Rabe tsaya ka k'arisa dani Mana.
"Yagana kece da wannan yamnan,? Yaushe rabon ki da k'auye kin gujemu Saboda kin samu duniya ke da y'ar ki.
"Nifa Matsala ta da Kai kenan Rabe Shegen surutu ne da Kai.
Yauwa Rabe Wai naji Labarin ance Asabe Uwar Sharri ta dawo.?
"Ai ke dai Bari kawai Yagana wato dai in fad'a Miki Bariki ba riba in Kinga Uwar Sharri sai ta baki Tausayi bakyace itace Asaben Nan Yar gayu ba.
"Da gaske Rabe.?
"Wallahi da gske nake fad'a miki, sai kinje Zaki ganta.
Jikin Yagana ne duk yayi sanyi ga wani tsoro da ya k'ara Kama ta.
*************************
JOS
"Niko Ina Zan ganki Baiwar Allah Ina kika shige yau shekara Ashirin da biyu kenan, ko a wani hali kike ciki ban sani ba Nasan yanzu yarinyar ki tayi girma, Allah yasa Kuna gurin hannu na gari. Share hawayen ta tayi ta d'auki Envelope din da ya fad'o ta maida cikin Akwatin ta rufe Akwatin ta fito.
*************************
"Hajiya karki damu gaskiya muna ganin Sauki Sosai akan da insha Allah zamu samu Nasara."
"Allah ya yarda Mallam ya kawo Mata k'arshen matsalar Nan.π
"Ameen ya Allah Hajiya."
*************************
KANON DABO
Koda me kazo anfika Wai inji kanawaππ nidai nasan fad'i suke ba gskya bace.ππ€ͺ.
"What ba ta Mutu ba.! Ta fad'a cikin d'aga murya, "sai da na fad'a maka kar a samu matsala James. Yanzun tana wani Asibiti ne.?
Dole ne a bita har Asibitin a k'arisa ta.
"Angama Hajiya.....baza'a k'ara Samun Matsala ba.
"Ok ban bukatar jin wani labari in ba na mutuwar Mami ba.
"Sorry sweet Zahraty dole in rabaki da wannan Matar don Bata can-canci kulawar ki ba, ta hakan ne kawai zai sa kije ki Nemo Asalin ki.βοΈβοΈβοΈβοΈβοΈ
Sister Nafeesat saura inji bakin ki kince ya Miki kad'an sai na tafi yajin aikin typing ehee πππππ₯΄π₯΄
Zeey Yar mutan Zazzau ce πππ₯°π₯°
*'BOYAYYAR 'KULLI*πππ
STORY
AND WRITING
BY
ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
PAGE 21
"yauwa Zahra ko,?
Dama Ina so in sanar da ke zamu maida Hajiya Abuja domin a can za'ayi Mata aikin. Doctor yace bazai samu daman k'arisowa Nan ba.
"Ba damuwa Doctor yaushe ne za'a tafi da itan.?
"Eh yau da karfe Tara na dare anriga ma anyi booking flight da zaku tafi a Kai.
"Doctor waya biya kud'in flight d'in.?
"Eh wani ne ya zo d'azu yace shi relative d'in ku ne duk Abunda ake buk'ata a fad'a mishi zai bayar ba sai an nemeki ba.
"But Amma Doctor ban gane ko waye ba fa.
"To Malama Zahra nidai haka ya cemun, ya k'arisa maganar Yana tafiya Abun shi ya bar ta Nan tsaye Tana Mamaki da tunanin ko waye haka.
Yaya Sadeeq ne ya fad'o Mata a rai to kodai shine ya dawo. Kai Ina bashi bane ma da shine da ya Kira ta.
Sun sauka Abuja lafiya, bayan sun huta ne Likita yayi duk Abunda ya dace yanzu sai su jira ranar aiki Nan da sati biyu.
Karfe Sha biyu na dare yayi musu a cikin Asibitin Shika don cika aikin Hajiya Khausar Mai Zamani.
Sai dai an samu akasin don Basu ga Mami ba a d'akin, sunyi Mamakin yanda akayi Basu ganta ba.Haka suka koma suka fad'a ma Khausar Basu ganta ba, bata so haka ba but duk in da suke ma zasu had'u Alkawari ne tayi ma kan ta sai ta kashe Mami.
