ba.
************** *********
MAIDUGURI
Yau kwanan Hanif Bakwai a Asibiti bai Farfad'o ba, haka Kuma kowa ya rok'i Zahra taje ta dubo Hanif taki Zuwa, hakan Kuma yayi ma Mama Hanifa ciwo sosai, duk da bata Nuna ma Zahra hakan ba.
Mami ko Sosai take fushi da Zahra ko gaisuwan ta bata Amsawa haka daddy a gidan a gurin mutum hud'u kawai take Samun relief Suma din kawaici kawai suke mata, daga Momy Kaka, sai Mama Hanifa, sai Jannat, sai Fannah Maman Sadeeq, Saboda Sosai jinin su ya had'u da Zahra.✍️✍️✍️✍️
Tom ya zarah zata kasance zata Amince kuwa ko bazata Amince ba,
Ga Kuma Sadeeq da Amaryan shi Zahra'u.
To wannan chakwakiya insha Allah zai kare ne a page na gaba wato page d'in k'arshe.
Taku Yar mutan Zazzau sarauniyar kanawa 😏🙄🤣💃🥰😍💖
Share
Comments
Like.
*'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭
STORY
AND WRITING
BY
ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Wannan page d'in naku ne duk wani masoyi na littafin Boyayyiyar K'ulli son so fisabilillahi Ina yinku iya wuya🥰😍🥰💖💖
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 35
*************************
KANO
..........."James ka tabbatar kayan Nan sun iso, domin bana so a samu Matsala fa.
"Karki damu Hajiya. Ba wani matsala da za'a samu.
"Ok hakan Yana da k'yau."
Wucewa sama tayi Abun ta tana taku d'ai-d'ai.
Waya take dannawa ta d'ora a kunnen ta Alamun Kira takeyi.
"Hello Hajiya Bahijja ya maganar mu ne kin San kayan fa yau zasu iso, kin ce Alhajin zai kirani bai kirani ba, kin San ni ban harka da k'ananun mutane Koh, Ok Alhaji Shamo sunan shi,? Ba damuwa sai ya iso.
Murmushi tayi had'i da cewa, "Alhaji Shamo zaka shigo hannun y'ar, Wanda kayi yunkurin kashewa baka samu dama ba to ita zata kashe ka. Domin sai na d'aukar ma uwa ta fansa.
Niko nace wooh Khausar d'in mu aikin ki na k'yau fa.🤣🤣
*************************
MAIDUGURI
Zuwan Hajiya Jiddah ne da Maman Jos suka tasa Zahra a gaba sukayi Mata tatas sannan suka ce Aure ba fashi Kuma sai ta Auri Hanif.
Momy Kaka tace bazai yuwu a takura ma yarinya ba in bata son shi ya hak'ura.
Hajiya Jiddah tace bata Isa ba Dole ta Aureshi Hajiya Jiddah irin matan nan ne masu zafi.
Sai ya zama kowa lallashin Zahra yakeyi a gidan don ta Amince.
Mama Hanifa har k'asa ta durkusa gaban Zahra tana rokon ta, ta Amince ta Auri Hanif tayi Mata Alkawarin duk randa Sadeeq ya dawo Hanif zai sake ta ta Auri Sadeeq.
Sosai Zahra ta fashe da kuka, Saboda ita kad'ai tasan meke damun Zuciyar ta, ba Wanda zai tausaya Mata ne. Rungume Mama Hanifa ta yi tana kuka Tabbas baza ta tab'a iya kin mata wannan Alfarman ba. Ita wacece da k'anwar Mahaifin ta zata duk'a a gaban ta. Zata faranta musu rai Amma tasan har Abada Yaya Sadeeq shine farin cikin ta, Kuma Nan ba da dad'ewa tasan zata Mutu.
"Na Amince Zan Auri Hanif indai hakan zai sa Ahalina a farin ciki.
Gaba d'aya suka had'a baki gurin Fad'i "Alhamdulillahi."
Ita ko Jannat tashi tayi ta rungume Zahra suka cigaba da kuka.
Alhamdulillahi Hanif ya farfad'o, Kuma anyi mishi K'yakk'yawan Albishir d'in Auren Zahra, Wanda haka ya Kara mishi Samun sauki.
Kwana biyu aka sallamoshi. Sosai Zahra take bashi kulawa duk da ba Wai tanayi ne a son ran ta ba sai don farin cikin Family d'in ta.
Wanda hakan ba k'aramin dad'i yayi ma kowa ba na wannan Family. An tsayar da ranar Auren Zahra da Hanif Nan da wata uku, Saboda zasuje ummara su dawo sannan ayi bikin.
