Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
12 / 12
ƙarfi tare da furta. "Wayyo ALLAH Naaaaaaa, wayyo zan mutu wayyo wayyoooooo..... Tayi maganar tana dafe ƙirjinta wanda hakan ya janyo hankalin mutanen dake cikin ɗakin da basu san da ita ba, Aunty fa'iza ce ta fito idanunta jajir itama se share ƙwalla take kama ta tayi tana bata baki suka shige cikin parlour'n, inda Ashman ɗin ke shimfiɗe da dukkan alamu dama ita kawai ake jira. "Umma tun yaushe ya mutu amma ba'a faɗa min ba? Babu wanda zai ƙira ni kuma!!!?" Ta faɗi tana zamewa ta zauna gabar gawar dake suturce cikin likkafaninta ashirye tsafff. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" haka ta shiga nanatawa ganin yadda fuskarsa tayi daga² duka jikinsa se sake fidda jini yake. "ALLAH ya maka Rahama *NASEER* ya sa masu ceton mu ne, ALLAH na gode maka Ni A'ISHA!!!" Ta furta tana kifa kanta akan gawar kafin tamkar wacce aka zabureta kuma ta ɗago ta fara masa adda'a Sosái. Tana cikin masa sega Yaya Khaleel ya shigo tare da Yaya Habu, ɗaukan makaran sukayi suna fita da ita inda tabi makarar da kallo idanunta na wani kalan rikiɗewa su rune. Batayi kuka ma sema rumtse idanunta da tayi lokacin da taji kukan su Amaan da little Aysha tare da jalila. Ƙuri tama wuri guda aranta tana ayyana. _Shin wai sai zuwa yaushe zata dena zubar da hawayenta ma tarin ƙaddarorin dake bibiyar Rayuwanta ne?_ _Shin yaushe ne babin rayuwarta zai juye zuwa wani mataki na daban?_ _Shin sai zuwa yaushe ne rayuwarta ita da ƴaƴanta zatayi haske? Yaushe zasuji daɗin rayuwa ita da ƴaƴanta tamkar ko wanne Rai me numfashi?, Yaushe haske zai ratsa cikin rayuwarsu ita da ƴayanta?_ _Shin dama laifi ne dan ƙaddararta tazo mata a baybay ta yadda batayi zata ko tsammata ba?, Ashe haka dama duk wanda ƙaddara me tafe da tarin ƙalubale suka cukuykuye rayuwarsa yake ji? Wani irin ɗaci da raɗaɗi me zafin gaske take ji a duk loƙacin da zata buɗi idonta taga wani ƙalubale ya sameta_ _Da ace ana zaɓen ƙaddara data jima da juya tata ƙaddara! Bafa zaɓen ƙaddararta tayi ba itace ta zaɓeta da tayi rayuwa da ita a haka, ba kuma itace ta tsara ma kanta yanayin rayuwar da suke a ciki ba ita da yaranta dan me rayuwar na zata barta haka nan ba?_ _Ita kaɗai tasan tarin abubuwan da suke cunshe a cikin Rai da ruhinta, wanda suka kusa tarwatsa zuciyarta ta buga ta dena aiki ma baki ɗaya, domin tasan tana dab da bugawar ne bama don Allah yayi ta a mace me tsananin haƙuri da shanye irin kowanne abu bane komi girman sa a cikin zuciyarta da tuni numfashinta ya jima da barin gangar jikinta tabbas....._ A bayyane kamm wata nannauyar ijiyar zuciya ta sauƙe. Wanda ya saka Ummanta buɗe baki da kyar ta iya furta. "Ke me haƙuri da juriyace A'isha, kici gaba ALLAH ne ke so kaunar ganinki cikin waɗan nan jerin ƙaddarorin" Kanta ta ɗago tare da kallon mahaifiyar nata cikin raunatacciyar murya ta shiga faɗin. "Nima bansan abinda ke