*************************
KAUYEN ZULUM
Sosai Yagana ta tsorata da ganin yanayin Asabe.
"Asabe haka kika koma,? mun shiga uku, ni da nazo ki kaini gurin wani Bokan domin Naga Alamun Boka Duna yanzu aikin shi ba yayi, sai in zo in ganki cikin wanan halin. Ta k'arisa maganar Tana kuka
Waiyo ni Yagana Ina Zan sa Kai na Anya ba K'ulli da muka b'oye bane yake bibiyan mu Asabe."?
"Ga Bintu can da tsohon ciki ga matsanancin Ciwon ciki da yaki barin ta kullum cikin firgici, ke Kuma ga halin da kike ciki Anya ba sakayya muke gani ba Asabe, na fara karaya ni, na fara jin tsoro.
"Yagana Ina so ki taimaka ki kaini gurin Alhaji Bukar don mu warware K'ullin nan.
"In banda abin ki Asabe in mun ce zamu warware K'ullin nan ta Ina zamu fara.? Bari dai in tashi inje gidan Guggo Hajinjin in kwana gobe Zan dawo mu k'arisa maganar mu."
*************************
JOS
Driver ne da sauri ya taso yazo ya Karb'i kayan da ke hannun Hajiya ya zuba a boot, ya zagaya ya bud'e Mata kofa sai da ya tabbatar ta zauna sannan yaje ya tada Mota.
"Hajiya gidan Marayun muka nufa.?
"Eh Haruna, Amma kafin Nan ka biya dani ta kasuwar Taminus akwai inda wasu mabuk'ata suke Zama suke bara.
"To Hajiya angama Uwar Marayu.
Sun isa kasuwar haka almajirai suka mamaye ta suna farin cikin ganin ta, da kan ta ta fito ta rarraba musu Sadaka tana rokon su su taya ta Addu'a Allah ya bayyana Mata Yar ta da jikan ta a duk inda suke. Haka suka dunga zubo Mata Addu'a kamar ba gobe da fatan Alheri, har kuka sai da Hajiya tayi suka shige Mota suka wuce gidan Marayu haka Nan ba ta raba musu duk kayan da ta kawo. Suna ta farin ciki da mata Addu'a, daga Nan suka wuce Masallatai ta bada Sadaka don asa y'ar ta a Addu'a,Daga Nan gida suka dawo.
"Masha Allah Hajiya an samu yanzu ta fara magana fa."
"Da gaske Mallam,? Alhmdulillahi ta fad'a wani Abu game da ita kuwa.?
"Gaskiya bata fad'a ba, kawai cewa take Ina yarinyar ta."
"Zan iya ganin ta Mallam.?
"Kiyi hakuri Hajiya bazai yuwu ki ganta ba, sai dai Zuwa Nan gaba in ta k'ara jin sauki.
"To shikenan Mallam Allah ya kaimu ya k'ara mata lafiya, bari in tafi na bar gurin sai da Abinci na ba kowa.
*************************
ABUJA
...............Bayan sati biyu
Anyi ma Mami aiki cikin Nasara, Kuma aiki yayi kyau Sosai inda nan da Sati d'aya za'a warware Bandage d'in da aka nad'e ta dashi. Sosai Zahra ke kula da Mami yayin da Mami tayi sanyi Sosai tare da alkawarin Sadeeq na dawowa zata Yi musu Aure, don Sadeeq bai da Matar Aure sai ita. Sosai Zahra taji dad'i maganar Mami.
Inna Suwaiba ma na iya k'ok'arin ta.
*************************
"Ka tabbatar bincike da kayimun dai dai ne.?
"Eh ranki ya dad'e wallahi iyakan binciken kenan, ko waye Zaki sa haka zai Miki.
"Ok good job, kaje Zan nemeka.
Wani murmushi tayi mai ma'anoni da-ban da-ban.
"Ranki ya dad'e su Esther fa sun sauka suna Airport, Kuma yau Hajiya kulu daga Adamawa zata turo da kayan nan Kuma tace masu kyau ne Sosai Zaki tura mata da Miliyan d'ari biyar in ciniki ya kama, Saboda kayan nata zafafa ne.
