Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
chanza mata, take tausayin shi ya kamata!!!hanun ta tasaka ta kamo nashi sannan ta rufe idonta Bangaren Mum kuwa dadi takeji sosai mara misaltuwa,koh ba komai yau ta dawowa danta da farin cikin daya rasa a sanadiyar ta A bangare daya kuwa kunyan Hajiya takeji badan kadan bah!!saboda irin rashin kyautata mata datayi a zaman su,amma yau itace ta fitar da ita daga halin datake ciki Ta daukan waa kanta alqawarin kulawa da Hajiya kamar yadda zata kula da mahaifiyar ta,sannan kuma da surukar ta wato Hamdiyya Ganin tayi shiru da alamu akwai abinda take tunani yasa Hajiya tace "Me kuma kike tunani?bayan komai yanzu ya wuce tinda ta yadda ta dawo dakin ta,saidai kawai a kiyaye gaba sannan amanta da baya da abunda suka faru" Tasowa tayi tasaka gwaiwar ta a akasa a gaban Hajiya sannan ta riko hannun ta tace "Ki yafemun Hajiya nasan duk abubuwan dana miki ban kyauta miki bah,na daukeki bah a bakin komai bah!!!na dauki wayanda basa kaunata a matsayin wayanda suka fimin zuri'a ta daraja,ina mai neman yafiyar ki dan Allah" "Babu komai ni dama ban rike ki a zuciyata bah!!!balle kuma har ince ban yafi miki bah,dama nasan duk daren dadewa zaki gane gaskia,zakisan suwaye masoyan ki da gaske,ban taba daukan ki a matsayin suruka taba saidai a matsayin yata,kece dai kike kallon abun da ban,amma yanzu komai ya wuce karki damu Allah ya iyar mana" Da Ameen suka amsa,farin ciki a wurin Dad yau baya misaltuwa,abinda ya dade yana jiran ganin shi yau ya gani,godiya yayi wa Allah ******** Jin yanaso ya juya amma kuma yaji hanun shi a rike yasa ya bude idon shi,kallon ta ya tsayayi yanaso ya tabbatar cewa bah mafarki yakeyi bah!!!dan koda Hajiya tace zataje ta dawo da ita bai kawo cewa yau zataje bah Yana cikin wannan tunanin ta bude idonta,itama kallon nashi takeyi kamar basu san juna bah,tashi yayi daga kauncen dayake ya zauna,itama tasowa tayi ta zauna a bakin gadon "Hamdiyya dan Allah karki cemun mafarki nakeyi,kece kika dawo gareni kodai mafarkin ne?" Dariya ya bata, dan haka ta fara dariya kamar wacce tasami tabin hankali,da kyar ta tsayar da dariyar sannan tasa hannunta ta mintsine shi, ai kuwa ya zabura!!!dariya tasakeyi sannan tace "Yanzu ka tabbatar ba mafarki kakeyi bah?nice dai in kuma in koma ne toh barin je na cewa Hajiya kace na koma" Rungumeta yayi sosai kamar za'a kwace mai ita yace "Dan Allah karki sake tafiya ki barni,ni kadai nasan yadda naji a lokacin da bakya tare dani!!!kiyimin alqawarin bazaki kara tafiya ki barni bah" Zame jikin ta tayi daga nashi sannan ta riko hannun shi tace "Nayi alqawarin bazan sake barinka bah saidai in rigaka mutuwa nayi,wannan mah dan babu yadda zanyi ne!!!tun kafin na hadu dakai nake rokon Allah dayasa wanda zan aura mahaifiyar shi nada rai saboda in dauketa a matsayin mahaifiya ta,in kyautata mata kamar yadda zan kyautatawa Ummee nah,amma kuma hakan bai samu bah" Shiru ta danyi sannan ta cigaba da cewa "Yanzu komai ya wuce Mum tana sona tanason zamana dakai,dan haka babu wani dalilin