Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
tace "Yaya Sadeeq yaushe ka dawo ne.? Murmushi yayi Mata Yana k'okarin fitowa, ya d'auki Akwatin ta yasa a boot yace Mata "muje Madam Tambaya. Ya fad'i haka Yana Murmushi. Bata rai tayi ta fara Yi tamkar zatayi kuka, "Nidin ce zaka cema Madam Tambaya koh, Allah ni ba sunana kenan ba🙄, Kuma na fasa shiga Motar taka kaje Zan biyo ta haya. Kama kunnen shi yayi "Sorry My Baby Zahraty, shiga mu tafi kin San hanyoyin namu babu kyau. Shiga tayi Tana ta b'ata fuska, yaja suka tafi. Sun Isa gida karfe Tara na dare, Khausar kawai suka tarar a Falo tasa wasu matsiyatan Kaya, Wanda gara babu kanta yaji Attached dama ita Bata da wani gashi Sosai. Tana kwance Tana latsa wayar ta kirar Apple plu. Binta sukayi da kallo gaba d'ayan su, ita ma wani kallon gefen Ido tayi musu ta kawar da kan ta ta cigaba da latsa wayar ta. "Twinie baki ganni bane...? Ko well come bazakiyi mun ba. Ta karishe maganar ta Tana Zama kusa da ita, ta Kai hannu zata rungume ta. "Karki sake ki tab'ani ko cewa akayi Dole sai na kula ki iyee? Tashi tayi ta shige d'aki Abunta ta bar Zahra zaune gurin. Jiki sanyaye Zahra ta tashi ta ja trolley d'in ta, Dama shi Sadeeq tunda suka shigo ko tsaya bai yi ba yayi wucewar sa. Washe gari tun karfe hud'u Mami ta tashi Zahra tace ga wankin da Khausar ta dawo dasu can daga School ita ma nata na Nan a cikin Basket Laundry. Gashi Washing machine d'in su ya lalace, Haka Zahra ta tashi taje ta fara wanki....✍️✍️✍️✍️ Ban ganin Comments din ku fa more Comment more typing ehee 🙄🙄. Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰 *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ Wannan page d'in na kune na baku kyauta Boyayyiyar K'ulli fans kuyi yadda kuke so🥰🥰🥰 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM PAGE 17 Sosai ranar Zahra ta wanku don Bata kammala wankin Nan ba sai karfe Sha biyu, sanan ta samu ta karya, ga kayan sunyi masifan datti don harda su panties da breziya da su boom short. Bayan ta zauna Tana hutawa sai ga Khausar ta fito Tana wani mik'a had'i da yamutsa fuska. Ke Zahra ki had'a mun oat yanzu. Tana gama fad'i haka ta juya Abun ta, girgiza Kai Zahra tayi ta tashi ta shiga kitchen don had'a mata, jitai kamar ana kallon ta, waigawa tayi da sauri had'a Ido sukayi dashi Yana jingine da kofa Yana Mata murmushi. "Zahraty baby wa yayi wankin can,? In ce dai ba ke kikayi ba.? "A'a Yaya a washing machine ne fa. Ta juya ta cigaba da k'okarin juya oat d'in da take damawa. "Zamu Sha oat kenan.? "Uhmm na Khausar ne ma Yaya sai dai Kai in kana so In dama ma wani. Kallon da yayi Mata ne ya hanata k'arisa maganar da takeyi, langwabar da Kai tayi Alamun kar yace komai. Fita yayi cikin fushi, Tana Kiran shi ko waigota baiyi ba. Direct d'akin su ya shiga ya same ta a kwance Tana Danna waya, wani tsawa da yayi Mata sai da wayar ta fad'i a hanun ta, ta Mike a tsorace don duk iskancinta Tana tsoron shi. "Me na fad'a Miki eyeh,! Ita d'in Baiwar kice ko Yar aikin ki da Zaki dunga sata aiki, ba laifin ki bane laifin Mami ne da ta d'aure Miki gindi