Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 11
na, da k'yar Hajiya zata lallasheta. Bayan sati d'aya Hajiya ta shirya Dija tsaf don suje su dubo y'ar uwan ta Wanda ita k'adai ta rage mata a duniya gashi ita Allah bai bata Haihuwa ba shiyasa take matuk'ar son Dija. "Hello rabin jiki yau fa Ina Nan Zuwa Zan kawo miki y'ata da nake ta baki labari Wanda nace Miki tana fama da matsalar tab'in hankali Amma yanzu taji sauki fa. Wallahi kuwa duk shekarun Nan Kuma baki tab'a ganin ta ba, kedai bari kawai ni sai tana mun Kama da Aunty Fad'imatu, bari dai sai munzo Zaki gan ta. ************************* ABUJA Zagaye ta takeyi tana tafi fuskan ta d'auke da Murmushi, "Mamin mu kenan Yar Dubai, Ina Mai tabbatar miki da baki can-canci Zuwa Dubai ba da K'auyen Zullum kika dace, bayan na karya kafafuwan ki sai kije ku had'u da kanwar taki Asabe take ko wace,? Wahalalliyar Uwar ku Wanda Bata iya tarbiya ba tayi jinyar ku, da shi Uban naku da yake k'okari shi uwar ku na warware wa, ok kar in cika ki da Surutu Hajiya Laurat kin San nasan komai, ni Yar k'anwar ki Asabe ce Wanda ta haifeni a yawon ta Zubar d'in ta, ta Kuma tsallake ni ta tafi gantalin ta Legos bayan ta tafka wani b'arnan a gidan da take aiki, bayan taje Lagos duniya tayi mata juyin Masa ta dawo da cuta kala-kala Wanda Uwar ku take jinya, nasan baki San ta dawo ba Koh,? We'll dama bazaki sani ba tunda rabon ki da K'auyen tun lokacin da Daddy ya matsa kuje shine kuka d'auko ni kikayi mishi karyan cewa Uwa ta ta rasu, a hanyar ku ta dawowa kuka tsinci Zahra, shine kika Had'a kika raine mu tare, yayin da ki fifitani a kan ta ni Kuma baki San hakan na matuk'ar b'atamun rai ba, don duk duniya ban da Daddy sai ita sai Yaya Sadeeq sune mutanen da nafi so, Saboda haka a yau Zaki fuskan ci hukunci daga gurin Baby Khausar d'in ki🀣. "Masoyi." "Na'am Masoyiya ta." "A sallami Suwaiba jirgin su ya kusa tashi, sannan a dan kiramun Samuel yazo ya dan karyamun kafafuwan tsohuwar nan yanda bazazu Kara wani Anfani ba. "Haba Khausar yanzu da Abun da Zaki sakamun kenan, Mami ta fad'i haka cikin kuka Wanda tun da Khausar ta fara magana tayi suman wucin gadi.✍️✍️✍️✍️ 🀣🀣🀣🀣🀣🀣Wlh yau tsokana nakeji shiyasa nayi Dan wannan page d'in In kuna son kari anjima ku taimako da Maltina da MadaraπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€£πŸ€£πŸƒπŸƒπŸƒ Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ’– *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. ************************* PAGE 25-26 JOS Hajiya da Dija sun Isa gidan Hajiya Jiddah, sun shiga falon ba kowa sai Karan AC da TV da yake aiki. Dattijuwan mai aikin gidan ne ta fito tana ma Hajiya sannu da zuwa, had'i da ajiye musu drinks a faranti da ta d'auko tare da fad'in "Hajiyar na ciki bari a Kira muku ita. "Barshi bari mu k'arisa cikin kawai, Hajiya ta fad'i haka had'i da kamo Hannun Dija suka haye sama, ita Kuma Mai aikin ta koma kitchen. Sun shiga d'akin dai dai Hajiya Jiddah tana