Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 11
Zamani Ina za'a samu kamar ki masu Taimako,tun da Baiwar Allah Nan tazo gurin Nan kike d'awainiya da ita.Allah ya biyaki ita Kuma ya Bayyana Yan uwan ta. "Ameen dai ya Allah πŸ™.Kai ta rumfa tayi ta shiga gida ta dauko Mata Abinci da Paracetamol da kaya,da k'yar ta Bari a ka canja Mata kayan ta bata Abincin ta fara ci.tsayawa tayi Tana kallon ta cike da Tausayi da k'auna ita dai tun da taga yarinyar Nan Allah ya d'ora Mata Tausayi da K'aunar Yarinyar a cikin Zuciyar ta Kuma Tana ji a jikin ta akwai wani B'OYAYYIYAR K'ULLI a tare da ita Kuma zata cigaba da Addu'a Allah ya Bayyana Mata wannan K'ullin. ************************* LAGOS "Kai Ashawo kana shanawa fa,Ina uwar sharrin naka.?Ina son zata mun wani aiki ne. "Kai dallah Shamo kyale Yar durun uba Wai ni zata kawo ma Bariki bacin ni na yaye ta a Barikin Nan.karamar Yar Tasha kawai yanzu na gama jibgan shegiya,Kama ta nayi da wani Shegen Inyamuri fa a d'akina tirmi da tabarya.shine kawai na K'addamar musu shine ta gudu. "Amma dai wallahi ta ban Mamaki Dan Maicin Uwan ta ai gara da ka jibgi shegiya.zama ta dawo tunda ai bata da kowa sai Kai. "Ba dolen ta ma ta dawo ba.jiran shegiya nakeyi yau in kwana huce Haushi na a kan ta. "Shege Ashawo kaji dadin ka,ka Shana kawai Aljannan na mai rabo ne, mudai mun San ko uwar mu take rabawa ba dole ta bamu ba. Tafawa sukayi suna dariya,ya wuce Abinshi.shi Kuma yaci gaba da hura sigarin shi. ************************* ZAZZAU BIRNIN SHEHU Dawowan su Makaran ta kenan aka tsuge da ruwan Sama. "Zahra!!Zahra!! Mami ne take kwala ma Zahra Kira da taji shigowar su yanzu. "Na'am Mami ganinan Zuwa Ina cire Uniform ne.da sauri ta k'arisa cire Uniform d'in ta Nufi d'akin Mami,tura kofan tayi had'i da Sallama."Mami sannu da gida mun dawo. "Yauwa sannun ku da dawowa,ga cefane can a Kitchen kije ki d'ora girki.kafin Nan ki samama Khausar Abunda zataci kin San dai bata jure Yunwa.tashi ki tafi Kuma kiyi ki gama karki tsaya wannan shiriritar naki har Yayan ku ya dawo baki gama ba. "To Mami,ta fad'i haka Tana Mik'ewa don Zuwa Kitchen din.haka ta tarar da kitchen din kaca-kaca ga kayan wanke-wanke tun na safe.haka ta fara gyara kitchen din sannan ta d'ora girkin ta Kama wanke-wanke kwanoni kafin Ruwan ya tausa.tana kammalawa ta je d'aki don yin Alwala tayi Sallah la'asar kafin ya dafu, dama ta riga ta kaima Khausar Comflesk.tana Zuwa ta ganta sai Barcin ta takeyi cikin kwanciyar Hankali don ko Uniform d'in bata cire ba.girgiza Kai tayi ta shige toilet ta d'auro Alwala ta fara Sallah.✍️✍️✍️✍️ Share Comments Like More Comment more typing. Zeey Yar mutan Zazzau ce😍😍😍😍 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ B'OYAYYIYAR K'ULLI 😭😭😭 STORY AND WRITTEN BY ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU. MARUBUCIYAR GIDAN GADO WAZAN AURA 1&2 AND KNOW B'OYAYYIYAR K'ULLI. DEDICATED TO TO B'OYAYYIYAR K'ULLI FANS INA YINKU IYA WUYA YANZU NA FARA JIN KWARIN GWIWAN TYPING KUN SAN COMMENT NA ZABURAR DA WRITERS. LOVE YOU LODI LODI πŸ’–πŸ’–πŸ’–. BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM. HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKEEL. (School