bayani da kan ka.
"Hhhhhhhh!!! Tabbas kin kyauta da kika kawo ta, ke Bintu ki sani cewa shekara ta Hamsin Ina wannan harkan,ba Wanda ya tab'a mun gardama sai ke, ki sani wannan cikin nake dole sai an ba Aljani mai gizo yasha jininshi sannan aikin mu zai cigaba da tafiya,in har mai gizo bai Sha jinin shi ba komai zai iya faruwa don duk wani Boyayyiyar K'ulli sai ya warware.ku tashi ku bani guri. Ku dakata ku dakata. Dole ki bar Sallah in cikin ki ya Kai wata takwas, Saboda a lokacin Aljani mai kitso zai zo ya shanye cikin, Kuma kidai na jin karatun kur'ani, kar Kuma ki ajiye kur'ani a d'akin ki.ku tashi ku bani guri da fatan zaku kiyaye Abunda nace muku.
"Eh! Eh! Boka zamu kiyaye.
*************************
Duk sun fito kowa yayi Shirin tafiya, Daddy kawai suke jira ya fito.sai gashi ya fito. Dama komai ya kammala tafiya kawai ya rage musu.
Sun Kama hanyar Katsina. Suna tafe daddy Yana ta ma yaran nashi Nasiha, Sosai Nasihan ya ratsasu tun daga Mota suka rumgume juna ita da Khausar suna kuka mai Tsuma zuciya,har Mami sai da tayi kwalla taji Tana kewar yaran nata. Karfe Sha d'aya suka isa Cikin garin Katsina, bayan sun shiga Makaranta D'aki guda Daddy ya Kama ma Zahra a hostel komai an sa Mata a D'akin har da kayan kallo, Haka Khausar ta taya ta suka shirya komai a kitchen d'in ta da ke d'akin, bayan sun kammala suka fito da Abincin da Mami tayi musu tun daga gida suka ci, har dambun Nama Mami tayi ma su Zahra Kuma Daddy yaji dadin haka Sosai. Sukayi sallar Azahar suka fito don su tafi, Aiko Zahra taje ta rungume Mami Tana kuka, Khausar ma Zuwa tayi ta rungume su, duk da bawani shiri sukeyi ba Amma wannan shine karo na farko a rayuwan su da bazasu kwana guri d'aya ba.sai da Daddy ya zare su ya sasu a Mota sannan suka rabu.ya Kuma lallashi Zahra ya Kara Mata Nasiha. Sannan suka tafi ita Kuma ta koma Hostel.
Sun koma gida ana Kiran sallar Magriba.sai da dare Yayi taje kwanciya Nan ta Kara kewar Yar Uwar tata, waya ta d'auka kaman zata kirata sai Kuma tayi tsaki ta jefar da wayan.ta juya kwanciya.
Washe gari haka su Daddy suka Kai Khausar Makaran ta Kano. Tunda Mami ta dawo taji gidan ya Mata fad'i gashi ranar Daddy ya koma Kaduna.
Kenan haka zata kasance in ta Aurar da yaran nata.✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Like
Comments
Wlh Rashin Comments din ku shi ke sani kasalan yin muku typing.Amma da Ina ganin Comments kacha kacha wlh kullum zaku dunga ganin posting.in kun gyara in gyara Ehe🙄🥴
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍🥰🥰💖💖💖.
BOYAYYIYAR
K'ULLI😭😭😭
STORY
AND WRITING
BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
LAA YUKALLIFUL LAAHU NAFSAAN ILLAAH HUS'AHAA.
PAGE 13
Da Asuba Dadddy ya d'auki wad'an Nan akwati Nan ya sasu a Mota, Yana fitowa Masallaci sallar Asuba, Ya Kama hanyar Katsina. Karfe takwas na Safe Daddy ya isa Katsina direct School d'in su Zahra ya wuce,ya kirata, bugu d'aya ta D'auka lokacin ta fito wanka kenan Tana Shirin Zuwa aji, Saboda suna da aji karfe Tara na safe.
