Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 11
kana ya je ya tashi Khalipha dake ta barcin gajiya "Wash Yaya Uwair barcin bai isheni ba" "Jekai wanka kazo kaci abinci saimu fita muje mu gano Rubina" ya mike ya shiga wanka Uwair ya kawo masa kayan daya siyo masa yana fitowa ya gansu ya rinka murna da ɗoki yana aikawa Yayan nasa godiya, Uwair murmushi kawai yayi ya fita daga ɗakin Khalipha ya shirya ya fito falon yana sanye da jibgegiyar rigar sanyi, tareda Uwair suka ci abinci kana suka fita kai tsaye Uwair gidan abokinsa ya nufa da sukai karatun likita tare a jami'ar bayaro yana nan yana aiki sun jima a gidan nasa sun sha firar yaushe gamo shiya bawa Uwair mota ɗaya daga cikin motocinsa yace yayi amfani da ita kafin ya tafi suka rabo bayan yai masa alkawarin ziyarta sa ya duba Rubina a wayarsa ma yai waya da Ummi da Baffah, Kwanan Rubina biyu a hospital suka dawo gidan da su Uwair suka sauka bayan an basu magani tareda saka ranar da zasu mata aiki, Uwair ke kula da ita sosai shike haɗa mata ruwan wanka ya fito mata da kayanta ya fita a ɗakin saita gama shiryawa zai dawo abinci da kansa ke bata kulawa dai ta musamman yake bata kusancin da suka samu yasa suka kuma shakuwa da juna soyayyar Rubina ta kuma zagaye ilahirin jini da ɓargon jikinsa a yanda yakeji a yanzu a shirye yake tsab bada Hajiya Umma ba koda Baffa zai iya fafatawa, daran ranar daya kasance za'ayiwa Rubina aiki kusan kwanan zaune yayi kan dadduma yana addu'o'in samun nasara yai kuka sosai kuma yai yakini su ukun suka tafi hospital ɗin har bakin ɗakin da za'a shiga da Rubina ya kaita tana kuka sosai jikinsa shima yai sanyi musamman ganin Khalipha da shima ke kukan, tsawon sa'o'i suka shuɗe kafin aka fito da Rubina daga ɗakin zuwa wani daban hankali tashe yabisu ganin Rubinan ko motsi batai, kwana guda tai a yanayi na barci kafin ta farka Dr na tsaye a kanta yana mata magana Uwair dake zaune gefanta ya ce "Kinji abinda ya ce Rubina ki buɗe idanunki a hankali Rubina ki ambaci sunan Allah" "Yay meer kana kusa dani kenan tsoro nakeji idanuna sun min nauyi" "Buɗe su ki buɗe a hankali Rubina na kagu nai tozali da idanunki ko zuciyata zata sami salama daga kuncin da take ciki tsawon kwanaki" na motsa idanun nawa a hankali kafin na buɗesu gaba ɗaya hasken da na gani sosai sainai saurin maida idanun nawa na rufe na ƴan sakanni kafin na sake buɗewa idanun nawa dishi dishi nake gani ba sosai ba kamar can baya "Yay Meer na ganka ina Khalipha bana gani sosai" Uwaimir ya kalli Dr ya ya faɗa masa abinda Rubina ta ce Likitan yai murmushi yana magana da Uwair "Kinaji Rubina ya ce zai zama normal zasu ɗoraki kan magani ganin naki zaina daɗuwa kinji" kai kurum na ɗaga ina kallon Khalipha dake makale bayan kujerar da Uwair ke zaune, Rubina magani suka bata haɗe da glashin da zai kara mata karfin gani suka koma gida, a ranar Ummi ta sauka a kasar tunda zata taso sukai magana da abokin Uwair hakan yasa shiya ɗakkota a filin jirgi, Uwair daya fito daga kicin ya dafawa Rubina Copi jin alamar suna da bako yasa ya buɗe kofa sakin baki yayi cikeda