Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 11
sun tafi Mai da Rayuwar shi ne gaba d'aya. Suna fitowa suka tarar da ana rirrik'e Bintu tana fisfisgewa tana cewa wlh sai na tona Asirin Yagana kin kori Fad'imatu don in Auri Alhaji Koh,wani k'ara ta saki. Maganar da tayi dai dai su Momy sun fito Kuma taji Mai take fad'i, kawai ganin Momy sukayi tayi baya zata fad'i da Sauri Zahra ta rik'o ta, had'e Kiran Driver, da gudu driver yazo suka sa Momy a Mota mama ma ta shiga sai Asibiti aka wuce da Momy. ************************* K'AUYEN ZULUM Inna Tasallah ne ta fito da buta a hannun ta zata bayi taga wasu samudawan mutane suna shigo musu gida ba ko Sallama. "Bayin Allah lafiya kuwa,,,,,maganar ne ta mak'ale lokacin da taga an shigo da Mami kafafuwa na lilo, "innalillahi wa'innah illaihirraji'un ๐Ÿ™† Laure me Zan gani haka hatsari kikayi ne.? Sudai suka jingine Mami suka jefa Mata jakar ta da wayan ta suka k'ara gaba. Fashewa Mami tayi da kuka, "Innah Kinga inda rayuwa ta juya Mana baya koh.? Shiyasa ake cewa mutum yabi duniya a hankali, tabbas nayi kuskure Ina Asabe ta haifomin Masifa da bala'i dama duk Wanda aka cema shege sai yace Uwar shi ba tayi komai ba, Asabe tazo ta fad'a mun waye uban Khausar,? Rarrafowa Asabe tayi ta dafa bango ta fito a dudduk'e, zaro Ido Mami tayi tana Nuna Asabe "meya sameki Asabe.? K'arisowa tayi ta rungume Mami suka ci kukan su, sannan Asabe ta Bata Labarin Abunda ya faru da ita, itama Mami ta Bata Labarin komai. "Yanzu kina nufin kice mun Khausar ta karya ki,? Ta fad'a cikin Mamaki da jimami, Tabbas Khausar bata Yar a k'asa ba domin Baban gagarumin Dan fashi ne mare Imani gashi matsafi yanzu haka ma shi ya dawo dani gida daga Legos tun daga haka bai k'ara waiwaya ta ba, Saboda a yanzu Banda wani sauran Anfani a gurin shi. "Tabbas Khausar bata Yar a k'asa ba Ashe magaji mafiyi, yanzu haka zamu cigaba da rayuwa a haka,? "Ba gara ke ba ma kinyi Aure Niko da na biye ma Yagana na tashi a tutar babu, Kuma Alkawarin kud'ad'en da tayi mun Taki cikawa. Ina son inje in tona Asirin Yagana a gidan Alhaji Bukar Mai Dala. Zaro Ido tayi Mami tana Fad'in "yanzu Asabe shaidanancin naki har ya Kai wannan katafaren gidan,? Wanda kin San duk duniya anaji da mutumin nan, Tabbass kashin ku ya bushe. "Uhmm yarinyar Yagana ne fa take Auren shi bayan mun Kori matar gidan. ๐Ÿ˜ฒZaro Ido Mami tayi tana Fad'in "kina nufin wannan bak'ar Yarinyar nan nata Bintu ita ce take Auren Alhaji Bukar d'in.? Lallai kam Asiri yayi aiki, ya kamata kije ki kwance K'ullin da kukayi kuwa. "In Allah ya so kuwa don yanzu Naga darasi a rayuwa ta, duk inda na zauna na tashi sai dai kiga gurin ya jike da ruwa Mai wari ga tsutsotsi. "Ai naji Alama shiyasa duk na kosa ma ki tashi ki tafi. ************************* Jeji ne da ya Amsa sunan sa jeji, Wanda wasu dogayen bishiyoyi da ganyayyaki suka tsagaye shi ga wadataccen Ni'ima a gurin inda ga wani k'orama ruwan cikin shi k'ar-k'ar Yana ta gudu, wata K'yakk'yawan yarinya ne Zaune gurin ta saka k'afafun ta a ruwan tana wasa dashi, da sauri ta ciro kafafuwan ta tana kallon ruwan da k'yau, in har ba gizo idon ta yake Mata ba tabbas jini