwa daga kinje zatai maki hoto a wayarta zata turawa maza wanda ya zaɓe ki shikenan ke kin zama tasa zai rinka mu'amala dake kamar matarshi kuɗi kuwa sai kin ture bata harka da kana nan maza sai waɗanda sukaci suka tada kai ko waɗanda aka tara aka bar masu idan ma bakya son harka da maza ga mata nan irinki zakuyi harka su biyaki" "Kai gaskiyya bazan iya ba Ayyah wannan saɓon Allah har ina, kai bazan iya aikatawa ba, yanzu ke kina nufin bin mazan kike?" "Har mata ma ina bi ni nan da kika ganni ba binda bana yi indai za'a biyani to zanyi komai bazan iya zama da talauci ba kullum kana tunanin yaya zakayi kasami abinda zaka ci ka zo kana rara gefe kana bin gidan mutane neman abu shi yasa naga bazan iya ba na nemawa kaina mafita harta sabulu fa da sai dai na siya da kuɗina yanzu ba gashi ba komai na gidan nan ni nake mana na ɗaukewa Ummanmu komai yara kanne na na makaranta mai kyau" "Cab Allah ya shiryeki Ayyah, kinga tafiyata ma ni ki bar kuɗin naki ma nagode" Salima ta mike ta fita daga ɗakin tayiwa mahaifiyar Ayya sallama ta tafi gidansu tai murna sosai sanda taga Mama tadawo ta shiga tambayarta ina ta sami kuɗin data sai sabuwar waya mai tsada haka, mama tai murmushin yake ta ce "Jiya da naje gidan Hajiya Sakina nake gaya mata banda waya ashe babban ɗanta naji shine ya siyo min yau da zan taho yaban yama ce na gaidaku" "Kai aikuwa naji daɗin wayar nan Mama dani ta dace bari mu mata caji, kai aida cajinta ma bari na saita WhatsApp facebook da komai yanzu muma mu shigo gari mu rinka ganin abinda ke faruwa a social media" Mama dai batace mata komai ba taci gaba da sabgoginta na gida Ayyah bayan fitar Salima daga gidan kwafa tayi ta ɗauki wayarta ta kira lambar hajiya sai kuma dai kawai ta katse kiran, minti ɗaya tsakani kiran Hajiyar ya shigo ta ɗaga kiran "Ayya lafiya naga kin min flashing" "A'a uwarmu ba flashing na maki ba kiranki nai niyyar yi kuma dai saina fasa kiran nace bari nazo sai muyi magana" "Bana gida ai Ayya koma maine gaya min ta waya yanzu" Ayya ta kwashe yanda sukai da Salima ta gayawa Hajiya, Hajiyar tai dariya kana ta ce "Karki wani damu da kanta zata kawo kanta gareki bari zanyi magana da malam na kan tudu zata kawo kanta daman irinta nake nema badai kince akwai kyau da diri ba ai zance ya kare bazanyi sanya ba yanzu zansa ya min aiki a kanta" Ayya ta kashe wayar tana murmushi ta ajje ta fito taci gaba da wankinta 🔯🔯🔯🔯🔯 Ummi wajan shida ta shigo gidan a gajiye alwala tayi kasancewar ana gafda fara kiran sallar mangariba ta leka ɗakin Rubina tana tunanin barci take taga wayam ba rubinan saitai tunanin ko suna part ɗin Ummu itada Khalipha ta shimfiɗa dadduma ta tada sallah jin an gama kiran sallah anan cikin masallacin dake jikin gidan, bayan ta idar tana azkhair wayarta tai ring ginin yayarta ke kira yasa tai picking call ɗin "Fatima hau Online muyi magana" ta katse kiran ta kunna data "Uwair" Ummi ta ambata ganin sakonsa ya fara shigowa kamar zata buɗe sakon nasa sai kuma dai ta duba na yayar tata har suka gama magana ta kashe data ta ajje gefe sannan ta tuna da sakon Uwair da bata duba ba ta ɗakko