Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 11
washe baki nakai wayar kunne na na shagwaɓe murya "Allah nayi fushi Yayana ba yau kace zaka dawo ba kuma baka zoba bani da waya fa zamana ba waya ya daman har ramewa fa nayi" "Allah! da gaske ƴar lukutar Ummi ta rame mu gani bari na katse ina laptop ɗin Khalipha muyi vidio call" na daɗa haɗe rai kamar yana kallo na ce "Aina daina taɓawa Khalipha komai nasa jiya har gori yamin akan kawai na ɗau wayarsa nai game ai insha Allah bazan kuma taɓa komai nasa ba, nama gayawa Yaya Amjad yatawo min da laptop nima" Uwaimeer ya ɓata rai kamar yana gabanta aɗan fusace ya ce "Waya ce ki tambayi wani abu sau nawa zan gaya maki komai kike so ki gaya min nasai maki" "To kayi hakuri ni da naga kana ta ginin nan ga biki ya matso shi yasa ma fa na tambayesa anjima idan mukai magana da shi zan gaya masa yabarshi yayana zai tawo min da ita" "E ki gaya masa, gobe zan zo, zan taho maki da wayarki sannan in nazo sai muje asiyo laptop ɗin" "To nagode Allah yakara arziki yakawo karin girma a wajan aiki" "Amin, wane a kusa dake?" ta kalli inda Nura ke zaune yana cin snack ta ce "Nuri ne yazo dubani" "Ba kin warke ba name kuma zai rinka zuwar ma mutane gida, bama wannan ba wane bakon masoyi a wayarki?" na ɗora hannu aka tareda mikewa tsaye na kasa cewa komai ni gaba ɗaya ma na manta da wannan halittar, "Bazaki magana ba waton bakiji maganan dana gaya maki ba ko Rubina yaushe muka fara haka dake, kodai aure kike so" "Ni bance maka ina son aure ba ni bana ma sonsa fa shine kawai yake shirmansa" "To ki jini da kyau zanyi bloking ɗinsa zan kura gaya masa karya sake maki tex messages kina jina idan ya sake zansa a kawo min shi nan inda nake zan basa gwale gwale irin na sojoji, Rubina bata kowa bace akwai mai ita yana nan ina ta masa tanadinki" "Ni yaya duk ba wannan ba yanda zanyi Baffa yabarni maganar makaranta ni ita tafi damuna ba wata soyayya ba" "Gobe innazo zamuyi maganar jirgin safe zan biyo anan zanyi breakfast fancake kunun gyaɗa doya da kwai na keso" "Bakada damuwa Yayana kafin ka sauka na gama komai nida Khalipha zamu zo tararka a filin jirgi in Ummi ta bamu aron matar ta" "Ki cewa Khalipha ya karɓi makullin motata a wajan Ameer ko ma dai zanma Amir ɗin magana yabawa Khalipha key ɗin" "Tam sai gobe mu kwana lafiya" "Kin gaji da jin muryata" "E mana na gaji wannan muryar taka wazai yi marmarinta inba Anty Raiha ba" Uwaimir yai dariya tareda katse kiran wayar, karaf idanuna cikin na Nuraddeen dayai kuri yana kallona da alama ya jima yana kallon nawa batare dana sani ba, ya sauke ajjiyar zuciya har sannan idanunsa cikin nawa ya ce "Uwaimir ɗan Ummi ne?" "A'a ɗan Hajiya Umma ne" "Ok" yafaɗa tareda mikewa ya ce zai tafi, harya fara tafiya ya nufi hanyar fita daga ɗakin ya juyo ya kalleni ganin ina zaune anan inda nake zaune ya jiyo yadawo kusa da ni ya miko wayarsa ya ce "Samin lambar Ummi anan" na karɓa ba musu na saka masa lambobin Ummin na mika masa wayarsa "To kizo ki min rakiya mana" na mike ina dariya muka jera nida shi muka fita har wajan gidanmu na raka sa inda ya ajje motarsa