Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 12
ƙira ya sanar mata ni kuma na ƙira Aunty fa'iza na sanar mata zuciyata a soye. Duk wanda yaji cewar ciwon zuciya ke ya jinjirar se ya jijjiga saboda ba abu bane da aka saba samu kasafai anan haka. 6:32pm Dr Asia Maleek ta fito hannunta naɗe da Baby showel ɗin da nake da tabbacin na jaririya tace. Dan haka jikina har rawa yake na nufeta har ina kusa cin tuntuɓe da mutumin da ban san ko waye shi ba, sedai ƙamshin da naji yamin kama da wani wanda na taɓa sani, amma kuma dake ba wannan bane a gaba na ya sanya ni ci gaba da tafiyana ina amsar baby'n a hannuna. "Sorry A'ISHA MUSTAPHA baby'n ALLAH ya nufa bame kwana bace, Se dai muyi adda'an ALLAH yasa macetanmune..... Wani irin sarawa kaina yayi da wani kalan masifan ƙarfin daya sanya ni yin baya. Ƙoƙarin zubewa nake yi amma kuma na hana hakan domin nasan wannan ɗin ma zai wuce kamar koda yaushe,kamar yanda na saba. Dan haka na aroma kaina wani kalan jarumtaka da kwarin gwiwa ina goge hawayen da suka sauƙo min nayi wani murmushi me ciwo na saɓa baby'n a kafaɗa na furta musu, Babu komai wannan ɗin ma zan iya ɗauka. Daga nan naja hannun A'isha mukayi waje idanuna na ganin jiri² ina Fitowa Yaya khaleel yayo wurina tare da tambayar har an sallamemu. Sau ɗaya na kalle kana na kalla Baby showel ɗin dake hannuna kaina na jijjiga masa kafin na furta. "Babu ta tafi ta huta da wannan duniyar tamu, ta tafi ba tare data ɗauki laifin kowa ba Yaya khaleel Se ALLAH yasa masu cetone" daga nan nayi gana zuwa inda Motarsa ke parke. Na buɗe motar kenan zan shiga najiyo muryan da yanzun kaff duniyar nake jin nafi tsana sama da komai wato muryan Hameed. Ban dakata ba kamar yanda ya buƙata seda na kwantar da baby'n cikin motarmu kana na juyo zuwa gare shi. Cike da wani kalan tsana mara algus na cakumi wuyar rigarsa na jijjiga da ƙarfi kana na furta.... "Me kazo yi anan? Me kazo ka min kuma? Ko duk abinda ka aikata mana be isheka ba bayan baby'n da kai sanadiyar mutuwar ta tun kafin ma tazo Duniyar, tarin ɓakin cikin ka da tarin damuwarka suka taru suka dirar mata da ciwon zuciya jinjira, jinjirar ALLAH ta'ala ta mutu ata sanadiyyar ka Hameed... Muɗin ma ba zaka ƙyale ba seka biyomu 00 ka ƙarasa ganin bayanmu tun da dama sauran ka ƙiris ya rage maka? Kafff Duniyar nan ban taɓa jin na tsani wani abu sama dakai ba HAMEED USMAN DATTI!, Na tsane ka tsana mafi muni da haɗari, ka shiga cikin Rayuwata da yaudara da cin amana, ka zalumceni, kaci amana ka rugaza min gobe na da duk wasu fata da burikana harda ma mafarkaina, In Sha ALLAHU banyi maka baki ba Hameed Amma se rayuwa ta koya maka hankali bi'izinallah, Duk yanda naso tsaida zuciyata na kasa seda nayi kuka zuwa lokacin wasu tsirarun mutane harsun fara taruwa a kanmu, dan haka Yaya khaleel yaja yazaunar dani cikin. Har ma shiga na sake yunƙurowa cikin muryan ihun na sake furta. "Wallahi ko inda ƙofar gidanmu take ka kalla ban yafe maka ba Hameed bare kayi tunanin zuwa ayi sitarar *MARYAM*" nayi maganar ina jan murfin motar Yaya khaleel yaja motar inda yasa A'isha a gaba ni kuwa ina gidan baya rungume da babyna da ALLAH be bata lafiyar da zata sha Mamarta koda sau ɗaya bane. Tun a asibitin Yaya khaleel ya ƙira Bappa ya sanar dashi dan haka muna isa wanka kawai aka mata idona fall da hawayen tausayin tamu rayuwar,dan ita kam ta huta Tata ta ƙare tazo a me kyau ɗin ta ta koma a me kyau me