wayar ta lalubo sunan sa bata tsaya buɗe hoton dataga ya turo mata ba ta fara karanta rubutun dake kasan hoton _Ina mai neman afuwarki Ummi gamu bisa hanyar tafiya landon Rubina zataga likita insha Allah tana gani da idanunta zamu dawo dan Allah karki ɗaga maganar nan na riga na gayawa Hajiyarmu na koma aiki ne batasan nan na taho ba_ Ummi tai murmushi kawai tareda masa fatan alkhairi ta ajje wayar bayan ta kalli hotonsu daya turo mata "Uwair da zan bari wani a gidan nan ya auri Rubina dakai ne amma kash bana jin zan amince da kai idanma ni na amince hajiyarka bazata taɓa bari ba" ta mike ta fita part ɗin Ummu su tattauna kan tafiyar nan tasu Rubina, bayan sallar insha tai shirin barci itada autanta Usham dake ta tambayarta ina Yaya Rubina da Khalipha bata ce masa komai ba haryai barci itama har ta fara barci karar wayarta ya farkar da ita ganin vidio call ne tai saurin tashi ta saita tana murmushi Baffah ne ya bayyana zaune cikin wani ɗaki Babba daga gani ɗakin hotal ne yasha gyara "Barka da dare amaryata gaba ɗaya kun birkitani hankalina yayo gida kano" "Barka dai Baffa, ka kwantar da hankalinka ka zauna kai Ummararka cikin kwanciyar hankali ɗanka yai maganin komai yau Uwair sun tafi Londan shida Rubina" "Amma mai yasa kika barsa mai yasa baki faɗa min ba?" Baffah yafaɗa a zafafe "Nima banda masaniya ga komai saida ma suka tafi sannan ya sanar dani nasa Aliyu dai yafara min shirin binsu nima cikin satin nan" "Bansan mai Uwaimir ke nufi ba da Rubina mai yasa zaiyi haka ba shawarar kowa" "Mai yake nufi kuwa ai kaima ka sani idan kaga kare na shinshinar takalmi ɗauka zaiyi" "Tayaya mutumin dayake da ranarsa aka bikinsa fa yanzu satittika suka rage" "Zai gama zagaye zagayansa yadawo yazo ya bayyana ne" "Tun tuni nake jiran randa zaizo min da maganar yanason Rubina amma yaki bansan mai ya kudurce a xuciyarsa ba ko kuma jira yake na basa ita, kowa ya kalli idanun Uwair yasan akwai tsantsar soyayyar Rubina a ciki" "Nidai mubar wannan maganar ranka yadaɗe inason binsu England" "Ok zansa asai maki ticket a sama maki visa ki ban nan da sati guda nima daga nan can zanyi" "Sati yai yawa Baffah, zuciyata bazata iya jurar nan da sati guda ba Baffah, kai ba karamin mutum bane kasan inda zakabi tafiyar nan tawa ta yuwu nan da kwana uku" "Kin fiya rigima mai kike gudu karki sa na ɗaura masa aure da ita gobe a masallaci" da sauri Ummi ta katse Baffah da "A'a dan Allah kar a mana haka bance Rubina nason sa ba kabarta ya nemi soyayyarta da kansa" "Kin basa dama?" Ummi tai murmushi tana aikawa Baffa da wani kallo yana maida mata shima "Barci zan ka kira sauran matanka" "Kin sani ai aduk sanda nai tafiya irin haka saina gama vidio call da duka su sannan nake kiranki sabida ke ɗin ta dabance yanzu mai zan samu" "Baffah kaga fa autanka na kusa ka barni nai barci cikin salama" ta faɗa tana lumlumshe idanu "Ai ban hanaki ba koma ɗan kiss ɗin nan bazan samu ba kenan" kasa Ummi tai da kanta tana dariya kasa kasa ya buɗi baki zai magana Amjad ya turo kofar ɗakin ya shigo da sallama, Ummi tabi Amjad da kallo ganin ya zauna a kujera ɗaya tal dake