mata da miji kowa ma zai hakura,Ummee tace toh Allah yasa albarka,da Ameen Abba ya amsawa.
Tana shiga daki ta shiga toilet tayi alwala sannan ta dauki wayarta ta kira kamal,fadamishi abinda abbanta yace tayi.dadi yakeji kamar ance an bashi ita sannan yace nagode sosai my dear nasan insha Allah kin zama tawa ta har abada,and den inaso kimin alkawarin zama dani a cikin dadi koh kuma akasin haka...hamdiyya tace nayi maka nima kamin hakan!!!cikin jin dadi yace tin ranar dana fara ganin ki nayiwa kaina wannan alkawarin,yanzu dai ki kaunta kiyi bacci sosai naji bash yace gobe ne zakuyi kamu ne koh me?dariya tayi tace eh haka ne toh sai da safe!!kamal yace toh shekenan nima zanzo goben na ganki,zare ido tayi tace a'a fah banda maza!!dariya yayi yace ni bance zan shiga cikin ku bah wurin ki kawai nace zanzo kuma zanzo,gud nyt!!bai jira mai zatace bah ya kashe wayar, murmushi tayi sannan tayi addu'a ta juya ta kaunta.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
HBD dear luv Hauwa Muhammad (slim small) age wit grace Allah ya rayaki musha biki chilled is ur day.....!!!!
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
4⃣3⃣➖4⃣4⃣
A yau ne da misalin karfe 1:30pm aka shaida dauren auren *Maryam saleem*da kuma *bashir Abbas* wanda yasamu damar halarta mutane masu yawan gaske,anyi dauren aure har mutane sun fara wastewa.a cikin gida kuwa kawaye sai tsokanan maryam akeyi ita kuwa hamdiyya cewa takeyi su bari dan ita gaba daya tausayin Maryam din takeji a cewar ta haka kurum mutum na zaune a gidansu wani yazo ya raba shi da iyayen shi waishi ya aure ta!!!
Mum ce a zaune a kan kujera inda kamal ke zaune a kasa ta gefen ta,cikin muryar rashin wasa take cewa kamal ka zabi wacce kakeso ka aura koh?toh ina mai sake jaddada maka niba ita nakeso bah hafsa *itace zabina* amma tunda kai kace ga yadda kakeso ba damuwa amma kuma kasani bazan taba karbar ta a matsayin surukata bah har abada kuma ka fadamata cewa karta yadda ta dauke ni a matsayin suraka koh kuma tasa a ranta wai zataji dadin zama dani idan ta shirya zama cikin kunci toh bismillah zata iya shigowa ka tashi ka bani wuri,tashi yayi jikin sa a sanyaye yayi hanyar fita har ya kai kofar fita ta kira sunan shi!!!amsawa yayi ya dawo ya zauna,sannan tace bashir yace kawar matar da ya aura ne koh?daga kanshi yayi yace eh!!sannan tace meye sunan ta?shiru yayi yana tunanin me kuma zatayi da sunan ta,cewa tayi ba dakai nake magana bah?cikin sanyin murya yace sunan ta hamdiyya Dan Allah mum......bai karasa bah ta dakatar dashi ta cewa ka tafi abinda na tambayeka kenan,haka dai ya tashi ya fita yana nazarin mai mum za tayi da sunan hamdiyya.
Tun bayan sallar magrib sauke shirye- shiye na zuwa wurin dinner,bayan sallar isha'i mai makeup tazo ta musu kwalliya ta kece raini sunyi mutukar kyau ba kadan bah,haka lkcn lafiya yayi mutane suka fara fita ana tafiya wurin dinner.tare suka fito su uku Maryam, zainab,hamdiyya, Zainab da Maryam ne suka shiga motar daya!! zainab na cewa nasan ke chewing gum dinki yananan yana jiranki!!!dariya tayi tace ai kinsani kuje dai sai mun hadu da haka ta rufe musu kofar motar ta nufi wurin motar kamal.ya jingina da jinkin kujera kamar wani mai bacci haka ta shiga cikin motar da sallama,dagowa yayi yana kallon ta ba karamin kyau tamishi bah ya kasa daina kallon ta gaba daya,hade rai tayi tace kallon fah?murmushi yayi yace gaskia ni ban yadda da wannan kwalliyar bah tayi yawa ynxu in munje nasan ido zai dawo kanki,dariya tayi tace nidai mu tafi Dan Allah yanzu ma sai da zainab tamin sharri!!tada motar yayi yana cewa kinyi kyau sosai my dear,murmushi tayi tace tnx.suka Kama hanyar tafiya,ba kamar kullum bah ta saba in suna tafiya sunayi suna hira amma yau bah haka bane,cewa tayi meke damunka yau?kallon ta yayi sannan ya maida duban sa kan driving din da yake yi sannan yace babu komai me kika gani?hmm tace sannan kuma tace kaidai kawai kace bazaka fadamin bah amma I'm sure sumtin is wrong,parking yayi gefen titi sannan ya kalle ta yana cewa hamdiyya pls kimin alkawarin bazaki rabo dani bah zaki zauna dani har abada!!murmushi tayi tace ai mun riga da munyi wannan alkawarin tin ranar koh?shaqwabe fuska yayi yace eh munyi amma mu sakeyi,dariya sosai tayi tace toh nayi maka shekenan dai koh?daga kanshi yayi yace eh shekenan nima nayi miki,toh mu tafi!!sai yaji yadan samu relief haka suka bar wurin suka wuce wurin dinner.
