wannan garaɓasa ta wuceki domin taken mu shi ne 𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝘿𝙀𝙇𝙄𝙂𝙃𝙏 Koda kuɗinka seda Rabonka...
Se kun zo
♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Domin ALLAH da kanshi yace kamata yay ace dukkan wata alaƙa ta kasance tamkar ta hannaye da Idanu.
Idan hannaye su ka ji ciwo idanu su zub da hawaye idan kuma idanu suka zub da hawaye hannaye su sha re Wannan hawayen, dan me yasa ni bazan ma nawa uban ƴaƴan adda'an shirya ba. Yeah domin sosái har yanzun nake Son miji na Hameed domin soyayyar ita ce farkon abinda ya fara motsa zuciya da Ruhina.
Dan haka nakanyi ƙoƙari wajen shanye duk wani abu da nake fuskanta a cikin gidana da akazo aka fini matsayi da ƙarfin iko ta ƙarfin tuwo. Yanayi harya kaimu nida Hameed mun koma tamkar wasu maƙiyan juna, a daidai lokacin ne na na sake yunƙurowa da ƙarfin adda'a Sosái ba dare ba Rana har ALLAH Ubangiji ya kawo min sassaucin komai. Duk yanda kuke tunani ko nace da ku nake tunanin ummih to kuwa ta zarce hakan domin ita kanta wata iriyar baƙar sheɗaniyace ta musamman.
A ɓangare guda kuma game da sauran dangi dama alhali duka ta gama maimayesu da tarin kyautattukanta na banza, se kace da ni ɗin miye banwa dangin mijin ba. Sedai kunsan ance dangin miji ba'a taɓa iya musu zaka shekara dubu ne kana kyautatamusu amma na rana ɗaya kawai idan ka gaza duk wannan tarin shekarun da kai kana kyautatamusun sun tashi a banza ne a tutar wofi shi ne taken dangin miji... Domin kuwa kusan kowa zan iya cewa yana da wannan ciwon ba wa ni kaɗai na ba. Kowa se ya koma na ummih ciki kuwa harda manyan matan abokai wanda ada muke tare dasu sosái se dai da akace a wannan zamanin amana tayi ƙaranci,yarda kuma tayi wuya tabbas haka wannan batun yake ba hasashe bane na ƴan lissafi. Bilkisu kuwa dama tuni itama ta jima da shiga tsakanin sumayya kishiyar ta da ummih kishiyata seta janye ummin gareta, sedai take ita Bilkisun irin waɗan nan mutanen ce masu fuska biyu takan iya sarra kanta sauda dama domin kawar da zargi.. Sosái take ganawa sumayya kishiyar ta wuya ta cikin ruwan sanyi ba tare da ko mutanen gidan sun fa'in taba... Daga daidai lokacin ne sumayy6ta dawo cikin rayuwata da kuma niyar taimakona da sanar dani duk wata kulla kullar da Bilkisun da kuma ummih keyi... Se dai kunsan wani tarin abin mamakin? Samm sammm sumayya bata taɓa nuna damuwa akan duk irin abubuwan da take fuskanta a gidan ciki kuwa harda irin yarda kishiyarta ta mallake uwar mijin su. Sammm sammm bata laifi duk wani laifi na sumayya ne, ita ba mutum bace me yawan surutu tamkar dai ni shi yasa ko iyayenta bata taɓa fuskanta da duk irin abubuwan da take fuskanta a gidan auren nata... Abinda yake gabanta shi kawai take yi domin ita dai Indai tana tare da waya to shikenan zance ya ƙare, akan yi mata abu dan taji ciwo amma dake itama tana da salon nata wayon seta nuna ai ita shashashace bama tasan abinda ake ba. Ire iren waɗan nan abubuwan da take nunawa se Bilkisu ta dinga yawo tana prouding cewa ai sumayya kishiyar ta tsoronta take ita da mijin duk tsoronta suke. Takanyi Murmushi kawai ta sha re zantukan Dan kaff ɗaya da biyu na dawo mata. Matsala ta Farko data fara fuskanta shi ne shiga ɗakin mijinsu da kishiyarta ta fara aduk ranar kwananta. Anan ne ta fara damuwa domin duk ranta yake ɗakinta kawai sedai suga mata da zummar cewa wai abu tazo ɗauka. Sumayya tun tana tunanin Mijin ze ɗauka wani mataki akan hakan amma kuma se baya taɓa iya ɗaukar ko wanne mataki akan Bilkisun... Sau da tari idan abubuwa suka mata yawa takan shige ɗaki tayi ta kuka me isarta kana ta wanke fuskata ta fito tamkar komai be faru ba, Tabbas ire iren waɗan nan jaruman zuciyoyin ya kamata a jinjinamawa irin na sumayya.
