kaita?wallahi nima bansani bah,zainab ce tace barin kira yaya Sadeeq naji a wanne asibiti suke daga haka ta fara kiran number shi har ya katse bai dauka bah tana kokarin kara kiran shi sai kiran shi ya shigo dauka tayi da sauri tana cewa wai meya sami hamdiyya ne?munzo baba Haruna yace kun kaita asibiti,wane asibitin?fadamata yayi bata ce komai bah ta kashe wayar ta fadawa kamal,motar ya nufa yana cewa mu tafi toh daga haka suka bar kofar gidan baba Haruna na cewa Allah ya kiyaye hanya ya bata lafiya.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Here it's cums to ur page,I dedicated dis page to u zahra(zoora'u) Amaryar barmo Allah ya barki da barmo😉😉
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
4⃣7⃣➖4⃣8⃣
Doctor ne ya fito daga cikin ward din da'aka kauntar da ita,wurin shi suka nufa suna tambayan shi meke damunta duk da sunsa abun bazai wuce ulcer bah tunda shine ciwon dake damunta!!!cire glasses dinshi yayi sannan ya kalli Sadeeq yace wai kai har yanzu bazaka iya dinga duba hamdiyya bane?Sosa kanshi yayi yana cewa nifa ban ma sani bah sai bayan sunzo ne Mubarak ke fadamin shine nazo,tabe baki Dr hisham yayi yace ai kuma sai kayi,anyway ulcer dinta ne ya tashi nasan kun daina lura da cin abincin ta kuma tana fama da zazzabi mai zafin gaske saboda haka tana bukatar hutu anan zuwa nadan wani lokaci insha Allah zata samu lafiya!!Ummee ce tace hisham ai kasan halin qanwar taku biki sukayi kuma ba'a gida take bah nasan achan din ba abincin take zama taci bah Allah dai ya sawaqe!!!Ameen suka amsa dashi sannan Dr hisham ya musu sallama ya wuce office dinshi su kuma suka shiga cikin dakin da hamdiyya take.
A cikin harabar asibitin sukayi parking sannan zainab tace barin kira yaya Sadeeq sai ya fadamana ward din da take,koh kulata baiyi bah dan shi gaba daya hankalin shi ba'a nan yake bah!!!kiran yaya Sadeeq tayi yace bari ya fito ya shigo dasu ta amsa da toh.sanda ya fito ganin ta da wani da baisani bah yasa yake ta kallon su saida ya karaso ya bawa kamal hannu suka gaisa sannan yace musu suzo su shiga ciki,shida Zainab suna gaba shi kuma kamal na bayan su,yaya Sadeeq yake cemata Waye wannan kuma?dariya tayi yace sirikin nakane baka sani bah kuma?cewa yayi nikam ban sanshi bah inaga dai Mubarak ne ya sanshi da haka dai suka karasa zuwa dakin.
Bacci takeyi sosai abunta haka suka shiga cikin dakin yaya Mubarak ne a zaune a bakin gadon da take kwance akai,Ummee kuma na zaune akan wata kujera ita da abba,gaishe su shida zainab sukayi, zainab ta karasa gefen gadon ta zauna tana kallon kawar tata sannan ta kalli Ummee tace Ummee me akace yana damunta?murmushi Ummee tayi tace ulcer dinta ne ya tashi!!Abba ne yace Waye wannan kuma?bangane shibah,Mubarak ne yace shine surukin ka fah!!murmushi yayi yace kaini kamal Ashe ai ban sanka bah ya aiki?cikin jin knata kamal yace lafiya lau ya mai jiki kuma?da sauki suka amsa sannan Abba ya tashi ya cewa Sadeeq yazo ya maida shi gida zuwa anjima zai dawo,shima Mubarak tashi yayi yana cewa nima tafian zanyi tunda naga har yanzu bacci takeyi,itama Ummee cewa tayi ai nima tafiyan zanyi tunda ga zainab sai ta zauna da ita saboda inje in kwaso abubuwan da zamu bukata!!!kallon zainab tayi tace ai ba damuwa koh zainabu?dariya tayi tace babu komai sai kin dawo,sallama sukayi da kamal dan sunga bashi da niyyar tafiya yanzu suka barshi shida zainab.
