ya k'ariso ya rungume Daddy ya bashi peck a goshi, ya koma gurin Mamin su da take ta zuba murmushi take kallon d'an nata cike da so da k'auna da kulawa.
K'arisawa yayi kusa da Mami ya rungume ta "I miss you Mami.
"Miss you too my sweet Son.
"Au ni bakayi Missing d'ina ba, my Yaro na.?
"Sorry Daddy na. To ku kuma duk kun wani k'ame kaman Sojoji baza Kuzo ku yimin well come ba.
Da sauri Khausar tazo ta rungumeshi tace "well Com my sweet brother we miss u too.
Kallo ya maida kan Zahra da ta tsaya ta kasa daga kan ta. Kura mata ido yayi, da k'yar ya tattaro ragowan kuzarin shi, yace mata "Baby Zahra baza kimun Well come d'in bane.? K'arisowa gurin shi tayi sai ta duk'a zuwa k'asa tana fad'in "ina yini Yaya Well Come back. Kafin ta kai k'asa ya d'ago ta ya rungume ta a tare suka saki ajiyar zuciya.
"I so much miss you my one and only lovely sister. Duk a cikin kunnin ta ya rad'a mata wannan kalaman. Shiyasa su Mami basuji ba.
"To Son sake ta Muje Mana. Dare nayi duk da Zaria da kaduna ba wani nisa bane.
"Ka barshi kawai Daddy Yara, ni fa Abun Son mamaki yake bani inda yake Nuna banbanci a tsakanin Yaran nan. Haba don Allah to ni ban son haka. Har suka karisa Mota Mami tana Fad'a har sai da Daddy ya dakatar da ita tayi shiru.
************************
Sun isa gida ana kiran Magriba.shiyasa suna isa su Daddy da Yaya Sadeeq suka wuce Masallaci, su kuma Su Zahra suka wuce cikin gida don yin nasu Sallah.
Sai da sukayi Sallah isha'i sannan kowa ya hallara a Falo don cin Abincin.
Suka zauna suka fara cin Abinci. Bayan sun gama ne. Suka fara hira yaushe rabo, duk wanda ya gansu yasan Happy family ne.
"Yauwa Daddy gobe insha Allah ina so in shiga cikin City gurin Guggo.
"Ok tunda Lahadi ne sai ku tafi da k'annin ka. Tana ta korafin sun rabu da zuwa gaishe ta.
"To shikenn Daddy Allah ya kaimu, Amma islamiyan fa.?
"Zan kira Islamiyan in sanar bazasu samu zuwa ba. Ai hakan yayi.?
"Eh yayi Daddy. Yauwa tsarabar ku yana cikin d'aki Zahra ki d'auko muku sai Mami ta raba muku ke da Khausar.
"To Yaya." Mik'ewa tayi da nufin zuwa d'aukowa.
"Zahra dawo. Ku barshi sai da safe.... Ku tashi kuje ku kwanta kar ku manta kuyi Addu'a. Mami ta Fad'i haka fuskan ta d'aure ba wani alamun walwala a ciki.
Daddy ya tashi "to ni zan shiga ciki, kar dai ki manta da abunda na fad'a miki satin da ya wuce. Bayan ya gama fad'a mata yayi shigewar shi ciki.
Yayin da Mami gaba d'aya jikin ta yayi sanyi ga k'oshi ga kwanan yunwa, don tana Matuk'ar son Auren ta, kuma tana san Daddy kaman yadda take son rayuwar ta. To Amma ya zatayi da Alk'awrin da ta d'aukar ma kanta cewa Khausar bata da Miji sai Sadeeq don ta haka ne kawai zata cika B'oyayyiyar burin ta. Gashi Daddy yana so ya hanata cika burin ta, Kai akwai Matsala fa.
"Mami matsalar mene.?
Figigit tayi don batayi tunanin Maganar ta fito fili ba. "Son ina cikin Damuwa ka tayani da Addu'a kaji.