Ana haka kwasan sega sumayya ɗauke da ciki seda itama tay shekaru biyar bata haihu ba a lokacin ita kuma Bilkisu shekararta goma sha biyar da aure tunda nima ta rigani a gidan naje na tarar da ita. Nan fa Hankalin Ahmad gaba ɗaya ya dawo kan sumayya sedai ba irin na haukar nan ko wanda zai sanya kishi ba, farin ciki kamm ba'a magana a wurin mijinta Ahmad se dai me surukuwarta sammm bata farin ciki da cikin. Matsala ta ƙaru kenan amma haka taci gaba da zaman haƙuri ko nace mukaci gaba da zaman haƙuri nida sumayya har ALLAH ya sauƙe ta lafiya daren juma'a wayewar asabar ta haifa ɗiyarta mace. Murna wajen Ahmad kamm ba'a magana da duk wani masoyinsa, Ranar suna yarinya taci suna Fateemah uwarta take ƙiranta da Nailerh.... Tsiransu da ummih kishiyata wata biyar itama ta sake haihuwar Namiji again yaranta uku kenan... Nikam har lokacin jalila kaɗai gare ni sedai ni ɗin ma ban wani ɗauki lokaci ba na fuskanci cewar ina ɗauke da wani sabon cikin.
Sammm wannan karon banyi murna da samuwar wannan cikin ba kasancewar duk Rayuwar ma ta sire min aka wllh. Ranar suna dangin su ummih suka zo daga Rano inda aka zo da ƴar yayar mahaifiyarta da ALLAH ya mata rasuwa tun tana yarinya, So kuma se take a wurin matar ubanta bata jima da kammala Secondary School nata ba. Daga nan ummih ta riƙe baby a wurinta ta dawo da zama dindindin wurinta...
★
Haka lokaci yaci gaba da tafiya kullum da sabon hargitsin da rashin tsarin da yake zuwar mana dashi, Ni kuwa fanni na renon ciki na nake yi cikin rashin walwala da cunkusher zuciya da ta jima da wahalar rabuwa da rayuwar ma baki ɗaya. Masu iya magana sukan ce , Zaman lafiya yana buƙatar haɗin kai daga kowane ɓangare tabbas haka ne indai za'a baka haɗin kan wannan ba komi bane game da Abokiyar zamantakewar ka. Da so samu ne ma mu so juna idan akai haka me aka rasa? Babu domin kuwa zama lafiya yafi zama ɗan sarki, Amma ga wasu abokan zaman ahar kullum burinsu bai wuce ace kawai suna treating na abokan zamantakewar suba.
Ahar kullum duk sanda zan fuskanci mahaifiyana da matsalolin gidan aure na da na tabbar se naga zasu min illa suna nemar kasheni da raina. Takan ce dani...
"_Aisha komai na rayuwar duniya da kike kalla ɗan haƙuri ne, haƙuri da Juriya sune jigon kowanne rai me numfashin dake numfasa a cikin wannan doron duniyar! Rashin su kuma kan iya haifar abinda samm sammm daga ƙarshe bazai yi kyau ba. Kiyi haƙuri Aysha bazan gaji da baki haƙuri ba. Abinda zance dake shi ne kije ki rungumi yaranki, ki rungumesu tun suna yaransu! Su samu shaƙuwa mai ƙarfi dake kafin kowa, ta yadda sune zasu zame miki garkuwa a kan duk wani ƙunci da zai tunkaro rayuwarki. Kyaun halinki kan iya maye gurbin munin fuskarki.
