Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 11
daga rukon da tayi mai, shimfid'a wani tattausan Abu yayi tamkar dadduma ya fara Sallah, Jero Salloli ya dunga yi har sai da yaji Zuciyar shi ta natsu akan ya gama biyan sallolin da ke kanshi. Tun da ya fara Sallah take ta kallon shi ita dai tun da take yawan Zuwa k'asashe bata tab'a ganin masuyin irin wanna Abun ba kodai don bata lura bane, da sauri ta d'auko wayar ta, ta shiga ta fara searching meye Sallah Nan da Nan aka turo Mata, kasancewar ba wani turanci ta iya Sosai ba sai ta sa translation d'in shi to hindi, haka ta dunga bi tana dubawa har ta kammala. Ta d'ago ta tanbayeshi sai ta ganshi ya tasa Abincin da ta shigo dashi Yana ta ci dama yunwa yake ji Sosai, bai tab'a cin Abinci Mai d'adi haka ba. Zuwa tayi ta tasa shi a gaba tana kallon shi tamkar TV. Alama yayi Mata da hannu Wai lafiya take kallon shi, girgiza Mai Kai tayi da yimai alama da cewa kawai Yana burgeta gashi yanayin skin d'in shi da gashin kanshi iri d'aya da na Abbiyyu har hasken fatar su ma. Murmushi yayi Mata yayi Mata Alaman ya gode....suna Zaune kawai ji sukayi an shigo d'akin. ************************* ************************* K'asar Cameron "Alhaji gaskiya ya kamata ka koma gida kasan halin da iyalan ka suke ciki don nasan dole Laure bazata tab'a iya rik'e tarbiyan da ka basu ba. "Doctor kenan ai Ina Nan ne Amma duk Abun da ke faruwa na sani sai dai har yanzu an kasa gano min inda d'ana d'aya tilo yake Wanda Ina jin tsoron farkawan Mahaifiyar shi tace mun Ina yake ban San Amsar da Zan Bata ba.......✍️✍️✍️✍️✍️ Share Comments Like *Yar mutan Zazzau ce. 😍😍🥰🥰💖💖* *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. ************************* PAGE 30 CAMEROON BIRNIN GABON ........."Abun da ni yafi damu na shine yanda kafin Fannah ta Farfad'o in samo Mata d'an ta. "Ranka ya dad'e Wai ni Abun da nake ta jin Mamaki Wai dama iyalan ka basu San kana da wata Mata bane,? Gaskya ni Ina son inji yadda akayi ka Auri Fannah, Kuma gata ita tamkar ba ta cikin jinsin bak'ak'en fata, a Ina Kuma kukayi rayuwa da ita.? "Doctor kenan da alama ka Zama Dan jarida ne Koh.? "Ran Barrister ya dad'e ai dole in Zama Dan Jarida tun da Ina tare da kai, ni dai kawai a fitar da ni duhu nasan Yan Boyayyiyar K'ulli fans ma zasu so jin ya'akayi haka, daga k'arshe sai in basu Labarin basajan da kayi musu na cewa ka mutu, bayan ba ka mutu ba🤣. "Wato Kai Doctor k'ok'arin ka ka tuna mun Asiri kowa yaji Koh😔, to shikenan ka gyara Zama yanzu zakaji Mai ya faru da sanadiyar Aure na da Fannah. Ah so o'o har an gyara Zama aji labari to kwalelen ku mu had'u a Next page in ma Naga Comments din ku da yawa🤪🏃🏃. ************************* JOS Su Hajiya Jiddah da Hajiya Haulat da Fad'imatu sun Isa airport, bayan Hajiya Jiddah tasa anyi musu booking d'in flight da duk wani Abu da zasu buk'ata sun iso da mintoci jirgin su ya Iso suka shige suka d'aga sai BORNO. ************************* MAIDUGURI Zaune suke gaba d'aya a falon gidan Alhaji Bukar inda daga kwana biyu Zuwa uku