Shirin Mik'ewa ta fito, "kice mun kun iso ma, Ina y'ar tawa,? Kin San tunda kikace mun tana Kama da Aunty Fad'imatu na kosa in......maganar ce ta kasa k'arisawa sakamakon ganin jidda da tayi, jikin ta har Yana rawa tana Nuna ta da hannu,,,,, "Alhmdulillahi ya Allah πŸ™ ka Anshi Addu'a ta ka dawo mun da d'iyata gida, Dija kece? Da sauri ta k'ariso ta rungume Dija. Gaba d'aya Hajiya kan ta ya kulle ta tsaya kallon ikon Allah. "Yar uwa ta Ina kika samo ta,? Tsawon shekarun Nan kina tare da ita ban sani ba, garin ya hakan ta faru.? "Yar uwa ta labari ne mai tsawo mu zauna. "Shekaru Ashirin da d'aya da suka wuce na fito Ina Shirin bud'e rumfa Abinci na ga hadari ya had'u sosai, Ina bud'ewa ruwan sama na b'allewa haka na d'auki lema na dunga kaiwa da dawowa tsakanin gida da rumfa ta, kawai na fito na k'arshe da yake lokacin gari bai gama haske ba kawai sai naji na buge mutum da tukunyar da na ajiye, har naji tsoro Sosai da na haska sai Naga wata a kudundune tana ta rawan sanyi ga ruwa Yana ta dukan ta, Nan da nan na ajiye tukunyar na kamo ta muka shiga rumfa na zaunar da ita. Fita nayi naje na samo Mata wasu Kaya a gida Nan fa ta kafe bazata cire jikakkun kayar ba, sai ta nemi ma da ta gudu, haka na hakura na kyale ta sai na kunna mata wuta na kawo kusa da ita ko ta rage rawan sanyin, tana zaune ni Kuma Ina ta aiki na har yaran da suke taimaka mun suka zo, bayan mun gama Abinci ne Naga tana ta kallon Abincin da Alamu Kuma akwai yunwa tattare da ita, sai Na zubo mata Abinci cikin flate da ruwa na kawo mata sai naga ta bini da kallo ita bata karb'a ba ita bata dai na kallo na ba. Sai na ajiye mata na tafi na cigaba da aiki na, bayan anjima da dad'ewa na dawo naga bata ci ba ga Alamu tana son ci Amma bata San yanda zata cin ba don har yanzu kallon Abincin take, Zuwa nayi na zauna kusa da ita na debo Abinci na mik'a mata Nan ma kallo na ta tsaya Yi, sai da na bud'e bakin ta na zuba mata, shima bata son yanda zata tauna ba balle ta had'iye, in tak'aita miki Yar uwa har cin Abinci sai da na koya mata, na tanbaye ta sunan ta sai tace mun Dija tun daga nan bata k'ara magana ba, sannan ita haukan nata basa son gida duk yadda nayi k'okarin shiga da ita gida to sai nayi wata d'aya ban k'ara ganin ta ba, haka muka dunga rayuwa da ita da dad'i ba dad'i wataran sai in shafe wata uku ban gan ta ba haukan ya tashi kenan haka Zan ta bi lungu da sako Ina cigiyar ta, Amma haka Zan dawo ban same ta ba inyi kuka in share hawaye, Saboda tun ranar da naga yarinyar nan Allah ya jarabceni da son ta, Ashe kina da alak'a da ita, Yar uwa ki bani Labarin meye alakar ki da ita don ni dai a iya sanina baki da wasu y'ay'a ban da Habi da ta Auri dan gidan Aunty Fad'imatu Wanda mu duka mun San basu duniya. ************************* "Tabbas Yar uwa Ina ji a jiki na wannan yarinyar Aunty Fad'imatu ce, wata rana naje Maiduguri kamar yadda na Saba zuwa domin in Kara duba wa ka anji Labarin wani daga cikin Ahalin mu,? Kamar