dazai sa na tafi na barka" Tunda ta fara magana Mum na tsaye tana jinta,kwalla ta share sannan ta karasa cikin dakin tace "Tabbas ina qaunar ki har cikin raina Hamdiyya,qaddara ce kawai ta shiga tsakanin mu" Cikin jin dadi suke kallon ta lokacin datake magana, sake neman yafiyar Hamdiyya tayi ita kuma tace babu komai,sannan tace suje parlour ga abinci nan an kawo musu Babu musu suka tashi sukaje parlour ita kuma Mum ta koma part dinta tanamai jin dadi a ranta Suna cikin cin abinci wayarta ta fara ringing ganin mai kiran ta yasa tayi murmushi tare da amsa kiran Daga dayan bangarenn muryar yaya Mubarak ne yake cewa "Maimakon ki bari sai nace ki koma shine kika tafi abinki batare da munyi sallama bah koh?saboda kina sauri kije kiga mijin ki" Turo baki tayi kamar yana ganin ta sannan tace "Nifah ba haka bane,nima naso muyi sallamar ai amma kuma bakanan" Dariya yayi yace "Toh ai shekenan Allah ubangiji ya baku zaman lafiya mai daurewa a tsakanin ku,sannan ki kara da hakuri I will miss u" "I will miss u more,nagode sosai sai mun sake magana" Daga haka suka katse wayar,kamo bakin ta Kamal yayi yace "Wai yaushe zaki daina shagwabar nan in anyi magana ki turo baki kamar wata karamar yarinya" "Ehmana har yanzu ni karamar yarinya ce in fadamaka" Dariya yayi sannan yace "Karamar yarinya dai tananan a cikin ki amma ke yanzu kin tashi daga yarinya kin zama babba" Itama dariyar tayi bata sake cewa komai bah,haka suka cigaba da cin abincin su cikin jin dadi da qaunar juna. ✍✍✍ [1/22, 10:55 PM] ‪+234 813 539 4575‬: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣ NA Khadeejah Saleehu Dedicated to hauwa Muhammad (slim small) 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍ 8⃣5⃣➖8⃣6⃣ Yau kauna biyu kenan,abunda ya faru tsakanin su Mum da kuma Hamdiyya Tunda suka koma gida shida Mum part dinshi ya wuce kai tsaye,sallah ce kawai take fitar dashi daga nan,koh Dad mah a masallachi suke haduwa amma bai taba yiwa Kamal magana akan Hamdiyya bah Abun duniya duk ya taro ya mishi yawa ya rasa mezaiyi,Abinci mah da kyar yake iya samu yaci,shima sai Mum ta matsa masa dan gaba daya baida appetite Yau ne hajiya ta dawo daga tafiyar datayi,taga chanji sosai a wurin Mum abun har mamaki ya bata,amma kuma dai batace komai bah!!!ganin har yanzu bataga Kamal bane yasa tace "Wai nikam ina Kamalu ne?koh kuma baisan yau zan dawo bane? shiyasa bai zo bah?dan mun dade bamuyi magana dashi a waya bah!!" Shiru babu wanda ya amsa mata tambayan ta,kallon su ta tsayayi sannan tace "Wai koh bakuji ina magana bane?kowa yayimin shiru,meya faru da Kamalu din?" Dad ne yayi gyaran murya tare da cewa "Yana part dinshi,inaga baisan da dawowar ki bah bari amishi magana" "Ikon Allah yaushe Kamalu ya kuma dawo zama a gidan nan,ku fadamin meke faruwa mana kun banni a duhu" Duk abunda ya faru Dad ya kwashe ya fadawa Hajiya babu abunda ya boye mata "Allah ma halicci!!!kai kuma saika zauna kana kallon su bazaka je da kanka kabasu hakuri bah su bari ta dawo dakin ta bah sannan kuma saika kubar yaro yana zaune,kuma