nan jerin abubuwan kaɗan ne, kuma a haɗa da takurawar kishiya data dangin miji da uwar mijin kanta. To ina mutum ya kama kuwa kunga dole ne mutum shi ma ya newarwa kansa mafita. Dan haka itama take roƙar ALLAH ya yanke mata ƙarshen wahalarta akan zaman gidan. Don a kullum dama can cikin tsoro take domin gani take a har kullum lefen jama'ar gidan kan iya shafar ta duba da cewar yanzun tsaff lefin wani yake shafar wani, to kamar haka itama take tsoron kar tarin zunufan da ake aikatawa a gidan su shafeta, dan a cikin matasan yaran matàn da ake aurowa cikin su akwai wacce malaminta har gida yake zuwa idan Mijin ta baya nan ya zane ta da rubutu, tun daga kan yatsarta babba har zuwa saman ƙirjinta. Gaba ɗaya samarin gidan ba kintsatstsu bane kawai sune naɗe ne da fatar akuyar alhalin kurayene su masu farauta.
★
A can Hospital kuwa babu jimawa Dr Asia Maleek ta iso, dake itama tsohuwar friend ɗin Aysha'n ce dan haka da kanta ta sake dubata tare da baby'n da bata da wani cikakkiyar lafiya. Daga nan aka basu sallamar yaya khaleel ya ɗebe su ita da Aunty fa'iza suna ta sake kwantar mata da hankali har suka iso gidan.
A tsanake Yaya khaleel ya yi parking motarsa nesa da inda Bappa'n su ke zaune yana hutawa, inda indai baya wurin kasuwancin sa. To kuwa tabbas zaka sake shi ne akan tabarmarsa, da jarida a hannunsa zaune yana shan iska yana karanta abarsa, ko kuma ka same shi da Radio yana sauraren shirye shiryen da ake yi. Aunty fa'iza ce ta fara fitowa ɗauke da sabuwan haihuwan naɗe cikin fari tass ɗin Baby showel, a natse ta biyo bayan aunty fa'izan ƙafafunta sunyi fari tass na halamar sabon jini, se ɗan kumburin da be gama saɓewa ba. Ajje jaridar dake hannunsa Bappah'n yayi tare da amsar baby'n idonsa na sauyawa zuwa wani yanayi na daban.
"Baiwar ALLAH kiyi haƙuri kinzo a lokacin da bai dace ba, Amma babu komai, Kowanne ɗan Adam akwai yadda Allah kan jarabce shi. To cikin kudirarsa ya jarabce ki ne a daidai lokacin da Mahaifiyar ke ke tsaka da amsar tata jarabawar!, ALLAHU ya raya *MAYRAMA*." Ya faɗi kasancewar tun suna Hospital aunty fa'iza ta ƙirashi ta sanar masa da sunan da Aysha'n take son ya maimaita mata huɗu ba...