kullum dai haka na dawo ba ko Labarin so ko Mai Kama da su, muna tafiya mun kusa fita cikin garin Maiduguri Naga kamar ana tare mu, lokacin Kuma Asuba ce to kin San yanayin hanyar garin namu sai a hankali, driver na yace mu wuce kawai haka Yan ta'addan nan keyi su samu su farma mutum dai dai munzo wucewa ta gaban wacce take tsayar damu din, na ce ma driver na ya tsaya muji me take so ba don yaso ba ya tsaya, fitowa dukan mu mukayi muka k'ariso gurin ta "Baiwar Allah lafiya Ina Zaki da wannan tsohon ciki haka ga kaya.? Fashewa tayi da kuka tana mai durkusawa bisa gwiwan ta, "don Allah Mama ki taimaka mun, Inna koma gida kashe ni zasuyi dani da Abun da ke ciki na. Ina jin haka nace ma driver na yasa Mata akwati Nan ta a boot, ni Kuma na kamata muka shiga Mota, bayan mun Isa gida da kwana biyu ta kwashe duk Labarin ta ta sanar da ni anan na fahimci cewa tabbas ita din jinin mu ce, don dai mu di'n mun dai na Zumunci da Yar uwan mu ta sanadiyar Mahaifiyar mu da ta kwaso mu ta gudu da mu Jos kasancewar ta ita Yar Jos ce, sai muka tashi bamu San wasu dangin mahaifin mu da yawa ba, sai Yar uwan mu guda d'aya Wanda muke uba d'aya Mace Mai son Zumunci tana Aure ita a Maiduguri ta Auri wani Babban soja inda ta haifi Yara uku biyu Maza d'aya Mace itace Auta Wanda tun da aka haifeta bamu tab'a ganin ta ba Saboda lokacin mun dai na zuwa gurin Yar uwan mu Saboda sabanin da muka samu da ita akan Auren yarinya ta da yaron ta, a haka Kuma sai da akayi Auren ni Kuma a lokacin bana so na fison ta Auri wani Dan uwan Mama na, haka ta dage sai da ta Auri dan Yar uwa ta tun daga nan muka yanke Zumunci da su, bamu k'ara Neman su ba sai wani fad'a da akayi na bokon Haram muka je nida Yar uwa ta muka tarar an Kona gidan su ance kawai an wayi gari ne aka ga gawar Mijin ta da wasu a gidan Wanda ake kyautata zaton sune, haka muka ci kuka muka dawo gida muna Nadaman Abun da muka aikata. Dija taci kuka yayin da su Hajiya ma suke ta kuka gaba d'aya suka rungume Dija suna jin wani son ta a Zuciyar su Saboda irin Soyayyan da suke ma Mahaifiyar ta Mace Mai son Zumunci da Yan uwan ta. "Tabbas a lokacin da kuke tunani Mahaifiya ta da yan uwana basu Mutu ba, mahaifin mu dai ya mutu a wani yak'i da sukayi da Yan Boko Haram, lokacin da aka zo Kona gidan lokacin Yaya Sadeeq shi Yana zaune a Abuja ne yana aiki har da matan shi suna can da Zama, ranar yazo Maiduguri, kawai ji sukayi ana hayaniya a kofar gida Yaya Sadeeq ne ya lek'o kawai sai yaga Yan ta'adda ne suke Shirin Kona gidan su, to dama akwai wani kofa ta baya haka su Umma da yayyina biyu suka d'auke ni lokacin Ina da shekara goma a duniya muka fice ta kofar baya, haka su Umma suka dunga cin gudu ga k'aran Harbe harbe, kawai basu an Kara ba suka ji harbi ya sauka a Kai na dai dai hannu na, ihun da nayi ne da Karan harbin ya k'ara gigita Umma na, ni Kuma bayan an harbe ni kawai na tafi luhh, Sosai Umma ta saka kuka tana girgiza ni tana Kiran sunana, Amma ina