ga dukkan nin alama bazai saurari ni bah!!! Murmushi mummy tayi tace ai inbai saurare kibah zai saurari mahaifiyar shi dai koh?toh yanxu zan kira ta na fadamata wulaqan taki da yayi,ai Hafsa sai nasan yadda nayi naga kin shiga cikin daular nan ta gidan nan koh da kuwa baya sonki
Wayarta ta dauka ta fara kiran mum batayi wani ringing sosai bah mum ta picking call din tana cewa kai hajiya Maimuna kin manta dani kauna biyu!hajiya Maimuna tace ai ba haka bane yanxu Hafsa taje gidan ku dan tayiwa kamal barka da zuwa amma wallahi hajiya halima bakiga yadda kamal ya wulaqanta Hafsa bah,ni ina ganin tunda baya sonta kawai mu hakura amma hajiya halima nayi matukar kwadayin in hada zuri'a dake saboda zumunchin mu yafi haka amma babu damuwa hakan ma zamuyi zumunchin insha Allah.hajiya halima tace kima bar wannan maganar hajiya Maimuna ai zumunchi kamar ma mun hada ne da yardar Allah ai shi kamal din bashi ya haifi kanshi bah ki barmin komai a hanuna ina mai tabbatar miki zanyi handling komai auren kamal da Hafsa kamar anyi shine hajiya Maimuna bari kuma ya dawo zai fadamin dalilin daxai sa yamata wulaqanchi amma kuma koh cikin gidan bata shigo mun gaisa bah,murmushi hajiya Maimuna tayi tace wai ai fushi tayi shiyasa tama kasa shiga gidan!hajiya Halima tace Allah sarki kice mata tayi hakuri zan jaa mishi kunne bazai sake yin hakan bah insha Allah!!murmushi hajiya Maimuna tayi tace toh ba damuwa hajiya Halima ya wuce sainaji daga gareki daga haka sukayi sallama suka katse wayar.kallon Hafsa mummy' tayi tace bana fada miki bah ai auren ku dole ayi shi indai inada rai su dukka suka saka daria harda taafawa kamar wasu frnds.
Suna fita daga gidan bash yace zainab fah ita baza taje taga wurin bane?Maryam tace eh Umma zata aike ta toh shiyasa tace muje kawai karta bata mana tym, bash yace owk daga haka suka kama hanya zuwa wurin daza ayi dinner. Parking yayi a wajen da motoci ke yin parking su dukkan su suka fito suka shiga cikin wurin!!hamdiyya ce tace bash ai wurin yayi babu wata bukatar a chanxa wani wurin amma kuma an kama inda zaayi kamu da walima?bash yace duk ankama zamu iya zuwa kuga nan din maa in kunaso.Maryam ce tace aa basai munje ba koh besty? Hamdiyya tace eh basai munje bah I trust u bash nasan wurin yayi tunda nan din ma yayi,daria bash yayi yace toh godia nake.duk maganar da akeyi kamal bai saka musu baki bah sai faman kallon yadda hamdiyya take magana a nutse cikin murmushi yakeyi!! Bash ne ya lura da kallon da kamal ke yiwa hamdiyya matsowa kusa da kamal din yayi ya daga mishi gira yace ya how far kallon da kake mata fah a nawa ne?murmushi kamal yayi yace koh nawa akace inbiya zan biya!!kallon shi bash ya tsaya yi da mamaki sai Chan yace da gaske?kamal yace da gaske mana koh mun tabayin irin maganar nan dakai?cikin jin dadi bash ya girgiza kanshi yace aa dan yasan abokin nashi indai yasamu hamdiyya a matsayin mata yaji dadi.Maryam ce tace mu tafi koh?dan zamuje mu ansa dinkin mu kuma zamuje muyi wa mai lalle magana jibi zamuje!!daga haka suka fita motar suka shiga suka wuce direct wurin mai dakin suka nufa dan bash yasan wurin saboda tare suka kai dinkin.suna zuwa ansan dinkin sukayi dan already angama kuma dama sun biya kudin dinkin daga nan wurin mai lallen suka wuce suka fadamata akan jibi suna so suzo suyi lalle, cemusu tayi babu matsala amma suzo da wuri suka amsa mata da toh suka wuce.motar suka dawo suka cewa bash yanxu gida zai kaisu shekenan kuma,bash yace toh daga haka suka kama hanyar gida.
