kuma Hameed ya faɗo ɗakin tamkar wanda aka ingizo shi har wani huci yake. A hankali na ɗago kaina tare da masa sannu da zuwa. Be ko amsani ba ya fara da cewa... "Amma tsabar kutumar ubanci kina ji na buɗe maƙogwaro ina ta raraka miki ƙira kikai banza dani ko?" Ya kai ƙarshen maganar yana ta wani huci tamkar kububuwa.
"To yanzu daddy'n Amaan me kuma kake Son na maka?, Ka ƙirani ina Sallah, bayan na idar na amsa baka me kake so na maka kuma bayan wannan?" Na bashi amsar idaniyata na tara ruwan hawayen takaici da ɓacin ransa sosai. Tamkar wani ƙaramin yaro haka ya ca ke a kaina tare da furta... "Ohhhh haka ma kika ce kenan, to idan kin idar da Sallar ki je gidanku na sa...ke...ki A'isha!!!..........."
Wannan kalma ta saki ita ce ta girgiza duniyata dama duk wani tunani nawa. Wannan kalma ita ce kalmar data bugu kunnuwana tanayin gaba da duk wani abu me rai da motsi a cikin jikina na wucin gadi... Wannan kalmar kuma ita ce kalmar da ta sanya ni tariyo rayuwata ta baya. Ina tunanin shin ina wannan tarin Mahaukacin *SO da ƘAUNAR da HAMEED* ke min? Shi ke nan duk wani buri da fata na sun tafi a hofi kenan? Shi ke nan na rasa Hameed tamkar yadda na rasa choices ɗina na zama ɗaya daga cikin fitattun wannnan ƴar jaridar ta baya, wato *ROYAL BLUE* _(ROYAL KINDNESS)_ duka tarin waɗan nan abubuwan da na yi making a cikin rayuwata shikenan sun gudu, tamkar yadda ƙaddara ta ta zaɓa min hakan?. A take naji ƙafafuna na ɗaukar wani irin sanyi, kaina na wani irin saramin tamkar wacce aka bugama guduma. Wani kalan kaiwa ɗurƙushe nayi daga tsayen dana miƙe babu shiri saboda yadda na ji juwa da hajijiya na nemar zubar dani, Cikin wani irin ɗacin da naji yazo yamin tsai a ƙahon zuciyana na fashe da wani irin kuka na fitar rai. Kafin cikin muryan kukan na shiga furta... "Yan zu daddy'n Amaan ni ka saka?, Don ALLAH kace min da wasa kake naji na gani zanci gaba da zaman yarana In Sha ALLAHU zan ci gaba da jure komai daga gare ku, kamin ko wanne irin hukunci ne amma plssss don ALLAH ban da saki, kalmar ta yi min tsauri da yawa wllh....
Daga tsayen da yake a kaina yaja yana matsaya tare da furta. "Ehhh ki je gidanku na sake ki A'isha, tun da ni dai banga uwar abinda nake miki ba, kullum ni shikenan bana cikin farin ciki ta sanadiyar ki" saurin kallonshi nai da rinannun idaniyata jin wai baya farin ciki ata sanadiyya ta, "kaji tsoron ALLAH,kaji tsoron ranar mutuwa daddy'n Amaan, yau shekaru ɗaɗɗai har shekararmu goma sha biyar cif da cif da aure, ina bautata maka kai da danginka amma duk ni ce me laifin da ka ɗora ma alhakin hakan? " Nayi maganar ina me runtse idona wasu hawaye na gangaro min daga idanuna zuwa kan tafukan hannayena dana sanya ina tare su.....
Wannan shi ne silar warwarar komai da ƙaddara ta jima kullewa. Babu komai masu iya magana suka ce yau da gobe ai duk ɗaya ne, Kamar yanda nake Roƙan ALLAH ya haskaka min gobe na tafi jiyana kyau.....
