Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 12
harda wacce tayi bayan tayi sallar magrib wacce wata iriyar adda'a ce me tsananin ƙarfin da Idan kayi ta nan take ALLAH yake kawo maka mafita. Bayan ta kammala wannan adda'ar ne ta cira hannunta sama idaniyarta na tsiyanyar da ruwan hawayen ta ce. "Ya ALLAH! Ya mujibud da'awati ya Rabbil alameen idan har ci gaba da zamana a cikin wannan gidan baya da amfani, to kuwa na roƙe ka da kyawawan sunayen ka akan ka kawo min ɗauki da mafita cikin sauƙi ba tare da naci gabata da cutuwa da wahaltuwa ba. Ko sauƙe hannunta batay ma sega Hameed ɗin nan kamar wanda aka je ho yazo kanta yana huci magana ba da yawa bace ko nace sa'in sar da sukay wanda sammm ita batayi tsammanin irin wannan abun bane ze faru da ita Hameed ɗin ya yanka mata saki ɗaɗɗai har biyu kan yaran ƴar kishiyarta Hafsa da sukayi faɗa da ashman. Duk uwa duk Rintse ita uwace ta dake son ta ginu akan ginshiƙi da kuma tarbiyan yaranta. Se dai kashhh ashe bata da Wannan Rabon wannan adda'ar da tayi take ALLAH ya bata sakamakon ta, domin kuwa ci gaba da zama da Hameed shi ne babbar halaka da dana sanin Rayuwar da zata tayi har ƙarshen Rayuwarta... Wata gajiyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe mara sauti ko kaɗan tana ci gaba da adda'ar da idan wani mahaluki ya yita Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce da za'a yaye maka shijjabin dake tsakanin sama ta bakwai zuwa ƙasa da se kalla mala'ikun da suka miƙe domin kawo maka ɗauki ko sassaucin dake cikin Rayuwarka. Wannan mala'ikun wannan yana shi ne wanda zai ceceka wannan ma yana shi ne zai je domin kuwa jiga jigan sunayen ALLAH'n da ka ambata da irin neman ɗaukin da kake yi cikin gaggawa. _YA WADUD_ _YA ZAL'ARSHIL MAJID_ _YA FU'ALILLUMA YURID_ _AS ALUKA BI'IZZIKALLAZI LA YURAM_ _WA MULKIKALLAZI LA YUDAM_ _WA NURI WAJ HIKALLAZI MALA ALKANA ARSHIM LAJJINI MIN HAZAL MUJIRIM_ Ko da ta kammala adda'o'in nata kasa tashi daga kan prayer mat ɗin tayi domin jikinta da duk ya sake yin sanyi tana tunanin irin Ƙaddarar da Rayuwa ta zaɓa mata a wannan karon. samm bata ji zatayi jayayya da abinda ALLAH ya ƙadarta mata ba sedai tana jin zafi da raɗaɗin duk abubuwan da suka faru da Rayuwarta tun daga lokacin da Hafsa ta shigo cikin rayuwar Auren su............ Ta jima tana saƙe-saƙe a cikin Rai da Ruhinta idan kuma tayi duba ta wani fannin ma hakan kamar Alkhairi ne gareta da ALLAH ya tsame ta daga cikin gurɓatacciyar badaƙalar Rayuwar da ake aikata a cikin gidan auren nata, Domin halaka ce take gani ƙiri da ƙiri Mijin nata na aykatawa a ɓoye da ƙanwar matar tasa amma fa a nasa ganin. Domin tuni ita ALLAH ya jima da fahimtar da ita sedai babu yacce ta iya haka kuma babu yanda zatayi. Ban da shegen kule kulen ƴan mata a cikin sa ƙamar ɗan busuru, domin kuwa ko bunsuru ya shafawa Hameed ɗin lafiya. A takaice dai baya iyaka kule kule ya ƙare ba harda neman matan banza na waje Saboda da kawai yana da kuɗi yana sakar musu nera.... Shigowar Ummah ɗauke da kwanon abinci ne ya dakatar da