in banda harara,saida suka gama dariyar su Zainab tace
Me kuwa zai cinye ki in banda kamal?shiyasa muka tafi kuma koh parlour bamu karasa kaiwa bah sai gasu sun shigo abokanen nashi ma hanasu shigowa yayi dan baida ta ido!!!kinga kuwa ashe muda yazo ya samemu a dakin nan janmu zaiyi ya fitar damu waje"
Bata kula ta bah haka dai suka cigaba da hirar su mutane nata zuwa ganin amarya har yamma tayi kowa kuma ya watse ya koma inda ya fito,haka ma su Zainab suka tafi.
Saida akayi sallar isha'i sannan ya shigo cikin gidan.Amarya har ansakeyin wani wanka,shima wannan yayi sannan suka ci abinci dan hajiya ta sake aikowa da abincin,sannan kuma aka shige bacci.
✍✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA ❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated dis page to u Maryam S indabawa, marubiciyar Mijin Umma nah!!!nagode sosai da gudun mawarki a gareni Allah ubangiji ya bar zumunchi,ana mugun tare🤝🤝.
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
5⃣5⃣➖5⃣6⃣
Ansha shagalin biki a inada akayi walima ranar alhamis,wanda yasamu hallarta mallamai sukayi wa'azi mai ratsa zuciyar duk wani musulmi mai imani!!!tun ranar Hamdiyya take ta faman kuka Abu kadan ne zai sakata yin kuka koh abinci ma sai Ummee tayi da gaske sannan ta karba taci,dan cewa takeyi ita fah batajin yunwa Dan Allah a kyaleta!!!sai Zainab taje ta fadawa Ummee cewa Hamdiyya taqicin abinci sannan tazo ta sakata a gaba sai taga taci sannan ta kyaleta.Maryam ita da Zainab su suke dibe mata kiwa a koda yaushe dan dole haka Zainab ta dawo gidan da kauna tunda aka farayin bikin,ita kuma Maryam bashir yace ina shikam bazai yadda bah saidai kullum sai wurin sha dayan dare yake zuwa daukan ta.washe garin ranar da akayi walima wato ranar jumma'a kenan ranar akayi kamu,tunda aka fara hidimar bikin Hamdiyya taqi yarda su hadu da kamal wayar ma bah koh wani lokaci da takeyin picking bah wani lokacin har sai ya mata text akan Dan Allah ta dauka,toh koh daa ta dauko ba wata maganar kirki akeyi bah sai ta katse wayar.
Ance rana bata karya yau ne ta kama ranar da za'ayi daurin auren kamal da Hamdiyya.da misalin karfe biyu na ranar asabar aka shaida dauren auren *kamal Muhammad Usman* da kuma Amaryar da *Fatima umar farouq* wato (hamdiyya) Wanda yasamu hallarta mutane bah kadan bah daga gari daban daban,wai a hakan ma dan ansaka bikin kusa kusa ne da mutanen dazu hallarta bikin sai sunfi yawan hakan saboda wasu ma basu sanibah!!!gaba daya bakin kamal ya kasa rufuwa aboka nai sai faman tsokanan shi sukeyi shi kuma shi kadai yasan irin dadin dayake ji a ranshi,saidai cikin ranshi yanata addu'ar Allah ya bashi ikon sauke nauyin da Allah ya daura mishi, ya kuma sa kar mum dinshi ta dinga tsangwamar Hamdiyya.
Wata daga cikin abokanin wasan Hamdiyya ce ta shigo cikin dakin dasu Hamdiyya suke zaune,shigowa tayi tana guda tana cewa "shekenan yau Hamdiyya anzama matan aure kin shiga sahun manya har abada insha Allah sai kuma abar makalewa su Abba da Ummee su huta Allah ya baku zaman lafiya." Koh kallon ta Hamdiyya batayi bah balle ta tanka mata haka ta gama surutanta ta fita su Maryam sudai sai dariya sukeyi suna tayata.suna cikin haka wayarta ta fara ringing ganin kamal ne yasa taqi ansa kiran har ta gama ringing,wani kiran ne ya kara shigowa sai Zainab tace "wai ke miye haka mutum ya ta faman kiranki amma saikiqi dauka Dan Allah ki dauka kiji mai zaice miki" "tabe baki tayi tace toh me zaicemun iyaka yace mun an daura auren koh ba shekenan bah"?haka wayar ta sake katsewa bata dauka bah,shi kuma bai hakura bah haka yasake kiran wayar da sauri Zainab ta dauki kiran ta karawa Hamdiyya a kunne tana mata alama da ido irin Dan Allah kiyi magana!!!