A hankali take bude idonta bata sauke a koina bah sai akan kamal,kallon ta yakeyi kamar bai taba ganin ta bah suna hada ido tayi saurin dauke kanta,maida kallon ta tayi ga Zainab!!!!murmushi zainab tayi tana cewa besty kin farka ya jikin?da sauki ta ansa sannan tace Ummee nah fah?Ummee taje gida dauko Abu tana nan dawowa,kamal ne ya karaso wurin gadon yace ya jikin my dear?da sauki tace ba tare data kalle shi bah ganin haka Zainab ta tashi tace barinje na fadawa Dr kin tashi bata jira me zatace bah ta fita daga dakin.
A bakin gadon ya zauna yana kallon ta sannan yace meye kuma yake miki ciwo?ba tare data kalle shi bah tace babu koina!!ji tayi ya riko hannun ta kallon shi takeyi alamar ya sake mata hannun ta,amma yayi kamar bai gane mai take nufi bah!!!cikin sanyin murya yake cewa laifin mena miki jiya kika tafi baki fadamin bah kuma nata kiranki baki daga bah?shiru tayi bata cemishi komai bah sai chan tace ka sake mun hannu nah!!!bazan sake bah saikin fadamin meya faru,hawayen da batasan da zuwan su bah taji sun gangaro mata!!!ya salaam daga magana sai kuka kuma?toh kiyi hakuri ki fadamin laifi nah saina baki hakuri.cikin muryar kuka tace meyasa kasan mahaifiyar ka bata sona bata son aure nah dake kasa na fara sonka? meyasa ka turo niman aure nah?meyasa ka boyemun?kasa bata amsa yayi ya koma tunanin a ina kuma taji haka??kwace hannun ta tayi daga nashi tana cewa ka tafi tinda baka da amsar bani!!!ya bude baki zaiyi magana kenan Dr hisham ya shigo cikin dakin,hannu ya bawa kamal suka gaisa sannan yace Yar Abba ya jikin?share hawayenta ta shiga yi sannan tace naji sauki, dariya Dr yayi yace wannan halin baki nanan dai toh miye na kukan kuma yanzu?koh akwai inda yake jiki ciwo ne?zazzabi nakeji ta amsa mishi da haka!!Toh kiyi hakuri ga magani nan sai kisha zaki daina ji insha Allah!!!bata rai tayi dan babu abinda ta tsana irin magani dan gwara a mata allura ya fimata sauki,dariya yayi yace kinga dai su Abba basa nan Allah zan miki dure gwara ma ki ansa kisha!!!dariya kamal yayi yace yi hakuri Dr bani maganin zan bata tashaa,shima dariyar yayi ya mikawa kamal maganin sannan yace inbata shaa bah inanan dawowa kuma kinsan halinah daga haka ya fita a dakin.ruwa ya dauko yace ki bude bakin ki na baki kisha pls!!!mika mishi hannu tayi ba tare data kalle shi bah tace kabani,bai mata musu bah haka ya mika mata maganin.saida ta rife ido sannan ta watsa maganin a bakinta ta nayi tana girgiza kai,dariya ta bashi duk da hankalin shi a tashi yake haka zainab ta sake shigowa dakin ta samesu ganinta da kamal yayi yace mata barin je na dawo pls ki kula da ita, dariya tayi tace ba damuwa sai ka dawo!!haka ya juya ya fita daga dakin zuciyar shi duk ba dadi.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to Hauwa Muhammad (Slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