D'aga Mata Hannu tayi da mata alama da ido, nan da nan ta tashi ta je ta mik'a mata wayan ta, Kira ta danna ta d'ora a kunnen ta. "Hello Hajiya Kulu kin San ni ban son yawo da hankali Kuma bana siyan k'anan Kaya in har kin San kayan ki ba masu zafi bane kar ma su k'ariso Kano kin dai gane ko,?
Daga can bangaren aka ce "haba baby ke kin San nima bana harkan k'ananan Kaya ai zasu iso ai zaki gansu za Kuma ki tabbatar. Yauwa Baby wallahi Alhaji Lawalli ya matsamun fa akan maganar ku, ki bashi dama kawai ki dama wallahi sai kin ninka darajan ki.
"Dakata Hajiya Kulu bana son shirme kin gane ko, kin San dai ni ba Yar iska bace, duk iskanci na inayin Mai lasisi ne, ban shirya zubar da mutunci na ba na y'a Mace kin gane ai, ganina a bariki bashi zai sa na Zama Yar ta zubar ba, Saboda haka ki fita Ido na,har yanzu tarbiyan Daddy da Mami bai gama tafiya ba. Tana gama Fad'in haka ta kashe wayar ta.
Zama tayi a kujera ta fara jera tsaki. "Ke Hanna ki fad'a ma Jame yaje Airport ya d'auko su Esther, tana gama Fad'in haka ta haye sama.βοΈβοΈβοΈβοΈβοΈβοΈ
Much love πππππππ
Zeey Yar mutan Zazzau ce πππ₯°π₯°.
*'BOYAYYAR 'KULLI*πππ
STORY
AND WRITING
BY
ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
πππKar Wanda ya fara yace mun yayi kadan fa eheπππ
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
PAGE 22
Sosai Zahra ta ke ta cigiyar Yaya Sadeeq a Abuja, Amma duk yanda take tunanin Samun information a kan Haka bata samu ba, ga Mami ta damu akan shirun Sadeeq d'in gani takeyi duk laifin ta ne, ta Zama uwa Mai son zuciya da musguna ma y'ay'an ta idon ta ya rufe akan son zuciya da Cika burin ta na Boyayyiyar K'ullin da ke ran ta. Gashi tana Shirin rasa d'an ta d'aya tilo ita Ina zata ganshi, "Ya Allah ka Bayyana mun yaro na," ta fad'a Haka tana mai goge kwallan idon ta.
Haka sati ya zo aka warware ma Mami aikin, Kuma Alhmdulillahi aiki yayi k'yau Nan da kwana uku za'a Sallame su.
"Yauwa Suwaiba kindai ji Mai na fad'a miki Koh karfa ki bari a samu matsala.?
"Insha Allah Hajiya baza'a samu Matsala ba gidan ma angama cinikin shi Naira Miliyan dubu d'ari.
π²"Kai haba Suwaiba,?
"Wallahi kuwa Hajiya kud'in na gurin Aliyu, da kud'in Zinaren nata,yace gobe da karfe Sha d'aya na dare Visa mu zai fito sai mu d'aga sai Dubai, wato Hajiya kinyi dubara fa in ba haka ba haka Zaki tashi a tutar babu.
"Ke dai bari kawai Suwaiba aini wannan k'una yazo mun a dai dai, kin San Ina ta tunanin dama ya zamuyi. Sai ga Mafita yazo Mana. Kinga in har muka tafi sai taje ta k'arata Kuma ta Nemi iyayen ta nidai nayi gaba su Inna ma na dunga musu sako kam don bazan iya Zaman k'auye ba. Dariya sukayi suka tafa, "Amma Suwaiba kin iya zubin mutanen kirki fa.
Washe gari Zahra tayi ma sweet Jannah waya tunda dama tana Zaria akan cewa taje mak'otan su ta bada ajiyan kayan ta ta karb'a ta ajiye Mata a gurin ta gobe suna nan dawowa.
...........karfe Sha d'aya dai-dai na dare, Mami ne ita da Suwaiba suke ta sauri a cikin Asibiti yayin da doctor ke binsu a baya, bayan ya tabbatar da ya ba Zahra maganin barci sai nan da Awa biyar zata farka. Suna Isa kofan get suka mik'a ma doctor kud'in shi sukayi Mai godiya dai-dai Motan da zai d'aukesu ya iso suka shige.