har an canza ma gidan fasali an k'ara gyara gidan inda aka ware ma Zahra Falo guda had'e da d'akunan barci biyar, ko wanne da kalar furnitures d'in da yake d'akin. Kai tsayawa fasalta muku Falon Zahra da had'uwar da yayi ma b'ata lokaci ne kawai ku kwatan ta k'yan shi da aljannar duniya. Ruwan kanku bazai k'are ba sai ma kunga Sashin Maman Zahra Anan ne dukiya tayi kuka tamkar ba a San zafin ta ba ba Abun da babu a sashin sai dai in har bashi a duniyar ga Kuma wani safaya sashi daban a gidan shima. Kullum sai sun taro a falon tun daga ranar da aka fara sanarwan cigiyar Fad'imatu har yau, kullum tunanin su Fad'imatu tana hanyar Zuwa. To tabbas yau hasashen ku ya zama gaskiya domin Fad'imatu ma yanzu haka ta sauka a Maiduguri. Saukar su kenan a filin jirgin Saman suna k'okarin Samun Abun hawa, bayan mintoci kad'an suka samu Taxi, Fad'imatu ne ta hau gaban Motar duk da shekaru da yawa Amma ba Abun da ya goge a Zuciyar ta daga sunan unguwar har Zuwa layin gidan Alhaji Bukar Mai Dala. "Hajiya Ina muka nufa ne Ina ta magana tun d'azu. "Yi hakuri Malam pompomari zaka Kai mu layi na hud'u. "Tom ba damuwa k'udin ku dubu d'aya. "Muje Malam ba matsala. Haka suka Kama hanya har suka iso unguwar, unguwa ce ta masu hannu da shuni Wanda duk Wanda ka gani a unguwar ya Amsa sunan shi. Da kwatance har suka iso kofar gidan, fita sukayi suka sallami Mai Taxi suka fara buga gate din gidan. "Dallah waye zai damemu da buga gate ya jira inzo in bud'e Mana, cewar Mai gadin gidan har yazo zai bud'e Yana mita, yanzu haka irin Yan Maulan Nan ne da sassafe a damu mutane...... Maganar tashi ce ta mak'ale lokacin da yayi tozali da Fad'imatu don ba zai tab'a iya manta wannan fuskan ba a rayuwar shi. "Don Allah ranki ya dad'e ki mun rai tuba nake, da gudu ya koma gida Yana cewa "ranka ya dad'e Hajiya ta dawo tabbas yau Rahman gidan Nan ya dawo, haka har ya shiga falon ya Fad'in Alhaji Hajiya ta dawo Yana fad'i Yana nuna hanyar kofa, kafin kace kwabo sai gashi ana rige rigen fita da Alhaji da Momi da Mama Hanifa yayin da yaran suka rufa musu baya don gani wacece wannan da iyayen su suke d'okin gani haka. Kan kace Mai duk ma'aikatan da ke gidan sun Bayyana a bakin gate din gidan. Alhaji Bukar Yana isowa yaga farin cikin rayuwar da gudu ya rungume ta sai ga hawaye Yana zubo Mai shar Shar. Ba Wanda bai ji tausayin su ba a gurin, tun da Matar ta shigo Zahra taji duk duniya bata da kamar ta duk irin son da take ma Mami Ashe ba so bane, sai da tayi Ido biyu da wannan Matar, kawai ji tayi an rungume ta, kallon Wanda ta rungume tan tayi taga Ashe Matan ne, a hankali take jin wani irin farin ciki, Natsuwa, da kwanciyar Hankali Yana ratsa dukkan wani jijiyoyi na jikin ta tabbas wannan wata bangare ne na Rayuwar ta. "Zahraty ki yafe mun na gaza kula dake ba laifi na bane laifin Laluran da ya sameni ne. Haka dai suka dunguma suka koma falo, Nan a ka zauna kowa ya natsu Zahra aka fara cewa ta bada Labarin ta, Nan ta kwashe duk Labarinta ta basu ba Wanda baiyi kuka ba a Falon. "Tabbas y'ata kin rayu