ya fita.
Bayan ta shirya ta sauko akan dinning ta samesu dukka,gaishe su tayi suka amsa sannan taja kujera itama ta serving kanta ta fara cin abincin cikin nutsuwa.Ummee ce tace wai nikam hamdiyya meye naki nasaka bakar riga ne?cewa tayi Ummee saboda lallen da zamuje ne yasa banason saka wasu kayan karsu baci!!ya mubarak yace yau ma fitan za'ayi kenan?Allah dai ya shiryeku,hamdiyya koh kula shi batayi bah sai cigaba da cin abincinta tayi.yaya Sadeeq yace yau sis hala bakya jin yin magana ne? naji baki tanka bah,hamdiyya tace kamar kasani yau banson surutu shiyasa na kyaleshi amma yaci bashi kuma sai ya biya!!dariya sukayi haka suka gama cin abinci kamar kullum hamdiyya ce ta raka abban nata har mota sai da ya tafi sannan ta shiga ta shiga cikin gidan,suma su yaya Sadeeq kowa ya kama gabansa sai ita da Ummee dake zaune a parlour.
Suna fita gidan su maryam sukaje bash ya kirata a waya yace ta fito su tafi.daga nan kuma sai gidan su hamdiyya,Maryam ce ta shiga dan ta kirata su tafi !!!A parlour ta samesu hamdiyya ta daura kanta akan cinyan Ummee,da sallama ta shiga ta gaishe da Ummee sannan tacewa hamdiyya wai ke sai yaushe zakisan kin girma ne?kullum kidinga danewa Ummee kafa,Ummee tace fadamata dai maryamu!!!harararta hamdiyya tayi tace bansani bah yar sa ido kawai,dariya maryam tayi tace toh sai ki tashi mu tafi dan zainab tacemun tana chan.hamdiyya tace oooo zainab batayin african tym daga haka ta tashi suka wa Ummee sallama Ummee tace toh a dawo lafiya suka ce Ameen sannan suka fita.
Cikin motar suka shiga hamdiyya tace ango ka kasha kamshi gud mrng bash yayi dariya sannan yace kema ai zaki sha kamshin ne nan bada dadewa bah insha Allah!!murmushi tayi bata tanka mishi bah tacewa kamal abokin ango ina kauna kamal yace saida kika fara gaishe shi sannan zaki kulani?bash yace yau kujimin mutumin nan,maryam ce tace nidai Dan Allah mu tafi dan nasan yanzu zainab ta gama kulewa zamusha harara, hamdiyya tace zamusha kam!!daga kaga bash yaja motar suka bar compound din gidan suka kama hanya zuwa wurin mai lalle.
Suna tafe suna dan yin hira kadan -kadan har suka isa Koh da sukaje har anfara yiwa zainab,hamdiyya tace Aunty zee tun kafin a yiwa amaryar ke har anfara miki?Zainab tace toh zamu ta jiranku ne?bash yayi dariya yace a'a hajiya zainab gwara da aka fara yimiki,zainab tace yauwa ango Ashe ka gane.bash ne yace toh in angama muku zamuzo mu dauke ku,toh suka ce sannan suka tafi su kuma suka zauna.