ki ke Abun da kike so, Kuma yanzun Nan zanyi maganin ki. Zare belt d'in da yake jikin shi ya farayi. ************************* JOS Rirrik'eta akeyi Amma Tana dad'a watsar da mutane, kuka Sosai Hajiya takeyi don ita ji take tamkar jinin ta ce Dijah,zata iya biyan ko nawa ne don ta Samu lafiya. "Hajiya kiyi hakuri insha Allah komai yazo k'arshe duk wahalar Nan da suke bamu in har suka ji wuya da zafin Ayoyin Ubangiji zasu fita, suna da tsananin taurin Kai ne ko magana sun k'iyi, Amma ba Abunda yafi karfin Ubangiji. Sosai Hajiya ke kuka tana fad'in "Allah ya yaye Miki Dijah ya Kuma saka Miki duk Wanda yayi Miki wannan Abun Allah ya mayar Masa. ************************* K'AUYEN ZULUM Sosai Uwar Sharri ke jin jiki yayin da Innah Tasallah take iya k'ok'arin ta gurin Mata Yan jike-jike irin nasu na Yan k'auye Amma har yanzu ba wani cigaba sai Uwar wari ma da gaban ta yakeyi Yana fitar da wasu irin Manyan tsutsotsi. Duk da girma ya Kama Innah Tasallah Amma tsakanin d'a da mahaifi sai Allah, Haka take wannan d'awainiyar. Kullum maganar Asabe Allah kar ya d'auki ran ta Bata je ta kwance K'ullin da ta d'aura ba. Haka zata zauna Tana sunbatu da maganganu kamar mahaukaciya. ************************* ZARIA BIRNIN SHEHU Dukan ta yakeyi kamar ya samu jaka, gaashi Mami Bata Nan a gida ta je unguwa. sai da Zahra tazo ta rungume ta, tace sai dai ya dake su tare, Tana kuka Khausar na kuka. Yar da belt d'in yayi ya fita ransa a b'ace. Kama ta tayi ta d'aga ta ta zaunar da ita a bakin gado, da sauri ta shige toilet ta had'a Mata ruwa Mai Zafi ta Kamata ta kaita toilet tace ta gasa jikin ta. ************************* MAIDUGURI "Muddin ba'a bayar da jinin jaririyar Nan ba ga Mai gizo komai zai iya wargajewa don kun San cewa dai ba a hayyacin Alhaji ya Auri y'ar ki ba Koh.? To ku tabbatar cikin na cika wata Tara a kawo mun ita Nan, ki tashi ki tafi Boka ya Gama magana....✍️✍️✍️✍️✍️✍️ More Comment more typing. Bafa na ganin Comments din ku fa ko bakwa bukata ne.? *Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰* *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM PAGE 18 Mami ce ta shigo taga Khausar kwance, jikin ta duk ya fashe, Alamar duka. "Baby Khausar wa yayi Miki wannan dukan haka.? Mami ta fad'a Rai b'ace. Tana d'aga Khausar da Zazzabi ya lullub'e ta, ta d'ora ta a jikin ta Tana Shafa Mata kai. Kuka Khausar ta saka, Tana Fad'in "Zahra ce tasa Yaya Sadeeq ya mun dukan tsiya, haka kurum ban musu komai ba. "Tabdijam lallai ma wlh yau sai tasan cewa ruwa ba sa'an kwando bane, Tashi muje a kanta Zaki Rama dukan Nan. Jin haka yasa Khausar ta Mike Zuciyar ta fal farin ciki. Zahra Tana cikin fere doya a kitchen Tana ta sauri don kar Mami ta dawo bata gama girki ba. Ga Khausar bata ci komai ba, kawai jin duka tayi ko ta Ina sun rufe ta da shi. "Don Allah Mami kiyi hakuri, menayi muku ne.? Sai da sukayi Mata duka Sosai sannan Khausar ta d'auko tukunya da ke kan wuta ta d'ora ma Zahra a cikin ta, wani k'ara ta saka yayi dai-dai da shigowar Sadeeq falon. Da gudu ya k'arisa kitchen din, ganin su Mami a tsaye Tana