Gudun kada sanyi ya kama baby'n Bappa ya sallamesu da wuri dan basu wani jima ba, suka shi ge cikin gidan. Nan matan Bappa'n suka shigo suka sake dubata da mata sannu. A cikin zuciyarsu kuma suna ƙus ƙus ɗin masifar da Yaya khaleel ya shigo yana yi, na rainin hankalin da Hameed ɗin ya masa na ƙin amsa woyar shi da yay. Duk da cewan dare ne amma hakan be hana Umman Aysha zagewa tama Aysha'n wanka me kyau da ruwan zafi ba, Aunty fa'iza kuma tama baby'n. Tana fitowa Anty fa'iza ta miƙo mata woyar ta da ake ta ƙira tun shigarsu wonkan. Kallo ɗaya tama sunan da tay sev da No ɗin ta ɗauke kanta. Don In Sha ALLAHU ta bar shi kenan har gaban abada. Shi kuwa daga ata can ɓangaren Hameed da har wani kuri kuri yake na cewar ai zuwa yanzun ta gama jigata, shi ne ya ƙirata yace ya mayar da ita se dai kuma yaji saɓanin hakan,dan haka yata ƙiranta babu ƙakkautawa wanda har Umma seda ta shiga maganar tace ta amsa mebi yayi ladamane, Amma haka ta mirje Idonta taƙi amsa Juyin duniya Umman tayi amma A'isha sammm taƙi amincewa tayi waya da Hameed ɗin, duk kuwa cewan da uban ƙiran da yake ta zabgawa duk wani mahulikin dake gidan. Amma tayi kunnen uwar shegu da kowa tana mantawa da lamuransu duka, Ganin wankin hula na neman kai su dare ne ya sanya Umma da kanta ta faɗama Bappah wai ko ALLAH zai sa a dace, sai dai shi ɗin ma gaba tasa shi ta ta masa kuka, dan haka shi ma se duk jikinsa yayi sanyi sosai, Nasiha sosai ya mata akan muhimmancin Haƙuri da kuma kawaici akan ko wanne irin abu ne, ita ma ɓangaren surukuwarta ƙiranta ta tayi sedai itama taƙi amsa. Domin kuwa Directly Yaya khaleel na sauƙe su bayan ya gama zazzaga masifarsa a gidan ya nufa gidan su Hameed ɗin kai tsaye. Daga nan ya buga musu wonin ɗin cewa kuma wllh basu Isa a basu yaro ko ɗaya ba, ciki kuwa harda sabuwar haihuwan da tayi a yau ɗin. Jin fa wannan maganar na haihuwa se ya mugun tashin hankalin Hameed don shi a nashi tsarin a yau ɗin da yake son ya komar da ita ɗakinta. Komai be sake birkita hankali da tunanin sa ba se da short message nata ya shigo mata kamar haka.
_Har gaban Abadan Abada AYSHA MUSTAPHA WAZEER, bata yi kala da matar da idan har tariga da tabar wuri ayi tunanin zata dawo bace HAMEED, kwarai kayi kuskus da saɓanin fahimta don Idan har na bar waje to ka sani na barshi kenan har gaban abada, karma kayi tinanin zan dawo gare ka a karo na biyu, dan idan nariga na rena kasuwa ko sautu bana mata Hameed, kusan zan iya cewa kafi kowa sanin hakan,Don AYSHA MUSTAPHA WAZEER Mace ce too majestical classic ko a gida ba'ayimata tayi biyu, dan idan tariga tayi nisa bata amsa kiran ko waye, ka ƙaddara cewar wannan ba Aysha ta gidan Hameed bace!. Wannan wata sabuwa ce, sabuwar haihuwa ma kuwa tana da aji irin wadda duk namijin daya zauna tare da'ita shima yakan iya banbanta da sauran mutane bare kuma abokanta, kai da ka ganta kasan mace ce iya mace duk wani mutumci daya kamata mace tabawa kanta AYSHA MUSTAPHA WAZEER ta jima da mallakawa kyakykyawar halittarta, kai da kaga jininta tin a ido zaka tabbatar maimaita class se jaki ita kuwa AYSHA A'1 ce tin daga kindergarten har masters shiyasa ake kiranta da Majesty girl ko Kuma too classic wannan shi ne Nick name nata bama iya school ba har mahaifinta yakan ƙiranta da wannan name ɗin idan yana jin wasa, Kuma ina son ka sani ba kuɗi ba ne mabuɗin ko wanne farin ciki, wadatuwa da abin da kake da shi shi ne sirrin farin cikin ka na har gaban abada, a wancan lokacin farin ciki daga gareka shi ne duka wani fata da buri na, Amma kai da ka tashi cewa kake, ka wadatani da komai tun daga kan suturu ci da sha dame ka rage???, *FaRIN CIKI* tabbas shi na rasa daga gareka Hameed. Yanzu wannan AYSHA'r ta rigada tayi nisan da bata jin ƙira, dan haka I don't care your time right now?_
A takaice Hameed ya maimaita wannan saƙon yafi sau cikin masaƙi, domin kuwa tsaff rayuwarta ta baya ta ringa dawo masa irin aji da kuma jin kanta. Tabbas be kyautama kansa ba be kuma kyautamawa SOYAYYA'R su ba. A cikin Rayuwa ya zalunci Aysha,yaci Amanarta kwarai yima Mace kishiya ba laifi bane, amma kuma rashin adalcin dake tattare da yin kishiyar da kuma fitinar dake cikin ta itace abar ƙi ga kowacce mace. Domin burin matan suke aure mijin wata babban burinta na farko shi ne shiga ta ruguza wannan SOYAYYA'R da aka jima ginawa. Ta fitar da uwar gidan ta raba yaran da mahaifinsu wannan shi ne....