maryam tace hamdiyya I need more explanation!! Hamdiyya tace 4 wat?maryam tace naji kina cewa zainab aunty ne yau,dariya tayi tace toh ba dole na bah tunda yaya sadeeq yace ita yakeso.maryam tace ke dan Allah da gaske?hamdiyya tace wallahi da gaske jiya yake fadamin wai in mishi campaign,zainab pls ki aminche mishi wallahi da gaske yakeyi.harararta zainab tayi yace shi baida baki ne?sai kece zaki fadamin,hamdiyya tace toooh fah kiyi hakuri dama sharar fage nakeyi masa zan bashi number ki anjima zai kiraki,maryam tace woow gaskia naji dadi kunga nasan kusan tare za'ayi auren ku kenan.Zainab tace me kike nufi?nan Maryam ta fadamata ai kamal nason hamdiyya kuma da gaske yakeyi Zainab tace hope dai kin aminche?Dan guy din ya hadu kuma nasan halinki da iskanci,maryam tayi dariya sannan tace ai da gudu wannan karon ta aminche dariya sukayi dukkan su haka dai aka cigaba da musu lallen sunayi suna hira.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to hauwa Muhammad (slim small)
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
3⃣5⃣➖3⃣6⃣
Bayan sun tafi a mota bash yake cewa kamal yane naga kayi shiru?numfashi kamal ya sauqe sannan yace mum fushi takeyi dani fah gaisuwa tama da kyar take amsawa all cos of dat stupid gurl!!bash yace nifah abinda nake tsoro kar ayi auren nan mum bataso nasan hamdiyya bazata taba jin dadin zaman bah wallahi, kamal yace bash hamdiyya *ITACE ZABINA* so babu abunda zai hanata jin dadin zama dani saboda ina sonta!!bash yace kamal bazaka gane bane amma indai mum bataso toh duk son dazaka nunawa hamdiyya ragagge ne amma ina fatan Allah yasa mum ta hakura,ameen kamal yace sai kuma yace kasan wai har tana cewa koh na aure wacce nakeso sai na aure Hafsa nd u knw dat banida niyyar yin mata biyu shine ma babban dalilin da yasaka nakeson auren wacce nakeso!!!bash yace tab ashe akwai aiki kuwa yanxu dai kawai ka dage da addu'a komai zaizo da sauki insha Allah!!!amma ka fadamata abinda dad yace?eh na fadamata tace zata yiwa Ummee magana sannan ta fadamin yadda sukayi, bash yace toh yayi kyau amma koh da wasa kar hamdiyya tasan cewa mum dinka akwai wacce takeso ka aura dan ni nasan za'a samu matsala dan zaiyi wuya ta aminche,kamal yace bazata sani bah insha Allah!!!!komai zaiyi daidai,bash yace toh Allah yasa.
Lalle mai dan karen kyau aka musu baka gane wacece amaryar a cikin su saboda kowa nata yayi kyau dama shagon har saloon sukeyi zainab tace gwara fah muyi saloon din nan yau tunda akwai sauran tym dan goben nan zai mana wuya hamdiyya tace gaskia kam gwara muyi yau din,haka dai suka yanke shawarar yin saloon din akayi musu.wayar hamdiyya ce ta fara ringing ganin yaya Sadeeq ne yasa tayi dariya ta picking call tana cewa cwt bross ya akayi?daga dayan bangaren ya Sadeeq yace I hope dai kin isar da saqo nah koh?dariya tayi tace na isar babban yaya amma tace ai kana da baki mai yasa baka fada da kanka bah?shema dariyar yayi yace yanzu kona Ina? Fadamishi inda suke tayi sannan yace toh mata zanzo na dauke ta na kaita gida saina fadamata tunda inada bakin!!!hamdiyya tace toh angama sai kazo daga haka suka kashe wayar.
Kallon zainab tayi tace yaya Sadeeq yace zaizo ya dauke ki!!zainab tace shi ya kawo ni da zaizo dauka nah?hamdiyya tace kai ni har na fara jin tausayin yaya nah wallahi wannan masifar take gashi shi kuma baida hayani,Maryam tayi dariya tace bawan Allah bah ai sai tasa ya koya masifar shima!!zainab bata Kai ga amsa musu bah wayar Maryam ta fara ringing call din tayi picking daga dayan bangaren bash yace Amarya kun gama ne?maryam tace eh mun kusa zaku iya tahuwa inbaku da nisa daganan kamin kuzo mun gama,bash yace toh kamal yace wai shi zaizo ya dauki hamdiyya bazata shiga mota ta bah!!dariya Maryam tayi tace lalle kamal toh shekenan sai dai kunzo daga haka suka kashe wayar.
