Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
a fusace ta shammaci Hajiya Zainab takai mata wani duka a fuska sai ga jini ya fara zuba daga hancin Hajiya Zainab ɗin, da sauri Ummu da shigowarta gidan kenan ta dawo daga unguwa ta ruko Ummi ganin tana kokarin sake kaiwa Hajiya Zainab wani dukan "Subhanallah Ummin Rubina mai zan gani haka yau mai yasa zaki biyewa Maman Rahama kuzo kuna wannan abin kunyar kamar wasu kana nan yara" "Barni Ummu barni yau na nunawa matan nan ba tsoronsu nake ji ba, ba Baffah bane sabida shi daman nake ragawa kowa a gidan nan to daga yau na daina ɗagawa kowa kafa wanda duk ya taka ni nima zan taka sa akarshe maine dai sakine ko to ya sakeni na ɗauke Rubina na bar maku gidan da ita natafi inda zamuji daɗin rayuwarmu" "Ki tafin mana wane bai sani ba kowa ai daman ya sani wajan biye biyan mazanki kika samo cikinta ai" Hajiya Umma ta faɗa wacce bata daɗe da zuwa wajan ba "Na samo ɗin ki bari mata masu aji suyi magana ba irin kiba mara mutunchi da asali" da kyar Ummu ta iya jan Ummi zuwa part ɗinta tana vata vaki tareda nuna mata illar biye ma Hajiya Zainab da tayi, acan Hajiya Umma itama ta taimakawa Hajiya Zainab jinin dake zuba daga hancinta ya tsaya taci gaba da mita tareda cin alwashin saita kawo karshan zaman Ummi da Rubina a gidan kota halin kaka, Amjad da Uwaimeer sanda suka shigo gidan sukaga ma'aikatan gidan mata da scurity sunyi cirko cirko suna magana kasa kasa sam basu kawo komai ba azatonsu sun sami labarin haɗarin Rubina ne kai tsaye Uwaimeer ya wuce part ɗin hajiyarsu shima Amjad nasu part ɗin ya nufa ya tarar Ummu na rikeda Ummi da har sannan take mita da sauri ya karasa gaban Ummu yana tambayarta lafiya nan ta zayyane masa komai Amjad ya shaida masu abinda ya sami Rubinan Ummi ta gyara kanta suka koma hospital Hajiya Zainab ta koma part ɗinta tana mita ta kira lambar Baffah tana kuka ta fara magana "Baffah ka dawo gidan nan kafin matarka ta kashe ni, harni wannan yarinya Fatuma zata saka hannu ta daka" "Zainab wai mai yasa bakwason zaman lafiya ne in an girma asan an girma mana kuna abu kamar kana nan yara" "Zakace haka mana Baffah tunda ba nice na taɓa ta ba to wallahi ko ka taka mata birki ko kuma na aika a rama min" "To yi hakuri bari nazo gidan muyi maganan yi hakuri" kwafa Hajiya Zainab tayi ta katse kiran tana zagaye a falon nata Baffah yabi Ummi da kallo ganin yanda ta shigo ɗakin tana cika da batsewa ko kallon inda yake batai ba, Baffa yai murmushi kana ya ce "Kinga tsautsayin da Rubina ta gamu da shi yau ko?" "Ka kira haka da tsautsayi mana bayan ɗanka Sulaiman shiya biyo driver suka tawo suka barta a can wannan ba tsautsayi bane gangancin Sulaiman ne" "Kiyi hakuri ai tafaru ta kare nan da ƴan watanni Rubina na gidan mijinta kilama bata kanon ma gaba ɗaya" wani kallo Ummi taiwa Baffah kafinta ta magantu "Aure kuma Baffah dan Allah ba yanzu ba duka nawa Rubina take sixteeen fa dan Allah ka bari ta cika burinta a karo na farko na roki wannan alfarmar dan Allah" Ummi ta karashe magana tana haɗe hannunta biyu waje ɗaya alamar roko "Idan nai haka zai tabbata kenan banyi adalchi a tsakaninta da sauran ƴan uwanta