Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 11
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [7/10, 1:29 PM] maman sauban: 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode one 1️⃣ *Taɓa ka lashe* Tsananin sanyin da ake a gari yasa yau gaba daya na kasa fita ko babban falo ina kwance cikin ɗakina nannaɗe cikin lallausan bargo, ganin kwanciyar bazata kai min ba yasa na sakko a hankali daga gadona na buɗe labule ina hangen compound na gidan garin yayi duhu sosai yanayin kamar na damina irin ruwa na gafda zuba, hazo ke zuba sosai a garin, takalmina dake ajje kofar bathroom na saka na shiga wanka na haɗa ruwa mai zafi sosai nai wanka na fito ina rawar sanyi nai saurin kunna room heater ɗakin yaɗan ɗimama na shafa cream mai kamshi na saka riga da wando na sanyi na kawo jibgegiyar rigar sanyi mai ɗan tsayi wacce ta wuce gwiwata na saka hular sanyi na naɗe kaina da karamin mayafi na feshe jikina da arebian oud mai daɗin kamshi, na fito daga room na karasa Danning room, tsit wajan ba kowa da alamar su Yaya Salman sun gama break kila har sun bar gidan ko kuma suna part ɗin Ummu, murmushi na saki sanda na hango mahaifiyata farin cikin rayuwata ta fito daga ɗakinta tana sanye cikin dubai abaya tai rolling mayafin abayar tana tafiyar nan tata ta kasaita Ummi mace yar kwalliya da son ado inkaga yanda take ɗaukar wanka bazaka ce itace ta haifemu ba, "Ummie Barka da safiya" "Barka dai Rubina sai yanzu kika tashi tun safe Baffa ke mita wai yanata kiran wayarki a kashe" ɗan ɓata rai nayi cikin shagwabar data zamar min jiki na ce "Ba Yah Uweer bane jiya yaita min masifa danna daɗe a online muna hira a group ɗinmu na school har yana gaya min waida saurayi nake chat ni kuwa nai zuciya na kashe wayar ma gaba ɗaya kuma Allah koya kira a wayarki ko wayar Yah Aliyu bazan ɗaga ba" na faɗa ina daɗa haɗe rai irin ba sauki ɗin nan "Nidai ba ruwana bana cikin wannan faɗan naki keda Yayanki inna shiga ciki ma ni zaku watsawa kasa a ido, Baffa yace inkin tashi ki kirasa" "Ummie shima fushi nake da shi ya tafi yai zaman sa a Dubai yaufa satinsa biyu kenan" "Wai fushin har Baffa ma ana yi da shi to lamarin babba ne bari na bar wajan nan kafin abin ya shafan" Ummie ta faɗa tana barin danning ɗin naci gaba da cin abincina hankali kwance saida na gama sannan na nufi part ɗin Ummu, natarar bata nan Sun futa dasu Yah Salman da sauran yaran gidan sa'anni na, nadawo nazo na ɗauki kur'ani na na koma garden zan karasa haddar da zan bayar anjima a islamiyya, nayi nisa a karatuna har bansan sanda Hajiya Umma tazo wajanba sai jinai an daka min tsawa tsawar data firgitani sosai jikina na karkarwa na mike sai kuma nai saurin tsugunnawa har kasa kamar yanda mahaifiyata Ummie ta koyar damu in zamu gaida manyanmu harga Allah ina matukar tsoro Hajiya Umma kusan zance nan duniya ba wacce nakejin tsoro kamarta "Hajiya Umma ina kwana" "Ban sani ba bansan inda kwanan yake ba, munafuka shegiya wacce batada asali, ban gaya maki karna sake ganinki a garden ɗin nan ba na yan gidane masu asali ba irinki ba bara gurbi, a karo na karshe zan kara jaddada maki karna sake ganinki anan idan har kika kuma gangancin zama a garden saina maki tabon da har abada bazaki taɓa mantawa dani ba shegiya" Hajiya