Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 11
har uwar Maigidan bamu kyale ba har gidan ta naje na barbad'e magani a gadon kwanciyar ta. Lokacin da Alhaji ya dawo lokacin na samu naje na zuba Magani cikin girkin da Matan gidan tayi ma Maigidan, har d'akin shi sai da aka barbad'e magani. Na Kira wani yaron Shamo yazo don ya shiga D'akin Matar gidan don aikin mu ya tafi yanda muke so. Haka ko akayi komai ya watse, mun watsa family mun haddasa Rashin zaman lafiya, daga k'arshe mukayi k'ulle k'ulle mu a gurin Boka inda bamu wani Sami matsala ba gurin Auren Alhaji da Bintu yarinyar Yagana, Nan Yagana suka bud'e duniya sabuwa inda suka mance da kowa, ciki kuwa har dani hakan yasa na kudiri aniyar sai na d'au fansa, kwatsam sai ga Alhaji Shamo yazo ya d'auke ni muka fita K'asar inda anan na gane Ashe shidin fashi yakeyi Kuma Yana cikin kungiyar Asiri mafi muni, haka yayi matuk'ar tsorata ni. Kwatsam wata rana na tashi da Nak'uda inda Shamo ya kaini Asibiti na haifi zankadediyar y'ata K'yakk'yawan gaske, sai dai inda aka samu matsala Ina haihuwar ta ce sai na bashi ya sadaukar da ita ga kungiya, hankali na ba k'aramin tashi yayi ba, hakan yasa nayi duk wani Abu da zanyi Saboda kullum kud'i yake turamun a Account d'ina shiyasa bansha wahalar gudu Zuwa dawowa gida ba, Ina dawowa na tarar da Yaya ta tazo ita da Mijin ta zasu tafi ban bari mun had'u da Mijin nata ba sai dai na bata kyautar y'ata. Kunji Abun da ya faru kenan don Allah ku yafe mun nazo Ina rokon ku.πŸ™πŸ™. "Ni Alhaji Bukar da Ahalina mun yafe Miki albarkacin Yar Uwar ki da ta rainamun y'ata duk da Azabtar wan da tayi Mata. Allah ya yafe Mana, sanan muna son ki bamu Labarin inda kika tsinci Zahra. "Bayan mun zo k'auyen mu da Mijina muna kan hanyar mu ta komawa, kasancewar ta Jos muka bi mun iso wani k'auye da ake ce ma jingir muna gab da fita garin Motar mu ta lalace, tsayawa mukayi ga yarinya sai kuka takeyi haka Alhaji ya fita domin Neman inda zai samu ruwa don da alama injin Motar ne tayi zafi, kawai Ina Zaune Ina jiran shi na ganshi da akwati da yarinya niki niki. "Alhaji lafiya Ina ka samo wannan yarinyar fa.? *Laurat Ina so ki had'a yaran Nan ki rikesu karki tab'a nuna musu cewar ba mune iyayen su ba Ina son Yarinyar nan. "Ya za'ayi kawai kazo mun da yarinya baka mun bayani ba kace mun in rik'e ta, haka fa mukayi da Kai akan Sadeeq, haba Alhaji ya za'ayi in raini Yara biyu lokaci guda.? "Kinga Laurat zintar yarinyar Nan nayi a cikin dajin nan, Kuma indai raino ne Zan samu Miki Mai Taya raino. "Shikenan Allah ya tayani rik'o. "Ameen ya Allah πŸ™ ko kefa. "To kunji inda muka tsinci Zahra. Sosai Fallon akayi ta kuka. Ana cikin haka ne aka ce an k'ara yin wasu b'aki Maza biyu Mace d'aya, aka ce su shigo. "Daddy dama baka mutu ba,? Baya tayi ta zub'e yayin da Daddy idon shi akan Fad'imatu. "Fad'imatu dama kina rayee.....? ************************* MASARAUTAR AMRISH Zagaye d"akin ta fara yi, tabbas suna cikin had'ari matuk'ar Ansh ya tona musu Asiri. Shiru Sadeeq yayi Yana zare ido, gaba d'aya ma ya k'asa yin Addu'a. Da sauri kibd'iyatu ta juyo ta Kama shi ya mik'e domin har yanzu bai