Maryam tace hamdiyya kinji mutumin ki wai shi zaizo daukan ki,hamdiyya tace ke nifah ku xanbi gwara ma yazo tare da bash din dan yagi mishi.maryam tace kedai kika sani in yazo kice bazaki bishi bah!!!kiran wayarta yaya Sadeeq yayi yace mata gashi nan yazo tace toh gasunan fitowa,hamdiyya tacewa zainab aunty nah ga yaya nah yazo kizo ku tafi!!dariya maryam tasa sannan tace kai su zee ansamu matsayin aunty,hamdiyya tace wai Maryam ina ruwanki ne?Maryam cikin dariya tace a'a babu ruwa nah muje.ita dai zainab wannan karon bata ce musu komai bah suka fita a cikin motar suka sameshi yana ganin su ya fito karasawa sukayi cikin dariya hamdiyya tace toh bross gatanan Allah ya kiyaye hanya!!!shima dariyar yayi yace ameen ku ba yanzu zaku tafin bane?hamdiyya tace waa ai kuyi tafiyar ku karmu hanaku yin soyayya yadda ya dace bashir zaizo ya dauke mu,harara Zainab ta watsa Mata amma tayi kamar bata ganta bah ta cigaba da dariyar ta dama ta gefen yaya Sadeeq din take,yaya Sadeeq yace lil sis zaki fara koh?kama kunnen ta tayi tace afuwan!!sannan ta bude mishi murfin motar ta kama hannun shi tace toh ku tafi dan auntyn nawa ta matso ku tafi,girgiza kai kawai yayi sannan ya shiga motar nan ma zainab harararta tayi,hamdiyya tayi dariya tace ki shiga kuma banda tsiwa dan nasan ki,shiga motar tayi ba tare data kula hamdiyya bah yaya Sadeeq yaja motar suka bar wurin.
Duk yana kallon su tun da suka fito yana tsaye a jikin motar shi ya nade hanun shi yana kallon yadda take murmushi cikin ranshi yace Allah yasa wannan farin cikin naki ya daure har abada,sannan mum dina tayi accepting naki as her daughter in-law!!!amma kuma ganin har rike hannun yaya Sadeeq tayi kuma sai ya samu kanshi ajin wani irin haushi kuma a lokaci daya yake tambayan kanshi da wanene wannan da har take mishi fara'a haka?Maryam ce tace kee hamdiyya gafa mutumin ki chan fah a tsaye!nda maryam din take mata nuni dashi ta kalla,cikin kananun kaya yakee yanzu da alama yaje gida ya chanxa ya mata kyau sosai suna hada ido tayi saurin sauke kanta sannan suka karasa wurin shi.suna zuwa bash shima yana karasowa fitowa yayi sannan yace finally har ka rigani zuwa!!dariya maryam tayi tace gashi nan kana gani,shidai kamal baice komai bah haka itama hamdiyya!!sai bash ne yace toh let's get going hamdiyya pls kije kamal ya sauke ki dan yace bazaki hau motata bah!murmushi tayi ba tace komai ba sai kuma tacewa Maryam toh sai goben da safe zanzo ki gaida mama,Maryam tace toh Allah ya kaimu daga haka kowa ya shiga mota suka kama hanya.
Har suka bar wajen bai cemata komai bah itama kuma bata cemishi bah a cikin zuciyar ta kuma tace lalle mutumin nan dan rainin wayo ne,toh meyasa maa yace zai maidani gida?yasan ba zaiyi magana bah!!!tana cikin tunanin nan taji yayi parking a gefen titi da sauri ta dago kanta tana kallon shi,shima kallon nata yayi sai kuma ta sauke kanta.cikin wata irin murya mai kashe jiki yace wanene shi?kallon shi tayi sannan tace who?Dan ita tama mantaa wai yaya Sadeeq yazo,kamal yace wanda kike tayiwa fara'a harda kama hannun shi.cikin ranta tace ooo shiyasa yake ta wani shan magani lalle kuwa yanada aiki,ta zata acikin ranta ta fada ashe a fili ne sai ji tayi yace sosai kuwa inada aiki dan inada kishin abunda nakeso!!!daga kanta tayi tace yaya nah ne fah yazo daukan zainab ne.sai yanzu ya danji dadi sai kuma yace amma ranan bashi nagani bah,hamdiyya tace eh shi lokacin bayanan.ajiyar zuciya ya sauke sannan ya yiwa motar key suka kama hanya yanzu ya daina fushi ya fara mata hira.