choice ) PAGE 9 ************************* ZAZZAU BIRNIN SHEHU Khausar ne ta tashi Tana yamutsa fuska sakamakon wani Mummunan Mafarki da tayi. "Twinny Lafiyan ki kuwa.? Ki tashi kije ga ruwan wanka can na had'a Miki kiyi ki Alwala kizo kiyi Sallah ga Abincin ki Nan a dining. Tashi tayi ba tare da tace Mata k'ala ba ta shige toilet. Ita Kuma ta tashi ta fita don yi musu wankin Uniform kasancewar lokaci Damina ne shiyasa take so ta wanke da wuri Saboda ta samu su Sha iska kafin su tafi islamiya. Sai ta kwaso komai dare in sun dawo ita zata goge musu. a haka ma in Khausar najin wulakanci tace Wai Basu fita ba kayan ko Basu gogu ba. Wanki ta keyi Tana muraji'an karatun Zadul muslimat don yau shi zasuyi, Kuma ustaz Hassan duka yakeyi duk wacce bata iya ba.kuma kusan kullum sai anyi daru da Khausar akan bata iya ba,Kuma ko tace tazo tayi Mata tilawa bazata zo ba sai dai ta d'auko wayar Mami tayi ta game. ************************* Kwanci tashi ba wuya a gurin Ubangiji gashi yau su Khausar sun kammala Exam.sai farin ciki sukeyi sai dai ance baza'ayi taron Senth forth ba Saboda halin da kasa ke ciki game da rashin tsaro da kwanciyar Hankali. "Mami yaushe Daddy zai dawo da Yaya Sadeeq .? "Daddy ku ya tafi Abuja wani shari'a kuyi mishi Addu'a Allah ya basu sa'a. "Insha Allah Mami ai mun San Daddy mu mai gaskya ne da Amana Kuma Allah Yana bayan mai gaskiya.ko Khausar.? "Hakane Zahra.ni Mami fa na gaji da zaman gida ne, yauwa Mami Wai mai akayi ma Yaya ranar da zai tafi naga ran shi a b'ace.? "Nima ban sani ba Khausar.shi da Daddy ku ne.ku tashi kuje kuyi Sallah Time d'in Sallah yayi. ************************* LAGOS Gudu takeyi na fitan hayyaci Amma Basu fasa binta ba kanta ba ko d'ankwali kafar ta ba ko takalmi ta cikin kasuwa suka ratso.Abun da zai baka Mamaki ba Wanda yayi yunkurin taimakon ta sai dai ma ratsewa da akeyi ake bata hanya.ta gaji iya gajiya Amma bai sa ta fasa gudun ba,Kai daga gani kasan gudun ceton rai takeyi.dai dai zata fita daga cikin kasuwan ne cikin Wanda suke binta ya samata kafa ta fad'i Tim a kasa,Amma duk da haka kokarin yunkurawa take ta gudu.Amma Ina ta makara kafin ta tashi sun k'ariso sun zagaye ta kowa Yana hura hanci da ka kallesu kaga irin Manyan Inyamuran Nan marasa Imani. "Oga this girl na tired us Abeg let us kill stupid girl woo. "No oya bring her to my House I wanna sleep with her. You Anybody like come do. Sakin ihu tayi Tana musu magiya don Allah su rufa Mata Asiri, wlh bata yaudare shi ba guduwa mai da kud'i zatayi ba.Amma ko sauraran ta Basu Yi ba haka suka sab'a ta a kafad'a.tana ihu gwanin ban Tausayi.suna isa wani katon gida Wanda ko ta Ina a gidan Security ne gasu Nan birjik daga ganin idanun su ba alaman Imani a idanun su.wani d'aki a ka bud'e aka jefata a ciki,tun karfe Sha biyun Rana suke kanta gaba d'aya Security gidan in wannan yayi ya sauka sai wannan yayi,wasu ma a cikin su ta baya suke Amfani da ita tun Tana kuka har ta kasa gaba d'aya idon ta ya bushe haka makogwaran ta don komai Basu bata ta ci ba. a gaban suka ci Abinci suka dawo suka cigaba da sukuwa a kanta tamkar jaka