Bayan yayi parking koma wa yayi ya zauna bashi da alamar fita,a'a kai bazaka shiga bane?dagowa yayi yace nidai shiga zan shigo dan banason naga wani yana kallon ki in kin shiga zan shiga,dariya tayi tace toh shekenan sai ka shigo daga haka ta shiga cikin wurin.ai kuwa nan take kallo ya koma kanta da kyar ta karasa saboda kallon da mutane ke mata,Ummee ta hango hakan yasa ta karasa wurin ta rungume ta tayi ta baya tana cewa I Miss you Ummee jiya ban ganki bah!!kedai koh a ina saikin nuna halinki,zagayowa tayi tana toro baki Ummee bakiyi missing dina bah koh?muryar ya Mubarak taji yana cewa sosai kuwa munyi missing dinki!!juwuya tayi da sauri ta reko hannun tana cewa nima nayi missing dinku sosai, ina yaya Sadeeq hope dai yazo?kafin su bata amsa sukaji MC na cewa hamdiyya ta fito pls zata bamu biography na Amarya.kowa a wurin ya koma kallon ta ina zata fito haka mum din kamal da ta samu halarta wurin!!cikin nutsuwa take tafiya haka ta isaa wurin MC ta ansa mic din a hannun shi ta fara magana cikin harshen turanchi cike da kwarewa,haka ta gama ta mika mic din ta koma wurin ummen ta ta zauna,haka bikin ya cigaba da gudana cikin jin dadi da nishadi suna cikin yin hotona da kawayen su taji wata ta dafata jiyowa tayi wacce ta dafatan tace kece hamdiyya koh?daga kai tayi tace eh nice!!!tace toh wata mata na waje wai kizo tanason ganin ki,toh tace muje koh daga haka suka fita.
A cikin motar suka sameta tana zaune,cikin ladabi hamdiyya tace ina wuni amsawa tayi a daqile da lafiya!!ganin irin kallo da taga tana mata yasa tace dama cewa akayi kina kirana,koh kinason wani abun ne?fitowa tayi daga motar tana qare Mata kallo sannan tace eh nasan baki sanni bah toh nice mahaifiyar kamal!!!kara sunkuyar da kanta tayi,mum tace a'a ki dago kanki dan ni bah surukarki bace dan ni bake nakeso dana ya aura bah!!in kinason zaman lafiya da kwanciyar hankali toh ki fita a harkar dana dan bake zai aura bah nayi mishi mata,ina ganin sanda keda mahaifiyar ki da Dan uwanki suke nuna miki qauna!!toh banason ki auri kamal wannan farin cikin ya gushi dan muddin kika aure shi keda farin ciki har abada kindai ji na fadamaki ki wuce ki bani wuri.
ummee ce ta hango ta tsaye karasawa tayi ta dafata tana cewa meya sameki?dagowa tayi da jajayen idonta ta rungume Ummee tana cewa muje gida Ummee kirjina nah ciwo,dago ta tayi tace kai hamdiyya shine nayin haka nasan tunda aka fara bikin nan bakya cin abinci shiyasa yanzu haka ulcer dinki keson tashi!!toh barinje na kira Mubarak ya maidamu da haka ta daga ta wuce kiran Mubarak.