Har cikin gida ya shigar da ita sannan yace kin fadawa Ummee?cewa tayi a'a zandai fadamata inna shiga.kamal yace pls kina shiga ki fadamata dan na matso naji ance an banike,dariya tayi tace toh zan fadamata daga hka sukayi sallama ta shige gida shi kuma ya wuce.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to *itace zabina* member's I luv u all....ina godiya da addu'ar Ku a gareni Allah ya bar zumunchi.
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
3⃣9⃣➖4⃣0⃣
Bayan tayi sallar asuba ji tayi baccin gaba daga bai ishe ta bah dan haka ta koma ta kaunta.karfe 8:35am Ummee da taga bata fito bah yasa ta shiga cikin dakin,bakin gadon taje tana tashin ta!!tashi tayi ta zauna tana murza idon ta,Ummee tace wai ke meye naki na komawa bacci kuma yau koh ba yau bane zakuyi kamu bah?cikin muryar wanda bacci bai isheshi bah tace yau ne Ummee kawai dai naji baccin yaqi isata ne,tabe baki Ummee tayi tace toh hakura zakiyi ki tashi kiyi wanka sai kizo kiyi breakfast!tashi tayi tace toh,sannan ta shige toilet ita kuma Ummee ta fita daga dakin.
Bash ne a dakin kamal yana cewa Dan Allah Mallam ka tashi a baccin nan haka mana kaifa nake jira,cikin Bacin rai kamal ya tashi ya zauna yana cewa kai dai wallahi kanada matsala bash!!eh ai dole kace inada matsala tunda ba wurin hamdiyya zamuje bah da wurin tane ni zakazo kana tashi ai!!baice mishi komai bah ya tashi ya shige toilet yana tsaki,shi kuma ya koma parlour zaman jiran shi.
Bayan ta gama shirinta ta sauko kasa Ummee ta tarar a parlour zama taje tayi a kusa da ita,Ummee tace ki wuce kije kici abinci koh?langwabewa tayi tace Ummee ki bari su Abba su fito mana sai muci,Ummee ta watsa mata harara sannan tace su abban jiran ki zasuyi tayi? toh su har sun fita mah abinsu in zakije kici kije kici,tashi tayi tana cewa shine yau Dan na makara baza'a jirani bah!!!Ummee dai bata cemata komai haka taje ta zauna ta fara cin abincin fuska a yamuste dan ita ta fiso tanacin abinci da yan uwanta.
Bayan ya gama shiryawa ya fito parlour ya samu bash a zaune shima zaman yayi yana cewa ina jinka yau kuma mai za'ayi daza kazo kana tashi nah? kamar a kanka aka farayin aure,girgiza kai kawai yayi sannan yace dani kake zancen ai za'a zo yin nakan koh?wallahi zaka ga tsiya,dama mum ce tamin waya wai tanaso ta ganni.....baikai ga karasa maganar bah kamal yace me tace maka?maganar hamdiyya tamaka koh?dariya bash yyi yace haba miye haka aidai ka bari na karasa maganar koh zaka dinga jefumin questions haka kamar ina gaban alkali!!!banma je bah tukun nace sai nazo na fadamaka dan nasan nima bazai wuce maganar hamdiyya zatamin bah.sauke numfashi kamal yyi sannan yace kasan miye duk abinda ta tambaye ka ka fadamata gaskia tunda dai kai kasani hamdiyya bata da wani aibun nunawa,tashi yayi yace haka ne barinje naji toh!!shima tashin yayi yace nima wurin dad zanje dan abban hamdiyya yace suje gobe,murmushi bash yayi sannan yace toh Allah yasa ayi a sa'a,da Ameen ya amsa sannan suka fita daga part din nashi.