ranar batayi tunani zata farka ta ganta da rai ba,don Suman ta bakwai suna yayyafa Mata ruwa in ta farko su cigaba.gaba d'aya jikin ta yayi weak Nan da Nan ta fara Nadaman shigowa Bariki ta fara tunanin yanzu in sun kashe ta sun kashe banza.bata da wani gata a matsayin ta na karuwa, ta tuna irin Abubuwan da ta aikata a baya tabbas bata tab'a nadama irin ta yau ba,In Allah yasa Tana da sauran Shan ruwa a duniya zataje ta warware B'OYAYYIYAR KULLI da ta had'a sannan ta nemi yafiyan iyayen ta in suna raye.tana wannan tunanin ne taji wani abu ta duburan ta tamkar karfe shine har cikin cikin ta,bata gama jin wannan Azaban ba ta karajin wani ya shigeta ta gabanta ji tayi sun kwashe da dariya.tun daga Nan bata Kara sanin inda kanta yake ba. "Hello Shamo kana jina wallahi har yanzu Uwar Sharri bata dawo ba yau kwana uku kenan,wallahi Abun yayi Matukar d'agamun Hankali kar yazo taje ta fad'a a hannun gang din Yan Yahoo ko Yan cult kasan Zaman Legos sai da ta ka tsantsan. Ok don Allah kayi sauri sai muje mu nemo ta. ************************* JOS "Hajiya akwai Sakwara.? "Eh akwai Alhaji shiga Bari a kawo ma,komawa tayi tama wata yarinya magana taje ta kaima Alhaji Sakwara a falo.ta Amsa Mata,ta tafi domin Kai Mata can na hango Dije Tana zaune tayi shiru tana kallon kan titi.k'arisawa Hajiya tayi hannun ta d'auke da plate din Abinci."yauwa Dije ga Abincin ki ci sai kizo in Miki wanka.karbe Abincin tayi.tana mai k'ale Mata kafada Alamun bata son wankan. "Aiko sai kinyi wanka yau satin ki guda fa kenan bakiyi wanka ba. Turo baki tayi Tana hararan HajiyarπŸ™„. "Duk ki gama yau sai kinyi wanka.ta fad'i haka Tana Mik'ewa taje ta cigaba da aikin ta. ************************* Daddy ne ya shigo cikin gidan had'i da Sallama. Da gudu Yan gidan duka suka fito suna murnan ganin Daddy. "Alhaji shine baka sanar damu kana kan hanya ba. Ina so in baku suprise ne.kuma gashi yanzu na baku ya fad'i haka Yana murmushi.zaunawa yayi yace My Beautiful babbies kuzo Nan in muku wani albishir. Da sauri suka k'arisa kusa da Daddy suka sashi a tsakiya."oya duk ku rufe idon ku.bayan su rufe ni ya ciro musu wayan su sabbi a kwali kirar Infinix Smart 5 Aiko suka rungumeshi suna murna πŸ’ƒπŸ’ƒ. "Dama Daddy Ina taso ince ka siya Mana Saboda duk freands din mu suna da phone Ashe ma Yana ran ka.inji Khausar. "To yanzu dai gashi Nan na siyo muku gift d'ina kenan na graduation.sannan Kuma gashi na samo muku Admission ke Khausar za kiyi Al-kalam University Katsina,Ke Kuma Baby Zahra zakiyi Sky land University Kano murna Zahra ta fara ta kwararo ma Daddy Addu'a,sai ta ga Khausar ta bata rai ita da Mami,daddy shima ya lura da hakan sai yace musu "Hajiya lafiya ko bakiyi farin ciki bane.? "No Daddy yara gani nayi gara a Kai Zahra Katsina tunda tadan fi Khausar wayo zata iya kula da kanta,Ita Kuma Khausar a dawo da ita Kano Saboda yafi kusa Kuma kaga Khausar Ba lafiya ta cika ba. "To shikenan tunda Kinga hakan yafi.ke Zahra sai kiyi hakuri kije Katsina ita Kuma Khausar din taje Kanon. "To Daddy indai hakan shine farin cikin Mami da Yar uwa ta na hakura Allah yasa hakan shine mafi alheri.da Ameeeen duka suka Amsa.kowa ya tashi yayin da Zahra kwata-kwata bataji dadin haka ba.