*************************
Sosai Soyayya ta shiga tsakanin Sadeeq da Zahra'u, inda har ya kasance mu'amula na Aure ya shiga tsakanin su. Tun daga lokacin Allah ya dasa ma Sadeeq Soyayyan Zahra'u yake jin bazai iya rabuwa da ita ba.
Bayan sati d'aya........
Sosai Zahra'u take Zazzabi inda take Maman Yara ta fahimci Ciki gare ta, Aiko Sosai su baba Tsoho sukayi farin ciki yayin da gaba d'aya kunya ta rufe Sadeeq da Zahra'u.
Haka dai suka wanzu suna tafiya har sai da suka Kai tsawon wata uku kafin su iso garin Zulum.
*************************
BAYAN WATA UKU
Sosai Zahra ta saki ran ta ta mik'a ma Ubangiji lamuran ta da fatan hakan ya zama Alheri a gareta Amma duk da haka Yaya Sadeeq na nan a ran ta.
Yau suka tashi da Shirin zasu k'auyen su Mami don su k'ara tuntub'an ta akan Maganar Yaya Sadeeq.
Kowa ya shirya ya fito yayin da Hanif ya fito ran shi a b'ace, don ganin yanda Zahra take ta wani rawan jiki akan tafiyar don shi har ga Allah Yana jin ya tsani wannan Sadeeq d'in.
*************************
K'AUYEN ZULUM
Suna isowa garin Zahra'u ta fara Amai Sosai, Nan suka tanbaya wani don Allah suna so a kaisu gidan Maigari.
"Ba damuwa kuzo muje, duk inda suka bi sai an kallesu Saboda yanayin shigan su.
Kasancewar gidan Maigari mak'ota ne da gidan su Mami, hakan yasa ta kofar gidan su Mami suka zo wucewa ji kawai sukayi ance, "Sadeeq Kai ne.?
Da Sauri suka waigo duk da irin Raman da Mami tayi da bak'i da kod'ewa bai hana Sadeeq ya gane ta ba, da sassarfa ya isa gareta ya rungume ta Yana Mai cewa. "Mami meya sameki, me ya kawoki Nan garin.? Dai dai lokacin da Motocin su Zahra suka iso, da gudu Zahra ta fito Motar ko gama tsayawa ba tayi ba.
"Yaya Sadeeq Sadeeq.!!!
Da sauri ya saki Mami ya juya don jin muryan Wanda duk duniya bazai mance da muryan ta ba.
"Zahraty kece haka, kin ga inda kika k'ara girma da gudu ta k'ariso zata rungume shi, dai dai lokacin da Zahra'u ta tare ta, "Malama karki tab'a mun miji. Ta fad'a a zafafe. Kasancewar yanzu taji hausa sosai.
Wani gigitaccen Mari Zahra ta Kai ma Zahra'u, had'i da nuna ta da d'an yatsa, "ke kin Isa kice mun Yaya Sadeeq d'ina zaici Amana ta ya Aureki.
A rud'e Sadeeq ya rungume Matarshi ya d'aga hannu tamkar zai Mari Zahra, ko Mai ya tuna sai ya fasa.
"Haba Zahraty meyasa Zaki Mare ta baki ga bata da lafiya bane.
"Oho Yaya Sadeeq da gaske kenan matar ka ce Koh.? Lallai na yarda Maza baku da Amana ni na tsaya jiran ka Kai har Aure kayi, kawai juyawa tayi zata tafi ta yanke jiki ta fad'i. Gaba d'aya sukayi kan ta.
Yayin da kibd'iyatu tasa ma Sadeeq kuka "dama haka jinsin ku suke da son kansu,? Wlh sai ta koma K'asar su tunda a gaban shi har wata zata mare ta ya k'asa rama mata.
Baba Tsoho ne yayi gyaran murya, sannan duka suka dawo da kallon su gareshi duk da fuskokin su shida Mai gaskiya da Matan shi duk a kulle ne da rawani.
"Ya kamata ku mu tafi gida sai a warware komai a can, tunda an ga juna komai yazo da sauki.
Sun dunguma sun koma gida a babban falon bak'i na Alhaji Bukar suka yada zango, bayan an zauna ne baba Tsoho ya bud'e fuskan shi, Daddy jiki na rawa ya Mike Yana Fad'in, "Baba dama kana raye,? Bai gama Mamaki ba Sai da Mai gaskiya ya bud'e fuskar shi shima,
"Sadeeq.!!
Daddy da Hajiya Jiddah suka had'a baki gurin Fad'in "Ina Khadijatul kubrah.?
"Mama gani nan," cewan Maman Yara da ta mik'e tazo ta rungume Mahaifiyar ta.