"Mami Damuwar mene? Ki fad'a mun abun da ke damun ki, kin san duk d'a na gari bazai so yaga Mahaifiyar shi cikin damuwa ba.
"Sorry my Son kawai ka tayani da Addu'a komai zai warware insha Allah.
"To shikenn Mami Amma don Allah kicire Damuwar nan a ran ki.
"Karka damu d'an albarka farin ciki na ina alfahari da Haihuwar ka.
*************************
Washe gari
Wasu had'addun takalma ne da dogayen riguna masu kyau ya siyo ma su Zahra kowa bibbiyu. Uku Mami taba Khausar taba Zahra D'aya tace mata. "Ke ai irin wad'an nan kayan ba so kikeyi ba. Asali ma ba son kwalliyan kikeyi ba gara a ba wanda tasan darajar kwalliya.
Wani takaici ne ya rufe Zahra kaman zatayi kuka, kuma duk masu kyau ta kwashe ta ba Khausar ko bazata sa ba ya kamata a bata tunda hakk'in ta ne.
"Amma Mami ina son kayana ai kuma ni bance bazan sa ba. Kuma hakk'ina nane. Mami ko dai ba ke kika Haifeni ba.? K'iyayyar da kike Nuna mun yayi yawa Haba don Allah.
"Ke baki da hankali ni kike Fad'a ma haka Zahra yaushe kika zama Mara kunya.? Duk duniya kina da Uwar da ta wuce ni ne, in d'au cikin ki wata Tara in haifeki in rai ne ki, sannan ki bud'e baki ki fad'a mun haka. Mami ta karishe Maganar cikin fushi.
"Don Allah Mami na kiyi hakuri ban Fad'i haka da nufin in bata miki rai ba don Allah ki yafe mun.
" naji ku tashi kuje ku shirya kar Yayan ku ya shigo baku shirya ba, kuma saura ki fad'a mai abun da ya faru. ✍️✍️✍️✍️✍️
More comment more typing
Comment
Share
Vote
Like
Yar mutan zazzau ce😍😍😍
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
B'OYAYYIYAR
K'ULLI 😭😭😭
STORY
AND WRITTEN
BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B'OYAYYIYAR K'ULLI.
DEDICATED
TO
TO B'OYAYYIYAR K'ULLI FANS INA YINKU IYA WUYA YANZU NA FARA JIN KWARIN GWIWAN TYPING KUN SAN COMMENT NA ZABURAR DA WRITERS. LOVE YOU LODI LODI 💖💖💖.
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKEEL.
(Our problem 2 )
PAGE 5
*************************
"Insha Allah Mami bazan fad'a ba.
Khausar ne ta bita da Harara had'i da tab'a baki. "Wai ni Mami meyasa ki haifemu tare da wannan yar kauyen.? Komai nata sai tayi kauyanci, kwata_kwata bata waye ba kamar ba jinin ki ba. Nifa ji nake banjin ko d'igon son ta a rai na.
"Ke Khausar!! Ashe baki da hankali ban sani ba. To Zahra yar uwan ki ce duniya da Lahira baki da kamar ta don ciki d'aya kuka fito ke da ita. Kar in kara jin haka.
Kuka ta saka. "Haba Mami shine zaki wani rufeni da fad'a don na Fad'i Abun da ke zuciya ta. Tashi tayi cikin fushi had'i da tab'ara zata tafi. Da Sauri Mami ta rungumo ta jikin ta.
"Haba yar lelen Mami kiyi hakuri kin san ban son in ga kina fushi. Kece kika b'atamun rai kin san in Daddy ku yaji wannan zance duka daga ni har ke bazamu ji dad'i ba, kuma ni zai d'ora ma laifi karshe ma yace in bar mai gidan shi. Kin san Daddy ku bai had'a ku da kowa ba da komai a duniya kullum burin shi yaga kan ku a had'e yaga kuna son junan ku. To yanzu ke a tunanin ki in har Daddy ku yaji abun da kike fad'a, sai ran mu ya b'aci.