✍️✍️✍️✍️✍️✍️ Share Comments Like More Comment more typing eheeπŸ™„πŸ™„ Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍😍 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ B'OYAYYIYAR K'ULLI 😭😭😭 STORY AND WRITTEN BY ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU. MARUBUCIYAR GIDAN GADO WAZAN AURA 1&2 AND KNOW B'OYAYYIYAR K'ULLI. DEDICATED TO Duk wani Masoyana da Wanda na sani da Wanda ban sani ba Ina son ku nimaπŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM. HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKEEL. (School preparing) PAGE 10 ************************* ZARIA D'aki suka shige kowa taje ta jona wayar ta a chaji,a jikin bed d'in ta kasancewar kowacce kusa bed d'in ta akwai sucket. Fita Zahra tayi don Zuwa Kitchen had'a musu Abincin dare,kasancewar Daddy na gida Kuma kar yayi Fad'a shine Khausar ma ta bita kitchen din suna aikin tare.duk da rabi da kwatan aikin Zahra keyi.bayan sun kammala ne suka jera a dining.Suka koma d'akin su don yin Sallah Magrib. Kowa ya iso gurin cin Abinci,sun zauna suna cin Abinci.Bayan sun kammala ne suka koma falo suka Zauna a ka fara hira. "Daddy yaushe zaka siyan Mana Mota.? "Oh Khausar yaushe kuka isa hawa Mota ku Bari sai kun Kai 300L sai in siya muku,kin ga a lokacin Kuna da 22years kenan. "Amma dai Daddin yara ya kamata ka siya musu ko guda d'aya ce su dunga sharing, Saboda a gidan Nan fa Motoci biyu ne fa daga naka sai na Sadeeq.kuma gaskya Mota biyu a gidan Nan sun Mana kad'an. "Bari mu gani to bayan na gama musu registration.in har naga Ina da hali sai in siya musu. "Yauwa Daddy Allah ya Kara bud'i. "Ameeeen yaran Daddy nidai Abunda nake so daku please ku daure kuyi karatu Sosai kunji yara na.Zahra na Law zata karanta ke Kuma pathologist ko.? Kice gaba kad'an zaki canza ma Mamin ku fataπŸ˜€. daddy ya karishe maganar Yana murmushi.Yanzu dai ku shirya gobe in Allah ya kaimu zan kaiku kuyi shopping d'in makaranta, da duk Abunda kuke bukata,kunga sai inji da registration din. "To Daddy mun gode Allah ya ja kwana, ya Kara bud'i ya saka da Alheri. "Ameeeen Yan Albarka.ku tashi kuje ku kwanta dare yayi. "Mami gud night sweet dreams, daddy gud night sweet dreams too. "Ok my children kar ku manta da Addu'a. Washe gari........ Kowacce ta had'a wayar ta,sun d'ora layin da Daddy ya siya musu har Kati ya sa musu da Numbers d'in Yan gidan, Number Shi da na Mami da na Hajiya Guggo.bayan sun had'a ne Zahra ta Kira Number Yayan nasu don tabbass tayi Missing d'in shi Sosai, ringing D'aya ya dauka kaman Yana jira. "Hello dawa nake magana.? Jin muryan shi da tayi sai taji wani farin ciki da sanyi a ran ta sai taji duk wani damuwar da take ciki ya tafi Saboda jin muryan Yayan ta mai son ta mai share Mata hawaye daga shi sai Daddy take jin dadin su sai ko Guggo in tazo. "Hello Wai dawa nake magana an kirani anyi shiru. "My sweet heart Yaya."ta fad'a muryan ta a sanyaye. "What kind of surprised my baby.? Ya kike da fatan kina lafiya wannan phone din waye.? "Kai Yaya duka wannan tanbayar ni kad'ai zan Amsa." "Sosai ma kuwa, Da fatan kina