Har cikin gida suka shiga da hamdiyya duk da tace ya sauke ta amma yace aa fita tayi ta musu sallama tace toh Maryam sai jibin dan gobe hutawa zamuyi daga jibin kuma nasan babu wata maganar Hutu har sai kuma angama biki.Maryam tayi dariya tace toh ba matsala Allah ya kaimu kallon bash tayi tace toh ango sai anjima bash yace toh hamdiyya mun gode ki huta gajiya!!hamdiyya tace toh nima nagode kallon kamal tayi taga ita yake kallon nan din ma harararshi tayi tace sai anjima sarkin kallo baisan sanda yayi dariya bah yace da wanne idon kika san ina kallon ki in kema bah kallon nawa kikeyi bah?tabe baki tayi tace Ohoo...ta sakeyi wasu Maryam sallama ta wuce abinta.bash ne ya juya motar mai gadi ya bude musu suka fita yana cewa atoooh sai faman kallon yarinya kakeyi kamar kasamu TV!kamal yace eh ai TV nasamu dan rainin wayo.dariya bash yayi yace maryam kamal fah bestyn ki ta kama sa,maryam tayi dariya tace ai babu komai ni dakai na zan shige mishi gaba!kamal yace yawwa amaryar mu Allah ya miki albarka maryam tace ameen daga hka
suka sauke ta sukayi sallama ta shiga cikin gidan su kuma suka kama hanyar gidan su kamal.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to hauwa Muhammad (slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
2⃣1⃣➖2⃣2⃣
Har suka gama aikin su mas'ud nanan a parlour a zaune shida Mubarak bai tafi bah duk da yasan ba lalle bane hamdiyya ta saurare shi.fitowa tayi da abincin dasu ka gama ta wuce dinning area dashi tana jera shi,daidai nan abban ta yayi sallama suka shigo tare da yaya Sadeeq, da sauri ta nufi wurin abban nata ta rungume shi sannan tamushi sannu da zuwa, shima shaafa kanta yayi yace sannu mama nah Allah y miki albarka cike da fara'a tace ameen abba nah sannan ta juya wurin yaya Sadeeq ta ansa brief case din hannun shi tace wlcm bross!!yaya Sadeeq yace tnx sis ya kike?tace lafiya lau,ya aikin?yace alhmdll daga haka suka karasa cikin parlour, gaisawa Sadeeq da mas'ud sukayi sannan mas'ud ya gaishe da abba cikin sakin fuska da fara'a abba ya amsa mishi gaisuwar sa haka Ummee ta fito ta samesu itama sannu da dawowa tayiwa abba ya amsa zama suka danyi suna Dan taba hira kadan kadan shi kuwa mas'ud gaba daya su yakeyi yayi magana da hamdiyya, haka har lokacin salla yayi Abba yace su wuce masallachi daga haka dukka suka wuce sai mas'ud da yayi zaman shi.umme ma tashi tayi ta wuce sama,hamdiyya ta tashi itama zata wuce taji mas'ud ya kira sunan ta juyuwa tayi dan a zatonta shima ya wuce masallachin ne cewa yayi hamdiyya pls sai yaushe ne zaki dinga saurarata ne Dan Allah?hamdiyya ta tabe baki tace yaya mas'ud pls mubar maganar nan cos I dnt lyk it at all,na fadamaka I'm nt interested pls,na dauke ka a matsayin brother ne kawai so pls mu barshi a Hagan zai fimun dadi bata jira mai zaice bah tayi wuce warta abun ta, ya Dan dade a tsaye a wurin sannan ya dauke car key dinshi ta fita.
Da sallama ya shiga cikin parlour mum din nashi a zaune ya sameta akan kujera tana shan fruit kusa da ita yaje ya zauna yace ina wuni mum,da wani irin kallo ta bishi dashi tace da ban wuni bah zaka ganni ne?da mamaki yace mum meya faru koh namiki wani laifin ne bansani bah?gyara zama tayi tace uban waye yace ka wulaqanta Hafsa dan tazo maka sannu da zuwa? Murmushin takaici yayi yace mum Dan Allah yanzo akan yarinyar nan ne zakiyi fushi dani?mum tace nayi fushi dakai din wallahi kamal ka guji bacin raina ina fadamaka koh?kamal yace mum Dan Allah kiyi hkr amma wallahi banason Hafsa nifah ynxu nasamu wacce nakeso.wata irin tsawa mum ta daka mishi wanda yasa yayi saurin dago kanshi tace wallahi kamal u wnt to see the other side of me shiyasa zakamin wannan maganar banzan na fadamaka Hafsa zaka aura koh kanaso koh bakaso babu wata wacce zan ansa a matsayin daughter in-law dina inba Hafsa bah, kaji dai na fadamaka daga haka ta wuce ta barshi a zaune a wurin.