Tin da mutane suka fara watsewa yake duba inda zai ganta amma bai ganta bah kuma yata kiran number ta bata dauka bah daga baya mah ta kashe wayar,bash ne ya karaso wurin shi yana cewa meya faru kuma? Numfashi ya sauke yana cewa banga hamdiyya bah kuma nata kiranta bata picking bah yanzu ma wayar a kashe ne!!!toh inaga ta tafi ne kazo muje nasan in taga missed Call dinka zata kira,tashi yayi yana cewa haka zata tafi bata fadamin bah bayan tasan ni zan maida ita?nidai Jiki nah na bani akwai wani abun,dafashi bash yayi yace bakomai insha Allah mu tafi,daga haka suka tafi zuciyar shi na saqa mishi akwai wani abun daya faru.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to Hauwa Muhammad (slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
5⃣1⃣➖5⃣2⃣
*bayan sati daya*
Haka dai soyayyar su ta cigaba da gudana amma a dayan bangaren hamdiyya gaba daya inta tuna abunda mum din kamal ta fadamata sai taji kamar ta hakura da kamal din gaba daya,mafi yawanchin lokota Ummee ce ke bata kwarin gwaiwa tana cemata karta damu insha Allah babu matsalar da zata sameta ta daiyi qoqarin kyauta tawa mum din kamal ta zauna da ita a matsayin mahaifiyar ta intayi haka komai zai wuce.shima kuma hakan ne a bangaren kamal kullum koh gaishe da mum din yayi da kyar take amsawa kuma kullum sai ta maimaita mishi maganar saifa ya auri hafsa koh yanaso koh baya so,dad din shi dasu Jamal ne ke kwantar mishi da hankali a koda yaushe.
A yau ne kuma dad din kamal suka kawo sadakin hamdiyya,shima kuma Abba zuwa gobe ne zasu kai sadakin auren zainab da yaya Sadeeq dan tuni shima anje an tambayan mishi auren zainab kuma anbashi yanzu dai sai shirye-shiryen biki kawai tinda su dad din kamal sun nema alfarma nan da 3wks suke so ayi auren hakan ne yasa suma su Abba suka nema alfarmar mahaifin zainab yasa musu rana daya da auren hamdiyya amma yace musu suyi hakuri amma sai nan da wata biyu Dan akwai tafiyar da zaiyi,badan sunso bah haka suka hakura akan sai nan da wata biyun.
Gaba dayan su zaune suke a parlour kamar kullum suna hira,Mubarak yace Allah sarki sis yanzu fah nan da 3wks bakya gidan nan kina chan gidan mijinki koh?ya karashe maganar da sigar zolaya.take a wurin idon ta ya fara ciko qwalla tama kasa cemishi komai,Abba ne daya gane so takeyi tayi kuka yayj saurin cewa Mubarak banason wulaqanchi ai bautar Allah zataje ba wani abun bah kuma a gari daya muke da ita duk sanda taji kewar mu zatazo ta ganmu,muma kuma duk sanda mukaji kewar ta zamuje mu ganta koh bah haka bah mama nah?daga kanta tayi tace haka me Abba nah kana jin yadda take maganar kasan kuka ne keso ya kufce mata,shima kuma Mubarak fin duk sai yaji babu dadi yaji dama bai fadamata haka bah dan tausayin ta yake ji yasan sun saba da ita sosai komai tare sukeyi sunayi suna fada shi kanshi yasan zaiyi missing dinta sosai ba kadan bah,sai kuma yace ehmna ni koh baki zo bah ma ni dakaina zqn dinga zuwa miki kinji koh? wasa nake miki,ji tayi zuciyarta ta sanyi tace da gaske kakeyi?ya Mubarak yace da gaske mana,tashi tayi ya zauna kusa dashi ta miki mishi hannu,ya gane me take nufi hakan yasa shima ya bata hannun nashi yace I promise!!!shima yaya Sadeeq ya tasu yazo ya daura hannun shi akan nasu yace nima I promise zan dinga zuwa miki koda sau daya ne a shekara,dariya su dukka sukayi sannan suka cigaba da yin hirar su cike da nishadi.