"Alhmdulillahi Allah Mai yanda yaso, shiyasa tun da Naga yaron Nan nasan jini nane. Ashe yaron ka ne Habibullahi, Nan da Sadeeq ya kwashe duk Abun da ya faru da shi ya basu Labari, ba Wanda bai mai kuka ba a falon.
Bayan haka ne Mai gaskiya ya fara bada labarin su.....
"Bayan an turamu K'asar Mali da wata biyu, wani dare Ina Zaune a bayan d'aki na a cikin barack Ina yin waya sai naji maganar wasu Mutane suna Fad'in, "ai mun riga mun gama shirya duk wani plan don har oga ma ya Amince za'a yi ma Sadeeq Mai gaskiya sharrin cewan shi dan ta'adda ne. Kunga life in prison, sannan Kuma ni Zan Aure Matar shi.
Sosai hankali na ya tashi na lallaba na koma gida na tarar da Khadijatul kubrah na zaune ta kasa barci. Kiran ta nayi nace ta had'a Kayan mu zamu bar Barack di'n nan, Khadijatul kubrah ta kasance Mace Mai biyayya bata tab'a mun musu a duk Abunda nace mata.
Haka muka bar K'asar Mali muka yanki Daji duk da nasan zamu iya had'uwa da Yan ta'adda, Amma zuciya ta ta kek'ashe akan gara mu Mutu a hannun Yan ta'adda da A b'atamun suna.
Munyi tafiya na tsawon watanni muna tafe muna yada zango, Bayan shekaru Masu yawa muna tafe a daji har Mata ta ta haihu ta haifi Yan biyu, duk wani d'awainiya nida ita mukayi dama muna tafe da Akwatin mu kafin lokacin da mu ka rabu da Akwatin sanadin wasu Yan ta'adda da suka biyo mu, haka da k'yar muka Sha.
Kwatsam wata rana sai gamu a wani had'add'en daji Mai Ni'ima, anan muka had'u da Baba ya gina gida Yana zaune lokacin da muka ga juna munyi farin ciki munyi Mamakin cewan Baba bai mutu ba.
A Nan yake bamu Labarin cewan Yan ta'adda suka d'auke shi, da k'yar ya samu ya kub'uta daga hannun su, Kuma ya kasa gane hanya.
Haka muka cigaba da Zama a dajin Nan tsawon wasu shekaru, kafin zuwan wad'an Nan Yara shine muka samu hanya kunji tak'aitaccen Abun da ya faru damu.
"Ikon Allah,! Ubangiji Mai yanda yaso tabbas kud'iran Ubangiji da buwayan shi ya girmama , shine mai tsara komai yadda yaso.
Allah mun gode ma da ka k'ara had'a fuskokin mu, muna rayayyu.
"Ke Kuma Fannah ga Yar uwan ki nan domin yanayin shigar ta da suturar ta iri d'aya ne da na jikin ki lokacin da muka tsince ki.
"Baba Tsoho ko baka fad'a ba wannan itace k'anwar Mahaifina da ta b'ace Safni don Ina ganin ta na gane ta, domin akwai k'aton pic din ta a ko Ina na cikin gidan Sarauta.
Da sauri Fanna ta taso ta rungume Zahra'u, daga lokacin komai nata ya fara dawowa Nan take ta tuno da komai.
Nan fa kowa ya kaure da Murna, Ashe ma Yar uwa ta na Aure cewar Sadeeq, bayan yaji Labarin komai daga bakin Daddy.
Bayan komai ya lafa da kwana biyu aka k'ara taruwa kan maganar su Zahra.
Baba Tsoho ya fara magana "to ke yanzu Zahra wa kike so cikin Sadeeq da Hanif.?
"Ni Baba na hakura da Yaya Sadeeq don bazan tab'a iya Zama dashi da kishiya ba, gara in Auri Hanif.
Tsalle Hanif yayi had'i da fad'in Alhamdulillahi.
"Haba Zahraty karki mun haka, kin San duk duniya kece Mace ta farko da na fara so.
"Nima tabbas ka Auri Zahra sai ka sakeni na koma K'asar mu in yaso a kashe ni. Cewar Zahra'u, tana gama Fad'in haka ta tashi tayi tafiyar ta.
"To Yaya Sadeeq sai kayi hakuri ka rungumi Matar ka Zahra dai tace ba tayi ehee🙄, taso mu tafi my Zahraty. Mik'ewa sukayi suka fice daga falon, tana fita ta fashe da kuka.