Lallai a cikin irin tarin ƙaddarorin da suka taru suka min rubdugu suka min taron dangi wani kaɗai na ba, baku ji komai ba domin kuwa *A CIKIN LABARINA* wannan kaɗan né daga irin yadda ƙaddara tazo ta kwankwasa ƙofarta, gashi ta tafi ta barni bansan kuma da wanne salon zata dawo min a mataki na gaba ba,
Daga ranar da Hameed ya sake ni daga lokacin ne kuma na fahimci cewa akwai banbanci mai tarin yawa tsakanin jiya da yau da kuma gobe. Dan ba komai bane kake tsarawa a cikin Rayuwarka kuma ya tafi maka daidai ba, wannan ɗin kuskure ne da saɓanin lamba, dan kuwa ni tawa ƙaddarar data tashi bayan Rabani da buri da kuma fatana da tayi, bata barni haka ba seda ta ɗauke Ni tayi cilli dani cikin tarin tarkacen ta me cike da sarƙaƙiya da matuƙar wahala sosai. A yanzun haka da nake zaune akan gadona na asibiti da jaririyar ALLAH'r da na haifa a yau ɗin ba wanda yayi kwana ɗaya kenan da rabuwana da mahaifinta. Ban san ta yaya ne zan Mu'amulanci yau ɗina ba bare na yi amfani da jiyan dana rigada na bar ta, dan gyaran goben yarana ba, domin kuwa Rayuwa kala kala ce, kamar yadda ƙaddara itama take kala kala ce. Waɗansu zaka kallesu tun farkon Rayuwarsu dama ta jarrabawa da ƙaddara ce, wasu kuwa zaka kallesu ne a lokacin da suke tsaka da jin daɗin rayuwar anan kaɗɗarar su ke kutso musu kai wasu kuwa dama can fari tas dake zuwa musu tun daga farko har ƙarshensu, gashi nan dai kowa da nashi kalar, inda nidai tawa tazo min farko fari tasss me cike da zallar nishaɗi, tsaƙiyar kuma baki ƙirin, ƙarshen kuma se ilahu shi kaɗai yabar ma kansa sanin abinda ya tsara min a gobena data yarana. Inda nake roƙonsa sassauci da muma rangwame akan koma menene ya sameni da sauƙi......
*BACK TO DAWOWA LABARI*
Zamu ɗora daga inda muka tsaya, bayan inda ta haihu, kun san dama tana kwance me a gadon asibiti take bamu wannan labarin, na irin baƙar rayuwar data ɗanɗana a gidan Zaɓinta HAMEED USMAN DATTI, to yanzun ta dawo daga duniyar bamu labarin, kai tsaye zamu ɗora daga inda muke....
Wannan shi ne ƙarshen labarin gidan Aure Naaaaa...
Duk wanda ya shirya biyoni domin jin me gobena zata haifar min to kuwa lallai ƙofa a buɗe take, domin yanzun ne hasalin wasa ɗan gasken ze fara, ƘWARAI kuwa _NI AYSHA MUSTAPHA WAZEER_
*ROYAL BLUE* na ke cewa Lallai haka abin yake....
Wata kalan nannauyar ajiyar zuciya na sauƙe, bayan dawowa daga *DUNIYAR LABARINA* dana tafi baku... Tare da kallar jaririyar macen dai da ake min yaɓen maganganu akanta, take a wurin na ɗaga yarinya ta na mata ƙiran sallah tare da mata huɗu ba da suna.......