"Insha Allah Mami bazan kara ba kinji Mami.
"Yauwa Ke Khausar kun shirya ne ku fito mu tafi. Ina Zahra.?
"Kai Yaya har ka shirya bari in je kaya kawai zan sa na riga nayi wanka, Sister ma nasan ta shirya tunda ita shirin ta ba wuya yakeyi ba.
"Ok ku Sameni a Mota. Ya wuce yaje ya tsugguna a gaban Mami.
"Mami na kin tashi lafiya.? Da fatan kina cikin koshin lafiya.?
"Ina lafiya lau yaron kirki meya hanaka fitowa muyi breakfast.? Ya kuma gajiyar tafiya.
"Lafiya lau Mami Wallahi gajiya da barci ne ya hanani. Kuma ina son inje insha Kokon Guggo mai dad'in nan, saboda nayi Missing din shi daga nan ince ta koya ma su Zahra saboda suzo su dunga damamun kinga na huta da zuwa can sha.
"Kai Yaron kirki Lallai Guggo ta iya dama Koko, da Alama dashi zata siye Zuciyar Mijin nata.
"Ai kaman kin sani Mami. Ya Fad'i haka yana Mik'ewa, "to Mami na sai mun dawo.
"To a dawo lafiya dan Albarka. Allah ya tsare mun ku ya dawo mun da ku lafiya.
"Ameen ya Allah Mami, don Allah kice musu suyi sauri su fito don na kosa in ga Uwargida ta.
"Ok gasu nan bata gama rufe baki ba sai gasu sun fito, sunyi Matukar kyau don kaya kala d'aya suka sa, haka gyale ma sai dai gyalen Zahra kato ne ta lullubashi a kanta har jikin ta. Sabanin na Khausar da yake k'arami a kafad'a ta d'ora shi.
"Masha Allah yaran Daddy sunyi kyau, sai ina za'a da Safen nan.?
"Daddy Zamu gidan Guggo ne cikin City.
"Daddy su ka manta kenan na fad'a maka zasuje.
"Ke dai Bari Mamin Yara wallahi na Mance. To a dawo lafiya a gaidamun ita da kyau, ku cemata insha Allah inanan shigowa.
"To Daddy, Mami mun tafi sai mun dawo suka Fad'i suna ficewa daga Falon.
Tun da suka doso idon Sadeeq na kan Zahra inda tayi mai wani Masifan kyau, duk da Khausar tafi Zahra komai, Amma shi kawai Zahra shi yake hange in ta doso tana disashen duk wani kyawu na y'a Mace a idon shi.
"Yaya tunanin mai kakeyi muna ta Magana kayi shiru.?
"Oh sorry ban san ma kun kariso ba. Ke Khausar ban fad'a miki cewa in Zamu fita ki dena Hawa front seat ba,? koma baya Zahra dawo gaba.
Fita tayi tana zunburo baki.
"Yaya Sadeeq da ka barta a gaban ni in zamu dawo sai in hau gaban.
"Shut up dama shawaran ku nake Nema. Zaki dawo ko sai ranki ya B'aci ne.? ai a tsorace sukayi exchange na seat don sun san halin Yayan nasu baya musu da wasa.
Tun da suka fara Tafiya idon shi a kan Zahra yake, ganin inda ta d'aure fuska, haka da ya leka khausar ita ma. Murmushi yayi "Haba my Twince Sisters d'ina fushi kukeyi da Yayan naku kun san bai jure ganin kyakkyawan fuskan ku a d'aure. Ku muje Apple white kusha Ice cream. Sai mu wuce.
Suna jin haka sai kowa ta fara Washe baki don suna matuk'ar don Ice cream, karma Zahra taji.
"Hello Guggo kin tashi lafiya.?