take gani a cikin ruwan nan, Bata Gama tunani ba ta hango kamar mutum a cikin ruwan, da sauri ta fad'a ciki tana wani iyo tamkar kifi Nan da nan ta Isa gurin da ta hango mutum din ciroshi tayi da k'yar, Nan ta fara Danna Mai ciki Nan da nan ruwa ya fara fitowa daga bakin shi, da sauri ta koma ta d'auko jakar ta ta fito da kayayyaki ta fara gyara Mai raunin da ke jikin shi, gani tayi kamar an yankeshi ne da wuk'a, Nan da Nan ta wanke Mai Ciwon tas ta d'aga shi ta jingina shi da jikin bishiya, Kara kunnen ta tayi saitin Zuciyar shi taji tabbas Yana aiki. Kallon mutumin nayi da k'yau sai Naga tamkar Yaya Sadeeq fa..โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ Yar mutan Zazzau ce ๐Ÿ˜๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ Kar Wanda ya ban hakuri daga baya Inna cireka rashin yin Comments ya ja maka๐Ÿ™„๐Ÿ˜...๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿƒ *'BOYAYYAR 'KULLI*๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *๐Ÿ’ฆ{Arewa ginshiฦ™in al'ummah}๐Ÿ’ฆ* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ Wannan page d'in naku ne Masoyan Asali son so fisabilillahi tabbas Ina jin dadin Comments din ku Sosai. Sister Adama Maman Ahmad My kakus Sister Nafeesat My sweet Aboki inkiyan ka sai fa na fad'a Saghiru bakano๐Ÿคช๐Ÿคช๐Ÿคช Da duk Wanda ban ambaci sunan su ba Kuma Ina yin ku irin Sosai d'in na love you Lodi Lodi ๐Ÿคฃ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿ’–. BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. ************************* PAGE 28 A hankali ya fara bud'e idanuwan shi, sai dai dishi-dishi yake gani, yanayin gurin da ya ganshi ne yasa ya ware idon shi gaba d'aya. K'okarin tashi ya Zauna yake yi Amma ya kasa tashi. Yarinyar da ta tsinto shi ne ta shigo d'akin hannun ta d'auke da wasu Magunguna, ganin shi ya farfad'o ne yasa tayi sauri ta k'ariso gurin gadon da yake ta ajiye farantin Magungunan a kan wani dan k'aramin teburi dake jikin gado. D'akin yake k'are ma kallo domin ya had'u an k'awata shi da wasu labulaye ga wasu shimfid'un kafet tamkar katifa masu launi da ban da ban ko wani lokaci canzawa sukeyi, ga wasu fulawowi da aka ma jikin bangon d'akin kwalliya dasu tamkar an shuka su sai bada wasu kalar kanshi suke, gadon da yake kwance ya kalla gado ne irin Mai rumfar nan an sa ma labulaye masu canza launi irin shimfid'un kafet din d'akin, a jikin labulayen ga wasu kwayayen wuta suna haskawa suna d'auke wa, duk da d'akin ba wani girma da tarkace gado ne kawai sai wani korido da akayi mishi wasu decoration na fulawowi sai ya bada kofa Mai angle da zai Kai ka cikin koridon inda wasu kyawawan kujeru ne aka jerasu a gurin ga fulawowi gefe da gefen su ga wasu kyawawan tsuntsaye suna yawo a gurin suna ta rera wak'oki. Sosai d'akin ya birge Sadeeq. Hakan yasa tana ta magana bai ji ta ba, sai da ta tab'a shi sannan ya kalle ta, Magana ta k'ara yi Mai sai dai bai gane yaren da take yi ba, hakan yasa ya bita da Ido da ta Kara magana sai yace ma ta, "ke ni bana jin Abun da kike cewa fa, ke waye Nan Kuma Ina ne,? Wannan duniyar bata yi Kama da duniyar Mutane ba don kema kanki wannan kyan naki ya zarce na mutane sai