Umma ta karasa faɗa tana murɗe min kunne tsananin zafin azabar danaji a kunne na yasa nakai hannuna na rike hannunta da har sannan hannun nata ke rike da kunnan nawa tana murɗawa "Kiyi Hakuri Hajiya bazan sake zama ba, na rantse bazan sake zama a nan ba har karshan rayuwata dan Allah karki ciremin kunne" na faɗa ina kokarin fashewa da kuka sosai "Yanzu dai bazan cire maki kunne ba amma tabbas kika sake muka kuma haɗuwa dake koba anan ba to tabbas zan bar maki tabon da bazaki taɓa mantawa dani ba" da sauri na bar Garden ɗin na koma part ɗinmu ina kuka sosai na ajje kur'ani na saman kujera na zauna kan tayals tareda kifa kaina jikin kujera ina kuka sosai kamar an sanarmin rasuwar Baffana "Subhanallah Rubina mai nake gani haka waya taɓa ki kike wannan kukan?" Ummie ta tambayeni hankali tashe "Ummie mai nayiwa Hajiya Umma ta tsane ni maina tsare mata mai yasa kullum take aibata ni tana kira na da mara asali Ummie da gaske banda asali mai yasa kullum maganarta akan hakane maine bara gurbi? mai ya haɗina da shi mai yasa zata hanani zama a inda tasan nafi kaunar zama a cikin gidan nan" Numfashi Ummie ta sauke tareda zama kan kujera ta ɗora kan Rubina a cinyarta tana shafawa ta kasa cewa komai saboda tsananin takaicin da zuciyarta ke ciki "Yi hakuri Mamana yi shuru ki sani nan gidan ubanki ne ba wanda ya isa ya hanaki zama a inda kike so ba wanda ya isa, wallahi an kaini karshe a gidan nan ya zama dole na nunawa Matar nan matsayinki a gidan nan hakurina yakare" UMMI ta sauke kaina daga cinyarta ta mike a fusace ta fita, Hajiya Umma na hakimce a kayatatcan falonta tana kallo, Ummie ta shiga kamar an jefo ta "Hajiya Bintu Hajiya Bintu" Ummi da idanunta suka rufe da ruwan masifa ta fara kwalawa Hajiya Umma kira sanda ta shigo wajan nata sam bata kula da ita a zaune ba saida taji maganar Hajiyan, Hajiya Umma ta gyara zama haɗe da murmushi ta kalli Ummi data shigo ɗakin a fusace "Fatima wannan kiran mafarautan fa na lafiya ne?" "Hajiya Bintu a gaskiyya kin kaini karshe abinda kike yiwa yarinyar nan yayi yawa a cikin gidan nan ina ɗaga maki kafa ne sabida bana son ganin ɓacin ran Baffa amma ke naga bakisan zuru ba to anzo dai dai inda bazan cigaba da ɗaukar rainin hankalinki ba akan Rubina kibar yarinya ta yi yanda taso a gidan ubanta" Wani kasaitaccan murmushi Hajiya Bintu tayi tana kallon Ummi kallo na baki isa ba kafin ta magantu har sannan babu ko ɗigon ɓacin rai a fuskarta "Gidan ubanta! ke yanzu Fatima da kina da kunya da hankali har zaki kira nan gidan da gidan uban Rubina, hmm naji a tafi a hakan amma ke idan so ya rufe maki idanu har kin manta hanyar da aka sami Rubina toni son bai rufe min nawa idanun ba bazan cigaba da zuba idanu wata can mara gata da asali tafi ƴaƴanmu na sunna watayawa a cikin gidan nan ba, a bayyane yake kowa na gidan nan yasan yanda akai aka sami Rubina dan haka kada ki kuma kuskuran shigo min part akan maganar banzar ƴarku mara asali ba," "Alhamdullila kindai yarda yar tamu ce ko to masha Allah tunda tana dani a gidan nan daga yau ba wanda ya isa ya taka ta ya zauna lafiya daga ku har ƴaƴanku mu zuba mu gani" Ummie ta fito daga ɗakin har sannan huci take na tsananin ɓacin rai, tana shiga Part ɗinta ta tarar babban ɗanta Aliyu ya zo shiya lallashi