Lokacin data shigo dakin kaya ta chanza sannan ta shiga bayan gida kamar kullum tayi alwala ta fito tazo ta kaunta sai kuma ta tuna da wayarta akan mirror, tashi tayi zuwa dauko ta a zuciyar ta kuma tana cewa nasan kamal ya ta kira yau zan shaa mita,ai kuwa kamar tasani 5missed call's tagani na kamal sai kuma 3missed call's na mas'ud.gadon ta koma ta kaunta tayi dialing number kamal yana fara ringing ya picking call din bata bari ya fara magana bah ta riga shi farawa da cewa kayi hakuri na bar wayan a dakin ne I'm sorry!!!dariya ta bashi sannan yace wato kinsan kinyi laifi koh?nace miki kidinga ajiye wayar a kusa dake koda yaushe a koh wani lokaci danni zuciya ta kawai nake yi amma da duk bayan 10mins zaki dinga ganin kira nah!!!!itama dariyar tayi tace toh naji amun afuwa zan gyara,da haka dai suka dan taba hira sannan sukayi sallama amma badan yaso bah dan shi koh kauna zasuyi suna magana bai damu bah.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA ❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to Hauwa Muhammad (slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
4⃣1⃣➖4⃣2⃣
A yau ne za'a tambaya wa kamal auren hamdiyya!!!karfe 12:20pm su dad din kamal sukayi parking a cikin gidan su hamdiyya,part din da'ake sauke baqi anan aka sauke su.anyi musu tarba mai kyau bayan sun gama gaisawa suka farayin magana akan abunda ya tarasu a wurin,dad ya nemawa kamal auren hamdiyya kuma Abba ya bashi dan tunda ya ganshi yaji zuciyar shi ta nutsu dashi duk da baisan kamal bah amma jikin sa yana bashi insha Allah mutumin kirki ne.anan dad yake cewa abba suna rokon alfarman cewa basaso auren ya wuce nan da wata daya in babu damuwa!!!Abba ya aminche da batun nasu kuma sunji dadi da hakan,a haka dai suka tashi suka ce zasu wuce sosai kowa yaji dadin haduwa da kawo haka dai suka fita akan nan da wani satin za'a kawo su sadaki, Abba har wurin motar su da sukayi parking ya rakasu saida suka tafi sannan ya shiga cikin gida.
Hakan ne ma yau zasuyi walima yadda suka tsara,shiga ta kamala sukayi sukaje wurin walimar still dai kamal nanan a manne da hamdiyya duk wani motsi da zatayi akan idon shine yaqi yarda ta hau motar kowa a cewar shi yanada kishin da bazai bari ta hau motar wani bah,shidai bash sai tsiya yake mishi amma hakan bai dame shi bah koh kadan!!!haka aka gama walima malamai kala-kala sunzo sunyi wa'azi mai ratsa jiki bama Amarya kawai bah harda sauran jama'a,sai gab da magrib aka tashi a wurin walimar saboda sai bayan la'asar aka fara.kamal a mota yake cewa hamdiyya nasan yanzu an riga an bani ke insha Allah kin zama tawa har abada sauri ma nakeyi na koma gida naji abinda dad zai fadamin,murmushi tayi tace in kuma akace ba'a baka ni bah fah?anbawa wani!!wani wawan birki ya taka saida ta tsorata kallon shi tayi taga har idon shi ya chanza kala.wani kallo yake mata dayasa ta sauke idonta daga kallon da take mishi,dakyar ya iya cewa Dan Allah karki sakemin irin wannan mugun fatan na rasaki,Dan Allah kinji koh?kallon shi tayi tace nifa wasa nakeyi bah fata nake maka bah,nidai kice bazaki sake bah koh ma miye,kama kunnen ta tayi tace toh bazan sake bah I'm sorry!!! Dariya yayi yace yawwa koh kefah da haka suka bar wurin yau dinma a gidan su maryam ya sauke ta dan Maryam taqi yadda su tafi gida wai sai angama biki.
Kowa na gidan na zaune a cikin parlour'n hajiya,dad ne yayi gyaran murya yana cewa toh alhmdll yau munje nida su uncle majeed nemawa kamal auren wacce yakeso kuma alhmdll anyi mana tarba cikin mutunchi da girmamawa bugu da kari mahaifinta yabamu auren ta nan da wata daya insha Allah za'ayi auren saboda haka mun ajiye nan da wani sati za'a kai sadaki insha Allah.wani irin dadi yaji ya mamaye zuciyar shi,hajiya ce tace alhmdll burina ya kusan cika Allah ubangija yasa albarka ya kuma sa ayi damu!!!Ameen sukace fa'iza tace wooow muma mun kusa muyi biki a gidan mu!!!Jamal yace ai ke dama babu wani Abu dake ranki sai biki,turo baki yayi tace eh din!!!mum ce ta tashi tsaye tana cewa toh yayi kyau tunda ka nuna mishi ban isa dashi bah,amma inaso kasani yadda kaje ka nema mishi auren wacce yake so haka zakaje ka nema mishi auren wacce ni nakeso kuma wallahi kunji na ranste sai kamal ya aure hafsa koh kuna so koh bakwa so saidai kuma in zai chanza wata uwar in yace bazai auri hafsa amma dai bani bah bata jira mai zasu ce bah tayi ficewar ta.girgiza kai dad yayi sannan yace karka damu kamal ai kai namiji ne kuma Mijin mata hadu saboda haka tunda ga abinda mahiafiyar ka tace kaima kuma kasami wacce kakeso yanzu addu'a zamuyi Allah ya tabbatar mana da alkhairi.hajiya tace eh lalle kam abun ya girma Allah dai ya kyauta suka amsa da Ameen kowa ya tashi ya kama gaban sa.