ba, inda zan iya barin mace tai karatu bayan ta sami mijin aure to Sanah ce sabida kokarinta da burinta ako da yaushe amma na take haka na mata aure to akan Assama'u ma bazan karya wannan dokar tawa ba" "Baffah Rubina batada wani wanda kesonta a hanzu ko yazo da maganar aure" "Gani ko yanzu a shirye nake dana karɓarwa kaina auranta" da sauri Ummi da Baffah suka kalli bakin kofa inda Aliyu ke tsaye bakin kofar ya harɗe hannayansa a kirji yana murmushi, Ummi ta wurga masa harara batare da ta ce komai ba ta karasa gaban gadon da Rubina ke kwance, Baffah yai murmushi irin nasu na manya kana ya ce "Na baka dama kaje ka nemi soyayyar Rubina idan har ta amince maka na baka ita...."Ni kuma bada yawuna ba ban amince Aliyu ya tunakari Rubina da wannan maganar ba mai kuke zato wanne hali kuke ganin Rubina zata shiga ni a gaba ɗaya gidanka ma bazan taɓa laminta wani ya ce yana sonta ba" Aliyu ya buɗi baki zai magana Ummi ta katse sa da "Billahil aIzim Aliyu kai sake wani sirri ya fita har Rubina tasan ko ita wacece ban yafe maka nona daka sha ba" "Subhanallah Fatima maine haka mai kike kokarin yine kin san kuwa mai kika faɗa" "Na sani Baffa ina sane sabida ina cikin hankalina" Aliyu ya koma ya jingina da bangon ɗakin dayake ji yana zagayawa da shi ya jima a haka yana bin su Baffa da idanu da suke ta musayar yawu kafin zuwan su Uwaimer da Daddy Mahmud yakatse masu maganan 🔯🔯🔯🔯🔯 Alhaji Sammani ya fito daga cikin motarsa yana sanye cikin shiga ta mutumchi kai tsaye ya shiga cikin division ɗin ya nemi da yana son magana da D P O daga farko ƴan sandan dake gaban kanta sun so masa gardama amma daya fito da I D card ɗinsa nan da nan sukai masa iso wajan D P O bai jima a ciki ba aka kawo masa Sani aka cike takardu ya tawo da shi bayan ya sallami D p o ɗin dayai masa rakiya har wajan motarsa, a mota suna tafe yana yiwa Sani faɗa akan laifin da ake tuhumarsa da shi saida yakaisa bakin titin layinsu sannan ya sauke sa ya ce ya karasa gida bayan ya basa 5k yace yaje ya canza askin kansa yayi mai kyau sannan yai gaba, Mama tana zaune a tsakar gida tana gyara shinkafa saiga sallamar Sani tsam ta mike tana yiwa Allah godiya kafin kuma jikinta yai sanyi tuna yanda sukai da Alhaji Sammani, ta karɓi wayar Salima ta shiga ɗaki tasa lamabar Sammanin ta kira sa amma tai ta ring bai ɗaga ba, shi kuwa Alhaji Sammani ɗokacin yana tare da Matarsa dan bayan ya sauke Sani gidansa ya wuce Mama ganin Alhaji Sammani bai ɗaga kiran ba yasa ta bawa Salima wayarta taci gaba da sabgoginta na gida tana jin Salima da Marwa nawa Sani faɗa batace masu komai ba, acan gidan Alhaji Sammani kuwa jin ring na waya yayi yawa yasa matarsa tai magana da "Alhaji wayarka fa ake kira kana ji" "To wayarki ko tawa Halima? ko haka kurum daga ganin bakuwar lamba saina ɗaga kira bansan wane ba" wani kallo na tuhuma matar tasa tai masa kamar zatai magana kuma dai saita fasa taci gaba da kokarin haɗa masa abincin da take "Amma Abban widad ka dawo da wuri, nifa na zaci ma ko shigar dare zakayi?" Alhaji Sammani ya gyara zama kana ya ce "Ai ina gaya maki ba ina kadunan ba kawai yau da sassafe saiga kira daga katsina wai akwai wata