"Assalamu alaikum Daddy Ina kwana, da gaske daddy kana makarantar mu to ganinan fitowa shaf-shaf ta sa Kaya ta shirya ta fita bakin hostel.
Tun daga Nesa yake kallon ta cike da tausayawa Saboda bai San wani irin rayuwa zata shiga ba in bashi a raye, gashi yanaji a jikin shi tamkar ya kusa barin iyalan shi, Kuma duk ciki yafi son Zahra Saboda hakurin ta, Yasan duk irin musgunawan da Mami takeyi Mata, kawai dai Yana kau da Kai ne. Har ta k'ariso bai sani ba ya shiga duniyar tunani.
"Daddy lafiya kuwa Ina ta Sallama kayi shiru,? Kuma na ganka duk cikin damuwa.?
"Lafiya lau Zahra jiya kin ga Alert Koh.?
"Eh Daddy na gani, Allah ya k'ara bud'i yaja kwana daddyn mu, Yauwa Daddy Wai har yanzu ba'a samu Number Yaya Sadeeq d'in ba.?
"Ameen ya Allah baby Zahra, Allah ya Albarka ci rayuwan ku duk in da kuke, Har yanzu ba'a Samu wayar Yayan ku ba, Nasan ya kashe ne Saboda Yana fushi dani. Bud'e boot d'in Motar shi yayi ya fito da Akwati babba guda d'aya ya mik'a Mata. "Fatimatu Zahra. Da sauri Zahra ta d'ago Kai don tasan in dai Daddy ya Kira ta da wannan sunan magana mai Muhimmaci zai Mata.
"Na'am Daddy."
"Wannan akwatin da kike gani, Abubuwa ne Masu Matukar Mahimmaci a rayuwarki da na Yayan ku, na kasa yarda da kowa Wanda zan Damk'a mai wannan Akwatin sai ke, Ciki kuwa har da Mahaifiyar ku na k'asa yarda da ita, Ina so ki tabbatar kin samu guri mai Muhimmaci kin Adana shi Amma Banda gida, don bana buk'atar inda Akwatin Nan ya fito gida ya koma,don babban Had'ari ne zaman shi a gida. Sannan Ina so karki tab'a bud'e Akwatin Nan har sai Labarin mutuwa ta ya riskeki.yana Gama fad'in Haka ya shige Mota ya tafi.
Kuka Zahra ta fashe dashi duk jikin ta yayi Sanyi da kalaman Daddy sai Tana ganin tamkar bankwana yake Mata. Dafata taji anyi ta baya da sauri ta waigo, ganin Ruk'ayya ce da sauri ta rungume Ruk'ayya Tana kuka, Haka Ruk'ayya ta ja ta da Akwatin suka shige hostel.
Dadddy bai tsaya ko Ina ba sai Kano. Direct Makarantar su Khausar yaje. Ya dunga Kiran wayar ta bata d'auka ba sai ya fara tunanin ko Tana Class ne, wani Abokin shi ya Kira da yake lecturing a school, Cewan Yana Neman Khausar Habibullahi Zaria, yace zai sa a duba mai ita Wasa-wasa sai da Daddy yakai karfe biyar na Yamma ba'a ga Khausar ba, Kuma har Class d'in su anje ga Yan Class d'in Nan ma suna Lecture Amma ita ba ta Nan, Abun yayi Matukar ba Daddy Mamaki. Haka ya shiga Motar shi Yana Shirin tafiya sai ya hango Khausar an sauke ta a Mota tasa wasu matsiyatan Kaya harda Attarch kamar ba y'ar Musulma ba. Jiri ne yaji Yana Shirin d'iban shi, me hakan ke Nufi tarihi zata mai-maita kanta kenan. Ina tarbiyan da ya ba su Khausar, Tun daga Nesa Khausar ta Hangi Daddy yana jingine da Motar shi, gaban ta ne ya fad'i don tasan Daddy bai iya fushi ba.
"Daddy Sannu da Zuwa Amm amm dama ban dad'e dama fita ba na d'an je Neman wani Book ne gashi ma ban samu ba.
