Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 12
duk abinda yasa gaba!, Kusan ce zan iya ce dake duk wasu jirage da zaki kalla masu ɗauke da tambarin wannan tsuntsuwar ta *MIKIYA* to kuwa na shi ne mallakin sane A'isha kin ga kuwa kama wannan babban zakaran a hannunmu dole se da ke ne zaku buga domin duk wani fata da yaƙinina akan kune *𝙍𝙊𝙔𝘼𝙇 𝙆𝙄𝙉𝘿𝙉𝙀𝙎𝙎 * se dai a cikin Royal ɗin ma ke ce 𝙏𝘼 𝘿𝘼𝘽𝘼𝙉 𝘿𝙄𝙉 𝘾𝙄𝙆𝙄𝙉𝙎𝙐 kuma kece kwarin gwiwa ta *𝘼'𝙄𝙎𝙃𝘼 𝙈𝙐𝙎𝙏𝘼𝙋𝙃𝘼 𝙒𝘼𝙕𝙀𝙀𝙍* plssss 👏 kiyi abinda ya kamata na roƙeƙi domin cewar.......         Wani irin bugawa dummm naji zuciyana tayi ƙirjina na harbawa duk da bana da tabbacin cewar shi ɗin ne ko ba shi bane, amma dai ko me ne ne bana da buƙatar ci gaba da sauraren abinda bai shafeni ba. Dan haka kai tsaye na dakatar dashi kasancewar ni ba wani matsayi ko sanin shi ba Masoyin media bane ya sani dakatar da zancen haka nan ina cewa kawai shikenan.... Shiru yayi kasancewar ya rigada ya san koni wacece tsafff zan ce na fasa yana ci gaba da cikani da surutu akan mutumin da ban damu da nasan ko waye shi ba, directly na fita a office ɗin dan son nayi saurin tattara duk wasu tarkacena dake cikin office ɗin kafin zuwa lokacin da zan dawo bakin aikina bayan bikina kenan... Kammala aikina kenan wannan baƙar me nacin tsiyar nan Juliet ta sake dawowa da batun cewa md yace na zama a shirye da gashi nan zuwa.... "All right okay" Na Bata amsa ina me ci gaba da harhaɗa tambayoyin dana gama tsara masa da zanyi... ★ Gudu sosai bugaggun motocin suke akan shimfiɗeɗiyar kwaltar da zata sadaka da wannan rantsatstsen gidan jaridar namu na *𝙈𝘼𝙃𝘼𝙉𝙂𝘼𝙍 𝙕𝘼𝙈𝘼𝙉𝙄 𝙏𝙑 * duk inda suka gilma kuwa mutane basu hanyar wucewa suke, dubada da irin uban gudun da motocinsu keyi na tashin kai da tashin gari. dukkan hanyar da suka biyo kowanne mai abun ha wa  ƙoƙari yake ya basu hanyar wucewa kar a halakashi. Har wasu na Allah wadai da su wasu kuma na musu fatan shiriya ne kawai. Har zuwa lokacin da suka kawo cikin gidan jaridar ba tare da mamallakan motocin ma yasan da cewar sun iso ɗin ba har seda yaji motocin sun tsaya... Ahankali ya buɗe idanunshi jin motocin sun tsaya kafin ɗaya daga cikin tight securities ɗin dake zagaye da shi gaba da baya cikin su wani yay saurin buɗemai motar yayi da sauri, A wani kalan gadarance ya fara zubo farare tasss ɗin sawayensa da suke sanya cikin wani shegen Hermes Birkenstock sandal wadda a kalla kuɗin sa zai iya kaiwa $96000, kasan cewar takalmin launin baƙi ne sai yayiwa farar ƙafarsa bala'in kyau.... Kafin uban jikin ya bayyana inda yake sanye cikin wasu shegun suit sky blue wanda suka may wani irin shegen kyau na ban mamaki, Se wayar sa da kuma Ipad nashi dake riƙe a hannunsa yana tsaiwa kan diga digansa... Hannunsa ɗaya na ɗauke da wata rantsatstsiyar wriswacht samfurin ƙirar Delux. Har zuwa yatsar hannunsa me ɗauke da dogayen fararen farata dake sanye cikin wani zobe na ring diamond guda ɗaya mai ƙyau sosai a yatsar nashi... Wata zazzafar iska ya shaƙa yana soma bin parking space ɗin wajen da kallo dayaji flowers da kallon komai da yake looking neat a perfect kaman ba gidan jarida ba... wani