basu ankara ba Umma tayi tuntub'e muka fad'i nida ita take ni na dunga gangarawa Rami ga ramin Mai Matuk'ar zurfi, gashi wad'an Nan mutanen sun kusa kamo su, haka Ina kallon su Umma suna kallona suka tafi suka bar ni. Ta k'arisa maganar Tana kuka, cigaba tayi da cewa "tun daga Nan ban Kara sanin inda Kai na yake ba sai bayan wasu kwanaki Wanda ban San ko tsawon kwana nawa bane na farka na ganni a wani had'add'en d'aki ga hannu na da bandage jiki na duk naji rauni, da gudu naji wata Matashiyar yarinya ta fita tana cewa Momy ta Farfad'o, haka suka shigo suna ta mun sannu, haka nayi jinya ta har na warke, na cigaba da rayuwa a gidan cikin kulawa da Soyayya tamkar Yar gidan tabbas su Momy sun min karamci, ana cikin haka yaron Momy ya d'awo daga K'asar India inda tun da ya ganni yace shi ya samu matar Aure. Haka akayi mana Aure muka tare cikin kulawa da k'aunar juna inda Hanifa kanwar miji na take matuk'ar Sona Koda yaushe tana gida na indai Mijina baya Nan har Momy na mun tsiyar na kwace mata Yar Auta, haka muka Kai shekara biyar bamu tab'a haihuwa ba, tun Abun bai damun mu har ya fara damun mu, Momy ne ke lallashin mu, kwatsam aka ce Hanifa zata tafi karatu America, haka muka Yi kukan rabuwa tamkar kafin ta dawo d'aya zata mutu a cikin mu. Tushen bakin cikin______________, Sanadiyar wani rashin lafiya da nayi aka d'auko mun wasu Yan aiki su biyu da Yar Dattijuwa da budurwa Wanda zamu zo sa'a d'aya da ita suna mun Yan aikace aikace Amma ban yarda sumin girki ba, Ashe Ciwon da nake tayi ciki gareni tunda masu aiki na suka fahimci haka sai Naga gaba d'aya sun canza, iya k'okari na Ina kyautata musu Amma Basu taba gani su burin su in bar gidan yayin da Asabe take tuggun in bar gidan ta Auri Alhaji, ita Kuma Yagana burin ta in bar gidan yarinyar ta ta Auri Alhaji, Momy kullum cikin zuwa gidan take domin dubani, ta dunga tanbaya ta Mai nake so, Mai ke damuna, ni har kunya ma nake ji, bayan ciki na ya Kai wata bakwai ne na dai na ganin Asabe na tanbayi Yagana tace mun ai Asabe ta tafi k'auye bata da lafiya, kwatsam ranar wani safe Ina kwance sai ga Asabe tazo mun da ciki kato kamar nawa ta tsayamun a Kai "Aunty ki tashi kiga aikin da Mijin ki yayi mun don shi yayi mun ciki Kuma Ina haifewa Zan ajiye Miki ki had'a ki Rai na da naki don ita ma gidan uban ta ne, Mik'ewa nayi da k'yar na nuna Asabe da yatsa nace "karya kike yi Asabe Mijina yafi karfin ki, na yarda da miji na Ina gama Fad'in haka na shige d'aki na fad'a gado na fashe da kuka zuciya ta tana ta mun wasiwasi akan al'amarin ranar ko Alhaji ya dawo bayan na had'a Mai ruwan wanka na fito naje kitchen don in sama Mai Abun da zaici, don duk halin da nake ciki ban barin masu aiki suyi ma miji na girki, na Fito rike da farantin Abinci don yace in kawo Mai ciki ne bazai ci a Falo ba, dai dai na Kai benen k'arshe naga Asabe ta fito daga d'akin shi taci uban ado cikin ta ya fito yayi Mata kyau kasancewar Asabe shuwa Arab ce farace Sosai