cikin koshin lafiya,ba Abun da ke damunki.? Da fatan Mami basa takura Miki.? "A'a Yaya na, Wai yanzu kana inane.? Daddy ya siya Mana waya nida twince sister na,shine na Kira in fad'a maka. "Baby please karki sake kiyi wani Chat in ba WhatsApp,Saboda ban son ki koyi shirme da hauka, karki bama kowa Number ki.kinji ko my Baby. I miss you too baby ki kulamun da kanki kinji karki fad'a ma su Daddy munyi waya,har da twince sister naki. "To Yaya insha Allah bazan fad'a musu ba.I love you too my Yaya.tana fad'in haka ta kashe wayar Tana mai rufe ido,murmushi d'auke a fuskar ta. ************************* MAIDUGURi "Haba Yagana kin San tsawon lokacin Dana d'auka Ina fatan Samun ciki a gidan Nan sannan kice mun Wai in Zubar,to Bari kiji ni har na tura ma Alhaji Text ma Ina d'auke da juna biyu,tun a wayar ya bani kyautar Motar shi da duk Nigeria shine na biyu a hawa irin ta.ina ga na haifi yaron ko Yarinyar.kai wallahi bazan iya zubarwa ba, to Yagana maganar Boka maganar Allah ce,ni Kinga ma kashe wayata zanyi in har bazaki mun maganar arziki ba.kit ta kashe wayar ta tayi cilli dashi kan kujerar dake falon. Safa da marwa ta farayi Tana zagaye Falon.wata Dattijuwan Mata ne ta shigo d'auke da wani Dan karamin faranti d'auke da karamin Cup cike da Madara mai sanyi, tazo ta duk'a a gaban ta had'i da sunkuyar da Kai. "Ranki ya dad'e lokacin Shan Madarar ki tayi.bata Gama rufe baki ba ta d'auke ta da Mari had'i da fad'in, "Dallah Fice mun a Nan waya fad'i Miki Ina bukatar kowa kusa da ni a yanzu.madarar ta d'auka ta juye Mata a fuska had'i da jefar da kofin ya fashe,ta juya a fusace ta shige bedroom."kar in fito Kuma inga datti a gurin nan.ta fad'i haka tana mai bugo kofa. Girgiza Kai tsohuwar tayi Wanda a haife ta haife ta Amma tayi Mata wannan tijarar.haka ta tashi jiki sanyaye ta fita don kwaso Abun da zata gyara gurin kafin ta dawo tayi Mata wani cin Mutuncin. ************************ LAGOS Lungu da sako duk inda suka San zasu ganta sun duba Basu ganta ba. Hankalin Shamo gaba d'aya ya tashi. Bayan sunyi Mata fata fata ne.washe gari da Safe suka fita suka jefar da ita a saman gada,ko suturar arziki babu a jikin ta.Kowa yazo sai dai ya wuce abinshi don irin haka ba sabon Abu bane a Lagos,in har ka kalle ta baza kaso ka k'ara kallon ta ba.don tamkar Matacciya. Shamo ne suka zo wucewa har sun gota suka dawo baya. "Kai Mutumina kamar Uwar sharri fa nake gani kwance. "Kai Ina ba ita bane, mai zai kawo ta Nan. "Kai kwarankwatsa itace saboda wannan kayan tasa randa muka rabu da ita. Haka suka k'arisa kasancewar gari ya fara duhu a lokacin sai suka kunna toch light din wayar su. "Innalillahi Aradun Allah itace ,haka suka ciccibeta sukayi shatan taxi sai gida✍️✍️✍️✍️✍️ Share Comments Like More Comment more typing ehee πŸ™„πŸ™„ Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ B'OYAYYIYAR K'ULLI😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU. BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. YA HAYYU YA K'AYYIM PAGE 12 Kwanci tashi bai da wuya a gurin Ubangiji yau gashi watan su Zahra uku a school. Inda Mami har ta gaji da kewan Yan matan nata ta hakura. Gashi