A yayin da munin halinki kan iya maye gurbin kyawun fuskarki a cikin jama'a....kiyi godiya ga ALLAH Sarkin Sammai da Ƙassai,wanda ya ba mu lafiya tare da ni'imar Musulunci. Akodayaushe ki zama me tawakkali da duk abinda ya tsara miki kana kada ki yarda ki zama ɗaya daga cikin matan nan masu zargi akan abokanan zamansu. Ina so ki zama jajirtacciyar mace a gidan aurenta da yin kyakkyawan zato ga Abokiyar zamanki. A kace wai motsi yafi lafewa tukuwcin da zan baki shi ne ki sake tashi tsaye da tarin adda'o'i wa ubangijinki da yaba ki kariya. Nima ina nan ina tayaku dukanku da tarin adda'o'i na zaman lafiya da baku kariyarsa a koda yaushe tashi kije IN SHA ALLAH zakiyi Albarka da jin daɗin Rayuwar aure ko ba yanzu ba wannan yaƙinin nake yi a koda yaushe akan ki Aysha. Shi ya sa bana taɓa yarda wannan yaƙini da kuma kwarin gwiwar su gudu ni mahaifiyace jigo ya yarana ALLAH ya albarkaci rayuwarki da ta sauran ƴan uwanki Aishatul mebeen...._"
Wani dogon numfashi naja inajin kwarin gwiwa akan koma menene ze tunkaroni to UBANGIJI Na zai kareni zai kuma kawo min shi da sauƙi...
Ji na yi kaina yana wani irin saramin tamkar ana zare min wani abu. Wanda nasan baya rasa nasaba da tunanin da ahar kullum nake zafafa kaina dangane da lamarin daddy'n su Amaan.. Rike kan na yi sosai don jin da nai tamkar kan na ƙoƙarin ficewa daga gangar jikinane,cike da karfin hali na fara karanto duk adda'an da tazo bakina. wani irin bubbugawa naji tsakar kaina nayi kamar ana dukan ƙarfe da ƙarfe. Lips ɗin na rawa-rawa na shiga furta.....
"A u zu bi wajhillahil Karimi,
Wabi kalimaatil-lahil lati laa yujaawizuhunna barran wa laa fajiran, wabi asmaa'illahil husna kulliha, ma alimtu minha wa maalam A'alam min sharri khalaqa, wa zara'a wa bara'a, wa min sharri ma yanzilu minas sama'i, wa min sharri ma ya'aruju fiha, wa min sharri ma zara'a fil'ardh, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min fitnatil-laili wan-nahaari, wa min tawarikil laili wan nahari, illa tariqan yatruqu bikhairin ya Rahamanu. Wa min sharri kulli daabbatin Rabbi akhizun bi naasiyatuha Inna Rabbi ala siradin Mustaqim..." Nakai ƙarshen adda'an ina nufar window'n parlour na tare da ɗaura hannuna kan heart ɗina da duk single beat remains him of her in his arms, ahankali na ɗaga kai ma kalli plain Royal blue chiffon curtains ɗin dake jikin babban window'n ɗakina dake kaɗawa sosai sakamakon iskan da akeyi na hadarin da yama samaniya ƙawanya ta hanyar yi mata ado da gajimare, zuwa lokacin garin ya fara duhu sosai kaman irin tsakar dare ɗin nan sabida hadari sai walkiya sama take,
A haka me gidan ya shigo ya sameni tsaye kaɗan kaɗan nake sakin ijiyan zuciya. Zagayeni yayi da hannuwansa kafin a hankali ya ziro ɗaya ta ƙasan doguwar rigar baccin dake jikina yana sauƙa saman ƙirjina...