"Dakata Khausar d'auki Akwatin can ki bar gurin Nan kafin Rai na ya Gama Baci dake. In kin so ki Adana in kin so ki wulak'antar.yana Gama Fad'in haka ya shige Mota Abin shi. Gaba d'aya Khausar ta shiga Damuwa don ta San shirun Daddy ba Alheri ba ne, Zai iya Zuwa ya k'are a kan Mami. Haka dai jiki a sanyaye ta d'au Akwatin ta shige Hostel.
*************************
MAIDUGURI
Zaune takeyi a Falo ta zabga tagumi gaba d'aya Abun duniya ya dame ta.
"Ranki ya dad'e na gama Had'a Miki ruwan wankar . Hannu kawai ta d'aga Mata, ta fahimci me take nufi, sum sum ta wuce Abun ta, Tana mamakin me ke damun Uwar d'akin nata kwana biyu.
*************************
Da tambaya tambaya har Ashawo ya isa gidan su Uwar Sharri, lokacin dare yayi Sosai karfe Tara na dare. Wani Tsoho ne ya fito jin irin Sallaman da ake ta rafkawa. "Lafiya Mallam daga ina.?
"Yauwa Baba don Allah Nan ne gidan Mallam Tsalha.?
"Eh yaro Nan ne, nine ma Mallam Tsalha.
"Ok to ko ka San wannan.? Yana mai Nuna mai Uwar Sharri.
Jiki na rawa tsohon Nan ya fara Nuna Uwar sharri da Hannu jikin shi na rawa...."Asabe kece a Haka.? Asabe Kinga inda duniya take bida Mutum Koh.!! Fashewa yayi da wani kuka Mai cin Rai, Yana juyawa gida da sauri Yana k'wala Kiran "Tasallah fito ga Asabe.
************************
ZARIA BIRNIN SHEHU
Tunda Daddy ya dawo gida ya shiga Damuwa Sosai ganin Halin da ya ga Khausar a ciki, ga Shari'an da sukeyi gaba d'aya a sark'ak'e yake, jiya dai da yaje Kano ya Kara tattaro wasu shaidun da Yana gabatar dasu anzo k'arshen Shari'ar. Ciki kuwa har da wani USB Camera da wani Recording. Duk Daddy ya gama tattara komai ya Zuba su brief case d'in shi Yana jiran gobe in Allah ya kaimu yaje ya gabatar dasu a gaban kotu.
Karfe D'ayan Dare 1:00AM
Dare ya tsala ba Abun da akeji sai harbe-harbe, Daddy ne ya Mik'e firgigit. Mami ne ita ma ta tashi tun lokacin da ta fara jin harbe-harben. K'aran ihun mai gadi suka ji, Basu Gama jimami ba sukaji an bankad'o kofar Falon...✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Like
Comments
More Comment more typing
Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍😍
*'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭
STORY
AND WRITING
BY
ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
B'OYAYYAR
K'ULLI 😭😭😭
STORY
AND WRITING
BY
ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU.
ALHMDULILLAHI NA GODE ALLAH DA YA BANI IKON DAWOWA DON CIGABA MUKU DA LITTAFINA MAI SUNA A SAMA. ABUNDA YASA KUKA JINI SHIRU MUNYI WALIMA SAUKA NE NA ISLAMIYA.
INA SON KU FANS💖💖💞💞
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
WAMAN YATAWAK KAL ALAL LAH FA HUWA HASBUN
PAGE 14
Daddy da sauri ya Mike zai fita, Mami tayi sauri ta rik'o shi. "Don Allah Daddy Yara kar ka fita. Bata Gama rufe baki suka bankad'o kofar, wasu Manyan mutane ne gwanin ban tsoro sun rufe fuskokin su da mask suka shigo d'akin hannun su d'auke da Manyan bindigogi. Sai da suka k'are ma d'akin kallo tukun na suka ce. "Barisster Habibullahi Sadeeq Koh.? Wato Kai Mai gaskiya Koh...? Ka tashi ka D'auko Mana CD da wad'an Nan takardun da ke hanun ka, ko yanzu ka gangara lahira.