damuna ba Ummah! Kawai dai inajin yanayin cinkushewar zuciya ne, da rashin jin dadin yanayin rayuwar ma baki ɗaya, Amma In Sha ALLAHU abinda kawai na sani shi ne bazan taɓa iya juyama tarin ƙaddarorina baya kona guje musu ba, zuciyata kawai ke amsar bugun Ummanmu..... Tace da Umman tana kwantawa a kan ƙafafun Umman, kanta ta shafa cike da ƙaunarta me ƙarfi tace da ita. "Ce ALHAMDULILLAH domin ALLAH shi ne abin godiya a koda yaushe! A'ISHA" ALHAMDULILLAH ɗin kuwa ta furta tare da duk sauran adda'oin da suka zo mata cikin baki. Yaran ne suka shigo su uku suna jerewa a gabanta suma suna kwantar da kansu jikinta,Dukansu ta haɗe tana rungumesu ƙamƙam tamkar wacce take tsoron a sake rabata dasu..... ★ 𝔸𝕁 𝙈𝘼𝙅𝙀𝙀𝘿 Directly kai tsaye daga nan gidan su Maman SOFIA ya nufa Maman matarshi data rasu, wacce kuma a yanzun hakan yake auren ƙanwarta FATEEMERH take hannunsa tare da yarinyarta ɗaya itama data haifa masa Afnan. Ko gidan be shiga ba yace a fito masa da AFNAN da kuma AREEF zasu wuce Lagos. Babu jimawa kuwa sega ɗan gurds nashin nan ɗauke da AFNAN ɗin, AREEF kuma wata dattijuwar mata riƙe da hannunsa. Yana ganin Maman ya fito yana gaidata daidai tana kawowa wurin Motarsa, "Tafiya haka babu notice ASAAD, to shikenan ALLAH ya sauƙe ku lafiya ganan saƙo a tafima da Fateemerh A gaida Hajiya sosái itama ga nata saƙon nan tayi maganar tana nuna kayan da akayi Parking nasu already. Godiya yay yana mata godiya da haka aka gama zuba kayan a boot ma motar, kafin yaran su shiga suna sanya shi tsaƙiyarsu nan driver yaja hancin motar suna barin gidan. Kai tsaye se airport lokacin ƙarfe 3 cif². *Lagos* Misalin ƙarfe biyar na yamma manyan motocin AJ MAJEED ɗin dake cikin garin Lagos suka ma airport ɗin tsinke. Wasu irin zafafan motocin kusan goma sha biyar su Range Rover, Bugatti Veyron, Toyota Highlander, Toyota Tacoma, Ferrari California, gefe guda kuma ga wasu mahaukatan manyan jifa jifai har guda biyar da aka ware su baƙaƙe wulik dasu. motocine a wurin babu colourn da babu, shi kansa airport ɗin kewaye yake da tsaro na musamman. Kasancewar magana ake ta _THE BILLIONAIRE ASSAD JUNERD MAJEED_ Wanda al'ummah ke son ya zamo musu shugaba a kasarsu shi kuma samm ya ƙiya hakan yana fisgewa, domin samm shi a ra'ayin sa babu siyasa sam a ciki.. Ahankali cikin takun izza dajin kai ya fara tako matakalar benen, wanda izzar ke haɗe da mummar ɓacin ran daya taho dashi daga Kano. Su kuma samudawan sa na aikin su na take mai baya, cikin sauri manyan security'n dake zagaye da airport ɗin suka shiga bashi kariya wa kallon da jama'ar airport ɗin ke binsa dashi, harma da masu dasa masa Camera's,Yana sanye ne cikin Wani arnen cashmere valley wanda kallo ɗaya zaka ma yadin ka tabbatar da ba karamin kuɗi aka narka wurin siyen shi ba... Ahankali yake taka Fararen santala² sawayensa da tamkar wanda bai taɓa taka ƙasa da su ba haka suke, don tsananin taushi da kuma yadda