ita. Lallashinta tayi ta samu da ƙyar taci abincin bada yawa ba kana tace taje inji Baffansu. Shima Nasihar ya mata Sosái tare da faɗa mata ai har Mahaifin Hameed ɗin ma yazo Engineer Umsan datti kenan. Batayi murna ko jin daɗin hakan ba sedai a ranta ta kuɗiri In Sha ALLAHU ita da gidan Hameed har ƙarshen duniya. Don shi kuskure sau ɗaya ake aikata shi kuma shi ya rigada ya gama aikata nashin. Tare da sumayya suka kwanta a daƙin dake kusa dana Umman nasu. Tun tana hawaye har hawayen suka zo suka ƙafe se idaniyarta dake sake soye mata zuciyarta na sake ɗaukar ɗumi da irin ɗacin da take ciki... ★ Can kuwa Ɓangaren Hameed bayan ya dawo gidan se yaga gidan ya masa wani irin mummunan duhun da shi kaɗai kawai yake iya kalla, bayan uban streetlight ɗin dake zagaye da gidan na hasken sola. Shi kaɗai yaji zuciyarsa na wani kalan tafarfasa da jin zafin kanshi Amma kuma wata zuciyar na kallon tabbas daidai ya aykata ga AYSHA 'n domin ai Rena mishi wayo ta so yi koma yace tayi dan haka yaja wani uban tsuki daidai nan cokalkalar matarsa Ummi ke shigowa. Zama tayi dap dashi tare da kwantawa a jikinsa cike da barikanci take may maganan yayi haƙuri wai kar yasa damuwar komai a Ransa. Dake dama in akace komai akai da jaki se yaci kara nan ya biye mata suka shirirince abinsu. Bayan tayi bacci ya ɗauki wayarsa yana hawa Online tare dama Baby ƙabwarta da dake riƙo magana. Farko pisc na emog ta fara turo masa alamar tayi fushi. Kafin ya mata Voice dogo me ɗan tsayi nan ma taƙi bashi amsar shi. Tashi yay jikinsa har na haɗawa da rawa ya sauƙo ƙasa kasancewar dama ba yau ya saba hakan ba. Kai tsaye ɗakin ummin ya nufa inda baby ke ciki kwance, ita kuma ummin ya baro ta can upstairs nashi. Tura ɗakin yay daga shi se boxer da best...... Yana shiga ya kamo ummin tare da kwantar da ita jikin sa yana ɗago kanta ya haɗe bakinsu wuri guda tare da soma lalubarta. Sun jima haka kafin daga bisani ta janye jikinta domin gudun kar ɗaya daga cikin yaran su farka ko ita ummin ta farka taga baya nan ta biyo sahu. Sallama sukai yana tafiya bayan ya bata 20k yace ta kara kan jarin seda babykit da dake yi a gidan.... 🤗🤗 _To ya kuka ji salon labarin ya fita ko kuwa da gyara dai?..._ _Fatar dai ya nishaɗantar da Masoya Mabiyan AMMEY LAYLERH 💐💋?_ _Ya salon labarin ze tafi?, Shin Aysha zata koma gidan Hameed uban ƴaƴanta har huɗu ga cikin na biyar haihuwa yau ko gobe ko kuma yaya?_ _Bafa mu ce komi ba domin ko alƙalamina ban dasa ba wannan kawai somin taɓi ne daga cikin labarin, domin kuwa tafiyar me ɗan saho ce_ _Shin zakuci gaba da bin alƙalamin AMMEY LAYLERH ✍️ domin ci gaba muku da wannan zazzafan LITTAFIN me cike da ƙalubale da ƙaddarorin Rayuwa?