soldier ne yay saurin ƙarasowa wurin da yake tsayen yana sanye da na soldier hannunsa riƙe da Ipad ƙirar apple. Cikin girmamawa ya sarama AJ ɗin da yake jingine da jikin motar yayi folding hannuwansa a saman ƙirjinsa. Cikin harshen nasara ya masa magana directly kuma suna nufar cikin tamfatsetsen gidan jaridar namu. Mutane ba da yawa bane suka rufa masa baya har zuwa cikin ainihin inda za'a gudanar da firar.mutum biyu na tare da shi ɗaya gefensa na hagu ɗaya kuma gefensa na dama, taku yake cikin irin na manyan jaruman nan wanda ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa kasan cewar shi ɗin cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma lafiyayye kakkarfa ne ke tinkaro ka. Fuskar nan a ɗin ke tsaff wanda idan me ƙaramin zuciya ya kalle shi nan take zuciyar zata iya bugawa ya mutu awajen saboda tsoron yadda fuskar 𝘼𝙅 ɗin tayi yau abun ba'a magana. Sabo da cewan yanayin da yake ciki a yau ɗin ya wuce tunanin duk wani mai tunani. sai tashin fitinannen kamshin yake kansa sanye cikin wata Black ɗin Luxury pcap ta Versace... Mutane biyu ne suka tsaya daga bakin ƙofar shiga inda za'a gudanar da firar,biyun kuwa na binsa har ciki bayan an nuna masa masauƙinsa yakai zaune kan sofar office ɗin zama irin na ɗora ƙafar nan ɗaya kan ɗaya yana kin amsa gaisuwar dasu md ke famar miƙa basa haka kuma yaƙi zare baƙin shade ɗin daya toshe idonsa dashi... Har zuwa sanda md a wannan karon yayi amfani da landline phone ɗin dake cikin office náshi zuws nawa office ɗin yana sanar min ni kawai ake jira.... Se da gabana ya sake bugu amma ina shanye hakan kasancewata mutum bame nuna rauninta akan kowanne abu ba. A natse na miƙe ina ɗaukar Samsung Galaxy note S7 tawa riƙe a hannuna.... Na fara tafiya cikin nutsuwana da kuma amsar bugun da ƙirjina keyi, A natse na sanya zaratan Chocolate hand nawa ina tura ƙofar Room ɗin.... Sassanyan ƙamshi da daban ɗin da naji wurin na mun ne ya sanya ni shaƙar numfashin da ban shirya masa ba ina haɗiye ƙamshin dana shaƙa har zuwa cikin cikina kana sauƙe ijiyan zuciya. Kafin na buɗe lumsassun idanuna kai tsaye suna sauƙa a kansa wanda yasa zuciyana kusan yin tsalle ta fito daga cikin ƙirjina ta faɗo ƙasa duk kuwa kasancewar bawai na ga koda ƙwayar idanunsa bace. Amma kai tsaye zuciyana ta gama sanar min da cewan shi ɗin ne, Tun daga sanda naji kaifafan Idanuwan sa na yawo a kaina yana ƙare ma ko ina na jikina kallo. "Ohhhh shittt! Ya ALLAH!!!" Na furta inajin zuciyana na ɗaukar zafi sosai game da bibiyar Rayuwana da wannan ɗan bala'in ke yi.... Gyaran muryan da md yamin ne ya dawo da zuciyana daga hutun wucin gafin data tafi... "Bismillahi A'isha ƙara so mana?" Wani kalan zazzafan numfashi na fesar ina ƙara sa shigowa a zafafe tare da zama kan study table mai makon mazauni nake fuskantar shi...... Kai tsaye cikin zafin zuciyar dake ɗibana akan sa da kuma son ya fita a cikin Rayuwana gaba ɗaya na saƙala Microphone ɗin da ake ƙoƙarin maƙala min, Ni na maƙala da kaina ina me farawa da furta... "Why? Dan me me yasa sau da tari wasu mutanen sukafi shishshji a inda ba'a da muradansu ba? Me yasa yanzu mutane