mamakin ganin Ummi amma ganin Sadik a bayanta yana rikeda jakarta yasa yai murmushi ya bata hanya ta shigo, Ummi Oyoyo Rubina ta faɗa tana mikewa daga inda take zaune ta nufo ummin da gudu ta rungume ta, cikin shauki Ummi ta rungume Rubina tana kallon idanunta dake saye cikin glass ta ɗago kanta a ɗimauce "Rubina da gaske da gaske kina gani na Uwata wayyo Allah abin godiya wai har anyi aikin kai masha Allah, Uwair banida kalmar da zan iya gode maka da ita kasani a farin ciki bana wasa ba" "Ummi bakida kalmar da zaki iya gode min amma kinada abinda zaki ban nayi farin ciki fiyeda wanda kikai yanzu Ummi dan Allah ki tsaya min Baffah yaban Rubina" "Kai dakata" Ummi ta katse shi da sauri ganin Rubina ta aikawa Uwair wani kallo cikeda shock na maganar dayai "Ummi ji wata magana ta Yay meer dan Allah wai Baffa yabasa ni, toni ɗin ta wace daman aini taka ce, kanwar ka ce fa ni banda sama da kai ko yaushe ina gaya maka kaina daban ne a cikin yayuna" Uwair ya shafi sumar kansa kalar ta fulanin yola data sha gyara ta kwanta luf a kan yana murmushi ya ajje copee cup ɗin hannunsa yaɗau car key ɗinsa ya fita yana ce wa Ummi "Bari na samo maki abinci gidan nan bamu da komai" bai jira abinda zata ce ba ya fita daga gidan, Ummi ta zaunar da Rubina a kusa da ita kan kujera tana bin khalipha da kallo dayake sakkowa daga kan step yana mata kallon mamaki "Wai daman kece kika zo ina sama naji karan door vell na zaci ma ko yayanmu ne ya fita shi yasa fa na shiryo da sauri na fito na zaci Rubie na ɗakinta" Ummi ta kafe Khalipha da kallo ganin yanda cikin sati guda yai kiba kamar ba shi ba, "Kana nan zaune hankalinka kwance?" "Ummi kasar nan tayi billah addu'a ma nake Allah yasa na samu Baffa ya amince yaya Uwaimir yace zai ɗauki nauyin karatuna anan to Baffah dai muke shakka" "Uhmm wai mutumin da bai gama junior ba shine yake zancan cigaban karatu" Ummi ta ce tana bin gidan da kallo "Yanzu duk shi Uwair ɗin ya kama maku wannan gidan kuke rayuwa abinku lalle ai magana kuma ya ce aishi karamin ma'aikaci ne ba wani kuɗi yake samu ba ko ina ya samo waɗan nan" Rubina na jikin Ummi ta kasa motsawa nan da can har Uwair yadawo ya kawowa Ummi abinci da kwalban ruwa dana lemu yana mata sannu da hanya, Baffah yaso daga saudiyya ya wuce Londan amma bai samu dama ba ranar da Ummi tabar kasar daran ya sauka a nageria, a ɗakin Ummi tafiyar ta kama sa tanada sauran kwana guda gashi bata nan hakan yasa Hajiya Umma ta tarɓesa, Nuraddeen na zaune cikin office ɗinsa wajan sha ɗaya na safe kiran wayar daya shigo masa yanzu yasa yaɗauke ganinsa ga system ɗinsa dayake kallo, da sauri ya ɗaga kiran ganin kiran da kullum yake jira ne daga gidansu Rubina daya faɗawa ɗaya daga cikin scurity na gidan cewar duk randa Baffah yadawo dan Allah yakira ya faɗa masa "Barka da aiki" Barka dai brister daman nace bari na kiraka na sanar dake dawowar Baffah" "Na kuwa gode sosai zan shigo anjima da yamma insha Allah" "To Allah yakaimu" Scurity ya faɗa yana katse kiran, Nuraddeen yai shuru tareda zubawa wayarsa idanu kafin kuma gabansa yai wata irin faɗuwa ya maida ganinsa ga system ɗinsa yana cigaba da aikinsa bai bar office ɗin ba sai wajan uku na rana ya koma gida lokacin yatarar gidan sai Innah lameen bai dawo daga kasuwa ba, wayar kanin nasa ya kira ya sanar masa yadawo da wuri zai masa rakiya gidansu Rubina Baffah yadawo.... 