dai aljanu. Tsayawa tayi tana kallon shi, duk da bata jin Abun da yake cewa sai taji gaba d'aya yaren da yayi Mata magana dashi ya burge ta, shidin ma gaba d'aya ya burge ta hakan yasa take ta kallon shi tamkar zata had'iye shi. "Ke Wai lafiya kike ta kallona tamkar mayyah,? Ya Allah Wai waye ni,? Mene suna na daga Ina nake.? Motsi taji Alamun kamar ana tab'a kofar d'aki, da sauri ta tura Sadeeq ya kwanta ta rufe shi da wani tattausan blanket ta sauke duk wani labulaye na gadon kafin ta tashi taje ta bud'e kofar d'akin. Wata K'yakk'yawar Mata ce take tsaye a bakin kofar da alama Mahaifiyar ta ce, tasha wasu Kaya tamkar Sari ta nannad'e jikin ta dashi har kan ta tayi mayafi dashi ga wasu zobuna da sarka masu kyau da tayi ado dashi kafa da hannaye da kan ta Wanda ya ratsa ta tsakiyar kan ta a tak'aice dai tasha k'yau Sosai Kuma baza ka tab'a gane tsufan ta ba. Rab'awa tayi zata shiga D'akin y'ar nata, da sauri ta tare ta tana Fad'in "Ummiyu ya haka Zaki shiga mun d'aki ba tare da izini na ba, kin San dai wannan babban zunubi ne da in Abbiyyu yaji zai iya hukun ta ki fa. "Wai ke kibd'iyatu Mai kika d'auki kan ki ne a Masarautar nan,? Kar ki man ta nifa Mahaifiyar ki ne, Kuma tabbas Ina ji a jiki na da Abun da kike b'oye mun a D'akin nan, Kuma Mai yasa kika sallami Hadiman ki.? "Meye matsalar ki da ni,? Bana buk'atar su Hadiman ne shiyasa na koresu, tana gama Fad'in haka ta shige d'akin ta ta kullo kofar ta bar Ummiyyo a tsaye a bakin kofar. Karkad'a Kai tayi tace "wlh yarinya Zaki zo hannu na sai Naga bayan ki a Masarautar nan tamkar inda Naga bayar y'ar uwan mahaifin ki ta bar garin Nan domin bana buk'atar kowa ya gaji sarautar Masarautar nan sai ni, ciki kuwa har da ke y'ata da na haifa da ciki na, don ban da Imani a kan Mulkin nan. Juyawa tayi tana tafiya cikin isa da tak'ama. Masarautar Amrish kenan wani gari ne da ke kan iya ka da Maiduguri da Mali, Wanda Asalin su daga India suka taso, Wani mutum ne da iyalan shi dan Yana yawon fatauci, Wanda yake shine shugaban tawagar, suna da yawa ciki kuwa har da matan su da y'ay'an su, shi ya kasance Yana da Mata d'aya da Yara biyu Mace da Namiji, shi shugaban tawagar sunan shi Amrish yayin da sunan Matar shi Zinta sunan babban yaron shi Biju da k'anwar shi Safni. Sosai Amrish ke son yaran shi, Yana da wani Aboki Wanda ya kasance tamkar shine Wazirin shi, Yana da y'a sunan ta Amrita Wanda suke matuk'ar son juna ita da Bijay, in da kwata kwata Safni bata son ta Saboda Amrita ta cika rawan Kai ga rashin Natsuwa ga wulak'an ta na k'asa da ita, Wanda hakan na b'ata ma Safni rai kasancewar ta Mai Tausayi da son na k'asa da ita. Abun da yasa Amrish ya tsabi su zauna a dajin nan Saboda guri ne tamkar dausayi ga k'oramu masu kyau da fulawowi masu k'anshi, a tak'aice dai guri ne Mai cike da Ni'ima ga K'asar Noma, shi Kuma mutum ne Mai Noma da kiwo da safara, hakan yasa ya kafa Masarautar shi anan kasancewar shi dama can jinin Sarauta ne shi a birnin Mumbai na India, bayan wasu shekaru Masu yawa Amrish ya rasu sai Matar shi Zinta da Bijay da yake mulkan Masarautar shida k'anwar shi Safni ita ce Waziriyan shi, yayin da yake Auren