zazzaga ma Zahra Masifa, ita Kuma Khausar hannun ta d'auke da tukunya Tana zazzare Ido. "Haba Mami me tayi Miki ne? Don Allah ki daina Azabtar da yarinyar Nan Haka Kuma wallahi kinci Amanar Daddy. Don Amanan mu Daddy ya bar Miki. Juyawa yayi a fusace zai tafi, "Sadeeq zonan." Mami ne ta kirashi tunda yake da Mami Bata tab'a Kiran sunan shi ba sai yau. Zuwa yayi ya zugunna a gaban ta yace, " gani Mami." "Sadeeq daga yau ni Mahaifiyar ka Hajiya Laurat nace duk ranar da ka Kara kula yarinyar Nan Allah ya isa ban yafe ma ba, ko ka Kara ganin Ina Mata wani Abu kayi magana. Gaba d'ayan su d'agowa sukayi cike da firgici da Mamaki suna kallon Mami, Ashe har tsanar da Mami tayi ma Zahra ya Kai haka, Sadeeq ne yake Fad'in haka a Zuciyar shi yayin da hawaye ya wanke Mai fuska. "Mami don Allah kiyi hakuri ki janye wannan kalaman naki a Kai na, wlh yamun tsauri da yawa. "Ka tashi ka bani guri kafun in tsine maka ka bi duniya, kasan inda na tsani yarinyar Nan kuwa,? Tunda tazo gidan Nan Alhaji ke nuna Mata Soyayya ya fifitata akan kowa, har Kai da kake d'an shi, ta kanta Alhaji yace zai iya Saki na fa." Ke Zahra na tsaneki har cikin zuciya ta. Tana gama Fad'in haka ta juya Abun ta, Khausar binta tayi tai shigewan ta d'aki. Kuka Sosai Zahra takeyi tabbas yanzu tasan gatan ta ya rasu, Jan jiki tayi ta shige kitchen don k'arisa Abunda takeyi. Karfe bakwai na Yamma dai dai Sadeeq ya bar garin Zaria, do yau yace komai Dare sai ya bar garin, bazai tab'a dawowa ba har sai Mami ta janye kalaman ta a kanshi, Takarda ya ajiye ma Zahra a kitchen ya tafi kowa baiyi ma Sallama ba. Fitowan ta kenan daga kitchen ta kammala wanke-wanke da kimtsa kitchen din, tsayawa tayi tana tunani, da sauri ta koma kitchen din dai dai gurin sink taga wani takarda taga Kuma an rubuta Zahraty. Jikin ta na rawa ta bud'e takardan ta fara karantawa. "Zahraty kiyi hakuri ki rungumi kaddara, ki dage da karatun ki, na tafi bazan dawo ba sai ranar da Mami ta Neme ni da kan ta. Ki kulamun da kanki, karki manta har Abada Ina son ki, sannan na Mai da sunan ki a Asusun Albashi na duk wata Albashi na zai shigo ta Account d'in ki ne, kiyi duk wani hidiman karatun ki dashi, ban so ki roki kowa, Sannan akwai takardun kadarorin daddy da yake hannu na, yace akwai fake din a hannun ki da Kuma na kananun kadarorin shi, yasan meyasa yayi haka sannan a cikin Abunda ya baki akwai wani Akwati karami ki Adana shi da kyau duk Randa mukayi Aure zamu bud'e tare muga meye a ciki. Bye bye Zahraty ki kulamun da kanki. Kuka Sosai Zahra ta zauna takeyi, "Allah ya tsaremun Kai yayana a duk inda kake.tana Gama fad'an Haka ta tashi ta tafi d'aki. ************************* JOS "Hajiya gaskiya za'a d'au tsawon lokaci kafin Yarinyar Nan ta warke, kin San Asiri farat d'aya yake shigan mutum Amma fitan shi sai anyi da gaske. "Shikenan Mallam nidai fatana ta samu lafiya Allah ya dubemu. Ta fad'a Tana mai Mik'ewa "to Mallam na tafi Allah ya saka da Alheri. "Ameen ya Allah Hajiya ai ba damuwa wannan Abu tamkar jihadi ne. ************************* K'AUYEN ZULUM Fisge-fisge takeyi