Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na neman zubo mata!!haka ta tashi ta fita a cikin parlour ta barsu anan zaune.kusan minti biyar da tafiyar mum babu wanda yace wani abu a cikin su,da kyar kamal ya iya cemata tazo suje wurin hajiya,haka ta tashi tabi bayan sa jiki duk a sanyaye suka nufi part din hajiya Ita da Jamal suka samu a zaune suna hira,suma zaman sukayi suka gaishe da hajiya ta amsa cikin jin dadi sannan Jamal ya gaishe su. Abubuwa kala-kala hajiya yasa aka kawo musu tanata jansu da hira tanayi tana tsokanan kamal Tadan sake jikin ta babu laifi suka dan taba hira dasu hajiya,sai Chan kamal yace ta tashi su tafi!!!hajiya tayi charaf tana cewa "Wai kamalu meyasa kake haka ne?daga zuwan Ku zaka wani ce ta tashi Ku tafi kamar ana mintsinin ku,dalla ka matsa min babu inda zataje sai dare koh kuma ma ta kauna anan." Tabe baki yayi sannan yace "Kefa kin cika rigima tsohowar nan,gidan su fah zan kaita ta gaishe su shine zaki wani ce sai dare?ki bari wani satin zan kawo miki ita" Jin ance za'a kawo mata ita wani satin yasa tabarsu suka tafi ta musu rakiya har bakin motar sannan ta dawo part dinta Yana gama parking a cikin gidan ta fito da sauri daga cikin motar zata shiga cikin gidan "baba Haruna mai gadi yace haba yar gidan Abba bazamu gaisa bah zaki wuce?" "Zamu gaisa mana baba Haruna na matsu naga su Abba ne shiyasa" Dariya yayi sannan suka gaisa ta shige ciki da sauri Ba karamin jin dadin ganin yan uwanta tayi bah har kwallar jin dadi saida ta zubar,sun shaa hira sosai dasu Abba dan bayan kamal ya shigo sun gaisa yace zaije ya dawo da daddare sai bayan sallar isha'i yazo daukan ta,ji tayi kamar tace bazata bishi bah!!!haka dai ta fito sukayi sallama dasu Ummee sannan suka kama hanyar gida ✍✍✍ [1/22, 10:55 PM] ‪+234 813 539 4575‬: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣ NA Khadeejah saleehu Dedicated to Hauwa Muhammad (slim small) 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍ 6⃣3⃣➖6⃣4⃣ Fitowar ta Kenan daga kitchen tana goge Hannunta da towel,ganin mutane tayi a zaune akan kujera Kamar an dasasu kai!!!saida gabanta ya fadi ganin wayanda ke zaune,mum ce sai Kuma mahaifiyar Hafsa da ita Hafsa.jiki a sanyaye ta karasa Cikin parlour daga gefe ta samu ta durkusa ta gaishe su kanta a kasa Babu wanda ya amsa mata gaisuwar a cikin su,sai mum datace "dama nan din gidan ubanki ne dazamu tayin sallama baki amsa mana bah?" "kuyi hakuri mum wallahi banji bane shiyasa" "inma kinji Inma bakiji bah duk daya,nidai na kawo miki matar da Kamal zai aura ne nanda yan kaunaki Kadan masu Zuwa!!!Domin ni *itace zabina*" Duk wannan abun da akeyi Kamal na daki baisan meyake faruwa bah.cikin muryar tsawa mum tasake cewa "yaron nawa mah sai nace ki kiramun shi?dan nasan yana ciki,ki wuce ki kirashi in kuma bazaki iya bah ni sai naje na kira shi" Tashi tayi jiki duk babu kwari ta nufi hanyar dakin Kamal!!!saida takai daidai kofar shi ta tsaya ta qirqiri murmushin dole ta daura akan fuskar ta sannan ta tura kofar dakin A zaune yake yana danna wayar shi jin an bude kofar yasa ya dago yana kallon ta,kana ganinta zaka gane akwai abinda yake damunta!!karasawa tayi ta zauna kusa dashi tana cewa "tun dazu kazo ka wani zauna a daki kamar mace!!!toh mum sunzo suna parlour ka tashi kaje tana jiranka" Cikin jin mamaki ya ajiye wayar datake hanunsa sannan yace "mum Kuma ita dawa?" "ikon Allah kaje ka gani mana dan tun dazo tazo tanata sallama banji bah ina kitchen" Numfashi ya sauke sannan ya tashi ya fita a dakin Kujera