Amrita, har a lokacin ba jituwa a tsakanin Safni da Amrita, lokaci guda aka Nemi Safni a ka rasa tun daga Nan Kuma ba Wanda ya k'ara tunawa da ita. A ka d'ora Amrita a matsayin ta, yayin da Mahaifin Amrita ke juya duk wani Akalan sarautar ta fanni y'ar shi da take Auren sarki yayin da Mahaifiyar sarki ta Zama tamkar Yar kallo a Masarautar, sai dai tun da aka haifi kibd'iyatu ta fara basu matsala don ita halin ta d'aya da Safni don har Kama ma suna yi tamkar ita ta haife ta, hakan yasa kwata kwata Amrita bata son ta, shi Kuma Bijay Yana matuk'ar son Kibd'iyatu Saboda kaman ta da k'anwar shi, Wanda bazai tab'a iya tanbayar Ina take ba. Sanan su suna da wani doka a garin duk Wanda aka Kama ya shigo da bak'o kashe shi akeyi shi da bak'on, Kuma duk wani ahali na garin suna da wani tab'o a jikin su Wanda in har kana da alak'a da garin sai an haifo ka da wannan tab'on. Wannan shine tak'aitaccen tarihin Masarautar Amrish. Bayan kibd'iyatu ta koma d'aki ta tarar da Sadeeq ya mik'e Yana kallon agogon da ke d'akin Alamun lokacin Sallah yayi to yanzu ma Salloli na kwana nawa ne a kanshi, to shi taya ma zai ma wannan Aljanar magana ta gane, turanci yayi Mata sai yaga ta maida Mai domin suna jin turanci kasancewar tana fita duk k'arshen shekara yawan bud'e Ido ta fi Zuwa k'asashen Turai, hakan yasa take da bud'e Ido fiye da Yan garin, ita Kuma ta kasance jaruma tana son wasan harbi da kibiya shiyasa tana yawan sa gasar duk k'arshen wata ita take cin gasar, da Kuma gasar tseren cikin Ruwa. Maganar da ya Kara Mata ne ya dawo da ita daga tunanin da takeyi. Ta tanbayeshi da d'an karamin turancin ta Wanda Bata wani goge ba, "me kake so.? "Ina son inyi wanka Kuma in Yi Sallah. "Meye Sallah Kuma.? Zaro Ido yayi Yana mai cewa "Wai baki San Sallah ba,? To me kuke bautawa.? Yaye Mai wani d'an guri tayi a D'akin kawai sai yaga wani d'an k'aramin gunki a ajiye, anyi Mai kwalliya da Zinarai. Dama har yanzu akwai masu bautar gunki a duniya, lallai tabbas Akwai Abun da Allah ya tsara Mai shiyasa ya kawo shi gurin nan, dole yayi Anfani da damar shi gurin ganin sun dawo hanya madaidaiciya. Yana cikin wannan tunanin yaji hannun ta a jikin shi ta Kama shi domin ya tashi, ji yayi Hannun ta Tamkar Auduga Saboda laushin shi, a hankali har ta Kai shi gefen Daman shi ta yaye labulen gurin kawai sai ga kofa ta Bayyana wani Abu ta matsa gefen kofan kawai sai ya bud'e shiga dashi tayi har cikin bayin, Haka ya zama tamkar d'an k'auye don tamkar ba a cikin Band'aki yake ba, k'ok'arin cire Mai Kaya takeyi nufin ta zata Yi Mai wankan, rik'e Hannun ta yayi yace ke mu a Addinin mu ba haka akeyi ba, babu kyau Mace ma ta tab'a Namiji Haramun ne, tsayawa tayi tana juya maganar a cikin ran ta, nunnuna Mai komai tayi ta had'a Mai ruwan wanka Wanda yaji turaruka da filawa, sannan ta fita ta bashi guri. Wai su komai sai sun sa filawa ne lallai fure na da Muhimmaci a gurin su. A haka har ya gama ya fito gani yayi bata a D'akin sai wasu Kaya masu k'yau da aka ajiye Mai a gefen gado da mayuka da turaruka sun Kai kala biyar, zaunawa yayi Yana shiryawa duk da har yanzu Ciwon hannun shi na mishi zafi, riga ya d'auka Yana Shirin