ganawa ta musamman da zamuyi da gwamman katsina a daran yau shine fa ba shiri na baro kaduna na shigo kano da wuri danna samu na ɗan huta da yamma nabi jirgi zuwa katsina" ta ɗan ɓata rai kaɗan tana kallon mijin nata kana ta ce "Yanzu Abban Widad yau ma bazaka kwana a gida ba gaba ɗaya satin nan fa baka kano baka Abuja kaduna yau kuma katsina gaskiyya nidai wannan karon dani za'ayi tafiyar nan" ɗan zaro idanu Alhaji Sammani yayi kafin ya basar ya saki murmushi "In tafi dake kuma haba sai kace nine na mamajo sarkin mata, tona ajjeki a ina duka awa nawa zanyi na dawo nai maki alkawarin gobe karfe goma na safe nadawo gidan nan nima kwana biyu ina matukar kewarki" "A'ah nidai Allah ban yarda ba gaskiyya dani zaka" "Mubar maganar nan Halima ni kaɗai zanyi tafiyata nai maki alkawarin da safe zan biyo jirgi zakiga kamar a gida na kwana" bata sake cewa komai ba tamaida hankali ga danna wayarta ya mike bayan ya kammala cin abincin ya shiga ɗakinsa yana faɗin "Halima bari na ɗan warware gajiya a ɗaki ina futowa" ya nufi ɗakinsa Halima ta bisa da kallo harya shige ɗaki ta sauke ajjiyar zuciya kafin ta mike ta shiga ɗakinta itama, Alhaji Sammani na shiga ɗakinsa ya saka key ya zauna gefan gado ya dannawa lambar da aka kirasa yanzu kira wacce yake zaton Abu ce ke kiransa sai dai muryar da yaji ta amsa masa sallamar dayai ta doki dodon kunnan sa lokaci ɗaya muryar ta doki zuciyarsa yaji ya kwaɗaitu da son ganin fuskar mai wannan muryar..... 07039793439 🌹 *RASHIN MAHAIFANA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Association* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW RASHIN MAHAIFANA Episode seven7️⃣ *Kirkirarran labari ne in wani Ɓangare yai dai dai da wani ko wata ayi hakuri arashi ne* "Hello hello banaji" Salima ta faɗa jin shuru tai saurin katse kiran tana kallon Mama "Mama wannan kamar lambar da kika kira jiya fa" Mama ta karɓi wayar dai dai kira ya sake shigowa ta danna wajan amsa kira ta kara wayar a kunnanta tai sallama, Alhaji Sammani ya sauke ajjiyar zuciya kana ya amsa sallamar tata "Alhaji barka da rana ya aiki na gode sosai da kokarinka ɗazun nan naga sani yadawo mungode sosai" "A ba komai ai yiwa kaine, amma wannan wayar wace?" "Ta Salimah ce" "Ok to to hakane fa na tina jiya kin gaya min kin saida taki to bari na siyo maki wata babbar taki in mun haɗu anjima saina baki" "To" ta faɗa jiki a sanyaye sukai sallama tabawa Salima wayar, Salima ta karɓa tana aikawa Mama kallon tuhuma, harta mike zata shiga ɗaki ta ce "Mama wannan ɗin wai waye kika kira" "Kanin hajiya Sakina ne shiyaje yatawo da Sani daga wajan ƴan sanda" Salima ta gamsu da maganar mahaifiyarta ta juya ta shiga ɗakinsu ta kwanta lamo tana tunanin mafita ga rayuwarsu, mama har akai mangariba jikinta sanyaye yake ta rasa ta yanda zata sanar da yaran nata zata fita harma taje wani wajan ta kwana sai sake sake take a ranta, wayar salima ta karɓa tai bloking lambar Alhaji Sammani sannan ta goge lamban bayan sallar mangariba ta mike tai wanka tai sallah ta kalli Salima dake zaune tana danna waya ta ce "Salima zan fita gidan hajiya Sakina zani anjima zan dawo" "Mama mariri a daran nan