cikin k'unci ta wani fannin Kuma kin rayu cikin gata tunda kin samu ilimi da kulawa a gurin daddy ku da yayan ki, Zan so Inga hotonan bayin Allah Nan da suka rainamun y'a. Dubowa Zahra tayi ta mik'a Fad'imatu tana Fad'in ga Hoton daddy Nan in kikayi gaba duk Zaki ga na sauran harda Kaka. Mik'ewa Fad'imatu tayi had'i da jefar da wayan kawai sai tayi baya luuu zata fad'i gaba d'ayan su taso wa sukayi suna rige rigen rik'e ta. "Hanifa Kira doctor don Allah, to Wai ma me ta gani a wayar cewar Hajiya Jiddah tana mai d'aukar wayar ta duba. "Ikon Allah Mai yadda yaso wannan ai Habibullahi ne Yayan Fad'imatu, da gaske kusan a tare suka had'a baki gurin Fad'i. Mamaki ne ya cika Zahra, tana mai k'ara Imani da Ubangiji Mai tsara dukkan komai, wato ma wan Mahaifiyar ta ya rik'e ta, don yanzu ta fara gane cewa duk da ba'a fad'a Mata ba tasan Fad'imatu Mahaifiyar ta ce. Bayan ta Farfad'o ne tazo ta rik'e Zahra tana mai cewa"Zahra Ina Yaya na yake ki fad'a mun dama suna raye harda Mahaifiya ta. Girgiza Kai Zahra ta fara yi, "kiyi hakuri Mami ko wani Mai rai Mamaci ne tabbas Dadddy da Hajiya tsohuwa sun rasu. Wani kuka Fad'imatu ta fashe dashi. Sai da sukayi Mai isan su duka ba Wanda ya dakatar dasu sannan Fad'imatu ita ma ta basu Labarin duk yanda akayi. Kowa dai a tak'aice ya bada Labarin Abunda ya sani. Suna Shirin tashi suje suyi Sallah ne aka ce musu sunyi bak'i sunce akwai Abu Mai Muhimmaci da zasu sanar da Alhaji, Momy ne tace ace musu su shigo. Can sai gasu sun shigo, gaba d'aya kowa na falon sai da ya toshe hanci, yayin da kan Zahra ke duke bata d'ago ba sai taji muryan Wanda baza ta tab'a mancewa da ita ba tace "Zahra'u.! ************************* MASARAUTAR AMRISH "Kibd'iyatu wanene wannan dama Abun da kike b'oye wa kenan a D'akin shiyasa dana fad'a Miki Zan zo Miki hira kikace a'a.? "Dakata Ansh Ina ruwan ka dani eye da zaka zo kana mun ihu a d'aki, Soyayya ce nace banyi ana Dole ne eye🙄. "To shikenan Ina rantsuwa da Masarautar mu sai na tona Asirin ki yau d'in Nan. Yana gama Fad'in haka ya biga kofar ya fita.✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ Comments Like Share Yar mutan Zazzau ce 😍 sarauniyar kanawa😏😏. *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM ************************* PAGE 32 MASARAUTAR AMRISH Ana Kai su kurkuku, a ka fara d'aure Sadeeq da wata katuwan igiya Wanda bazai tab'a iya kwance wa ba in ba kwance shi akayi ba. Ita Kuma kibd'iyatu kafafuwa kawai a ka d'aure mata da hannu sab'anin Sadeeq da aka d'aure shi jikin gini. Wuta suka fara hurawa ana zuba wasu k'arafuna a ciki, yayin da wasu ke gyara wasu Manyan bulalai tamkar Wanda za'a duka jaku na dashi. Zaro Ido Sadeeq yayi ganin Abubuwan da suke yi, Yana tunani a cikin Zuciyar shi badai duk su za'ayi ma Azaba da wannan Abun ba. A hankali ya fara karanto Addu'a dake bakin shi Yana Mai Neman agaji gurin Ubangiji. Kawai ji yayi an d'ora mai wannan k'arfen na cikin wuta a saitin bayan shi. Ihu yayi Yana Kiran Ubangiji, Sosai kibd'iyatu taji wani k'arfi yazo Mata Wanda Bata