yanzu Daddy sai k'arshen sati yake dawowa yayi kwana biyu ya koma,Saboda wani shari'a da suke ta fafatawa. Sadeeq ko tunda ya tafi Abuja Neman aiki ya samu aiki a gidan shugaban k'asa Wanda a ka bashi matsayin mai yad'a labarai na gidan gwamnati gaba d'aya. Sannan Yana fushi da su Daddy a kan maganar Zahra, don shi Yana tunanin sun b'oye mai wani abu ne, hakan yasa yak'i dawowa gidan, a kan cewa har sai sun sakko sun Bayyana Boyayyiyar K'ulli da suke B'oyewa zai dawo. Wata rana ne da ya zame ma su Mami ranar Bak'in ciki Wanda baza su tab'a mance ranar ba. Ranar da suka rasa Hajiya Guggo sakamakon gajeruwan jinya da tayi. Cikin dare jikin nata yayi tsanani Sosai ga Daddy ga Mami suna zaune a gefen ta a Asibiti A.B.U Shika, da k'yar ta daga Kai ta dubi Daddy tace mai...."Habibullahi Ina ji a jiki na bazan tashi ba, naso a ce kafin in Mutu naga Abubakar Sadeeq domin in Mallaka mishi Abun da ya ke so, duk da cewan ban so hakan ta faru ba Amma Ina ji a jikina sai K'ullin da muke b'oye musu ya Bayyana duk daren dad'ewa. Saboda haka ko bayan Raina ku Aura ma Sadeeq Zahra. "Don Allah Hajiya ki dai na fad'in haka Zaki tashi insha Allah, in har kika mutu wa nake dashi kuma.? Na rasa Dan uwa na mafi soyuwa a rai na a lokacin da nake buk'atar shi, kema kina Neman ki tafi ki barni. "Kayi hakuri Habibullahi mutuwa dole ce, nasan ko yanzu Ubangiji ya d'auki rai na nasan b'uri na ya cika, na baka tarbiya Kai da D'an uwan ka na baku ingantaccen ilimi ka mallaki komai a yanzu.k'asa k'arisa maganar tayi Saboda tarin da ya sark'e Mata wuya.Kalman shahada ta farayi, bata d'au dogon lokaci ba rai yayi halinsa murmushi kwance a fuskar ta. Fad"in tashin hankalin da Daddy ya shiga ma b'ata lokaci ne. Washe gari su Zahra suka iso ita da Khausar. Sun ci kuka kaman ba gobe karma Zahra taji gashi sun nemi Number Sadeeq Basu samu ba kwata-kwata. Haka gida ya cika yawanci Yan uwa da Abokan Arzik'i ne Saboda kowa ya San Hajiya Guggo Mace ne mai Tausayi da mutunci. ************************* JOS Tun safe yau Ciwon Dija yayi tsanani, don k'okarin guduwa ta dunga yi, Sai fisge-fisge takeyi. Maza ne da yawa suka rirrik'eta. Ba Abun da Hajiya Hauwa takeyi in Banda kuka 😭 Saboda Tana matuk'ar tausayawa Dijah Halin da take ciki. ************************* MAIDUGURI Tafiya sukeyi a cikin wani taxi, Ashawo ne rungume da Uwar sharri da ta Zama daga kallo sai kallo ko Zama batayi, dai dai wani maraba a ka kawo su, mai taxi d'in ya sauke su, Wani mutumi ya tayashi suka kamo ta suna Mata sannu suka shimfid'e ta, kafin su samu A kori-kuran da zai Kai su cikin k'auyen Ashawo sai tsaki yakeyi. Sai Can Yamma suka samu Motan da zai k'arisa dasu Cikin K'auyen. ************************* ZARIA Anyi bakwai kowa ya watse Su Zahra ma sun koma Makaranta. Inda har lokacin ba'a samu Number Sadeeq ba. Bayan Wata d'aya Daddy ne Zaune a D'akin shi Yana Had'a wasu takardu a cikin wani akwati, Wasu hotuna ya D'auko da wasu Fararen Abu mulmulallu farare tas dasu sai d'aukar ido sukeyi a k'ulle a wani leda da yawa shima ya saka a Akwatin. Bayan duk ya birkice D'akin nashi ya had'a komai,. Wani k'aramin akwati ya k'ara D'auko wa ya zuba wasu takardu a ciki, ya maida ya k'ulle su duka ya ajiye a gefe. Wayarshi ya jawo ya cire Security Transfer kud'i yayi ma Sadeeq a Account d'in shi na miliyan Ashirin. Sannan yayi ma su Zahra na Miliyan goma-goma. Sannan ya kashe wayar shi ya kwanta.