yasamu ya zauna sannan ya gaishe su,mummy din Hafsa ce kawai ta amsa gaisuwar Gaishe shi Hafsa tayi amma yayi kamar baiji bah!!harara mum ta watsa masa tace "hala ka kurmance ne?ana gaishe ka kamar bakaji bah" Wani irin takaici yaji sannan yana mamakin wai meyasa mum takeyin haka?menene amfanin ta dauko wayan nan mutanen suzo gidan shi?da kyar ya bude baki ya amsa gaisuwar batare daya Kalleta bah "nazo da Hafsa ne danna tabbatar maka inanan akan maganata na auren ku da ita!!kuma itama matar ka nasake maimaita mata Kaima kuma inasake maimaita maka kaji da kyau" Kallon ta kawai yakeyi danshi yama rasa mai zai cemata Tashi tayi tana cewa "ku tashi mu tafi dan dama abinda ya kawoni kenan inbanda haka babu abinda zanzo nayi a gidan nan" Suma mikewa sukayi suka bi bayanta kamar jela,Hafsa kuwa sai faman rangwada akeyi wanda kuma akeyi danshi hankalin shi gaba daya ba'a kanta yake bah Yafi minti goma a zaune a wiring koh motsawa baiyi bah,tashi yayi ya shiga cikin dakin daya barota Tayi ruf da Ciki gaba daya abun duniya ya dameta!!jin an zauna kusa da ita yasata tashi ta zauna sannan tace "badai har sun tafi bah daiko?" Kallonta ya tsayayi dan kana ganinta kasan qoqarin boye damuwar ta kawai takeyi "wai miye kaketa wani kallo nah? kamar kasamu TV!!!ina tambayan ka kayi shiru" Girgiza Kai yayi ya kamo hannun ta sannan yace "ki 'kara hakuri komai zai wuce insha Allah!!!Nasan abunda ta fadamin haka ta fadamiki amma kuma kinata kokarin boye damuwar ki kina nuna kamar babu komai!!!bazan bari ki tozarta bah a rayuwa da yardar Allah" "Da murmushi tace babu komai tana fadan abinda yake ranta ne kuma ni banga laifin tabah ai danta isa damu ne shiyasa tayi hakan!!! Saboda haka karma ka damu ninasan komai lokaci ne dadi koh wuya akwai ranar dazaizo duk sun wuce" Jiyayi zuciyar shi tadanyi sanyi sonta yana kara shiga ransa sannan yana mai adduar Allah ya barsu tare cikin jin dadi da kwanciyar hankali. ✍✍✍ [1/22, 10:55 PM] ‪+234 813 539 4575‬: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣ NA Khadeejah saleehu Dedicated to u sis (pinky) Allah ya baki lafiya ya raba lafiya musha suna 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍ 6⃣7⃣➖6⃣8⃣ Kafin ya dawo ta tashi tayi wanka tana shirya abinci akan dinning sai gashi ya shigo Kujera yaje yasamu ya zauna dan baima lura da ita bah,kusa dashi tazo ta zauna tayi shiru batace komai dan tasan duk sanda yaje gidan mum rai a bace yake dawowa A hankali ya dago yana kallon ta,itama kallon nashi takeyi "yaushe kuma kika fara boye mun abinda ya faru?kikace mum cewa kawai tayi inje tana nema nah amma baki fadamin abinda ya faru bah" "Toh idan ma nafada maka mezakayi mum itace a gaba damu dole muyi hakuri da duk wani abu dazai fito daga wurinta!!!itace uwar mu bamu bane iyayen ta bah.nasan koh na fadamaka ranka ne kawai zai baci,toh ni kuma banga amfanin hakan bah Tunda ta fara magana yake kallon ta tausayi take bashi bah kadan bah yana tuna maganar da bash yake fadamishi nakar yaje ya aura yar mutane tazo batajin dadin zaman.ta tashi cikin yan uwanta da iyayen ta cikin so da qauna amma yanzu gaba daya yanzu komai ya juye Dakyar tasamu ta lallabashi sukaje suka ci abincin datayi musu ****** Rayuwa ta cigaba da tafiya ako yaushe mum bata da wani buri daya wuce taga ta muzguna wa Hamdiyya *Bayan wata takwas* Gaba daya mum ta tayar da hankalin kuwa akan sai Kamal ya aure Hafsa Dakyar dad yasamu ya shawo kan Kamal akan ya yarda ya aure Hafsa tinda shima ya aure wacce yakeso dan haka ya aure wacce mahaifiyar