San lokacin da ta kwance kan ta ba, Nan aka fara fafatawa tsakanin ta da sojojin kurkukun. Yayin da Sadeeq ko ya dad'e da Suma Saboda Azaba. Wasu Mata ne suka fara durowa ta sama sun rufe fuskokin su, kafin kace me sun gama da sojojin. Haka suka d'auki Sadeeq suka fice tare da kibd'iyatu. Sosai ake fafatawa har suka samu nasaran fita daga kurkukun, Nan da Nan labari ya Kai kunne Sarki cewa Kibd'iyatu ta gudu ita da bak'on nan, dai dai lokacin da Amrita ta iso taji Abun da ake sanarwa Mai martaba kafin yace komai, ita ta rigashi cewa aje a had'a manyan mayak'an garin su shiga dajin Nan duk inda take su dawo da ita. A tabbatar an kawo ta ita da bak'on nan. Haka aka had'a mayak'an kace zasu je yak'i ne suka watsu domin kamo su kibd'iyatu da Sadeeq. ************************* MAIDUGURI Dai dai shigowar Alhaji Madou mijin Mama Hanifa. "Barisster Habibullahi Ina Amana ta da na baka, ya akayi Kuma baka Mutu ba,? Bayan naje office din ka da ke Kaduna ance mun ka rasu.? "Ya kamata duk mu natsu muji komai. "Ka dubamun k'anwa ta da yarinya ta. Bayan an duba su Zahra ne sun Farfad'o kowa ya natsu a falon sannan Hajiya Jiddah tace ma Daddy Habibullahi Ina d'an uwan ka Sadeeq da Matarshi, kullum dasu nake kwana nake tashi.? Ina Kuma ka samo wannan Mai zubin indiawan.? "To Alhmdulillahi nasan dai yanzu kowa Anan ni yake sauraro yaji Mai ya faru. Da farko dai lokacin da Yan fashi suka shiga gidana dama nasan da zuwan su, domin naji Mata ta Laurat suna waya dasu domin tabbas gida na in har ba jagora baza ka tab'a iya shigowa ba. Bayan naji duk yanda suka shirya da yawan kud'i da suka ce zasu bata ne, sai na tattara duk wata dukiya ta da kadarori na da na Dan uwa na da ke hannu na na Damk'a Y'ata Zahra domin nafi yarda da ita, tunda a lokacin Sadeeq ya yi fushi dani Saboda nace bazan Aura Mai Yar uwar shi ba. Bayan na tura ma kowannen su Miliyan biyar biyar a Account d'in su ita Kuma Laurat Miliyan goma, duk Abun da nakeyi Laurat bata sani ba, sai na bar kad'an daga cikin Abubuwa da na Mallaka a gidan don Inga iya gudun ruwan Laurat. Bayan Yan fashin sunzo dama cikin d'ayan biyu ne ko su kashe ni ko inyi rai Amma burin su su kashe ni haka burin Laurat ma. Sai dai dama na riga na sanar ma Yan Sanda suna farawa Yan sanda suka zo. Haka yasa da sauran rai na a duniya aka d'auke ni sai Asibiti, bayan munje Asibiti dama mun riga mun gama magana da Doctor kasancewar shi dama Aboki na ne, yayin da Laurat suka gama magana da yan fashin akan cewa zasu biyoni Asibiti su k'arisa kashe ni. Hakan yasa doctor ya mun wata Allura na tsawon Awa Arba'in da takwas ma'ana kwana biyu kenan, in akayi ma wannan Alluran zakayi tamkar ka Mutu. Hakan yasa kuka ga Tamkar na mutu bayan an Kai ni da wasu Awanni Doctor yaje ya cironi a cikin k'abarin yayin da muka Kama hanyar Zuwa Cameron ni da Fannah da Doctor ya cigaba da kula damu a can. Nasan zaku so kuji wacece Fannah.? Wannan Amsa Alhaji Madou ya Kama ta ya baku ita. Kowa juyowa yayi Yana kallon Alhaji Madou. "Alhamdulillahi Fannah dai wata Baiwar