har yaushe kikaje yaushe kika dawo" "Zuwan ya zama dole Salima inta kama ma zan kwanan yau Babanku banan gidan yake ba in kunjini shuru ku rufe gida" "To" Salima ta faɗa jiki sanyaye ta saka hijab ɗinta taiwa Maman tasu rakiya zuwa titi har tahau abin hawa sannan ta dawo gida, kai tsaye Mama hotal ɗin da suka saba haɗuwa da Alhaji Sammani ta nufa ta shiga kanta tsaye kasancewar ba wannan ne zuwanta na farko ba harta ɗakin dayake zama ta sani hakan yasa kai tsaye ta nufi can, lokacin data shiga ɗakin yana zaune kan kujerar dake cikin ɗakin yana kallon wasan kwallon kafa a t b daga shi sai gajeran wando ko arzikin singlate babu a jikinsa yana ganinta ya wani washe baki yana mata dariya kallo ɗaya Mama tai masa ta ji gabanta ya faɗi ta raɓa gefan gado ta zauna har sannan gabanta na faɗuwa "Harna zaci bazaki zo ba nayita kiran layin nan na ɗazu da mukai waya baya shiga kinga wayarki" yafaɗa yana ɗago mata kwalin sabuwar waya tsadadda, mama ko kaɗan bataji wayar ta burgeta ba "Na siyo maki babbar waya wacce zamu ringa vidio call sannan daga yau bana son mu kuma haɗuwa dake anan a kwai keɓantaccan gidana dake wajan gari mu koma can da hulɗa" Mama dai na zaune gefe ta kasa cewa uffan, harya gama kallon kwallo yadawo kusa da ita yafara sarrafata tana jinsa hawaye kawai ke zuba daga cikin idanunta wai yau ita ke zina da auranta abinda bata aikata lokacin kuruciya ba sai gashi yanzu da shekarunta tana aikatawa tsawon lokaci tana jinsa yana sarrafa jikinta tun bata biye masa har shaiɗan ya kawata mata abin ta fara mayar masa da martani kasancewar ta jima bata ji irin haka daga mijinta ba tsawon shekaru, sun jima sosai a wata duniya kafin suka dawo duniyarmu, gaba ɗaya Alhaji Sammani ya gigice sabida yanda sheɗan ya kawata masa Mama yaji daɗinta fiye da na duk matan dayake hulɗa da su, washe gari da kyar ya barta ta tafi sai nan nan yake da ita ya bata wayarta da kuɗi dubu ashirin bayan sunyi alkawarin sake haɗuwa nan bada jimawa ba ta nufi gida cikeda ɗokin ganin iyalanta 🔯🔯🔯🔯🔯 Nuraddeen jiki sanyaye yake tuka motar tasa tsakanin shida Lameen ba wanda yai magana har suka karasa gidansu bai shiga da motar ciki ba yai parking ɗinta a wajan gida suka shiga gidan a tare, Innah na zaune cikin babbar barander tana shan iska taga shigowar Lameen da Nura a kallo ɗaya datai masu ta lura ba lafiya ba, tabisu da kallo har suka karaso inda take Nura ya zauna gefan tabarmar da take kai Lameen ya tsaya daga tsaye ya jingina da bango ta bisu da kallo kafin ta maida hankalinta duka ga Nura ta ce "Lafiya kuwa Nuraddeen maiya sameka bayan fitar taka ina motar ka? kai Lameenu yaushe ka fita daga gidan nan naga motarka na zaci kana ɗaki kana barcin naka daka saba" "Innarmu Nura ne ya gamu da tsautsayi ya buge wata yarinya" "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku ni Fatsima la'ilaha illallahu yanzu ina yarinyar maiya same ta Nura garin yaya haka ta faru" "Innah tsautsayi ne karki tashi hankalinki dan Allah ba wani ciwo bane babba tana ma asibitin da kike ganin likita" Inna ta mike tana laluban mayafinta ta shiga ciki ta fito sanye da hijab "Kai Lameen kaini asibitin yanzu