Bayan ta gama ta dawo parlour kiran zainab ya shigo wayarta picking call din tayi,zainab tace wai ke baza ki fito bane koh menene?murmushi tayi tace ganin nan zuwa yanzu insha Allah auntynah!!!tsaki tayi tace kedai Allah ya shiryeki daga haka ta kashe wayar,kallon Ummee tayi tace Ummee zan wuce yanzu ke sai yaushe zakizo?Ummee tace kafin a tafi wurin kamun zanzo nace Mubarak yazo ya kaini dan munyi waya da maman maryam din tace babu wani abu da za'ayi zan iya bari sai anjima naje toh banso naje nata zama,cewa tayi toh Ummee sai kinzo Nina tafi,Allah ya kiyaye hanya tamata sannan ta fita.
A parlour ya samu dad dinshi yana karanta newspaper a kasa ya zauna ya gaishe da dad din,amsawa yayi yace ka tashi lafiya?lafiya lau yace sai kuma yayi shiru.ajiye newspaper dad yayi yace akwai magana ne hala?Sosa kai yayi yace eh dama abban tane yace wai kuje kuyi magana gobe!!!murmushi dad yayi yace toh Masha Allah naji dadin hakan,kuma zan nema alfarman ya saka auren nan bada dadewa bah saboda banason wata matsala.cikin jin dadi kamal yace nagode sosai dad Allah ya kara girma,Ameen ya amsa dashi sannan kamal ya tashi yace zanje part din mum,toh yace mishi sannan shi kuma ya fita.
Gidan har ya Fara cika da mutane da mama ta fara haduwa,gaishe ta tayi cikin ladabi!!!mama ta amsa tana cewa hamdiyya sai yanzo? Daria tayi tace eh wallahi su maryam suna ina?fadamata inda suke tayi sannan ta wuce zuwa wurin su.tana shiga Maryam ta watasa mata harara tana cewa sai yanzu koh?zuwa tayi ta rungume ta tana cewa Amarya fah bata fushi kiyi hkr,dariya sukayi dukka sannan suka cigaba da shirye-shiryen su.
Yana shiga y gaishe da mum ta amsa cikin rashin sakin fuska sannan ta tashi ta fita daga parlour, kallon bash yayi yace kaga abinda nake fadamaka koh?murmushi bash yayi yace karka damu komai zai wuce insha Allah kazo ka rakani ni zan tafi!!!tashi sukayi suka fita a hanyar fita bash yake cewa tambaya ta tayi wai nasan wacce kakeso ka aura?shine nake cemata eh kawai Maryam ce,kamal yace sai tace me kuma?batace komai bah tadai girgiza kanta ya karashe maganar yana murmushi.hararar shi yayi yace miye na dariyar kuma?dafa kafadar shi yayi yace ba komai Allah ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi a haka suka karasa mota ya shiga yana cewa toh sai mun hadu dan nasan zakace kai zakaje ka kaita ka dawo da ita.murmushi yayi yace kamar kasani dan bazan yarda ta Hau motar kowa bah gaskia,shima murmushin yayi yace toh Allah ya kaimu daga haka ya tafi.
Mai makeup tazo har gida ta tsantsara musu kwalliya ba karamin kyau sukayi bah,fitowa sukayi gwanin ban sha'awa suka kai Amarya motar da zata shiga,tunda suka fito yake kallon ta bai dawo cikin hankalin shi bah sai da yaga wani na cemata tazo ta shiga motar nan su tafi!!!wani takaici yaji yayi saurin karaswa wurin,ganin mutum kawai tayi a gabanta yana mata wani irin kallo dariya ma yaso ya bata amma ta dake tace Ashe kananan?baice mata komai bah sai cewa da yayi kizo mu tafi sannan yayi gaba,girgiza kanta kawai tayi ta bishi a baya.shi ya bude mata ta shiga ta zauna sannan shima ya shiga ya tada motar suka tafi,sai da suka fara tafiya yace har agama bikin nan ban yarda ki shiga motar wani bah Dan Allah.dariya mara sauti tayi tace toh dan ita harga Allah dariya yake bata in yanayin haka.a haka suka isa wurin ta fita ta shiga wurin.