5⃣3⃣➖5⃣4⃣
Kwance tashi babu wuya,kwanaki nata tafiya haka ma lokaci nata tafiya yau saura 1wk bikin kamal da hamdiyya.mum din hafsa ce a gidan su kamal suna zaune ita da mum din kamal a cikin parlour,mum din hafsa tace nida hajiya Halima na Riga dana cire rai wai da cewa zamu hada zuri'a tunda dai ke kinkasa yin komai na hanayin wannan auren gashi shirye shirye sai gudana sukeyi babu wani abu dayake dakatar da wannan auren!!!abunda nakeso ki gane hajiya Maimuna shine banda ikon hanayin wannan auren tinda kowa na gidan nan nason auren,karki manta nacemiki har yarinyar nasamu namata barazana da kuncin rayuwa inta sake ta aure kamal, amma hakan baisa ta saduda bah tana ganin kamar wasa nakeyi koh kuma bazan iya aikata hakan bah,ina mai tabbatar miki sai yarinyar nan ta bar gidan kamal da kafar ta kuma auren kamal da hafsa yananan kamar yadda na fadamiki indai nice na haifi kamal,na barsu ne su cigaba da hidimar su nima tawa nanan zuwa nayi miki alkawarin nan saboda karma ki daga hankalin ki,kinji koh?naji amma Allah yasa kiyi yadda ki kace danni na fara cire rai wallahi.
Lokacin dasu mas'ud da iyayen shi suka samu labarin cewa har ansaka bikin hamdiyya ba karamin bakin ciki sukaji bah babu ma kamar mas'ud,mahaifin mas'ud har gida yaje yasamu Abba yaci mishi mutunci na cewa wai ya hana danshi auren Yar shi ya dauke ta ya bawa bare,sannan ya Kara da cewa zaiga abunda bare zai musu tunda har suka girmama wani na waje akan na gida.shidai Abba bai tanka mishi bah haka ya kare sababin shi ya nade rigar sa yayi tafiyar.hka shima mas'ud da suka hadu da hamdiyya ya fadamata sai taga yadda su kamal zasu wulaqanta ta tunda ta zabe su akanshi dan uwanta,data fadawa Ummee,sai Ummee tace mata karma tasaka wannan abun a ranta da yardar Allah babu wani abu da zai sameta sai alkhairi.
Har ankai lefe na auren kamal da hamdiyya amma duk wannan abun hajiya ce kawai take ta shirye shiryen bikin dan mum koh kallo basu isheta bah koh da aka kaimata lefen tagani qin gani tayi a cewar ta mezata gani tunda ba auren takeso bah.su fa'iza kuwa sai rawar kai akeyi za'ayi bikin yayan ta danma wai tana tsoron mum dinta.da sauri fai'za ta fito tana cewa Dan Allah yaya kamal kayi hakuri na barka kanata jirana,tsaki yayi yace wallahi da tafiya ta zanyi inaga dama bason ganin nata kikeyi bah!!dariya tayi tace haba dai aunty nawa guda zance banason gani kaima kasan bazai yiwu ba ai,haka dai ta shiga motar shi kuma yajaa motar suka nufi gidan su hamdiyya dan yanason yaji abubuwan da takeso fa'iza kuma ta matsa mishi akan sai ta bishi.