gama warkewa ba da raunikan jikin shi. Wani mayafi ta samu ta nad'a Mai ta rufe Mai fuska ta kamo hannun shi sukayi hanyar fita, dai dai lokacin da Maman ta da baban ta suka shigo d'aki ga fadawa biye a bayan su. "Dama na fad'a Miki duk wani Abun da kike b'oye wa sai ya fito fili, wato bak'o kika shigo Mana dashi bayan kin San dokan Masarauta Koh, tabbas ko da kike y'ata Dole a hukun taki domin ke d'in Mai laifi ne. "Y'ata Mai yasa kika aika ta wannan mummunan zunubin,? Yau Ina cikin tashin hankali a kan Zan rasa ki gashi ke kad'ai na Mallaka a duniya. Kin San Dole Masarauta ta hukunta ki da horo Mai tsanani na tsawan wata biyar da kisa ta hanyar jefewa. Kaico na yau y'ata ta aika ta wannan zunubin, Kai Kuma bak'o wani tsautsayin mutuwar ce ta biyo da Kai ta Masarauta na.? "Abbiyyu ba yajin me kake cewa baya jin yaren mu, Abbiyyu Ina Neman Alfarma ga Masarauta cewa don Abun bauta a mun duk hukuncin da za'a mun Amma kar ku kashe shi ku barshi ya tafi. "Ke dakata.! Har ke Zaki fad'a Mana Abun da ya dace to baki Isa ba, Dole a hukunta ku dukan ku, sarkin yaki ku tafi dasu kurkuku mafi Azaba ayi ta gana musu Azaba har Nan da wata biyar kafin ita a Mata kisa ta hanyar jefewa shi Kuma ta hanyar rataya. Ta k'arisa maganar Tana mai fashewa da kuka na munafunci Wanda Bai Kai ciki ba, rungume ta sarki Bijay yayi Yana mai bata hakuri da cewar zasu zauna da Masarautar don ya rokan ma Y'ar shi sasaauci don bazai tab'a iya yarda a kashe Mai y'a ba Kuma ita kad'ai gareshi ita yake ta gaje shi. Jin haka yasa hankalin gimbiya Amrita ya tashi ta k'ara fashewa da wani kukan, dole yau ta ziyarci dodon Zafin ta don ganin ba a ma kibd'iyatu sassauci ba, don hakan zai kawo Mata matsala gurin Samun kujeran Mulkin Masarautar Wanda shine burin ta da na Mahaifin ta. Haka aka Kama su Kibd'iyatu aka tafi dasu, Sadeeq bai k'ara rud'ewa da Masarautar ba sai da aka fito dasu, tabbas Masarauta ce Mai Matuk'ar birgewa da girma Wanda in kana cikin ta Tamkar kana wani dausayi ga Ni'ima ko Ina ga kwalliyar furanni kala kala Wanda suka k'awata garin, ga kanshi ko ina, ko Ina na garin a tsaftace ko tsinke bazaka gani a k'asa ba, haka aka ratsa dasu ta tsakiyar gari yayin da mutanen garin suke firfitowa suna binsu da kallo wasu na Tausayi wasu na Allah ya k'ara. Tana fita bata zame ko Ina ba sai kogon da Dodon ta yake bayan tayi badda Kama tasa wani riga da ya rufe har fuskan ta. Tana Isa Dodon ya fara Mata magana cikin damuwa. "Mai girma uwargijiya ta tabbas wannan bak'o da yazo garin Nan babban matsala ce da barazana gare ku duka Yan garin domin na duba Naga cewa akwai Abubuwan Mamaki da yawa a tare dashi, tabbas karki bari ya k'ara kwana uku a garin Nan ba tare da kin kashe shi ba, in har ba haka ba to akwai Matsala Sosai ki tafi! Ki tafi! Uwar d'aki na ki hanzarta bamu da isasshen lokaci.