yafi wannan daɗi?, Harda Alhaji DATTI Mahaifin Hameed akayi janazar baby'n anan cikin gidanmu daga baya. Dake jaririyace yasa ana suturtata bayan anyi adda'a aka watse se iyaka Bappa'n mu da Yayyanmu maza se makwaftan da ake mutumci haka. Nan mutane suka ɗan soma leƙowa suna ma matan gidan gaisuwa dan nidai kamm babu wanda ya sake ganin idona tun bayan dana gama yima jinjirata adda'a aka amsheta zuwa makwancinta na gaskiya. ★ A kwana a tashi hasarare rai, se gashi yau ALLAH ya kawo mu kwana uku da rasuwar Maryam, Inda Ummih suka zo ita da Baby kwanwarta ko nace matar mijinta, Maman Hameed ma tazo randa akayi rasuwar so washe garin ranar bata dawo ba se yau da ake mata sadaka ta cikarta kwanaki uku kwance a cikin ƙabarinta. Daga nan kowa ya dena zuwa yaran gidan aurarru. Ko ranar bakwai ma adda'a kawai aka mata Bappa'n mu yace kada kowa yazo, Haka rayuwa ta fara lula mana tana mana nisa inda ƴan gidanmu manyan yayyena da Bappa'nmu suka rufe ido suka hana Hameed yaransa, farin cikin hakan wurina kuwa ba'a magana, haka yana ji yana kalla aka hana sedai Ashman yakan je ya kwana biyu. Amma A'isha kamm bata taɓa yarda taje ba, shima idan yaje ya dawo tamkar almajiri haka yake dawowa gidanmu. Wasa wasa se gashi ina dosar watanni bakwai a gidanmu. Duk yacce Hameed da abokanan sa suka kai ga nacin bikon nayi haƙuri na koma kodan yarana haka na share su, tun dai yaran gasu a hannuna. Tun yana kallar abin wasa har hakan ya soma tada hankalin sa, gashi dama Ummin ba wani girki ta iya na kuzo mu gani ba kawai aci ne kar a mutu. ★ Nan fa manema suka fara min caaa aka sedai samm bana taɓa bada fuskar hakan, sema aikina da nake ta ƙoƙarin ganin nasa gaba. Tun da Bappa'nmu da kyar ya yarda ya barni, dan da farko hanawa yayi way yanzun nayi girman da na wuce aikin jarida. Alhamdulillh cikin Ikon ALLAH kuwa aikina ya kankama inda na buɗe wata sabuwar ƙungiya me suna, 𝙈𝘼𝙏𝙎𝘼𝙇𝘼𝙍𝙈𝙐 𝘼𝙔𝘼𝙐 _Mata mu farka_ haba Malam zo kayi kallon yanda wannan A'ishar ta baya data jima da mutuwa a zuciyoyin masoyanta ta fara dawo musu fiye ma da farkon. Sammm bana wata shigar da bata dtace ba kullum cikin abayoyi manya nake, da hijjabai manya da yaya khaleel ya sai min sabbi wajen guda goma. Da Nosemark ɗina tamkar baya haka nake zuwa na dawo, Alhamdulillh duk iya kwakkwafinka baka isa kamin kallo ɗaya kace ni ce mahaifiyar yara huɗu ba, dan irin kyakykyawan jikin nan ke gareni. Anan na fara fuskantan take taken md na son ya bijiromin da batu akan ƙulluwar soyayya, babu ɓata lokaci na taka masa birki nace idan dan ina gidan jaridar sane zan iya tafiya nabar masa abin shi, anan fa ne ya shiga taytayinsa domin ta bakinsa yace tun da yay rashin *ROYAL KINDNESS* Har yau be sake samun koda kwatankwacin muba. Gefe guda kuma ga wani makwafcin anguwar mu ya nace kwarai da gaske seya Aure ni me suna Dr Hamza. Duk yanda nake yakice mutumin da yagar dashi yaƙi yakicuwa, haka ze fita da yarana ya musu shopping na hauƙa da ɗaukar magana matashin magidanci ne me yara uku, wanda tun ina buduryar yaso ni naƙi shi shi ne a wannan karon ya dawo da ƙarfinsa, wanda suka sha faɗa da mahaifin yaran idan sun haɗu wajen shopping. Daga baya ma se kawai ya fita a rayuwar yaran da tawa Rayuwar wanda dama ni hakan nake da buƙata. Se dai me? Wata sabuwa ashe zaunen bata ƙare ba. 