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode Eleven1️⃣1️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* Sanye ya fito cikin dakakkiyar shadda marun gezna ɗinkin ta zarce ya kafa hular zanna bukar sai baza kamshi yake ya tsaya nan falon yana kallon kofar ɗakin kaninsa Lameen ya taɓe baki "Lameen dan Allah ka fito kana ɓata min lokaci da yamma fa naso muyi tafiyar nan amma kai zamanka a kasuwa baka dawo ba sai mangariba ni dana sani ma bakai nace ka rakani ba" Lameen daya fito daga ɗakinsa hannunsa rikeda hula yana kokarin sawa yai dariya yana kallon Innah da itama fitowarta kenan daga ɗakinta tana murmushi idanunta nakan Nuraddeen "Kaima yaya Nura ji wata magana towa kake da shi sama da ni nidai nasan ko ina zaka bazaka iya tafiya babu ni ba sabon nan na tun yarinta bai barmu ba, nima haka wataran zaka rakani zance wajan budurwata" Nura ya kaiwa Lameen duka ya goje tareda zuwa bayan Innah ya tsaya yana leken fuskar lamin daga bayan Innah "Innah walahi ɗan nan naki ya raina ni waye zai rakasa zancen wajan budurwa katon dani zan tsaya ina rakaka zance, ni kana ɓatan lokaci zanyi tafiyata" "Innah mu zamu tafi ki mana addu'a ga Lameen zai ɗau hanyar nemowa Nuraddeen auran Rubina" Nura ya dafe kai yana aikawa kanin nasa wani kallo kana yamaida ganinsa ga Innah da har sannan tana tsaye inda take tana murmushi "Innah nidai na hakura da tafiyar nan jiwai zai nema min aure kamar wani kawu Jazuli" "Kai wasan ya isa haka waje zaku mai mihimmanci ko shiga nutsuwarku Allah yabada sa'a yatabbatar da alkgairi a lamarin nan Nura nai farin ciki sosai gidan Baffah gidane na mutumchi sai dai sun fimu komai mudai dama ba wasu masu kuɗi bane rufun asirin Allah ne karka ɓoyewa Baffa kai waye ka gaya masa gaskiyya karka sake ko a waje ɗaya ka masa karya idan Allah ya nufa Rubina matarka ce sai kaga anyi abu cikin mutumchi Allah yai mana jagora" "Amin Innarmu" Lameen da Nura suka haɗa baki wajan faɗa kana suka fita, Lameen ke tukin motar yayinda Nuraddeen ke zaune seat ɗin mai zaman banza yana danna wayarsa ya ɗago ya kalli kanin nasa shima shi yake kallo suka sakarwa juna murmushi "Lameen ji nake gaba na na faɗuwa, son yarinya nan ya shige ni ban shirya ba, maganganun Innah na yanzu sai yasa naji kamar ban dace da Rubina ba ita ƴar manya ce kadai ga gidansu kaga mahaifinta bama haɗi sun fimu nesa ba kusa ba" Lameen yadafa kafaɗar Yayan nasa yana tuki da hannu ɗaya "Hausawa sunce faɗuwar gaba asarar namiji, kasa haka a ranka Yaya ka nemi soyayyar yarinyar idan har tana sonka to an gama komai nasara na tare damu insha Allah yayana kadai ka tsara kalamai na gaskiya yanda kake sonta Allah yasa itama ta soka" "Amin nagode! kullum ina alfahari daya kasance Innah ce mahaifiyarmu data nuna mana haɗin kanmu Allah yajikan Baba" Lameen ya