Duk abunda akeyi ashe dad dinshi da Jamal qaninshi suna tsaya suna jinsu karasowa dad yayi ya zauna a kusa dashi sannan ya dafa kafadar shi sannan yace son!!kamal ya dago idon shi da har sun koma jaa yana kallon dad din nashi dad yace karka damu babu Wanda zai aura maka wacce bakaso, kaji koh?sbd haka ma karka damu,amma da gaske kakeyi kasamu wacce kakeso koh kuma ka fadamata haka ne dan ta hakura da maganar? Kamal yace a'a daddy da gaske nakeyi kuma wallahi daddy ina sonta banason hafsa koh kadan a rayuwa ta,dad yayi murmushi yace toh ai komai ma zaizo da sauki kawai Ku daidaita tsakanin Ku da yarinyar ni zan shige maka gaba.cikin jin dadi kamal ya riko hannun dad din nashi yace nagode sosai daddy Allah ya kara girma dad ya shaafa kanshi yace ameen kamal sannan ya tashi shima yabar parlour, Jamal ne ya matso ya zauna kusa dashi yace at the end who is d lucky garl?duka kamal ya kaima Jamal sannan yace ina ruwan ka sarkin gulma?daria Jamal yayi yace da ruwa nah mana kasan dole nace mata lucky garl dan ta cire tuta.kamal yayi daria sannan ya tashi yace nine dai na cire tuta inta aminche mun,shima Jamal din tashi yayi yace wane ita tace bata aminche bah,Kai ni I cnt wait to see dis lucky aunt of mine,fa'iza ce ta karaso parlour tace me too...daria kamal yayi na ganin kowa ya goya bayan shi banda mum sannan yace karku damu very soon zaku santa daga haka ya fice zuwa part dinshi.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to hauwa Muhammad (slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
1⃣9⃣➖2⃣0⃣
Tana shiga cikin parlour mas'ud ta tarar a zaune shida yaya Mubarak wani irin takaici taji ganin mas'ud a gidan nasu.da kyar ta karasa cikin parlour gaishe su a daqile Wanda koh kallon mas'ud din batayi!!cewa yayi qanwa ta kauna biyu nata kiranki baki picking call din ba,tabe baki tayi tace eh bana kusa da wayar ne shiyasa!!ganin yau har ta tsaya bashi amsa yasa ya kara cewa toh kuma shine bazaki kiran bah bayan kinga missed call? Dan siririn tsaki tayi tace 2dys banda tym ina busy bata jira mai zai ce bah kuma ta kalle yaya Mubarak dake kallon yadda take yin maganar kamar ansata dole tace yaya Mubarak Ummee fah? Mubarak ya girgiza kai yace tana kitchen daga haka hamdiyya ta wuce kitchen din ta barsu anan zaune.sannu da aiki tayiwa Ummee sannan ta fara taya Ummee girke girke,chan yaya Mubarak ya shigo kitchen din yace haba hamdiyya kinsan fah mas'ud yazo gidan nan ne saboda kee amma kinyi kamar bakisan da zuwan shibah!!hamdiyya tace yaya Mubarak kafasan banaso yaya mas'ud yana shiga harka taa nikoh ganin shi wallahi banason yi....Ummee ce tayi saurin katse ta da cewa karna sake jin kince haka koh ma menene mas'ud dan uwanki ne shi saboda bakya sonshi bashi zaisa kice zaki wulaqan tashi bah!!hamdiyya tace toh Ummee kiyi hakuri bazan sake bah Amma wallahi banason yana shiga harka ta,Mubarak yace sis nasan mas'ud bai dace dake bah amma atleast ki dinga bashi respect amatsayin shi na brother dinki kinji?hamdiyya tayi murmushi tace toh naji cwt bross zan gyara!!Mubarak yayi dariya yace dats my sis Allah ya baki miji nagari itama dariya tayi mubarak ya koma parlour su kuma suka cigaba dayin aikin su.