AYSHA kuwa tana gama tura wannan message ɗin tayi block nashi tare da goge No náshi, da duk wani abu daya danganci Hameed ɗin. Idan tace komai to kuwa tabbas tana nufin komai ɗin. Domin a rayuwa Namiji ya mata fentin da har gaban abada bazai taɓa goguwa ba daga cikin Rai da Ruhinta. kamar yadda rana ke fitowa tana komawa wata ya maye gurbinta ya samar da hasken dake haskaka duniya a cikin dare.
A lokacin da ruhi da zuciya da gangar jiki suke samun nutsuwa da hutu, mizanin yadda numfashinta ke sauƙa akan tafukan hannayenta tana tarar ruwan hawayen ƙarshen da In Sha ALLAHU ta gama zubarwa akan Hameed, Kai Bama iyaka shi ba da duk wani Namijin dake cikin wannan duniyar idan har ya wuce mahaifin ta. Hawaye ne da ke bi ta gefe da gefen fuskarta suna sauƙa a cikin tafukan hannayenta, wanda take jinsu kamar ɗigar dalma a cikin zuciyarta, haka zafinsu ke ƙara birgita kanta da tunanin ta suna ci gaba da zana mata tabon ɗa Namiji. Wanda kai tsaye idan wani zai tambayeta miye damuwarta? Miye ƙaddararta?, Miye jarabawarta To kuwa Tabbas zata ce HAMEED USMAN DATTI shi ne ya haɗa duka waɗan abubuwan wuri guda ya cakuɗe mata ya tumurmushe su a cikin can ƙasar ƙarƙashin rurin wuta koma dai tace narkakkar dalma...
Da wani kalan gudun ceton rai da fitar numfashi take ƙoƙarin danne zuciyarta kamar koda yaushe wajan barin gangar jikinta, don wannan ɗin ba zata taɓa barin ya zama shi ne destiny ɗin ta ƙaddarar data yi wa rayuwarta dabaibayi wajen fitar ranta na karshe ba. Lokacin wajen ƙarfe sha ɗaya na dare ne, Amma har yanzu hawaye bai daina zubowa daga idanun Aysha'n ba,kamar yadda lokaci ke wucewa haka hawayenta ke ƙaruwa maimakon raguwa....
Shigowar umma ne hannunta ɗauke da baƙar ledar da Bappa ya bata ta kawo mata,zama tayi a gefen inda Aysha'n ke zaune har zuwa lokacin jaririyar ta kwance akan ƙafafunta data naɗe. A natse ta dafa kafaɗar Aysha'n ahankali saboda, wanda ya sata ɗagowa a sanyaye ta juyo tana kallon Umman da jajayen idanunta da suke rine sosai. Umman bata ce komai ba har na wani ɗan Lokaci tana kallon yarinyar nata. Kafin daga bisani ta furta.
"I know Aysha bana da kalmomin da zan baki baki wajen sanyaya zuciyarki a wannan lokacin!, Kamar yanda babu wanda zai iya kashe wutar da ke balbala acikin Rai da Ruhinki sabo da But trust me, I can imagine your pain akan kaina, amma kuma babbar gudun mawar da zan baki a matsayina na mahaifiya shi ne, kawai zance ki dage da haƙuri da kuma dannar zuciyarki da fawwalama ALLAH duka lamuranki. In sha ALLAHU Lokacin da baki tsammani ba, Zai sauya miki damuwarki zuwa farin ciki mara iyaka. Tamkar yadda yake juya dare i zuwa rana...