suka fiye son cusa kansu inda basa da kwarjini ko ƙimar a Mu'amulance su ba? Me yasa marasa zuciya suka fi yawa a cikin wannan duniyar tamu ne?..... Nai maganar idanuna na cikowa da hawayen da ko ni bazance ga dalilunsuba.. tare kuma da furta "𝘼𝙎𝘼𝘼𝘿 𝙈𝘼𝙅𝙀𝙀𝘿 dan me yasa ba zaka fita daga cikin Rayuwar wannan baiwar ALLAH'R dake dap da zama mallakin wani saɓanin kai ɗin ka ba? Dan me ba zaka nesanta Rayuwarka da tawa Rayuwar ba? Ina son kayi nisan zangon da duk gudun ceton ran da zanyi na gaza cin maka inaso ka fita daga rayuwana na har abada abadan gaban abada ASAAD..... Wani lafiyayyen lalataccen Murmushi mara sautu ya saki yana zare shade ɗin dake rufe da fuskansa wanda tsananin kwarjin hakan yasa ni duƙar da kai na ƙasa ina gaza kallonsa...tamkar kuma daga sama naji sauƙar kalamansa wanda suka fi min ɗigar narkakkiyar dalma tsaƙiyar ƙirjina yana me furta.... "Mummunar ɗabi'arki na mugun hali yasa na janye daga gareki and Ina son ki fahimta wani abu waike wacce iriyar zuciya gareki ta dabbobi da bata son faɗin miki gaskiyar abinda kike so da kuma wanda baki so?" Yay maganar ne kyawawan fararen hannuwansa dake zube cikin aljihun tsadaddun suits ɗin dake sanye a jikinsa yana zare ɗaya, tare da ɗaukar glass cup na Pineapple energy drink ɗin dake ciki yana kaiwa bakinsa ya masa kurɓa ɗaya. Su kuwa securities biyun dake tare dashi sake gyara zaman bindugunsu suka sake yi a tsare cikin shirin kota kwanar karɓar umarni daga uban gidan nasu. Kafin ya fesar da wata zazzafar yana miƙewa tsaye tare da fara takawa yana nufo inda nake.... Babban yaronsa Dmail Micheal na take masa baya tamkar me masa jagora.... Cikin takun cikakken gwarzon namijin dake kan ganiyar taken samartakarsa yake takunsa cike da gwaninta yana sake tunkaro inda nake zaunen. Kaina ya ranƙwafo ta inda ni kaɗai ce zan iya jin duk abinda zai ce saidai Microphone ɗin dake sanye ga kowannenmu ya sanya maganar namu fita kai tsaye.... "Ashe keɗin kanki kin san cewa me arha CE haka ban sani ba tunda har zaki Iya shiga cikin ko wacce tarkacen shara right?" Cikin son na bugar da tashi zuciyar nima na saki nawa ƙayataccen murmushin daya ƙara ƙawata kyawun fuskana a karo na farko ina miƙewa tsayen daga runfar daya min... Sai kuma na ɗan taɓe bakina tare ta sakin wani murmushin takaici kafin cikin maganata ta kai tsaye ba tare da jin shakku ko tsoron komai ba, Tare da kallon cikin tsaƙiyar idonsa kai tsaye na shiga mayar masa da amsar sa da cewa. "Ai abu me tsada ne yake birge kowa koda kuwa mutum yasan bazai sama shi wannan abun ba, Amma duk da haka yakan Iya tsayawa yayi tayi duk da yasan zaren ba kalan yadin bane, amma ze so ya dandali arziƙi yakuma bar arziƙi a inda arzikin yake saboda farin jini halittane me tarin baiwa!. Wadda duk tsadar Abu se yana da farin jini yake birge kowanne halitta, just if u been a black stomach man ok tell me now but u are very amazing me for ur talked" nayi maganar da nasan dolen dole ta bugeshi tabbas.... Kenan saƙo na yakai inda nake son yakai ɗin... Shi kuwa Aj majeed tun da na fara motsa lips nawa ya zuba ya zuba min kyawawan idonsa, kafin kuma