babu wanda ya damu daya sanar dani halin da'ake ciki" Tashi tayi da saurinta kamar zata tashi sama,ta nufi part din Kamal!!!Da sallamar ta,tashiga parlour'n shi Jin muryar Hajiya yasa ya tashi yana cewa "Aaaa su Hajiya yaushe a gari kuma?shine koh kicemun yau zaki dawo" Kana ganin shi kasan yana cikin damuwa daurewa kawai yakeyi "Saboda nima ka damu ka fadamin abunda yake faruwa koh?shiyasa nima zance maka zan dawo Yau" Ya gane indata dosa,hakan yasa ya kuma ya kishingida da kujera!!!ita kuma ta nema wuri ta zauna tace "Duba yadda ka koma dan Allah?yanzu kana ganin wannan ce mafita a gareka?ka zauna anan baza kaje kasan yadda zakayi ka dawo da matar ka bah? " Hajiya taya zan dawo da ita?koh kadan Hamdiyya tunani takeyi bada ita na damu bah,ta dauka saboda cikin jikin tane yasa mukeso ta dawo,kuma bah haka bane.tace inada san kaina dayawa,wanda nasan dole tayi tunanin haka!!tun kafin na aure ta tasan Mum bata sonta amma haka na lallabata ta yadda mukayi aure,nazo na kara aure batare data sani bah,ta tafi gidan su da wata daya ban neme tabah!!!sai yanzu,shiyasa nace zan batta tukun nah wataqila nan gaba ta tausaya min ta dawo gareni!!!banason in sake shiga hakkin ta.Amma ni Hamdiyya *itace zabina* Allah yasa ta gane haka" Tausayin shi duk yagama kamata, dafa shi tayi tace "Karka damu insha Allah yau zan dawo maka da matar ka,zaku cigaba da zaman ku cikin aminchi da yardar Allah" Bata jira mai zaice bah ta tashi ta koma part din su Mum tace "Ku tashi muje gidan su Hamdiyya mu dawo da ita,mu kara basu hakuri akan abunda ya faru" Babu musu suka tashi suka bita zuwa gidan su Hamdiyya Sunyi magana da dama a tsakanin su Dad ya sanar musu da cewa baya kasan ne saida ya dawo ya samu labarin abunda ya faru kuma yace "Abunda yasa kuma banzo bah shine inaso su gane kuskuren da sukayi,nasan yanzu dukkan su sun gane laifin su!!dan haka ina rokon ku da kuyi hakuri ku barta ta koma dakin ta" Abba ne yace "Babu komai itama kuma nasan yanzu bazata ce bazata koma gidan mijin ta bah,bari aje a kira ta" "A'a ku nunamin dakin nata inje da kaina in mata magana" Haka kuwa akayi Ummee ta nunawa Hajiya dakin ta sannan ita kuma ta Shiga Akan abun sallah ta sameta ta idar da sallah,da sauri Hamdiyya ta tashi ta nayi wa Hajiya sannu da zuwa, sannan suka koma bakin gado suka zauna Maganganu masu dadi Hajiya ta dinga yiwa Hamdiyya harsai data yadda ta gamsu,sannan tace mata ta tashi tazo su tafi Haka babu musu ta biyota suka fito suka samu su Ummee,Hajiya tace "Toh nayi bikon kishiya ta,ku tashi mu tafi koh?" Dariya sukayi su dukka sannan suka sakeyi musu godiya Rungume ummee taje tayi,ta kuma rungume Abban ta,sannan su kuma suka saka mata albarka,bayan haka suka kama hanya suka tafi,amma taso ace sunyi sallama da yaya Mubarak da yaya Sadeeq amma bah dama. ✍✍✍ [1/22, 10:55 PM] ‪+234 813 539 4575‬: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣ NA Khadeejah saleehu Dedicated to hauwa Muhammad (slim small) 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍ 8⃣9⃣➖9⃣0⃣ Bayan sun gama