Cikin yanayi na kamar na yi kuka na ɗago ina kallonsa ina kuma sauƙe wata ajiyar zuciya ganin irin kallon da yake bina dashi. Kan nawa ya kwantar a saman ƙirjinsa tare da shafa fuskana cikin nutsen murya
ya ce. "Kuka kike Ashsha?"
Kamar wacce nake jiran wanin ya tankani dama ma se kawai na fashe masa da kukan da yake fitowa tun daga cikin ƙarƙashin zuciya..
Yadda na lafe jikinsa shi a nashi ɓangaren se yanayin yanda na lafe ɗin ya saukar masa da wata zazzafar kasala. Wanda ya sanya shi lumshe idanu ba ma ta irin tarin damuwar da suka jima ƙunsa min yake ba ta kansa yake yi. Jin yadda ya fara lalubanane ga kaina dake min shegen ciwo kawai na shiga kuka ina dukan ƙirjin sa da hannuwana cikin rashin kuzari da karfi nake furta... "I hate you Hameed!, I hate you Hameed I hate you I hate you, nayi nadamar Auren ka,naji na tsani aurenka na tsana har da kai. Kai me son Kan kane da yawa Hameed ba ka damu da damuwana ba ina kukan abinda ke damuna amma kai ta samawa kanka mafaka kake yi a jikina I hate you wllh...... Zuwa lokacin jikina har jijjiga yake kafin a hankali ya tako inda nake da nayi baya dashi.
"Okay please stop crying am sorry Ashsha ba haka bane wllh ke ma kin san I love with all my heart ko? Pls ki dena saka damuwana a ranki na roƙeƙi" yay maganar yana wani haɗe hannayensa alamar bada tabbacin hakan kenan. "Sabo da zan mutu ko? To In Sha ALLAHU damuwarka kaida banzar matarka basu Isa ɗaukar Rai na ba Hameed se abin da ALLAH yayi. Damuwarka kuwa na jima da yakice abata na bisne ta cann cikin wani baƙin ramin da zaiyi wuyar tonowa Se dai ta fidda sabon tsirrai" nakai maganar ina zubewa zaune kan ƙafafuna. Duk shi ma se jikinsa yay sanyi ganin irin kukan da nake.Shima se ya kai zaunen a inda nake tare da janyoni jikinsa ya rungume yana bubbuga gadon bayana a hankali, kafin cikin ƙaramar murya ya shiga faɗin. "I m so sorry Ashsha I m sorry" domin fa duk yanda akai ƙoƙarin rabani dashi duk da an kashe wannan SOYAYYA'R tawa dake cikin ransa wani sa'in takan motsa Kanta da kanta domin soyayya ba ƙarya ba. Ni kuwa kaman cemun yake na ƙara volume ne. Kuka nake da gaske kukan takaicin daya dade yana shaƙamun, ƙara tuno wasu abubuwan nake ina ƙarama kukan nawa ƙarfi sosai. Kwantar dani a jikinsa kawai yayi yana sakin numfashi me ɗumi sosai shima.
Na lura dashi sosái a duk irin haka ta faru ko yayi mun wani abu da har takaini da zubda hawaye. Yakan rungume ni ne ya shigar dani jikinsa kawai nayi ta kukan har iyaka yina yana aikin bubbuga baya na har nayi shiru dan kaina kuma. Idan kuma ƴan abun na kusa sedai ya ƙara kasheni da zafafan maganganun sa ya fice ya bani wuri. Se da nayi me isa ta dan kaina har bansan lokacin da bacci yay awon gaba dani ba a jikin nasa, kwantar dani yayi bayan ya rage min kayan jikina tare da zuba min idanu...