"Lafiya lau Habibullahi, ya yaran naka, wai mijina ya dawo kuwa.?
"Eh Guggo ya dawo jiya suna hanyar zuwa ma gidan ki yanzu haka.
"Kai kai har da Yan biyu kyautar Allah, kace Zama bai ganni ba bari in tashi in tarbi mai gida, don ni ban ta kishiyoyi.
Dariya Daddy yayi.
"Yauwa Hajiya Guggo ina neman wani alfarma gareki, ko da Sadeeq ya tambaye ki wata Magana game dasu don Allah kar ki Bayyana musu B'OYAYYIYAR K'ULLI nan.
"Ikon Allah Habibullahi mai ya kawo wannan zancen kuma,? Nayi tunanin an dad'e da rufe wannan babin.?
"Maganar Bazai yuwu ta waya ba, Amma sai na shigo unguwar✍️✍️✍️✍️🤣
Share
Comment
Like
Vote
ZEEY YAR MUTAN CE😍😍😍😍
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B'OYAYYIYAR
K'ULLI 😭😭😭
STORY
AND WRITTEN
BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B'OYAYYIYAR K'ULLI.
DEDICATED
TO
DILLALAI FAMILY
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
INNALLAHA MA'ASSABIREEN.
(Our problem 3 )
PAGE 5
*************************
Sun isa gidan Guggo karfe Tara na Safe. Tun daga kofan get d'in gidan su Zahra suka fara kwala ma Guggo kira.
"Y'ar tsohuwa.! Y'ar tsohuwa.!
"Oh Ni Fadimatu wa'innan fitinannun Yaran sun iso kenan. Ta Fad'i haka tana fitowa daga falon ta.
Rungume su tayi duka su biyun tana jin k'aunar su a cikin ran ta.
"Munyi Missing d'in ki kwana biyu, muna ta cewa Daddy ya kawo mu bai kawo mu ba.
"To ba gashi yanzu Yayan ku ya kawo ku ba.
"Wai ni haka a ke tarban Mijin, kin wani shareni sai ta kishiyoyi kikeyi.
"Wayyo Yi hakuri Mijin. Sakin su tayi taje ta rungume shi, mu shiga ciki na tanadar ma hadadden Kokon ka yasha kayan kamshi.
"Yauwa my sweet Uwargidas. K'arisawa cikin Falon sukayi. Falon komai tsaf saboda Hajiya Guggo akwai tsafta komai nata tsaf_tsaf ne. Zazzaunawa suka yi a falon kowa ta ciro Ice cream din ta ta fara sha.
Guggo kuma ta shige kitchen, sai gata ta fito da Jug a hannun ta da kananun Cup, ta ajiye musu ta kawo musu k'osai yaji kayan miya da yaji.
Duka suna ganin K'osan suka ajiye Ice cream d'in suka sauko suka Baje a falon. Zahra ta Zuzzuba musu Kokon a Cup ta mik'a musu ita ma ta zauna suka fara sha. Suna sha suna Santi.
Bayan sun kamnala sha ne, Suka kwashe kayan sukaje kitchen, Zahra na wankewa Khausar na d'aurayewa tana sasu a inda ya dace. Har suka gama suka gyara komai na Kitchen d'in.
"Guggo don Allah ina son muyi wata Magana ko zamu je baya ne.?
"Lafiya dai ko Mijin.?
"Lafiya Lau akwai Abun da ya shige mun duhu ne. Nake son k'arin Bayani.
"To shikenan muje, ka d'auko mana kujerun Roban nan sai mu zauna a kai.
"Angama Hajiya kin san ni mijin Hajiya ne ai, sai abun da kika ce. Ya Fad'i haka yana dariya.
Bayan sun Zauna ne. Hajiya Guggo ta dubeshi tace mai. "Ina jin ka mai gidan.