cin abincin sannan ya tashi yaje yayi wanka,bayan ya fito yace itama taje tayi wankan amma tace koh tayi bata da kayan dazata saka Daukan wayan shi yayi ya kira fa'iza akan ta kawo mata wasu kayan,sannan ita kuma ta tashi ta shiga wankan,fitowar ta yayi daidai da shigowar fa'iza Cikin murna fa'iza tayi kanta tare da cewa "Welcome back auntynah,wallahi nayi missing dinki sosai,ya jikin ki?" Dariya Hamdiyya tayi sannan tace "Naji sauki mana koh baki gani bane?kuma mah bakiyi missing dina bah nasani" Fa'iza zatayi magana kenan Kamal yace "Kee dan Allah ki kyaleta ta saka kaya kar sanyi ya kamata,kinzo kin cika mutane da surutu sannan kin wani dane ta salon ki kayar da ita" "Oooo Allah ya baka hakuri,auntynah sai kin fito koh?" "Toh nagode" Daga haka ta juya ta fita ita kuma ta saka kayan ta,bayan ta gama Kamal yace tazo su tafi!!kallon shi ta tsayayi sannan tace "Ina kuma zamu?nifah na gaji bacci nakeso nayi" "Gidan mu zamu koma mana!!!dama dan bakya nan ne yasa na dawo nan,in munje chan kyayi baccin" Ganin tanaso ta mishi musu yasa ya kama hannun ta suka nufi part din Mum,saida suka kusa shiga taga bashi da niyyar sake mata hannun haka yasa ta kwace hannun tare da cewa "Nufin ka haka zamu shiga?ka wani rike mun hannun kamar yarka" Murmushi yayi sannan yayi gaba itama ta bishi a baya,haka suka shiga suka samesu sunata hira gwanin ban sha'awa Suma zaman sukayi aka danyi hiran dasu,chan anjima Kamal yace su zasu tafi!!! Mum da Hajiya sukayi saurin hada baki da cewa "Ina kuma zaku tafi" Dariya suka bashi ganin yadda sukayi maganar kamar bada matarshi yace zai tafi bah,sannan yace "Gidan mu mana zamu koma,koh kuma dama mun dawo nan da zama ne?" Rike baki hajiya tayi tace "Yau ga ja'irin yaro,toh idan akace bazata bika bah fah?" "Ai kema kinsan bazai yiwu bah!!kindai fada ne" "Aaaaa sosai kuwa dole ka fadi haka tunda namaka mai wuyan ai" Mum tayi dariya sannan tace "Toh wai mah saurin me kakeyi?kabari mana sai gobe koh jibi sai ku tafi" Ganin yadda yayi da fuskar sa yasa Dad yace "Kai ku tafi abinku zaman me zasuyi anan din?ai gwara su koma gidan su kuma" "Yawwa Dad shiyasa nake sonka nagode" Tabe baki sukayi sannan Hajiya tace "Toh mukuma kace baka son mu shine zaka birgeni" Haka dai suka gama surutun su,suka fito raka su har bakin mota,sannan sukayi sallama su kuma suka kama hanyar gida Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin so da kaunar juna duk da akwai ranar daza ace wani yayiwa wani abunda baiji dadi bah,amma haka zasu bawa junan su hakuri su cigaba da zaman su ba tare da kowa yasan halin da suke ciki bah A wannan lokacin kuma Mum ta kira Kamal akan ya rubutu sakin dazaiyi wa Hafsat ita da kanta zata kaimusu,ai kuwa kamar jira yakeyi haka ya rubuta mata saki ukuu,Mum batace komai bah ta karba ta wuce gidan su Hafsa Lokacin dataje gidan ta samu baban Hafsa nata bala'i akan Hafsa ta koma gidan mijin ta inyasu inta Haifa masa cikin koh sakin tane yayi Muryar Mum sukaji tana cewa "Ai sun san cewa cikin bana Kamal bane shiyasa kaga basu ce zataje