Domin wannan ɗan abin kawai kansa har ya fara sara masa,shi kaɗai yake ayyana akaf faɗin duniya babu abinda yake ruɗashi da hargitsashi irin na. Don nasan duk wani lungu da saƙo da zan shiga na tayar masa da hankali sedai in ban soba, in banda fitina irin tawa duk me ya kawo waɗan nan munanan kalaman? Domin fa har a lokacin niɗin nan dai ni ce maƙale a cikin rai da Ruhinsa. Yana cikin wannan tunanin Ƴar gwal ɗin sa ummih ta ƙira shi tana ta rinja masa kuka wai ba ta da lafiya yazo zata mutu. Jikinsa har rawar tashin hankali yake ya fice a ɗakin har yana ƙoƙarin cin tuntuɓe. a zaune ya tarar da ita dirshan tana sharɓar kuka riƙe da cikin ta. "Subhanallah ummih me ya faru? Ko cikin ne ke miki ciwo kanta ta ɗaga mishi tana riƙe hannunsa ta ɗora a kan cikin. Ɗaukarta kawai yay Yana nufar compound na gidan, tun kamin ya ƙara so inda Motarsa ke fake yake ƙiran get man ya buɗe mar get. Kai tsaye asibiti ya nufa da ita aka ƙarfe ta cikin gaggawa kasancewar kafin ya isa ya ƙira babban amininsa Dr Basheer cewar gashi nan zuwa iyalin sace babu lafiya. Nan aka amsheta aka kwantar aka ce da shi ya koma gida se zuwa safe, be so amma kuma dole ya dawo gidan. Kai tsaye ɗakin ummin ya ƙara kowama baby ya tarar tana kallo abinta dan shi ɗazun ko ma kula da ita beyi ba kansa ya ɗauka chajin. Tana ganin sa tayi saurin gyara ɗaurin ƙirjin dake jikinta, sannu da zuwa ta masa jikinta har na ɗan rawa. Be amsa taba se da ya fara duba yaran yaga duk bacci suke yi kana ya nufi inda taken. Taku yake yana nufar ta ita kuma tana sake ƙanƙame jikinta akan gadon. Tsai ya a kanta yana ƙare mata wani irin shegen kallo na tin daga sama har ƙasa. Zaune yakai gefe da inda take zaunen kana a wani irin hankali ya sanya hannunsa yana shigar da bata cikin nasan. Ɗumin da yaji a cikin tafin wannunsa ne ya sanya shi kallonta gumin hannun na Rasha shi. Wanda ya saka shi sanya hannuwansa ya miƙar da ita tsaye yana ci gaba da kallonta kafin ya matsota jikinsa. Ya mannata da jikinsa yana sauƙe wata shegiyar ijiyar zuciya. A hankali ya kwantar da ita saman ƙirjinsa yana shafa gadon bayanta a hankali. Dake dama can yarinyan me buɗaɗɗen idanu ce amma kuma tana da shegen wayo ya saka farat daya baka isa gane fuska biyu gare ta ba. Ijiyan zuciya itama ta saki tana zagaye shi domin dama wannan ɗin shi ne mafarkinta kodan yanda yayar tata ko nace uwar ɗakin nata take koɗa mijin nata. Sannun sa ya zira ta cikin zanin da ke jikinta yana ɗorawa akan bra ɗin dake jikinta. Kwantar da ita yayi akan gadon yana bin kanta tare da haɗe bakinsu wuri guda. Kissing juna sosai sukai se dai ko kusa be ɗauka hanyar kusantar taba. Amma ba laifi kammm Ansha Romance dan sun jima sosai. Se wajajen ɗaya da rabi ya baro dakin yana janwoni jikinsa muka kwanta ba tare da nasan abinda ya aikata ba. Ko da asuba dake duk baya tasha ni ke tashinsa dama cann, idan kuwa a ɓangaren ƴar gwal ɗin sa yake kuwa se safiya suke sallah...
Koda ya fito se na kalla kamar alamar wanka yayi, dan haka sena gaza haƙuri har seda na furta..
"Daddy'n Amaan kamar wanka naga kayi fa?" Fuskarsa ya matse sosai daidai yana ɗaukar sallaya ya shimfiɗa murya can ciki ya furta.
