Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 11
har an tsaida rana watanni biyu masu kuwa sanin kanka ne ba abinda zaisa Baffah ya janye wannan maganar" Uwaimir ya sauke numfashi tareda goge zufa baice komai ba ya fice daga part ɗin yana hango su Rubina itada Nuraddeen dake ta faman dariya, "Allah Rubina ki daina min dariya kinsan yanda na mato a sonki kuwa son da nake maki baki min ko rabinsa" Rubina ta aika masa harara irinta masoya tai kamar zatai shuru sai kuma dai ta ɗago ta kallesa murmushi shimfiɗe a fuskarta "Bantaɓa soyayya ba My Noor, akanka nasan maine so, nidai nasan a rai da zuciya ina matukar son ka Haske na kaine fitilar data haske zuciyata ta kamu da kaunarka a zuciyata bakada tamka" Nuraddeen ya kafe ta da idanunsa yana aika mata da sihirtatcan kallo "Gare ni nima haka take Husmy ina maki son da bansan adadinsa ba, kullum Lamen na tsokanata idan yaga na bada himma ina waya dake, ina rokon Allah yanuna min ranar da burina zai cika ace fatiha Nuraddeen ya zama na Husnah" Na rufe fuskata da hannuna jin furucin Nuraddeen ina murmushi "A'a fa Husmy ki daina rufe min wannan kyakkyawar fuskar nan taki ki barni nayita kallonta bana gajiya washe garin randa aka kaimin ke yini guda zanyi cur a gida ina zaune na saki a gaba inyita kallonki" nai dariya kawai batare dana tanka masa ba, ya kalle agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya mike "Bari na koma gida yau naga gidan cike yake da baki, inaga kuma sai ranar pharty insha Allah zan halarta" na ɗago na kallesa kafin nace "An baka gate pass ne?" "Yayanki Amjad ya kawo min har office ɗina dana ɗaurin aure yace inji Baffanmu" nai murmushi muka jera da shi nai masa rakiya har kofar gidanmu inda ya ajje motarsa bai shigo da ita ciki ba saida naga tafiyarsa kana na dawo cikin gida Washe gari ranar juma'a ranar Anty Raihana zatai arabi'an night shima mun halarta inda MGG ya kayatar da wajan aka sha shayi da Kubza munsha rawar larabawa sosai na sake cikin kawaye da ƴan uwan Raihana da basu da wulakanci ko kaɗan duk da ƴan gidanmu da yawa sunje wannan karan amma ba wanda ya tanka min haka nima ba wacce na kula cikin yayun nawa da suka nuna kamar basu sanni ba, dukansu ƴan ɗakin Hajiya ne da manyan ƴaƴansu, washe gari asabar tun safe gidan yaɗau harama baki ta ko'ina zuwa suke ƴan uwan Ummi ma yayunta mata guda biyu sunzo daga Maiduguri sai ranar naje aka min gyaran kai lalle ja da baki ranar dai wuni nayi a shagon meenah dake zooroad ban dawo gida ba sai bayan sallar la'asar muka dawo nida Halisa kawata, abinci kawai mukaci muka fara shirin tafiya wajan phartyn da za'a fara shida na yamma, wanka kawai mukai a gida muka tafi gidan mai make'up nida Halisa acan muka shirya kyau iya kyau kam masha Allah nayi sanda Mai make up ta gama ɗaura min head ja daya matukar kara haska kyakkyawar fuskar tawa nida Halisa sai muka fito kamar wasu twince kasancewar lace ɗin namu da ɗinkin duka iri ɗaya ne, Yaya Uwair ya rinka kirana kamar me ni sam na manta kayan da zai sa yau suna waje na da sauri na karasa gida bayan na ɗaga kiran nasa yana min masifar ina na tafi na rasa maiya maida Yaya Uwaimir faɗatacce kwana nan nan, sanda na kawo masa kayan sak yayi yana kallona kamar yau ya taɓa gani na harya buɗi baki zai magana kawai ya amshi ledan kayan yai gaba nima na koma ciki ina neman Yaya Salman da zamu tafi tare da shi a motarsa, shida dai dai muka fito nida Salman da Halisa na buɗe gaban motar zan shiga Yaya Salman dake zaune mazaunin driver yaimin gyaran murya tareda nuni da na koma baya Halisa ta zauna a gaba, nai dariya dan tun jiya na ranfo sa na buɗe seat ɗin baya na shiga ina dariya saiga Raudah ta fito da sauri