A cikin gidan sukayi parking sannan ya kirata a waya ya cemata gashinan shida kanwar shi fa'iza!!!ce mishi tayi gatanan zuwa,ba'a fi minti biyar bah sai gata ta fito,wani irin kyalli takeyi don tun last weak Ummee tasa ake mata gyaran jiki fatarta ta kara kyau ga kuma laushi.da murmushin ta ta iso wurin da suke,fa'iza ce tace auntynah ina wuni?murmushi tayi tace kai haba dai a nan zamu gaisa kuzo mu shiga ciki sai mu gaisa koh?kamal yace mufa bah zama mukazo yibah da zakice mu shiga ciki!!!harararshi tayi sannan ta rike hannun fa'iza tace mu shiga kinji sis? kai kuma kayi ta tsayuwa tinda ba zama kazo yibah nan suka wuce suka barshi a tsaye,dariya yayi yabi bayansu!!!part din baki ta kaisu suka zauna sannan tace tana zuwa, kamal yayi saurin cewa nidai dan Allah kizo muyi magana karki ce Zakije kawo wani abun kuma.hamdiyya tace waini Kai nace zan kawo wa abu komai?dariya fa'iza tayi tace yi hakuri auntynah ki barshi daga gida muke karki kawo komai,tsuke baki tayi tace wato kin biye mishi koh?sannan ta koma ta zauna tace inajinka meya faru?zama ya gyara yace dama sonake inji koh akwai abunda kike bukata already dai an kama wuraren daxa'ayi duk wani events.girgiza kai tayi tace babu komai danake bakuta na gama komai,numfashi ya sauke sannan yace toh shekenan inda wani kiyi mun magana mu zamu tafi zanje na sauke fitinan niyar nan in wuce wurin bash yana jirana!!!tashi sukayi hamdiyya tayi dariya tace toh bari su gaisa da Ummee bata jira mai zaice bah ta jaa hannun fa'iza suka fita, shima fitar yayi yana cemusu su sameshi a wurin motar.
Ummee ga kanwar kamal nan tare sukazo,gaishe da Ummee fa'iza tayi Ummee ta amsa cikin fara'a sannan tace ya mutanen gida kowa yana lafiya?lafiya lau tace sannan ta tashi tace barin je kar yaya ya tafi ya barni dan zai iya!! dariya sukayi sannan tayi wa Ummee sallama suka fita.a cikin motar suka sameshi fa'iza ta bude gaba ta shiga ta zauna tana cewa toh auntynah sai kuma biki zamu kara haduwa,murmushi tayi tace toh nagode sosai sis ki gaida gida, sannan ta leka cikin motar tace oga sai anjima toh!!!bai kulata bah sai fitowa dayayi daga cikin motar ya tsaya ta gaban motar,ganin ya fito yasa ta bar wurin fa'iza ta koma wurin shi, kallon ta yayi yace wai meke damunki ne?kallon shi tayi da mamaki tace me kuma nayi?ajiyar zuciya sauke yace kee babu Wanda yake cemiki kin rame ne?tunanin mekike yi?ana ganin ki ansan kina cikin damuwa daurewa kawai kikeyi,yanzu ki fadamin menene problem dinki?tunda ya fara maganar kanta ke kasa hawaye keso ya zubo mata amma tanata kokarin mayar dashi,shirun daya ji tayi yasa ya matso kusa da ita saiji tayi kawai ya kamo hannun ta ya nufa part din baki da ita, kalle kalle takeyi taga babu kowa a wurin sannan ta fara kokarin kwace hannun ta amma ta kasa saida suka shiga ya zaunar da ita akan kujera shima ya zauna sannan yace inajinki ki fadamin miye damuwar ki?