"Mafarki nayi" Da wani kalan kallon renin hankali na bishi don ba yau ya saba min irin wannan renin hankalin ba. Ko idan ina hali na rashin sallah yakan yimin irin hakan idan na tambayeshi se yace min mafarki yayi. Dake na san halin kayana ciki da bai se kawai na ɗauke kai zuciyata na min soya sosái domin sau da dama nakanji nikam na zamana da Hameed ya ƙare, sedai idan na waywaya baya Yarana! Yarana su ne abin duba na idan na tsallake na barsu kenan me gari ya waya? Na tsallake na barsu domin halin mahaifinsu to su ɗin kuma fa? Idan na tuna ire iren waɗan nan abubuwan se duk naji gwiwa na tayi sanyi, da ganin laifina tun farko da ban tsaya da kyau nama yarana zaɓin uba na gari ba. Sedai ya zanyi a haka allon ƙaddara ta yazo min babu kuma yacce zanyi na sauya daga mummmuna zuwa kyakkyawa har se sanda ALLAH ya so...
Se a washe garin ranar nakejin ummin bata da lafiya, kallo ɗaya nama baby a lokacin naji wani mugun bugawar zuciya. Dan wllh ba karya ba se na ga gizagon fuskar Hameed kwance saman nata fuskar. Adda'a nayi ina korar sheɗan tare da Istigfari a raina kar na ɗauka alhakinta. Dan kawai mijina ya kasance manemin mata ai bai cancanta kowa ma na fara masa kallon abokin harƙallar saba. Kuma ya iya takun sa kai duk iya kwakkwafinka baka isa gane cewan Hameed manemin mata bane. Duk muka ɗunguma muna zuwa duba ummih wanda ashe laulayin shigar sabon ciki gareta. Mun jima sosai acan kana muka dawo gida na ɗora girkin rana wanda nayi tafi da dare..... Tuwon ɗanyar shinkafa na mana da miyan kuɓiya da taji uban kifi da tarugu haɗi da kayan ƙamshi. Se sallar la'asar muka koma inda bamu dawo ba se magrib wanda aka sallamota muka dawo gida tare. Dane na fita daga kwanana ta amshi girki amma ban bari tayi girkin ba na mana, Baby tasa tahau saman sa ta gyara masa wanda lokacin ina wankin uniform kayan su jalila ne da yayyanta seda naji ƙafafu na sun ɗauki wata irin rawa. _Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un_ na furta a raina ganin wani sabon kafirin. Yanzun wannan gandamemiyar buduryar zaka aika gyara ɗakin mijin aurenka na Sunna?, Wllh jahilci da rashin tunani samm sammm be yi ba a rawa. Wankin da ban iya ƙarashi ba kenan se Amaan ne ya ƙarasa musu, haka rayuwarmu ta koma duk ranar da yake ɗakinta baby ke masa komai ita wai tana uwarta aiki. Haka yake samunta ya shafe abarsa tasss se ga yarinya ta fara ɗaga hanci sama ƴar aunty'n da ta fara ƙirana dashi ta dena se dai ta ƙirani da Maman Ayman. Amma kuma har zuwa wannan lokacin be taɓa kusantar taba sedai suyi taɓe taɓansu iyaka san ransu har ta kai ta kawo ko ni ce dashi se fara tsiromin da na turo mishi baby zata masa abu kaza. Anan na fito masa a mutum na rattaɓa masa rashin hankali nace ya fita a saugana da wannan mugun jahilcin domin ita ummin in bata da cikakken hankali da tunani to ni inada. Dan haka na taka masa birki nace ranar girkin ummin dai sayi abinda zasuyi abinsu. Chart kuwa na soyayya abinsu suke yi, ko nace na rashin mutumci. *LA ILA HA ILLA ANTAS SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN* domin kuwa seda fadar hakan dan a lokacin ne na shiga tsananin azabar da seda na riƙo ALLAH daya ɗauki raina na huta. Ga takurawar matan uban Hameed ɗin ga uwarsa itama dake Rano ta koma ta ummi komai dai a daidai wannan gaɓar ya gama taruwa ya lalace min, Ya zamana tsabar muguwar tsanar da aka dasa min duk ran girki na idan nayi dake muna kaiwa matan uban haka za'a wulaƙanta shi Hameed ya shigo ace masa sammm sammm yanzu abinci na baya dahuwa kuma kaɗan nake bayarwa. Haka zezo ya hauni da bala'i da masifar babu gaira babu dalili wai na koyo wani salon bakin mugun hali ne, ai da duk ba hali na yake ba. Duk me cikakken hankali kuwa a lokacin kallo ɗaya zewa Hameed ya gane cewar baya a cikin taytayinsa ne mace ta gama kwance masa kai.