"Don Allah..! Kar ku kashe shi zai baku. Dadddy Yara don Allah ka basu. Mami ta fad'i haka cike da rud'ewa. "Gaskiya bazan tab'a iya bayarwa ba sai dai ku kashe ni. Daddy ya fad'a cike da kwarin gwiwa.
Bai gama rufe baki ba suka rufeshi da duka da kasan bindigan su, sai da suka tabbatar ya ji jiki suka Kara tanbayar shi. "Zaka fad'a Mana ko bazaka fad'a ba.? Suka fad'i haka cikin tsawa.
"Don Allah Daddyn Yara ka basu mu huta.
Ogan ne Yana yaran shi umarnin suje su bincika Mai gidan ko Ina da ko Ina. Suna cikin Haka ne suka fara jin jiniyar Yan Sanda, Aiko ogan nasu ya ba daddy wani duka a Kai da K'asar bindigan su tuni Daddy ya sume. Haka suka Fice a gidan a guje, Nan aka fara musayar Wuta da Yan Sanda, da k'yar suka samu suka gudu. Nan da nan aka fito da Daddy aka tafi dashi babban Asibiti A.B.U. .
Mami taci kuka tun dare ta sanar da su Zahra, Asuba ya musu a cikin Zaria ne Haka suka had'u suna ta kuka. Suna cikin wannan halin ne sai ga likita ya fito yace musu, "zaku iya shiga ku ganshi Amma karku dame shi da surutu, Haka sukayi rige-rigen shiga D'akin.
"Sannu Daddy. Kawai binsu yayi da kallo Yana hawaye. "Ku matso kusa Dani Yara na. Laure kema ki k'ariso, Laure Abunda na dade Ina B'oyewa shekara da shekaru sai ya Bayyana, Tabbas mutuwa Mai tonon Asiri, Ni na san bazan tashi ba. Amma don Allah ki cika ma Hajiya Guggo wasiyyar ta na had'a Auren Zahra da Sadeeq. Da sauri su Zahra suka d'ago suna kallon Daddy fuskan su cike da alamar tanbaya. Tabbas ba ciki d'aya kuka fito da Sadeeq ba, Mahaifiyar ku zata baku Labarin wata Rana. Tari ne ya sark'e Daddy ya fara yi, can sai ya fara Aman jini had'i da kalmatush shahada. Nan Daddy yace ga duniyar ku Nan.
Ihu Zahra ta saka Tana girgiza gawar Daddy, Nan da Nan likitoci su shiga Aune-Aune suka tabbatar da Rasuwar shi sannan suka Mika musu gawar shi. Haka suka dawo gida. Tun a Mota Zahra ke gwada Number Yaya Sadeeq da k'yar ya shiga.
"Hello Baby kiyi hakuri wlh wata yafiyar gaggawa ta taso mun Zuwa India sai jiya na dawo. Yasu Mami da Daddy, da Yar tsohuwa ta. Fashewa tayi da kuka."Yaya kazo gida ba lafiya. "Zahraty Lafiya me ya faru.? Ya fad'i Haka cikin rud'ewa. Khausar ne ta fige wayar tace mai "to ai sai ka dawo gida Daddy ya rasu. "What! Daddy ya rasu fa kika ce.? Ya fad'a a rud'e.
Cikin sauri yayi waya yace ayi mishi booking na flight da zai kaishi kaduna yanzu-yanzu. Cikin mintoci aka Gama komai ya Kama hanyar Kaduna.