yanzu" Lameen da Nura suka kalli juna Nura ya mike ya kama Inna suka shiga ciki ya zaunar da ita kan kujera ya zauna gefanta ya saka hannunsa cikin nata ya ce "Inna na gaya maki karki damu, Baban yarinyar yace nadawo gida na huta anjima saina koma ki kira mai tayaki aiki a girka abinci sai a tafar masu da shi anjima bayan nai wanka saimu koma tare" "E fa kuma hakane Nura nida harna fara ruɗewa to bari na kirata a waya saita zo kai Lameenu zo mu fara aikin tare da kai kai kuma Nura jekai wanka ka canza kayanka zuwa sannan mun gama Allah yasa munada komai a gidan nan kamar ka san haka zata faru jiya kayo uban siyayyar nan Allah dai yamaka albarka Nura" "Innarmu Nura kaɗai banda ni" "To yi hakuri bansan kashigo ba ai kaima Allah maka albarka" Innah da Lameen keta aiki cikin kicin ta kira wayar yarinyar tace mata bata nan sun fita unguwa da Mamanta, har Nura yai wanka basu gama ba shima ya shigo suka taru suka dafa haɗaɗɗiyar shinkafa da miya da taji tsokar nama dai dai misali girkin sai kamshi yake suka kammala komai Lameen ya zuba komai cikin babban basket suka fito a bakin titi suka tsaya suka sai ruwan roba katan biyu da lemun gora shima katan biyu, lemo ayaba kankana duka suka saya sannan suka ɗau hanyar hospital "Ummina wayyo Ummi kaina hannuna wayyo Yay Meer zan mutu" da sauri Uwaimir da gaba ɗaya hankalinsa ke kan Rubina ya karasa gaban gadon ya ruko hannun Rubina mai lafiyar a ruɗe yafara magana da "Rubie Rubina buɗe idanunki kin ganni anan kusa dake ga Ummi ma" "Yay Meer idanuna sun min nauyi kamar bazan iya buɗe su ba" "Zaki iya zaki iya Rubie ambaci sunan Allah kice bisimillah sai ki buɗe su a hankali, maza maza buɗesu dan Allah nagansu" ahankali ta fara motsa idanun nata kafin ta buɗe su tarwai akan fuskar Uwaimir takai hannu ta shafo fuskar tasa sannan ta maida ganinta ga Ummi dake tsaye a gefe, ta zare hannunta daga na Uwaimir ta mikawa Ummi hannu, Ummi ta karaso gaban gadon tana gyarawa Rubina gashinta "Sannu mamana Allah yabaki lafiya kinji kin gamu da tsautsayi" hawaye suka zubo daga idanun Rubina Uwaimir yasa hannu ya goge mata zuwan baffa gaban gadon yasa Uwaimir yai baya ya bawa Baffa waje "Sannu sannu Asma'u kinji Allah yabaki lafiya" "Baffana" na faɗa a hankali ina kai hannuna mai lafiyar na ruko hannunsa "Baffah bana son hospital mu koma gida Baffah" "Sannu to zamu koma amma sai kin warke kinji yarinyata Allah yabaki lafiya" "Assalamu alaikum" Innah tai sallama ta shigo ɗakin bayanta Lameen ne da niki nikin kaya a hannunsa shima yayi sallama kamar yanda tayi "Alaikus salam sannunku da zuwa" Ummi ta faɗa da fara'arta kamar ta sansu ta nunawa Innah wajan zama tareda faɗin "Sannu mama ga wajan zama" Innah tai murmushi tana faɗin "Na zauna kuwa bari na fara duba mara lafiya" Nura ya shigo shima da sallama hannunsa rike da lemu da ruwan da suka siyo ya gaida Baffa cikin girmamawa kafin ya gaida Ummi yana tambayarta yamai jiki, yabawa Uwaimir hannu sukai musabaha kafin ya koma kusa da Lameen ya tsaya yana kallon Innah "Nuraddeen zoka ga mara lafiyan taka ta farfaɗo" inna ta faɗa batare data juyo ta kalli Nuran ba ahankali ya tako yazo har gaban gadon