furta amin kasan laɓɓansa lokacin dayai parking a kofar gidan Alhaji Baffah Yarima, suka fito daga motar suka shiga gidan ta karamar kofar gate mai gadin gate ɗin farko yataso suka gaisa suka shige ciki gate na biyu scurity ya taso da sauri yaba Nura hannu suka gaisa yana murmushi ya kalli Scurity Sadam ya ce "Ka sanarwa da Baffah yana da baki" Sadam yaɗau waya ya kira Alhaji Baffah ya ce a shugo dasu falonsa na baki, Nura suka bi Sadam zuwa cikin kayataccan falon Baffah dayake saukar baki wani ni'imtaccan kamshi ne yadaki hancinsu lokacin da suka bayyana a falon nan kasan carfet suka zauna zaman su kenan Baffah ya shigo ta wata kofa daban da alama ita daga part ɗinsa take, fuskarshi ɗauke da fara'a ya zauna kan kujera yana faɗin "Takwara wai kaine daman kuma ka zauna a kasa dan Allah ku tashi ku zauna kan kujera" Nuraddeen yai kasa da kansa "A'ah Baffah nan ma ya isa Ina wuni an dawo lafiya" "Lafiya kalau alhamdulillah fatan mun sameku lafiya?" "Lafiya kalau Baffah" "To masha Allah ga mutuniyar taka suna birtaniyya ta sami matsalar idanu suna can itada Uwaimir yau Ummi ta bisu ance ma anyi aiki cikin nasara nima jibi nakesa ran zanje na gano ta" Nura ya muskuta ya gyara zama ya daɗa kasa da kansa kana ya ce "Daman Baffah nazo ne akan inaso amin izinin fara neman auran Rubina da gaske nazo ba yaudara ba idan Rubina ta amince dani zan turo magabata na kuyi magana ta manya ban sanar mata ba na bari kafara bani izini tukun" Baffah yai shuru na ƴan sakanni yana wani tunanin daban a zuciyarsa kana ya numfasa "Masha Allah Nura nai mamaki daman har yanzu akwai irinku a duniya da zasuga yarinya suna so basu bayyana mata ba su fara neman izini daga iyayanta nayi murna kuma zanyi farin ciki idan ya kasance Rubina ta amince da kai na yaba matuka da tarbiyarka na baka dama ka nemi soyayyar ta idan har ta amince ka fito ayi magana bana son dogon zanje cikin watanni biyu nakeso a yi komai a gama sannan ina son kazo gobe da mahaifinka muyi magana" "Baffa mahaifimu shekaru goma kenan da Allah yai masa rasuwa sai dai inba damuwa zan iya zuwa tareda Mahaifiyata" "E! duk ɗaya ne maganar aure ba ɓoye ɓoye ka sani shi yasa nakeson sanar daku komai a kaina kamar yanda nima zan saka amin bincike a kanka" "Tam insha Allah Baffah zamuzo gobe iwar haka" "Badamuwa Allah yakaimu nama cika ku da magana ko ruwa ban kawo maku ba" Baffa yafaɗi haka da murmushi a fuskarsa ya karasa gaban babban fridge ɗin dake ɗakin ya ɗakko goran ruwa dana lemu ya aje a gabansu "Baffah alhamdulilah a koshe muke" "Aiba abinci na kawo maku ba lemu ne da ruwa kuma ya zama dole sai kun aha zakubar falon nan" Lameen ya ɗauki goran lemu ya buɗe yasha ya ajje saura Lameen ma yasha na ruwa kana sukai masa salama, bayan sun koma gida suka sanar da Innah yanda sukai ta ce goben insha Allah saje da Nuran, Nura yaita kiran lamban Ummi bata shiga yana son suyi magana yaji yajikin Rubinan saida yatawo ya tina daya karɓo lambar da zai sami su Ummin acan london yanzu kuwa ba dama ya kira Baffa ya ce yaturo masa lamba, haka yai hakuri ya jure har washe gari da