don ta fini fari, Nan da Nan naji wani kishi ya turnik'eni Amma sai ban nuna Mata komai ba. Murmushi ta mun tayi fari da Ido tace mun, "Hajiya naje ma rabin Rai na sannu da zuwa ne kuma su gaisa da yaron shi don nasan Namiji Zan Haifa Kinga kuwa mu ke da gida. Ta k'arisa maganar Tana murmushi ta wuce ta tafi, wani kuka ne yazo min Amma haka na danne na shiga D'akin da pant da breziya na fara cin karo a kan gado, ajiye Abincin nayi na juya da sauri ban Kara komawa d'akin ba Wanda hakan shine shiga na d'akin na k'arshe inda da dare Ina cikin barci na naji ihu a cikin d'aki na da sauri na tashi na kunna fitillar d'aki wani mutum na gani kwance kusa Dani daga shi sai gajeran wando ga Kaya Nan ya Zubar ko Ina, da sauri na mik'e jiki na na rawa dai dai lokacin da Alhaji ya shigo, "dama cuta ta kikeyi Fad'imatu, bazan tab'a yafe Miki ba, haka nake binshi nake rokon shi ya saurareni yaki saurara na wayata ya jefo mun yace wad'an Nan text din Kuma fa daga Ina suke.? Jikina na rawa na d'auki wayar Ina dubawa text ne kala kala har Wanda Wai ni na tura Ina fad'a ma wani Ina d'auke da cikin sa, Amma zance na Alhaji ne, haka na duke a gurin Ina kuka Sosai, ana haka sai ga Momy tazo naje da gudu na rungume ta a tunani na Zan samu sauki da fahimta a gurin Momy, ga Mamaki na sai Naga Momy ta hankad'e na fad'i Haka Momy ta rufe Ido tamun korar kare ita da yaron ta suka ce inje in nemi uban ciki na Kuma har Abada kar in k'ara dawowa gidan nan, haka da k'yar suka barni na kwashi wasu kayan da sauran kayan jarirai da Alhaji yasa don ba Abunda ba'a siyama baby ba har d'aki musamman aka gyara ba Abun da ba'a sa ba na yarinya, yace in har na haihu zai Sama ta Fad'imatu Zahra zamu dunga ce Mata Zahra Saboda sunan Momy ne nima sunan Umma na ne Kuma suna na, haka na fita Ina kuka Ina waigen d'aki na Ina fitowa harabar gidan Naga Asabe da Yagana suna shewa suna farin ciki, "Allah ya raka taki gona, kafan gaba ya cin ma na baya. Ahayye duka suka Kara tafawa, girgiza Kai na nayi na tafi bance musu komai ba. Bayan na fito ne na lura wasu mutane na bina shine fa na tare Abun hawa na hau muka dunga yawo na rasa Ina zani shine ya sauke ni a gurin da kika ganni. ************************* "To yanzu Ina yarinyar an haife ta,? Kuma a Ina aka haifeta anan gidan koko ta bar gidan Nan da ciki,? "Eh ta haifi santaleliyar yarinyar ta Mace Mai Kama da ita, bayan zuwan mu da sati uku, komai nayi ma yarinyar an samata suna Fad'imatu Zahra, inda bayan haihuwar Zahra da wata uku aka nemi Dija aka rasa bata ba Dan Akwatin Zahra da kayan ta masu Muhimmaci yake, irin su dan kunnin diamond da mahaifin ta ya siya Mata da wani katon envelope na tarihinta da Dija ta zauna ta rubuta Wai Koda ta mutu a ba Zahra ta gani, had'e da hotunan ta da na yayyin ta Dana ba Dija da katin haihuwar Zahra duka Yana cikin karamin Akwatin, kawai Neman ta nayi da Akwatin na rasa, nayi cigiya Sosai har gidan Radio bata ba Labarin ta, haka na hakura na