ya janye yana basarwa tare da sakin wani shegen murmushin nan nashi da mutane kema lakabi da na mugunta. Kafin ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan sduty table ɗin da nake zaune yake kana ya furta cewan... "Se dai kin yi kuskure ɗaya TASHA na zaɓama kanki mutumin da samm sammm 𝘽𝘼𝙆𝙄 𝘿𝘼 𝘾𝙀 𝘿𝘼 𝙎𝙃𝙄 𝘽𝘼 domin kuwa kin gefa kanki ramin daya kasance gaba kura ne baya kuma damisa ƴen Matana... A wani irin mugun fusace na furta "𝘽𝙖𝙣 𝙙𝙖 𝙘𝙚 𝙙𝙖𝙨𝙝𝙞 𝙗𝙖 𝙠𝙤𝙙𝙖𝙞 𝙗𝙖𝙣 𝙙𝙖 𝙘𝙚 𝙙𝙖 𝙠𝙖𝙞 𝙗𝙖?" Daga haka na sanya kaina ina raɓa shi na wuce ta gefensa harna wuce kuma na sake dawowa tare da sake furta.. "Again Remember ka sa ni ayau zaka ƙara tabbatarwa mutum crismatic ako' Ina na daban ne kuma yana da wuyar samuwa and ka rubuta ka ajje har gaban abada *AYSHA MUSTAPHA WAZEER* Ba taka bace domin nafi ƙarfin mutum In classical irinka. ina gama faɗin hakan na raɓa ta tsakanin mutanensa biyu masu riƙe da bindigu ina rufo musu ƙofar da karfin masifa.... Tun daga lokacin ban sake jin kome kama da sunan sa bane. A duk lokacin da zanyi kuka nakan tuna da maganganun sa daya ta min hannunka mai sanda sedai a lokacin giyar sosayyar ta gareni ta lulluɓe ganina da jinina... Haka aka yi bikinmu cikin farin ciki duk da kasancewan yanda media ta ɗauka a wancen lokacin na irin hazon da AJ MAJEED ɗin ya tayar ya kuma fuske yana tafiya tare da manta da abinda yay abunsa... Sosái akai shagalin bikinmu domin kuwa Aure akamin irin na ƴaƴan gata, Se dai matsala ta farko da aka fara samu ashe mahaifinsa Engineer Usman datti baya tare mahaifiyarsa a wancan lokacin kuma shi uban yana zaune a anan cikin Kanon ne. Inda kuma adai nan cikin families nasu yamin ginin a zimmar cewa daga baya zai ware min gidana daban. Duk a lokacin ban fa'inci komai ba dangane da hakan illa dai kawai ni aura min shi. To dai ganan an aure min ɗin haka aka tattara ni aka miƙani anguwar bello dake Kanon dabo..... Hannu bibbiyu tarɓa naga tarɓa ta musamman aka man a gidan inda naji hankali da nutsuwa na sun sake kwanciya da hakan domin dama ni bame son zama nesa da mutane bace dan ko babu komai jama'a ma Rahama ne aiiii.... A wannan daren soyayya kamm naga soyayya daga HAMEED USMAN DATTI domin a wannan daren ya maidani cikakkiyar macensa kuma mallakinsa...... *TUSHEN KOMAI* _To bazan ce komai ba kam anan sedai nace muje zuwa cikin labarin ɗin kai tsaye a page na gaba..._ _Ina My Royal FAN'S 💃🤸 nawa? Free page's ya kusan ƙarewa kuma wllh wannan tafiyar ta musamman ce kamar yanda komai yake daban da saura aha, Idan kuma kin rasa babu Ruwan AMMEY LAYLERH🤗_ _Shin me Aysha'n mu take nufi da TUSHEN KOMAI ɗin data faɗi?.... Shin wai ma yaya akai aka haihu a Ragayane???.. kun san dukan amsoshin suna ina?