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
_Idan kun kimtsa tsafffff se ku biya kuɗin ku cikin sauƙi domin jin yadda tafiyar zata kaya._
_Fatar masu karatu basu manta da ASAAD JUNERD MAJEED ba (AJ MAJEED) ɗin mu?_
_Shin ze dawo cikin rayuwar AYSHA MUSTAPHA WAZEER ne? Ko kuma yaya?,Shin wata ƙaddarar ce zatay halinta ko kuma me kuke tunani da hasashe?...._
_Hummm tofa tirƙa-tirƙa kenan, Lallai fa wannan littafin cike yake da tarin ƙalubale masu tarin yawa, dan kuwa bamu ce komai ba a cikinsa. Da kaɗan kaɗan sannu a sannu zamuna tsakura muku komai, ta yanda labarin zai fi tafiyar muku a yanda kuke so🤗🤗🤗_
_Shin nace yaya batun Baby da kuma ummih yayarta, 🥺 karfa kuma manta amanar mijinta take son ci😩_
_Yaya Maman Hameed zatayi idan taji HAMEED ɗin ya rabu da Aysha'n mu? zata yi murnane ko kuwa me kuke ganin zatayi, kar fa ku manta gefe guda ga kulla kullar da ake ciki ta mutanen gidansu, idan kuma muka koma gefe hammmm ba'a cewa komi🤗_
_Kuna tunanin DANGIN MIJIN Aysha'n mu? Ko kuwa baku tunani?, ALLAH Sarki wai ina labarin Sumayya'n mune ta gargajiya 🤸🤸🤣? ,Kaiiii wllh a cikin WANNAN littafain akwai abubuwan ma da kanka baka isa kayi zatar su ba, domin......_
*Hajiya idan kin shirya saye kawai ki antaya min 1k ɗin Ni kuwa AMMEY LAYLERH in antaya ki Sabon Paid update group Nawa na DUNIYARMU 🌏 Me cike da tarin ƙalubale.._
3206656358
Maryam Nasiru
First bank
0810449321
🌏𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐🪐
𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚🤦
https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Official Mirrah💐
♡
Page 15&16
*End of Last free Page's 🤗*
✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫*
(J.W.A)
♡
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
★★
Ina masu son shiga adashe amma kuna fargaba yar uwa ki tsarkake zuciyanki kizo kiyi adashe cikin aminci da kwanciyar hankali babu rigima ko tashin hankali cikin lfy zakiyi adashin ki kuma mugama lfy
*Weekly 3k kwasa 30k slot 6 to 10 available*
*20k kwasa 20k slot 5 to 10*
*1k kwasa 10k slot 4 to 10 available*
*5k kwasa 50k slot 7 to 10 available*
*Monthly 50k kwasa 500k* slot 4 to 10 available*
*20k kwasa 200k slot 9&10 available*
*10k kwasa 100k slot 6 to 10 available*
*5k kwasa 50k slot 3 to 10 available*
★★★
TESTED AND TRUSTED @queen 𝙍𝘼𝘽𝙄'𝘼 𝙒𝘼𝙆𝙄𝙇𝙄 _skincare 🥰
Is very good with zero side effects👌
Available Glow up your skincare routine with Vaseline Intensive Care....
Shin Ina manyan matan suke ƴan kwalisa masu ji da gayu?🗣️ To maza ku hanzarta kumatso kusa dan kuwa haƙiƙa tabbas duk macen data amsa sunanta mace ya kamaci ace tazo Queen 𝙍𝘼𝘽𝙄'𝘼 𝙒𝘼𝙆𝙄𝙇𝙄, domin kuwa ta zo muku ne da ingantattun haɗadɗun kayan gyaranjiki masu matuƙar gyara fata cikin ƙanƙanin loƙaci ba tare da sunyima fata lahani ba, domin kayan Queen 𝙍𝘼𝘽𝙄'𝘼 𝙒𝘼𝙆𝙄𝙇𝙄 products ne bawai na bleaching ba, zasu gyara ma mutum fata ne ya fiddo mashi da ainihin natural beauty ɗin mutum, haƙiƙa duk wacce batayi anfani da kayan Queen 𝙍𝘼𝘽𝙄'𝘼 𝙒𝘼𝙆𝙄𝙇𝙄 ba to kuwa tabbas anbarta acan ƙarshen bayama kuwa. Yana maganin Pimples, black spot,sunburn, stretchmark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Waɗan nan su ne jerin sabulan da muke da...