_ _Idan mun shirya let me gooooo kawai guy's🤸🤸💃💃💐 Shagaliiiiiiii_ *AMMEY LAYLERH ✍️☑️* 08104493215 🌏𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐🪐 𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚🤦 https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Official Mirrah💐 ♡ Page 3&4 _Dedicated to My Oummu Naaaaa 💐💐💘 and My Mommah Naaaaaaa ♥️♥️💘 UBANGIJI yama Rayuwa Albarka_ *THE WRITER'S OF* _KAREN BANA_ _MIKIYA_ _ƘAUNA BIYU_ _JALAAL AREEF_ _TA DABAN_ _ongoing DUHU na DUKAN duhu And DUNIYARMU 🌏_ ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *_𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭_* Best kayan kwalam 09025859622 or 09163353050 *END OF DISCUSSION PACKAGE* Now available in- candies package stop in and stock up on a sweet piece of summer! 🍬🍔🧆 𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭: ce ta shirya tsafff domin kawo muku. Samosa Spring rolls Filled doughnut Glazed doughnut Puff puff Shawarma Cupcake Birthday cake Bento cake Egg roll Milk cake Candy's Alewar madara Gullisuwa Tsami gaye Coconut laddo Milky gireba Albishir Mandula Sayen daya ko sari muna aikawa ko ina cikin aminci muna karɓar order bikin suna ko aure Location zamfara state ,gusau What's no :-09025859622 or 09163353050 Hajiya karki bari wannan garaɓasa ta wuceki domin taken mu shi ne 𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝘿𝙀𝙇𝙄𝙂𝙃𝙏 Koda kuɗinka seda Rabonka... Se kun zo ♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Ko a washe garin ranar ma Aysha da wani irin mutuwar jiki ta tashi dan se wajajen sha ɗaya ta farka bayan tayi sallar asuba. Ko da ta farka ta tarar yaran har Sun tafi school ita kuma jajila na wurin sumayya a goye duk da kasancewar ta wuce goyen kuwa dan wajen shekararnta 3. Fita tayi bayan ta ɗan watsa ruwa a jikinta kai tsaye tana nufar cann farfajiyar barandar gidansu. Inda iyayensu mata kafff suke ayyukansa acan da aka ware musu runfar girki. Tun da ta doso wurin taji yadda idanun matan mahaifin nata biyu suke a kanta domin kuwa basu da labarin abinda ke faruwa a gidan. Su dai sunga duka yaran a gidan wanda dama lokaci zuwa lokaci sukan zo gidan su kwana. Babban mayafin dake jikinta ta sake janwo shi zuwa katon cikin da anan ne tafi jin idanun nasu akai. Ummanta kuwa tana daga can cikin rumfar girkin kasancewar ita ce da gidan su kuma suna daga wajen ne suna wanke² In wannan ta saɓa se ta bawa wannan haka suke, ko nace haka ƙa'idar me gidan take. Wacce ke ɗakinsa itane zatayi girki da su kuma sauran matan ɗaya tayi wanke wanke ɗaya tayi shara... So se duk Ranar girkin Umman suke haɗuwa suyi shara da wanke² tare. Idan kuma ba na Umman bane basayi tare sedai abar Umman da wanke² ita kuma sammm sammm bata taɓa damuwa da hakan... Tun da dai yau babu matar da acikin su zata ma ƙazafin cewa suna mata ba daidai ba se dai ɗan banzan munafincin tsiya, ita kuma babu ruwanta da munafincin su tun dai ai ba zaginta akai ba ba kuma a gaban Idonta ake munafincin nata ba. Mama ce da shegen son gulma da munafircin dake cin ta ta washe baki tare da karkaɗe hannunta daga cikin ruwan tana me furta. "A ahhhh Me sunan Hajiya yau kuma zuwan sassafe aka mana ne?" Tayi maganar murmushi kwance saman fuskarta. Wani murmushin da aka ce yafi kuka ciwo ta ƙalalo tana mata tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da hannuwanta biyun ta ce. "A ahhh Wllh Mama anan na kwana