*************************
JOS
"Ku su waye Ina Baby na,? Ina Hajiya ta.? Ku fad'a mun ta K'arisa maganar tana mai fashewa da kuka.
"Alhmdulillahi, Masha Allah Khadija kina jina.?
"Na'am ku su waye Nan a Ina nake,?
"Assalamu alaiki Hajiya kizo fa yau munyi Nasara, aiki yayi k'yau.
"Mai Napep kayi sauri mana.
"To Hajiya kiyi hakuri kin San yau akwai go slow ne.
"Allah dai ya kaimu lafiya ance y'ata ta warke, Mallam Mai Napep ka tayani murna yau kimanin shekara Ashirin da uku tana fama da lalura sai yau Allah ya yaye Mata, Lallai Ubangiji maji rokon bawa ne.
"Lallai Hajiya Naga kina son wannan y'ar taki, Allah ya Kara mata Lafiya.
"Ameen ya Allah π, dai dai lokacin da suka iso Alhuda Islamic center, dubu d'aya ta mik'a ma mai Napep ko ta kan Amsar chanjin batayi ba.
Barci takeyi Amma firgigit ta farka, Addu'a ta farayi, kafin ta Shafa ya Allah kasa mafarkin na ya zama gaskiya Dija y'ata ta dawo gareni.
Tashi tayi tayo Alwala tazo tayi nafila raka'a biyu kowacce raka'a ta karanta fatiha da kulhuwallahu, bayan ta idar ta Mai da goshin ta a k'asa tayi ma Annabi S.A.W salati sai ta karanta la ilah ha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zaleem kafa arba'in da d'aya, sannan ta fara yo ma Ubangiji kirari da sunayen sa kyawawa sanna ta roki bukatun ta.
Yar uwa wanna Sallah sadaka ce na baku ku gwada ki gani in dai ki daure kika rike wannan Sallah baki da shamaki gurin Amsar Addu'a ki insha Allah,sannan Ina barar Addu'an ku duk Wanda yayi Sallah Nan ya sani a cikin Addu'a shi Allah ya cikamun buri na na Alheriπ.
Game da matsalan da muke fama dashi Kuma a kan garkuwa da mutane da Yan bindiga.
In har kika rike wannan Yar uwa insha Allah Allah zai kareki daga sharrin masu garkuwa da mutane.
Duk bayan Sallar Asuba in kinyi Azkar kin Gama
Ki karanta
Salamun k'aulin min rabi Raheem.
Kafa d'ari da talatin da d'aya 131.
Bayan Sallah la'asar ma haka Zaki Karan ta
Da bayan Sallar Magriba.
A kalla ki samu kwana talatin kinayi, insha Allah Yar uwa Allah sai ya tsare ki daga sharrin su.
Allah yasa mu dace.
Bayan ta gama duk wani Addu'an ta ta Shafa sannan tayi shafa'i da wutiri. Ta kwanta tana mai Addu'a.
*************************
MAIDUGURI
Sosai ake rik'e Bintu tana fisfisgewa kamar Mai Ciwon farfad'iya.
Da Sauri Yagana ta shigo gidan a rud'e, Saboda wani mummunar Mafarki da tayi da Bintu tana Zuwa tarar da Bintu inda take wani juye juye kamar Macijiya tana kanan nad'ewa ga ciki, gashi jini ya b'alle Mata sai zuba yake yi tamkar an bud'e fanpo. Wani ihu ta yi ta k'arisa gurin Bintu da gudun ta tana rungume ta, sai ji kawai tayi anyi jifa da ita, da gudu Bintu ta shige kitchen d'in gidan ta d'auko wuk'a ta bi Yagana dashi tana fad'in "wallahi sai na kashe ki Yagana tana fad'a tana dariya da kuka a had'e. Sosai Yagana take gudun ceton ran ta, haka suka dunga zagaye gidan nan da k'yar aka samu manyan Samari su goma ma'aikatan gidan suka rik'e ta aka k'wace wuk'ar suka sata a d'aki suka kulle.