"Guggo don Allah ki Fad'a mun Mami da Daddy su suka Haifemu gaba d'ayan mu ba wanda yake bare a cikin mu.?
"Sadeeq Lafiyan ka kuwa,? meyake damun ka? Meya kawo wannan shirmen.
"Ke k'adai ne nake da kwarin gwiwan da zan fad'a ma abun da ke Damuna, Wallahi Kaka tun da aka Haifi Zahra nake mata wani Mahaukacin so, na zata kawai irin So ne na jini na Yaya da K'anwa sai yanzu da Zahra ta k'ara girma na kara tabbatar da Son Aure Nake Mata, So kuma na har Abada wanda bazan iya jure Kallon ta da wani D'a Namiji ba a Matsayin Miji in ba ni ba. Don Allah ki taimaka ki Fad'a mun, in har Zahra Cikin mu d'aya da ita mai zai sa inji haka. Don Allah ki Fad'a mun Kaka ta. 🙏🙏
"Haba Sadeeq wannan wani irin Hauka ne.? Rana tsaka zaka zo ka tada mana hankali ina ka taba jin anyi wannan kwamacala.? Kar in karajin wannan maganar kaji koh.? Ko Mahaifiyar ku ban yarda taji Maganar nan ba, tashi kaje ka d'auki K'annin ka ku tafi.
Jiki ba kwari ya tashi, idon shi yayi jajawur.
Da sauri Khausar ta bar bakin Kofan bayan ta gama jin duk Abun da ya faru tsakanin Yaya Sadeeq da Kaka.
"To me hakan yake Nufi,? Shin dama yawan kulawar da Yaya yake Bama Zahra, da yawan goyan bayan ta da yakeyi dama Son ta ya keyi. Innalillahi Allah gamu gareka wannan wani irin Jarabawa ne Allah zai D'ora musu, ace jinin su kuma yana son Yar uwan ta, kuma kanwar shi Ciki D'aya. Dole Mami taji Labarin nan domin ta d'au Mataki.✍️✍️✍️✍️✍️
Comment
Share
Like
More comment more typing..!
Zeey yar mutan zazzau 😍😍😍😍
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B'OYAYYIYAR
K'ULLI 😭😭😭
STORY
AND WRITTEN
BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B'OYAYYIYAR K'ULLI.
DEDICATED
TO
Kamal bakano😜😜
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
ALLAHUMMA ANTA RABBEEY LA'ILAH HA ILLA ANTA KHALAK'ATANI WA ANA ABDUKA WA ANA ALA AHDIKA WAWA ADIKA MASTAD'A ATIKA FAGFIRLEEY FA INNAHU LA YAG FIRUL ZUNUBA ILLAH ANTA. 🙏🙏
(Continue )
PAGE 7
*************************
Sun kama hanyar gida kowa da abun da take sak'awa a ran ta, Yayin da shi kuma Sadeeq tuk'in kawai yakeyi Amma baya cikin hayyacin shi. Ikon Allah kawai ya kai su gida. Haka kowa ya fita shiru_shiru, shiga sukayi Falon Had'i da Sallama, Tarar da Falon sukayi ba kowa Alamun Mami bata a Falon. D'akin su suka wuce suka fara ciccire Mayafan su. Khausar duk ta kosa taje gurin Mami ta Fad'a mata abun da ke faruwa. Fita tayi Zahra na mata magana ko kallon ta ba tayi ba ta fice.
D'akin Mami direct ta Nufa, ta kama Handle d'in kofan zata Bud'e sai taji kamar Mami na wani Magana. Dakatawa tayi don Zahra tayi lafiyar yin lab'e.