Da daddare a parlour Abba yake fadawa su Ummee yadda sukayi da iyayen kamal,mubarak yace wato sis tasami Wanda take so shine koh ta fadamin koh?yaya Sadeeq yayi dariya sannan yace ina kuwa zata fadamaka bayan tasan zaka saka ta a gabane,ai yanzu ma bata tsira bah zata dawo ta sameni ne.Ummee ce tace kaga mubarak banason tsiya karka sa ta farayin kuka tun yanzu dan kasan halinta,nan ma dariya yayi yace toh shekenan.yaya Sadeeq yanaso yayi magana amma kuma ya kasa Abba ya lura da hakan,cewa yayi Sadeeq kamar kanason kace wani abun koh?cewa yayi cikin in-ina dama nima so nake aje a tambaya min auren,Abba yace auren wa za'a tambaya maka?Zainab yace frnd din hamdiyya!!! Ummee tace eh lalle da kyau dama nasan za'a rina ai kallon ka kawai nakeyi ai,dariya sukayi ya Mubarak yace nima baza'a barni a gida ba kowa nima zan fito da mata,Abba yace eh gaskia kam Allah y muku albarka gaba ki dayan ku kai kuma Sadeeq sai ka fadamata ta fadawa iyayen ta su saka mana ranar da zamuje koh?da toh ya amsa sannan kowa ya tashi ya shiga dakin sa.
Juyi kawai yakeyi akan gado dan gaba daya ya kasayin baccin,maganar mum dinshi ce kawai take mishi yawo a qwaqwalwar shi,shi kanshi yasan baya son hafsa kuma bashi da aqidar hada mata biyu a rayuwar shi kuma mah wai hamdiyya za'a ce ya hada da hafsa.kamar yana magana da wani cewa yake pls mum ki gane cewa hamdiyya *itace zabina* mana,da ita nakeso nayi rayuwata cikin jin dadi da kwanciyar hankali!!bana son hafsa ban taba son ta bah koh da na aure ta bazan iya mata as all hi bah wallahi kamar ya zauto haka yayi ta magana shi kadai har bacci ya dauke shi.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated dis page 2 ur hajjoh jamoh suraka a wurin barmo Allah ya bar kauna....!!!!
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
4⃣5⃣➖4⃣6⃣
Tunda suka koma gida babu abunda takeyi inbanda kuka,Ummee har ta gaji da tambayan ta meya sameta haka ma yaya Mubarak yayi tambayan har ya gaji ita dai kawai tace musu qirjinta ke mata ciwo kuma gashi ta kasa cin komai.Ummee ce ta shigo cikin dakin ta karasa ta zauna gefen gado kusa da hamdiyya,dago ta tayi sannan tace yaushe kika fara boyemun abinda ke daminki nasani koh da qirjin ki na ciwo amma akwai abinda ke daminki bayan wannan saboda haka ki fadamin,in kuma kinada wani sirrin da kike gani bai kamata ace nasani bah toh zaki iya boyewa a ranki daga haka ta maida ita ta kauntar da ita sannan ta tashi zata tafi.riko hannun ta tayi ta sake fashewa da wani sabon kukan cikin muryar kuka take cewa zan fada miki Ummee nah babu abinda zan iya boye miki,komawa tayi ta zauna sannan tace inajinki?tashi tayi ta zauna sannan ta fadamata yadda sukayi da mum din kamal.shiru Ummee tayi na dan wani lokaci sannan ta reko hannun hamdiyya tace abinda nakeso dake shine kiyi hakuri kuma ki dage da addu'a Allah ya zabamiki abinda zai zama alkhairi a gareki amma bah wai ki zauna anan kiyi ta kuka bah nima kuma zan tayaki da addu'a kinji koh?amma ni nasan koh da ita batason auren mahaifin shi naso kuma shima yanaso tunda har mahaifin shi yazo ya nema auren ki kuma abban ki ya bashi!!!dagowa tayi da sauri tana kallon Ummee sannan tace Ummee ni bazan auri Wanda mahaifiyar shi bata sona bah ki fadawa Abba ya basu hakuri nima hakura dashi wallahi ta karashe maganar tana kuka,shaafa kanta Ummee tayi sannan tace kar kice haka 'yata na fadamiki ki nema zabi a wurin Allah ki kai mishi kukan ki zai jibinci lamuranki maganar ace musu an fasa basu auren ki bai taso bah tukun kedai kiyi addu'ar dana cemiki kinji koh?daga kanta tayi tace toh naji Ummee daga haka Ummee ta tashi tace mata bari taje ta hado mata tea tasha.