ta haife shi bah" Cikin razana suke kallon Mum,shi kuma baban Hafsa yace "Haba Hajiya wannan wacce irin maganar banza ce kikeyi?ban gane bah cikin Kamal bane,toh inba cikin shi bane na waye? " Ai su ya kamata kayiwa wannan tambayan nikam bansan na waye bah" Nan ta kwashe komai da ya faru ta fadamishi sannan tace kuma ya tambaye su intayi musu karya,sannan ta ciro takaddan saki ta mika musu Tambayan su ya shiga yi amma sun kasa bashi amsa sai uban kuka da sukeyi,nan yace Mum din Hafsa ta tashi ta bar mishi gidan shi dama ya gaji da halayen ta,ita kuma Hafsa tunda yar sace babu yadda zaiyi da ita,Idan ta haifi abinda yake cikinta dole ta mayar dashi wurin uban shi Haka Mum ta tashi ta tafi ta barsu,itama mummyn Hafsa ta tashi tabar gidan dan babu yadda zatayi ********* *Bayan wata takwas!!!* Cikin hamdiyya ya gama tsofa haihuwa koh yau koh gobe,kullum a cikin addu'a takeyi Allah ya kawo mata da sauki dan Maryam tace mata akwai wuya kasan cewar ita ta riga data haihu,ta haifi danta namiji mai suna *Aminu* Shi kuwa Kamal kullum cikin karfafa mata gwaiwa yakeyi tare da yimata duk wani abu datace tanaso Itama zainab haihuwa koh yau koh gobe jira kawai sukeyi A bangaren mas'ud kuwa shida iyayen shi sun gane shirmen da sukeyi ba daidai bane,hakan yasa mahaifin shi yaje suka sulhunta ta Abban Hamdiyya zumunci sukeyi sosai yanzu Bangaren yaya Mubarak da fa'iza kuwa soyayya ake shaa babu kama hannun yaro tunda har iyayen su sunsan da maganar kuma an tsayar da ranar aure ****** Tunda ta tashi da safe takejin jikin ta babu dadi,har Kamal yagane hakan amma daya tambaye ta tace babu komai haka ta wuni a sukwani duk bata jin dadi Da daddare mah bawani bacci ta samu bah sai juyi da take ta famanyi,da safe Kamal ya gane bata da lafiya amma saboda karfin hali tace ita lafiyar ta qalau,haka ya kyaleta ya fita wurin aiki Aikuwa ya fita bada dadewa bah nakuda ta tasu mata gadan-gadan duk ta rasa yadda zatayi!!!!shima a wurin aiki ita kawai take fado mishi a rai dan haka ya tashi ya kama hanyar gida Baiwar Allah duk ta gama galabaita haka ya shigo ya sameta,ya salam!!! yace tare da daukan ta zuwa mota Sakata yayi a ciki ya kama hanyar asibiti da ita,suna zuwa aka wuce da ita labour room Ya kasa zaune ya kasa tsaye ya dauki waya ya fadawa Mum,itama a rikice tace mishi gatanan zuwa Kusan 30mins kenan da shigan su amma shiru basu fito bah har Mum ta karaso ita dasu fa'iza Dr.ne ya fito sukayi saurin karasawa tare da tambayan shi koh ta haihun "Congratulations!!! Ta samu twins mace da namiji,kuma duk lafiyan su qalau" Murna a wurin su ba'a cewa komai babu mah kamar Kamal,suna cikin haka aka fito da ita da babies dinta zaa wuce dasu dakin da zasu sami hutu Haka suma suka dunguma zuwa dakin sai faman sannu suke mata,meqa mata babies din Kamal yayi tare da cewa "Kinga abinda kika haifamin?babu abinda zan iya cemiki,amma dai nagode Allah ya miki albarka!!" Da ameen suka amsa sannan aka kira su Ummee mah aka sanar dasu Kaunan su daya a asibiti aka sallame su suka koma gida Ranar suna namijin yaci sunann Abban Hamdiyya wato umar faruq sannan macen tace sunan Mum din Kamal wato Halimah Murna a wurin Hamdiyya baya misaltuwa dama burinta inta haihu ta yiwa Abban ta takwara,haka aka gama hidimar suna lafiya aka watse Zainab mah ta haihu inda ta haifi yarta ta mace mai suna fiddausi *Bayan wata daya* Akayi auren Mubarak da Fa'iza anyi shagalin biki kamar babu gobe aka kai amarya dakinta. *End...