Ya iso gida yazo ya tarar da gida a cike tun daga kofar gida har cikin gida, kawai ya yanke jiki ya fad'i.✍️✍️✍️
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍
Well come back na dawo insha Allah da Zafi na👊👊👊
*'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭
STORY
AND WRITING
BY
ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 15
*************************
Haka aka d'auki Sadeeq aka shiga dashi ciki Ana mishi fifita, Nan aka Kira family doctor d'in su. Bayan ya iso ne yayi Mai gwaje-gwaje da Allurai, yace su barshi ya huta Saboda jinin shi ya hau sosai. Zahra ce ta zauna dashi, yayin da Khausar ta d'ukufa bincike a D'akin Daddy,wani Deary ta gani a D'akin Daddy cikin wani karamar kit Yana ta d'aukan ido. Jikin ta na rawa ta bud'e Deary ta fara karan tawa, wani zufa ne ya fara keto Mata jikin ta har rawa yakeyi, Dama Sirri da Mami take cewa sai ta tona kenan, ta shiga uku ita Khausar indai haka ne to ba Wanda ya can-canci Auren Yaya Sadeeq sai ita. "Wallahi indai Ina raye ni Zan Auri Yaya Sadeeq, Zama tayi a gefen gadon Daddy tamkar Wanda take tunanin wani Abu. Zunbur tayi ta mik'e ta fita, d'akin su ta shiga ta fara kaiwa da dawowa.
Zaune suke a Falo kowa shiru-shiru Mami ne taga fitowan Khausar daga d'akin daddy, da sauri ta tashi ta bita Zuwa d'akin su. Ko Sallama ba tayi ba, tace "ke Khausar me kikaje yi d'akin daddy ku.? Tanbayar a bazata tazo ma Khausar. "Wai dama Mami Abunda kuka Dade Kuna b'oye Mana kenan.? Ta jefa Mami da wannan tanbayar. Jikin Mami ne ya fara rawa, "Zo Khausar fad'a mun me kika gani,? Kwashe duk Abun da ta gani a deary d'akin Daddy tayi ta fad'a ma Mami, Murmushi Mami tayi tace Mata"Alhmdulillahi Khausar tun da kin riga Kinga Abunda muka dad'e muna b'oye muku, yanzu kin sani Saboda Haka nake so in sanar dake cewa Sadeeq baida wata Matar Aure sai ke. Da sauri ta rungume Mami Tana mai jin wani farin ciki a Zuciyar ta don ita yanzu tun da taga wannan Deary d'in take da wani Manufa a Zuciyar Wanda b'oyayyiyar sirrin ta ne.ko Mami ma bazata sani ba, Haka suka rabu kowa da nashi kud'irin a Zuciyar shi.
KAUYEN ZULUM
Kuka Sosai Asabe takeyi Tana rokon baba Tsalha da Inna Tasallah akan su yafe Mata, "Inna tabbas Bariki ba riba, don ban kwashi komai a ciki ba sai tarin nadama. Allah na tuba Innah Ina so naje in warware sharrin da nayi domin Ina ji a jiki na shi ke bibiyata. "Wai Asabe sumbatun me ki keyi Haka ne.? Wani sharri ne Zaki warware kina kwance Rai a hanun Ubangiji. "Innah Ina ajiya ta.? "Ajiyar ki na gurin Yar Uwar ki.
*************************
MAIDUGURI
Ta Kama yau Alhaji Bukar Mai Naira ya shigo cikin garin Maiduguri, in da ya sauka cikin farin ciki da Nishad'i don ya kosa ya isa gida don ya ga cikin Bintu, don har ya cire Rai zai Haihu a duniya.
Da gudu Bintu ta fito taci Ado da wani rantsattsen Lafaya ta nad'a shi ta fito a Kanurin Asali, Dan cikin ta ya fito yayi Mata das a gaba. Rungume Alhaji tayi ta na Mai sannu da Zuwa. Bayan ta taimaka Mai yayi wanka ya shirya suka fito falo ya zauna don cin Abinci, Yana ci Tana zuba Mai shagwaba tare da kisisinar ta. Bayan sun Gama ne sun koma falo suna zaune, Alhaji yace...."Bintu ki fad'i duk Abunda kike so tukuicin farin ciki da kika sani a yau, gaskiya nayi farin ciki da cikin nan. Dole za'a Nemo Doctor da zata cigaba da kula da cikin don ban son Abun da zai sameshi Allah ya sa ki haifi Mace in sama Mata Fad'imatuz Zahra sunan Mahaifiya ta. Murmushi Bintu tayi had'i da kashe murya da k'ara shagwabe fuska, "Alhaji ni gidan gonan ka na Borno nake so ka bani. "An gama Uwargida ran gida daga ke ba wata. Wani farin ciki ne ya lullube Bintu...