Nan ma shirun tayi saida ya Kara cewa inajinki?cikin rawar murya tace babu komai fah,girgiza kai yayi yace daga magana sai kuka?share hawayan tayi sannan ta dago kai tana kallon shi tace nace maka maka ba komai kawai dai already na fara missing family dina ne tun yanzu I wonder yadda za'ace zanyi weaks wai ban gansu bah!!murmushi yayi yace chan din da zakije ba mutane bah ne su?girgiza kai tayi tace nidai bance bah ka tashi kaje fa'iza na jiranka,zanje ai amma pls ki cire duk wata damuwa aranki duk sanda kikeyi missing din gida ai zakizo ki gansu and den ni bazan ma bari ki dinga missing dinsu sosai bah I will always be by ur side,kinji koh?murmushi tayi tace naji!!shima murmushin yayi ya tashi yana cewa gud gurl in kikeyi dariya kinfi kyau gashi kwananan sai kara kyau kikeyi,miye sirrin ne?tabe baki tayi tace ohooo!!dariya yayi yace toh koma dai miye zan sani daga haka ya fita ya nufi wurin motar.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to Hauwa Muhammad (slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
4⃣9⃣➖5⃣0⃣
Bayan ya fita daga asibitin gida ya wuce kai tsaye,part din hajiya ya shiga da sallamar shi wuri ya samu ya zauna yayi shiru!!!fitowa hajiya tayi daga kitchen ganin shi a zaune yasa ta karasa tana cewa meye kuma ya faru kamalu?numfashi ya sauke sannan yace kishiyar ki ce bata da lafiya tana asibiti, yanzu ma daga chan nake,subhanallahi!!!amma ya jikin nata?da sauqi ya bata amsa!! sannan yace amma hajiya kinsan kuma abinda ya bani mamaki?girgiza kai tayi tace a'a mai kuma ya faru?hamdiyya ce take cemun wai mahaifiya ta bata sonta,shine nake tunanin a ina taji wannan maganar waye ya fadamata?nidai nasan bashir bazai fadamata wannan maganar bah tunda shi da kanshi ya bani shawarar karna fadamata.ajiyar zuciya hajiya ta sauqe sannan tace kasan me nakeso dakai?karka yarda ka gina rayuwar auren ka akan boyewa matar dazaka aura wani abu,ya kamata ace ka fadamata tun farko taji maganar daga bakin ka amma bawai taji a bakin wani bah!!yanzu dai ka bari idan ta samu sauki ta koma gida sai kaje har gidan su ka fadamata komai kaji koh?daga kai yayi yace naji hajiya insha Allah zanyi haka nagode sosai da gudunmawar da kike bani.
*Bayan kauna uku*
Ta ishe kuwa da fitinar ita dai ta samu lafiya a sallame ta,haka aka discharging dinsu suka koma gida.kamal ne a zaune a part na baki na gidansu hamdiyya yafi 20min anan zaune yana zaman jiranta.Ummee ce a dakin hamdiyya tana cewa wai ke meyasa taurin kanki yake da yawa ne?zaki tashi kije koh saina bata miki rai?tashi tayi idon ta ya cicciko tana son tayi kuka sannan ta dauki hijab dinta har kasa ta saka tayi hanyar fita,har takai bakin kofa Ummee tace in kinga dama kije chan kiyi tayin kukan tinda baki da hankali!!share hawayen tayi sannan ta fita daga dakin.
Sallama ciki-ciki tayi kamar bata sonyi ta samu wuri ta zauna tana wasa da yatsun hannun ta!!!tunda ta shigo yake kallon ta sai chan dai yace har yanzu fushi kikeyi dani wai Dan Allah?bata amsa shiba ta cigaba da wasa da hannun ta!!!tashi yayi ya zauna kan kujerar dake kusa da ita,murya kasa-kasa yake cewa Dan Allah hamdiyya kiyi hakuri inda nasan boye miki wannan maganar zata sakiyin fushi dani wallahi da bazan boye miki bah,kuma abinda yasa na boye miki shine a tunanina bazaki aminche mun bah kuma nasan insha Allah indai har munyi aure mum dina zata karbe a matsayin daughter in-law dinta Dan Allah karki barni hamdiyya pls!!!kuka ne yakeso ya kufce mata amma tayi kokarin dannewa sannan tace da bakinta ta fadamin cewa bata sona,bani takeso ka aura bah,shine zakace wai zata amshe ni a matsayin daughter in-law a ina din?nidai kawai ka kyale ni kaje ka auri wacce mahaifiyar ka takeso.zuciyar shice yaji tana mishi zafi a lokaci daya kuma zuciyar na tambayan kanta wato mum da kanta ta fadawa hamdiyya haka kenan?jin shirun da yayi yasa ta daga kanta tana kallon shi,shima kallon nata yakeyi hakan yasa ta sauke kanta kasa!!!da kyar ya samu ya iya bude bakin shi yace hamdiyya karki manta alqawarin da muka wa junan mu pls na cewa da dadi da babu dadi zaki zauna tare dani,ina rokon ki da Allah karki karya wannan alqawarin kece *zabina* karki barni Dan Allah,dani zaki zauna bada mum dina bah kuma nasan mum dina zata soki koh bah yanzu bah I promise u dat.