"Kina jina koh Hajiya Halima Wallahi ina cikin Damuwa don da alama burina bazai cika ba, domin kuwa Alhaji Habibullahi yana neman kawo cikas a gurin cikar Burina. Kin san dai Plan d'in da muka shirya a kan Cewa zan Aura ma Sadeeq Khausar. Saboda Khausar tafi Zahra wayo da komai, ita zata Zama tsani na cikar Burina. To Wallahi Alhaji Habibullahi ya ce duk randa na furta wani Abu da zai Bayyana B'OYAYYIYAR K'ULLI a bakin Aure na, Hankali na ya tashi na rasa meye Solution.? Ok shikenan sai kin zo. Kashe wayar tayi ta fara Zagaye d'akin cike da damuwa.
"Tabdijam Aure kuma nida Yaya Sadeeq. Wai meke shirin Faruwa ne wannan wani irin kwamacala ne kodai akwai Abunda su Mami suke Boye mana ne. Tabbas koma meye sai na binciko shi. Juyawa tayi ta fasa shiga D'akin ta koma D'akin su, Tarar da Zahra tayi tana duba takardun ta.
"Sister wai Yaushe ne za'a Fara Exam d'in.?
"Wannan Weak d'in da zamu shiga, Amma Sister wani Course kike son yi ne in mun ci Jamb din mu.?
"Ina tunani Kamar genocolgy zanyi fa. "Masha Allah Course d'in nada matuk'ar kyau kice Sister nawa Likitan Mata zata Zama. Allah ya bada sa'a. "Ke kuma mai Zaki karan ta.?
"Ni ina son in gaji Daddy ne Law nake son karantawa tunda Yaya Sadeeq yaki ya cika ma Daddy Burin shi, shine nake so ni in cikamai.
"To Allah ya cika mana burin mu duka, bari inyi wanka. "Ok sai kin fito.
*************************
Wata Hamshakiyar Mata na hango tana Zaune a kujera ta Dora kafa d'aya kan d'aya, ga fruit a gaban ta tana sha. Ga wata yarinya a gefen ta tana Matsa mata kafafu.
"Ke je ki d'auko min ruwa cikin fridge."
"To Momy. Yarinyar da ke Matsa mata kafan ne ta tashi don zuwa kitchen d'auko Abun da wannan Hamshakiyar Matan ta aike ta. Sai a lokacin na kare ma Matar kallo Mace ce Hamshakiyar mai kimanin shekara Arba'in a duniya Fara ce sosai tamkar ka Taba jini ya fita, da ka ganta kasan hutu ya zauna tattare da ita, Kuma Mace ce ita mai Izzah mai son a girmama ta, kuma a girmama Izzan ta, Ba kowa bace Face Hajiya Nafisa Matar Hamshakin D'an kasuwan nan wanda kaf Africa an san da Zaman shi, saboda yawan Companonin shi da gida je da kadarorin da ya Mallakar, Wato Alhaji Bukar Mai Naira ba wanda bai san shi ba.
Sai dai ya kasance bai taba Haihuwa ba duk da yayi Aure_Aure da yawa kowa tazo sai dai ta fita ba tare da ya samu Haihuwa ba.Hajiya Nafisa itace Uwar gidan shi ita kadai ce ta iya jure Zama dashi haka. Ita ma d'in tana Zaune dashi don cikar wani B'OYAYYIYAR K'ULLI nata wanda tana cimma Nasara zata k'ara gaba. Tun Abun na damun Alhaji Bukar har ya hakura ya Fawwala ma Ubangiji.
Sallaman da akayi yasa ta tashi da Saurin ta. "Lale lale da Masoyi shine baka sanar mun kana Hanya ba.
"Kar ki Damu Masoyiya, akwai taron da zamuyi ne na wani Sabon Company na da zan B'ude a Kaduna.
"Ok to mu shiga ciki kayi wanka, in sama ma abin da zaka ci.