ya shiga ya tafi sannan nadawo cikin gida ban wuce part ɗinmu ba na shiga na Ummu jin hayaniyar su yaya Usman da alama kwallo suke bugawa ina gafda shiga cikin part ɗin naji an jawo min rigata ta baya na tafi luu zan faɗi naji an haɗa ni da bango nan take gani na gaba ɗaya ya ɗauke na kwalla wata kara ina ihun kiran sunan Ummina *sakamakon wasu dalilai yasa na daina fitar da link na group ɗina idan har kinsan novel ɗib nan yamaki kina son cigaba da karantawa to kai tsaye yiwa Anty Mami magana ta wannan lambar zatai adding naki a cikin group ɗinmu da muke posting* 07039793439 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode Eight8️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* "Wayyo Allah na Ummi wayyo idona na daina gani, Yaya Khalipha yaya Usman kuzo ku taimake ni" ji nai an rufe ni da duka a duka jikina kafin na soma jin maganar Hajiya Umma tana faɗin "Yawwa Amir dakar min ita daketa iya karfinka naso ma ace dana haɗa kanta da ginin nan na haɗa mata jini da kwakwalwa ta haukace ma kawai mu huta banda iskanci da rainin hankali mai zakiyi da makullin motar ɗana da har zai zagi kaninsa dan kawai ya ce bazai baki makullin motar ba, ubanki ne yasai masa motar shegiya mayya mitsiyaciya mara galihu, yau saina nakasa ki yau saina maki illar da wannan kyan naki bazai amfane ki ba idan ma kyan ke ruɗar Uwaimeer yau zan kawo karshan sa zan nakasa ki" "Ummmiiiiii" nafaɗa da wani sautin da ban sake sanin inda kaina yake ba, Ummi na zaune gefan gadonta tana danna waya chat suke da yayarta dake maiduguri tana sanar da ita dawowar da aka masu da aiki kano Ummi na murnar ta sami ƴar uwa a kano, Khalipha ya shigo hankali tashe sai haki yake ya tsugunna yana nuna wa Ummi hanya yana haki "Ummi...ummi ki fita ga Hajiyarsu Yaya can zata kashe maki Rubina Ummi kilama sun kasheta itada Yaya Ameer" Ummi wurgi tayi da wayarta kan gado ta futo a guje ko arzikin mayafi babu a kanta sai hular kanta ta fito da gudu kamar wata karamar yarinya wata irin fincika tayiwa Hajiya Umma saiga Hajiyan yarab a kasa takai hannu ta bugawa Amir a kirji ya saki Rubina ta faɗo a hannunta ta fara girgiza Rubinan tana kiran sunanta "Driver!! Driver kawo mana mota da sauri dan Allah" Ummi ta koma part ɗinta ta ɗakkowa Ummi hijab a cikin nata a mota ta bata ta saka ta shiga motar suka nufi Asibitin malam Aminu kano da Rubina "Kai Ummu na rasa wacce kalar zuciya Hajiya keda ita mai Rubina ta tsare mata ne data tsane ta haka nikam wannan shine karo na karshe da zan kuma ɗaukar rainin Hajiya Umma a wannan karon da kaina zan shigar da report wajan ƴan sanda su mana tsakani da Hajiya Umma da Rubina na godewa Allah dayasa Baffah baya gari bare har ya taka min burki naga kamar shima tsoronta yake ji" "Ummi muyi fatan Rubina ta samu lafiya komai za'ayi saiya biyo baya ni ganima nake kamar bata numfashi" Ummi zaune a recepsion ta kama kanta kusan ta kasa aikata komai duk abinda ake bukata Ummu keyi ita dai tana zaune kamar wata stetus bin mutane kawai take da kallo har sanda Aliyu ya shigo hospital ɗin shida Abbakar babban ɗan Ummu, "Sannu Ummi ya