ya kalli Rubina kallo ɗaya kana ya ce "Ya jikin Allah yakara lafiya" daga haka baice komai ba ya juya ya koma kusa da kaninsa ya tsaya, Innah ta kalli Baffah cikin girmamawa tana mai basa hakuri kan tsautsayin daya faru "Ba komai Hajiya ai kaddara tana kan kowa" Baffah yamaida hankalinsa ga Ummi ya ce "Fatima zan koma gida sai dare zan dawo inaga ma zanyi magana da Dr ɗin nan a canza mata hospital ko zuwa gobe ne" Ummi tabi bayan Baffah tai masa rakiya har wajan da Amjad ke zaune cikin mota yana jiran fitowar Baffan, Ummi tai masa fatan sauka lafiya ta maida murfin motar ta rufe masa ta koma ɗakin daya rage daga Uwaimir sai Su Innah "Hajiya ga Abinci nan munzo maku da shi ba yawa" "Mungode Allah yasaka da alkhairi, Uwaimer zuba mata abincin taci" Uwair ya mike ya ɗauki plat ya ɗauraye kana ya zuba mata abincin ya karasa gabanta, Rubina ta kauda kai gefe ta ɓata fuska "Yay Meer ni na koshi fa" "Mai kikaci? kila rabonki da abinci tun safe fa, dan Allah tashi ki wanke bakinki ki ci" "Nidai A'a" ya ajje plat ɗin abincin kan pridge ɗin dake gaban gadon ya harɗe hannunsa a kirji yana kallo Rubinan, Ummi ta karaso wajan ta taimakawa Rubina ta zauna ta kawo mata ruwa ta kuskure bakinta sannan ta ɗakko abinci tai bisimillah takai mata cokalin abincin bakinta ta karɓa ba musu ta fara ci, Uwaimeer ya fita bayan ƴan mintina sai gashi yadawo ɗakin hannunsa rikeda leda mai tambarin shoprite ya zauna kusa da Rubina ya buɗe ledar lemun da taga ya fito da shi yasa ta washe hakora takai hannu da sauri ta karɓi kwankwanin lemun da har Uwair ya buɗe mata ta kafa kai ta shanye sa tas bata damu da sanyin sa ba, "Thank you Broth" murmushi kawai yayi bayan ya fito mata da choculate ya mika mata, kafin wani lokaci ɗakin ya cika da yayun Rubina mata ƴan ɗakin Ummi, Ummi da mamaki take kallon Warisha ta ce "Waya gaya maku Rubina na hospital" "Uwaimeer yai posting a family group" Ummi ta kauda kai gefe tana kallon ƴaƴan nata mata, tai murmushi kawai, washe gari Baffa ya canzawa Rubina hospital bayan yabawa Nura hakuri aka cigaba da kulawa da lafiyar Rubina Uwaimeer ya koma wajan aikinsa sai dai ko yaushe suna wayada Rubina wani binma vidio call suke ta wayan Amjad ko Ummi, kafin wani lokaci Rubina ta warware hannunta ya warke aka sallaesu suka koma gida akaci gaba da kula da ita, Nura da farko bayan sun koma gida yakanje kullum ya dubata ganin ta ji sauki sosai yasa ya daina zuwa sai jifa jifa Rubina yau ina zaune gaba ɗaya rashin waya a hannuna yadaman data Ummi nake amfani hakan yasa yau da muna wayada Yay Uwair na masa korafin rashin wayata "Rubie nasai maki waya tun randa tsautsayin nan yasameki simcard ɗinki na cikin wayarma suna nan a wajena da tsohuwar wayarki" "To yaushe zaka zo?" "Cikin satin nan zan samu nazo ko kwana ɗaya nayi kinsan yanayin aikinmu Rubie" "To Allah ya kawo ka lafiya" NURADDEEN Yau kwanansa biyar kenan baije yaga mara lafiyarsa ba gaba ɗaya sai yaji yadamu sosai, Allah Allah yake yau ayi sallar juma'a yaje baisan maike fisgarsa ba yake son yakai mata ziyara, bayan sallar juma'a da kyar yabari akai la'asar ya nufi gidan Alhaji Baffah Yarima a kofar gidan ya faka