WANENE MAS'UD
Mas'ud ya kasance da wurin yayan abban hamdiyya!!mas'ud irin samarin nan ne wanda zasu ce suna son wannan in sunga waccan suce suna so,toh hakan ne yasa da yace yana son hamdiyya ita kuma taji nan duniya babu Wanda ta tsana irin mas'ud shi kuma ya nace dole ita yake so ya aura da ya takurawa mahaifin shi da maganar sai mahaifin nashi yasamu abban hamdiyya akan ya bawa mas'ud auren hamdiyya shi kuma abban nata yace bazai mata auren da bataso bah indai tace tanason mas'ud toh zai aura Mata shi in kuma tace aa shekenan, koh da aka tambaya hamdiyya sai tace aa daga nan abban nata yace toh shekenan tunda tace bataso amma duk sanda tace tanaso a shirye yake da aura mata mas'ud din!! Hakan ne yasa har yanxu mas'ud ke bi biyar hamdiyya akan ta so shi su kuma iyayen shi yanxu fushi sukeyi da iyayen hamdiyya akan cewa sun hana dan su auren yar su wannan kenan.
CIGABAN LABARI.....
Har cikin gidan su ya shigar da kamal,kamal yace wai nufin ka bazaka shiga bane?bash yace gaskia bazan shiga bah kaidai ka gaishe da mum,kamal ya tabe baki yace zataji har ya bude kofar motan zai fita sai kuma ya tsaya yacewa bash frnd!! nifah da gaske nakeyi akan maganar yarinyar nan wallahi tun danake ban taba ganin wacce ta kaunta min a raina bah irinta pls u have to help me out!! Murmushi bash yayi yace karka damu kamal zanyi matukar farin ciki kasamu hamdiyya a matsayin matar auren ka dan yarinya ce wacce tasan ya kamata and I promise u dat I will do all dat I have to do to see u 2gether wit her insha Allah!!!!murmushin jin dadin an yabi hamdiyya kamal yayi yace toh nagode bash amma ina jin tsoron koh wani ya rigani,bash ya dafa kafadar kamal yace karka damu a iya sanina hamdiyya babu Wanda take kulawa insha Allah zata zama matar ka!!kamal yaja numfashi yace toh Allah ya yarda mun, in haka ta faru zanfi kowa farin ciki bash ya zungure shi yace ni fita min a motar zan tafi. kamal yayi daria yace ai dole kamin wulaqanchi tunda kaga ina neman abu a wurinka daga haka ya fita a motar shi kuma bash ya juya motar ya tafi abunshi yana mai jin dadin yau abokin shi yasamu wacce yake so kuma hamdiyya abun ya mishi dadi bah kadan bah.
Direct part din hajiya ya wuce dan yayi mata wannan babban albishir din data dade tana zaman jiran shi dan koh iyayen kamal basu damu da rashin auren kamal bah kamar yadda hajiya ta damu.babu kowa a parlour nata kai tsaye bedroom dinta ya nufa tura kofar dakin yayi da sallama a kwance ya sameta jin sallamar kamal yasa ta tashi zaune tana cewa kamalu sai yanxu ka dawo kai koh gajia bakayi?kamal ya bata rai yace wai Dan Allah hajiya bazaki daina cemun kamalu bah?nazo da murna ta namiki albishir amma kinaso ki baramin rai.hajiya ta tabe baki tace toh yooo wanne albishir zakamin mai dadi?nifah inba matar aure kasamu bah babu wani albishir mai dadi zakamin atoooh....kamal yayi dariya yace toh in shidin zan miki fah?gyara zama hajiya tayi tace kai kamal Dan Allah da gaske kakeyi? Kamal yayi murmushi yace da gaske mana wallahi hajiya yau nasamu irin matar danake so in aura.dariyar jin dadi hajiya tayi tace kai alhmdll amma wallahi naji dadi yau mara musaltuwa Allah ubangiji yasanya muku alkhairi aciki Allah kuma yasa ayi damu.kamal yace ameen hajiya amma fah saidai ban fada