Allah ce da na tsince ta, Kowa yasan ni din babban Soja ne, akwai watarana mun fita zagaye don ganin yanda aikin Yara na yake tafiya nida Mahaifin su Barisster Habibullahi da Dan uwan shi Sadeeq, sai muka tsinci Baiwar Allah Nan a yashe a cikin daji tamkar Bata Numfashi da farko mun yi tunanin Aljana ce Saboda tsananin k'yawun ta, haka Sadeeq ya yi k'okari ya bata taimakon gaggawa kasancewar shi likita Mai kula da sojoji. Bayan ta Farfad'o ne muka rasa yanda zamuyi da ita, a lokacin tun da ba lokacin zamu koma gida ba, Haka dai Genaral Muhammad ya d'auke ta ya dawo da ita gidan shi dake Cikin Maiduguri. Bayan mun dawo da watanni a Nan muka gane ba Musulma bace ita duk da kaman ta samu tab'in hankali. Sai muka sa Mata Suna Fannah muka musuluntar da ita. Da yake ni na tsince ta sai General ya nema ma Dan shi Barisster Habibullahi Auren ta, bayan tsawon lokaci ni Kuma an turani wani course a can Uk na dawo na tarar da mummunan Labarin cewar Genaral da iyalan shi gaba d'aya sun Mutu. Iyakan Abun da na sani kenan. Daddy ne yaci gaba daga inda ya tsaya gurin cewar, "tabbas haka ake ta cewar Mun Mutu Amma ba gskya bace ya Basu Labarin yanda suka bar Maiduguri. Ya Kuma Basu Labarin cewa Fannah dama tana Kaduna tana ganin likita a can shiyasa dasu ka bar garin suka yanke shawarar kawai su koma kaduna da Zama. Innah Jidda sai dai kiyi hakuri Saboda tun bayan barin mu Maiduguri aka tura Sadeeq K'asar Mali ya d'auki Matar shi suka tafi bamu k'ara jin Labarin su ba naje Barack din nasu yafi a k'irga Amma har yanzu shiru ba Labarin su. Ya k'arisa maganar cikin jimami. Bayan mun koma da wasu watanni kawai Fannah ta samu ciki Sosai nida Umma ta mukayi murna haka, sai dai cikin Yana matuk'ar bata wahala a haka aka maidoni Zaria yin wani aiki haka na dawo Zaria na bar Umma tana kula da Fanna. Bayan wasu tsawon watanni Fannah ta Haifa sankacecen yaron ta Wanda gaba d'aya ita ya biyo ga k'yau kaman shi yayi kan shi, sai dai doctor yace bazata iya shayar da yaron ba balle rainon shi tun da har yau bata cikin hayyacin ta, sai dai mu nemi wata ta shayar dashi Koda da Madara ne ana biyan ta. Ana haka ne muka had'u da Laurat banyi wani tsawon bincike ba ganin yanayin yanda ta Nuna mu ita d'in na Allah ce, Kuma na gan ta Ainihin Shuwa Arab shiyasa na Amince Mata mukayi Aure bayan munyi Aure da wata shida Umma ta dawo Zaria ita ma, sannan ne na bijiro ma da Laurat cewan zata rik'e mun yaron dan uwa na da ya mutu ya barmun da k'yar ta Amince sai da Umma tasa baki tun daga Nan rainon Sadeeq ya dawo hannun Laurat Sosai ta bashi tarbiyan da ya kamata kasancewar ta Mai fuska biyu Kuma ta Nuna Mai so da uwa zata Nuna ma d'an ta, sai dai daga baya na fahimci cewan tana rik'on shi ne Saboda nace Mata Mahaifin shi ya mutu ya bar Mai dukiya masu tarin yawa, Wanda kusan dashi muke rayuwa hakan yasa ta k'ara jawoshi a jiki kaman ta had'iye shi. Kunji Abun da ya faru, bayan mun koma Camaroon da Fannah cikin ikon Allah mun had'u da wani Malamin Musulunci Wanda yayi k'okari ya karya tsafin da ke