Rubinan?" Aliyu ya tambayya sanda ya zauna kusa da mahaifiyar tasa, Abbakar na tsaye kamar gunki wayarsa tai kara alamar kira ya shigo ya ɗaga kiran ganin Baffa ne "E! gamu munzo hospital ɗin, e to ban sani ba Baffah bana gidan ina gidana Usman ya kira ya gaya min abinda ya faru da nazo gidan saina tarar sun taho hospital gamu dai yanzu munzo" yai shuru alamar yana sauraron ɗaya ɓangaran kana ya ce "A'a Baffah Ummi kaɗai muka gani gata nan bari na bata wayar" ya mikawa Ummi wayar "Abbakar ɗauke min wayarka a gabana kafin ya ragargaza maka ita anan bazan maganar ba bazan magana da shi ba bare ya hanani abin da nai niyya, ku kaini police stetion dan Allah na shigar korafi na" "Abubakar sa wayar a speaker ina jinta" yai kamar yanda mahaifin nasa ya ce Ummi taji muryar Baffah na magana "Fatima dan Allah kiyi hakuri kina jina kibar komai a hannuna zan tawo gida zan ɗau mummunan mataki akan Bintu" Ummi bata ce komai ba sai mikewa da tayi tabar wajan tabi Dr office ɗinsa "Kiyi hakuri Hajiya Rubina idanunta sun samu matsala jijiyoyin idanun sun tsaya a aiki yanzu dai muna kan bincike mu gano shin zasu tashi suci gaba da aiki ko kuma sun mutu kenan" Ummi ta jingina da bango tareda zamewa ta faɗi kasan tayals ɗin ɗakin ta fashe da kuka "Wayyo Allah na wayyo ni Fatima yau naga bakar rana yau naga masifa ido buɗe mai nake shirin ji, Rubina ta rasa idanunta Dr dan Allah a cire nawa a saka maka, dan Allah Dr kutaimaka min ku taimaka" ta karashe faɗe tana fashewa da kuka "Kiyi hakuri bamu ce ta makance ba har abada muna saka ran idan jijiyoyin idanunta basu matu ba zata dawo taci gaba da gani koda ba kamar na kowa ba" Ummi dai bata saurari mai yake cewa ba kuka kawai take Ummu ta kama ta suka shiga ɗakin da Rubina take "Ummi ummi bana gani duhu nake gani Ummi kina ina bakya jina ina idanuna ina gani na ya shiga ba kowa ba kowa a kusa da ni na farka fa Ummi kimin magana dan Allah Ummi kodai bana duniya ne kodai Hajiya ta kashe ni ne Ummi nasan koba kowa a kusa dani nasan ke kina tare dani kimin magana Ummi wayyo inaga na mutu shikenan na bar duniya na daina ganin Ummina Baffana Yayana Uwaimeer Yay Meer kana ina ina kake to kazo kai kazo wajena da sauri" Ummi ta rungume Rubina tana kuka sosai jin kalaman ƴar tata ta ce "Gani Mamata gani a kusa dake, ji kamshina kiji kamshin jikina Uwata ina tare dake har karshan numfashi na Assamu'u Husnah" "Ummi maiya sami idona maiya sa na daina gani to" "buguwa ce amma yanzu muna hospital verysoon zaki fara gani kinji Rubina ta, idan har kuɗi suna magani insha Allah zan nema maki magani ki dawo gani koda komai dana mallaka zai kare zan fara magana da Dr afara nema mana hospiral mai kyau a faɗin duniya ko ina ne zan kai ki insha Allah Rubina ko idanuna zan iya mallaka maki ni asamin nakin nasan zaki kula dani zaki min komai" Rubina ta kankame Ummi ta fashe da kuka jin sabuwar kaddarar data afko mata a wannan rana kuma "Ummi mainayi wanne zunubi na aikata sati biyu da suka wuce na karye yanzu kuma idanuna wayyo Allah na tuba Allah ka yafe min" shigowar Dr yasa Ummi ta saki Rubina tana kallon Dr