ɗakin hannunsa rikeda leda, washe baki yayi yana ɗagowa Ummi hannu "Barka da dare uwa ta gari" "Amjad na Baffa kuna nan abinku?" Amjad ya shafi kansa yana murmushi "Ai munkusa dawowa" "Allah yadawo daku lafiya to vari na barku haka kuyi barci ga amanar Baffah nan ka kular mana dashi" ɗif ta katse tana dariya acan ma Baffah da Amjad dariyar sukayi lokaci ɗaya kafin Amjad ya fito da take away babba daga ledan daya shigo da ita ya mikawa Baffah "Ga shinkafar Baffanmu na samo maka ita mai zafin gaske" "Allah yamaka albarka Amjad yakamata kaima ka fara neman matar aure" "Baffah layi baizo kaina ba ga Yaya Uwaimir nan sai yayi sannan zan fara saka rai, Uwaimir a cikin jirgi yana rungume da Rubina dake barci hankali kwance tai blance a jikinsa tana barcinta bil hakki, shuɗewar wasu awanni yasa ganin bata tashi ba yatashe ta taci abinci bata wani ci dayawa ba ta kuma komawa barcin nata, sanda suka sauka kasar dare yayi ga wani tsananin sanyi da ake a kasar, kamar yanda ya zata motar hospital tazo ta ɗauki Rubina ta wuce da ita shida Khalipha suka wuce gidan daya riga ya kama masu suka sauka, tsananin sanyin dayake ji yasa ya rinka tunanin ita Rubina a wane hali take yanzu da kyar ya iya barci da asuba yatashi yai shiri ya nufi hospital ɗin duk da tun tuni sun sanar masa basa bukatar mai jinya, a yanayin daya tarar da Rubina yaji daɗi sosai waton inda akaci gaba anci gaba, ya tsaya yana kallonta da murmushi a fuskarsa "Ya meer Yay kana ina ne wai kamshinka nake ji na tabbata kana ɗakin nan kazo matso kusa dani Yayana nai missing naka" Uwair yai murmushi ya karasa inda take zaune ya kama hannunta ya sumbata kana ya shafi kanta dayake sanye da hular sanyi babba "Nima nai missing naki Rubie aƴan awannin naji na kasa aikata komai ke kawai nakeson gani" "Yay kunyi waya da Ummi?" "Bamuyi ba sai anjima inna samu nasaita simcard ɗina zan kirata zan koma masauki yanzu daman so nake naga a yanayin da kike" "Ina cikin aminci Yay nagode sosai da kulawarka akaina yau na daɗa tabbatar dani ta dabance a wajanka yayana Allah ya faranta maka ya kare mana kai yayana, jiya ina zuwa nan suka fara bincikar lafiyar idanuna suka haska min wata fitila mai hasken gaske, sun ban magani nasha suna saka min magani a idona duk bayan awa ɗaya naji ɗaya daga cikin dectors ɗin na cewa nan da four days zasu min aiki ya tabbatar min da gani na zai dawo" "Masha Allah haka mukeso ai Rubi ki zama cikin aminci anjima zan dawo na yini anan muna tare" tun tana iya jiyo takun tafiyarsa hartaji ɗiff ta maida kai ta kwanta tana tuna ɗimbin alkhairin Yayan nata a ranta bata ganin ko cikin yaran Ummi da suka fito ciki ɗaya akwai wanda yakai Yaya Uwaimir sonta" Uwair na fita shopping yaje ya masu sosai yasaiwa Khalipha da shi kayan sanyi sabida yaji yanayin garin ba sauki sanyi ba misali, Khalipha tun bayan dayai sallar asuba barcinsa kawai yake hankali kwance yana naɗe cikin bargo ɗakin ba sanyi sosai kasancewar akwai room heater a ɗakin shi yasa har Uwair yafita yadawo bai sani ba, Uwair ya shiga kichin na gidan ya ɗora masu noodies saida ya kammala

Chapter 7 of 11