daga part ɗin Hajiya Umma itama ta shigo motar muka tafi, Waje yayi waje haka kuma biki yayi viki duk da amarya da ango basu karaso ba amma wajan ya kayatu sosai ana ta kiɗa dj na sakin kiɗa har na kasa jurewa na shiga ina rawa nida Samiha ɗiyar Daddy da wasu daga cikin kawayan Anty Raiha, bakwai sannan aka bada sanarwar shigowar ango da amarya kowa ya koma seat ɗinsa aka zubawa kofa idanu, wani sanyin daɗi ne ya lulluɓe zuciyata sanda na hangi shigowar Yaya Uwair shida Anty Raiha yana sanye cikin sky blue ɗin shadda ya baza uwar malum malum ita kuma na sanye cikin lace sky blue itama mai yarfin fulawoyi fari, da akaiwa ɗinkin amare doguwar riga tai masifar mata kyau tasha ɗauri irin na amare ni sai naga ma tafi angon kyau, na saita wayana na tashi ina masu vidio sanda Dj ya saki sautin wakar bikin nasu yayin da Mc ke zuzuta zuwan amarya da ango, lallausan murmushi Uwair ya sakar min lokaci dana fara zuwa zan masu vidio kafin wani lokaci sauran yayu suma sun fara masu vidio har suka karasa wajan zamansu, yayin da waje yai tsit aka tsaida sauti na ɗan lokaci kafin aka gayyaci Anty Amina da tazo ta buɗe taro da addu'a, ta kwararo ta kuwa ba karya ansha addu'ar zaman lafiya ga ango da amarya sai sannan Ummi da Ummu suka karaso wajan bayan kammala addu'a Mc ɗin mai abin dariya ya ce "To jama'a atafawa amarya da ango" ji kake Raf raf gaba ɗaya wajan an ɗau tafi kafin Dj ya saki sauti nan fa aka fara rawa cikin tsari kowa na zaune a wajansa yayin da wajan takwas na dare aka fara zuwa karɓo abinci abinci ne kala kala sai wanda ranka keso, Ango aka fara kawo wa ya ciyar da amaryarsa a baki kafin itama ta basa abincin a baki kai masha Allah taro yayi sosai sanda naga Uwair da Anty Raiha a tsakyar fili Ummi ta bani rafas na ɗari biyu naje na rinka yiwa Yaya Uwair liki sai vidio ake mana camera man ya ɗauke mu hoto ina tsakiyar ango da amarya sai murmushi nake akayi mana da yay Meer na ɗan kwanto jikinsa ina murmushi haka duka gidanmu akai hoto gaba ɗaya aka kuma ware jikoki akai masu nasu daban Wajan tara da rabi su Ummi suka tafi, mukam bamu tafi ba sai sanda aka tashi lokacin sha ɗaya na dare muka koma gida a gajiye, washe gari aka ɗaura auran Uwaimir da Anty Raiha inda aka wuce da shagalin biki har zuwa yamma da aka fara shirin zuwa ɗaukar amarya da za'a ƙai gidan Yaya Uwair dake bechi da mangariba muka je gidan nida Kawaye na yaya Amjad ya kaimu amarya nata kuka na rinka tsokanarta bata kulani ba mukai masu Allah sanya alkhairi muka dawo gida, Uwair sai goma na dare ya shiga gidan nasa shida abokinsa Naupal sai Captein Hisham su biyu rak sukai masa rakiya gidan nasa bayan ƴan nasihohi da sukai masu sukai masu fatan zaman lafiya da zuria ɗayyi ba sannan suka tafi, Uwair ya shigo ɗakin Raihana bayan yai masu rakiya ya kuma yi sallama da gate man ya koma ciki, yai murmushi bayan ya zauna kusa da Raiha ya mikar da ita tsaye suka shiga bayi tare sukai alwala suka fito yajasu sallah raka'a biyu bayan yai masu addu'o'i yai mata tambayo yi kan addini ta basa amsa daya gamsu dama ya zaci hakan tunda Alhamdulillah ba baya ba gidan nasu kuma taje islamiyya, ya fita ya shigo da gasasshiyar kaza da madarar shanu mai ɗimi, da kansa ya ciyar da ita taci dayawa ba laifi shine ma bai wani ci daya ba kasantuwar damuwa ta cika masa ciki, ita ta fara kwanciya sannan shi bayan yai wanka, a wannan daran bai saurarawa Raihana ba yamaida ta cikakkiyar mace, batai masa wani raki ba saima kokarin taya ɓera ɓari da tayi suka taru suka farantawa juna rai duk da kuwa taji azaba, yataimaka mata tun daran ta gyara jikinta suka koma suka kwanta sai asuba suka tashi yai alwala bayan yai wanka ya wuce masallacin dake