✍️✍️✍️✍️✍️✍️ Nima din dai Banda isasshen lokacinπŸ™„πŸ€ͺ🀣 Zeey Yar mutan Zazzau ce sarauniyar kanawa πŸ’ͺπŸ‘Š Share Comments Like πŸ˜πŸ’–πŸ₯°πŸ₯°πŸ’–πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯° *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ Ranar muke jira yau gashi tazo kowa da tanburan shi gashi munzo Yaya Sadeeq ya angwance da Gimbiya kibd'iyatu πŸ€ͺ🀣🀣. SADAUKARWA Wannan page d'in na sadaukar dashi gareki sisto Adama Allah ya baki lafiya yasa kaffara ce agareki, fans ku sata a Addu'a πŸ™. BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. ************************* PAGE 33 ................Sosai su kibd'iyatu suke gudu tamkar walkiya, wani guri suka iso tamkar wani gari Amma ba kowa garin bud'e kofar garin sukayi suka shiga. Masha Allah wannan gari ma yafi Masarautar Amrish had'uwa Sosai, bayan sun shiga ne suka wuce cikin wani guri suka ajiye Sadeeq suka fara Basu taimakon gaggawa. Bayan ya farfad'o ne suka ce Mata "ya shugaba dole ku bar gurin Nan yau don Mahaifiyar ki bazata barki ba, domin yanzu haka ta had'a jarumai domin nemo ku. "Tabbas maganar ki haka take, a yau zamu bar garin Nan, ku kawo Mana kayan marmari bayan wasu Awanni sunyi shiri Sosai aka fitar musu da ingarman dokuna suka hau suka fara tafiya. Sunyi guzuri Sosai, bayan tafiyar su ba dad'ewa mayak'an garin su suka iso cikin birnin basu gansu ba. Haka suka zagaye dajin basu samesu ba, gashi Sarauniya tace karsu sake su dawo ba tare da sun gansu ba. ******* ******** ***** Sosai sukayi tafiya Mai nisa sannan suka yada zango a gurin wani bishiyoyi masu tsawo, Kibd'iyatu ta Kama Sadeeq ya sauko ta zaunar dashi ta k'ara duba mishi Ciwon nashi ta samishi magani, ta bashi Abinci ya ci tace Mai ya kwanta ya huta bari ta Dan zagaya gurin ta gani. Binta kawai yayi da Ido don gaba d'aya ya zama wani iri ko magana ba ya iya yi, Saboda Azaban da yake ji a jikin shi, barci ne ya fara d'iban shi, kukan dokunan su yaji da haniniyar su da sauri ya farka yaga kibd'iyatu ta dawo da wani irin gudu ta kamashi ta d'ora shi kan doki ita ma ta haye da gudu suka bar gurin. Gudu sukeyi ba kad'an ba domin kuwa mayak'an garin su ne suka kusa gano inda suke da taimakon Sarauniya, domin duk ta inda suka bi tana ganin su da taimakon dodon tsafin ta. Sunyi tafiyar kusan kwana uku kafin su fara isowa wani dajin mai matuk'ar duhun bishiyoyi. Dole suka kunna fitillar da suke haskawa, suna cikin tafiya sai ganin wani gida sukayi a dajin da akayi shi da katako da ganye, tsayawa sukayi suna kallon gidan a hankali kibd'iyatu ta sauka taje tana zagaye gidan sai ta jiyo tamkar maganar Mutane Kuma irin yaren Sadeeq sukeyi da sauri ta kutsa Kai cikin gidan. Ji tayi an rik'e ta an sa Mata wuk'a a wuya, "wacece ke yau tsawon shekara Ashirin da hud'u muna dajin Nan ba wani mahaluki da ya tab'a shigowa Nan sai ke.? "Mai gaskiya sake ta, tabbas lokacin barin mu dajin Nan yayi domin dama ita muke jira shekara da shekaru, Amma Ina saurayin da kuke tare dashi.? Mamaki ne ya cika kibd'iyatu jin wannan tsohon na mata magana da yaren garin su. Cewa tayi gashi can a waje, ta fad'a haka tana mai juyawa tana kallon matan da ta fito D'auke da wasu kyawawan Yara da aka musu ado da ganye tamkar sutura a jikin su, sai dai sudin bak'ak'e ne kamar yadda Mahaifiyar su take Amma irin bak'in Nan Mai k'yau. "Mai gaskiya ku fita ku shigo da Saurayin Nan domin bamu da lokaci Sosai yau ko gobe ya kamata mu bar dajin nan in