sukaje da Innah a inda ya tarbe su jiya yauma can suka zauna bayan an gaisa Baffah yafara korowa Innah jawai bai da faɗa mata asalin wacce Rubina, Innah ta numfasa bayan Baffah ya gama magana ta ce "Hakika kayi kokari dan ba wanda zai zaci haka ni ta ɓangare na ba bu wata damuwa ɗana kowa ne ga Nura nan idan har ya amince zai auri Rubina a haka to ina bayansa zaɓinsa shine nawa" Nura ya cire hular kansa yana fufita da ita duk da kuwa A c dake aiki a ɗakin can ya numfasa ya ce "Baffah na amince zan auri Rubina sanin ita ɗin wacece bai rage kaso ɗaya daga cikin son danake mata ba sai kaunarta da tausayinta da suka karu a zuciyata zanci gaba da adana maka wannan ɓoauyan sirrin har zuwa sanda da kanka zaka sanar da ita ko ita ɗin wacece tunda har Innata ta amince da zaɓina nai maka alkawarin ko kanina Lameen bazai san wannan maganar ba zata tsaya a tsakanina da Innah kawai" "Masha Allah nayi farin ciki sosai Takwara na, kuma na baka dama daga yau ka nemi soyayyar Rubina fatana ta amince da kai tabbas idan ta sameka ta yi dace da masoyin kware" Innah sukaiwa Baffa sallama bayan Nuraddeen ya karɓi lambar Uwair ta can zai kirasa ya haɗa sa da Rubinan, London Ummi ta gama shirinta na kwanciya barci ta kalli Rubina dake zaune a kusa da ita, Uwair ya buɗe kofar ɗakin ta shigo da sallama hannunsa rike da System da sabuwar wayar daya saiwa Rubina tun a randa tai Candy, yaiwa Ummi barka da dare bayan ya zauna kan sofa idanunsa nakan Rubina dake danna wayar Ummi "Rubie ga wayarki da system ɗin danai maki aljawari" da sauri ta ajje wayar Ummi nan kan gadon ta tawo da gudu ta faɗa kan Uwair dake zaune, da sauri yasa hannu ya cirota daga jikinsa ya kankance ido yafara aika mata ruwan masifa "Waike yauahe zaki girma sau nawa ina gaya maki ki daina faɗo min jiki irin haka bakiga kin girma bane yanzu da da aiba ɗaya bane" Ummi kallo ɗaya taiwa Uwaimir ta kauda kai tana murmushi, Rubina ta koma gefan gado ta zauna tana kallon Uwair dake ta faɗa har sannan idanunsa rufe, taja tagumi hawaye suka wanke mata idanu yana buɗe ido yai tozali da hawayanta gaba ɗaya ya ruɗe yadawo kusa da ita yasa hannu ya janye mata tagumin "Kinga toyi hakuri nai maki masifa nima bansan nayi ba kin gane kawai ki daina faɗo min jikina idan nai maki wani abu da kikai farin ciki kimin addu'ar samun cikar burina kina ji ko Rubie dan Allah daina hawayan karya haifar maki matsala kuma a idanunki" ya ɗora mata wayar da System ɗin a kan cinyarta ya mike ya fita daga ɗakin, Ummi ta kalli Rubina da har sannan bata taɓa wayar da system ɗin ba "Kinji haushin abinda yai maki gaskiyya ya faɗa maki Rubina ki daina irin haka" kai kurum na ɗaga mata na ajje Wayan da system ɗin kan madubi na fita daga ɗakin na shiga ɗakin da yake, yana zaune kan tayels ya ɗora kansa a gefan gado duka hannuwansa ya ɗora akan nasa na jima ina kallonsa kafin nai magana "Yay meer" da sauri ya juyo yana kallona batare daya ce komai ba, na karasa inda yake zaune na tsugunna na kama hannunsa na rike ina kallon cikin idanunsa da har sun canza launi na ce "Kayi hakuri bazan sake ba kaji