* Alhamdulillah ina mika godia ta ga Allah(S W T)daya nunamin na gama littafin nan lafiya. Sannan kuma yan grp din *itace zabina* baza manta daku bah nagode sosai da soyayyar ku a gareni ana mugun tare!!! Yan gungiyar mu *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* koma bazan manta daku bah Allah ya kara muku basira ya daukako duniya da lahira. Bazan manta da kaibah *uncle muktar* na gode sosai da gudunmawar ka a gareni da karfafamin gwaiwa da kayi,I hrt u irin da yawa din nan Ina kike *Khadija Abba(idan rana ta fito)*kema bazan manta dake bah nagode sosai da soyayyar ki da kuma gudunmawar ki a akaina Haka kema *Hauwa Muhammad(slim small)* Allah ya barmu tare nagode da soyayyar ki bazan iya cewa komai bah!!! My cwt dota halima(chamo) Hajjo jamoh(Mrs barmono) Zahra(Mrs barmo) Mommyn zahra Munnira yuguda Mum mubeenah Hauly hydar Mancy Maman salma Samira Walilin baba Hajiya jamila Cwt mmn khalipha Hadiza sardauna(namcy) Cwt pinky Mmn usee. Koma duk bazan manta daku bah da kuma soyayyar ku a akaina da addu'ar ku ina matukar sonku!!! Kunada matukar yawa masoya duk da ban kira sunan ku bah ina matukar yin ku wallahi masu bina private masoya ina mika godiya ta a gareku. Tnx all 4 d luv nd care🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽.❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣ NA Khadeejah saleehu Dedicated to hauwa Muhammad (slim small) 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍ 8⃣9⃣➖9⃣0⃣ Bayan sun gama cin abincin sannan ya tashi yaje yayi wanka,bayan ya fito yace itama taje tayi wankan amma tace koh tayi bata da kayan dazata saka Daukan wayan shi yayi ya kira fa'iza akan ta kawo mata wasu kayan,sannan ita kuma ta tashi ta shiga wankan,fitowar ta yayi daidai da shigowar fa'iza Cikin murna fa'iza tayi kanta tare da cewa "Welcome back auntynah,wallahi nayi missing dinki sosai,ya jikin ki?" Dariya Hamdiyya tayi sannan tace "Naji sauki mana koh baki gani bane?kuma mah bakiyi missing dina bah nasani" Fa'iza zatayi magana kenan Kamal yace "Kee dan Allah ki kyaleta ta saka kaya kar sanyi ya kamata,kinzo kin cika mutane da surutu sannan kin wani dane ta salon ki kayar da ita" "Oooo Allah ya baka hakuri,auntynah sai kin fito koh?" "Toh nagode" Daga haka ta juya ta fita ita kuma ta saka kayan ta,bayan ta gama Kamal yace tazo su tafi!!kallon shi ta tsayayi sannan tace "Ina kuma zamu?nifah na gaji bacci nakeso nayi" "Gidan mu zamu koma mana!!!dama dan bakya nan ne yasa na dawo nan,in munje chan kyayi baccin" Ganin tanaso ta mishi musu yasa ya kama hannun ta suka nufi part din Mum,saida suka kusa shiga taga bashi da niyyar sake