_ _TO duka waɗan nan amsoshin suna a kundin cikin littafin DUNIYARMU 🌏 Me cike da tarin ƙalubale..Hajiya karki bari ayi tafiyar nan babu ke, Kuzo ku mallaki naku domin jin abinda littafin zai zo muku da shi, domin kuwa ƙumshe yake da tarin abubuwa masu ban mamaki, da kuma sabon salo Zubi da tsari. Haɗi da Kitimurmurar kishiya da uwar miji. makirci, soyayya, cakwakiya, zamba cikin aminci, tare da ɗan karan munafunci daga ɓangarori daban daban...._ 08104493215 *AMMEY LAYLERH ✍️☑️💪* 🌏𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐🪐 𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚🤦 ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Official Mirrah💐 ♡ Page 9&10 ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *_𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭_* Best kayan kwalam 09025859622 or 09163353050 *END OF DISCUSSION PACKAGE* Now available in- candies package stop in and stock up on a sweet piece of summer! 🍬🍔🧆 𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭: ce ta shirya tsafff domin kawo muku. Samosa Spring rolls Filled doughnut Glazed doughnut Puff puff Shawarma Cupcake Birthday cake Bento cake Egg roll Milk cake Candy's Alewar madara Gullisuwa Tsami gaye Coconut laddo Milky gireba Albishir Mandula Sayen daya ko sari muna aikawa ko ina cikin aminci muna karɓar order bikin suna ko aure Location zamfara state ,gusau What's no :-09025859622 or 09163353050 Hajiya karki bari wannan garaɓasa ta wuceki domin taken mu shi ne 𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝘿𝙀𝙇𝙄𝙂𝙃𝙏 Koda kuɗinka seda Rabonka... Se kun zo ♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Bayan bikinmu da wata biyu na dawo masa da magana akan ina son ci gaba da aiki, nan ya ƙara jana da salo na yaudara kan cewar na bari na cikata 3 Months haka Mana. Haka na haƙura domin kasheni Sosái yake da zazzafar SOYAYYA'RSA gareni, sedai kafin 3 Months ɗin ma ta cikata na fara jinya wanda har ta kaimu ga zuwa asibiti. Awon farko kuwa likita ta tabbatar mana cewar ina ɗauke da ciki ɗan watanni biyu da sati ɗaya. Wato a daren da aka kaini idan lissafina ya bani dede na sama shigar wannan cikin. Cikin Amaan kenan haka muka dawo gida cike da wani irin tarin farin ciki ko kafin mu dawo har ya ƙira su Baba Matar mahaifinsa me irin sunana sedai muna kowa na kiranta da Baba ne... Koda muka dawo haka matan gidan suka dinga shigowa yimin sannu kasancewar tuni harmun saba dasu. Kuma ban fara kirki ba kullum matan mahaifin nasa dake biyu ne suke dafa abinci su bamu nida matar Yayansa Ahmad wacce nazo na tarar a gidan sedai a tun farko bata wani bani fuskar sakewa dan haka nima se ban wani cika nuna damuwa ko shiga cikin lamuranta ba. Wanda Mijina shike riƙe da gidan nasu domin akwai shi da son zumunci ammafa kafff gidan suna Masifar tsoronsa wanda ashe nima ma farko farko ne dan har mamaki nake yi idan naji har matan uban na tsoronsa. Sedai nima tafiyar bata wani yi nisa sosai ba ya fara bani Ruwan guma gumansa. Wato ashariya babu kalar wacce be iya ba idan kakuji yacce kai tsaye yake iya ambatar sunana yana furta...."Aysha zan** ci kaza kaza da uban*ki" abin yakan bani mamaki amma ganin kowa ba ƙyalewa yay ba ya sanya ni shafama kaina lafiya ina bin sahun masu kwantar da kan nima... Amma hakan baya taɓa soyayyar mu domin SO na hauka yake nuna min, Duk abinda ya gani daya danganci suturar jiki zuwa kayan ƙwalam yakan rarumo ya kawo min kuɗi kuwa bana da matsala dasu ko nawa ne kuwa. Sedai kuma ALLAH ya jarrabi wannan Ahalin