*************************
ZARIA BIRNIN SHEHU
"Sannu Yaya Sadeeq, ya jikin naka yanzu.? "Naji sauki Zahraty shikenan Daddy ya tafi ya barmu a wannan duniyar, Cikin garari, yanzu ba mu da kowa sai Mami da Yan uwan ta gashi har yanzu Mami taki Bari mu San Family d'in ta, ko zuwa zatayi sai dai ta tafi ita kad'ai Kuma su Basu cika Zuwa Nan ba, shi Kuma Daddy dama su Uku Hajiya ta Haifesu kamar yadda ya haifemu. Sai dai su biyu Maza ne Mace d'aya Asalin su Yan Maiduguri ne wani Hari da Boko Haram suka Kai ne yasa suka dawo Nan da k'yar in da Yar Autan su Daddy ta b'ace ba'a ganta ba har yau. Ya k'arishe maganar Yana share Hawaye. Zahraty yanzu kece Matsala ta, don nasan Mami ta tsaneki daddy ne ke dakatar da ita Amma zanyi iyakan k'okari na na ganin na baki farin ciki.
Yau ta Kama sati biyu kenan da Rasuwar Daddy inda Mami ta Tara yaran nata domin yin musu bayani Abunda Daddy yace, sai dai ta canza nata.
*************************
JOS
"Tabbas Hajiya wannan yarinyar Tana tare da Sihiri Mai karfi a jikin ta, Wanda kafin a karya shi za'a Sha bakar wahala. Amma insha Allah zamuyi Anfani da Ayayoyi karya Sihiri da sauran Magungunar da suka dace sai dai Zaki barta anan har sai mun Gama Mata duk Abun da ya dace. "Shikenan Mallam ba damuwa Allah ya taimake mu ya bamu sa'a.......✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comments
Like
Vote
Insha Allah Zeey Yar mutan Zazzau ta dawo da karfin ta comments din ku shine karfin gwiwa ta Ina son ku fans🥰🥰🥰🥰
Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍💖🥰
*'BOYAYYAR 'KULLI*😭😭😭
STORY
AND WRITING
BY
ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Yanzu aka fara wasan kudai kawai ku cigaba da bin Yar mutan Zazzau.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 16
*************************
"Abun da yasa na Tara ku Anan shine Sadeeq zaka Auri Khausar. Da sauri suka d'ago fuska suna kallon Mami cikin Mamaki, Banda Khausar da ta cigaba da Danna wayar ta. Ko ta d'ago Saboda ta riga ta San komai. "Mami bamu gane me kike Nufi ba ki Mana bayani Taya Zan Auri Khausar Tana k'anwa ta.?
"Haka Daddy ku ya bar wasiyya Saboda Khausar da Zahraty ba ni na Haifesu ba. Sadeeq kai kadai na Haifa Su Zahra D'auko su nayi a gidan Marayu ni da Daddy ku. Kuka Sosai Zahra takeyi yayin da take jin wani Soyayyan Yayan nasu Yana ratsa ta, meyasa to Mami tafi son Khausar a kan ta. "Mami in dai Haka ne to ni Zahra nake so ba Khausar ba. Da sauri Zahra da Khausar suka d'ago kan su a tare, suna kallon Sadeeq d'in. Fashewa da kuka Khausar tayi ta rungume Mami, "Wai me nayi ma ka Yaya Sadeeq ka tsaneni, meyasa kafi son Zahra a Kai na da Mai Zahra ta fini eyeh!.?