cikin unguwar, sanda yadawo gidan har Raihana ta koma barci shima bayanta yaje ya kwanta yai barcin har tara da Rabi na safe basu farka ba, sai goma da ƴan mintina suka ta shi shima yunwa ce ta farkar da Raihana da take jin cikinta wayam, ta shiga kichin tana kokarin tafasa shayi ya shigo shiya taimaka mata suka haɗa tea suka soya patoto sannan suka fito suka sha tea da bread tareda soyayyan dankali, ganin sha ɗaya har tayi yasa yai wanka ya fita kafin baki su iskesa a gidan Kamar da wasa sai gashi na kwashi sati guda banga fuskar Yay Uwair ba tun ina kiransa a waya harma na daina na zuba masa idanu kawai, nama maida hankali ga islamiyarmu da ake mana screning na sauka kuma ina cikin ƴan hadda, Alhamdulillah na haye harma an tsaida mana rana sati uku masu zuwa, Uwair satinsa uku a kano yafara shirin komawa wajan aiki, yana tsaye gaban closet yana zuba kayansa cikin haɗaɗɗiyar trabilling Bag ɗinsa sabuwa ɗau, yayin da Raihana ke gefan gado tana shashshekar kuka ya juyo ya kalleta yana mata dariya sai kuma yadawo kusa da ita ya zauna ya kamo hannunta ya rike cikin nasa "Nace kizo mu tafi kinki kuma kinzo kin tsaya kinata min koke koke" "Inna bika zan sami matsala a karatuna kaima ka sani ni ba inda zani kayi tafiyarka kawai, ina kukan zanyi missing naka ne sannan gida sai ni kaɗai kasamo min wacce zamu zauna tare" "Toni yanzu wazan kawo maki Raiha kiyi hakuri ki daure kawai ki zauna ke kaɗan, banda kanne mata dasai nace hajiya ta turo maki su' "Ga Rubina nan kace tazo ta tayani zama mana" yaɗago yai mata wani kallo kafin yaci gaba da haɗa kayansa bai ce komai ba, harya gama shirin sa na tafiya tana zaune gefan gadon tana kuka "To naji yi shuru tashi na sauke ki gidan namu in yaso da dare sai ku tawo tareda Rubinan" ta saki ranta ta shirya suka wuce gidan nasu saida yafara kaita suka gaisa da Baffa kasancewar Lahdi ce Baffan baya zuwa ko ina, sannan ya suka wuce wajan Hajiya anan sukai sallama ɗaya daga cikin drivers na gidan ya kaisa airport, hajiya Umma ke meme ta hana Raihana fita duk yanda ta kula Raihanan nason fita ta shiga wani part ɗin Hajiya najin Raihan na waya da Rubina tana gaya mata tana gidan tazo part ɗin Hajiya, ita Rubina ma kasa cewa Anty Raihan komai tayi, taci gaba da sabgar gabanta bataje kiran nata ba ita bazata iya tuna shekara nawa rabon da kafafunta su taka kofar part ɗin hajiya ma bare ta shiga ciki, da dare Raihana tai shirin komawa gidanta sai cewa hajiyan tai ta zauna a gidan bari asa Amir ya ɗebo mata kayanta na sawa, saida tai kwana biyu sannan Baffah yasan tana gidan, ya kalli Hajiya dake kokarin zuba masa abinci cikin plat ya ce "Mai matar Uwaimir take min a cikin gidan nan yau har kwana biyu?" "Waida danaga baya nan shi yasa nace ta zauna taɗan kwana biyu, kuma kaga gidan sai ita kaɗai ba daɗi" "To ba'a gidan nan ba, ki gaya mata ta fito su tafi bari na kira Rubina su tafi tare saita rinka ɗebe mata kewa" wani kallo ta wurgawa Baffah amma ganin yanayi na fuskarshi yasa ta haɗiye bakin cikinta tana ji tana gani haka Rubina da Raihana suka tafi zuciyarta kamar tayi bundiga Lafiya kalau muke zaune a gidan nida Anty Raiha kusan komai nike yi duk da itama Raihanan ba baya ba wajan son tsab ga iya girki tare zamu dafa abinda ranmu keso muci mu kwanta barci kullum muna waya da Yay UwAIR ta wayar Antyn har aka shiga satin saukarmu na koma gida gidan ya zama sai ita kaɗai, ansha hidimar sauka sosai ƴan uwa sunyi min kara karma Yay na Uwair yaji labari kusan komai shi yayi min jota biro clander da babbar jaka mai rubutun sunana a jiki nai walima sosai wacce Baffah yakashewa kuɗi ba karya kari kiri Hajiya ta fito ta nuna hassadar ta dan ranar saukar barin