na tuba" ya kakalo mirmishi ya ce "Ni banyi fushi dake ba Rubie Yay Meer ɗinki baya taɓa fushi da Rubinan sa, jibi zanbi jirgin safe zan koma wajan aikina ga Ummi nan tazo kuci gaba da zuwa hospital kuna ganin likita" "Yanzu Yay tafiya zakai ka barni nidai mu tafi tare ai naji sauki idan nasa glass a idanuna ina gani sosai" "Kidai zauna ɗin yau saura sati Uku bikina da Raiha inaso na tafi a larasa ginin kasan nan saman a yanda yake zan barsa wata nakewa tanadin sa" na zaro idanu ina kallon sa da mamakin maganar tasa "Yay Mee wai da gaske wata ka gano cab amma baka kautawa Anty Raiha ba" "Ita waccan daman tun tuni take a zuciyata ban sami dama bane amma yanzu na fara ganin haske da ace zan sami yanda naso da ita zan aura daga ita bazan kara wata mata ba sabida tsananin son da nake mata na rayu da kaunarta yau sgekaru da dama kenan, Rubina kimin addu'a Allah ya mallakamin Husnah" na washe baki na ce "Lah sunan mu ɗaya a ina take najw na ganta dan Allah nai mamaki ashe duk son nan da kakewa Raiha akwai wacce zata iya takushe soyayyarta a zuciyarka" "Tabbas inason Raihana saidai ko wacce mazauninta daban a zuciyata kawai kidai sani Husnah ta dabance a zuciyata tafi ki kwanta barci" na mike na fita daga ɗakin na koma na tarar Ummi batai barci ba har sannan naɗau wayana ina dannawa cikeda jin daɗi, ya saitan komai facebook whatsapp instergram duka Raihana sun fito daga lacture itada kawarta Rahima suna tafe suna hira can Rahima ta canza akalar hirar tasu dai "Raiha biki nata matsowa yau saura sati biyu kenan banga kin fara shirye shirye ba" "Hmm" Raihana ta sauke numfashi ta ce " Sonake wai saura sati biyu saina fara gyaran jiki maganin sanyi dai na fara sha Momy ba na bani wasu maganin mata kuwa nidai inaga bazan sha komai ba" Rahima ta tsaya daga tafiyar da take tana aikawa da Raihana wani kallo kamar zata kai mata duka ta ce "Bazaki sha komai ba kamar yaya yau nakejin wani shirme a wannan zamanin da mazan kar sukw kallonmu kice bazaki sha komai ba iya maganin sanyi zakiyi ai wallahi karma ki soma wannan gangancin magani zaki sha sosai ina gaya maki zan yiwa yayata magana tana zamfara ta iya haɗin amare na bala'i zan bada kuɗi a kawo maki amma fa ba'a fara sha sai ana saura sati guda auran karki kai kanki bamu shirya ba" Raihana tai dariya suna cigaba da tafiya har suka fito daga cikin makarantar hirar bikin suke da tsara event ɗin da zasuyi, "Amma dai Raihana zakiyi allurar planing karkije daga shiga ki kwaso tsaraba kalli dai yanda kawarmu Safiyya ke fama da laulayi duka ko wata uku ba'ayi da bikin ba" "Wallahi Rahima kamar kin shiga zuciyata nima tunanin dayake raina kenan ina ta cewa anya ba Allura zanyi ba nifa so nake na mori amarci na ba daga zuwa sai ciki ba kaita fama da laulayi" "Ai bama cin amarcin ba ni karatun nan nafi jiye maki ma munyi rabi saura rabi mai zai hana satin bikin muje hospital amaki allurar wata uku daga nan sai ki cigaba da yi bayan wata uku ukun" "To haka za'ayi ma Allah yakaimu lokacin" "Amin" Rahima ra faɗa ita ta fara samun abin hawa ta tafi kafin daga baya Raihana