suke sumil luwai. Wata kafurar Black blue ɗin Mota ƙirar Mercedez Benz aka buɗe masa, yaran kuma aka buɗe musu wata baƙar jeep Wrangler, cewa yay a dáwo masa da yaran tashi motar dan haka cikin abinda bai gaza kiftar Idanu ba aka dawo masa da yaran motan da yake, driver najan motar da suka sanya a tsaƙiyar jerin manyan motocin, suna ɗauka hanyarsu. Tafiya ba wata me nisa bace ta gaisu gaban wani haɗaɗɗen house mension, Hong sukayi sau ɗaya get man ya wangale musu haɗaɗɗen get ɗin gidan. Kai tsaye suna danna hancinan motocinsu gidan, A wajen da aka tanaja domin ajjiye motoci, tarin motocin suka faka. Kafin mutanen dake ciki sanye da baƙaƙen suit suka firfito suna bada tsaro wa na cikin motar. dukansu sanye cikin baƙaƙen kaya gaba ɗayansu manyan bindigune a hannayensu. Cikin da zafin nama ɗaya daga cikin security'n ya isa ga motar dake tsakiyar duk ƙofofinta a kulle yayi knocking baƙin glass din motar, wata gajeriyar magana sukayi sannan ya sake zagayawa right side na seat ɗin bayan motar ya buɗe ƙofar, yana ja baya cikin girmamawa don bawa mamallakin cikin fitowa. Sai da yaja wasu ƴan sakanni kafin kyawawan sawayensa su fara fitowa, sai daukar idanu suke saboda tsananin kyau da tsafta, Saida ya sake ɗaukar wasu sakannin kafin ya zuro dukka jikinsa zuwa waje. Zara zara hannunsa ya sanya yana fara ciro afnan kafin ya miƙama AREEF hannu ya fito dashi. Har zuwa lokacin nan kuma kyakkyawar fuskarsa mai cike da wani irin kwarjini haiba da cikar zati na ɗin ke tsaf babu alamun fara'a ko kaɗan tattare da ita. Kyakkyawar soft fatar jikin san nan me murjajjen jiki se ɗaukar Idanu take, Lallausan sumar nan kuwa da tasha uban gyara yayi luf luf kwance ƙasan ƙeyarsa saboda wani irin gyara na musamman da akayi mata, Baƙar sumar da Sky blue cashmere ɗin dake jikinsa suka haɗu suka sake haskaka farar fatarsa tarrrr tamkar fitowar rana a farkon wuni. Wani irin daddaɗan ƙamshine ke tashi a jikinsa irin me ɗaukar hankalin nan. Ko yaya ka ƙara taƙi kaɗan kusa dashi kana iya shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa da ba lallai ka gane ainihin wanne irin turare bane,saidai yakan sanya nutsuwa ga duk wanda ya shaƙa ya kuma ƙara kwarjini ga ma'abocin ƙamshin. Compound na gidan ya shiga ƙarema kallo,kyawawan fararen hannuwansa zube cikin aljihun tsadaddan cashmere ɗin dake jikinsa,Sake gyara zaman bindugunsu security'n sa suka sake yi a tsare cikin shirin kota kwanar karbar umarni daga gareshi. Wata zazzafar Iska ya ɗan furzar kafin ya taka zuwa gaba yana saɓar afnan ɗin akan shoulder nashi, tare maza wajen biyar suka take masa baya biyu daga ciki sukayi gaba kamar masu masa jagora,sauran kuma suna biye dashi. Cikin takun cikakken gwarzon namiji yake takunsa har zuwa gaban ƙayataccen Royal parlour'n da yake ƙawace da wasu irin Italian Wikipedia Sofa's. Daga nan duka security'n suka tsaya a parlour'n. Zaune ya tarar da Fateemerh cikin