tana ihu Saboda wani Azaba da take ji a fatan jikin ta, inda gaban ta yake fitar da wani ruwa Mai kauri had'e da jini ga wani uban wari, Haka take cisge gashin kan ta, Tamkar Mahaukaciya. Kuka Sosai Inna Tasallah takeyi, "Mallam ka taimaka ka sauko daga fushin Nan da kakeyi da ita kayi Mata Addu'a ko taji Salama. "Kinga Tasallah ki kyaleni Abunda Asabe ta shuka shi take girba fa, ba Abunda Zan Mata Kinga fita ta ma, ya shura takalman shi yayi gaba abinshi. Kuka Sosai Inna takeyi don Asabe tana tsananin Shan Azaba. ************************* MAIDUGURI Kwance take jikin ta ba inda Bai Mata ciwo, ga wani Azaban Ciwon ciki da take fama dashi yau gurin sati d'aya kenan, gashi komai taci sai tayi Aman shi, Hankalin Alhaji duk ya tashi, an Kira likitoci sunkai goma don suga Mai ke damun ta, Amma Amsar d'aya ce Lafiyan ta k'alau. Ita Kuma ita kad'ai tasan Azabar da take Sha a jikin ta da cikin ta. ************************* Khausar ne d'akin Daddy tayi watsa watsa da d'aki kamar Mai Neman wani Abu. Wani drawer ta janyo zaro Ido tayi ganin me ke cikin drawer, jikin ta na rawa ta jawo jakan da ke hannunta ta shiga loda kud'i Nan a ciki sai da ta kwashe zaf ta Mai da ta rufe ta fito, ficewa gidan tayi taje banki ta sa kud'in. Ta ja Motan ta tayi gida Tana Zuwa ta d'auuki trolley d'in ta ta saka a jaka, ta kwashe duk wani Abu nata tasa a boot d'akin Mami ta shiga taji Alamun kaman Tana wanka, bincike ta farayi a D'akin da sauri da sauri gwala-gwalan Mami ta tattara tasa a cikin handbag d'in ta, biro ta fito dashi a Jakarta da takarda tayi rubutu ta ajiye, ta fice Abun ta. Tana Zuwa ta hau Mota ta fita a tsiyace, dai dai lokacin Mami ta fito wanka kenan, idon ta ne ya kaima ta kan takardan da ke side drawer nata, da murmushi a fuskar ta ta k'arisa Tana "Yan matan Mami har an Fice kenan Allah ya dawo mun da ke lafiya. Maganar nata ne ya mak'ale lokacin da taga me ke cikin takardan. "Mami karki sake ki nemeni, Kuma karki nemi gold d'in ki, sannan in kin koma garin ku kin tarar da Uwata kice Mata na tsane ta har Abada. Ki Kuma bar Zahra ta Auri Yaya Sadeeq don da ita yafi dacewa ba Dani ba, ni burina ya riga ya cika na samu Abunda nake so, ki manta da wata Khausar a duniyar ki. Kiyi jimami lafiya.🤣 Wani jiri Mami taji Yana d'iban ta kawai jitai ta zub'e a gurin...✍️✍️✍️✍️✍️ Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍 Nasan wasu da yawa zasu ji dadin page d'in Nan koh Ni Kuma bakin ciki nakeyi wayyo Mamin mu😭😭. *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ 🤣🤣🤣🤣🤣🤣Yau Ina so Inga comments din ku fa. Masu farin ciki sai ku Kara farin ciki.don Naga alama bakwa K'aunar Mami🙄🙄. BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM ************************* PAGE 19 Take stroke ya Kama Mami. Ihun da tayi ne yasa Zahra fitowa da gudu Tana shigowa d'aki ta tarar da Mami kwance b'arin jikin ta ko motsi baiyi. "Innalillahi wa'innah illaihirraji'un Mami meya same ki.? Fita tayi ta dawo ta d'auko Kaya ta sa Mata, ta Kama ta ta d'ora ta a gado, Tana yi tana kuka waya ta d'auka ta Kira doctor. "Hello doctor please