gidan tayi sai can dare ta dawo, akwana a tashi bikina da Nuraddeen na gabatowa har ya rage saura sati biyu hidima sosai ake da shirye shirye saura kwana goma mukaje hospital kwajin jinin, ina zaune recepsion banyi aune ba sai gani nayi kawai Lameen ya ruko Nuraddeen sun fito daga labotory ɗin na mike nabi bayansu ina tambayar Lameen maiya same sa, bai tanka min ba harya saka sa a motar da muka zo ya zaunar da shi ya buɗe min back seat na shiga na zauna sannan Lameen ya zauna mazaunin driver yatashi motar muka fita daga hospital ɗin, jikina yai wani irin sanyi lokacin dana hangi Nuri ya jingina kansa jikin seat na motar idanunsa na zubar da hawaye Lameen na tuki baice komai ba har muka karasa unguwarmu suka sauke ni, sanda na shiga gida na tarar da Ummi itama hankalinta tashe ta ruko hannuna ta zaunar da ni kusa da ita, ina zama Baffah ya shigo shima cikin damuwa sosai, nai mamakin ganin Baffah a part ɗinku ba kasafai ya fiya shigowa wajan matan nasa ba sai babban abu yataso "Kiyi hakuri Rubina ba damar aure tsakaninki da Nura jininku yazo ɗaya shi As kema haka, yanzu Dr nawwal ta kirani ta sanar min" na dafe kaina ina jin lokaci ɗaya yai wani irin sara min na shiga cikin tashin hankali daman abinda aka gaya masu kenan shi yasa Lameen ya ruko sa "Innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un" ita kawai nake iya maimaitawa a zuciyata har ban sani ba ta fito fili, banyi aune ba sai ciwon kai kafin dare zazzaɓi ya rufeni nayi kuka nayi bakin ciki na kira lambar Nuraddeen yafi sau talatin bai ɗaga ba ashe yana hospital an kwantar da shi, tabbas wannan rana naga bakin ciki nama rasa ta ina zan cigaba da rayuwa ba Nuri, naje har hospital na dubasa ina kuka sosai na gaya masa ya cire damuwa na amince zan aure sa bazan haihu ba mu zauna a haka ba yara, shima ya yarda da maganata amma san manya suka ki aminta muna ji muna gani dole muka rabu da Nuri, na shiga damuwa sosai duk kibata ta zaizaye na fara wata irin rama, sanda Uwair yazo weekend ya ganni shima ya shiga damuwa sosai yayita lalashi na da ban hakuri, ya lallaɓa Baffah ya samar min admision a ɗaya daga cikin jami'ar garin nan mai zaman kanta, makaranta ce special yawanci malaman su turawa ne ganin na samu wannan damar yasa na kauda duka wata damuwar soyayyar Nuri nabawa karatuna mihimmanci na manta da duk wata soyayya ban bawa ko wanne namiji dama ya tunkare ni da zancan so ba naɗau zigar Yay Meer na zauna daram a kanta dayace karna sake na bawa wani dama yazo yace yana sona Baffah zai min aure batare dana cika burina na zama cikakkiyar likitar mata ba, lokacin da Yay Meer suka tafi America na wata uku da zasuyi na koma gidansa gaba ɗaya bisa umarnin Baffa, wasa wasa daga wata uku saida suka shafe shekara guda basu dawo ba sanda suka dawo naga Yayna Uwair ya zama kato abinka dama can ga kiba ga tsayi ya wani kara kyau ya zama babban mutum, karin girma aka masa tareda canjin wajan aiki ya koma Abuja gida kayatacce aka basa ba cikin barreck ba cikin manyan gidajan gwamnatin tarayya gida cikeda scurity tako ina sojoji birjik duk yanda yaso Raihana ta koma can kin yarda tayi wai ita bazata iya barin aikinta ba ta tafi wani waje daban da bata san kowa ba, yaci gaba da zamansa sai weekend yake zuwa shima ba ko yaushe ba, Uwair kuɗi sun zauna sosai yake jikani ta ko ina banda matsala a sirrince ya canza min motar hawa duk wata inada kaso cikin albashin sa nan da nan nima na canza na zama katuwa ta daman abinka da mai jikin girma cikin wannan shekaru na kammala karatuna na zama cikakkiyar likitar mata, ba karamin daɗi Uwair yaji ba sanda yaga na fito da first mukai murnar kammalawa na koma gida na zauna sai kuma Baffa ya