jikin Fannah inda har yanzu bata gama warkewa ba, don har yau bata San komai game da ita ba, sai dai an karya duk wani siddabaru na jikin ta. Abun da yasa ko kuka ganni a Nan Ina bibiyar duk wani labari dangane da iyalaina da Laurat ta tarwatsa mun, ta haka ne na gane cewar Zahra y'ar kace, sai dai nayi Mamakin ganin y'ar uwa ta d'aya tilo Wanda muka dad'e da cire rai da ita a gidan Nan ita da k'annin Mahaifiyar mu da Kuma Laurat duk Mai ya kawo su Nan.? Alhaji Bukar ne ya kwashe Labarin komai game da Fad'imatu da Zahra da Laurat. Sai ga Daddy Yana kuka, ya bud'e Hannayen shi yace "zo gareni y'ata shiyasa nake Miki Soyayya na daban a cikin zuciya ta. Da sauri Zahra ta k'arisa ta rungume Daddy. "Yaya wato kafi son y'ar ka Dani Koh,? Ta fad'a Tana maiyin tamkar zatayi kuka. Gaba d'aya falon dariya aka Mata. "Yi hakuri Autan Umma zo kema da sassarfa ta k'arisa gurin Yayan nata ta had'a da Zahra ta rungume su. "Mami na tana kishi dani don Daddy yafi Sona Zahra ta fad'a cikin dariya da kuka. Gaba d'aya jikin Mami yayi sanyi. Tura keken guragun ta tayi ta Isa gaban Daddy. "Don Allah Habibullahi ka yafe mun wlh yau na k'ara tabbatar da hukuncin Ubangiji, Kuma wlh nayi Nadaman Abun da na Aika ta wlh sharrin shaid'an ne. Zahra y'ata ki yafe mun don Allah. "Mami ni na yafe Miki duniya da lahira sai dai banjin Zan iya yafe ma Yar uwan ki ba, ta rabani da Ahalina ta sa Mahaifiya ta gararin rayuwa. Kawai ta k'ara fashewa da kuka. Fad'imatu ne ta jawo ta ta rungume ta, "y'ata ki yafe Mata kamar yanda nima na yafe mata, kin San Ubangiji yana son masu hakuri. "Shikenan Mami na yafe Mata duniya da lahira Allah ya yafe Mana baki d'aya, gaba d'aya suka Amsa da Ameen ya Allah. Nan su Mami suka tarkata suka tafi Mami tana da na sani.✍️✍️✍️✍️✍️ Share Comments Like Zeey Yar mutan Zazzau ce sarauniyar kanawa 😏😏🙄 💖😍🥰😍💃💃Love you fans. *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM PAGE 31 ************************* MAIDUGURI "Mami ke ce.! Ta fad'a cikin kuka Mai ya sameki a kafan ki,? Shine kika tafi kika barni. "Zahra me kikeyi anan,? Wace wannan Mai Kama da ke, ta fad'i haka tana Nuna Fad'imatu. Murmushi Zahra tayi Mai Had'e da hawaye tace "Mami wannan da kike gani itace Mahaifiya ta wannan Kuma Mahaifina ta nuna Alhaji Bukar, Alhmdulillahi sanadiyar rabuwa da ke na had'u da Ahalina. Asabe ne ta Nuna Zahra jiki na rawa tace, "kina nufin kice mun kece Yarinyar Fad'imatu Wanda ta bar gidan nan da cikin ki 🤔. Allah Mai iko Mai yadda yaso cikin da mukayi ta k'okari zubar dashi Ashe da rabon sai yazo duniya. Don Allah ku yafe mun nasan in har baku yafe mun ba Allah ba zai tab'a yafe mun ba. "Da farko dai Sunana Asabe Wanda ake ma lak'abi da Uwar sharri. Ni Asalin Yar garin Zulum, na kasance tun farko na bana jin magana domin kuwa Mahaifiya ta ita take d'aure mun gindi bata son Laifi na Saboda sunan Innan ta aka Samun Kuma mu kad'ai ta haifa daga ni sai Yar uwa ta, gata ta Nuna Mami inda Mahaifin mu ke tsaya gurin bamu tarbiya yayin da Mahaifiyar ta ke lalatawa. In da tun Ina