gidan da wata mummunar mutuwar da tazo ta gitta tsakankanin farin cikin gidan zuwa aka sin sa wato mutuwar babban yayansu Malam Basheer Usman datti babban ɗa namiji a gidan duk da kasancewar ba uwa ɗaya ce ta haifesu amma suna Masifar ƙaunar junansu kuma suna da wani irin shegen haɗin kai bana wasa ba.... Sosai mutuwar ta girgiza kowa dake wannan Ahalin da yay accident ɗin mota daga Kano zuwa Kaduna.... Munyi kuka sosai da rashin babban mutum me kima a idon duniya wato babban yayansu Hameed wanda shi ne mutumin da yasa ake ma gidan kallon gidan mutanen mutumci mutane kuma na daban a cikin al'umma.... ALLAH Sarki Rayuwa shikenan fa ya mutu yabar yaransa biyu mace da namiji JURAIJ da kuma JANNAH ALLAH Sarki rayuwar kenan fa muma duk wataran na haka ne... Wanda tunda wannan mutuwar mahaifiyar Basheer ta koma wata abin tausayi domin kuwa abin a tausaya mata ce... Haka naci gaba da renon cikina cikin aminci har zuwa loƙacin da cikina ya shiga watan haihuwarsa... Inda a wani dare nakuɗar ta tasammin maza maza aka garzaya dani asibitin da nake zuwa awo... Nan aka amsheni cikin girmamawa anayin lebor room dani. Na ɗan sha wuya sosai kafin ALLAH ya sauƙe ni lafiya da kyakykyawan yarona Amaan... Tun da sauran safiya ƴan gidanmu da yayyena suka gama kammala cikin asibitin. Sha daya da rabi na safe aka bamu sallama kai tsaye Hameed na ɗibarmu zuwa gida. Ko kafin mu isa har an dafa ruwan zafi na wankan jego dan haka muna zuwa aka wuce dani toilet ɗaya daga cikin matan mahaifinsa na min wanka ɗaya kuma na wankar jaririn. Fessss na fito abuna tamkar ba haihuwar fari nayi ba haka mutanen anguwa da ƴan uwansa na kusa dana nesa suka dinga zuwa min barka... Har muka cikata sati guda ciffff da haihuwa Ranar suna Yaro na yaci sunan babban wan Hameed Basheer kenan wanda muke ƙiransa da Amaan amma kakansa da uwar Basheer ɗin sukan ƙira shi da MALAM... Haka A Ranar sunan duk dangin mahaifiyar Hameed dake Rano suka zo a ranar sunan ita kuma dama tana nan yau kwanakinta uku da zuwa... Manyan Raguna biyu aka yanka min haka dai akayi shagalin sunan duk da dai ba wani me yawa bane kasancewar har lokacin ana cikin alhinin mutuwar yaya Basheer ne.... Alhamdulillh anyi taron suna an watse lafiya daga nan muka ci gaba da wanka inda wata ƙanwar Bappa'nmu daga BAUCHI tazo min zaman wanka.... Sosai muke murmurewa nida jaririna Amaan inda mukayi arba'in cikin aminci na Ubangiji daga nan gwaggo Hadiza ta haɗa nata ya nata ta koma Bauchi cike da tarin uban Alkhairin da mutanen gidan suka mata shi kuwa uban gayyar ba'a magana.... Randa na cika wata uku da haihuwa Lokaci Amaan yayi wayonsa sosai na koma masa da maganar son kowama aiki na, nan yace shi baisan zance ba wllh babu inda zan fita aiki da Kula da baby na zanji ko kuma da fita aiki banda ayyukan gidan wanda nike yin abuna, wannan shi ne masomin komai domin kuwa na kafe kai da fata akan ni wllh sena koma gun aikina Kamar yanda shima ya kafe yace wllh ba zai barni ba aishi ba banzan namiji bane da zai bar matarshi haka kawai mutane na biye masa muryarta da kallar masa ita ba... Daga nan nayi yaji nayi tafiyana