ma ai!" Ɗan ja baya tayi tare da furta "Innalillahi to ALLAH yasa lafiya dai?" Dan a tunaninta ko yaji tayo duk da kasancewar yajin ba ɗabi'ar Aysha'n bace. Kuma ko su matan zasu iya rantsewa sau ɗaya Aysha'n ta taɓa yin yaji tsawon shekaru goma sha biyar cifff da aurenta.... Fitowar Ummah hannunta ɗauke da tea plask ɗin Baffansu ne ya bada damar zamewa tana gaida Umman kafin matan uban. Wanke wanken take shirin amsa Ladiyo tayi saurin dakatar da ita da faɗin. "A Ahhhh haba me sunan manya ta shi bar shi taya zan baki wanke wanke haka je ki huta" Ajiyar zuciya nannauya ta sauƙe tana juyawa tabar wurin tana nufar balconyn da tasan cewar bappansu na can. Acan ɗin kuwa ta tadda shi loƙacin Ummah na haɗa mishi zazzafan shayin daya gama jin kayan ƙamshi sosái. Ƙoƙarin kai wa zaune take kan carpet cleaning ɗin dake malale wurin yay saurin dakatar da ita. Nuni ya mata da plastic chairs ɗin dake gefe da inda yake zaune.. Zaman tayi kafin a hankali cikin nutsuwa sosái da kuma muryan da ɗaci da ciwo suka gama samun gurbi ciki ta furta. "Barka da safiya bappah!" Hankalinsa kachokamm y dawo dashi kanta cike da wani matsanancin tausayi da kuma son da yake mata na daban kan duk sauran yaran se dai yakan danne hakan ya buɗi baki a tsane murya cike da dattijan taka ya face da ita. "Barka mun tashi lafiya Hajiya tarh?" Ɗan sake sunkuyar da kanta tayi tare da furta. "Lafiya Alhamdulillh bappah" ta amsa idanunta na cikowa da wani ruwan hawayen da taji haka kawai na nemar gangaro mata. Kanta Bappa'n ya ɗago sama tare da sanya hannunsa yana sha re mata hawayen da suka zuba mata tare da furta. "Ki yi haƙuri Ayshatu komai ki ka ga ya samu bawa to dama cann hakan ki ƙaddara tsarin ALLAH ne!, Kuma ALLAH baya taɓa ɗora ma bawansa abinda yasan yafi karfinsa. Se dan sanin da yayi wannan bawan daya jabarta ɗin yana da ƙarfin zuciyar ɗaukar abinda ya ƙaddara masa. Idan kika yi hakuri to kuwa Tabbas za kiga ribar hakan, domin duk wani ƙarshen Haƙuri Nasara ce. Kamar yadda duk wani Ƙarshen Wahala Ɗaukaka ce,haka duk wani Ƙarshen Jarabta Darajace, Idan kikay haƙuri se kiga rungumi wannan ƙaddara da hannu bibbiyu se ki ga Ubangiji ALLAH yayi miki Abinda bakiyi zata ko tsammata ba. Ta shi kije Ubangiji ya miki Albarka ALLAH ya zama gatanki duniya da Lahira ALLAH yasa bakin wahalar kenan ALLAH yaci gaba da shiga cikin dukkan lamuranki Albarkachin Annabi Muhammad ( S. A .W) Ameen Yaa Hayyu Yaa Kayyumu. Jikinta ne ya soma rawa idanunta na sake cika da ruwan hawaye wanda har launinsu na sanjawa suna rikiɗewa daga fararensu su koma jajaye, wanda suke bayyana tsantsar ɗaci da kuma mikin dake bisne cikin Rai da Ruhinta. Kallo ɗaya zaka mata kai tsaye ka hango tsantsar tashin hankali da kuma damuwar da ke binne a cikin tsakiyar ƙirjinta. Kanta ta ɗago idanunta na zubar da hawayen data kasa riƙe su zuciya da kalamanta na rawa alamar cewa zuciyar nata na tafarfasa ne da wani nau in ciwo da kuma zafi maraisalta. Cikin sautin kuka Sosái ta furta "Wannan shi ne sakamakon da Hameed zemin kenan