shi takeso Haka ya yarda da maganar auren dan babu yanda zaiyi amma ya hana kwata-kwata a fadawa Hamdiyya duk wata hanya da yasan zata san maganar ya tushe har gida yaje yasamu Maryam akan karta fadawa Hamdiyya!!! taso yabari a fadamata dan tasan halin qawarta amma sam yaqi haka ta hakura Hajiya ma haka taso a fadawa Hamdiyya maganar amma Kamal yace bai yarda a fadamata bah haka su mum suka shiga shirye shiryen biki Da misalin karfe 2pm aka daura auren *Kamal da Hafsa* murna a wurin Hafsa da mahaifiyar ta kamar su zuba ruwa a kasa susha!!!babu wani shagalin biki da akayi dan sunsan Kamal bazai taba yarda bah Da daddare aka kawo amarya gidan ta.part din Hamdiyya suka wuce da ita sunata faman guda,hayaniyar dataji ne yasa ta fito daga daki mamaki ne ya kamata ganin su mum binsu da kallo kawai takeyi "Toh ga amaryar mu nan dai mun kawo ta yanxu nasan dana yayi aure,yanzu nasan nayi surika a rayuwa!!!duk da nasan Kamal bai fadamiki maganar auren nan bah saboda shi kanshi bai dauke ki a bakin komai bah hakan yasa ya hana kowa mah ya fadamiki" Gaba daya ta rikici takasa gane mai mum take nufi amma hakan baisa ta fita a cikin hyayacin ta bah tadai gane cewa kamal ne ya kara aure batare da kowa ya fadamata bah hasali mah shida kanshi ya hana a fadamata haka suka fita suka barta kanta duk ya juye ta rasa mai zatayi daki ta koma ta zauna tana tunanin wannan wacce irin rayuwa ci Ta yarda akan ita kuma da haka qaddarar ta tazo mata saboda haka bazata tayar da hankalin ta bah balle ta tayar dana wani zata zuba musu ido taga gudun ruwan su. wanka ta tashi ta shiga ta fito tana cikin saka kayan baccin ta taji an turo kofar dakin,bata juya taga waye bah dan tasan Kamal ne Cigaba tayi da shirin ta bayan ta gama shirinta ta juyu ta kalle shi tace sannu da dawowa abincin ka nakan dinning daga haka ta haura kan gado taja bargo ta rufe kanta amma sam bawai bacci takeji bah Koh da bata cemishi komai yasan yanzu tasan da maganar auren!!gaba daya yama rasa ta ina zai fara yimata bayani Babu wanda yayi bacci a cikin su kowa da abunda yake nazari a cikin ransa musamman ma Kamal dan baisan ta ina zai farayi mata bayani bah yasan laifin daya mata bana wasa bane. ✍✍✍ [1/22, 10:55 PM] ‪+234 813 539 4575‬: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣ NA Khadeejah saleehu Dedicated to hauwa muhammad (slim small) 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍ 6⃣9⃣➖7⃣0⃣ So yakeyi ya tashe daga baccin data keyi amma yakasa,danne zuciyar shi yayi ya fara tashin ta daga baccin A hankali ta fara bude idonta suna hada ido tayi saurin dauke kallon ta daga gareshi batare da tace mishi komai bah ta tashi ta shiga toilet wanka tayi sannan ta fito koh data fito shima baya dakin ya fita Key taje ta saka a kofar dakin sannan taje bakin gado ta zauna,batasan sanda kuka ya kufce mata bah,kuka tayi sosai harsai dataji babu dadi Ganin an murda kofar dakin ne yasa ta tashe taje tasake wanke fuskar ta sannan tazo ta shirya ta bude kofar dakin nata ta koma ta kaunta A bakin gadon yaje ya zauna ya kasa cewa komai!!!da kyar ya iya kiran sunan ta amma tayi kamar bata jishi bah kara kiran sunan nata yayi nan ma tayi kamar bada ita yakeyi bah Ganin zai takura mata yasa ta tashi zata bar mishi dakin jin ya rike hannun ta yasa ta tsaya batare data kalle shi ba Zaunar da ita yayi a kusa dashi,batayi yunkorin tashi bah dan gaba daya batajin karfi a jikin ta "nasan nayi miki laifin da bansan ta ina zan fara baki hakuri bah koh kuma yi miki bayani bah!!!amma dan Allah