motarsa ya nufi kofar shiga get na farko na gidan, ɗaya daga cikin scurity masu tsaron kofar ya mike yana yiwa Nura barka da zuwa tuni sun saba da shi kasancewar Nura mutum ne mai barkwanci gashi da hannun kyauta sam abin hannunsa bai damesa ba kusan duk randa yazo suma suna samun rabonsu "Barka da zuwa Brister" "Barka dai" Nuraddeen ya faɗa yana mika masu hannu sukai musabaha kana ya shiga can cikin gidan kai tsaye ya nufi part ɗin Ummi ya tsaya bakin gate ɗin sashin yana knocking, Khalipha ya zo ya buɗe masa kofa ya basa hannu suka cafke kamar wasu abokai "Khalipha cewa Ummi gani nazo" Khalipha ya koma ciki ya sanar da Ummi, Ummi ta gyara zaman mayafin abaya dake kanta kana ta ce "Kace masa ya shigo" Khalipha ya juya ya fita suka shigo tare, Nuradden ya tsugunna yana gaida Ummi "Barka da yamma Ummi fatan an wuni lafiya" "Lafiya kalau Nura ya gida ya Innah kwana biyu" "Inna tana nan lafiya tana gaidaku" "Muna amsawa ga waje nan zauna mana" Ummi ta faɗa tana nuna masa kujera, ya zauna ta kalli Khalipha ta ce "Ka cewa Habiba ta kawo ma bako ruwa da lemu da snack" Khalipha yace "to" ya mike ya nufi ɗakin da mai aikin take ya sanar mata abinda Ummi ta ce sannan ya fita, Ummi ganin Habiba ta kawo ta mike ta basa waje tana faɗin "Nuraddeen kasha ruwa bari na turo maka mara lafiyar taka, yau zaman ɗaka take" ta nufi ɗakin Rubina, Nura ya cire hularsa ya ajje kusa da shi ya saki murmushi yana kafe kofar ɗakin da Ummi ta shiga da idanu haka nan yarasa mai yasa zuciyarsa ta kagu da taga fuskar Rubina, minti biyu tsakani saiga futowar Rubina da Ummi a tare Ummi ta nufi kichin yayin da Rubina ta fuskanto inda yake zaune tana masa murmushi, wani abu yaji ya caki zuciyarsa lokacin datai masa murmushi "Lah Yaya Nuri kaine yau nayi fushi kwana biyu baka zo duba ni ba" Nura ya gyara zama yana jin wani sanyin daɗin sunan data kirashi da shi "Nurii" ya maimaita sunan a cikin zuciyarsa "To ayi hakuri na shiga sabgogi ne shi yasa amma amin afuwa yau gani nazo ya kike ya hannun" Na washe baki ina mikar da hannun na nuna masa "Kaga hannun ai ya warke nifa na zata ma bazai koma dai dai ba" na karashe faɗi ina dariya "Gashi nan kuwa ya koma kam masha Allah ya Baffah" "Baffah alhamdulillah jiya nan shida Yaya Amjad suka tafi saudiyya umara" "Masha Allah, ubangiji yadawo dasu lafiya" "Amin, yanaga baka ko sha ruwa ba" na faɗi haka ina mikewa daga inda nake zaune na buɗe gorar lemun na tsiyaya masa a cup na mika masa yasa hannu ya karɓa idanunsa cikin nawa ya ce "Thank you" na zuba masa snack a plat na tura masa a gabansa naja masa teble ɗin yaje gab da shi "Bisimillah" "Wai wannan duk ni kaɗai kawai ma samosa ɗin nan guda ɗaya ma ta isheni" "Ah haba ai kuwa sai ka cinye su duka" na faɗa ina ƴar dariya, ya zaro idanu kamar wata mace ya lumshe su ya ce "Ni awa na cinye wannan kuma ina zan kai abincin Innah" "Sai ka gaya mata a koshe kake kazo nan kaci snack" yai murmushin gefan baki yanabin Usham da kallo daya fito daga wani ɗaki hannunsa rike da waya yana ɗan gudu ya ce "Anty Rubina ga Yaya meer ɗinki ya kira Ummi ta ce na kawo maki" na gyara zama tareda karɓar wayar na

Chapter 5 of 11