bappah?, Ina yakai yardar da nake masa? Shin ina Wannan tarin SO da ƙaunar da yake min? Ashe na chanchanta hukunci har haka daga gareshi kenan bappah? Saki na fa ya...y..yi.... Bappah yanzu shikenan Hameed hukuncin da ya yanke a kaina shi ne yake ganin ya fi dacewa?. Da ciwo amma babu komai In Sha ALLAH na amshi wannan ƙaddarar da hannu bibbiyu bappah!!!" Ta kai ƙarshen maganar wani hawayen na sake tsinke mata ya wanko fuskarta. Muryar Bappa'n nata ta sake tsinta yana me sake cewa... "Tsantsar mai Imani shi ne wanda yayi hakuri da juriya da bin duk dokokin ubangiji maɗaukakin sarki ya gindaya mar. Na biyu kuma shi ne amsar ƙaddrarsa da hannu bibbiyu Idan har bawan da ALLAH zai jarabceshi da wani giɓi daga cikin rayuwa kuma yay haƙuri ya cinye wannan ƙaddarar to kuwa In sha ALLAH ko ba anan ba ze Amshi kyakkyawan sakamako mafi kyawu daga gare shi wannan faɗar ALLAH ce.... "Ina sha ALLAH Bappah..... Sai ta kasa ƙara sa maganan tana tashi ta juya ta bar wurin da sauri. Tana jin yanda ɗan cikin ta ke mata motsi kafar ya faso cikin ya fito wannan DUNIYAR tamu, Me cike da tarin ƙalubale iri da kala. Cikin ta shafa tare da ɗauke wata guntuwar ƙwalla a kwarmin Idonta tare da cewa. "Kayi/ko/kiyi haƙuri da duk irin ƙalubalen da zaka/zaki tarar a cikin WANNAN DUNIYAR tamu me cike da son kai!" Tayi maganar tana ci gaba da tafiya jikinta ba ƙarfi ko kaɗan haka take haɗa hanya. Wani irin ciwon lokaci ɗaya me taji ya taso mata marar na mata wani irin dunƙulewa wuri guda. Tana jin sanda cikin ya tattare yayo ƙasan mararta da ƙarfin bala'i da masifar daya sanya ta durƙushewa a wurin tana ambaton sunan ALLAH. Wani kalan yanka da karta taji marar nata ya sake mata wanda wani gumi ne ma zamu ce ko ruwa taji yana silalowa daga tsaƙiyar kanta ya gangangaro yana zubowa ta cikin wuyanta. Da wani kalan karfin da bata taɓa sanin tana da ba ta ɗamki bishiyar umbrella'r dake wurin tare da ambatar "YA WADUD" ɗin da seda ya amsa ilahirin wurin wanda ya sanya Ummah fara nufota hankali tashe. Cumota zuwa jikinta Umman tayi daidai nan babban su na ƙarasowa hannunsa ɗauke da key na ƙaramar motarsa. Dake har zuwa lokacin su Mama da Inna Ladiyo na farfajiyar suna ayyukan su ne yasu suma yowa wurin hankali tashe. Taimaka mata suke ƙoƙarin yi su cira Aysha'n amma duk sun gaza kuma daidai nan babban yayansu khaleel ya shigo gidan. Saurin Parking na Motarsa yay ganin hadda mahaifinsu tsaye a wurin. "Yawwa khaleel i maza taimaka kasa mana Hajiya a mota ka miƙa ta asibiti haihuwa ce" "Toh Bappah!" Ya amsa shi yana kinkimar Aysha'n yay wurin Motarsa da ita Mama tayi saurin rufa masa baya tana zarar himar nata akan igiyar dake farfajiyar gidan da suke shanya idan sunyi wanki... Kai tsaye wata haɗaɗɗiyar Communitty Health clinic ya nufa da ita. Cikin gaggawa nurse mata suka amsheta suna yin lebor room da ita, Taimakon gaggawa suka shiga bata ganin haihuwar ce tazo gadan gadan amma kuma an sama matsala irin haihuwar nan da ake ƙira dire zatayi. Ƙafafun a ƙasa kan kuma ya koma can sama dan haka wata nurse