ɗin "To Alhamdulillah sakamakon binciken mu ya fito jijiyoyin idanun Rubina basu gama mutuwa ba sanyi sukai zamu ɗorata a magani duk sati zakuna zuwa ganin Dr bayan sati huɗu zamu mata aiki insha Allah ganinta zai dawo" "Masha Allah mungode Dr Allah yasaka" "Amin hajiya zaku iya tafiya ga takardar magungunan da zaku siya a kula sosai da ita dan Allah" "Ba damuwa" Ummi ta faɗa bayan ta mike tana kallon su Abbakar dasuke tsaye carko carko shida Aliyu da Ummu "Abbakar ku tafi gidajanku muma zamu koma gida mun gode" "To Ummi Allah ya kara afuwa, sannu Rubina Allah yabaki lafiya" "Amin na faɗa ina makale jikin Ummina data kamo hannuna muka fara tafiya slowly tana kula da duk wani takuna har mukazo inda naji ta ce "Shiga mota a hankali kinji Mamana" Na shiga na zauna bayan na matsa harna tarar da mutum nakai hannuna na taɓa, "Rubina nice Ummu na rigaki shigowa motar zauna dai dai kinji" Ummu ta faɗa da tausayawa naji mun fara tafiya a motar na kai hannuna jikin Ummi ina laluba ta ta kamo hannun nata cikin nawa ta ce "Mamana ya akai" na kwantar da kaina a jikinta na fashe da kuka "Rubina nima kuka kikeso nayi, maine abin kukan to?" "Ummi tsoro nakeji karna makance inna makance shikenan bazanyi aure ba ko" tambayar tata tasa Ummi ta murmusa kana ta ce "Ko kin makance zaki aure Rubina saimu tafi tare gidan auran na rinka makikomai" nai dariya tareda ɗago kaina kamar ina gani HAJIYA UMMA Amir ne yataimaka mata ta tashi zaune ya kamata suka nufi part ɗinta yana mata sannu ganin yanda take ɗingisa kafarta "Amir lalle wannan yarinyar Fatima ta siyowa kanta masifa da kuɗinta sai nayi maganinta a gidan nan saina nuna mata ita karamar yar iska ce zanyi maganinsu daga ita har shegiyar ƴar tata" "Hajiya nifa tsoro nakeji bakiji yanda yarinyar ke kuka ba tana faɗin bata gani karfa muyi mata illa fa ina tsoron gamuwata da Baffah kinsan halinsa akan yarinyar nan" "To sai me Amir karma kaji wani tsoro shikansa Baffan anan ɗina nake ganinsa wallahi" Hajiya ta faɗa tana nuna tafin hannunta "To nidai hajiya kashe wayata zan bazan sake muyi magana da Baffah ba har sai yadawo kasar nan ma gamu kafin nan ya manta ko kuma na gudu adamawa gidan Nene itace zata hanasa duk wani abu dazaiyi ya hanu" "Ni kama tuna min da ita bari na maza ma na kirata nayi riga malam masallaci" Amir dai yasa kai ya fita yana zuwa harabar gidan yaga babban yayansu Mahmud wanda suke kirada Daddy ya fito daga motarsa yana kallon Amir ɗin daya gansa ya basar yai kamar bai gansa ba, a fusace Daddy ya karasa wajan da Amir ke tsaye jikin motar Uwaimir ya fisgi hannunsa suka shiga part ɗin Hajiya "Kai Mahmud lafiya zaka kamo min hannun ɗa haka kamar ka kama mai laifi" "Hajiya kunsan abinda kukayi kuwa keda Amir, Rubina fa ta daina gani gaba ɗaya Ummi nacan tana ikirarin zata shigar da kara mai kike zato zai faru a gaban ƴan sanda" "Komai zai faru yadaɗe bai faru ba Mahmud, akaini bangon duniya ma ba wajan ƴan sanda ba, duka kuma na daka ni na daketa ba shi ba bashida laifi komai duka nawa ne ehe, sai mai danna daki shegiyar ƴar da batada uba" "Hajiya niki gaya masa ya