Rubina tayi shuru ta shiga ɗakinta ta kwanta, kallon Ummi yayi yanayinta kaɗai ya kalla yasan ranta a ɓace yake "Kiyi hakuri Ummi kowa da kalar kaddararsa tun tuni nace maki ki bani Rubina na maidata gidana kika ƙi, bana son wannan tashin hankalin tun Rubina na kankanuwa ake wannan faɗi tashin yaki ya kare ke hankalinki ba'a kwance ba haka na Baffa daya na nan da tuni da shi ake wannan ɓacin ran dan Allah Ummi ki bani Rubina na kaita gidana kindai san Hannah zata rike Rubina da zuciya ɗaya" "Aliyu bazan baka Rubina ba abu biyu ne zai rabani da ita mutuwa ko aure waɗan nan sune dolan da zasu rabani da Rubina na hakura dole, yau shekara goma sha biyar kenan ina tare da ita rana tsaka bazaka raba mu ba" Aliyu kwantar da kansa yayi jikin kujera yana wani lumshe idanu yai murmushin gefan baki can kasan zuciyarsa yake ayyana wani abu wanda zuciyarsa ta jima tana son faɗa amma baya son faɗa ɗin karya tada zaune tsaye "Idan kar kin yarda zaki aurar da ita a yanzu to zan kawo wanda zata aura" "Ba neman kai nake da yata ba ka barmin abata tana zaune a gidan nan Allah zai kawo mata miji ba kuma yanzu zan mata aure ba saita cika burinta na zama cikakkiyar likitar mata" murmushin gefan baki Aliyu yayi kafin ya mike zai fita sannan yake sanar mata sunyi waya da Baffa zasu biyo jirgin dare da asuba zasu sauka zaije filin jirgi yatawo dasu "Allah ya kawo su lafiya bani zaka gayawa ba Yaya ce keda shi bamu ba" tana gama faɗar haka ta faɗa ɗakin Rubina inda ta tarar tuni Rubinan tayi barci tana takure tsakiyar gadon ta kudundune waje ɗaya, Ummi ta gyara mata kwanciya tareda lulluɓa mata blanket ta shafi kanta ta fita Sanye yafito daga bedroom ɗinsa cikin kakin soji ya zauna nan kan kujera yana saka babban takalminsa na sojoji ya gama sakawa ya mike yana kallon kansa a madubin dake manne a bangon ɗakin yana gafda juyawa zai bar wajan karaf idanunsa suka sauka kan karamin frame da aka zagaye sa da fulawoyi masu kyau ya karasa ya sumbaci frame ɗin mirmushi kwance a kan kyakkyawar fuskarsa kasan makoshi ya furta "I LOVE YOU" ya sake sumbatar hoton haɗe da shinshina fulawar yana shakar kamshin da take futarwa, da baya baya ya fara barin wajan yana ɗagawa karamin frame ɗin hannu tamkar yana yiwa mutum bye bye sai da yakai bakin kofa kana ya juya ya fito cikin barreck ɗin, ɗaya daga cikin matasan sojin dake tsaye ɗan gaba da gidan daya fito ya kalli agogo yana taɓe fuska ya ce "Gaskiyya Ice Man ka ɓata mana lokacin" baiko kalli inda wanda yai maganar yake ba kai tsaye ya wuce inda jerin motoci ke ajje ya buɗe gefan bakar mota hilux ya shiga ya zauna da sauri driver ya shiga yaiwa motar key sauran ma da sassarfa sukai tsalle suka hau bayan hilux ɗin suka zauna sannan driver ɗin yaja suka fita daga cikin barreck ɗin, tun wannan fitar da sukai ta sassafe basu suka dawo ba sai gefan nin mangariba dai dai kofar shiga gidansa motar ta tsaya ya fita daga motar yana kallon waɗanda ke zaune nan bayan motar ya ce "Ina yabawa da kokarinku sosai kuci gaba da kokari ganin mun cika umarnin da genaral Karaye ya bamu fatan nasara" "Nasaraaa" gaba ɗaya suka haɗa baki suka faɗi haka, ya juya ya shiga gidansa kafin motar tai gaba da saura a ciki, "Wash" yafaɗa sanda ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin nasa ya fara cire takalminsa kafin daga baya ya cire kayansa ya rage daga shi sai boxer da singelet mai kalar kakin soji, mikewa yayi ya shiga wanka a toleit ɗin dake nan cikin falon ya fito ya zura jallabiya blue mai duhu ya ɗau hanyar masallacin dake cikin bareck ɗin, sai da akai sallar insha sannan yadawo gidan nasa kai tsaye kicin ya nufa wanda ke shirye kamar kicin ɗin wata macan kokarin ɗora girki yayi cikin kankanin lokaci ya dafa jallop na taliya ya zuba a plat ya dawo nan falon ya kunna kallo yanayi yana cin abincinsa hankali kwance, lokaci bayan lokaci yake ta kiran wata lamba taki shuga anata sanar masa wayar a kashe take murmushi yayi yana dannawa Ummi kira "Barka da dare Umminmu" yafaɗa sanda yaji Ummi ta ɗaga kiran" "Barka dai soja mazan fama ya aikin an dawo daga daji kenan?" "Mundawo Ummi" "To masha Allah Ubangiji ya taimaka" "Ameen Ummi inata kiran lambar mutuniyar a kashe," Ummi takai kallonta ga Rubina dake can gefe da alama Homework ta ke "Gata can tana aiki kasan gobe monday ana nan ana home work" "Ummi a bata wayan tun jiya ban sake magana da ita ba wayan a kashe ko wani abun ya sami wayar ne?" "To banace ba nima dai tun safe banga wayar a hannunta ba" "Rubina amshi waya Uwaimeer ke magana" "Ni bazan karɓa ba ba faɗa yamin ba sabida nakai tara ina chat wai da saurayi nake chat bayan ni da su Hanifa muke hira a group na school shi yasa ma na kashe wayan gaba ɗaya gobe ma zan bawa Khalipha aje a siyar da ita" Uwaimeer ya dafa kansa tuna yanda sukai jiya wai daman yar wannan maganar yasa ta kashe wayarta gaba ɗaya, Ummi dai saka wayan tayi a speaker ta ajje ta nan kasan carfet kusada Rubina tai gaba abinta "Rubie nifa wasa nake Billah wasa nake maki aidai nasan bakida saurayi nasan kin min alkawarin bazaki taɓa kula kowa ba sai bayan kin cika burinki, to na maine jin haushin naji yi hakuri to" turo baki gaba Rubina tayi kamar yana gabanta ta harari wayar kana ta ce "To yaushe zaka dawo?" "Ni ko yanzu ma kika ce na tawo tawowa zanyi Rubinan Baffah" "To ran friday ka dawo inka wuce haka Allah saida wayar zanyi gaba ɗaya kuma ko ka kira a wayar wani na gidan nan bazan ɗaga ba" "To ki huce" "Aina huce ɗin amma dai yau bazamuyi doguwar waya ba inada homework mai zafi inayi gashi Yaya Salman baya nan daya taya ni" "To ki nutsu kiyi gobe a min snapping na homework ɗin naga mark ɗin da muka samu saida safe Take care" "Obay Byee" ta faɗa tana cigaba da nazarin aikin ta, Numfashi ya sauke yana wani lumshe idanu ya ajje wayar yana ajjewa kira na shigowa "Reiha" ya faɗa a flili fuska ba yabo ba fallasa ya ɗaga kiran "Baby dawa kake waya" Raihana ta faɗa rai ɓace "Rubie mana" Raihana zuciyarta taji tai sanyi da har ta hau jin tanata kiransa line busy a tinaninta ko da budurwa yake waya "Ok ya take kwana biyu bata kawo min ziyara ba" "Zamu zo tare inna shigo" hirarsu suka ci gaba dayi daga jin hirar zaka san ta masoya ce, bayan sunyi sallama ya kashe wayan ya ajje a gefe ya karasa gaban fridge yasha ruwa mai sanyi ya wuce bedroom ɗinsa yai shirin kwanciya ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya barci kira ya shigo wayarsa maida kallonsa yayi ga screen na wayar ganin Mahaifiyarsa ke kira yasa ya tashi zaune da sauri yai