yarinya na iya had'a sharri nasha kashe Aure a garin mu yafi a k'irga, Mahaifiyar mu ta kasance Mace Mai son Abun duniya inda Zaki kawo Mata kud'i ba ruwan ta da tanbayar in da kika samo, duk k'auyen mu mu kad'ai muke makarantar Boko daga mu sai yaran Mai gari, Mahaifiyar mu ta tsaya tsayin daka don muyi karatu ko ma samu mu Auri masu kud'i Saboda Allah ya wadata mu da k'yau, Dukan mu Mahaifiyar mu muka biyo Saboda ita d'in Asalin shuwa Arab ce. In da Mahaifin mu ya kasance Buzu ne. Sosai muke Alfahari da k'yan mu nida Yar uwa ta muna ji tamkar duk garin ba yamu. Yagana ta kasance k'awar Yaya ta. Bayan Auren Yaya ta da wani Mai kud'i a garin Maiduguri, da shekaru Masu yawa ita ma Yagana tayi Aure a K'auyen dake makwafta ka da garin mu in da Masifan ta da shedanancin ta ya hana ta Zama ta fito da ciki. Kwatsam sai ga Yaya ta an sako ta ta dawo gida Wai bata Haihu Mijin Kuma kullum sai ya bige ta yayi Mata gori. Bayan wani lokaci Yaya ta ta tafi kaduna gurin wata K'awar ta sai da tayi kusan shekara biyu tazo gida tana Fad'in ma Inna tayi Aure a Zaria. Kar in cika ku da surutu bayan wasu shekaru Masu yawa Yagana ta haihu ta haifi yarinya Mace har ta girma sai tana Zuwa birni don yin aikatau a biya ta ni Kuma lokacin na had'u da wani Saurayi na Yana zuwa Lagos sunan shi Alhaji Shamsu Ana ce Mai Shamo, haka ya dunga mun b'arin kud'i, hakan yasa ba kalar hotel din da bamu ziyarta ba a garin Maiduguri, haka Zan kwana biyu bana gida, Amma indai Zan dawo in kawo ma Inna kud'i ita ba ta da Matsala. Kwatsam Ina Zaune wata rana na dawo daga gantalina sai ga Yagana, na tarbe ta muka gaisa nake tanbayar ta kwana biyu tunda ba Yaya Laure ko ganin ta ba'a yi. "Ke dai bari kawai Asabe, kin San wani Abu kuwa.? "Sai kin fad'a Ina jin ki." "Wani taimako nake so ki mun don Allah, kin San yanzu gidan Alhaji Bukar Mai Dala nake aiki. "Ke don Allah.! Tab kice kin Zama Hajiya gidan da akace in kana aiki Albashin gidan bai yi K'asa da dubu d'ari ba. "Ke dai bari kawai so nake ki taimaka mun mu Zubar da cikin matan gidan Kuma mu kore ta, Bintu ta Aure shi. "Tab babban magana taya kenan.? Tunani na fara a Zuciya ta ai tamkar dama ne na samu ta yanda Zan ma Yagana wayau in Aure Alhaji Bukar. Nan da Nan na Amince inda a lokacin nima Ina d'auke da ciki ban sani ba Saboda cikin ba Mai irin wahalan nan bane, Kuma ko alama bai fito ba a jiki na sai dai Kara bud'ewa da nayi da jikina yayi lukui-lukui. A haka muka ajiye ranar da zamu gidan Boka inda mukaje muka karbo magani da yarjejeniyar cewa in komai ya Kammala Yagana zata ban Miliyan biyar jin kud'in da ta Anbata ne ya sa ni na janye kudiri na na Auren Alhaji Bukar, Saboda ni ma Allah yayo ni Mayyar kud'i ce. Haka mukaje gidan ta nunani a gurin matar gidan a matsayin kanwar ta Zan dunga Taya ta aiki. Bayan wasu kwanaki duk mun Gama Anfani da Magungunan da Boka ya Basu jira kawai suke Alhaji ya dawo, domin Sosai muka sama Fad'imatu kasala gurin yin Ibada, bayan ta kasance Mace Mai son ibada haka muka dunga k'ulle k'ulle mu

Chapter 9 of 11