inaso kiyi hakuri ki yafemin babu yadda zanyi ne,kuma ni bansan ta ina zan fara fadamiki wai zan kara aure bah,karkiyi fushi dani dan Allah" "Fushin me zanyi dakai kuma?yanxu ne mahaifiyar ka tasan kayi aure,yanzu ne tasan tana da surika.ban canci insan zaka kara aure bah shiyasa babu wanda ya fadamin,banida wani matsayin da zaisa nasan zakayi aure,hasali mah kai da kanka kace kar wanda ya fadamin zakayi aure saidai kawai naga an kawo maka matar ka!!karma ka bani wani hakuri dan shima ban da wannan darajar,ka tafi wurin amaryar ka wacce kakeso kuma mahaifiyar ka takeso" Numfashi ya sauke dan babu wani abu da kuma zai fadamata.tabbas yasan duk wacce akayi wa haka baza taji dadi bah!!!ji yakeyi daama ya fadamata tin da farko wataqila zata fahimce shi amma yanzu zaiyi wuya ta fahimce shi "kamal wannan shine irin jin dadin daka tanadar min a gidan ka?wannan shine kaunciyar hankalin dazaka samar min a cikin gidan naka?meyasa ka rabani da iyaye da yan uwa nah?ka kawo ni inda babu mai kaunata" Kuka ne yaci karfinta ta kasa karashe maganar dayake bakin ta.bai hanatayin kukan bah duk da har cikin ransa yake jin kukan nata,amma yasan kukan data keyi zaisa tadan samu saukin halin datake ciki Ganin bata da alamar yin shiru yasa ya fara lallashin ta!!! "Hamdiyya ban rabaki da yan uwanki bah dan in cutar dake!!!nida a tunani nah rashin fadamiki zaifi akan a fadamiki shiyasa ban fadamiki bah,amma wallahi ni bada wata manufa nayi hakan dan Allah ki fahimce ni" "Tunda mum take cewa ga abinda takeso na taba cemaka wani abun?itace take da iko dakai bani nake da iko dakai bah!!banida ikon hanaka yin abunda mahaifiyar ka ta umarce ka dayi,fadamin zakayi aure zai fimin dadi akan kawai a kawo kin wata a matsayin matar ka batare da kowa ya fadamin bah!!!amma ba damuwa Allah ya baku zaman lafiya" Kallon ta kawai yakeyi tun sanda ta fara magana "Naji nayi miki laifi amma dan Allah kiyi hakuri,kuma karkiyi tunanin dan bana sonki ne yasa nayi haka koh kuma dan baki kai matsayin in fadamiki bah.kin wuce duk wani irin matsayi a wuri nah" "naji ba komai Allah ya baka ikon yin adalci a tsakanin mu" Baice komai bah dan shidai yasan mum ta dora mishi abinda bazai taba iya dauka bah a rayuwar shi,bazai iya kallon Hafsa a matsayin matar shi bah balle har ayi zancen wai zai iya kwatanta ta da Hamdiyya Ganin tadan sake ranta yasa shima yadan samu nutsuwa.yananan tare da ita dan bayason yayi nesa da ita Har dare babu inda yaje sallah ce kawai take fitar dashi,bayan sallar isha'i ya dawo suka ck abinci Kallon shi ta tsaya yi dan ganin ya shiga yayi wanka ya chanza kayan shi sannan ya hau kan gado alamar bacci zaiyi "wai me kuma kake nufi dazaka zo nan ka kaunta?" tashi yayi ya zauna yana kallon ta sannan yace "ke zan tambaya me kike nufi ai?in ban kaunta anan bah ina kikeso naje na kaunta kuma? "kaga ka tashi ka tafi wurin matarka dan nasan tana chan tana jiran ka,amma bawai kazo nan ka kaunta bah" Jin ta kira Hafsa da matar shi yasa yaji nutsuwar daya dan samu ta gudu "Dan Allah karki sake fadamin haka banaso!!!anan na saba kauna saboda haka anan zan kauna babu inda zanje" babu yadda batayi bah ya tashi ya tafi bah amma yaqi.batason ace ita ta hanashi zuwa wurin amaryar shi sannan batason shiga hakkin ta dan itama yanzu tanada hakki akan shi!!!amma daga karshe mah qin kulata yayi sai jan bargo da yayi ya rufe kanshi,haka ta hakura taa kyaleshi dan babu yadda zatayi kuma. ✍✍✍ [1/22, 10:55 PM] ‪+234 813 539 4575‬: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣ NA Khadeejah saleehu Dedicated to hauwa muhammad (slim small) 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍ 7⃣3⃣➖7⃣4⃣ Tunda ta isa gida babu abinda take sai faman kuka,da kyar aka samu ta fada abunda ya faru.babu wanda bai tausaya mata bah a cikin yan uwanta da iyayen ta!!!rarrashen ta suka shiga yi saida suka ga tadan samu nutsuwa sannan ummee tajata zuwa daki ta hada mata ruwan wanka sannan ta fita a dakin Bayan ta dawo parlour abba ya cemusu su dinga kauntar mata da hankali kar wanda kuma yamata maganar komawa gidan mijin ta a yanzu a bari sai nan da wani lokacin,sun amince da batun abban nasu haka suka watse a wurin ummee kuma ta shiga kitchen dan tawa yar autar ta abinda zataci Sanda ta fito daga wanka bakin gado taje ta zauna tana tuna abubuwan dasuka faru hawaye na zuba daga idon ta!!!haka ummee ta shigo ta sameta Karasawa tayi ta zauna a kusa da ita,sannan ta shiga yimata nasiha akan ta kauntar da hankain ta komai na duniya mai wucewa ne,karta daga hankalin ta akan wannan abun,haka ta dinga kauntar mata da hankali daga karshe tace ta tashi ta shirya tazo suci abinci Tayi matukar kiwan yan uwanta, cin abincin dasukayi tare kawai ya isa yasa tadan samu sauki a ranta dan ya tuna mata lokacin datake gida yadda sukayi rayuwa cikin so da kauna Kullum suna matukar kokarin ganin sun kawantar mata da hankali suna kokarin ganin bata nema komai ta rasa bah A yanzu shirye shiryen bikin yaya Sadeeq suke ta famanyi kasan cewar wata biyun da mahaifin Zainab ya deban musu zaayi bikin abun bai yiwu bah haka aka daga bikin saboda mahaifin nata bai samu zama bah,amma yanzu kam an riga an tsayar da magana daya akan a cikin satin nan za'a daura musu aure Shirye shiryen bikin da akeyi yasake shagaltar da ita tanadan manta abubuwan dasuka faru kusan komai ita yaya Sadeeq ya dura akai "yanzu Kamal abinda kuka hadu kukayi kaida Mum kun kyauta kenan koh?wallahi danasan bazaka iya rike yar mutane bah da bazan taba zama maka jagora bah wajen neman auren ta bah!!!kuma wai babu wanda ka fadawa komai sai dazu da Maryam taje gidan su akan shirin bikin yayan ta da sukeyi taje abunda ya faru,ka kyauta sosai amman ina mai tabbatar maka da cewa kayi sake daka bari ka rasa Hamdiyya a matsayin matar ka,koh da iyayen Hamdiyya sun yadda ta dawo gidan ka toh ita kam bazata dawo bah dan da bakinta ta fadawa Maryam haka,sai kaje ka cigaba da zama da wacce aka aura maka" Tunda Bash yake magana Kamal ya kasa cemishi komai ganin babban abokin nashi dayake tunanin shi zai wuce mishi gaba wajen bawa Hamdiyya hakuri ya dauki zafi da yawa "Bash nasan nayi kuskure amma wai yazan yine?Mum tace bata yafemin bah idan har naje gidan su Hamdiyya koh kuma inna kirata a waya,kasan cewa Dad baya kasan nan balle na kaimishi kuka nah haka mah hajiya batanan toh wanake dashi yanzu?kaima danake tunanin zaka zamemin jagora ga abinda kazo kana fadamin" "i'm sorry to say Kamal amma nikam a yanzu bazan taba zuwa gidan su Hamdiyya bah dazance in bata hakuri ta dawo gidan ka,saika bari duk sanda ka tashi zuwa basu hakuri koh kuma ince sanda Mum ta lamunce maka dan nasan koh mai daren dadewa zakuyi danasanin abinda kukayi" bai jira cewar Kamal bah ya tashi ya fice abinshi ya barshi a zaune Zuwa yanzu kanshi ya gama daurewa baisan kuma mezaiyi bah nan gaba dama Bash yake ganin zai iya magance mishi matsalar shi amma kuma ga yadda sukayi ****** Duk yadda Hafsa tasan zatayi ta shawo kan Kamal akan yadinga shiga harka tayi!!amma abun yaci tura yi yakeyi mah baisan da zaman ta a