ba haka ba komai zai iya faruwa. "Baba Taya zamu bar dajin Nan bayan kasan so gurin Tara muna kwatan ta barin Amma bamu gane hanya." "Tabbas hakane Amma fitillan mu ta iso domin na dade Ina Mafarki game da Yarinyar nan zata zo ita da wani Saurayi da zaran Mun had'a su Aure zata Musulunta Kuma daular Masarautar su zata ruguje, Mahaifiyar ta dodon tsafin ta zai cinye ta, mu Kuma zasu zamo Mana jagoran zuwa ga Ahalin mu. "Masha Allah yarinya muje a shigo dashi. A hankali hawaye ya fara zubowa daga idon Matan Nan tana mai Fad'in Alhamdulillahi lokaci yayi Mafarki na zai Zama gaskiya. Sai gashi sun shigo rirrik'e da Sadeeq domin Yana jin jiki Sosai suka ajiye shi, a hankali Sadeeq ya fara tuno komai na Rayuwar shi bayan baba yayi Mai Addu'a a cikin ruwa ya bashi. A hankali ya fara furta "Daddy Ina Zahraty na, please karku kashe ni Banga Zahraty ba. "Alhamdulillahi hankalin shi ya dawo Normal. Yaro ya sunan ka? "Suna na Sadeeq." "Masha Allah Nan Kibd'iyatu da baba suka bashi Labarin duk Abun da ya faru da Kuma bukatun su, Amincewar shi kawai suke jira. "Yaro ka taimaka Mana wannan hanyar ne kawai zai fitar damu ya tseratar mu daga sharrin Masarautar Amrish. "Shikenan Baba na Amince, Amma da sharad'in cewa daga baya Zan sake ta in Auri y'ar uwa ta Wanda nake so. Har mai gaskiya zaiyi magana Baba tsoho ya dakatar shi yace Mai "ba damuwa yaro. Ita ko kibd'iyatu dama burin ta kenan don ita ta dad'e da kamuwa da Soyayyar shi a ran ta, ita jin shi takeyi tamkar jinin ta ko wani bangare na Ahalin ta. Kuma Kama yake Mata da k'anwar Mahaifin ta Safni. Haka aka d'aura Auren kibd'iyatu da Sadeeq akan sadakin na agogon zinarin da Mai gaskiya ya bayar domin shi ya zama waliyin Ango yayin da Baba tsoho ya zama waliyin Amarya. Suna gama d'aurawa suka fara Shirin tafiya bayan Sadeeq ya rama duka sallolin da ake binshi, Suma d'in basu d'auki komai ba sai guzurin Abun da zasu ci. Matar shi da yaran aka sa akan doki d'aya sai Sadeeq da Baba tsoho a doki d'aya yayin da kibd'iyatu da Mai gaskiya suke tafe a k'asa domin su din sun fisu lafiya. ************************* MAIDUGURI Sosai Family d'in ke jin dadin su yayin da aka ware ma Daddy sashi guda a gidan, ba a wani b'ata lokaci ba aka maida Auren Alhaji Bukar da Fad'imatu, yayin da suke Shan love d'in su don ji yake tamkar ya maida ta ciki Saboda Soyayya. Gefe guda Kuma Jannat da Hanif sun tare a gidan sunki komawa gidan su Saboda Zahra yayin da Hanif yake shige ma Zahra Sosai tun bata kulashi har ta fara biye mishi, don shi mutum ne Mai tsokana. Ya dunga had'a su ita da Jannat Yana tsokanar su, in kaji hayaniyar su kace Yan dambe ne. Yayin da Hanif yaje ya sanar da Momy granny shifa Zahra yake so. "In ban da abinka Hanif Ina Kai Ina Zahra Kuma kana dai ji Zahra tana da Wanda take so, Kuma baza muyi Mata dole ba. "To shikenan granny ai dama na dad'e da sanin baki son farin ciki na, wlh zaku iya rasani indai ban Auri Zahra'u ba. Ya k'arisa maganar Yana Mai ficewa cikin sauri, "Oh ni Murjanatu ya zanyi da yaron Nan ne, d'aukar waya tayi ta Kira Mama Hanifa tace tazo tana Neman ta. Zahra ne take kwance cikin makeken gadon ta sai juye juye takeyi barci ya k'aurace Mata sakamakon wani mummunar Mafarki da tayi Wai ga Yaya Sadeeq ya Auro wata Yar India. Sosai Zahra take kuka tanajin Zuciyar ta tamkar zata tarwatse, tashi tayi tayo Alwala tazo ta fara Nafilfilu tana fad'a ma Ubangiji Allah ya Yi mata zabin Alheri.