Daga dayan bangaren kamal yake cewa" haba dear meyasa zan ta kiranki kiqi dauka Dan Allah?"shiru tayi bata amsa mishi bah,"saida ya kara cewa Dan Allah kiyi magana"sannan tace "inajinka me kakeso nace toh?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Hamdiyya yau kinzama tawa ta har abada insha Allah!!yau ina cikin murnan da ban taba shiga bah a cikin rayuwa ta bah Allah ya bamu zaman lafiya my dear"
"Ameen tace" bata jira mai zaice bah ta kashe wayar ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi tanajin tsoron yadda zataje ta samu surukar ta koh zata karbe ta koh kuma tana nan akan bakarta ta bazata amshe ta a matsayin suraka bah.
Shirye shiryen zuwa wurin dinner sukeyi mai makeup tazo ta musu makeup nagani a fada inba kasan ta sosai bah bazaka gane cewa Hamdiyya bace.karfe sha daya da rabi aka fara tafiya saida kowa ya tafi sannan su Maryam suka fito suda Amarya,motar daza'a sakata suka shiga da ita kamal na zaune a ciki sannan su kuma suka shiga cikin motar bash suka kama hanya.
Kama hannun ta yayi yana murzawa a hankali yace "fushin me kikeyi dear?" "Koh bakya son zuwa wurin ne a fasayin dinner din?"girgiza kai tayi tace " a'a bah haka bane kawai dai ina jin tsoron mum dinka ne koh tana wurin."murmushi yayi yace" tana wurin amma babu komaai kinji koh karki damu." a haka dai suka karasa akayi dinner cikin nutsuwa da kaunciyar hankali Amarya da Ango sun bawa kowa sha'awa haka aka gama taron cikin jin dadi kowa ya koma gida, mum dai babu wani abun kunya da tayi a wurin a cewar ta ba yanzu bane zata farayin cin mutuncin bah.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah saleehu
Dedicated to hauwa muhammad (slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
6⃣5⃣➖6⃣6⃣
A haka rayuwar auren su ta cigaba da tafiya da dadi babu dadi!!Kamal nayin iya qoqarin shi dan yaga ya farantawa Hamdiyya yana bata duk wani lokaci nashi wajen kyautata mata
Bangaren mum kuwa duk sanda ta tashi zataje har gida tayiwa Hamdiyya rashin mutuncin dataga dama
Yauma hakan ne ta shirya fita zuwa gidan tace fa'iza tazo ta rakata,saida suka dauki hanya fa'iza tagane inda zasuje!!! Kallon mum tayi tace
"mum me kuma zamuje yi gidan yaya kamal?nidai Dan Allah inkinsan zaginta zakije yi driver ya tsaya na sauka nikam bazanje bah"
Harara mai rai da lafiya mum ta bankawa fa'iza
"Zuwa kamar kinje infada miki,kuma ni dama babu abunda zai kaini gidan nan illa inje in zageta tas!!!dan nayi alkawarin ita da kafarta zata bar gidan nan tinda ba gidan ubanta bane"
Dakyar fa'iza ta shiga cikin gidan saida mum tace saitaci mutuncin ta inbata shiga bah,hakanan babu yadda ta iya ta shiga gidan
Tana ganinta a gidan tasan abunda ya kawota gaishe ta tayi bata amsa bah sannan suka gaisa da fa'iza
Kitchen taje ta jero musu kunun aya da tayi da kuma snacks!!!a gaban mum taje ta tsoguna ta zuba mata kunun ayan data kawo mai sanyin gaiske sannan ta ajiye mata,tana durkushe a wurin ta dauki wani cup ta fara zubawa fa'iza
Tana cikin zuba mata taji mum ta watsa mata kunun aya mai sanyi sannan ta wurgar da cup din ya fashe
saida ta shide saboda sanyin dayake dashi wurin ta zabura ta tashi kuwa ta taka cup din daya fashe yaji mata ciwo take a wurin jini ya fara zuba
Da sauri fa'iza ta karasa wurinta ta riko kafar tata tana kallon yadda jinin yake fita taimaka mata tayi ta tashi a wurin tawuce da ita cikin dakin ta gaba daya fa'iza ta rikice ita kanta mum saida tadan tsorata dan yadda taga jinin na zuba