wani Mahaukacin tsadaddiyar abaya, ta yi crossing ƙafafunta harɗe saman sofa. Fuskarta mur tasha kunu sosái babu alamar rahama, hannun afnan taja tana wullawa AREEF wani irin kallo. kollo ɗaya Boss ɗin ya mata ya ɗauke kansa yana nufar saman sa yana ce da yaron yaje wurin Sister Nablah in bata nan yaje wurin Hajiyatsa tana can, yayarshi kenan da suke uwa ɗaya uba ɗaya data mutu ta barsu. Jiki a matuƙar sanyaye yaron ya haye nasu upsairs ɗin. Kai tsaye AJ MAJEED na shiga ɗakin barcinsa kayan jikinsa ya zame tare da daura fari tass ɗin towel wanda ya ma wani irin lago lagon dauri, kafun ya wuce bathroom kai tsaye cikin bathtube ya shige wanda ya hada ruwa me dumi da fresh out ɗin wankan daya zuba. Shower gal ɗin na metullarh sking ya ɗauka tare da soson wankansa ya fara sille jikinsa, A kalla sai da ya shafe mintuna masu dama kafin ya fito,tamkar wanda yake sauya fatar jikinsa fatar nan sai uban daukar ido da walainiya take, Ta kota Ina AJ MAJEED Namiji ne tsayayye da babu abinda yake masa shamaki da cikar zatinsa. Lafiyayyar fatarsa dake ɗaukan idonu ya kalla, ganin wato shi hutu da jiƙa cikin arziki da nutsuwa kansa wani abu ne na daban da idan Allah yayika cikinsu basa taɓa boyuwa ko yayane. kau da idanunsa da suka dan canza launi sakamakon shigar ruwa cikinsu da kuma guntun ɓacin daya taho dashi, ga kuma wanda Fateemer'r ta sake ƙuma masa yayi, yana mayarwa ga madubi yana ƙoƙarin tsane sumarsa data jiƙe da ruwa, Abu guda daya tak da zai fara gaya maka AJ MAJEED ɗin ba asalin bahaushe bane, kodan yadda farar fatar jikinsa take da kuma tulin gashin kansa da yake amsar kudade masu gwabi wajen gyaranta. A natse ya shirya cikin wasu Ash ɗin riga da wando Armless marasa kama jiki da nauyi, wasu tausassan flip flops sleepers ya zira a dogayen ƙafafunsa wadan da kamar basa taka ƙasa haka suke nan. Waya ya fito yana yi cikin yanayin sakewa kaɗan a wannan karon. Kai tsaye ya nufa wata Luxury door fuskansa na wadatuwa da wani annurin da zaka rasa daga inda ya tsintoshi. Yana sanya ƙafafunsa cikin babban parlour'n yaci karo da Hajiyar sa, yaransa biyu zagaye da ita cikin sakewa ba kamar a nasu bangaren ba. Zama yayi gurfa gurfa gabanta yana gaida ta. Cike da fara'a sosai ta amsa shi tana tambayan sa hanya, Alhamdulillh yace da ita fuskansa na sanjawa daga wannan annurin zuwa akasinsa. "Me yake faruwa da uban daraja haka?" Kamilalliyar dattijuwar matar ta tambayeshi cikin kulawa. Duk da yaransa matasa biyu na tare dashi haka beji ko kunyar ganinsu ba ya furta. *"TASHA CEEEE!!!"