Gaba daya jikin ta ya gama yin sanyi da maganganun shi da kuma tausayin shi dan ita kanta tasan cewa kamal na sonta so kuma bah na wasa bah kuma itama tana sonshi dan bata taba son wani bah irin shi a duk wayan dake cewa suna sonta,hasali mah ita bata taba tsayawa sauraron wani bah akan soyayya bah sai shi.shirun da tayi yasa yasake cewa pls mana hamdiyya ur silent is hurting me pls talk to me!!!goge kwalla tayi sannan tace toh me kuma kakeso nace maka?kicemun kin aminche mun,baza ki karya alkawarin da kika daukan mun bah pls!!!ajiyar zuciya tayi tace naji shekenan,murmushin jin dadi yayi sannan yace nagode sosai kuma insha Allah zakiyi zaman jin dadi a gidanah zan samamiki kaunciyar hankali mai daurewa da yardar Allah haka nan ma mahaifiya ta zata qaunace ki kamar yadda uwa ke son diyar ta kinji koh?daga kai tayi ta amsa da naji Allah yasa hakan in kuma hakan ya kasance zanfi kowa farin ciki,da Ameen ya amsa sannan yace insha Allah hakan ma zata kasance!!!haka dai suka Dan taba hira sama-sama tunda yawan cin hiran shi yakeyin ta daga baya ya tashi ya mata sallama akan zaije gida,suka fito tare ta wuce cikin gida shi kuma ya wuce wurin motar shi ya shiga ya tafi.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated dis page to u jameela salisu kura(Abokiyar fada nah).
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
5⃣9⃣➖6⃣0⃣
Da zazzabi ta tashi da kyar tasamu ta tashi tayi wanka sannan tayi sallah ,gaba daya haushin shi takeji koh kulashi batayi bah haka shima ya gaji ya kyaleta!!!komawa sukayi bacci sai wurin karfe 9:30am wayar kamal ta fara ringing cikin bacci ya dauki kiran,daga dayan bangaren Jamaal yace
"Haba mana bross duk angwan cin ne haka?tun dazu munzo munata buga kofa hajiya tasa mun kawo muku abincin karyawa amma shiru"
Tsaki yayi baice komai bah sai kashe wayar da yayi sannan ya tashi ya fita ya bude musu kofar.Jamal ne shida fa'iza,gaba yayi ya shige cikin parlour ya barsu anan tsaye batare da yace musu komai!!!kallon jamal fa'iza tayi sannan tayi daria,hararata yayi ya shige cikin parlour shima itama tabishi a baya tanata doka murmushi
A zaune suka sameshi yana kallon shigowar su saidai suka shigo suka zauna sannan suka gaishe shi,amsawa yayi sannan yace
"Meya faru da sassafen nan haka?"
Dariya suka fashe dashi su dukkan su,tsayawa yayi yana kallon su donshi baiga abun dariya anan bah.saida sukayi mai isar su sannan sukayi shiru kamal yace
"Wato kun gama rainani koh?ina tambayan ku kunamin dariya kamar kunga wani mahaukaci."
"Jamal ne yace Hajia ce fah tace mu kawo muka breakfast shine tun dazu muke ta faman buga kofah amma shiru."
Cikin murmushi fa'iza tace
"Yaya ina auntynah take ban ganta bah?"