gidan bah koh kallo bata isheshi bah Anyi bikin Zainab da yaya Sadeeq komai ya tafi daidai aka dauki amarya aka kaita dakin ta Rayuwa ta cigaba da tafiya a haka,har kawo yau Kamal bai nema Hamdiyya a waya bah koh kuma yaje gidan su,amma kuma shi kadai yasan irin halin dayake ciki na rashin jin muryar matar shi koh kuma ganin fuskar ta Haka itama a bangaren ta bata taba neman shi bah, sannan zuciyar ta nasake qona naganin koh da sau daya baitaba neman ta bah. ✍✍✍ [1/22, 10:55 PM] ‪+234 813 539 4575‬: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣ NA Khadeejah saleehu Dedicated to hauwa muhammad(slim small) 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍ 7⃣5⃣➖7⃣6⃣ *Bayan wata daya* Ya kamata ace taga al'adar ta tun satin daya wuce amma shiru bata ganta bah,gashi batajin dadin jikin ta koh kadan!!!abu daya take tsoro, ace tanada ciki hakan yasa ta nema abin gwada ciki ta gwada Positve ya nuna mata alamun tana dauke da ciki,hakan ba karamin tayar mata da hankali yayi bah!!!shiryawa tayi tazo ta samu ummee a kitchen ta shaida mata akan tanaso taje asibiti Kallon ta ummee ta tsayayi saboda itama akwai abinda take zargi agame da yar tata,bata mata musu bah sai cemata datayi meyasa bazata barri Sadeeq yazo ya duba taba!!!amma tace ba damuwa zataje ta dawo yanzu bah dadewa zatayi bah daga haka ta fita zuwa asibiti Gwaje-gwaje akayi mata aka sake tabbbatar mata da cewa tana dauki da ciki na wata daya da sati daya!!!hankalin ya kara tashi amma tayi kokarin boye damuwar ta sannan ta kama hanya ta koma gida A parlour ta tarar da yaya mubarak karasawa tayi ta zauna tayi mishi sannu,amsawa yayi yana cewa "ummee tace baki da lafiya,ya jikin naki?me sukace yana damun ki?" Kafin ta bashi amsa ummee mah ta iso cikin parlour'n,gaida ummee tayi,itama ummee tambayanta tasakeyi akan me likita yace yana damunta "ba wani abu bane fah!!!malaria ce kawai kuma ya bani magani yanzu zandai je nadan kwanta ne anjima zan shaa maganin" Bata jira taji mai zasu sake cewa bah ta tashi ta nufi dakin ta.girgiza kai kawai ummee tayi dan bata yadda da abinda yarta ta tafada bah. *Waiwaye* Kasan cewar Kamal baita bah shiga harkar Hafsa bah daga karshe mah ya sake komawa part din Hamdiyya dan idan yana chan yana danjin dadi aransa A parlour'n Hamdiyya mum dinshi tazo ta sameshi,fada ta shiga yimishi akan baya kula da Hafsa gashi yanzu harta sanar da mahaifiyar ta,toh yanzu mummyn Hafsa ce tacewa mum suzo su hadu a gidan Hafsa "Kamal ka tashi muje kabawa Hafsa da mummyn ta hakuri inba so kakeyi in bata maka rai bah" Tashi yayi yabi bayan ta badan yaso bah.jin maganar da Hafsa itada mahaifiyar ta sukeyi yasa Kamal da Mum suka tsaya sunaji "kinaji nah koh Hafsa?wannan cikin dayake jikin ki yazama dole mu durashi akan Kamal,ina nufin zamuce dan sane duk da banasa bane" "Amma mummy taya za'ayi ya ansa wannan cikin?bayan bamu taba hada wurin kaunciya dashi bah" "Ni nasan yadda za'ayi ai yanzu na kira mum dinshi akan tazo mu hadu kinga idan tazo muka fadamata cewa baya kauna a wurin ki zata sashi ya dinga kauna koh yana so koh baya so,ke kuma daga nan sai kisan yadda zakiyi ki jawo hankalin shi akan ki,in kuma yaqi koh kashe shine sai muyi kinga sai muje muce kinada ciki kuma nasa ne!!babu wanda kuma ya isa yace banashi bane zamu samu dukiya mai dunbin yawa dama wannan itace manufar mu akan su" Mum jitayi kafarta ta kasa daukan ta jin abunda aminiyarta take fada,babu wacce Mum ta yadda da ita kamar mummy'n Hafsa koh yan uwanta bata basu matsayin

Chapter 9 of 12