sako ni gaba da maganar na fitar da mijin aure, iya tunani na banda kowa hakan yasa nabawa Bakon masoyi damar ya bayyana gare ni idan har da gaske sona yake zai aure ni Hajiya Umma ba karamin haushi taji ba lokacin dataga na kammala school mai tsadar gaske haka jin datai Baffah na yawan maganar na fitar da mijin aure yasa ta kudurce a zuciyarta bazata taɓa bari Rubina tai aure ba hakan yasa tai shirin zuwa gidan Hajiya laurah suka tafi gidan bokanya, Yau ina gidan Yay meer tun sassafe muke ta shirye shiryan tarbar sa yai sati huɗu kenan bai zo kano ba yai nace muje masa Abuja nida Matarsa yai ya gama matarsa ta ce bazamu ba wajan la'asar yadawo yana sauka ni kuma na fara shirin tafiya gida yace na jira sa bayan mangariba zaije gidan sai mu tafi tare, na amince da haka suka shige ɗaki shida matarsa ni kuma na zauna nan falo, murmushi nayi ganin mini laptop ɗinsa ajje kan seater da alama manta ta yai dan baya sake da ita acewarsa sirrin sa ta aiki ce, ina karasawa kan seater ɗin na kula da jakarsa karama ta kakin soji kamar wacce akace na buɗe ta na buɗe wangale bakina nayi ganin Diary ɗinsa dana jima ina son ganinsa sau ba adadi na taɓa masa bincike a ɗakinsa na gidan amma ban gansa ba sai yau na koma gefe ina buɗewa ina bi ɗaya bayan ɗaya ina karanta rubutun dake ciki, jikina yaɗau karkarwa lokacin danai tozali da page ɗin danake son gani tun daga farko har tsakiya kalaman damuwa ne da nuna tsananin damuwar yanda zai iya sanar da wata cewar yana sonta da daɗa ɗan kalaman da suka saka jikina yin sanyi, sanda nai tozali da zanan hotona da aka zagaye da hert numfashu nane ya kusa ɗaukewa _Kece farin cikina murmushina damuwata na rasa ta wacce hanya zan bi na bayyanawa Rubina irin ysanain son danake mata wanda na rayu da shi tsawon shekaru na rasa ta yaya zan bayyana maki cewar aure ya halarta a gare mu ina sonki Rubie ina kaunarki zanci gaba da sonki har karshen numfashi na_ wani ihu na doka tareda yin zillo banyi aune ba sai gani ɗakin Uwair da yanzu suka fito daga wanka shida Matarsa yana sanye da karamin tuwel wata shaka dana kai masa na zaro idanuna "Gaya min ka gaya min tayaya aure ya halarta a gare mu, gaya min ta inda yaya zai iya auran kanwarsa to idanma da auran a tsakanin mu bana sonka bantaɓa kaunarka ba" nakai hannu kan dressing miror naɗau car key na Anty Raiha na fito daga ɗakin da gudu, "Ke Rubina Rubina zo kizo nace" nai saurin datso masu kofar na kullesu ta waje na shiga mota na tashe ta, yanayin yanda mai gadi ya ga na figi motar yasa ya buɗe min gate da hanzari, ni kaina bansan iya adadin tashin hankalin danake ciki ba Ikon Allah kaɗai ya kaini gida ko motar ban tsaya rufewa ba na faɗa gidan da gudu ina wani irin kukan da sai a yanzu ya zo min na faɗo ɗakin Ummi bako sallama tana tsaye gaban danning nai wani irin juyo da ita ina zare mata idanu kamar wata sa'a ta nace "Ummi gaya min ki gaya min ni wacece nida Yay Meer waye ba ɗanku ba ki faɗa min gaskiyya Ummi" tafi mukaji daga bayanmu tareda kyalkyalewa da wata dariya "Fatima yau ga ranar tonon silili yazo yau ga ranar nadama tazo ga ranar sakamako yau ga illar abinda na daɗe ina nuna maku ke da Baffah kuka ki ji yanzu sai ki san yanda zaki sanar da ita ta gurɓatacciyar hanyar da aka haifo ta" Hajiya Umma ta kuma kecewa da wata dariya tana nuna Ummi da hannunta da Ummin tai sak jikinta yai wani irin sanyi...... *Alhamdulillah anan na kawo karshan Littafin Rashin mahaifana Book One ga duk wanda ke son cigaban wannan labarin zai biya kuɗin karatu 300 kacal ta wanan asusun 9014569692 Rabi'atu Yusuf Idris monay point shaidar biya ta wannan lambar 07039793439 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11