sawa dai dai lokacin ta shigo d'akin, zaro Ido tayi ganin tab'on da ke kafad'ar shi da sauri ta k'arisa cikin d'aki tana mai tab'a gurin tab'on, " a Ina ka samu wannan tanbarin,? Kai waye.? "Wani tanbari Kuma,? Ni Kai na ban San ko waye ni ba, Abun da kawai na sani ni musulmi ne, kaman Zan iya tunawa sunana Sadeeq. ************************* JOS "Tabbas Ni yarinyar Fad'imatu ne da yayyina biyu da Habibullahi da Sadeeq sai yanzu na tuna da wani Abun. "To yanzu Ina zamu gansu,? Suna raye ko sun Mutu.? Hajiya Jiddah ce ta fashe da kuka, Zan so in k'ara ganin y'ar uwa ta da y'ata d'aya da na haifa a duniya, yanzu ya zamuyi a gidan radio zamu sa cigiyar su ko ya zamuyi.? "Addu'a ya kamata muyi da mik'a lamuran mu ga Ubangiji domin shi zai Bayyana Mana su, sannan mu had'a da cigiyar su. Sannan yanzu yaushe zamu Maiduguri,? Domin Dole zamuje mu samu Alhaji Bukar domin duk inda suke yanzu nasan Asirin da ke tare dasu ya karye. "Yar uwa ta ba inda zamu domin ai su suka Kori Zahra a gidan su Saboda haka sai sun Nemeta da kansu. "Shikenan Yar uwa ba damuwa duk yadda kika ce Haka za'ayi. ************************* MAIDUGURI Bayan an Kai Momy Asibiti ne, Mama Hanifa ta Kira yaran nata tace su same su a Asibiti sai su tafi da Yar uwan su da tazo, daga Nan su zo musu da Abinci da Abubuwan buk'ata. Suna zaune sai ga su Hanif sun shigo lokacin Zahra tana Sallah. "Wai Mama Mai ya samu grany ne? "My Jannat kece....! Zahra ta fad'a lokacin da ta idar da Sallah. Zaro Ido Jannat tayi taje da gudu ta rungume Zahra tana cewa "my sweet Zahraty Ina kika shiga Ina ta neman number ki baya shiga.? Ta fad'a cikin kuka......โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ Nasan yanzu wani zai ce na sa shi a duhu, daga baya yazo Yana cikamun bakin Wai yasan Mai zai faru a k'arshe, alhalin Bai sani ba, Dole yayi hakuri ya biyo shugaban shi Yar mutan Zazzau ta warware K'ullin da tayi๐Ÿคช๐Ÿคช๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ. Kowa yayi zagi a kasuwa, na feceeee๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿƒ. Amma fa ba tsoro naji ba๐Ÿ™„๐Ÿ˜. Share Comments Like Yar mutan Zazzau ce ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿฅฐ. *'BOYAYYAR 'KULLI*๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ STORY AND WRITING BY ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *๐Ÿ’ฆ{Arewa ginshiฦ™in al'ummah}๐Ÿ’ฆ* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM ************************* PAGE 29 MAIDUGURI "Dallah Malamai a Asibiti muke fa kun wani cika ma mutane kunne da koke-koke kaman gidan mutuwa, sai ance ma mutum yarinta na damunshi yace shi ba haka ba mtswwwww!. Cewan Hanif da tunda suka shigo bai tanka ba sai yanzu. "Eh d'in Ina ruwan ka damu,? Dan rainin wayo kawai dadin Abun ma Awa d'aya ka bani a duniya ba girma ta kayi ba ehe ๐Ÿ™„. "Wai ku meke damun ku,? cewar Momy da ta Farfad'o yanzun Nan. "A Asibiti ma sai kun nuna hali.? "Wallahi Kaka shi ya fara tsokana ta. "Ai ba sai kin rantse ba takwara nasan halin Mai katon kan nan dallah fice a D'akin nan. "Haba Momy Wai meyasa ke kullum goyon bayan Jannat kikeyi ne, ko don Kinga takwarar kice shiyasa, kaji