Cikin rawar jiki fa'iza tasamu gyara mata kafan jinin ya tsaya sannan ta gyara inda jinin ya bata batare data cewa mum komai
Saida ta gama sannan ta koma dakin Hamdiyya!!! hakuri ta dinga bata,ita kuwa tace babu komai!!! haka mum ta Shigo ta samesu
Kamar batayi wani abun bah ta kalle fa'iza sannan tace
"ai saiki tashi mu tafi koh?ke kuma kadan kika gani wallahi da kanki zaki bar gidan nan namiki wannan alqawarin kuma idan kamal din ya dawo kice mishi yazo ina neman shi"
Daga haka ta fice a dakin fa'iza mah tashi tayi tasake bata hakuri sannan ta fita
Bayan yadawo bai ganta a parlour bah dan haka ya wuce dakin kai tsaye.a cikin bargo take karasawa yayi da sauri ya zauna kusa da ita yana tambayan ta koh lafiya
"kaina ne yakemin ciwo tunda rana nakasayin komai"
"subhanallahi kuma yanzu ace kisha magani kice a'a yanxu ki tashi kiyi wanka sai inyi miki abinda zaki ci sannan kisha magani"
"A'a mum tazo tace kana dawo kaje tana neman ka!!!ni yanzu zan iya tashi inyi wankan kanka dawo zan hada mana abinci"
girgiza kai yayi jin mum tazo gidan yasan ita tazo tayi abinda ta saba sannan yace
"me tamiki ita tasa kanki ya fara ciwo koh?"
"A'a ni batamin komai bah tadai ce kaje tana neman ka"
Tashi yayi ya shiga wanka dan yasan bazata fadamishi komai bah amma shi yasan babu yadda zaayi mum tazo gidan nan ace kuma batayi wani abun bah
Bayan ya fito ya shirya sannan yace mata zaije ya dawo ya fita a gidan gaba daya ranshi baya mishi dadi.
A dakin ta ya sameta zama yayi akan kujera ya gaishe ta,kamar kullum yau mah bata amsawa gausuwar bah sai fada data farayi akan baya zuwa gida kullum
Hakuri ya bata akan zai dinga zuwa kullum sannan ya tashi ya mata sallama ya fita
Daidai zai shiga part din hajiya ya hadu da fa'iza gaishe shi tayi ya amsa har ya wuce sai faiza tace
"ya Kamal dan Allah ka kara bawa auntynah hakuri akan abunda ya faru ta kara hakuri komai zai wuce insha Allah"
Kallonta ya tsaya yi sannan yace
"metayi mata?"
Fada mishi duk abinda ya faru tayi!!!yama rasa mai zaice koh mai zaiyi haka ya fasa shiga part din hajiyan yayi ya wuce wurin motar shi ya kama hanyar gida
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to Hauwa Muhammad (slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAJURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
5⃣7⃣➖5⃣8⃣
Taci kuka harta gaji ta godewa Allah fuskar nan duk ta kumbura su Maryam sunyi bada hakurin harsun gaji har ta fara basu tausayi.
Ummee ce ta shigo cikin dakin da suke a zaune tana cewa.
"Wai Hamdiyya har yanzu kukan kikeyi?Toh kizo Abban ki na kiranki."
Tashi tayi batace komai bah tabi bayan Ummee suka shiga wurin Abba.
"gyaran murya Abba yayi sannan ya fara cewa Mama nah yanzu dai kinga rayuwa ta chanza kinzama Matar wani, kinzama Yar wasu,zaki fara sabuwar rayuwa a wani gidan na daban ba inda kika tasu kika ga kanki bah,saboda haka inaso kiyi hakuri da yadda zaki samu kanki ki dauki surukan ki a matsayin iyayen ki karki yarda ki Saba musu."
Haka dai ya cigaba dayi mata nasiha Ummee ma hakan ne ta danyi mata daidai gwargudu.A haka wata qanwar Ummee ta shigo cikin dakin tana cewa.
"Koh kun fasa bayar da itane?yan daukan Amarya tun dazu sunzo sunata faman jiranta amma kunzo kun riketa nan."
"Dariya Abba yayi yace ai mun riga mun bada ita ki dauki ta kikai musu mu mungama bamu yanzu."
Kamar wata mahaukaciya haka ta zabura ta rungume Abban ta tana yin wani irin kuka mai tsuma zuciya tana cewa.
"Abba ni bazan tafi bah banason in tafi in barku zanyi missing dinku,Dan Allah kace musu su tafi ni bazan je bah."