*Super lightening soap*
*Organic lightening soap*
*Baby soap*
*Lightening dilka soap*
*Attractive soap*
*Morocco soap*
_A kwai wanda yake saka haske akwai wanda yake maintaining na skin ba tare da ya saka maki haske ba_
Call or chat us on whatsAp to place ur order +2347048742957 business only🥰🙏🏻
_🌙✨ Eid Mubarak! ✨🌙_
_Wishing all my dear friends and family a very, very Happy Eid ul-Adha!, May this special day bring peace, happiness, and countless blessings to your home and heart.
Let's celebrate with love, gratitude, and togetherness 🐑❤️✨...._
_Society often points out our imperfections but seldom celebrates our growth and effort, This Eid, may we find peace in knowing our worth and joy in how far we've come_
♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Na mata huɗu ba da suna Maryama (Mumeenat) a cikin Rai da Ruhina kuma ina me furta _𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈𝙐 𝘿𝘼𝙎𝙊 Mai tagwayen suna, MARYAMU daso me sunaye da yawa, MARYAMU Daso Baiwar ALLAH!_, Ɗan girgizanin da aunty Fa'izah ne tayi ya sani ɗago kaina idaniyata cike ne taff da ruwan hawayen dana gama cin uban kuka na, harna gode ALLAH. Ashe wai ta jima tana ta sallamar ban ma san tanayi ba, zama tai gefe dani tare da amsar jaririyar hannuna ta saɓa a kafaɗarta. Tare da dubana cikin wani irin yanayi na jin tausayi sosai, don se a yau ɗin take jin zancen sakin nawa da Hameed yayi. Hannunta ɗaya tasa tana sake sharemin ruwan hawayen da suka gangaro min tare da faɗin.
"Kiyi haƙuri A'isha komai na cikin wannan duniyar da kike kalla ɗan haƙuri ne. Kamar yanda damuwa bata ƙyale rayuwa, Ita kuma rayuwa dole seda damuwa faɗin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ce wannan, kamar yanda yace ita nasarata sannu sannu ke zuwa to IN SHA ALLAHU zakije inda ake zuwa. Idan har kinyi haƙuri se ki by 6yy kalla ya zama mikki garkuwa. Kana ina son ki zama mai farin ciki da kuma godiya ga ALLAH a ko da yaushe, kuma a cikin kowanne yanayi naki ki zama me sanyawa ziciyarki wadatar Zuci, idan kikayi duba da cewar. Ranar da wani ze yi aure ranar wani zai rasa matarsa, Ranar da wani zai sayi moto to a ranar ne ake sace ta wani. Se ki kalla ranar da aka ɗauki wani aiki a ranar ne za'a kori wani daga aikin! Don haka ne nake Son ki gane cewar lokaci ne yake bama kowa damar dariya da kuma kuka!, Dan haka kema loƙacin dariyanki na tafe IN SHA ALLAHU A'ISHA!!!"
Takai ƙarshen maganar nata daidai lokacin da yaya khaleel yake shigowa cikin THEATER ROOM ɗin,hannunsa
ɗauke da leda me sa lo sa lo. Zama yay gefe da gadon dake dab damu gaida sa Aunty fa'iza tayi amma ni sai aikin shan zuciya nake idaniyata cike taff da ruwan hawayen da suka gaza taruwa. "Wani abu ya faru da ita ne fa'iza" kai tsaye tambaya ta farko kenan da yaya khaleel ya fara jefo mata. Itan ma kanta ta sunkuyar tana jin nata idanun na cika da ruwan hawayen itama.
"Wallahi yaya khaleel nima ban san abinda ke faruwa ba se a yau ɗin nake jin Hameed ya rabu da ita neee! Ya sake ta....." Wani dummm yaji kansa yayi haba no wonder biri yayi kama da mutum, shi yasa yata ƙiran Hameed ɗin yaki pick na call náshi. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin cikin muryan da tayi sanyi sosai ya furta.