kazo yanzun Nan ba lafiya. Bayan zuwan doctor yayi Aune-aunen shi ya gama, rubuta Magunguna yayi ya mik'a ma Zahra. "Kiyi k'okari ki siyo maganin Nan sannan Kuma jinin ta ya hau sosai, ta kamu da ciwun barin jiki. "Innalillahi wa'innah illaihirraji'un ya Allah ka yaye Mata wannan cuta. Sallama doctor ya Mata tare da Addu'an Allah ya kawo sauki. Ya tafi. Sosai Mami take barci Saboda Alluran Barcin da likita yayi mata. Haka Zahra tayi ta fama da jinyar Mami har sati biyu gashi an koma school, da k'yar ta samu wata tsohuwa da zata cigaba da kula da Mami, ita Kuma tayi Shirin komawa makaranta. Three months later Khausar ne Zaune a katafaren falon ta, na gidan da ta siya, ta ci Ado tayi masifan kyau hannun ta rike da roban ice cream Tana Sha hankalin ta kwance. "Ranki ya dad'e Kaya fa sun iso. "Ok James ka tabbatar sweet 18 ne don kasan ni na fi bukatar Wanda basu San har ka ba Wanda ni da Kai na Zan d'ora su akan hanya. Don sunfi kawo kud'i don kasan ni bana wasa da kud'i. "Eh Hajiya na tabbatar Kuma baki da matsala, Zaki samu yanda kike so. "Ok a Kira mun Hajiya Laila kace Mata Kaya sun iso. "Ok ba damuwa Hajiya. Juyawa yayi ya fita ita Kuma ta jawo wayar ta ta fara chatting. "Ma ana Kiran ki a waya." "Waye ne,? A duba a gani in Ina da appointment dashi to ayi received in Kuma Babu ayi rejected. Tana gama Fad'in haka ta tashi ta haura sama Tana tafiya cikin k'asaita da Isa irin na Manyan Mata. (Niko nace lallai Khausar kin samu duniya, Sister Adama da sister Nafeesat ya kuka ga Mutuniyar taku ne🤣). Zaune take ta zabga tagumi, gaba d'aya ta shiga cikin tunani, Murjanatu ne ta shigo ta dad'e a tsaye Tana kallon k'awar tata da gaba d'aya ta rame kamar ba ita ba. "Haba sweet Zahraty Kinga tunanin Nan naki Yana Neman ya shafi karatun ki, please Addu'a ya kamata ki dunga yi ba Abunda yafi karfin Ubangiji insha Allah Mami zata warke. Rungume ta Zahra tayi tace "nagode Sosai my Jannat insha Allah na dai na tunani, Zan Yi k'okari gurin mik'a lamurana ga Ubangiji. ************************* MAIDUGURI Sosai Bintu take jin jiki don Ciwon yau da ban na gobe da ban, ga cikin ta sai k'ara girma yakeyi tamkar Wanda zata haifi Yan biyu. Yagana ne ta tasa ta a gaba Tana kuka."yanzu gaba d'aya Bintu kin canza an rasa gane kan Ciwon dake damun ki, Dole Zan koma gurin Boka don wannan Ciwon da alamar tanbaya Abu yak'i ci yak'i cinyewa, ko mak'iya ne suke so suga bayan mu. Ta k'arisa maganar Tana share hawaye, ta fice a D'akin da k'udirin yau zata gidan Boka taji Mai ke damun Bintu. "Kar ma ki k'ariso Nan Yagana nima Ina cikin rud'ani da fargaba domin da Alamu aikin mu Yana Neman warwarewa domin Aljani d'an tsito yazo min jiya a rud'e jikin shi a k'one Yana fad'a mun akwai matsala babba. Zaro Ido Yagana tayi "Boka ka taimakeni kar Asirin mu ya tonu. Juyawa tayi ta tafi Tana kuka a hanya, Dole yau taje k'auyen Zulum don taji kamar ance Asabe ta dawo, Dole taje taji wani Mafita zasu samu. ************************* PLATAEU STATE Zaune take hannun ta rike da hisnul Muslim tanayin Azkar, kaman an tsikareta ta tashi ta shiga