Jikin sane yayi sanyi yasamu ya cireta a jikinsa daga rikon da tamasa sannan cikin sanyin murya yace.
"Kiyi hakuri mama nah ai dole ne ki tafi kinga suna chan sunata jiran ki kiyi hakuri ai zaki dinga zuwa kina ganin mu muma haka zamuna ziyar tarki,kinji koh?"
Kai ta daga mishi sannan ta sake shi ta juya wurin Ummee ta rungume ta,shaafa bayan ta Ummee tayi tace.
"Ki daina kukan haka ya isa kije Allah ya miki albarka ya baku zaman lafiya addu'ar mu kullum tananan tare dake."
Haka ta sake Ummee sai kuma taji an rike hannun ta data dagu sai taga yaya Sadeeq ne da yaya Mubarak.
Wani kukan tasake fashewa dashi mai ban tausayi sannan ta rungume yaya Sadeeq shima rungume tan yayi dan shi kanshi yasan zaiyi missing dinta ba kadan bah.haka ta sake shi ta rungume abokin fadan ta a kullum wato yaya Mubarak tana cewa.
"Zanyi missing dinku wallahi banason tafiya dan Allah kace musu su tafi su barni ni banason binsu."
Dago ta yayi yana kallon yadda fuskar nan tasha kuka sannan ya girgiza mata kai alama tadaina yin kukan sannan yace.
"muma zamuyi missing dinki amma ai zaki dinga zuwa mana muma kuma haka zamu dinga zuwa miki saboda haka karki damu muje in rakaki."
Haka ya fito da ita a rungume da shi kowa sai kallon su yake har suka bawa wasu tausayi dan kowa ya santa ita da yayan nata Mubarak.A motar daza'a sakata ya sakata sannan ya rufe kofar motar,har motar ta fita shida yaya Sadeeq sunanan a tsaye a wurin saida motar ta fita sannan suma suka shiga cikin gida.
Gida ne sosai na alfarma aka shiga dasu nan ne gidan da zata zauna.kai tsaye dakin ta aka wuce da ita,A bakin gado suka zaunar da ita masu guda sunayi masu addu'a suma sunayi haka kuma masu tsokanan sunata faman tsokanan ta.ita kuwa har kawo yanzu tanata faman shirgar kuka,haka mutane suka watse daga ita sai Maryam sai kuma Zainab.
Shigowar motocin da suka jine yasa Zainab ta fara cewa.
"Toh hajiya Maryam ki tashi mu fita tun kafin kamal yazo ya kuremu Dan kinsan zai iya dan naga rawar kanshi yayi yawa."
"Dariya Maryam tayi tace aikowa muje kafin yazo ya fitar damu."
Yau dai Hamdiyya babu bakin yin bakar magana sai cewa datayi.
"Dan Allah karku tafi kunji?"
"Dariya Zainab tayi tace ai tafiya ta zama dole yarinya Allah dai ya Baku zaman lafiya da zuri'a ta gari. "
Basuma jira mai zatace bah suka fita daga dakin suka rufu mata kofar.wani sabon kukan sake fashewa dashi abun tausayi.
A parlour suka tarar da kamal shida abokanan su,kallon su bash yayi yace.
"Har kun fito tun bamu shiga dashi bah?"
Harara kamal ya galla mishi sannan yace.
"Ku shiga ina din koma anan zaku tsaya dan na fiku sanin inda zan shiga."
Kama baki bash yyi yace.
"Eh lalle ai naga alama, toh nufa kunji kuzo mu tafi tun kafin ya koremu."
Dariya sauran aboka nan nashi sukayi sannan suka kama hanya suka fita suna mishi tsiya.shi kuwa koh a jikin sa sai binsu a baya dayayi ya rufe kofa ya dawo cikin gida.
A hankali ya turo kofar dakin,kusa da ita yaje ya zauna sannan ya riko hannun ta yana cewa.
"Toh kuma kukan na menene?koh kinaso na mayar dake ne?"
Da sauri tace.
"Eh nidai ka mayar dani Dan Allah"
Rungume ta yayi a jikin sa ya fara lallashin ta Dan ba karamin bashi tausayi tayi bah yasan ta saba sosai da yan uwanta,saida yaga ta samu nutsuwa sannan yace.