ta nufo wurinsu tana sharce zuba tare da tambayar Mijin patiend ɗin. Dake kowa baya da labarin abinda ya faru har zuwa lokacin ne ya saka yaya khaleel zaro wayarsa ya saka ƙiran Hameed ɗin dake abokin sa ne. Kai tsaye ya ƙira sa amma sau biyu tana shiga yana yanke ƙiran... Dan haka yasa ka khaleel ɗin yay ma wayar wani irin damƙe zuciyarsa najin kamar zata baro ƙirjinsa saboda ganin katse masa wayar ne Hameed ɗin keyi. Wayar ya ƙurawa ido yana sake saka ƙiran Hameed ɗin a karo na babu adadi. Ci gaba yayi da ƙiransa idanuwansa ko gani ba suyi sosai hakama hankalinsa da zuciyarsa duk basa aiki daidai kawai nurse's dake ta faman zaryar ganin ko mijin nata ya ƙara so. Ko ita kanta Maman da kanta Se da hankalin ta ya tashi ganin Hameed ɗin bay ɗaga wayar.Shiru tsit suka yi kwata kwata babu motsi ko hayaniyar mutane a bangaren da aka shiga da Aysha'n in banda zarya da Likitocin ke famar yi... Hannun yaya khaleel har rawa yake cikin tashin hankali yake ta sake saka ƙiran Hameed ɗin kamar wani zararre. Rintse idanuwansa yayi yana Addu'ar ALLAH ya kawo musu mafita. Domin samm mantawa ma yayi da ƙiran bappansu. Dan haka kai tsaye daga ƙarshe ya tura masa test messages kan cewa Aysha ce zata haihu ana buƙatar saka hannunsa za'a mata cs, hakan kuma sai yay daidai da isowar Bappah asibitin dan haka ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya yana nufar bappan nasu tare da masa bayanin komi. Jin abinda ke faruwa da ƙiran da khaleel ɗin yama Hameed ɗin yasa Bappah amsar takardar yana saka nashi hannun. Nurse's biyu ne a kanta kuma sune zasu mata aikin dan haka suka sanya mata kayan yin aiki suna shiga aikin ransu fall cike da roƙon ALLAH ya basu nasara.... Basu ɗauka wani lokaci me tsayi ba sukayi nasarar fito mata da baby boy. Sedai daidai da cire baby'n a cikin ta daidai da lokacin da tayi wani irin haɗiyar zuciya numfashin ta ya fice a guje daga gangar jikinta yana barinta yana mata bye-bye da duniya. Dan haka a mugun sanyaye da tashin hankali suka fito nurse's ɗaya ɗauke da kyakykyawan baby boy ɗin dake naɗe cikin baby showel irin na ɗaukar jarirai. Zuwa lokacin kuma Ummah tazo duk dai bata so zuwar ba amma Bappah yace da ita kawai su taho ita da Inna Ladiyo.dan haka suka biyo napep suka zo asibitin da ya musu kwatancin shima. Farar duguwar nurse ɗin ce ta nufo inda suke zaunen kai tsaye baby'n rungume a ƙirjinta. Kai tsaye ta miƙawa yaya khaleel baby'n wanda ya miƙa hannuwan sa yana karɓar baby'n cikin wani irin farin cikin da yake jin kansa ciki yana ƙoƙarin amsar baby'n Muryar nurse ɗin wacce take tafe da bayyanar da ɗaci da kuma sanyi duk a lokaci guda domin itama uwa ce tasan zafin haihuwa kamar yanda tasan zafin Rashin wani giɓi na cikin rayuwa tunda ta rasa uba tun tana ƙaramar ta, kana tazo ta rasa uwar data reneta bayan gwagwarmayar Rayuwa da suka sha. Kai tsaye ta fuɗi baki tare da faɗin. "Anyi nasarar cire mata baby'n cikin ƙoshin lafiya sedai ALLAH ya amshi ran Uwar babu!!!" tayi maganar ne kuma tana ɗauke kwallar data cika idanunta. Sakin