mata bah kuma ina tsoron tace bata sona dan gaskia ina mugun sonta ban taba jin son wata mace bah a rayuwa ta sai ita!!hajiya tace wacece ita daxata ce bata Sonka ai tayi kadan in fadamaka saidai inba kace kana sonta bah,bah kace kanaso bama ance ana sonka balle kuma kace kanaso ai kawai kaje kai tsaye ka fadamata da gudu zata aminche.murmushi kamal yayi yace hajiya ita ta daban ce ba irin sauran yan mata bace marasa kamun kai kedai kimun addu'ar samun nasara!!hajiya tace toh babu matsala zan maka amma nasan bazata qika bah da yardar Allah, kamal yace toh Allah yasa barinje part din mum daga haka ya nufi part din mum dinshi.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to kitchen nd novels grp luv u all guy's
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
2⃣3⃣➖2⃣4⃣
Yana shiga part dinshi toilet ya shiga yayi wanka,kayan baccin shi yasaka sannan ya dauko wayar shi number fa'iza ya kira yace ta kawo mishi coffee dan baijin zai iya cin wani abinci.a zaune ta sameshi jawo stool tayi ta daura mishi cup din akai sannan tace brother ga shinan kasha, dago kai yayi yace toh nagode daga haka ta fita a dakin,hakanan kuma yaji coffee ma bazai iya shaa bah tunanin maganar da mum dinshi ta fadamishi dazu kawai yake yi da kuma irin yadda yakejin son hamdiyya a cikin ransa!!wayar sa ya dauka yana kiran bash amma bai dauka bah kan gado ya koma yayi ruf da ciki yana tunani kala-kala da kuma mamakin yadda akayi ya fara son hamdiyya lokaci daya,yana cikin tunanin ne yaji wayar shi na ringing dauka yayi yace ina ka shiga inata kiran ka?daga dayan bangaren bash yace na shiga wanka ne lafiya meya faru naji muryar ka haka?tashe zaune kamal yayi yace zaka iya hadani da hamdiyya gobe?zare ido bash yayi kamar kamal na ganin shi yace kai Mallam tun yanxu har ka fara shiga tension?ai dai ka bari agama hidimar biki nah kafin ka tasu da naka koh?ajiyar zuciya kamal yayi yace kai Dan Allah banason wasa I'm serious abt it, inaso na ganta gobe inji koh zata aminche dani koh a'a!!Dan yau daga dawo wata mum ta hauni da fada wai ban kula Hafsa bah kuma wai koh inaso koh banaso ita zan aura!!! Dariya sosai bash keyi inbadan kamal yasan cewa ta hanyan bash komai zaizo mishi da sauki daya dade da kashe wayar,kamal yace bash banason iskanci kana jina koh ina fadamaka damuwa ta kana min daria!!bash ya tsagaita dariyar shi yace toh ai naji auren dole akeso amaka kamar wata macce Koh macce ai yanxu baa mata auren dole balle kuma namiji.tsaki kamal yajaa sannan yace ni bah wannan na kiraka ka fadamin bah, zaka hadani da Ita goben koh kuwa?nutsuwa bash yayi yace y nt?zan kira maryam yanzu na fadamata ita kuma sai ta kira ta tace mata gobe muna son ganinta nasan baza taqi bah, Sosa kai Kamal yayi yace yanzu kake magana!!Allah ya taimaka min ta aminche mun murmushi bash yayi yace insha Allah zata aminche Allah dai yasanya alkhairi amma fah ni inajin tsoron za'a iya samun matsala daga wurin mum tunda ita tace Hafsa takeso,kamal yace insha Allah babu wata matsala shiyasa nake so mu hadu da ita goben naji mai za tace kaga inta aminche min matsala ta zatazo da sauki,bash yace I hope so!! Allah ya zaba mana abunda yafi zama alkhairi kamal yace ameen sai goben in Allah ya kaimu daga haka suka katse wayar.