Amma idan na faɗa masa baya taɓa yarda, Su Hajiya ummi kuwa duniya sabuwa aka buɗe. Tabbas ummih tayi nasara a kaina a wannan gaɓar domin kuwa seda ta mayar dani me mugun halin karfi da yaji na gasken gasken ma kuwa, domin rayuwata na koma daga ni se ƴaƴayena. Na bushe na rama wanda a sunan ina matar Hameed yanzu mukan kwashi sama da wata guda komai da ya shafi auratayya ya shiga tsakanin mu. A wani dare kuwa mafi munin munanawa a gare ni shi ne daren dana gane cewar ina ɗauke da sabon cikin Hameed. Wanda har ga ALLAH wllh wllh na dena bewa kain haihuwa. Kuka!!! Kuka nayi kuwa iyaka kuka a wannan daren harna gode ALLAH domin wllh nan zaci zan ƙara haihuwa a wannan baƙin gidan ba daya jima da zama filin ƴan yaƙin sunkurun ƙarƙashin ƙasa a fannin yawon bin malamai babu yaro babu babba. Zuwa lokacin gidan ya sake cika da matayen kannen mazajenmu Allah sarki sumayya tun daga Nailerh bata kuma haihuwa ba itama. Ana nan anata zaman haƙuri itama dai. Don a daren ranar da tazo min da kukanta kan cewar daren jiyan Bilkisu ta faɗa musu daki suna a yanayi bame kyau ba idata Ahmad. Amma be ɗauki mataki ba har zuwa yau. Wannan fa shi ake ƙira gaba kura baya damisa. Ƙaƙaƙara ƙaƙa domin yawanci duk bata san halin da nake a ciki ba. Ƙalilan dai dake gidan sun riga da sun san cewar ummh ta jima da mallake Hameed. Cikin yanda ba zan iya fa'inta komai ba sumayya ta fara fargar dani abinda ka iya zuwa yazo tsakankanin Hameed da baby. Ta hanyar bani labarai masu kama da kalan namu yaya uwa ɗaya uba ɗaya ta ɗauki ƙanwarta da zimmar riƙe wa a wurunta, mijin da kuma ƙanwar nata suci amanar yayar tana zaune ƙalau. Ciki kuwa harda labarin data bani akan wani uncle ɗin ta da shima matarsa ta ɗauko ƙanwarta da uwarsu ta mutu dama sun jima da rasa uban. Ta riƙe a wurinta haka mijin nan ya zama bunsuru tsakanin yayar da kuma ƙanwar. Wa'iya zubillahi wannan babban zuni har ina kuwa. Anan take sake bani labarin wata makwabciyarsu da itama ubansu ya faɗi ya mutu uwar kuma irin iyayen nan ne masu shegen son duniya tayi aure tabar Yar a gidan uban. Shi ne akace babbar yayarta ta ɗauke ta tace sam wllh bata isa ba. Nan a cikin dangi akayi tayi da ita cewar batason wani nata ya raɓe tane kawai. Haka taji ta kuma toshe kunnuwanta kasancewan tasan mijinta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 12