my boy kyalesu nima Ina bayan ka. "Yauwa Mama na ta Kai na, ya fad'i haka cike da miskilanci. "Mama Wai ita bak'uwar bata iya gaisuwa bane da baza ta gaidani ba. Ya k'arisa maganar Yana satar kallon Zahra, Wanda in ba idon shi ne yake Mai karya ba Zahra tana Kama da Maman shi ta gurin idanuwan su, sai dai Zahra ita fara ce ta d'auko hasken Mahaifiyar ta jikin ta da hancin ta duk irin na Maman ta ne, idon ta da dan kumatun ta da dimple di'n da ke kumatun ta guda biyu duka irin na Maman shi ne, Asali ma da tayi Magana sai yaji Muryan ta Tamkar na Jannat Tabbas wannan suna da alak'a na jini da ita. Take yaji wani Soyayyar ta a cikin Zuciyar shi Wanda in har bai mallake ta ba hankalin shi bazai tab'a samun Natsuwa ba, tabbas ya samu matar Aure. Duk a zuciya yake wanna tunanin sai wata Zuciyar tace Anya Hanif baka d'auko Abun da ya fi karfin ka ba, don tabbas wannan daga ganin ta ta girmeshi, wata Zuciyar tace to sai me don ka Auri Wanda ta girme ka ai ba a kan ka a ka fara ba. Niko nace Hanif ba ruwa na zaka had'u da Yan b'oyayyiyar K'ulli fans fa yanzu su kakus da sister Nafeesat, da su Sister Adama, da Maman Ahmad,da sister Sadiya, da sister farida, Kai na gaji duka dai baki bazai iya lissafo ku duka ba. Wlh in ka matsa zasu zo har Maiduguri su cinye ka da Masifa don kana neman yi ma Masoyin su kwace fa๐Ÿคฃ. Nidai ba ruwa na kar Wanda yace mun wani Abu haka Labarin yazo sai dai kuyi hakuri ๐Ÿ™ˆ. "Tab lallai ma yaron nan bai da kunya, Zahraty ta girmeka kai ya kamata ma ka gaida ta ๐Ÿ™„. "Dallah Small girl waya kasa dake,? Yar shisshigi kawai. Kinji Baby kin zo lafiya, ya fad'a Yana mai kashe ma Zahra ido. Sai taji Abun ya Mata wani iri Wai Baby. Dariya Jannat ta kwashe dashi harda rike ciki, "Wai Baby dallah dubeshi Maman shi nace Mai Boy Yana ce ma wata Baby. "Dallah malama ya ishe ki ba da ke nakeyi ba. "Kai wayyo Allah na ni Hanifa, Wai ku don Allah yaushe zaku San kun girma ne,? Dallah Malama ki zuba ma Kaka Abinci ki zubo muku kuci, ku gama ku wuce gida da Zahraty ta huta. Dai dai lokacin Alhaji Bukar ya shigo a rud'e, "sister ya jikin nata,? Wlh Ina can jikin Bintu yayi tsanani sai tuge gashin kanta takeyi, ga jini na ta zuban Mata, yanzu haka likita yayi Mata Alluran barci za'a yi Mata aiki a cire Baby. "Uhmmm Allah yasa ma Baby ya Mutu, cewar Momy ta fad'a ran ta a b'ace. "Haba Momy in rai ya b'aci hankali ke nemo shi bai kamata kice haka ba, Ubangiji Yana fitar da Mai k'yau a cikin mare k'yau duk tsiya dan da zata haifa jinin ki ne tun da D'an d'an Yaya Bukar ne. "Ki mun shiru Hanifa! Bana buk'atar had'a jini da wannan zuri'a, Zahra kad'ai ta isheni rayuwar duniya ita da yaran ki, domin tabbas Ina ji a jiki na Zahra y'ar Bukar da Fad'imatu ne, Saboda haka yanzu duk inda Fad'imatu take a doron duniya insha Allah sai na Nemo ta domin itace matar da ta dace da Ahalina๐Ÿ˜ญ. Ta k'arisa maganar Tana kuka. "Don Allah Momy kiyi hakuri kamar inda Ubangiji ya Bayyana Mana Zahra haka zai Bayyana Mana Fad'imatu. Daga yau Zan bada sanarwa Zan sa kud'ad'e masu tsoka ga duk Wanda yaga Fad'imatu, Momy ma haka tace. Gaba d'aya kan Zahra ya kulle ta kasa fahimtar inda zancen