✍️✍️✍️ Share Comments Like Zeey Yar mutan Zazzau ce 😍😍😍 BOYAYYIYAR K'ULLI😭😭😭 STORY AND WRITING BY ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w _*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_ BISSMILLAHI RAHMANIR RAHEEM. ALLAHUMMA INNI AUZUBIKA MINAN NARR. PAGE 11 ************************* LAGOS "dole in d'auki Uwar sharri gobe in koma da ita k'auyen su,don ni bazan taba iya jinyar ta ba Ina naga kud'in da zanyi jinyar ta, duba fa ka gani ta bayan ta har hanji ne ke lekowa.Kalli gaban ta kamar kofar d'aki Ina Kuma take da sauran wani Anfani yanzu,kawai zan maida ta garin su a hakan ma ai nayi k'okari ko ya ka gani Shamo.? "Gaskya kam Ashawo tunda dama Bariki ai da mai Anfani akeyi, daga lokacin da mutum ya zama haka ai bai da sauran Amfani.Kawai ka maida ta ai ka Mata ma halarci. ************************* ZARIA Dawowan su kenan daga shopping su da Daddy. Mai gadi ne ya dunga shigo da kayayyakin da suka siyo. Mami ne ta fito daga D'aki "Daddy Yara kun dawo sannun ku da dawowa. "Yauwa Mamin Yara dama gobe insha Allah nake so Mukai Zahra makaranta,tun da na riga na kammala Mata komai. "To ita Kuma Khausar fa sai yaushe zata tafi,? Ko ita ba'a kammala Mata registration d'in bane.? Ta fad'i haka Tana yamutsa fuska. "Haba Mamin Yara Wai ya kike haka ne naga da Zahra da Khausar duk d'aya suke,Kuma ke kika haife su,ni bana son Abunda kikeyi din Nan. Naga Zahra garin da za'a kaita makarantar Nan yafi na Khausar nisa yakamata dukan mu harda Khausar din mu Rakata muga gurin da zata zauna, sai mu dawo Mukai Khausar Koh. Amma bana bukatan irin haka zai jawo mun rabuwan kan yarana Kuma kin San duk duniya bacin Mahaifiya ta Ba Wanda nake so Sama dasu. "Kayi hakuri Alhaji insha Allah na Bari bazan sake ba, gobe da wuri Zamu fita.? "Yauwa Uwar gida ta insha Allah karfe takwas zamu fita ki fad'a musu su shirya da wuri.kin san yaran naki akwai shiriri ta.ya karishe maganar Yana shigewa d'aki. Tsaki Mami tayi had'i da yamutsa fuska. "Aikin ka kenan kullum kar a raba maka kan Yara, sai kace a kanshi a ka fara yara.ni wallahi hakurina ya kusa Zuwa k'arshe a kan tijaran da kake mun a kan Yara.dole in d'auki mataki a kanka kuwa.ta karishe fad'in haka Tana wucewa d'aki itama. ************************* MAIDUGURI Tafiya sukayi Sosai a kafa, tunda sun bar motan su a bakin hanya. "Wallahi Yagana kafafuwa na sun gaji fa." "Wai Bintu yau muka fara Zuwa gurin nan, duk kin dameni haba don Allah duk Abun Nan da nakeyi a kanki ne fa, ba don Boka ba kin San ko Kallo baki ishe Bukar ba. A haka dai har suka isa gurin bukkan bokan da shi kad'ai ne a dokan Daji. "An gaida Boka Duna mugun Boka, ka kashe ka haukatar kasa anbi duniya,ka raba d'a da mahaifi,ka raba y'a da uwa. "Angai da fara mai bak'in Zuciya, ai nayi tunanin bazaki zo ba. "Ai dole ne in Amsa Kiran Duna. Boka gata na kawo maka ita kayi Mata

Chapter 3 of 11