✍️✍️✍️✍️✍️ Nasan yanzu zaku faramun Surutu maiyasa Sadeeq ya Auri kibd'iyatu haka Labarin yazo. Team Yaya Sadeeq da Zahra sai dai fa kuyi hakuri domin Sadeeq na gimbiya kibd'iyatu ne🀣πŸ€ͺπŸ€ͺπŸƒπŸƒπŸƒ. Share Comments Like Zeey Yar mutan Zazzau ce sarauniyar kanawa πŸ˜πŸ™„πŸ€£πŸ€ͺπŸ˜πŸ’–πŸ₯°. *'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ Wannan page d'in k'yau ta ne gare Yan k'ungiyar Arewa writers Ina yin ku son so fisabilillahi, Allah ya k'ara d'aukaka kungiya.πŸ™πŸ™ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. PAGE 34 ************************* MAIDUGURI Daddy ne yake ta zarya a D'akin shi, gaba d'aya hankalin shi Yana kan d'an shi kar maganar Laurat ya zama gaskya fa don cewa tayi tasa an kashe shi. Shi Kuma Daddy Bai yarda Sadeeq ya mutu ba. Sallaman da Hanif yayi ne yasa Daddy dakatawa tare da ba Hanif izinin shigowa. Shigowa Hanif yayi tare da durkusawa Yana Mai gaida Daddy, daga Nan Kuma yayi shiru ya kasa cewa komai. "Mallam Hanif lafiya kuwa,? Da alama akwai Abun da ke damun ka.? "Eh Daddy dama akan Maganar Aunty Zahra ne, umm umm. "Ka saki jikin ka Hanif kayi maganar ka, ka d'auke ni tamkar Mahaifin ka. "Daddy wlh tun ranar da na fara ganin Zahra Allah ya jarabceni da son ta Kuma wlh in har ban Aure ta ba Zan iya rasa rai na. Ya k'arisa maganar cikin kuka tamkar k'aramin yaro. Numfasawa Daddy yayi yace, "yanzu in banda Abinka Hanif Ina zaka Kai Zahra, Zahra Kuma ta girmeka ta baka kusan shekara uku, Anya bakayi zari ba.? "Wai Daddy meyasa kuke cemun haka, Taya Mace zata fi karfin Namiji bafa dambe zamuyi ba daddy, Aure zamuyi Kuma wlh bata fi k'arfi na ba, in Kuma baku yarda ba ku Aura mun ita ku gani Next year insha Allah Kuna da jika. Zaro Ido Daddy yayi yace "jeka Hanif Zan Neme ka, zamuyi shawara kaji. "To Daddy don Allah a duba buk'ata ta Kuma ayi mun AdalciπŸ™. Yana gama Fad'in haka ya fice daga d'akin da Zahra suka ci karo Alamun duk taji Abun da suka yi da Daddy. Wani kallon tsana da rashin so tabishi dashi, juyawa tayi ta fasa shiga d'akin Daddy. Bin ta yayi da gudu Yana k'wala Mata Kira"Zahra'u! Zahra'u!. Zahra tana Zuwa ta shige d'aki ta fad'a akan gado, ta fashe da kuka tabbas Hanif Yana so ya rabata da Masoyin ta, duk da Mami tace tasa an kashe Yaya Sadeeq ita bata yarda ba ta naji a jikin ta cewa bai Mutu ba Kuma zai dawo gare ta, suyi Aure su haifi Yara. "Zahraty kukan me kikeyi.? "My Jannat Hanif ne." "Haba Zahraty na yanzu har Hanif ne Zaki zauna kina mishi kuka, to Wai ma meya Miki.? Kwashe duk Abun da taji suna magana da Daddy tayi ta fad'a ma Jannat. "Tabdijam lallai ma Hanif bai da kunya kedin ce zaice Yana so,? Wlh bai Isa ba duk runtsi ko Nan da shekara goma ne sai mun jira Yaya Sadeeq ya dawo. "Baku Isa ba kuwa." Duka juyawa sukayi suka tarar da Mami da Daddy a bakin kofar d'akin, Mami ne tace ma Zahra Basu Isa ba. "Haba