Se kuma ta ɗan dagata tare da kallar jaririyar data fara motsi alamar zata farka, ko dai zatayi kuka kana cikin wata irin muryan kwantar da hankali ta ci gaba da faɗin.
"AYSHA Ina son ki rungumi duka ƙaddarorinki da zuciya ɗaya, Ki bar komai ga ALLAH domin kuwa shike maganin kowacce irin damuwa, kana ki yawaita adda'a ga yaranki ALLAH ya tsare miki su daga dukkan min wani sharrin me sharri. Kana kuma ina son daga yau, daga wannan rana me kama da haka ki dena ɓata hawayenki akan tarin kaɗɗarori da ƙalubalanki. Domin kuwa ba'a ma ƙaddara kuka Aysha"
Hannuwan Umman ta kamo cikin nata tare da haɗe wa da fuskanta damalmalalliya, kana cikin muryan daya jigatu sosai ta kuma wahaltu da kuka ta shiga furta.
"Ummanmu bawai ƙaddara ko wa ni kaina nake ma kuka ba, wa goben zaratan yarana nake kokawa! Ina tsoro! Ina matuƙar tsoro Ummanmu, ina tsoron ƙaddarar da ba tasu ba ta afka musu. Ina tsoron abinda mahaifin su yake aikatama yaran wasu shi ma a aikatawa nasa yaran Ummanmu. Wannan ma mace ce Ummanmu!, Itama mace na haiba dan me bazan ji tsoro ba? Don me ba zan yi kukan tsoron ba Ummanmu nayi laifi Kenan, Umma har habaici ake min kan cewar yarana mata ne, ƙaddarar mahaifinsu kan iya afkuwa kansu a koda yaushe ina jin matuƙar tsoron hakan wallahi ³ Ummanmu..... Se kuma wani kalan kukan ɗaukar rai ya sake sarƙafe ranta tana rufa kanta a jikin mahaifiyar nata, ta jima Sosái tana kukan Umman na aikin buga bayanta a hankali. Kukan jinjirar ne ya dawo da ita hayyacinta wacce dama tun da tazo duniyar bata sha Maman taba, don data dosa mata take rufe bakin ta taƙi amsa. Ummance ta fara janye jikinta ana Aysha'n kafin ta ɗago mata yarinyar tana cewa ta gwada ta gani ko ALLAH ze sa ta amsa yanzun. Se dai yanzun ma taƙi amsa dan haka kawai ta kifeta akan ruwan cikinta wasu sabbin hawayen na ɓalle mata.....
*BY AMMEY LAYLERH ✍️💐*
_To fa ALLAH Sarki Rayuwa, lallai Hameed a cikin maza kai ka cika butulun butululun butulun ma kuwa_
_Ummih ƙaddarar me zafi ce wacce ba'a iya mata kuka se dai zuciya ta ƙone ta soye idan har baki kintsu ba Wllh_
_Hmmmmmmm HAMEED kenan, Madallah da amsar da AYSHA MUSTAPHA WAZEER, ta baka daidai da kai, hakan yakin daidai Hundred percent ma kuwa☑️_
_Fan's ku mu je zuwa yanzu ne asalin wasar ze fara faaaaa,💃💃💃💃💃 inji Ni! AMMEY LAYLERH da kuma AYSHA MUSTAPHA WAZEER_
08104493215
°༺ 🌏𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐🪐*࿐
𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚🤦
https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Official Mirrah💐
♡
Page 17&18
*End of Last free Page's 🤗*
# SingleAndThriving
# HeartToHeart
# UsAgainstTheWorld
# LoveWithoutLimits
# HiddenHeart
# GlowingAfterGoodbye
# Heartbroken
# CryItOut
# LoveHurts
# Heartbroken
✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫*
(J.W.A)
♡
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
★★
♡♡♡♡♡♡
Ɗauke kanta ummah tayi idanunta na taruwa da ruwan hawayen tausayin Aysha'n mara adadi da misali. "Aysha ki dena kukan nan dan ALLAH! Ban son ganin koda ɓacin raine kwance a fuskarki bare kuma hawaye" Muryan ta ce ta soma rawa da ƙoƙarin karyewa dan haka tayi shiru tana sake damƙe hannuwan Aysha'n dake cikin natan da
ƙarfi, Tana yin ƙasa da idanuwanta da suke neman cikowa da ruwan hawayen itama. Amma cikin son ta kwarara ma ƴar nata gwiwa ne ya sanya ta ɗan lumshe fararen idanuwanta tare da dedeta bugun zuciyar ta kafin a bayyane ta shiga furta. "Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir³ Ra rabbi inni magalubun fantasir³ la haula wala quwwati illa billahil aliyal azeem³, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" haka ta shiga ambata da Aysha'n ta kama tana nanatawa. Ajiyar zuciya me sanyi Umman ta ta sauƙe a Ahankali wata irin nutsuwar hakan duk su duka biyun na baybayesu suna jin hankulansu na dawowa jikinsu kusan tare, take Aysha taji kaso mafi rinjaye na dacin da zuciyarta ke mata na zabtarewa yana guduwa nashi wuri. Saboda da yadda adda'o'in da suka karanto ɗin suka ratsa ta sosai tare da zuciyarta.
"Ki sani! Babu wani abinda zai faru sai da izinin ALLAH mai girma, Aysha'n! idan wani lokaci mai tsanani da wahala ya zo a cikin rayuwarmu, kafin komai mu sani cewa ALLAH yana da manufa da dalili na zuwan wannan al'amarin dake tare damu, kuma mu tuna cewa na ɗan ƙanƙanin lokaci ne abin zai zo ya wuce, tamkar ba'a taɓa yin saba.
Idan kuma wannan jarrabawar ta kusantar da kai ga Allah maɗaukaki to lallai wannan babbar ni'ima ce ƙari ne na lada. Haƙiƙa ALLAH Masani ne ga akan komai da yake wakana a cikin rayuwarmu, bawai mantawa yake damu ba!, Idan kuwa mukayi addu'a kuma mu nuna haƙurinmu mai yawa a gareshi se muga ya bamu mafita da madafa cikin sauƙi....
Se kuma ta ɗan dakata tana sauƙe ijiyan zuciya kafin taci gaba da faɗin.
"Kin ga kenan kin tsaya domin jiran Mahaliccin ki, kina jiran IN SHA ALLAH ɗin ki ta zama Ma sha ALLAH, yanzu lokacinsa ne maɗaukakin Sarki A'ISHA ki jira ki ga irin girman cika alkawarinsa kan masu haƙuri da sanya yaƙinunsu akan sa, saura kaɗan ɗacin da ke cikin zuciyarki ya zama zuma In Sha ALLAHU Uwata!. Domin yana saurarenmu! yana sane dake kema kuma tabbas zai ba ki fiye da abinda kika roƙa daga gareshi shi ne kaɗai wanda zai ba ki fiye da abinda kike nema da tsammanin samu daga wani, ke dai abinda zance kaɗai shi ne kici gaba da tafiya ɗoɗar bisa hanyar shi In sha ALLAHU za ki ga biyan buƙatarki ko ba yanzun ba muddin zuciya da Ruhinki zasu ci gaba da jure kowanne irin ƙalubale me tafe da ƙaddara.....