"IN SHA ALLAHU Gobe za tayi kyau fiye da yau ɗin ki Aysha, Kiyi haƙuri domin shi ne matakin kowanne nasara, da kuma mukullan buɗe ta kin ji Aysha, karki bari wannan damuwar yayi mentenal brain naki dawn, ALLAH zeji da lamarin zai kuma gyara gobenki da Ikon Rabbi, ALLAH kuma yasa hakan shi mafi Alkhairinki A'isha, domin dama ke ɗin bata mutumin daya kasance dabba bane." Haka yata bani baki tun hawayen na zubo min har suka dena zubowar, se ma sannu a hankalin dana fara jin jikina yana wani irin sanyi, Sannu a hankali kuma nake buɗe kunburarrun idanuwata, da suke yi min wani irin zugi saboda uban kukan da nake ci dasu, Nan shi da Aunty fa'iza Suka haɗe su biyu suka sake ganar dani, da kuma Juriya wajen shanye kowacce iriyar damuwa ce. Jin hakan ya sanya na fara jin yanayin ya yi min kama da kamar farkawa ne a cikin wata sabuwar duniyar ta daban ne.
A hankali na daina jin zugin da zuciyata da ƙirjina keyi suna raguwa,
Tamkar an cire min wani abu mai nauyi haka naji, ji nake tamkar wacce ta farka daga wani nannauyan bacci ne da yafi kama da na mutuwa. Jiki a matuƙar sanyaye yaya khaleel ɗin ya miƙe yana nufar office ɗin da ake son ganin sa don bamu sallama, jiki ba kwari haka yake tafiyar tunaninnika barka tai iri iri sun mishi tsai a rai game da cin mutuncin da Hameed ɗin ya musu. Haka har ya nufa wurin dr ɗin aka basu sallamar yana tahowa tare da wata nurse hannunta riƙe da irin baby kit ɗin nan da akan bama jarirai sabuwan haihuwa a cikin privete Hospital ɗin. Dake yau Dr Asia Maleek bata sama fitowa da wuri ba amma dai tace a dakace ta.
★
A can kuwa ɓangaren su Maman Hameed sammm bata ji labarin sakin ba se a washe garin ranar Ummi ta shiga fuskarta faɗaɗe da murmushin cin nasara ta furta."Mama kiyi murna kiyi rawa kiƙara yin rawa mama jiya dai Hameed ya saki Aysha"
Aikam se da Maman taji ƙirjinta ya buga amma tana basarwa, Se ma rungume ummin da tayi, kafin daga bisani Maman ta janwo hannun Ummin suka zauna tareda fadin. "Ke Ummih taya Hameed ɗin ze saki A'isha, Anya kuwa wannan zancen na jine?" Tayi maganar kuma alhinin mutuwar na bayyanuwa muraran a face nata. Normally ummin ta dawo tare juya zancen ta bama Maman a bay bay domin duk abinda take yi ta sani. Tun daga nan jikin Maman ya ɗan yi sanyi kuma, dan tun da ta shige ɗakinta ta kwanta a saman bed ɗin ta rasa abinda ke mata daɗi kuma, haka kawai taji fuskarta na tara ruwan hawayen da bata san ko miye dalilin su ba, A hankali ta lumshe idon tana ɗan faɗawa duniyar tunani....
A can cikin gidan kuwa kowa se a washe garin ranar yake jin maganar sakin da Hameed yama Aysha'n, wasu kamm sunyi murna sosai amma a munafurce, wasu kuma sunyi baƙin cikin jin hakan dan tamkar sa zare ma kusan. A lokacin da sumayya taji zancen wannan Mummunar zancen kuwa da kanta ya ɗebi wani jiri, se da tayi saurin dafe ginin ɗakinta. Kafin jikinta na wani kalan rawa ta isa ga abban Nailerh yarinyarta har zuwa lokacin jikinta wani irin saɓa rawar tashin hankali yake. A lokacin yana tsaye yana shiryawa ze tafi kasuwa ta faɗa daƙin tare da furta. "Abban Nailerh kaji wai Hameed ya saki Aysha!!!" Tayi maganar ne kuma idanunta na ciko da wasu ruwan hawaye.ganin yadda duk take nemar tashin hankalin ta ne ya sanya Abban Nailerh'n buga mata wata uwar tsawa tare da furta. "To kuma ni ina ruwa!, Tun dai ya rigada ya sake ta ba shike nan ba" daga haka ya sa kansa yana karasa fucewansa a ɗakin, yan jin cewa yau da ace uwa ɗaya suke da Hameed ɗin babu abinda ze hana shi masa shegen duka. Tun da dai shi baya da hankali da kuma hangen nesa, tun da har ya iya rabuwa da Aysha'n macen Rufin asiri.