su ya dosa, tanbayoyi ne cike fal a ran ta. "Momy Ina jin tsoron kar ya kasance tunanin da mukeyi akan yarinyar Nan ba haka bane yazo iyayen ta su kwace ta. Inji Alhaji Bukar yayi wannan maganar. "Ai duk duniya ba Wanda ya isa ya kwace yarinyar Nan a hannu na. Cewar Momy da ta yunkura ta tashi zaune. ************************* JOS Fad'imatu ne kwance a kan cinyar Hajiya Jiddah tana Mata tsifan Kai, ita Kuma tana rike da remote a Hannun ta tana canza tasha daga zee world zuwa Tashar Arewa, dai dai lokacin da hotan ta ya Bayyana a saman tv ana cigiyar ta ga duk Wanda ya gan ta za'a bashi kyautar Miliyan biyar, sannan in ita taji sanarwan ta hanzar ta Kiran Number waya kamar haka Saboda y'ar ta tana cikin wani hali a Asibiti Wanda tabbas likitoci sun gwada ta sun tabbatar da cewar tana buk'atar wani Abu ne, ita Kuma y'ar tace Mahaifiyar ta kawai take son gani kafin ta Mutu, Hoton Zahra aka Nuno kwance gadon Asibiti, wannan Kuma gata tana ta murmushi fuskan ta ya fito Sosai. Da sauri Hajiya Jiddah da Fad'imatu suka mik'e, "Mama yarinya ta Zahra tabbas ita ce a Ina suka samo ta, ta fad'a Tana mai fashewa da kuka. "Don Allah Mama mu tafi yau kar in rasa y'ata, Sosai Hajiya Jiddah ta tausaya ma Fad'imatu domin rashin d'a ba dad'i. "Karki damu y'ata yanzu Zan Kira Yar uwa ta shiryo mu tafi, bari in sa ayi Mana booking d'in flight. "Nagode Mama da gudu ta shige d'aki ta fara had'a Kaya domin yau zata ga rabin ran ta. ************************* MAIDUGURI Anyi ma Bintu Aiki an ciro yarinya katuwa sai dai yarinyar gaba d'aya tazo da wani irin siffa Wanda sai da likitocin ma suka ji tsoro, inda ya zamana sun kasa fito da yarinyar, kwanan Yarinyar d'aya ta mutu sakamakon tsotse Mata jini da Aljani duna yayi dama y'ar shi ce don cikin ma nashi ne. Hakan yayi ma Momy dad'i daga Nan tace ya bata takardan ta su bar gidan, Haka Alhaji Bukar ya saki Bintu saki Uku, Yagana ita ma karamar Hauka ne kawai batayi ba, ga wasu k'uraje da suka feso Mata a matse-matsin ta da ta sosasu sai su dunga jini had'e da wani ruwa Mai k'arni. Haka suka Kama hanyar k'auyen Zulum, suna isa Yan uwan Yagana suka ce Basu San wannan ba, don lokacin da suka samu duniya mantawa tayi dasu sai yanzu ne zata kwaso Mahaukaciya ta kawo musu gida. Aiko sai ga Asabe ta lallabo tazo ita da Mami da take tuka keken guragu da Khausar ta Aiko Mata dashi. "Hajiya Yagana surikar Alhaji Bukar, Ashe Kuma kema kin fara girban duk Abun da muka shuka, kamar yadda nima nake girba Koh.? "Hhhh Amma fa naji dad'i, to yanzu Ina kuka dosa ne? "Uhmmm Yagana kenan Ashe kina duniyar Nan naji duk Labarin k'ulle k'ulle da kuka yi ai, Allah ya kyauta yanzu sai a San nayi. Juyawa sukayi suka tafi Abun su. "Kece Yagana ko,? Dama Mai gari ne ya Aiko ni yace An bada umarni tun daga sama cewar kar a barki ki zauna a garin Nan Saboda haka an baki Awa d'aya ki gama Abun da zakiyi ki bar garin Nan. Fashewa da kuka Yagana tayi yau ne ranar farko da tayi ainihin nadama na gaske a Rayuwar ta. MASARAUTAR AMRISH "Kai ka fad'a mun gaskya Kai waye ne.?! "Ke na fad'a Miki ban San ni waye ba, dallah sake ni ya fad'a haka Yana mai kwace jikin shi

Chapter 8 of 11