zuba ma sarautar Allah Ido. "Kawai Ina kwance cikin dare naji kaman ana kirana, kawai na tashi na had'a kayan Zahra a karamin Akwatin na goye ta na fita, tun daga Nan ban k'ara sanin inda Kai na ke ciki ba, ban San yanda akayi na rabu da y'ata ba kila ma ta mutu yanzu, Allah sai ya saka mun tsakanina dasu Yagana sun cutar dani. Kara rungume ta sukayi suna Mai jin tausayin Yar taso tabbas tasha wahalar rayuwa. "To meyasa kike ce Mata Dija Yar uwa,? "Lokacin da na tsince ta ne tace mun sunan ta Dija.............., ************************* ABUJA Ba Imani ba komai James ya karya kafafun Mami Kuma irin karayan Nan rugu rugu Haka Mami tana kuka tana ba Khausar hakuri Amma ko kallon ta Khausar batayi ba ta juya ta shige d'aki ta fad'a gado ta fashe da kuka, "Mami kiyi hakuri Dole ne ki fuskanci wannan hukuncin. Haka ihun Mami na Azaba ya karad'e gidan, bayan an gama la'anta Mata kafa ne suka d'auketa domin tafiya da ita, sai ga Khausar ta fito lokacin kuwa Mami ta sume Saboda Azaba. Sawa tayi aka watsa ma Mami ruwan sanyi da aka fito dashi daga fridge. Firgigit Mami ta Farfad'o tana had'a wani uban zufa. "Mami kiyi hakuri dole ne in hukunta ki akan laifin ki, duk da halin ki Ina son ki, in kinje ki gaidamun da uwa ta da Kaka ta, Zan dunga lek'owa muna gaisawa, ga dubu d'ari nan ku dan rage zafi..........✍️✍️✍️✍️✍️✍️ πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜ Yau dai nasan na biyaku Saboda haka Inga comments da yawa.. In har banga comments ba sai wata satin Zan Kara yin wani posting πŸ€ͺπŸ€ͺ. Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°. *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ Wanna page d'in sadaukarwa ce gareki Kaka Raliyatu duk Wanda ya karan ta yasa ta a Addu'a πŸ™πŸ™. BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. ************************* PAGE 27 ABUJA "James ku dawo da ita. Dawo da Mami sukayi, "gata Hajiya. "Mami Ina kika Kai Yaya Sadeeq,? Tabbas anan na gaza cikawa Yan uwa na burin su na Auren juna, Tabbas kin San inda Yaya Sadeeq yake ki fad'a mun yanzun Nan. "Baby ko kashe ni zakiyi bazan tab'a fad'a Miki inda Sadeeq yake ba, domin ta haka ne nima Zan kuntata miki kamar yadda kika kuntata mun. "Ok shikenan Mami karki fad'a Amma ki sani duk wani motsin ki da zakiyi a kan Ido nane. James ku tafi da ita, sai nazo k'auyen. ************************* MAIDUGURI Zaune yake ya tasa Zahra a gaba ta Zama Mai Tamkar Madubi a hankali tunanin shi na shekaru suka fara dawo Mai, Wai Ina Fad'imatu take, ko ta haihu. Da sauri ya mik'e zai fita dai dai lokacin da Momy ta shigo d'akin hankalin ta a tashe, "Bukar Ina y'ata Fad'imatu da Abunda ke cikin ta kullum sai nayi Mafarki da ita tana cikin wani Hali ita da y'ar da ta Haifa......maganar tace ta mak'ale lokacin da tayi Ido hud'u da Zahra. "Bukar wacece wannan a Ina ka samo ta irin su d'aya da Fad'imatu.? "Momy wannan tanbayoyi haka wanne kike so in Amsa Miki, mu zauna tukun na. Zama sukayi kowa