Sake dakatawa Umman tayi tana
lanƙwashe yantsunta har sai da sukayi ƙara, sannan taci gaba da faɗin "Tabbas ni uwace maji ƙan ƴaƴanta A'isha, nasan abubuwa da yawa suna damunki a rayuwar gidan aurenki ina kau da kai nane a matsayina na mahaifiya me son ci gaban yaranta!,Shi yasa na kawar da kaina daga rayuwar aurenki, duk kuwa da irin ƙalubalen da kike samu saboda duk wata ƴa mace a duniya tana son kulawa daga wajen mijinta, tana kuma son ace miji yana sonta ya na kuma damuwa da duk lamuranta!, Da matuƙar ciwo da ƙona zuciya ace wata mace ce tazo sama ta ka ta rabaka da mijinka, ko da ace Mijin nan ba SO da ƘAUNAR sa kake ba tabbas hakan da matuƙar ciwo Sosái, ko kaima idan ka auna hakan a karan kanka kama kanka adalci kasan ba abu bane me kyau ka aikata ba. Sedai dama zuciyar ta tsiƙe Duniyar kawai ake nema bawai madauwamar ba!, ALLAH ze kare min ke a duk inda kika sa gaba Aishatu naaaa"
Kanta ta dago tare da kallon umman nata kafin cikin wata iriyar murya me rauni sosai ta shiga furta.
"Ummah dan Allah Yaya mace take ji daga sanda mijinta ya juya mata baya? Wanne irin zafi da radadi take ji dan Allah? Ko kuwa macen data gama gina mijinta sama ta ka Kuma wata tazo ta kwace mata shi? Umma wai kuwa sauran mata sun san irin daci da ciwon dake cikin hakan kuwa Ummanmu? ciwon da nakeji acikin zuciyata da ƙirjina yafi gaban bakina ya furta se dai nayi roƙo wa UBANGIJI maji ƙan bayinsa duk wacce tama wani irin hakan ya ALLAH ka hana mata sakewar zuciya da ruhi ta inda gashi dai mijin ta kama a hannu amma kuma zuciyarta ta rasa abinda ke mata daɗi ya nabiyyun Rahamati KHAIRAN, KHAIRAN, KHAIRAN, KHAIRAN IN SHA ALLAH......
Zazzabina da komai da nakeji na haɗiye take, zuwa lokacin lil girl ta koma bacci Umman kuma ganin na dena kukan ta fita bayan ta haɗa min ruwa me ɗumi tace na yi wanka nafi jin daɗin jikína kafin na kwanta. Hakan kuwa akayi na shiga banɗaki na sake wankan, na dawo saman bed cikin dabara ina tunanin baby'n da taki amsar Maman ta....
Yarana na kalla su huɗu kwance cikin kwanciyar hankali da nutsuwa se naji dama ni ce su bana da damuwar komai, Saurin kawar da kaina a kansu nayi bayan na musu adda'an bacci nasha teay ɗin kana na ɗauro alwala na kwanta ina sanya hannuna na dama na zagaye baby'n. A hankali nake jin bugun numfashin ta na fita da kyar a kuma slow. Danhaka na yanke shawarar gobe idan ALLAH ya kaimu da safe zan koma Hospital domin sake dubata, da haka wani wahaltaccen bacci yazo yayi awon gaba dani cike da tunanunika da mafarkai kala daban daban.