Mami Ina Hanif Ina Zahra, Zahra ai tafi karfin Hanif, in ba rigima irin nashi ba. "Jannat ki rufemun baki, to Wai da kuke Maganar ku ma Ina Sadeeq d'in yake,? Ina ce a gaban ku Laurat tace tasa an kashe shi. Daddy ya fad'a haka Yana goge kwalla a gefen idon shi. Da gudu Zahra tazo ta rungume Daddy tana mai fashewa da kuka, "wlh Daddy inaji a jiki na Yaya na bai Mutu ba Kuma zai dawo gareni, don Allah kar kumin haka daddy Zan shiga wani hali. "Kiyi hakuri Zahra ki ceci ran yaron Nan gashi can ya yanke jiki ya fad'i bayan fitowan shi daga bangare na, an d'auke shi rai a hannun Allah sun tafi Asibiti. Zaro Ido Jannat tayi jikin ta na rawa take tanbayar Daddy wani Asibiti ne.? Jini d'aya ba Wasa ba ita ma Zahra sai da taji wani iri a Zuciyar ta kawai bazata iya cin Amanar Yaya Sadeeq ba ne. Niko nace sai kiyi ta rike Mai Amanar, gashi can shi yayi Auren shi aiπŸ™„. ************ *********** Likitoci sunkai goma a kan shi don ceto rayuwarshi yayin da Momy Kaka da Mama Hanifa suke ta zarya sun k'asa Zama, su Daddyn Zaria ne da Daddyn Maiduguri da Mami da Matar Dadfyn Zaria da Jannat suka iso Suma a rud'e suka k'ariso, "ya jikin nashi to"?. "Alhmdulillahi Amma har yanzu likitocin tun da suka shiga basu fito ba, Mama Hanifa ta k'arisa maganar Tana kuka. Dai dai wani likita ya fito, "kune relative na Hanif Madou.? Har rige-rigen Amsawa sukeyi, yayin da doctor ya basu Umarni su biyoshi office din shi. Haka duka suka dunguma yayin da Maman Sadeeq ita ta Zauna, duk da har yanzu bata wani dawo Normal ba Kuma har yanzu bata jin yaren mu Sosai, shiyasa in ana wani Abu sai Daddy yayi Mata bayani take fahimta. Har yanzu Kuma bata tuno da d'an ta. Bayan sun zauna likita ya fara musu bayani, "Tabbas Zuciyar shi ta tab'u k'adan Saboda wani Abu da ya firgitashi, ko kuma yake tsoron ya rasa wani Abu lokaci guda sai Zuciya ta samu matsala matuk'ar bai samu Abun Nan ba, in har so samune ya kasance da ya farfad'o ya fara tozali da Abin da yake so, haka zai sa Zuciyar shi ta daidaita. "Ba damuwa Doctor insha Allah. Da gudu Zahra ta juya daga kofar Office din. ************ ************ Sunyi tafiya Sosai bani da tafiya ba, yayin da Kibd'iyatu ita take nuna musu hanya, domin ita d'in tana da sani Sosai game da dajin Abun da ke tsayar dasu kawai Sallah, a wannan yanayi ne Kibd'iyatu taga ita ma ya dace ta karb'i wannan addini Saboda ta lura cewa Addini ne Mai k'yau sannan mutanen cikin ta suna da had'in Kai tunda gashi sun had'u da su Mai gaskya Basu San su ba Kuma sun taimake su, Baba Tsoho ta fad'a ma tana so ta Musulunta. Dukan su sunyi Farin ciki da haka take ta Musulunta gurin Baba Tsoho. Hakan yasa Sadeeq ya fara sakewa da ita, har zasu danyi hira, Kuma Sosai take kula dashi yayin da ta dage gurin koyon addini da sauran Ibadu gurin Baba Tsoho, hakan yasa Sadeeq har ya fara jinta a ranshi. ************ ************* MASARAUTAR AMRISH Sosai suka tashi da wani firgici a garin yayin da kogin da ta zagaye garin ta fara Anbaliya hakan ya faru ne duk Saboda Musuluntar da kibd'iyatu tayi, domin Alkawarin Abun bautan su ne cewa duk randa wani yaron sarkin da ke mulki a lokacin