Sumayya'n kuwa yana fita ta jikinta ya soma wani irin tsuma kafin a hankali kuma, Tayi wani irin murmushi mara kyau irin na mahaukatan da aka cire ma rai da samun hankali. Kafin kuma daga bisani wasu hawaye suka ɓalle mata suna zubo mata, tafukan hannuwarta tasa tana tare hawayen tare da boye fuskarma cikin tafin hannuwan nata, tane me furta. "Wai me mutane suke ɗaukar wannan DUNIYAR ne? Madauwama? Ko kuwa wasu mutanen ɗauka suke ba za'a mutu bane?, Shikenan
duniyar Aunty Aysha ta sake rugujewa innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Jama'a Ummi tayi nasara akan Aunty Aysha ya RAHMAN ka jiɓanci lamarin wannan baiwa taka....
Daga haka ta kai zaune ƙasan files na ɗakinta tare da jingina kanta da bango, zuciyanta da ƙirjinta na wani kalan bugu mata da masifar ƙarfi kamar zasu faso daga ƙirjinta su fito, haka take ji. Maganganu take yi marasa kan gado da kuma rashin lissafi. Take idanunta suka kumbura sukai luhu². Hakan yasa ta runtse Idanun sosai tana ta ƙoƙarin ganin komai daya dinga faruwa basu dawo mata ba. Amma ina komai yaci tura haka ta ringa zeroying maind nata tun daga farkon yadda abubuwa suka soma faruwa, kamo daga tata rayuwar zuwa rayuwar Aysha'n. Lallai wata kaɗɗarar ma ni'ima ce a cikin rayuwarmu. Tabbas sumayya tayi kuka, tayi kuka, tayi kuka mai tsanani,kukan da ke ratsa zuciyar duk me sauraran sa, kuka ne wanda bashi da mafita akaro na ba adadi ta yi shi. Ahankali ta juyo ta na zubama Ahmad daya dawo ɗakin fararen idanunta akansa. "Kuka kuma Soumayyah?" Ya furta duk da yasan cewar ba abin mamaki bane kaɗan kenan daga cikin irin yadda Sumayya'n ke ƙaunar Aysha'n. Kanta ta girgiza masa tana kuma sha re Hawayen dake zubo mata still, hannunta ya kamo yana yin kan 3ster da ita suka zaune, kafaɗarta ya kama yana zuba idonsa kanta cike da shegen tausayi da tsantsan SOYAYYA'R da yake mata ya furta. "Soumayyah komai na duniya da kike gani ɗan haƙuri ne, sau da tari wata ƙaddarar se kiga ta zamo ni'ima a cikin rayuwarmu, yanzu haka Ubangiji ya raba tsakanin su ne domin bata farin cikin data rasa tsayin rayuwarsu ta aure. Ki ce Alhamdulillh!, Ce Alhamdulillh kiyi ta maimatawa In Sha ALLAHU KHAIRAN kin ji Sumayya tarh..." Kanta kawai take gyaɗa masa kafin daga bisani ta furta. "Na sani!, Na sani!!, Na sani abban Nailerh komai na rayuwa da yake faruwa da kowanne bawa muƙaddari ne tun daga Rabbis samawati, UBANGIJI yasa karshen wahalar Aunty A'isha kenan, Ubangiji yasa bata da rabon sake dawowa cikin wannan ƙangin data bari Albarkachin Annabi da Alqur'ani 🤲 na roƙe ka ALLAH." Daga nan ya sake kwantar mata da hankali kana ya tafi kasuwar, domin har ya fita yaji bazai barinta cikin mugun halin daya barta ba....
Wunin ɗaki tayi ranar bata fita can cikin gidan nasu ba. Haka tayi tama A'isha'n adda'o'i masu kyau kan ALLAH ya bata kariya a cikin sabuwar rayuwar da zata
fuskanta nan gaba.
Se a washegarin ranar kana ta fita cikin gidan, abinda yafi bata mamaki da ɗaure kanta shi ne, idan ta doshi wuri ana zance ana ganinta za'ai tiɓ alamar munafinci ake ba'a son taji. Haka har maganganu ƙananu suka soma tashi a cikin gidan, cewar yau magana yata mata tayi iska dashi alhalin ba haka akai ba juya zancen kawai akai. Don haka Maƙiyanta na gidan se suka sake samun damar baje kolin damar ci bata mutumci akan cewar dama ai ba cikakken mutumci gare taba, kunji fa ɗaukar ma kai........
Dake Ummin da ƙanwar nata shegun makirai ne se da suka bi sumayya har ɗakinta wai dama ita munafuka ce, wato an saki uwar ɗakinta shi ne ta ɓoye kanta, wannan abu da suka sake mata ya sake sakata cikin tashin hankali sosai. Domin sumayya irin mutanan nan ne da samm sukaƙi jinin aikata laifi, dan haka abinda basuyi ba idan akace tayi takan shiga cikin damuwar hakan sosai. Itama se taje jin duk gidan ya gama fita a kanta domin dama kawai itama zaman haƙurin take yi, Shi kuwa Oga Hameed babu abinda ya damesa da ƙananun maganganun dake tashi kan cewar son baby'n yake, kuma dai ganan duk kan alamu sun gama bayyana kansu, ko daga yanda zasuci uban wanka ya ɗauke ta wurare daban daban. Itama kuma mutuniyar dake hauke ke ɗibarta bata taɓa damuwa da inda suke yawan fita ɗin. Wani sa In harda jeji yake kaisu, wayar hannunta kuwa tuni ya jima da sanja mata bayan ya bama Ummin ta wajen hannunsa tsadadda da yake amfani da ita, So da kamar 3 Months se ya amshe ta hannun baby'n ya bata ta wajen Ummin,ita kuma ya sanja mata sabuwa. Ita kanta Sumayya'n idan ta kalla wani abu hamdala take yi da ƙara da A'isha bata gidan, don kuwa ciwon zuciya za'a ta ɗaura mata amma se ALLAH ya sauwaƙe mata tun da bata gidan ma baki ɗaya.
Ita ma kuma fatan ta ALLAH ya sauwaƙe mata ɗin, domin ko iyaka yaran gidan kaɗai sukan iya bugarwa da mutum zuciya ya mutu a banza. Don zaratan yarane matasa a gidan ƴaƴan kishiyar surukuwarta, dake uwar ba'a zaune take ba wani shegen kwarni yaran ke dasu. Kusan su uku komai a ɗakin Sumayya'n suke ita kuwa ma ɗayar matashiyar me suna Salma kafff kayanta na a ɗakin Sumayya'r ne. Komai a can take yi tun daga kamo wanka abincin ta, kai da ɗakinka baka da kataɓus ɗin komai. Gata irin matasan yaran nan ne da sammm basu san wata aba kara ko kawaici ba, ta kwanta tayi bacci iskar A/c ta fifita shi ne kawai. Haka kanta tsaye gadon Sumayya'r baya da shamaki da hawanta tayi kwanciyarta tasha bacci, ko ta sha chart nata ko kalla ko karatun littafi, amma haka zata tsallake ta bar mata abinta sedai ta gyara, duk dai abubuwa ne gasu nan marasa kyau da tsari a gidan, haka gandamemen samrayi ze shigo ya yi wanka a toilet nasu na waje. Ga shegen ɓakin surukuwarsu da baya ƙarewa na marasa hankali, dan kun san ance idan mutum ya fiye yawan zuwar maka gundurarka yake yi, barin ma ace irin se mutum yayi 2 Week's haka kuma baya ɗaukar 3 Months be dawo ba, duk waɗan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12