sakar min hannuna nai tafiyata abokai na na jirana zamu fita" ɗau Mahmad ya ɗauke fuskar Amir da mari jin yanda yake masa magana gatsal "Mahmud!!! ka kuma gangancin dukar min auta saina masifar saɓa maka ka sakar masa hannu yai tafiyarsa kafin nakai maka duka, idan kai baka kishina shi yana yi kai gaba ɗaya kana kan layin da Baffanku ya ɗora ku har maye kuda balle romansa mai akai akai wata can banza Rubina shegiyar waye baisan ita wace ba" Fuuuu Mahmud ya fice daga part ɗin Hajiyar ya nufi na Ummi daya hangi gilmawarsu yanzu 🔯🔯🔯🔯🔯 Nuraddeen shida Lameen zaune cikin gidansu karkashin bishiyun da suka zagaye wajan yai luf luf yana fitar da wani sanyin kamshi, ahankali Lameen ya ɗago idanunsa ya kafe yayan nasa da su wanda ya lura yai nisa a duniyar tunani yakai hannu ya taɓa sa, Nuraddeen yai girgigit ya ce "Na'am Innah" dariya Lameen yayi harda buga hannuwa ya ce "Ina kaga innar anan Innar da bata gidan nan ɗazu fa ta tafi gaya gaisuwa" Nuraddeen ya harari kanin nasa ya maida kansa ya kwantar jikin kujerar dayake kai ya ce "Kawai ka katse min tunani na mai daɗi gani ga ita a zaune cikin lambu muna bawa juna fure" Lameen ya zaro idanu yana dariya ya ce "Akaro na farko yau kayi zancan budurwa tun bayan rasuwar Hafizah" Nuraddeen ya buɗe idanunsa da suka fara canza launi ya kalli kanin nasa kana ya ce "Na mato dayawa Lameen lokaci ɗaya na faɗa kuma saina shiga irin sosai ɗin nan" Lameen ya kuma tuntsurewa da dariya harda tafa hannu "Wayyo Innarmu ga abin farin ciki gashi bakya gida ubangiji yadawo mana dake gida lafiya yau muyi farin ciki tuzuru ya kusa angwance wa" "Kai banza nifa zancan nan danake maka banfa faɗa mata ba, tsoro nakeji kar ace tanada wanda takeso" "Kanaji na yaya Noor kawai ka sami mahaifinta ai dattijon arziki ne ka fito sak ka gaya masa kana son ƴarsa yabaka dama ku dai daita, to in akwai maganar wani zai gaya maka in babu kowa kuma zai baka dama ku daidaita daga nan sai shirin biki bidiri wooni babban Aminin ango" Nura yakaiwa Lameen duka a kafaɗa ya ce "Ji baika kai bakaji kunya ba ta ina ka zama aminin ango kadai tsaya a kanin ango bama haka ba ya akai kasan wacce nakeso har kasan mahaifinta dattijo ne" dariya Lameen yayi kana yafara magana "To zamu gani Allah yanuna mana lokacin nidai nasan yaya Noor bashida Amini sama da ni, kuma tuni na gano ga wallahi yanda kake zarya gidansu Rubina ai kowa yasan ba iya duba lafiyarta kake zuwa ba harda gyara lafiyar taka zuciyar" Nuraddeen yai dariya kawai ya kalli agogon hannunsa ya mike ya nufi cikin gidan nasu yana sakin murmushi da cin alwashin Allah yadawo da Baffah lafiya ya gabatar masa da kansa Uwaimir yana tsaye gaban ɗan ginin dake kusa da gidansa hannunsa rikeda cup a hankali yana shan copi, lokaci ɗaya yaji gabansa yai wata irin bugawa da karfin gaske kafin ya kware da Copi ɗin dayake sha yai saurin zubo dana bakinsa kasa ya ajje cup ɗin ya shiga cikin gidansa ya ɗau wayarsa yana ambaton "Rubina", wayar Ummi ya kira tanata ring ba'ayi picking call ɗin ba harta katse ya kuma kira a wannan karon bugun farko aka ɗaga a maimakon yaji maganar Ummi