Sosai Yagana ke kuka tana Dana sanin Abun da suka aika ta gashi sanadiyar haka zata rasa y'ar ta d'aya tilo. Sosai Bintu take jijjiga kofar d'akin, take fatali da kayar d'akin ga jini na ta zuba mata yaki tsayawa. Cike da tashin hankali aka Kira Alhaji da yaje wani Meeting a Abuja akan yazo gida yanzu ba lafiya.
*************************
ABUJA
Sun isa Airport suna jiran kawai zuwan jirgi ne yayin da Aliyu yake Zaune kusa da Mami Yana mata bayanin yanda komai ya tafi dai dai jakar kud'in ya mik'a mata ita Kuma ta bud'e shima ta bashi kason shi yayi musu Sallama ya tafi Yana mai murmushi masu ma'anoni da yawa, Yana barin gurin ya Kira Jame ya sanar dashi komai is set up, cemai yayi ba damuwa zakuyi magana da Hajiya tana jiran ka guest house d'in ta dake maitama.
"Ba damuwa shikenan, ya kashe wayar shi ya hau motar shi sai gurin gimbiyar shi Khausar yarinya Yar k'walisa Mai tashe Wanda yanzu duk wata Hajiya da take irin harkan nan tasan Baby Khausar.
Mami ne ta mik'e jin an fara sanarwan ga jirgi nan, kawai ji tayi Suwaiba ta samata bindiga a wuya tace mata wuce muje......βοΈβοΈβοΈβοΈβοΈβοΈβοΈ
π€£π€£π€£π€£π€£More Comment more typing ehee.
Don yau nasan na saku a rububiπ€ͺπ€ͺπ€ͺ saura inji bakin wasu in tafi strike eheππͺ.
Sister Adama lafiya jiya banji Comments naki baππ
Zeey Yar mutan Zazzau ce πππ₯°π₯°.
Love you fansπππ
*'BOYAYYAR 'KULLI*πππ
STORY
AND WRITING
BY
ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
Jumma'at Kareem ππ to you All my fans
Karku manta da karanta suratul kahfi.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
PAGE 23
Jikin Mami na rawa ta kalli Suwaiba tace "lafiyan ki k'alau kuwa Suwaiba meye kikeyi haka.?
"Hajiya Laure kenan kema kin San Zan iya yin komai akan kud'i, kamar yanda kema kika aikata ciki kuwa har da Had'a baki da ke gurin kashe Mijin ki, da Kuma Batar da d'an shi da kikayi don kin San ba ke kika haifeshi ba Koh.?
"To Bari in fad'a miki nasan duk wani k'ulle-k'ulle naki, nima siyata akayi da kud'i ninkin Wanda kika bani da alkawarin Ina kawoki Zan d'aga sai Dubai π€·. Kinga Ina zanyi Wasa da dama ta, oya shiga Mota muje ko in fasa kanki da bindigan hannu na.
Jiki na rawa Mami ta hau Mota, tana shiga suka had'a Ido da Aliyu, zaro Ido tayi tana nunashi "harda kai ma,? Lallai duniya ba masu Amana yanzu."
"Hajiya kenan ke har Zaki fad'i masu Amana bayan ke ne no one na maciya Amana, kin tarwatsa iyalan ki Saboda son Abun duniya irin naki, kin sa y'ar marainiyar Allah cikin gararin rayuwa, shine kike tunanin Allah zai barki. Ya k'arishe maganar shi Yana mata murmushi da ya zama tamkar taken shi, yaja Mota suka tafi.
Fito da ita akayi suka sata a Mota duk tana barci, jakar ta da takardan da Mami ta saka Mata duk Yana rik'e a hannun ta bata saki ba, can hanyar fita garin Abuja suka je wani daji suka jefar da ita a gefen titi. Suka hau Motar su sukayi gaba abinsu.
Sosai Alhaji Bukar yake sharara gudu, hankalin shi duk a tashe jin Halin da Matar shi ke ciki da cikin jikin ta da ya kwallafa rai Yana so yaga gudan jinin sa a duniya kafin ya mutu.