Anyi komai cikin wadata da nutsuwa da kuma nishadi haka aka gama komai har mutane suka fara watsewa.shi kuwa gugan yana nan bai tafi bah Dan gani yakeyi in ya tafi wani zai kaita gida,haka tazo ta sameshi a cikin motar ta shiga ta mishi sannnu,amsawa yayi yana kallon ta sannan yajaa motar suka bar wurin.gidan su Maryam ya maida ita dan nan zasu kauna,fitowa tayi shima ya fito.suka danyi hira sannan yace mata gobe su dad dinshi za suje gurin Abba!!!cewa tayi Allah ya kaimu yace Ameen a haka dai sukayi sallama ta shige cikin sai da yaga shigarta sannan shima ya shiga ya tafi.
✍✍✍
[1/22, 10:55 PM] +234 813 539 4575: ❣❣❣ITACE ZABINA❣❣❣
NA
Khadeejah Saleehu
Dedicated to hadiza sardauna Allah ya baki lafiya my purplenky
🌐HAJOW🌐
🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S✍
3⃣7⃣➖3⃣8⃣
Bayan ta shiga gida a parlour ta tarar da Ummee da kuma yaya Mubarak a zaune shima bai dade da dawowa bah, gaishe su tayi sannan taje ta kaunta akan kafan Ummee tana cewa kai wallahi nagaji Ummee!!! Ummee tace toh ba dole bah ga lallen yayi kyau sosai,tashi zaune tayi tace aini nasan yayi kyau dan har yafi na amaryar kyau!!yaya Mubarak ne yace nikam Allah ma yasani lallen baimun kyau bah koh kadan ya karashe maganar yana murmushin mugunta.hamdiyya tace Ummee kin dai gansa koh?ai dama kai komai nawa bai da kyau kuma dama bance kace yayi kyau bah wayan da suke sona zai musu kyau!!dariya sosai yayi sannan yace haba my sis wasa nake miki yyi kyau sosai u know I luv u!!ke kima fadamin nawa ne kudin lallen?ni zan biya,murmushi tayi tace dubu goma ne zaka iya biya?cewa yayi mai zai hana ai koh da yafi haka ma zan biya saboda yayi kyau sosai.Ummee ce tace kamar da gaske!!Mubarak yace da gaske mana ku tsaya ku gani zan biya,hamdiyya tace toh mun tsaya zamu gani daga hka tacewa Ummee bari taje tayi wanka tayi sallar la'asar dan batayi bah!!!da toh Ummee ta amsa mata sannan tace kiyi sai kizo kici abinci dan tunda kuka fara hidimar nan taku cin abincin ki ya sake lalacewa dama chan ba ci kikeyi bah!!hamdiyya tace toh Ummee nah daga haka ta haura sama.
Part din hajiya ya wuce direct dan baya son yaje wurin mum dinshi yaga tanayin fushi dashi koh kuma tamishi maganar Hafsa!!da sallama ya shiga hajiya dake zaune tana cin abinci ta ansa mishi,karasawa yayi ya zauna sannan yace nima a kawo mun abincin.hajiya tace chan inda ka fito bata baka abincin bah?Ashe ma maruwaciya ce toh Allah ya kyauta,kamal yace kedai in bakiyi magana bah ba kyajin dadi wallahi,nidai in zakisa a kawomin kisa in kuma baxakisa bah in tashi na tafi!!hajiya tace toh ka tafin mana sai me cikin waye?daga haka tayi kiran asiya mai mata aiki tace ta kawowa kamalu abinci.