ya karb'i wani Addini ranar zai kifar da garin su. Sosai Sarki ya shiga tashin hankali, Mahaifiyar sarki ne ta fito domin ita d'in ta dad'e tana Addini Musulunci sai dai ba Wanda ya sani domin tana jin tsoron Mai zai je ya dawo, dalilin Musuluntar ta kuwa shine ta fita kewaya, wani dodo ya biyo ta duk masu tsaron ta suka gudu, ta sadakar da zata mutu kawai sai ganin wani mutum da fararen Kaya tayi Yana karanto wasu Abubuwa take dodon Nan ya k'one, Aiko taje ta rungume mutumin Nan tace Mai meyake so ta biya shi da shi, sai yace Mata ta karbi addini nin shi take ta karb'a, Kuma ya umarce ta da ta b'oye Addinin har sai lokacin da ya kamata ta Bayyana, sai ya zamana duk ranar jumma'at Yana zuwa ya koya Mata Abubuwa da ya danganci ibadu. Fitowa tayi dai dai lokacin da Mujahedeen ya iso Addu'a suka farayi a tsakiyar garin take Anbaliya ruwan ya fara komawa, garin ya dena girgiza komai ya tsaya cak. Farin ciki ne ya mamaye sarki yaje ya rungume Mahaifiyar shi Yana Fad'in "Amma mun gode, Amma wannan wani irin tsafi ne kikayi.? "Wannan ba tsafi bane Addu'a ce. Nan da Nan Mujahedeen ya fara musu wa'azi Yana janyo Ayoyi da hadisai Yana fassara musu cikin harshen su, jikin wasu yayi sanyi, wasu ko daga ciki ko a jikin su sai ma tafiya da suka fara yi ciki kuwa har da Amrita da Mahaifinta direct gurin Dodon su suka Nufa. Shi Kuma dodo Yana Nan bakin ciki yakusa kashe shi za'a daina bauta mishi, suna Zuwa Bai ko saurari Mai zasuce ba ya yi musu Loma d'aya bayan haka shima ya kashe kan sa. ************* ********** Sosai shak'uwa ta shiga tsakanin Sadeeq da kibd'iyatu, Wanda yanzu Sunan ta ya koma Fad'imatu Zahra'u ita tace a samata wannan sunan bayan baba Tsoho ya bata tarihin Mai sunan, da darajar ta, Nana Fad'imatu Allah ya Kara Mata yarda. Shi Sadeeq ma bai sani ba, sun fita farauta da Mai gaskya sun dawo yace Mata "kibd'iyatu zo ki had'a Mana wuta mu gasa Naman Nan. "Ni Sunana Fad'imatu Zahra'u, ko kace mun Zahraty. Ta fad'i haka tana mai hararan shi irin na Soyayyan Nan. Da sauri ya d'ago Yana kallon ta, "da yaushe kika koma sunan Nan ban sani ba,? Ya fad'i haka cike da Mamaki a fuskan shi. "Mijina ko sunan bai maka bane,? Naji tarihin Mai sunan ne da darajan ta yasa nace a Samun sunan, Ina matuk'ar son suna, Kuma Ina son duk wacce take da irin sunan. Ta k'arisa maganar Tana ruko hannun shi. Samun kanshi yayi da Mata Murmushi, murmushinda yake matuk'ar kashe Mata zuciya a duk lokacin da yayi Mata, ta jita ta Kara tsunduma a kogin son shi. "Karki damu Sunan yayi Sosai Saboda nima sunane Mai daraja a guna Kuma mafi soyuwan suna kinji Zahra'u. Rungume shi tayi tana maijin farin ciki. Maman Yara ne ta fito "oh Zahra kina Nan kina shirmen ko baki had'a wutar ba, ko da yake Allah ya sa ma kin iya had'awa domin nasan ku komai yi muku akeyi a matsayin ki na gimbiya. "Kai Maman yara, na iya Mana in mun fita kewaya Ina ganin yanda kuyangina ke had'awa shiyasa na iya ai. Haka suka cigaba da aikin su suna hira cikin Nishad'i da kwanciyar Hankali, yayin da gefe guda Kuma Baba Tsoho da Mai gaskya suke tattauna wani magana da nima Kai na ban ji me suke cewa

Chapter 10 of 11