picking call ɗin "Barka da dare Hajiyarmu" "Barka dai!" "Wai Uwaimeer mai kake nufi da kin zuwanka kana tuna nin kin zuwanka garin nan shizai hana maganar auranka da Raihana?" "Ba haka nake nufi ba Hajiya ai nace a tura kawai ama tsaida ranar bikin kawai basai nazo ba" "Ya kakeso nayi da Baffanka kadai san halinsa ko har idan ba daga bakinka maganar nan ta fito ba bazai taɓa aminta da maganata ba" "To kiyi hakuri zanzo karshan satin nan sannan zamuyi magana da Daddy shi sai yayiwa Baffa magana" bata sake cewa komai ba ta katse kiran RUBINA Yau Monday kamar yanda muka saba a gida a duk ranakun makaranta in akayi sallar asuba baza'a koma barci ba kowa zai fara shirin makaranta a ka'ida karfe bakwai dai dai muke fitowa mu shiga school bus wacce ke kaimu makaranta aduk asafiyar litinin talata laraba alhamis da juma'a Alhaji Baffah yarima shine mahaifinmu babban ɗan kasuwa dake kasuwanci da kasashe daban daban yana da manyan shaguna a kasuwar kwari da wambai ɗan asalin jahar adamawa ne kasuwanci ya kawo sa kano wanda har a yanzu anan kano yake rayuwa tareda iyalansa, yanada mata guda huɗu da albarkar yara maza da mata a kiyasi mazanmu da mata yaran Baffah mu talatin da huɗu ne Hajiya Ummah itace matarsa ta farko auran saurayi da budurwa tanada ƴaƴa maza guda biyar sai Mata guda shida cikin yaran nata babban ɗan Alhaji Baffa yake Yah Mahmud da muke kira da Daddy kamar yanda ƴaƴansa ke kiransa tun tuni yayi aure yanada babbar ƴa data isa aure, ta aurar da ƴaƴanta Daga Yaya Uwaimeer sai Yah Ameer su kaɗai suka rage a gabanta Amir shine autanta, Matar Baffanmu ta Biyu itace Hajiya Yaya tanada yara Takwas gaba ɗaya takwas ɗin nan ɗaya ce mace autarta Rahama , Mata ta uku Ummu yaranta Bakwai gaba layansu kuma maza ne, Sai Ummina data kasance Amarya a gidan Baffana mu mu Takwas ne ƴaƴanta Yaya Aliyu shine Babba sannan Anty Warisha Anty SANA yaya Amjad sai Salman Ni Assama'u da ake kirana da Rubina sannan kanne na guda biyu Khalipah ke bina sannan autan mu Usham, gidan Baffa wani irin gidane da sam matan nasa kansu ba a haɗe yake ba garama Ummi da Ummu suna shiri sosai amma kam Hajiya Yaya da Hajiya Umma kam kullum suna cikin faɗa sabida hali yazo ɗaya kowa ba hakuri Hajiya Umma ganin tanada manyan yara yasa take mulkin gidan kusan sai abinda tace dashi masu aikin gidan ke amfani hakan ke matukar bakantawa Hajiya Yaya rai da farko Baffa ya zuba masu idanu amma daga baya ganin kan ƴaƴansa na kokarin rabuwa yasa ya taka masu birki yai matukar kokari ganin kan ƴaƴansa ya haɗu waje guda akai sa'a kuwa kusan gaba ɗayanmu kanmu a haɗe yake in banda wasu daga cikin yayunmu mata dake taya iyayansu kishi gidanmu gidane na tarbiyya duk da yawanmu Alhamdulilah ba wanda ya fanɗare kowa yana da abin yi Baffa mutum ne na kwarai dattijon arziki duk cikin ƴaransa mata babu wacce ta taɓa wuce matakin scoundry daga sunyi candy yake masu aure sai dai da sharaɗin zasuci gaba da karatu karatun da yake ɗaukar nauyi da kansa har mace ta kammala karatun wasu na aikin gwamnati wasu kuma insun gama karatun ajje takardun kawai su ke gidanmu a yanzu daga ni sai Rahma muka rage mata a cikin gidan cikin tarin maza, Bakwai saura minti biyar na gama shirin makaranta na fito cikin Uniform ɗina Light Blue ɗin