d'aki ta d'auko wani Akwati kato, ta bud'e kayan jarirai masu kyau ta dunga fitowa dashi Tana cikin fitowa dasu wani pic da Envelope ya fad'o a ciki, da sauri ta d'auki Envelope din ta fara bud'ewa. ************************* ZARIA BIRNIN ILIMI Garin da ba Zazzau ba dajin Allah karfa kuce na so garin mu da yawa🙈🙈🤣🤣🤣. Sosai Mami take jin jiki duk da Baba Suwaiba na tsananin kula da Mami, Amma Mami Bata ganin Abun da take mata, kullum k'orafi haka Baba Suwaiba take hakuri da ita. Wataran karfe Sha biyun dare aka tashi da wani firgici, Wanda kawai aka ga gidan Su Mami ya fara kamawa da wuta. Gashi daga part din Mami ne wutan ya fi ci, Baba Suwaiba ne ta fito a rud'e Tana buga gidan kusa dasu Tana ihun a taimake su wuta a gidan su. ************************* KANON DABO "Ok ka tabbatar suna cikin gidan James.? "Eh Hajiya na tabbatar. Kuma ita Yar Uwar taki Bata dawo ba sai gobe kin San yau sukayi celebrate na kammala karatun su." "Ok good haka nake so kace musu zasu ji Alert gobe. Zaka iya tafiya. "To Hajiya angama. Juyawa yayi ya tafi, Yana tunani a Zuciyar shi, wannan wani irin rayuwa ce kice a Kona gidan ku.....✍️✍️✍️✍️✍️✍️ Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰. *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM PAGE 20 Zagaye d'akin ta takeyi, daga ganin ta kasan tana cikin damuwa. Zama tayi a gefen gadon dake bedroom d'in tana share hawaye a hankali ta furta "Sorry Mamin mu dole ne tasa na kashe ki don bana buk'atar jin Asalina don inaji a jiki na bani da Asali Mai k'yau daga yanayin halayya ta da d'abi'una. Nasan tabbas ni ba Yar halak bane, don duk Yar halak bazata aikata Abun da nake aikatawa ba. Tana gama Fad'in haka ta fashe da kuka, "Allah sarki masoyiyata Mai K'yakk'yawar zuciya Har a cikin Rai na ban tab'a tsanar ki ba Asali ma Ina son ki Allah ya Bayyana Miki Asalin ki ya Aurar daku ke da Yaya Sadeeq, don nasan ke kin fito daga Asali Mai k'yau k'addaran ki ne yazo Miki a Haka. Tashi tayi ta fito falo wayar ta ta d'auka da yake kan kujera, Kira ta fara yi ringing D'aya tayi aka d'auka, "Hello James Ina so ka bincika mun Halin da y'ar uwa ta take ciki ta koma gida kuwa,? Sannan Mami ta mutu ko Tana da rai.? Yanzun Nan fa nake buk'atar jin komai, tana gama Fad'in haka ta kashe wayar ta. ZARIA BIRNIN SHEHU ************************* Haka mutane ke ta watsa ruwa kaman ana k'ara wutan ne. "Don Allah ku taimaka ku fito da Hajiya tana ciki. Tana cikin maganar sai ga wasu sun fito da Hajiya duk ta kone, Haka akayi Asibiti da ita ana Zuwa likitoci suka Anshe ta sukayi Emergency da ita. Washe gari doctor yace Yana Naiman Yan uwanta Yana son magana dasu, baba Suwaiba tace "sai dai in baka Number yarinyar ta ka kirata. Zahra shigowar ta layin kenan a Motar ta da Yaya Sadeeq ya bar Mata taga gidan su a k'one. "Innalillahi wa'innah illaihirraji'un Mai ya faru ne, wani mak'ocin su ta hango ta fito da Sauri Tana tanbayar shi meya Sami gidan su.? Duk Abunda ya faru ya kwashe ya fad'a Mata, wani jiri taji ya fara d'iban ta, nan da Nan ta zauna ta fara fad'in Innalillahi wa'innah