Duk da Yana cikin wannan halin bai hana shi hango kamar mutum ne kwance a gefen titi, Kuma kamar Macece ma haske ta yayi da fitillar Motan shi yaga tabbas fa mutum ce, sai ya fara tunanin Anya ba irin y'an fashin Nan bane da suke irin haka, shiyasa Alhaji Habib yace ya bari ya biyo jirgi yaki bari, a haka har yazo ya wuce ta sai yaji bazai iya tafiya bai taimaka mata ba, yasan shidin Yana tare da kariyar Ubangiji Saboda shi mutum ne mai yawan addu'oi da dogaro ga Ubangiji, haka ya dawo baya yazo dai dai gurin yayi parking d'in Motar shi ya fito, k'arisawa yayi ya tsugunna ya yaye hijab d'in ta da ya rufe mata fuska da sauri ya mik'e,Yana mai ja baya tare da dafa kanshi da yaji ya wani Sara mishi, a Ina ya San wannan fuskan shi kuwa yayi yayi ya tuna ya kasa haka ya kinkimeta yasa ta a Motar shi ya dawo ya d'aukar Mata jakan ta yasa mata, yaja Motar shi suka fara tafiya.
Zaune take da wasu matsiyatan Kaya da su gara babu ta d'ora kafa d'aya kan d'aya in da zuk'a zuk'an Yan mata ke ta kaiwa da dawowa a falon suna shirya ma Masoyin Hajiya Abinci, wata budurwa ce da bazata wuce shekara Sha bakwai ba ta iso ta duk'a tare da mik'a ma ta wayar tana mai cewa "aunty ana Kiran ki a waya. Tana gama fad'i ta tashi ta tafi, dai dai lokacin da wayar ta k'ara ruri Alamun wani Kiran Yana shigowa, d'auka tayi ta Kara a kunnen ta "hello Suwaiba ya ake ciki komai yayi normal,? Ina Masoyi Kuma.?
"Eh baby komai Normal mun kusa isowa ma gidan yanzu haka, Masoyi Kuma gashinan Yana tuk'i.
"Ok sai kun iso, ku kula da kyau fa Koda nasan Masoyi ai baida matsala.
*************************
JOS
Hajiya na shiga ta rungume Dija tana Fad'in "Alhmdulillahi Allah Kai ne abun godiya.sannu Dija kinji, Mallam yau zaka Sallame mu koh.?
"Eh insha Allah Zan had'a muku wasu Magungunan da na shafawa da su hayaki da sabulun wanka duka, da Wanda zata dunga Sha da naci da Abinci.
Bayan Mallam ya Gama ma Hajiya bayanin Magungunan da ya basu sannan ya k'ara da cewa "karta dunga Zama ba Alwala sannan ta yawaita karatun kur'ani ko sauraro. Godiya tayi Mai Sosai suka kama hanya don komawa gida Hajiya sai jera ma Dija sannu takeyi, ita ko Dija sai binta da kallo takeyi tana mamakin wacece wannan matar.?
*************************
Hajiya ne ta fito hannun ta d'auke da tasbaha tana tasbihi, don ita ta kasance Mai yawan ibadu.
Sannan yawan yin Tasbihi na k'ara kusan ta bawa Zuwa ga Ubangijin sa, ma'ana Subhanallahi wabi hamdihi subhanallahil Azeeem.
Wata Yar dattijiwa ne ta shigo falon tana mai gai da Hajiya tare fad'in "Allah ya bayyana mana Dija hajiyan mu, fara mai farar zuciya. Sosai Hajiya Jiddah taji dadin Addu'a Mama Hansai, har tana Murmushi jerin fararen hak'oran ta sun bayyana cikin sassanyar Muryan ta mai d'adin tace "Ameen ya Allah Hansai nagode Sosai, har kin shigo,? Ya iyalan naki.?
"Lafiya lau Hajiya Suma suna miko gaisuwa da fatan bayyanar tauraruwan mu, don Ina ji a jikina ta kusa Bayyana insha Allah.
"In Allah ya yarda kuwa Hansai don nima Ina ta mafarkin ta, Allah dai ya kawo mun ita cikin Aminci.
Haka dai suka wanzu suna ta maganar bayyanar ta, don in har kana son kaga hiran Hajiya da farin cikin ta ka kawo Mata hiran y'ar ta masoyiyar ta, to zaku jima kuwa Kuna hira.