sai jin Khalipha yayi yana kuka kasa kasa "Kha...Kha...li..pha" Uwair ya ambaci sunan nasa a rarraɓe gaba ɗaya ya ruɗe jin Khaliphan na kuka "Na'am yaya Uwair" "Ina Ummi tana ina bata wayar muyi magana mai ya faru maiya saka ka kuka yanzu?" "Ummi ta tafi da Rubina asibiti Amir da Hajiyarku ne suka kamata a part ɗin Ummu sukai mata duka Yaya ina jinma Rubina ta mutu zuwa yanzu bafa ta numfashi aka fita da ita shikenan munyi rashi yaya Uwaimir Rubina ta mutu ta barmu" da sauri Uwair ya lalubi bango ya jingina kafin kuma ya sulale ya zauna kan tayels yana bin wayar da kallo kamar wani soko yakasa aikata komai ma zuciyarsa gaba ɗaya ta tsaya cak na ƴan lokaci kafin kuma ya mike a zafafe ya saki wani ihu ya ce "Ina karya ne karya kake Khalipha ba yanzu ba, ba yanzu mutuwa zata rabani dake ba Abar kaunata wayyo Allah Hjiya Amir mai kuka aikata haka" da sauri ya shiga ɗakin barcinsa ya saɓo jaka harya fito ya kalli kansa yaga kakin soji ne a jikinsa ya koma ciki ya cire ya canza kaya ya fito kai tsaye ya nufi tashar mota baya jin zai iya jiran jirgin safiya ya sani nan da safiyar ko basu kai kano ba kaɗan zai rage masu tunda kwanan hanya zasuyi, cikin mota yayi lamo ya kasa aikata komai kansa yakeji yana tsananin sara masa, layin Daddy ya kira saidai harta karaci ring ɗinta bai ɗaga ba, shikenan kila zancan Khalipha ya tabbata Rubina ta mutu, ya kunna data ya shiga whatsapp ɗinsa ya duba stetus na ƴan gidansu yaji ba wata magana ya duba group ɗinsu Baffah Family yaga nan ba ba wani labarin rasuwar Rubina ya koma group ɗinsu na iya ƴan ɗakinsu nan ma baiji komai ba, kawai ya kifa kansa a cikin kafafunsa yana sauke numfashi yana jin yanda motar daya hau ke shoshala gudu a hanya kasancewar homer yahau amma duk gudun nan shi gani yake kamar driver ɗin baisan aokinsa ba, anan kano kuwa Daddy yana shiga falon Ummi ita kuma tana kokarin kiran waya tana magana da Khalipha "Warisha nakeson na kira ita kaɗai zata ita tayani yakin nan tazo ta kaini wajan ƴan sanda na shigar da korafi na" "Ummi dan Allah kiyi hakuri kibar maganar nan ayita a cikin gida family isshue ne fa" "Kai kasan family ɗin Mahmud ni bansan shiba gari ne ko unguwa anan kanon, acuci ƴata kuma ana kokarin hanani na kwatar mata ƴancinta" "Fatima idan baki kwatar mata ƴanci ba kinci kaza kazanci nace ƴan sanda ko maza maza kira min su suzo su tafi dani kiga inzan kwana a hannunsu, kai kuma mara zuciya soloɓiyo daman nan ka taho bada hakurin kar a kira min ƴan sanda dan Allah ba ƴan sanda za a kiramin ba barikin sojoji suzo su tafi dani ina shirye daga nan suje su jefani a teku koba komai burina ya cika yau na nakasta yarinyar nan Alhamdulillah, Ummi ta mike daga kan kujerar da take zaune ta fara naɗe hannun doguwar abayar dake jikinta tana nufar Hajiya Umma, da sauri Daddy ya shiga tsakanin su ya tare Ummi daya lura ta fusata "Ummi wai maine kuke haka dan Allah dan girman Allah ku bari ku tsaya ayi magana ta fahimta" "Mahmud fita daga cikin maganar nan ka matsa ka bani waje kafin na baje ka a falon nan, yau saina ramawa Rubina abinda matar nan ta mata billahil