mata hannun haka yasa ta kwace hannun tare da cewa "Nufin ka haka zamu shiga?ka wani rike mun hannun kamar yarka" Murmushi yayi sannan yayi gaba itama ta bishi a baya,haka suka shiga suka samesu sunata hira gwanin ban sha'awa Suma zaman sukayi aka danyi hiran dasu,chan anjima Kamal yace su zasu tafi!!! Mum da Hajiya sukayi saurin hada baki da cewa "Ina kuma zaku tafi" Dariya suka bashi ganin yadda sukayi maganar kamar bada matarshi yace zai tafi bah,sannan yace "Gidan mu mana zamu koma,koh kuma dama mun dawo nan da zama ne?" Rike baki hajiya tayi tace "Yau ga ja'irin yaro,toh idan akace bazata bika bah fah?" "Ai kema kinsan bazai yiwu bah!!kindai fada ne" "Aaaaa sosai kuwa dole ka fadi haka tunda namaka mai wuyan ai" Mum tayi dariya sannan tace "Toh wai mah saurin me kakeyi?kabari mana sai gobe koh jibi sai ku tafi" Ganin yadda yayi da fuskar sa yasa Dad yace "Kai ku tafi abinku zaman me zasuyi anan din?ai gwara su koma gidan su kuma" "Yawwa Dad shiyasa nake sonka nagode" Tabe baki sukayi sannan Hajiya tace "Toh mukuma kace baka son mu shine zaka birgeni" Haka dai suka gama surutun su,suka fito raka su har bakin mota,sannan sukayi sallama su kuma suka kama hanyar gida Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin so da kaunar juna duk da akwai ranar daza ace wani yayiwa wani abunda baiji dadi bah,amma haka zasu bawa junan su hakuri su cigaba da zaman su ba tare da kowa yasan halin da suke ciki bah A wannan lokacin kuma Mum ta kira Kamal akan ya rubutu sakin dazaiyi wa Hafsat ita da kanta zata kaimusu,ai kuwa kamar jira yakeyi haka ya rubuta mata saki ukuu,Mum batace komai bah ta karba ta wuce gidan su Hafsa Lokacin dataje gidan ta samu baban Hafsa nata bala'i akan Hafsa ta koma gidan mijin ta inyasu inta Haifa masa cikin koh sakin tane yayi Muryar Mum sukaji tana cewa "Ai sun san cewa cikin bana Kamal bane shiyasa kaga basu ce zataje ta haife shi bah" Cikin razana suke kallon Mum,shi kuma baban Hafsa yace "Haba Hajiya wannan wacce irin maganar banza ce kikeyi?ban gane bah cikin Kamal bane,toh inba cikin shi bane na waye? " Ai su ya kamata kayiwa wannan tambayan nikam bansan na waye bah" Nan ta kwashe komai da ya faru ta fadamishi sannan tace kuma ya tambaye su intayi musu karya,sannan ta ciro takaddan saki ta mika musu Tambayan su ya shiga yi amma sun kasa bashi amsa sai uban kuka da sukeyi,nan yace Mum din Hafsa ta tashi ta bar mishi gidan shi dama ya gaji da halayen ta,ita kuma Hafsa tunda yar sace babu yadda zaiyi da ita,Idan ta haifi abinda yake cikinta dole ta mayar dashi wurin uban shi Haka Mum ta tashi ta tafi ta barsu,itama mummyn Hafsa ta tashi tabar gidan dan babu yadda zatayi ********* *Bayan wata takwas!!!* Cikin hamdiyya ya gama tsofa haihuwa koh yau koh gobe,kullum a cikin addu'a takeyi Allah ya kawo mata da sauki dan Maryam tace mata akwai wuya kasan cewar ita ta riga data haihu,ta haifi danta namiji mai suna *Aminu* Shi kuwa Kamal kullum cikin karfafa mata gwaiwa yakeyi tare da yimata duk wani abu datace tanaso Itama

Chapter 11 of 12