"muje muyi alwala muzo mu godewa Allah."
babu musu ta tashi sukayi alwala sukazo sukayi nafila sannan ya gabaatar da addu'a yayi mata yan tambayoyi ta bashi amsa,sannan kuma salon maganar ta chanza.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah saleehu
Dedicated to hauwa muhammad (slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
7⃣1⃣➖7⃣2⃣
Yau kauna biyar kenan da kawo Hafsa gidan Kamal a matsayin matar sa amma koh da sau daya Kamal bai taba koh kallon part dinta bah balle kuma ayi maganar ya shiga
Babu yadda Hamdiyya batayi bah akan ya shiga wurin Hafsa amma yaki!!!wani lokacin mah idan yaga tanaso ta matsa mishi da maganar sai ya tashiya barmata wurin
A bangaren Hafsa kuwa hakan bai dameta sosai bah saboda tana samu ta fita taje tayi ashararan cin ta a waje kamar yadda tasabayi da samarin ta
Mum ce da mummyn Hafsa a zaune Hafsa na daga gefen su tana faman zuba kukan munafirci abun da akayi da wanda ba'ayi bah duk saida ta fada,acewar ta Hamdiyya ce ta hana Kamal ya shigo part dinta sannan ta biyota ta cimata mutunci,saboda haka ita gaskia bazata iya zaman gidan bah
Cikin bacin rai mum ta tashi tsaye tama huci
"A yau dinnan basai gobe bah kuma basai anjima bah wannan matsiya ciyar yarinyar zata barmiki gidan nan sai yadda kikayi dashi!!!kuzo muje yau zatasan ta shigo inda ba'a bukatar ta"
Tashi sukayi suka bita a baya suna murmushin mugunta
Kamal na ganin mum yayi zumbur ya tashi daga zaunen dayake
Ita kuwa babu abinda take binshi dashi sai uban harara,saida tayi mai isar ta sannan tace
"sannun ka da aiki ka kyauta sosai wato an kawo maka yarinyar mutane koh ka leka kaga abinda aka kawo maka koh?wannan shidaniyar matar taka ta hanaka fita koh?"
Cikin shi da Hamdiyya babu wanda yace wani abu!!hakan yasake harzuga mum tayi cikin hamdiyya,tayi mata wani irin damka tana cewa
"wata dan ubanki kice mai juya min dan dana haifa a cikin ciki nah koh?yau kusan wata tara kenan dayin auran ku amma koh miyau har yanxu baki fara zubarwa bah balle kuma akai ga maganar amai!!!saboda kin gaji dayin karuwan cinki a waje kin gama zubar da yayan shege a waje, sannan zakizo nan kuma kice zaki mulkemu koh?toh kinyi kadan wallahi
Ance mai hakuri bai iyayin fushi bah!!!yau kam Hamdiyya tura takai bango hakurin datayi a baya yau batajin zata iyayin shi.dama ta dauki mum ne amatsayin mahaifiyar ta shiyasa duk abinda tayi tamata batace komai bah,amma yau kam ta kasa jurewa najin an kirata da sunan karuwa kalmar da babu wanda yataba kiran ta dashi,aikin da bata taba kusan tanshi bah balle kuma ta aika shi,ga kuma zagin mahaifin ta da akayi wanda duk duniya tanajin bata da wanda yafi matashi
hakan yasa itama yau ta gayawa mum maganar taga dama,ta manta cewa a gaban Kamal take,ta manta cewa da surukarta take magana.bawai ta zageta bah bane amma ta fadamata magana iya sun ranta,bata kaiga karashe maganar datake bakin ta bah taji Kamal ya dauke ta da wani irin gigitaccen mari
A zabure take kallon sa hawaye na sauka daga cikin idonta.shi kanshi baisan lokacin daya mata hakan bah!!!cikin murya kuka Hamdiyya tace
"wato dan yau na mayar da cin mutuncin da akeyimun shine zaka iya cire hannunka ka mareni koh?yayi kyau hakan,mahaifiyar kace ni kuma matar kace,zaka iya chanza mata a duk lokacin dakake so koh kaga dama amma kuma bazaka iya chanza uwa ba har abada"
Daga haka ta wuce cikin dakinta tabarsu a tsaye,kayanta ta fara hadawa a cikin trolley dinta,bawani kaya ta dauka bah ta rufe trolley dinta ta fito
A yadda ta barsu haka tazo ta samesu batare data sake cewa wani abun bah ta nufi kofar fita.jin an rike trolley din nata yasa ta tsayawa batare data juyu bah!!!cikin sanyin murya Kamal yace
"babu inda zakeji da kayan nan,dan Allah karki tafi Hamdiyya ki zauna komai zai zama daidai na rokeki"
"zaka iya hanani fita da kayan nan saboda kaika siyesu,amma bazaka iya hanani fita daga gidan nan bah"
Daga haka ta sake mishi ta fita daga cikin parlour'n!!!yayi niyyar ta bita amma mum ta hanashi kuma tace bata yafe mishi bah idan ya sake yaje gida su Hamdiyya koh kuma ya kirata a waya.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Wannan shafin naku ne masoyan *itace zabina*, nagode da kulawar ku a gareni!!Allah ya bar zumunchi.