* Ɗan waro idanunta matar tayi tare da itama da furta... "TASHAH Again???" Kansa ya gyaɗa masa yana kwantar da kansa jikin sofar da take zaune a kai. Wani kyakkyawan murmushin daya sanya shi kallonta tayi tare da daga hannuwarta tana me furta....... Inda AMMEY LAYLERH nace.... ★_ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ala kulli halin 🙏 🙏!!! Anan zamu dakata a book One ko nace free Page's na wannan littafi mai suna DUNIYARMU, me cike da tarin ƙalubale sai kuma Allah ya haɗamu da masu rabo a book two náshi danjin wacce irin cakwakiya za'a tafka a ciki_ ★Tofa masu karatu yaya take ne?. ★Mike shirin faruwa?. ★Shin me kuka fahimta dangane da Fateemerh matar AJ MAJEED? Ƙanwa ga marigayiyar matarsa SOFIA? ★Mi kalaman AJ suke nufi akan HAMEED? Shin waɗan nan kalaman zasu tabba ta ne kodai bogi ne?, ★Shin kun fuskanta Fateemerh kuwa, kamar fa adawa take yi da yaran da Yayarta ta mutu ta bari take yi, wacce aka AURA masa ita a ganin itace zata fi kowa kula dasu a wannan Duniyar bayan yayar tata, sedai Ashe Ashe lauje ne a cikin naɗi.._ ★Wayeb AJ MAJEED ɗin kansa ma wai tukunna? ★Shin ina labarin Ummih Matar HAMEED da kuma ƙanwarta Baby?_ ★Tofa wata daban gefe guda kuma gacan Aysha'n mu cikin damuwar da Ubangijinta ne kaɗai ze iya mata maganainta_ ★SHIN WAI MA MIYE DAWO DA AJ MAJEED RAYUWAR AYSHA'N A KARO NA BIYU NEEEE ? _★Hhhhh masu karatu akwaifa gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon shima. Hargitsi da cakwakiyar dake cikinsa kuwa. Hhhhumm ba'a magana, dan bama mu fara komai ba sai a book 2 Don bamu ko tsoma kafa ba a cikin littafin DUNIYARMU 🌏 _★Kai kar dai na cikaku da surutu ku shirya kawai tsaff domin warware muku zare da abawar dake cakude cikin wannan littafin, me ɗauke da tarin ƙaddarori kala da iri, masu kyau da marasa kyau_ _Duk zamu samu amsoshin waɗannan jerin tambayoyin namu ne idan mun shiga book 2 da yardar ALLAH. Nan na kawo muku ƙarshen BOOK 1 NA DUNIYARMU Wanda basu biya ba su hanzarta don kar ayi tafiyar babu su littafin DUNIYARMU Naira 1k ne kacal babu yawa_ _Ga duk mai son biya zai tuntuɓeni a wannan number_ 👇 08104493215 Ko wannan 08107880451 Wanda suke son biya zasu turo kuɗin su cikin wannan asusun bankin 👇 3206656358 Maryam Nasiru First Bank A turo shedar biya ta wannan number 08104493215 *_Kardai ku manta this one ma is not for free zaku Antayo 1k ɗin ku ta Asusun banki na 3206656358 Maryam Nasiru first Bank ko katin mtn ta wannan number 08104493215 vip suma is 1200 kamar yanda kuka sani masoya I no kuna bani goyon baya fiye da yanda nake tunani, musamman ma dai mutane na Telegram don haka ina ma kowa fatan Alkhairi don haka kar ku tsaya jiran ayi posting a sato muku na BABA NA BATI ku Antayo kuɗin ku karanta Cikin farin ciki da salama yanda kuke so sai najiku masoya karku sake ayi tafiyar PART 2 na DUNIYARMU BA TARE DAKU BA HAJIYATA by AMMEY'N LAYLERH'NKU me ƘAUNAR KU FAKA FAKA_* *Byeeeeeeeee my Re@l f@ns sai mun sake haɗuwa a cikin PART 2 gamai Rabo. Dan koda kuɗinka Saida rabonka littafin DUNIYARMU ba hhhhhhhhhhh To ai shikenan sai a gimtse koooo? A gimtse kawai baaaaa. _Hhhhhh lol 🤗🤣🤣🤣😅_ _Slow motions_ _AJ MAJEED he's going to shikenan 🤗🤗🤸💃_ *BY AMMEY LAYLERH ✍️* 08104493215 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 12 of 12