Kasa bacci yayi yanata faman gwada wayar ta amma taqi shiga gashi yanata kiran bash shima kuma bai dauka bah balle yace mishi yasa Maryam ta kira koh da Ummee ne suji koh lafiya.hka ma su Maryam da basu ga ta dawo bah sun ta nemam number ta amma a kashe sai chan Maryam tacewa Zainab yauwa Xee ki kira yaya Sadeeq kiji mana koh gida ta koma pls!!!sanda zee ta kira yaya Sadeeq shi kuma har ya kaunta saboda haka bai maji kiran nata bah kuma shi bai san hamdiyya mah na gida bah don a zatonshi yau dinma tana gidan su Maryam!!!haka dai suma suka hakura akan gobe sai zainab taje gidan nasu tagani amma bah hka suka so bah dan gaba daya hankalin su bai kaunta bah yanzun ma dan sunga dare yayi ne shiyasa suka hakura da sunje gidan.
*Washe gari*
Da asuba da kyar ta iya tashi taje tayi alwala sannan tazo tayi sallar da kyar dan bah karamin ciwo qirjinta yake mata bah bayan ta idar da sallar kasa tashi tayi akan sallayar tata haka ta duqunqune acikin hijab dinta nan take wani zazzabi mai zafin gaske ya kamata jikin ta yayi zafi sosai sai rawar sanyi takeyi.da misalin karfe 7:00am Ummee ta shigo cikin dakin nata a haka dai tazo ta sameta dai faman rawar sunyi takeyi da sauri ta karasa wurin ta tana kiran sunan ta dago ta tayi tana cewa wai jikin ne haka barinje na kira Sadeeq yazo muje asibiti daga haka ta fita kiran Mubarak yazo suka dauke ta suka wuce da ita garkuwa hospital dake garin Kaduna.
Yana tashi koh zuwa gaida su mum baiyi bah yayi wanka ya shirya sannan ya dauki car key dinshi, motar shi ya shiga kai tsaye gidan su bash ya nufa.part din bash din ya shiga ya tarar da bash ya fito daga wanka wuri ya samu ya zauna,da mamaki bash ke kallon shi sannan yace lafiya kamal yana ganka haka?wane irin lafiya Dan iskanci tin jiya nake ta faman kiran ka kaqi ka dauka and den har yanzu maganar nan danake maka wayar hamdiyya yaqi shiga kai kuma kaqi ka picking call dina nace maka kasa Maryam ta kira koh da Ummee ne taji.zama yayi yace wallahi kamal suma sunta neman number ta a kashe shiyasa ma jiyan ban dauki wayar ka bah dan bansan me kuma zance maka bah gashi yanzu is too early muce zamuje gidan su.nikam babu wani wuri dayamun dan yanzu chan zan wuce dan gaskia jiki nah nabani akwai wani abun basai ka rakani bah zanje ni kadai dan nasan kanada mutane da zaka sallama yau daga haka ya tashi ya fita zuwa gidan su hamdiyya.
A kofar gida ya tarar da zainab suna magana da baba haruna mai gadi,karasawa yayi ya fito suka gaisa sannan yake tambayan zainab koh lafiya?cemishi tayi nima yanzu nazo baba Haruna yake fadamin wai hamdiyya ce bata da lafiya an wuce da ita asibiti!!!cikin rudewa yake cewa baba Haruna meya sameta? wanne asibitin aka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 12