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DS JURIYA ONLINE WRITER'S✍
6⃣1⃣➖6⃣2⃣
Haka suka cigaba da zaman auren su cikin nutsuwa da qaunar juna!!bayan sati daya da gama biki kamal yace ta shirya zasuje gida ta gaishe da mum dinshi da kuma hajiya daga nan sai su wuce taga su Ummee!!!ba karamin dadi taji bah na zataje taga su Ummee dinta amma kuma a dayan bangaren zuciyar ta tanata tsoron zuwa gidan su kamal dan batasan me mum dinshi zata mata bah,haka dai ta fara shirin tafia.
A parlour ta fito ta sameshi yana zaune yana jiran fitowar ta,tana fitowa shima ya tashi yana cewa
"Kinsan Allah daa na tafi na barki,kinje kinyi zaman ki inata jiran ki!!!amma kuma kinsan miye?kinyi kyau sosai ke komai kika saka kyau kikeyi"
"Nidai mu tafi kuma ai bazaka iya tafiya badani bah tunda dai har kasa kamin rai akan zanje"
Dariya yayi sannan ya kama hannun ta suka fita a tare suka shiga motar suka kama hanyar zuwa gidan mum.
Sunata hira abin sha'awa dasu,sai kuma shiru ya dan biyo bayan hiran!!kallon ta yayi sannan yace
"Meya faru?naga kinyi shiru,koh bakya son zuwa ne mu koma?"
"A'a inason zuwa mana, ya za'ayi nace banason zuwa"
Murmushi yayi dan yasan tana shakkar zuwa gidan nasu saboda yasan har yanzu tana tuna abinda mum dinshi tamata,a hankali ya kama hanunta yace
"Karki damu babu abunda zata miki ki sake jikin ki!!!idan munje ma bawani dadewa zamuyi bah sai mu wuce wurinsu Ummee"
Murmushi jin dadi tayi najin ba dadewa zasuyi bah sannan ta daga mishi kai alamaun toh.
Bayan ya gama parking suka fito a tare,part din mum suka fara shiga babu kowa a cikin parlour sai TV dayake ta faman aiki shi kadai,cewa yayi ta zauna bari yaje ya kira mum!!!toh tace ta zauna,shi kuma yayi hanyar dakin mum
Da sallama ya turo kofar dakin,a zaune take abakin gado tana waya da mum din Hafsa!!!kallon shi tayi sannan tacewa mum din Hafsa ta bari zata kira ta daga nan ta katse wayar!!!gaishe ta yayi ta amsa sannan kuma tace
"Daga yin auren sati daya har ka fara mantawa damu yanzu yau kauna biyu kenan baka leko gidan nan bah kai wai mai mata"
Shiru yayi baice komai bah dan shi ba komai ya hanashi zuwa gidan nan bah sai maganar Hafsa da take mishi sai kuma yadda take fushi dashi,a hankali yace
"Mum tare da Hamdiyya muke tazo ta gaishe ki tana parlour"
Daa kamar tace bata bukatar gaisuwar amma kuma sai ta fasa sai kuma tace mishi
"Kaje ina zuwa tinda ni zanje gaishe tan ba ita zata biyo ni bah kaje ina zuwa"
Tashi yayi ya fita a dakin yana addu'ar Allah yasa karta wulaqanta mishi mata.
Da takama ta shigo cikin parlour ta nema wuri ta zauna tanata faman harare-harare cikin girma mawa da ladabi ta gaishe da mum!!!batare data amsa gaisuwar tata bah tace
"Ki rike gaisuwar ki dan babu wani amfani dazata min,ban daukeki a matsayin wacce zata gaishe ni bah balle har in amsa mata gaisuwar ta!!!wacce na dauka da hakan tana nan zuwa nan bada dadewa bah!!!kin gane koh?kai kuma daga yau karka sake dauko min wannan abun wai da Sunan tazo gaishe ni"
Tunda mum ta fara magana kanta yake kasa hawaye
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 12