wando da farar riga da ɗan karamin hijab ina goye da school bag ɗita hannuna na rike da ɗan karamin flask dana zuba tea ɗakin Ummina na shiga inda na ga bata nan kai tsaye na wuce ɓangaran Baffa inda nake zaton zan same ta acan da asuba ta gaya min zai dawo Yah Aliyu ya tafi ɗakko sa, ina shiga Yaya Sulaiman na kokarin fitowa daga ɗakin ya wani gallamin harara yai gaba shima yana sanye cikin uniform irin nawa, "Oyoyo Rubina Rubinan Baffanta" Baffa yafaɗa yana buɗe min hannayansa, na zube a kasa ina gaida Baffa cikin girmamawa tareda tambayarsa ya hanya "Hanya Alhamdulillah Mamana tsarabanki na wajan Yayanku Amjad zai baki" "Na gode Baffa Allah ya saka da alkhairi yakara arziki mai albarka" "Ke Rubina da yallah ki fito mu tafi zaki makarar da mu da kika san baku gaisa da Baffan ba ki fito da wuri mana ko salon kija mana makara" yaya Sulaiman ya faɗi haka cikin tsawa ya juya ya fice Baffa na binsa da wani kallo "Wai kuwa Alhaji Rubina kaɗai kayiwa tsaraba a gidan nan tun ɗazu yaranmu ke shigowa ba wanda kayiwa zancan tsaraba sai ita shafaffiya da mai" Hajiya Umma ta faɗa a hasale, kallon da Baffa yabita da shi ba tare da yace komai ba yasa tai saurin yin shuru ta kyauda fuska gefe Ina fitowa yaya Sulaiman ya fara min masifa kamar zai kawo min duka nai shuru bance masa komai ba na shiga mota driver yaja muka soma tafiya ina jinsa yana ta mita shida su Rahama amma bance masa komai ba sai ma book ɗina danake dubawa ajinmu ɗaya da Sulaiman ss 3 sam nida shi babu wata jituwa inhar ba jin sunan mahaifinmu kayi ba bazaka taɓa gane nida shi wa da kanwa bane hakanan Sulaiman shida kanwarsa Rahama suka tsane ni bansan dalili ba ko a school bama wani shiri, dana gama duba book ɗina na ɗago na kalli Hisham yanda ya takure a kusa da ni yana jin tsoron yai wani kyakkyawan motsi Rahama ta dakesa dan sabon tane dukansa a kullum in mun ɗauki hanyar makaranta, na janyo sa jikina sosai Usham yaro ɗan shekara bakwai Rahama da Sulaiman keta hira har muka karasa school muka sauka a mota muka shiga cikin makaranta nida Khalipha muka raka Usham class ɗinsa pramary section sannan Khalipha ya shiga class js Three na wuce ajinmu ina zama malamin Math ya shigo muka fara karatu, Yau juma'a komai cikin ɗoki nake ɗokin dawowar Yaya Uweer gida Yaya Uweer nida shi akwai shakuwa mai tsanani kusan duk gidan ba da wanda na shaku da shi kamar Yayanmu Uwaimeer duk da kasancewarsa ɗan Hajiya Umma amma ina matukar ji da shi cikin yayuna tun ina karama kusan shine komai nawa hakan ya haifar da alaka mai zafi tsakanina da shi mukanyi komai tare sanda yana jama'ar bayaro kullum muna tare shi yake kaini school daga nan ya wuce tasu ya karanci Medicine harya kammala karatu yafara aiki a asibitin malam rana ɗaya ya birkice Allah ya kashe sa soja yake son zama ba yanda Baffa da hajiyarsu batayi ba amma yaki dole Baffa ya kaisa makarantar horar da sojoji dake Abuja lokacin daya zama cikakken soja akai posting ɗinsa Kaduna da can yafara aiki daga baya kuma aka cillasa can kudu inda yanzu haka yana can calabar....✍🏿 Game bukatar cigaba da bin wannan novel zaiyi magana dani whatsapp kawai 07039793439 [7/11, 9:41 AM] maman sauban: 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writing by Mamie

Chapter 1 of 11