"Haba Zahraty Wai da me Yaya Sadeeq ya fini ne, ko don Kinga shi fari ni bak'i.? Don Allah ki daina kukan nan in ba haka ba nima Zaki sani kuka, haka ya dunga rarrashin ta har sai da yaga ya sata dariya sannan.
*************************
Bayan Wata d'aya
Kowa ya koma gida Yayin da Alhaji ya bama su Daddy kyautan gidaje kusa dasu.
Baba tsoho ya Auri Hajiya Jiddah ba'a wani d'auki lokaci ba suka tare gida d'aya da su Daddy sai dai kowa Sashin shi da ban.
Yayin da ake ta shirye-shiryen Auren Zahra da Jannat.
Bayan wata uku
Yau ne ya Kama dubban jama'a sun shaida Auren Zahra da Hanif Jannat da Mukhtar, Aure ne da ya samu halartan Manyan mutane daga wurare da ban da ban.
Bayan wasu shekaru
Zahra ne na hango d'auke da ciki, ga Kuma wasu kyawawan Yara Nan a falon suna ta Wasa, magazine d'in da ke Hannun ta ta ajiye "ke Momy Hani kun dameni fa, Daddy junior ku tashi kuje kuce ma Mama Zahra'u in tayi girki ta zubo mun.
Gaba d'ayan su tashi sukayi harda Wanda ba a aika ba ma suka fita suna hayaniya.
Yara ne su Biyar Daddy junior shine babba yaron Sadeeq na farko, sai Hanifa Wanda suke ce Mata Momy hani, ita da Fati kanwar junior shekarun su d'aya sai yan biyun Zahra'u duka Mata Hassana da Hussaina.
Sai Momyn Sadeeq da ta k'ara Haihuwa ta haifi Namiji da Mace,
Sai Mami ita ma ta k'ara Haihuwa har uku biyu Maza d'aya Mace.
Nan family sunyi Albrka yayin da farin ciki ya wanzu cikin zuri'a su.
"Aunty Zahraty na shigo Ina ta Sallama shiru tunanin me kikeyi ne haka.?
Hararan shi tayi had'i da jefa mishi magazine d'in hannun ta, "ka ga ka daina cemun Aunty Nan, sannan Ina tunanin rayuwa ce.
"Da fatan ba tunanin Yaya Sadeeq kike yi ba, ya fad'i haka cikin zolaya da Wasa.
"Haba ni yanzu Ina da Wanda ya fi mun my sweet husband d'ina ne Mijina yaro Mai halin manya Wanda ya iya tattalin Mace Allah ya barmu tare 🥰.
"Ameen ya Allah 🙏 Mace ta gari, muje ki bani Abinci in ci, ya fad'i haka Yana d'ago ta.
"Ya kamata ka fara yin wanka tukun na don naji kaman tsami kake yi.
Ta k'arisa maganar Tana dariya.
"Kai Kai lallai ma yarinyar Nan kinci bashi kuwa🙄.
*************************
A gurguje bayan tsawon lokaci Zahra'u da Momy Fannah da duk Ahalin sunje Masarautar Amrish inda suka tarar da komai ya canza har an gina Masallatai a garin, a Nan sukaji mutuwar Amrita da Mahaifiyar Momy Fannah bayan sunyi kwanaki suka dawo da Sha tara na arziki.
*************************
"Mahauka ta.! Mahauka ta.!
Wasu gungun Yara ne suke bin wasu mahaukata gunin ban Tausayi domin d'ayan ma jini ke zuba a jikin ta d'ayan ko duk Yara sun fasa Mata Kai da jifa. Kura Ido nayi da k'yau sai Naga Ashe Yagana ne da Bintu. Nace ikon Allah,
Allah kayi Mana K'yakk'yawan k'arshe......✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Alhamdulillahi Tammat bi hamdulillahi. Wa subhanakal lahumma wabi hamdika Ash hadu Allah ilah ha illallah.
Ya Ubangiji Ina rokon ka Abun da na rubuta dai dai ka bani ladan shi, Wanda Kuma nayi kuskure ka gafarta mun.
Yau na kammala littafina Mai suna Boyayyiyar K'ulli da fatan ya fad'akar Kuma ya nishadantar daku.?
Nasan da yawa zasu ce Basu ji ya Labarin Khausar ta k'are ba, to ku biyoni bashi a Littafi na na gaba Mai Suna waye Masoyi na gaskiya. Insha Allah zaku ji Labarin Khausar. Taku har kullum
Yar mutan Zazzau ce sarauniyar kanawa 😏😏💖🥰😍😍😍
I love you All
Mu had'u a Next Novel d'ina Mai suna Almajirai ma y'ay'a ne Wanda Zan fara posting jibi insha Allah 🙏.
Share
Comments
Like.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels