An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
🌏𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐🪐
𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚🤦
https://chat.whatsapp.com/GPqgcKaetS8DsxgpdSuLOc
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Official Mirrah💐
♡
Page 1&2
The Beginning of the Beginning
*THE WRITER'S OF*
_KAREN BANA_
_MIKIYA_
_ƘAUNA BIYU_
_JALAAL AREEF_
_TA DABAN_
_ongoing DUHU na DUKAN duhu
And DUNIYARMU 🌏_
*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*
~Alhamdulillh da sunan ka ALLAH zan fara, ya Ubangijin sammai bakwai da ƙassai bakwai ka bani dama da kuma lafiya da kaifin basirar damar rubuta wannan littafin da nake jin a cikin jinin jikina IN SHA ALLAH ze kawo gyara wa al'ummar mu~
_This novel is for you Ƙaunar ƙaunata 💘, Nainerh kd, se may Bestie Mee tarh Nanameerah, tare da Ta daban ɗita salma Ahmad Isa. This book na kyauta tun daga farkon sa har karshe i love my humies darling princess nawa💐💘_
_JAJIRTATTU WRITER'S Tabbas zan jima ina jinjina kalan baiwa da kuma ƙoƙarin da muke da, HAR ABADA ƘARSHEN ABADAN KUNE AMMEY LAYLERH kamar yanda AMMEY LAYLERH itace ku for ever never IN SHA ALLAH love U all my heart and soul MAMAN IHSAN TAWA UBANGIJI ya kare min ke a duk inda kike_
*MY HUMY DARLING PRINCESS TAWA BA,KUMA DAI KUNSAN WANNAN ZANCE NE WAI INJI MAGANA. Ayi tuya a manta da albasa dole ince Na'ima Sulaiman Sarauta Nimcy Luv har abada ƙaunarki ɗaya ce a gareni my Role model me zuciyar lu'ulu'u da Zinare*
_Special Thanks to Masoya masu bibiyana ina alfahari daku a ko ina a kowacce duniya kuke Love you all 💞💖💘💗_
✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫*
(J.W.A)
♡
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
_Wannan alƙalamin bawai zaiyi rubutu bane kamar yadda ya saba a baya ba, A ahhh wannan tafiyar ta musamman ce domin kuwa wannan tafiyar tasha ban ban da sauran tafiyoyinmu na baya, dan wannan tafiyar zanyi rubutu ne akan irin ƙalubalen dake faruwa damu ne a gidajen aurenmu, da yatta kishiya ke mallake mijinta ta hanyar asirce asircen da suka gama kewaye wannan duniyar tamu da kalolin ƙalubalen da muke fuskanta irin ɗaci da kuma raɗaɗin da mazajen aurenmu ke bamu a cikin wannan duniyar me tattare da tarin ƙalubale naban mamaki da al'ajabi. Kow ka kalla a wannan zamanin babban buri da kuma fatan dake danƙare a cikin zukatan mafi yawancin mutanen mu shi ne samun duniya a hannunsu.. Wannan littafin me suna DUNIYARMU ze fara zuwar muku nan bada jimawaba IN SHA ALLAH. Paid Book ne wanda zaka biya iyaka 1500 ɗin ka kaɗai dan ƙaruwa da abubuwan da suka mafi ƙarfin Naira million biyar. Domin kuwa abubuwa ne na musamman ƙunshe a cikin sa_
_ꨄFARKO.....
♡ Ɗurkushe takai a wurin tana dafe da daidai setin heart nata idaniyarta nayin wani kalan fitinannen masifan jan da kai tsaye idan ta kalleka dasu zasu iya tsoratar dakai tsoratarwa mafi muni ma kuwa,Kafin jikinta ya shiga wani irin jijjaga na tsantsan tashin hankali da ban mamaki. Wani irin azababben ɗaci da ciwo ne yazo ya mata tsai ya mata karen tsaye ya tsaya mata a tsaƙiyar ƙahon zuciyarta. Rinannun idanunta ta ɗago ta zuba akan babban yaronta Amaan me kimanin shekaru goma sha biyu wanda yake tsaye jikinsa na rawar tashin hankalin uwa mahaifiyar data kawoshi duniyar na zubda ruwan hawayen da suka fi dalma narka zuciya. "Mommy ki faɗa min dan ALLAH me ya faruuuu? Me ya faru dake mummyna?...." Yayi maganar cikin muryan kuka da tashin hankalin shima domin tun daga lokacin da mahaifinsu ya karo aure ya auri yar yayar mahaifiyarsa be sake ganin farin ciki madauwami kai tsaye a fuskar Mummyn nashi ba. Amma kuma na yau ɗin yasha ban ban da sauran domin kuwa ya shigo ne ya tarar tana ɗauke ƙwalla a cikin idanunta kuma batai gaggawar ɓuya ta goge ba kamar yadda tasha mishi hakan. Kai tsaye ta kamo hannun Amaan ɗin tana kallonsa cike da rauni da tsnanin tausayin halin da zata tafi ta barsu ta furta. "Amaan daddy'n ku ya SAKE NI! Gidanmu zan tafi...." Se kuma kuka yaci ƙarfin Zuciyarta tana rushewa dashi. Kwace hannuwansa a cikin nata yayi cikin wani irin tsoro ya waro idanuwansa waje yana dafe ƙirjinsa tare da cewa. "Shi daddy'n shi ne ya SAKE KI Mummy? To mi kika may? Me kika masa ina daddy'n yake naje wurin sa dan me zeyi hakan dan me ze aikata haka gareki Mummy???"
To she bakinsa tay da tafin hannuwanta kukanta na son kwace mata ta shiga jijjiga masa kanta hawaye na furari a cikin idaniyarta kafin ta aro wata irin jarumtar da ita kanta tasan ta dole ce ta furta. "Kar kaje Amaan! Kar kaje ya dake ka! ka barshi zan tafi gidanmu nima.....
Kwacewa yake ƙoƙarin yi daga gareta amma ta masa wani irin riƙon daya kasa kwacewar kuma cikin muryan kuka ya shiga faɗin. "Ki kyaleni naje Mummy ko kashe ni zayyi ya kashe ni in yaso ke ya ƙyaleki a gidanki ki zauna, dan me Daddy ze aykata haka garemu me kika masa duk abinda suke aykata miki su basu gani?" Hawayenta ta sha re tana kawar da kanta daga gare shi . cikin dakewar murya ta furta. "Turomin sauran ƴan uwanka ina Aysha take?" (Tana nufin mabiyiyarsa kenan ƴar shakara goma da watanni biyar) domin fikonsu ba wani yawa wannan haihuwar da ake ƙira da kunika tayi tsakanin su. Ana haka sega sauran yaran nata na shigowa harsu uku wato Aysha ɗin sai jalila da Ashman. Su duka ta haɗa ta rungume a jikinta tana jin zafin rabuwar da zatay dasu ta barsu hannun KISHIYAR da samm babu ko ɗigon tsoron ALLAH a cikin rayuwarta. Ita ba kanta take kokama da tausayawaba yaranta, yaranta sune take kokawa take kuma tausayawa.
Rayuwarta tun farkon ta jarrabawa ce, kuma hasalin rayuwar ta fara ne tun daga lokacin da daddy'n su Amaan ya mata kishiyar da tazo ta addabi rayuwarta. Duk da tana iyaka ƙoƙarin ta na ganin ta wanzar da fara'a da dariya a fuskarta, daga can cikin ƙirjinta kuma cikin wannan tsokar da Allah ya halasta a cikin tsaƙiyar ƙirjinta wanda ita wannan zuciyar ta zame mata sirrinta,wacce take iya ɗauke ko wanne irin dafi da zafi da ɗacin ciwo me azabar ƙuna, wanda raɗaɗin sa ya wuce na digar dalma kamar yadda zafin ciwon ya wuce na haihuwa a gareta. Daddy'n Amaan ya kasance shi ne komai da ko mai nata tun daga lokacin auren su tun na saurayi da budurwa. lokacin daya kasance shi ne ya zamo abin dogaronta na bayan ubangiji, abin alfaharinta ne bayan mahaifinta abin tunkaho da adon tane bayan suturar ta, kai tsaye zata iya ƙiran shi da garkuwarta ko kuma tace duniyarta baki ɗaya. Ta ya ya ma za'a ce zuciyarta ba zata mata ƙuna ba a yayinda data fuskanci rashin wannan kwarin gwiwar taya zata iya jurewa raɗaɗin rashinsa muddin numfashinta na bugawa daidai a cikin tsaƙiyar ƙirjinta? Ita UWA ce kuma MAHAIFIYA jigo ga yaranta.
Ban sani ba ko kun fara fahimtar inda labarinta ya dosa, ko kun samu wani ɗan clue daga tarin ƙalubalen data dinga fuskanta a gidan aurenta. Kawai dai abinda na sani sanan cewa kun ƙagu ku san wacece wannan baiwar ALLAH'R?, wacce irin tarin ƙalubale ta fuskanta a gidan aurenta kamar yadda na ƙagu NI! Kaina AMMEY LAYLERH mu tsunduma cikin labarin ɗin kai tsaye dan ta fitar mana da abinda ke cinkushe cikin Rai da Ruhinta a karo na farko a cikin duniyarta baki ɗaya.
Duk inda Ƙaddara take to kuwa kowa yasan cewar abokiyar tafiyar rayuwa ce, in har akace zuciya na cigaba da bugun numfashi kuma naci gaba da kai da komo a cikin tsaƙiyar ƙirjin ko wanne bawa to kuwa tabbas akwai tarin ƙaddara da tarin jarrabobin rayuwar dake tattare dashi. Se dai kowanne bawa da kalar tashi ƙaddarar ta wani tasha ban ban da wani. A cikin tafiyar rayuwar kowanne ɗan Adam yana fuskantar wasu tarin ƙalubale da jarabobin rayuwa.Wanda wasu loƙutan da dama sukan kaimu ga faɗuwarmu kodai mabuɗin nasarorin mu, wanda idan a cikin nasara da rashin nasara kayi gamo dakatar muke jin kamar mun rasa komai da komai namu ne dake cikin rayuwar tamu, Amma a cikin koyarwar addinin Musulunci rashin nasara ba wai kawai yana nufin ka faɗi bane, amma duk a yacce ka yadda ka sake miƙewa ALLAH lamuranka to daga nan ne hasalin rayuwar ke farawa.Tabbas duk wata nasara na cike ne da tarin ƙalubale na rayuwa mai tarin yawa kullum kwana muke mu tashi ba tare da Sanin waye Masoyin mu na gaskiya ba. Akwai Mutane da dama dake kewaye da rayuwarmu waɗan da Indai baka Mu'amulance su ba bazaka taɓa gane mutanen Kirki bane. Sau nawa ka taɓa zama ka yi magana ko ka yi mu'amala ko shiga cikin mutanan da ke cikin tsanani da tashin hankali na rayuwa da wanda suka shiga masifu?.
Komai na rayuwar ɗan Adam na tafiya ne bisa tsari da kuma ƙudurar ubangiji, komai kaga ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin rubutun kundin ƙaddarar sane, Wala ƘADDARA me ƙyau ko akasin hakan se dai masu iya magana sukan ce ita ƘADDARA abace mara tabbas nan dake takan iya sanjawa. Ita kuma yarda da ƙaddarar kanta me kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin cikakken Imanin ko wanne bawa. Cikin Rayuwar ko wanne baya bai zama lallai ace saika amfana da wanda yake a tare dakai ba, Wasu loƙutan maban banta akan sha wannan fama na kusa da kai da kake ma kallon Inuwar ka ko Allon jinginarka tashin farko kwatsam se kaga kaine zaka kyautatawa na kusa da kai, Se kuma kaga sama ta ka wani shi ne zai shigo cikin rayuwarkan daga nesa ya zamo shi ne Hasken ka majin ginar daka jima nema. Kamar yadda wai Akace salati baya hana ɗaukar rai se dai In mutuwa bata zo ba kamar kowanne rayuwar ɗan Adam yake nan cike da tarin salon ƙaddarori masu tarin yawa, akowacce duniya akuma koda yaushe ƙaddara tana tafiya ne daidai da rayuwa, haka kuma tana rayuwa da mune cikin farinciki ko akasin haka. Domin tana rayuwa damu ne tamkar inuwar mu, muna tafe tana bibiye damu wanda duk iya gudun ka duk iya saurinka baka isa kauce mata ba domin ƙaddararmu tana gudana ajikinmu ne tamkar jini.
Wani wahaltaccen numfashi ta shaƙa haɗi da ijiyar zuciya daidai lokacin da ɗan cikin ta ya wani irin toƙare mata mara, se a sannan ta dawo duniyar tunanin ƙaddarar rayuwar data jima faɗawa. Kan Amaan ɗin ta shafa cike da kwarin gwiwa kafin cikin muryan jarumtaka ta tace. "Amaan komai kaga ya faru da bawa to dama cann rubutaccene tun daga Rabbil Arsheem Azeem, ka sani wata ukuba da azabar idan sukay yawa ALLAH da kanshi shi ke kawo ma bawansa mafita ka ƙaddara wannan ɗin ita ce mafifitata Amaan. Kuma daga yau ina son ka riƙe cewa ita tsarkakkiyar zuciya bata fushi da Ƙaddarar da Ubangiji ya wajabta mata, Domin kuwa tsirin Imani ne hakan kuma shi ke tabbatar da cewa duk wani bawa bai isa shallakema tarin ƙaddararsa ba.... Kafin kuma ta rungume Amaan ɗin tare da furta.
"Ya Allah kai ne ka Jarrabeni da wannan kyakkyawar Ƙaddarar! Sannan kace idan munyi haƙuri da Juriya da duk wani Abu da zamu ci karo dashi A cikin Rayuwarmu ya Rabbil Arsheem Azeem ka bani wannan kwarin gwiwa da juriyarn iya ɗaukar hakan!!!"
Daga haka ta zare Amaan daga jikinta daidai lokacin da ƙanwarta sumayya ke shigowa room ɗin. Idanunta ta janye akan yayar tata tasan shikenan me afkuwa ce kawai ta afku Fuad ya saki Yayar tata duk da kasancewar bawai taji komai daga maganganun yayar nata bane, Amma daga yanayin data ganta da kuma Lugagge bag nata dake gabanta kawai ta san cewa ƙarshen wahalar yayar nasu ne ALLAH yay wa'adin cikarsa. Dan haka a natse jikinta a matuƙar sanyaye ta isa ga yayar tata tare da furta.
"Sorry Aunty Aysha!!!"
Daga hakan ma seta rasa mi ne zata ce mata ma se kawai idaniyarta dake cikowa da wani ruwan tausayin aunty'n nata tsantsa.
jalila, Ashman Aysha da kuna Amaan ɗin ne suka ƙanƙame Mummy'n nasu duk da basu san abinda ke faruwa ba. Kafin Amaan ya fita da mugun gudu yana fashewa da wani Mahaukacin sabon kukan ya nufa upstairs na mahaifin nasa. Sedai baya nan hakan shi ke nuna alamun cewa harya fice a gidan kenan.... Sumayya'nce ta ɗauka babbar trolly'n bayan ta miƙawa yayar nata shimar nata dogo har ƙasa loƙacin da ake idasa shiga sallar Isha'i. Duka yaran ne suka maƙalƙaleta dole zata tafi dasu kafin ta kalla abinda hali zeyi. Suna fitowa suka tarar da kishiyar nata ummi nata kai da komonta ta ƙure waƙa a cikin wayarta ita da yaranta biyu suna jin kiɗan harda rawa. Inda take ɗaya daga cikin su babu wacce ta kalla haka ta tasa yaranta gaba suna ficewa a gidan cike da tuƙuƙi da ƙunar zuciya... Suna fita ta yalyala wata uwar guɗa tare da faɗin. "Ai dama tin da kika yi kuskuren barina na shigo wannan gidan dama ya zama dole ya haramta ke a gareki Ayshaaa....
Ta yi maganar tana sake ƙure sautin waƙarta da take ji irin ta marasa kan gadon nan but ta mahaukatadai kawai.
Aysha kuwa suna fita a lokacin gidan yayi tsitttt kasancewar shi babban gida ne, babu wanda yaga fitar su har suka bar gidan. Cikin tsatsan tashin hankali take tafiyar tana duba wanda duba ɗaya me cikakken hankali ze mata ya san cewa tana cikin tsananin damuwa ne Damuwar da ta sanya canza yanayin fuskarta zuwa ganganr jikinta.
Gyara goyon jalila tayi duk kuwa da cewar uban jikin dake jikinta haihuwa yau ko gobe. Tafiya kaɗan sukai suka sama napep wanda sumayya ta tara musu itama idanunta ko gani sosai basu yi. Shi kenan abinda matan gidan su da matan baffansu ke so ya samu an saki aunty Aysha.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"
Ta furta a bayyane domin kuwa wannan shi ne mafi ƙololuwar wani sabon bigire na ƙalubalen da Aunty Aysha'n nata zata yanka. Ƙalubale ma kuwa me girman gaske haka Sumayya na wannan tunanin har me napep ɗin ya ajje su daidai bakin get na gidansu data kwatanamar. Kuɗin napep ɗin ta bashi tana sanya yaranta biyu gabanta Aysha da Ashman ita kuma tana jar trolley'n yayar nata suka tura ƙofar get ɗin sanin yanzu Baba Malam me gadin get ɗin yana masallaci Sallah. Ƙafarta ɗaya da ƙyar ta sanya mararta na mata wani kalan yankan bala'i da Masifa wata uwar zuba na yanko mata tare da faɗuwar gaban irin Mummunan halin da Ummanta zata shiga idan ta ganta tare da yara da suturarsu taji yau Hameed ya sake ta. Ina ba zata iya ba, ba zata iya fuskantar mahaifiyar nata ba domin tana son lafiyarta bata son gurɓata mata lafiya da tunani. Se dai kuma ina zata? Idan bata fuskanta Mahaifiyar nata ba? (Ba bu) ta bama kanta da kanta amsa domin mahaifiyarta ita ce duniyarta kuma Abokiyar sirrinta dan haka taji wani irin natsuwan hakan na zuwar mata tare da jan ƙafa daidai lokacin da take labulen parlour'n su. Tana zaune kan sallayar data kammala sallar Isha'i carbi riƙe a hannunta tana ja idanunta akan akwatun da Sumayya ta shigo da ita. Kafin ta sauƙe akan yarana da Aysha'n nata baki ɗaya. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe tana sake damƙar carbin dake hannunta da kyau.... Dama ita ba ALLAH'n musuru bace amma tun daga yanayin da tayi ƙiran Sumayya'n tasan ba ƙalau ba duk kuwa da cewar ba wannan bane karo na farko da Aysha'n kan ƙira Sumayya'n, sedai na yau ɗin ita kanta Umman seda ya yanki zuciyarta ya biyo ta ƙirjinta yana maƙale mata a ƙahon zuciya ashe tsabar girman kaunar dake tsakanin uwa ne da ɗan ta abinda ya farun da ƴar ta ya bugeta tun kamin ma tasan mi yake faruwan....
"Ayshatu ƙara so mana ki sauƙe wannan ƙiwwatun ta bayanki ki zo kiyi sallah karki ɓata lokacinta!" Tayi maganar cikin dakewa da son kawar da abinda ya toƙare mata ƙirji... A natse ta zame takarmin ƙafarta tana ƙara sa shigowa da sallama ɗauke a bakinta, tana zuwa ta zube gaban Umman Umman tare da kamo hannuwanta biyu ta kife saman fuskarta tana fashewa da wani cunkushashshen kuka irin me sarƙe zuciyar nan. "Ummah me na ma daddy'n su Amaan? Me na rage shi da shi da kafff cikin Rayuwar nan ya zaɓa yin watangaririya da tawa Rayuwatar da ta Rayu ne kawai da so da kuma ƙaunarsa!, Ashe da gaske ne maza idan suka ƙara aure sukan juyama matansu uwayen yaransu da suka haifa baya? Ummah zuciyata ina jin kamar zata faso ƙirjina ta fito! Ina jin kamar na yagota daga cikin ƙirjin nawa nayi jifa da ita ko nima na huta daga wannan Mummunar Rayuwa da nake a ciki.... Ummah Me ya sa ba zai ci gaba da hukunta nin da yake ba se saki Ummah........
Se kuma ta gaza ƙara sawa sakamakon kukan da yaci ƙarfinta sosái. Hannu Umman ta miƙa mata alamar ta sinto mata jalila dake goye, amsar yarin yar tayi tare da kuma da dafa kan Aysha'n cikin tausasa murya ta ce da ita....
"Haƙiƙa duk sanda ALLAH ya jarabceka to so yake ya ɗaga darajarka ne. Tabbas ko wacce Rayuwa tana cike ne da tarin ƙalubale iri da kala, Kuma babu wanda ya Isa ya kaucewa ƙaddararsa mai kyau ko Mara kyau sai Abinda ALLAH ya tsara maka domin shi ƙalubalen Rayuwa har abada basa taɓa ƙarewa se dai suyi sauƙi. Domin kuwa da an fita daga wannan matsalar sai a shiga wancan. Haka kuma za'a cigaba da tafiya har zuwa sanda rai zatayi halinsa. amma jajircewa da haƙuri su ne makullin cin nasarar ƙalubale a koda yaushe.....
ka nemi zaɓin ALLAH ba zaɓin ka ba don zaɓin ALLAH shi yafi cancanta agaremu ba zaɓin zuciyar mu ba ya dan haka ki roƙi ALLAH ya sa hakan shi ne mafi Alkhairinsa gare mi Ayshatu... In Sha ALLAH Nasarar ki na a gaba ne AYSHA domin wannan ɗin tamkar ya yanke miki wani giɓi ne na daga cikin tarin ƙaddarorin Rayuwar ki ne! Ta shi ki je kiyi sallar Kar lokacin ya ƙare miki....
Tun da Ummanta ta soma maganar ta sake matse jikinta wuri guda tana ta ƙoƙarin ganin ta tsayar da kukan daya taho mata tun daga cikin tsaƙiyar ƙirjinta, Sai dai ta gaza hakan duk yanda take daurewa kasawa tayi seda kukan ya kwace mata, gaban yaranta da tun farko bata son susan irin zaman da take yi da daddy'n su, tun tana ɓoye masu har ya kai yanzu yaran babu abunda ba su sani ba game da irin zaman da take yi da daddy'n nasu da kuma Ummih kishiyarta....
Kanta Umman ta shiga shafawa alaman tayi shiru ta daina, sake shigewa jikin ummman tayi tana sake sakin wani sabon kukan. ɗan bubbuga bayan ta ummah ta shiga yi tare da faɗin....
"Ya isa haka nan kiyi haƙuri ki daina kukan nan domin kuka baya taɓa maganin damuwa kiyi dua kawai ALLAH se ya mana maganin komai. Da ƙyar ta miƙe Idonta na sauƙa kan lil Aysha da Hameed ɗin ya mata takwara da ita. Lumshe idanunta tayi wasu hawayen masu ɗumi na sake wanko mata fuskarta tana sunkuyawa kan Aysha'n da har bacci ya ɗauke ta. Teddy ɗin dake gabanta tare da Book nata da tun yamma take bin uwar ta mata Home work bata sama da ma. Littafin ta ɗauka wasu hawayen masu tsananin zafi da ƙuncin na sake ciko Idaniyarta dukkanin jikinta na ɗaukar wani mummunan sanyi....
Idanuwanta na sake yin jajir tana jin wani abu naci gaba da yankar ƙirjinta zuciyarta na sake fidda asalin raɗaɗin samun kanta da tay cikin wannan matsayin.... Littafin ta janye mata gefe kafin ta shige bedroom na ummanta alwulan ta ɗaura kana anan bedroom ɗin ta gabatar da sallar tare da shafa'i da witirin data saba duk sallar ishar duniya. Ta jima Sosái tana adda'o'i masu girma ciki kuwa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12