yayi shiru da Abunda yake sak'awa a ran shi, kawai ganin ta sukayi ta fad'o d'akin ko Sallama babu tana kuka Sosai. "Momy Ina Zahraty meyasa tun da na dawo K'asar Nan shekara kusan Ashirin da biyar ban tab'a tunawa da ita ba sai yau, waccan da take Fallon take ta Hauka wacece ita,? Duk maganar da sukeyi Zahra na tsaye na kallon su cikin Mamaki to su suwaye wad'an Nan mutanen Ina Mamin ta ita da suke Asibiti Mai ya kawo ta nan,? Karfin halin tanbayar su tayi tace musu "Su waye ku Nan Kuma inane.? Gaba d'aya juyawa sukayi suna kallon ta an rasa Wanda zai bata Amsa, wayar Hajiya Hanifa ne yayi k'ara da sauri ta d'auko wayar ta kara a kunnen ta "Hello Jannat kin iso ne,? Ok Na turo Hanif ya d'auko ki Yana Airport d'in. Tana gama Fad'in haka ta k'arisa ta kamo hannun Zahra ta zaunar da ita kusa da su, sai ya kasance sun sata a tsakiya. "Yammata ya sunan ki.? "Sunana Fad'imatu Zahra Habibullahi Amma ana kirana da Zahra. Ku su waye Nan Kuma a Ina nake Ina jakata kuma.? Har rige-rigen maimata sunan sukeyi "Zahra Ina Maman ki take.? "Mama ta tana Asibiti a Abuja sakamakon gobara da mukayi ta k'one, ni baku Amsa mun tanbaya ta ba ni Mai ya kawo ni nan.? Duk yanda akayi ya tsince ta Alhaji Bukar ya bata labari, kuka ta fashe dashi tana Fad'in "Ina jaka ta, Hajiya Hanifa ne ta mik'a mata jakar ta fara zazzage jakar wayar ta ne ta fad'o tare da wata farar envelope, da sauri Zahra ta d'auki envelope din ta fara karantawa. "Zahra kiyi hakuri ban so nayi Miki butulci ba na gujeki Amma burina yafi mun ke, ki mance dani a Rayuwar ki karki k'ara tunawa da ko Mai Kama Dani. Tana gama karantawa ta fashe da kuka, "shikenan ni yanzu Banda kowa a duniya, Mami ta gudu ta barni bayan na gama d'awainiya da ita. Jawo ta jikin ta Momy tayi ta rungume ta, tace "karki damu yarinya ki d'aukeni tamkar Kakan ki wannan Kuma ki d'auke ta matsayin uwa, shi Kuma wannan a matsayin uba, dukan su da kike kallo y'ay'a nane Kuma zamu rik'e ki Amana kinji, yanzu ki bi Maman ki ku tafi gidan ta don bazai yuwu ki zauna a Nan ba, Kuma ga yarinyar ta can ta dawo daga kaduna taje bautan k'asa baku wuce sa'o'in juna ba, duk da nasan Zaki girmeta ita d'in girman dare d'aya ce, Amma fa zakiyi hakuri da sarkin k'orafi Dan uwan haihuwar tane da yake su Yan biyu ne, Kuma shidin akwai son girma.... "Kai Momy kin zauna sai ma yarana sharri kikeyi...."karbi nace tayo ma Mama Hanifa dakuwa, yo karya akayi Mai Yana ji da Kai k'ato kaman murhu. "Kinji y'ata tashi mu tafi nasan yanzu haka su Hanif sun koma gida. "Momy Mai yasa bazaku barta a Nan gidan ba, ji nake in kuka tafi da ita Zan iya shiga wani hali. Alhaji Bukar ne yayi wannan maganar da tun da suke magana bai ce komai ba sai yanzu. "Bukar kayi hakuri sai gidan ka ya kintsu tukun Zan iya dawo da Fad'imatu nan don Ina jin tsoron Abun da zai Kara faruwa, ku tashi muje. dukan Mik'ewa sukayi ba Wanda ya k'ara magana suka fice a falon yayin da Alhaji Bukar yaji kamar

Chapter 7 of 11