gidan mu naje na tsara duk abinda ake ciki, nan bappana yamin nasiha akan nabi komai na rayuwa a sannu domin komai ɗan haƙuri ne... Haka Ummanmu ma tamin faɗa da Nasihar sosai da dare yasa Mama da Ladiyo suka mayar dani wanda a hanya suka ta sake zugani kan cewar karna yarda a rabani da fata da kuma muradina wato aikina na jarida... Wanda nake ta sake haihuwa ban sani ba ashe fanfon iska suke min domin dai tuni Auren da nai a wurin Rufin asiri ke tsokale idonsu. Ganin yanda rai da rai kullum Alkhairina baya taɓa yankewa ga iyayen nawa wanda idan nay harda su ake laƙushe komai amma fa duk su hakan be musu ba...... Haka ko uban me na kawo Ummanmu bata da ƙyashin fito musu dashi su kasa suda yaransu duk kuwa da kasancewar suma sunfi ƙarfin abun. Koda aka medani ƙin mishi magana nayi har washe gari wasa wasa dai har seda muka kwashe kwanaki uku ban masa magana amma duk wani abin buƙatarsa ina basa tun da ga kamo kan ruwan wanka, abinci dadai duk sauran abubuwan fita haƙƙin mace akan mijinta nakan masa. A rana ta huɗun ne ya dawo daga kasuwa loƙacin ina zaune a parlour na nida Amaan Ina koya masa zama sedai fuskarnan babu annuri ko kaɗan domin wannan ba itace matsala ta farko dana fara fuskanta kawai ina ƙoƙarin danne hakan ne, domin kuwa na dade da fahimtar cewa Hameed nada shegen son mata kamar kamar me.... Da sallama ya shigo parlour'n hannunsa ɗauke da ledar da duk ze shigo seya shigo mana da ita, ɗauke kaina nayi ina masa sannu da zuwa zama yay gefena tare da raba ƙafafunsa biyu yana sanya ni tsakiyarsa kana ya ɗago kaina shi kuma yana kifo da nashi saman nawa.. Ido ya zuba min na tsawon minti biyu kafin cikin wani kalan kulawa da kuma tsantsan soyayyata gare shi ya furta min... "Murmushin ki yana da kyau sosái Ashsha!" Se kuma tay shiru cikin idanuwarsu na tara wasu abubuwa wanda sukafi kama da azabtuwa kana yaci gaba da furta... "Ka da ki bari koda da wasa ya ɓace daga wannan fuskar naki,yi murmushin mana pls Ashsha....." Yay maganar yana tura hannunsa cikin rigata ta saman wuyana zuwa cikin jikina yana min cakulkuli wanda hakan ya sani Yin murmushin hawaye kuma na zubo min duk a lokaci guda. Domin ba abu me girma yamin ba tsakankanin rabani da mafarkina da yay fa. Riƙe fuskar yayi yana kawo goshinsa dap da nawa shima yana murmushin me tafiya da zuciyana, murmushin naci gaba dayi kamar yanda hawayen be dena zubar min ba. A natse kuma ya haɗe gishinmu wuri guda yana saƙalo wuyana da hannunsa ɗaya yana ƙarasa haɗe bakinmu wanda na fashe da kuka ina ƙanƙame kansa kawai..... Tun daga nan ina ji ina gani haka buri da muradi na ke ci gaba damin nisa nisan daya nesantani da duk wani farin ciki nawa yana rabani da duk wasu kwalitis nawa.... Haka dole na jure komai ina fuskantar gidan aure na kawai wanda a kullum kwanan duniya abubuwa sake sanja min suke domin kuwa tuni daga nan cikin gidan da muke rayuwa ɗaiɗaiku daga cikin su haka kawai suka fara ɗora ma ransu ƙiyayyana me ƙarfin gaske mara hasali da tushe. A lokacin ne kuma ciki na biyu ya sake bayyana gareni wanda banso hakan ba sammm sedai niba me jayayya bace da

Chapter 5 of 12