ma ta sami nape tahau zuwa unguwarsu 🔯🔯🔯🔯🔯 Amir tsaye gaban falon Hajiya Umma dake saman benenta yana rikeda littafin karami yana nazarinsa kamar ance ɗago ya ɗago yana kallon waje, Salma tafe tana gyara zaman mayafinta sabida iskar dake kaɗawa a yammacin karaf idanunsa suka sauka kan kirjinta gabansa yai wata irin faɗuwa yai saurin kasa da idanunsa kafin yabar inda yake jingine da bango ya shigo falon ya biyo step ya sakko kasa yai sa'a hajiya bata a falon yai saurin shigewa ɗakinsa dayake shi ɗan gaban goshi hajiya ne kuma autanta yana nan ciki wajanta bai da ɗaki a boys Quaters na gidan yana shiga ɗakin sa yafaɗa kan gado yana faɗin wash Allah yai wani juyi can kuma ya mike ya fita daga gidansu ya zaga layinsu Amira ya zauna a dandamalin kofar gidan yana danna wayarsa kamar wanda ke jiran wani abun, Salima kamar wacce aka ce leko ta leko taga Amir zaune a kofar gidan nasu cikin mamaki ta kira sunansa "Amir" juyowa yayi da sauri yai sa'a Salima bako mayafi a jikinta sai ɗan kwali data ɗaura gaba ɗaya halittun kirjinta sun leko ta cikin rigar dake jikinta kasancewar ta zauna sosai a jikinta idanunsa akan kirjin nata ya sauke gwaron numfashi kafin ya basar ya ce "Kwana biyu banga gilmawarki ba shine fa nace bari na leko layin naku" Salima ta koma ciki ta sako ɗan karamin mayafinta shantali mini ta fito ta zauna kusa da shi tana dariya "Kasan nima rannan na gama cigiyarka wajan Ghali yace min baka nan kaje wudil makaranta" "Jiya nadawo nai weekend a gida shi yasa nace bari na nemi ki mu gaisa tunda ke bakya neman mutane" "Nifa da inada lambarka amma yanzu banda ita bansan ina ta shiga ba" ya kallo wayar hannunta ya taɓe baki kana ya ce "Kina babbar yarinya dake kina rike keypad gaskiyya yakamata ki canza waya kema ki faso gari, bari na mike na tafi zanje tal'udu na karɓowa Hajiyarmu atamfaofin ankon wana da za'ayi" Salima ta mike "Wai har tafiya zakai" "Ko zaki min rakiya na fito da mota mu tafi" Salima ta zaro manyan idanunta tana murmushi "Wace ni na shiga motarka irin taku ce sai ƴaƴan manya irinka" "Kema kin kai jirani kawai na shiga na fito da motar jirani a bakin layi sabida munafukai" Salima tai jim tana kallon kofar gidansu kamar ta shiga ta faɗawa Mama saima ta tuna Maman tun safe sun fita aikin abincin biki tasa kai ta nufi bakin layin..... 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode Twelve1️⃣2️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* Tana karasawa karshan layin ta hangi mota parke a gefe ta nufi wajan murfin motar da taga an buɗe mata yasa ta karasa da hanzari ta shiga kusa da mai tuki ta zauna "Karigani zuwa" yai murmushi yana mata wani kallo kasa kasa ya ce "Ko'a kafa nake ai na rigaki zuwa nan bare a mota nake wannan tafiyar taki ta musamman ai ba duk mata ba, wai ni kuwa Salima kina kallon kanki a madubi kuwa gaskiyya ke kyakkyawa ce so cut masha Allah" Salima ta rufe fuskarta da hannuwanta tana murmushi kafin ta ce "Nagode" yatashi motar suka fara tafiya slowly suna hira, cikin wayo da dabara ya nuna yana sonta da gaske auranta zai yi har

Chapter 8 of 11