*Yesterday*
Around 11:15am
Daidai na shirya bayan nayi wanka Ummanmu tama baby Bappa ya ƙira yaya khaleel yace ya zo ya maidamu Hospital, dan har yanzun baby'n bata amshi Maman ba,11:35 kuwa na cika sega yaya khaleel ɗin nan ma ya shigo gidan. Seda suka gaisa da mutanen gidan kana yace na fito wanda zuwa lokacin baby'n ma har ta fara fidda wani kalan wahaltaccen numfashin da ko daɗin ji babu. Tare da little A'isha na tafi nabar sauran a gida. Koda muka isa asibitin kai tsaye Maternity room na nufa. Dr Asia Maleek da Dr Meerah (AMMEY LAYLERH) ne suka amshi baby'n da jikinta ya zuwa yanzun sammm babu kwari tayi wani lagwab² zama nayi akan center chier ɗin roun na wurin tare da lil A'isha da ta buga tagumi. Sun jima sosái ciki kafin Dr Meerah AMMEY LAYLERH ta fito jikinta sanya ye cike da tsananin tausayin baby'n dama uwar baby'n ta zauna gefe da inda nake zaune. Ɗañ dafa kafaɗana Dr Meerah tayi tare da Lumshe idanunta,kana a natse cikin yanayin da zan fi fahimtar komai, ko nace zanfi iya amsar koma wacce iriyar ƙaddara ko wata sabuwar jarabawar data sake fuskantoni ta buɗe bakinta tare da farawa da faɗin. "_Komai na rayuwar ɗan Adam na tafiya ne bisa tsari da kuma ƙudurar ubangiji, komai kaga ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin rubutun kundin ƙaddarar sane, Wala ƘADDARA me ƙyau ko akasin hakan. Se dai wasu masu iya magana sukan ce ita ƘADDARA abace mara tabbas nan dake takan iya sanjawa. Ita kuma yarda da ƙaddarar kanta me kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin cikakken Imanin ko wanne bawa! A'ISHA MUSTAPHA WAZEER, I'm so sorry da hakan zan fara baki haƙuri, My baby Uñhealthy of her mother is affected infant baby girl. And tun baby'n na cikin mahaifa ta kamu da MUMMUNAN CIWON ZUCIYA! Ya danganta ko hakan na da alaƙa da irin tsanani ko matsin rayuwar da kike fuskanta har hakan yayi affecting na baby'n dako duniyar bata zo. Sau tari hakan na faruwa idan matsalolin rayuwa suka ma mahaifiyar dake ɗauke da tsohon ciki wacce ƙuncin rayuwa ya sako gaba jaririn dake cikin cikinta na fuskantar baraza wa hakan. Baby'n tana cikin mawuyacin hali a yanzun ki mata du'a ke mahaifiyane amma dai baby'n na cikin haɗari sosái fiye da tunani....
Tun da Dr Meerah ta fara min maganar na nema hankali da tunanina na rasa, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un 😭 wannan ɗin wacce iriyar ƙaddararriyar masifar Rayuwar ce ke bibiye dani babu dare babu Rana?. Wani kalan bahagon kuka na fashe dashi jikina na wani kalan tsuma na tsananin tashin hankali na shiga furta.
"Ya ALLAH wanne kalan laifi na aikata a gareka ba tare da sani na da nake fuskantar Rayuwa daga wannan se waccen? Ya ALLAH na roƙeka da kyawawan sunayen ka tsarkaka ka indai Rayuwana bata da wani amfani nan gaba ka ɗauki Rayuwana kawai na huta da wannan ƙalubalen Rayuwar haka nan! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, I hate you Hameed Wallahi I hate you na tsake!!!, Na tsaneka Hameed duk kai ne sila kai ne sanadin faruwar komai. Ka rugaza rayuwata da mafarkina duk hakan be isa ba? Se ya shafa jaririyar ALLAH da bata san komai ba, amma tsantsan cin amana da rashin imaninka ze shafeta tun ma bata zo Duniyar ba wallah......
Rufe min bakin da Dr Meerah tayi ne ya sanya ni gaza ci gaba da maganata. Kanta ta girgiza min tana zare farin glas ɗin dake Idonta, gorar ruwan dake hannunta ta ɓalle ta miƙa min kafin ta faɗamin wasu maganganu masu gina jiki ta koma Maternity room ɗin. Tafiyarnta babu jimawa Yaya Khaleel ya shigo tare da tambayar ya ake ciki, kai tsaye na faɗin masa komai idanuna fall da ruwan hawaye, little A'ISHA kuma na jingine da hannuna ɗaya idanunta ya kaɗa yay jajir itama. A gabana ya doka ƙiran Hameed tare da faɗin masa jinjirarsa na Hospital da shi ne mutum na farko dayay sanadiyar lalacewar rayuwarta tun kamin tazo duniyar Idan ma ta rayu kenan. Ummanmu ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 12