illaihirraji'un Allahumma ajirni fi musibati wa aklif ni khairan minha. Haka ta dunga nanatawa har taji ta samu Natsuwa a Zuciyar ta. Ta shiga Motan ta kenan taji Kiran likita tace mai gatanan Zuwa ma. Bayan ta Isa doctor yake cemata gaskya sai anyi ma Hajiya Aikin fata don wannan fatan nata gaba d'aya ya lalace, Kuma likita d'aya ne yake zuwa yin aikin duk shekara, ya kusa Zuwa Kuma a k'allah kud'in zai Kai Naira Miliyan biyar. Zaro Ido Zahra tayi don gaba d'aya kud'in da ke hannun ta ko Miliyan d'aya Bai Kai ba, Gashi kud'in da Yaya Sadeeq yace zai tura Mata Basu shiga ba ko sau d'aya Kuma ta dunga Kiran wayan shi baya shiga. Fita tayi a Asibitin jikin ta a Mace, komawa Mota tayi ta zauna ta fara tunanin ya zatayi, tunawa tayi da Zinaran ta da Yaya Sadeeq ya siyo musu lokacin da yaje Dubai, ita kala hud'u ya siya Mata yace ta b'oye kar Mami ta gani da sauri ta kunna Motar ta juya taje gida, tana Zuwa d'akin su ta wuce tunda ba ko Ina ya k'one a gidan ba, bincike ta fara yi a drawer ta, da k'yar ta ga guda biyu Bata ga sauran ba. Da sauri ta Nufi kasuwa don siyarwa. "Hajiya gaskiya da Zan baki shawara karki sayar da Zinaren kin nan." Don ainihin masu kyau ne zai Kai kimanin Naira Miliyan d'ari duk guda d'aya, ni a yanzu ma Banda kud'in da Zan siya. "To Alhaji don Allah ka taimakeni ka rike sarkan Nan duka ka bani Aron Miliyan biyar Mahaifiya ta ce a Asibiti za'a Mata aiki, insha Allah Zan kawo maka kud'in ka in karb'i sark'ata. "Ok ba damuwa, Hudu ka Bata Miliyan biyar. "Nagode Sosai Allah ya saka da Alheri. "Ba komai Hajiya, don Allah ko Zaki iya bani phone Number na ki,? Sunana Aliyu ana ce mun Haidar nine Mai shagonNan. Ya k'arishe maganar Yana Mata murmushi Mai birgewa, tabbas Aliyu ya had'u don black beauty ne ga Lulu eyes ga sajen shi da ya k'ara k'awata fuskan shi, Wanda dogon hancin shi ya k'ara fito da k'yawun shi ga dimple din shi, Kai in tak'aita muku Aliyu Haidar ya had'u ko ta Ina. Samun Kai na nayi da mayar mishi da murmushi nima. "Ba damuwa ga card d'ina nan, ta mik'a mishi dai dai lokacin da aka kawo k'udin ta karb'a ta k'ara mishi godiya. Tana tafe a hanya tana Murmushi ita k'adai tabbas mutumin Nan Yana da kirki Sosai ba don shi ba da sai dai ta rasa Mamin ta Wanda ita kad'ai ta rage mata yanzu take gani taji d'adi. Bayan ta biya kudin ne taje d'akin da aka kwantar da Mami ta tarar da Baba Suwaiba tana gyara mata kwanciya. "Sannu baba Suwaiba nagode Sosai da hidima. Sannu Mami ya jikin.? Duk da Ciwon da Mami keyi but bakin ta Normal ne Ciwon Bai Kama mata baki ba. "Lafiya lau Yar Albarka," sai ta fashe da kuka "Zahra ki yafe mun duk Abun da Nayi miki. Yanzu kin samu kin biya kud'in aikin.? "Haba Mamin mu karki damu ba komai, komai ya wuce naje na biya kud'in aikin, Nan ta kwashe yanda ta samu kud'in ta fad'a ma Mami. Albarka Mami ta dunga Sama ta da Neman gafarar ta. ************************* KAUYEN ZULUM .......Sauri take tayi bani da Sauri Ba kasancewar Yamma tayi Kuma hanyar k'auyen ba'a cika Samun Abun hawa ba, ga matsala rashin tsaro da K'asar mu ke ciki. "Yauwa

Chapter 5 of 11