"Bari kaji Sadeeq in dai ni na haife ka baka da Matar da ta wuce Zahra ita zaka Aura Dole kaji na gama magana. Ta tashi ta Basu guri. Khausar ne ta Mike ta yima Zahra wani wulak'antaccen kallo sannan taja tsaki tayi gaba. Sadeeq ne ya jawo jikin shi ya iso gurin da Zahra take zaune, da tunda aka fara maganar Bata ce komai ba sai kuka da take yi. Don ta dad'e da ji a ranta dama Bata da gata Daddy ne da Yaya Sadeeq gatan ta, Bata tab'a tunanin ta kamu da Soyayyar Yaya Sadeeq ba sai yau. "Zahraty kiyi hakuri ki dai na kuka duk runtsi duk wuya bazan Auri Khausar ba ke Zan Aura."
"Ka dai na Fad'in haka Yaya, kabi Maganar da Mami tace don yi Mata biyayya, ni Zan iya hakura da Abun da nake so don farin ciki Twinie na, har yanzu Ina son Khausar Soyayya ta ko digo bai goge a Zuciyata ba. Tana gama fad'i haka ta tashi ta shige d'aki ta bar Sadeeq a gurin.
ONE WEEK LATER
Sadeeq ne ya fito D'auke da Akwatin shi a hannu gasu Mami duk sun fito domin rakashi.
"Kadai ji me na fad'a ma Koh ka dunga Kiran mu a waya Kuma kana dawowa weekend Saboda yanzu ba da bane, Sannan maganar Auren ku bana so ya d'auki lokaci in ka dawo dai zamuyi magana. "To Mami ba damuwa.
Bayan tafiyan Sadeeq su Zahra sun koma school yayin da Khausar ta cigaba daga inda ta tsaya, domin yanzu ya Kai ma da cewa kaf School ba Wanda Bai San khausy babban Yarinya ba. Domin duk wani fati da za'ayi a School d'in sai da ita zai tafi dai dai, duk wani Club ta sanshi. Ga shaye-shaye da Less da tasa ma gaba.
Zahra ko ta dukufa karatu, don duk department d'in su ansa Zahra disntintion don tunda suka fara Abun da take d'auka kenan. K'awar ta d'aya ce a Makarantar Murjanatu Babagana Asalin ta Yar Borno ce. Ita ma akwai k'ok'ari sosai, shiyasa nasu yazo d'aya sai suka koma Room d'aya Abun su suna zaune tare, dukan su bawan zai b'oye ma y'ar uwan shi damuwar shi, Shiyasa Khausar ta ba Murjanatu Labarin Abun da ke damun ta sai dai Bata sanar da ita sudin D'auko su akayi gidan Marayu ba. "My sweet Zahraty karki damu ki cigaba da Addu'a wallahi indai Yaya Sadeeq mijin ki ne sai kin Aure shi. Nifa har Kama kukeyi mun dashi kawai kin fishi fari ne, Kuma wlh kunfi dacewa dashi. Nifa kin San Allah na tsani wannan Twinie d'in naki, tun randa tazo Nan d'in nan tayi Miki wannan rainin, wallahi bazan iya d'aukan rainin Nan ba, Tana ji kaman an d'aura ma mucciya zani, da tsawo kaman falwaya... "Kai sweet Janah wannan cin fuskan ya isa haka, kin tasani gaba kina ta kushe mun Yar uwa. Ta fad'a cikin bacin Rai😔.
"To Mai Yar uwa.! Yar uwan da Bata K'aunar ki, Amma ki wani Nace Mata, ba dama a fad'a laifin ta, Tashi Murjanatu tayi ta Fice Abun ta cikin fushi.
Lokaci na tafiya yayin da Abubuwa suke ta juyawa, Khausar ta Zama cikakkiyar Yar duniya bama ko da yaushe take attending Lecture ba, Saboda ta samu goyan bayan tantiran lecturers Tana Abunda take so.
Yau ta Kama anyi hutu inda kowa ke murnar Zuwa gida, Yayin da Zahra take ji kamar kar ta koma gida Saboda irin wulakancin da Mami da Khausar suke Mata. Bayan anzo an d'auki Murjanatu ta tafi, Zahra ta shirya tsaf don Zuwa Tasha ta hau Mota don dai tasan driver bazai zo D'aukan ta ba, fitowan ta get yayi Dai dai da k'arisowar Sadeeq. Da Mamaki ta kalleshi