*************************
MAIDUGURI
Sosai Bintu tayi b'arna a gidan daga dare Zuwa safe. Kowa ka kalla a gidan Yana cikin tashin hankali duk da rashin Mutuncin da Bintu take ma Ma'aikatan nata bai hana sun tausaya mata halin da take ciki ba. Don duk mai Imani ya gan ta sai yayi kuka, ga ciki haka dai suke zaune suna kallon ikon Allah,
Alhaji Bukar bai iso Maiduguri ba sai Sha d'aya na rana,tun a hanya yayi ma likitan shi waya ya sameshi a gida Yana Isa gida baiyi ta kan kowa ba ya ciccibo Zahra ya kaita bangaren shi ya kwantar da ita, kwata kwata ya kasa fita ya barta ji yake yana mata wani irin son da zai iya rasa komai nashi a kan ta. Soyayya irin ta y'a da Mahaifi, doctor ne ya shigo da sallama. "Yauwa Doctor ka dubamun ita mai ke damun ta,? Ya fad'i haka cikin damuwa.
"Karka damu Alhaji insha Allah zata samu lafiya. Dubata ya farayi bayan ya kammala ya kalli Alhaji yace "Alhaji muje falo ko. komawa falo sukayi suka zauna, "Alhaji ba wani matsala ke damun ta ba illah maganin barci da aka bata yayi mata yawa Saboda yafi karfin jinin ta, zata Kai tsawon kwana biyu tana barci kafin ta farka, Amma akwai Alluran da Zan mata yanzu zai karya maganin zata farka nan da Awa goma insha Allah.
"Ba damuwa Doctor ayi mata indai kasan ba Abun da zai same ta.
"Ba abunda zai faru insha Allah.βοΈβοΈβοΈβοΈβοΈ
Jumma'at Kareem ππ to you Masoyana
Zeey Yar mutan Zazzau ce ππππ₯°π₯°
*'BOYAYYAR 'KULLI*πππ
STORY
AND WRITING
BY
ZEE 'YAR MUTAN ZAZZAU
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*π¦{Arewa ginshiΖin al'ummah}π¦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
PAGE 24
Yana zaune cikin d'aki ya tasa Zahra a gaba ya kasa fita ko nan da falo ne, Sallah ma a d'aki yayi Yana mai Addu'a Allah ya farfad'o mishi da ita.
Ji kawai yayi an hankad'o kofa ba ko Sallama, da sauri ya mik'e daga kan darduman Sallah Yana mai kallon Yagana da ta koma tamkar Mahaukaciya ga wani irin rama da tayi.
"Hajiya ai da kin bari nazo basai kin..... ta katse Mai maganar da yake Shirin yi ta hanyar fad'in.
"Kaga dakata Alhaji..! Wato Ciwon y'ata bai dameka ba ance mun tun Sha d'aya ka shigo gidan nan d'auke da budurwan yarinya, dama cin Amana y'ata kakeyi,? Shine bari kazo har gida ma kowa ya gani. Yau ko sai na illata karuwar yarinyar da kazo da ita Mai budurwan zuciya kawai. Tana gama Fad'in haka ta juya aguje kaman Mahaukaciya, shiko Alhaji Bukar rasa ma Mai zaiyi yayi Saboda shi mutum ne mare son tashin hankali gashi Bai iya fad'a ba. Bai gama tunanin da yakeyi ba ya hangi Yagana da tab'arya zata kwala ma Zahra, Ai Bai San lokacin da wata zuciya ta zo mishi ba ya finciko Yagana ya tsinka Mata mari, dai dai lokacin da Zahra ta Farfad'o tana Fad'in, "Daddy don Allah karka k'ara tafiya ka barmu."
Gaba d'ayan su juyowa suka suna kallon ta don ta tashi ta Zauna.
A matuk'ar firgita Yagana ta yarda tabaryan tana Nuna Zahra da hannu "Fadimatu mai ya dawo dake gidan nan.? Alhaji wallahi bamu San komai ba akan Abun nan, Fadimatu kiyi magana da fatan dai baki fad'a ma Alhaji komai ba. Ai da gudu Yagana ta fita d'akin sai gurin Boka.
*************************
JOS
Sosai Hajiya ke ji da Dija, tana bata kulawa Sosai har yanzu Dija ta fara sakin jiki da Hajiya don yanzu har magana takeyi mata Amma ba sosai ba.
Sai dai wataran tayi ta ma Hajiya kuka tana Kiran Baby