Bayan ta fito daga wanka tayi sallah tana zaune akan sallayar ta taji wayarta na ringing a cikin jaka kan ta dauko jakar tayi picking call din har ya katse,ganin number kamal ne yasa tayi murmushi dialing number tayi yana fara ringing shi kuma ya kashe,kiranta ya sakeyi ta dauka da sallama!!amsawa yayi yana wani lumshe ido sannan yace kin shiga gida lafiya?hamdiyya tace ai kai zan tambaya ka kai gida lafiya?cewa yayi aini nafara tambayan ki koh?murmushi tayi tace toh lafiya lau,kaifa?shima murmushin yayi yace nima lafiya lau,ina fatan dai kin fadi sako nah daiko?hamdiyya tace ban fada bah zan dai fada!!kamal yace dan Allah kiyi kiyi ki fada dan na matso wallahi amma ke naga kamar baki damu bah.cewa tayi zan fada ai anjima zan kiraka na fadamaka,toh yace sannan yace ina jiran kiran naki nan bada dadewa bah pls!!hamdiyya tace toh shekenan ba damuwa sai ka jini daga haka suka kashe wayar,itaa kuma ta tashi zuwa race abincin kafin Ummee ta biyo bayan ta.
Direct dinning ta wuce tayi serving kanta dan babu kowa a parlour a cikin nutsuwa ta gama cin abincin ta har ta gama sannan ta tattara wurin.dakin Ummee ta nufa ta sameta tana karatun Qur'an,wuri ta samu ta zauna har sai da Ummee ta gama ta shaafa addu'a sannan tace lafiya dai koh?kai hamdiyya ta fara sosawa tana cewa dama.....dama....!!!ummme tace ke banason shashanci dama me?hamdiyya tace wai dama...wannan abokin bashir din nanne yace wai.....sai kuma tayi shiru.tsaki Ummee tajaa tace in bazaki ki fada ki tashi kiban wuri!!dama wai cewa yayi yanaso iyayen shi suzo suga Abba,Ummee tace toh wannan maganar ne saikin tajaan ta haka?lalle wannan abokin bashir din ya taki sa'a,finally dai yau kin samu Wanda kike so koh?ita dai hamdiyya kanta a kasa yake batace komai bah!!!sai Ummee ce tace toh shekenan ba damuwa zan fadawa abban duk abinda yace shekenan, hamdiyya ta tashi tace toh daga haka ta fita a dakin,Ummee dai murmushi tayi tace Allah yasa 'yata tayi zabi na gari.
Bayan kowa ya dawo sunci abinci suka danyi hira yarda suka saba kowa kuma ya tashi zuwa dakin shi.Ummee a dakin Abba take fadamishi yadda sukayi da hamdiyya!!!shima dariyar yayi yace toh yau mama nah ta samu Wanda take so kenan?Ummee tace eyyi tana sonshi kenan din tunda har tayi maganar,Abba yace toh kiramin ita nasan yanzu bata kaunta bah tukun,Ummee ta tashi tace toh daga haka ta fita kiran hamdiyya.
A kasa kan carpet din Abba take a zaune ta sunkuyar da kanta duk kunya ta lullubeta dan bata zata Abba zaiyi kiranta ba!!!Abba ne yace mama nah basai na tambayeki kih kina sonshi bah dan nasan kina son shi tunda har kika fadi yanason iyayen shi sunaso suzo,amma ya fadamiki sanda sukace sunason zuwa?gyada kanta tayi sannan tace yace wai ka basu tym,Abba ya sauke numfashi sannan yace toh kice mishi suzo jibi ai yayi koh?nan ma gyada kanta tayi tace toh,daga haka Abba yace zata iya tafia,tashi tayi ta musu sai da safe sannan ta fita.Ummee ce tace amma baka ganin jibi yayi sauri daga tambayan su?murmushin manya Abba yayi yace wuri kuma?ai ba ranar auren nasaka bah babu wani wuri da yayi kedai muyi mata addu'a Allah yasa shine mafi alkhairi dan ni kaina na gaji da abinda yaya yakemun kinga idan an fitar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 12