Tsaki yayi ya tashi yana cewa
"Bansani bah tunda kinbani ajiyar tane,kuma ku jirani ina zuwa"
Daga haka ya wuce ya barsu anan zaune ya shige daki fa'iza ta tabe
Kusa da ita yaje ya zauna yana kallon yadda take baccin kwata kwata baya son ya tashi ta,haka dai ya fara tashin ta a hankali.
A hankali ta bude idon nata kana ganin idon kasan baccin bawai ya ishe ta bane,sannan ta tashi daga kwance ta zauna tana kallon shi
Shima kallon nata yakeyi yana murmushi sannan yace
"Kije kiyi wanka fa'iza da Jamal sunzo sun kawo mana abinci sai kizo muci."
Daga kai tayi batace komai ta tashi ta shiga cikin toilet dan tayi wankan
Har yanzu murmushin yakeyi sannan ya daga hannun shi yayiwa Allah godiya daya mallaka mishi ita a matsayin mata ya kuma roka Allah ya bashi ikon riketa da amana,sannan shima ya tashi ya shiga cikin wani dakin daban dan yayi wanka.
Bayan ta fito daga wanka mai ta shaafa sannan ta fito da wani swiss lace pink colour ta saka batayi wani kwalliya bah sai yar powder data saka da kuma lipstick.
A zaune ya shigo cikin dakin ya sameta a bakin gado tanata gwada number Ummee amma bata dauka bah.karasawa yayi ya zauna sannan yace
"Bakiyi kwalliya bah amma kinyi kyau sosai!!me kuma kikeyi da waya?"
"Ummee fah naketa kira amma taqi ta dauki wayan kuma yanzu nasan ta tashi bansan meyasa taqi dauka bah"
Dariya taso ta bashi yadda takeyin maganar kamar zatayi kuka amma sai yadake dan yasan inyayi dariyar nan akwai matsala,a cikin zuciyar shi kuma yace wato har ta fara missing yan gidan su lalle kinada aiki!!!
"A fili kuwa cewa yayi nasan baqin dagawa tayi wataqila bata kusa ne amma intazo ta gani ai zata kira koh?yanzu dai ki tashi muje muci abinci"
Batayi mishi musu bah ta tashi dan itama bah karamin yunwa takeji bah daurewa kawai takeyi haka suka fita a dakin zuwa parlour
Gaisawa sukayi dasu fa'iza cikin fara'a sannan suka zauna suka fara cin abincin,ganin su fa'iza basu da niyyar cin abincin yasa Hamdiyya tace
"Ku baza kuzo muci abincin bane?"
Murmushi fa'iza tayi sannan tace
"Ai yau in mukaci wannan abincin toh hajiya muma saita cinye mu dan saida mukaci sannan muka fito, taci saura in munzo nan mu cinye muku naku"
Dariya Hamdiyya tayi tace" kodai kawai kuce baza muci bah amma basai kunce hajiya ce tace karku ci bah"
Haka suka gama cin abincin sannan suka farayin hira kamar dama Chan sunsan juna.sai wuraren sha biyu na rana kamal yacewa Jamal yazo su fita ita kuma fa'iza ta zauna da Hamdiyya dan yasan yanzu mutane zasu fara zuwa,Jamal sukayi sallama da Hamdiyya yace sai yazo cin abincin amarci sannan suka fita
Fitar shi bada dadewa bah saifa mutane suka fara zuwa.chan saiga Zainab da Maryam mah sunzo,a daki suka sameta da dariyar su suka shiga Maryam tace
"Amarya kinsha kanshi kin ganki kuwa?yadda kikayi kyau"
Harara ta galla mata sannan tace
"Bangani bah,inadai ke kingani?kuma da kuka tafi kuka barni miye ya cinye ni gashinan kun dawo kun sameni"
Dariya sosai suka dinga yi kamar mahaukata ita kuwa Hamdiyya babu abunda take binsu dashi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 12