abinda dama ba wai gama amsar shi yayi ba yaya khaleel ɗin yayi cikin mummunan shock ɗin da bai ma san yayi hakan ba. Nurse ɗin ce tayi saurin zubewa ƙasa ta tare babyn a hannuwanta cikin wani kalan tashin hankali Sosái. Wani kalan mugun bushashshen yawu Umma take ƙoƙarin haɗiyewa amma ya kasa wuce wa se ma yankar mata zuciya da maƙoshi kawai da yake yi wanda take jin kamar anasa wuƙa ne ana yankar mata zuciyar ne haka take ji. Se take jin kamar a mafarki tamkar a mafarki ne hakan ke faruwa dan haka ta shiga bin kowa dake wurin da ido dan ganin reactions na kowa ɗin kuwa, haka harta tsayar da idanuwanta akan Bappah da ke tsaye shi ba mutum ba shi ba butum butumi ba. Hakan yasa da ƙyar ta bakinta tana kallar nurse ɗin dake ɗauke da baby'n tana me cewa. "Me ne kika ce ma? an sauƙa lafiya ko? Maman baby'n faaaa???" Ta furta hannuwan ta da jikinta na soma wata rawar tashin hankalin da bata taɓa riskar kanta ba.... Numfashi me zafin gaske nurse ɗin ta sauƙe tana kallan Umman da jikinta ke wani kalan rawar tashin hankali. Wanda tambayar da Umman tay ne ya sanya Bappah ɗago kansa yana zubawa Umman idanuwansa da suke a mugun firgice ya kalleta yana son jin amsar tamyar likitar daga bakinta shima. Sunkuyar da kai nurse ɗin tayi tana kasa kallan idanuwansu da suka zuba mata ta buɗe baki kenan da niyar basu amsa wata nurse ta yo wajen a guje tana me furta... "Pls Help me know when you're ready patient and bata mutu ba tana numfashi!, Numfashin ta ya dawo SO muna da buƙatar taimakon ki Asia Maleek" Ai jikinta na wani shegen rawa ta zuba a guje baby'n ɗauke a hannunta tana yin ɗakin tiyatr Directly.. Taimakon gaggawa suka shiga bata wanda cikin Iko na Ubangiji yasa cikin ƙanƙanin lokaci ta farfaɗo. *Araund 2:15* Ahankali ta shiga buɗe lumsassun Idanunta da suka gama jigata. Se kuma tayi saurin Rintse su sakamakon hasken daya dake su da kuma Raɗaɗin da suke mata. Kukan baby'n shi ya sake tilasta mata sake yin ƙurin sake buɗe idanun adda'a ɗauke da bakinta. *AS ALUKA BI'IZZIKALLAZI LA YURAM, WA MULKIKALLAZI LA YUDAM YA ARRAHAMAN RAHEEMIN! YA HADIY YA SALAM!!"* Tayi adda'an ne idanunta na buɗe wa tarwar akan kyakkyawan baby'n da yazo duniyar yayinda take a bay bay bawai a dade ɗin ta ba. Domin kuwa yanzu abubuwa sun mata yawa cinkushe cikin ta yake da tarin Cin Amana, zamba cikin aminci,ha'intar kai da kai. Yayinda Amana tayi ƙaranci yarda kuma takau, kowa ya ɗuka yana tafiya a kife kansa kawai ya sani.... Cikin wani irin mugun nauyin da bakinta ya mata tare da ɗaya hannunta ɗaya ta ɗora kan face na baby'n ta na me furta. *"YA ZAL'ARSHIL MAJID, YA FU'ALILLUMA YURID! Malukul mulku zuljalali wal eekram k zama gata da kuma katanga da garkuwa ga wannan abin da bai riga yasan komai ba cikin wannan duniyar. Barka da shigowa sabuwar DUNIYARMU be tarin ban al'ajabi kala da iri Al-Ameen..."* Ta karashe maganar wasu hawaye Masu zafin gaske na zubo mata. Banda ajiyar zuciya babu abinda take sauƙewa akai akai, Tare da zubawa jariri sabuwar haihuwan dake gabanta nan

Chapter 2 of 12