*************************
ZARIA
Makaranta ne Babba wanda ta tara d'alibai kala_kala wato Gifat International School makaran ta ne sai wane da wane. Hall ne Babba inda na hango D'alibai cike a Hall din yayin da wasu ke bitan karatu wasu Kuma na hira, Can karshen Hall na hango Zahra tana Zaune ta na karatu. "Lah Zahra dama kina nan nake ta Neman ki. "To in banda abinki Eshart kin san inda zaki sameni ai. "To nidai duk ba wannan ba kin san Abun da wancan figaggiyar mare kunyar Kanwar ki taje tana cewa.? "Sai kin Fad'a."
"Wai Zuwa tayi tana ce ma su Zuhra da Zakiya da Jafar wai Baki da gata kudin ba yan biyu bane shiyasa ma ta fiki Haske aiki kikeyi a gidan su shine Daddy ta ya taimake ki. "Kai Eshart ni wallahi inda Sabo na saba da halin Khausar to mai zai dameki da ita. Yarin ta ne da shirme ke damun ta wataran zata bari. Tashi muje ki rakani Library in duba wani Abu.
"Ni wallahi Zahra kar Allah ya ban hakuri irin naki in zauna k'anwata ta rai nani. Juyawa tayi da sauri tana mai jin haushin Halin k'awar na ta. Zahra tana kwala mata kira ko waigen ta ba tayi ba. ✍️✍️✍️✍️
Like
Share
Comment
More comment more typing
Zeey yar mutan Zazzau ce😍😍😍
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B'OYAYYIYAR
K'ULLI 😭😭😭
STORY
AND WRITTEN
BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
MARUBUCIYAR
GIDAN GADO
WAZAN AURA 1&2
AND KNOW
B'OYAYYIYAR K'ULLI.
DEDICATED
TO
To Maccido Ina godiya Dan uwa Allah ya bar Zumunci.
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM.
HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKEEL.
(Different town )
PAGE 8
*************************
JOS
Kowa ya San garin jos gari ne Wanda in lokacin Damina da lokacin sanyi yayi suna da matsanancin sanyi. To hakan ya kasance lokacin Damina Kuma ba'a dad'e da d'auke ruwan sama da aka kwana a nayi a ka Kuma kusan yini Ana yi hakan ya takura ma mutane da yawa gurin fita harkokin su.Can na hango wata Mata ta rakub'e a jikin wani shago Tana ta rawar Sanyi,gaba d'aya kayan jikin ta sun jike,ga yunwar da take ji har ya galabaitar da ita da k'yar ta ke fitar da Numfashi.wata Mata ne ta k'ariso gurin da take rike da Lema a hannun ta,Saboda har a lokacin ruwan bai Gama d'auke wa ba.
"Subhanallahi Wai Dije a Nan gurin dama kika kwana ga ruwa kina gani me ya hanaki shiga cikin rumfa na ki kwanta gashi da alama har Mura ta kamaki da Zazzabi.taso muje ki cire kayan Nan in baki wasu kisa.bige hannun ta tayi had'i da mak'e Mata kafad'a ,Alamun baza ta bita fa. "Yunwa nake ji banci Komai ba...Kai ciwo. "To naji zo muje in baki Abinci sai ki Sha magani. Ta fad'i haka Tana d'aga.sai a lokacin na k'are Mata kallo K'yakk'yawa ce Sosai Kuma ta Manyan ta Amma duk da haka bai Hana k'yawun ta fitowa ba.Amma ga dukkan Alamu bata da Hankali. Amma duk da haka bata da wani Mummunan Kama. "A'a Hajiya ke da Mutuniyar taki ce.?
"Eh wallahi Habu,ka ganta Nan taje ta kwana waje ruwa ya bige ta ga Zazzabi ya kamata,jiya ni shaf na manta ruwa ya rud'ani na shige gida ban Mata shimfid'a cikin rumfa ba,gashi indai ban Mata shimfid'a sai dai ta kwana a waje Kuma a zaune,gashi kwata-kwata ba zata shiga gida ba,Ina tunanin ita Kuma kalar nata haukan kenan.
"Allah ya yaye Mata,gaskiya Hajiya kina k'okari wannan