Ita tayi serving din kowa sannan itama ta zauna ta fara cin abinci sai chan abba yace wai mas'ud ta tafi ne?dan koh a masallachi ban ganshi bah,sai a lokacin ne maa suka tuna da mas'ud, Ummee ce tace toh inaga ya tafin kenan amma koh sallama bai mana!!haka dai suka gama cin abinci hamdiyya ta tattara wurin takai komai kitchen sannan itama ta dawo cikin parlour ta zauna suka cigaba da hirar su gwanin ban sha'awa,yaya Mubarak ne ya fara tashi yace shi zaije ya kaunta dan ya gaji,hamdiyya tayi charaf da cewa wanne irin gajia kuma kai daba fita kayi bah yau aikin ma da kace zaka taya Ummee babu abinda kayi in banda kallo, Mubarak yace yanxu nayi magana dake ne?sai anjima kuma ace nina tsokane ki koh?Ummee ce tace kai kyaleta Dan Allah karka biye Mata, Abba kam murmushi yayi yace mama nah banda neman tsokana fah,Mubarak yace Ku kyaleta kawai zamu hadu da ita ai daga haka ya musu sallama ya tafi,suma din tashi sukayi kowa ya wuce dakin shi.tana shiga toilet kawai ta shiga tayi wanka tayi alwala sannan ta fito ta saka kayan baccinta ta hau gado,wayarta ta dauko taga missed call din Maryam murmushi tayi tace zansha surutu kuwa kiran maryam din tayi tace besty ya akayi ne? kin kira ina parlour,Maryam tace ai dama ke kullum wayar ki bata hannun ki,dama bash ne yace wai Dan Allah gobe yanaso suzo gdn ku shida abokin nan nashi akwai maganar ta zakuyi,yatsena fuska hamdiyya tayi tace magana kuma?wacce irin magana?maryam tayi tsaki tace aike ba'a abun arziki dake koh ma wacce irin magana ce ai kya bari suzo sai kiji koh?hamdiyya ta tabe baki tace toh Allah ya kawo su zan fadawa Ummee amma nifah banason wannan shegen kallon daya kemun,dariya Maryam tayi tace kedai Allah ya shiryeki wallahi ni banga wani kallon ki da yayi bah hamdiyya tace toh ni nagani saida safe bacci nakeji sai sunzo daga haka ta kashe wayar tayi addua ta kwanta.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to hadiza sardauna Allah ya baki lfy sis...luv u wujiga wujiga
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
2⃣5⃣➖2⃣6⃣
Ba wani baccin kirki yayi bah saboda tunanin shin hamdiyya zata aminche mishi koh a'a,ga kuma tunanin maganar da mum dinshi ta fada na bazata accepting kuwa a matsayin daughter in-law bah inba Hafsa bah.sai wurin karfe 10:15am ya tashi kallon lokaci yayi sannan ya tashi ya shiga toilet brush yayi sannan yayi wanka, fitowa yayi ya shaafa mai tare da feshe jikin sa da tsadaddun turaruka gaban wardrobe dinshi yaje ya bude ya dauko wata bugaggeyar shadda coffee colour yasaka ba karamin kyau yayi bah.bakin gado ya koma ya zauna ya dauko wayar shi ya kira bash!!gaisawa sukayi sannan kamal yace hope dai ka shirya? zanzo na dauke ka sai mu tafi,dariya bash yayi yace haba sarkin zumudi ai daa kabari anyi sallar jumma'a sai muje yanzu yayi wuri muje gidan mutane gaskia,Sosa kai yayi sannan yace toh Allah ya kaimu zanzo na dauke ka bash yace toh ba damuwa sai kazo daga haka suka kashe wayar.tashi yayi ya wuce part din mum dan ya gaishe ta,koh daya shiga babu kowa a parlour, bedroom din ta ya shiga ya sameta a zaune gaishe ta yayi ta ansa da kyar sannan tace wato dan nace maka ga wacce zaka aura shine har da qin zuwa cin dinner koh?kamal yace mum ba haka bane naji bana jin tune's ne shiyasa, harararshi tayi tace koh ma shi dinne kai dai kasani dan inanan akan bakata aure kai da Hafsa babu dashi,dago kanshi yayi yana kallon mum din nashi yaga da gaske takeyi babu wasa a tattare da ita!!marairaice mata yayi yace Dan Allah karki hadani da Hafsa wallahi banason ta akwai wacce nakeso pls mum,kallon banza ta mishi tace ka tashi ka bani wuri banason maganar banza abunda na fada shi za'ayi in kuma kai ka haifi kanka zanji,tashi yayi jiki a sanyaye ya fita daga dakin.
Part din hajiya ya wuce koh zai dan samu relief,a parlor ya sameta zaunawa yayi suka gaisa hajiya tace kamalu mai ya sameka Nagan ka wani iri meya faru?Abubuwan da suka faru ya fadamata,tsaki hajiya tayi tace yoo kaji maganar banza akan wannan ne zaka tada hankalinta?toh indai ina raye kuma na isa nafada aji a gidan nan wacce kakeso zaka aura saboda haka ma ka kauntar da hankalin ka.kamal yayi murmushi yace toh hajiya nah nagode,a part din hajiya yayi breakfast sunayi suna hira har lokaci yayisannan ya tashi yace mata zaije yaga kishiyar ta dariya tayi tace toh Allah ya bada sa'a yace ameen daga haka ya fita ya tafi.
Bayan sun gama breakfast su abba suka tafi wurin aiki,ita da Ummee suna zaune a parlour kiran maryam ya shigo wayarta dauka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 12