azim yau saina zubarwa da Bintu idanu a gidan nan dai dai nima a zubar min da nawa......" 07039793439 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode Nine9️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* "Mahmud idan baka matsa ka bata waje tazo ta zubar min da idanu ba saina saɓa maka, dan Ubanka matsa ka bata waje in batada hankali ta karaso nan wallahi sai dai a ɗauki gawarta" "Adai ɗauki gawarwaki dan wallahi kinyi kaɗan ki iya dukana na kyale ki ke a Mahmud ka bani hanya" "Ummi Hajiya dan Allah dan Allah ku bari haba mana" Warisha ce ta shigo ɗakin hankali tashe ɗazu sukai waya da Aliyu yake faɗa mata abinda yafaru nan take ta baro wajan aikinta ta shigo ta tarar da wannan hayaniyar, ita taja hannun mahaifiyarta takaita bedroom ɗinta ta fito ta kama hannun Rubina suka shiga cika ko kallon inda Mahmud da hajiya suke batai ba "Ummi gaskiyya yakamata kubarwa Hajiya gidan nan ko ki bani Rubina na tafi da ita har zuwa sanda Baffa zai dawo ni bana son wannan masifar ta Hajiya Umma gaba ɗaya taki bari gida ya zauna lafiya haba" "Ba inda zata kamar yanda nima ba inda zani ni sonake ma yadawo ya sawwake min na koma maiduguri cikin ƴan uwana na zauna nida Rubina daman nice dolanta ai" "Subhanallah Ummi daina faɗar haka dan Allah komai zai daidaita ni kawai sonai ace tuntuni Baffa ya fahimta sanda akaita ɗauki ba daɗin nan naso ya sake maki wani gidan da yayi hakan tun can lokacin da yanzu ba wannan maganar ake ba ai" Dakyar Mahmud yasamu Hajiya ta fita daga part ɗin Ummi har bayan insha yana gidan saida ya tabbatar da Hajiyar tayi laushi sannan yabar gidan bayan yaje ya kara bawa Ummi baki da rokon tayi hakuri karta kula Hajiya komai zatayi sanda ya koma gida ya tarar matarsa Sadiya ta cika tai fam azatonta wani wajan yaje yaki shigowa gida kamar yanda ya saba, ya kalleta yana murmushi sanda ya zauna cikin falon nasa yakai ganinsa ga yaransa da suka zubawa Tv idanu, Samiha babbar ɗiyarsa ta karaso inda yake tana dariya "Daddy barka da dawowa yaufa munyi fushi tuni har munyi dinner Momy tace kaje zance" Daddy yai dariya yana kallon matar tasa ya ce "Ke mamana manta da rigimar momynku ina can gidan Hajiya yau gidan gaba ɗaya ya runcaɓe sai rigima suke kamar wasu kananun yara da kyar na samu na yayyafawa wutar ruwa na baro gidan nikam mai zanyi da mata da yawa fitinarsu ma aitasa wannan ƴar kibar tawa ta zaizaye" ran Sadiya yai fari tai dariyar dabata shirya yiba Samiha ta koma wajan kannanta suka cigaba da kallo "To muje danning ga dinner ɗinka can a warmars" "Gadai sauran abincinka can zaki ce" sukai dariya lokaci ɗaya kafin suka jera zuwa danning ɗin Uwaimir karfe takwas na safe ya sauka tashar motar unguwa uku, gaba ɗaya yayi wani zuru zuru kamar mara lafiya adaidaita ya tsare zuwa unguwarsu lokacin da adaidaitar ta shigo layin ba karamin sanyi jikinsa yai ba shi gaba ɗaya yagama amanna Rubina ta mutu sanar masa ne kawai ba'ayi ba, ko kirga kuɗin daya bawa mai nape bai tsaya yayi ba kai tsaye ya faɗa gida zagayawa yayi ta can baya inda Hajiya bazata gansa ba ya faɗa part ɗin Ummi, Ummi

Chapter 6 of 11