𝘼𝙎𝘼𝘼𝘿 𝙅𝙐𝙉𝙀𝙍𝘿 𝙈𝘼𝙅𝙀𝙀𝘿 Nasan dai duk me sauraro da wanda yake biye dani wannan ɗin ba suna bane da zai manta cikin sauƙi ba. Se gashi ya dawo cikin Rayuwana tsilim babu zata babu tsammata. A ranar farkon haɗuwar wata ranar Saturday ne nakai jalila Hospital bata jin daɗi. So ba Hospital ɗin da muka saba zuwa bane, anan jalila ta haɗu da wata kyakykyawar baby girl fara ce sosai. Nan suka yi ta wasannin su tare bayan an gama mata scanning na jini. Nan yarinyar tayi ta bama jalila labarin daddy'n ta, har take tambayar jalilan wai ita bata da daddy'n taji bata mata zancen daddynta ita, wannan maganar karaf a cikin kunnuwana, Ashe shima cikin nasa kunnuwan, nan take idanuwana suka ɗan yi raurau amma ina fiskewa abuna. Abinka da yaro babu hankali aikuwa jalila tayo guna tana min kuka wai ita ma ina sabon daddynta da kullum nake cewa ze zo har yanzun be zo bane? Kasa riƙe kaina nayi dan haka nayi saurin shigewa wani roomdonper ina share hawayena. Ina barin wurin ya kamo hannun jalaila tare tsugunnuwa daidai tsahonta, kallonta yayi da kyau tare da furta. "Da kyau Beauty girl, kina son ganin sabon daddy'n ki ne?" Kanta ta ɗaga mishi wani lalataccen Murmushi yayi da har zuwa lokacin yake nan akan ganiyar samartakarsa. "Okay to shikenan kina son ni in zama new daddy'n naki ne beauty?" Kanta ta sake gyaɗa masa tare da yin tsalle ta rungume wuyansa tana murnar farin ciki. Kallonta yayi tare da raɗa mata, "To maza ki shiga ciki kice da mummynki new daddynki na gaida ta badan halinta zai dawo a karo na biyu..... Da gudun ta kuwa ta bar wurin tana nufar room ɗin da Mummy'nta ta shige, Da kallo ASAAD yabi bayan jalila har ta ɓacewa ganinsa,wata iska me zafi ya furzar daga bakinsa, domin tun a ranar da babynta ta rasu ya ganta dan yana wurin shi ne ma wanda suka yi karo bata lura ba shi ma be lura ba, se daga baya yagan ita ne, So sanin mutumci da kuma martabar Aure yasa be ko waywayenta ba, seda ya gama uzirinsa cikin Hospital ɗin ya fito zai tafi nan ya ganta, inda ta riƙe rigar Hameed tana yaɓa masa wannan maganganun, A loƙacin da ji yayi idan har ne kama Hameed take a wurin yayi daga daga da namomin jikinsa to wllh be huce ba, amma kuma ya ƙyale hakan yana bin bayan motarsu, daya lura da kamar Hameed shi ma su ya biyo take ya bama uban securities náshi umarnin su yi kidnapping ash car ɗin dake bin bayansu, dan kuwa wannan maganar ta *TASHA'NSA* da yaji akan bata yafe masa idan har ya halarci suturar ƴarta bata yafe masa ba ne yasa shi cikata mata aikinta. Daga inda yake zaune cikin Luxury Rolls Royce Dawn ɗin da yake ciki ya fesar da wata iska me zafi, tabbas se a yanzun ya sake yarda har yanzun shi ne garkuwar A'ISHA, Shi ya sa ALLAH ya ɗauke ran matarsa daya AURA Yasmine bayan ansha fama kafin ya amince a aure ta, So haihuwarta biyu ALLAH ya amshi rayuwarta, tun daga nan ya fara bibiyar tarihin rayuwar gidan aurenta ta baya, anan ya gama fahimtar komai dan haka yayi alƙawarin se ya nunama Hameed Babban kuskuren daya tabka, yana kalla se aure ta a karo na biyu kuma ya ci gaba da zame mata garkuwa har sai ya tabbatar da cikar kammaluwar farincikinta tamkar yanda shi ya gaza yi. Left hannunsa ɗaya ya ɗora saman center console na motar ya ɗauki lates phone nashi, tare da yin baya dayin baya da kujerar motar ya a ɗora ƙafarsa ɗaya kan console na motar yana gyara zaman kujerarsa sosai yayi relaxing, kana ya soma lalubar number wata no da bata yi kama data ƴan 9j ba ya doka ƙira......... A natse na fito daga gidan jaridar namu tamkar kullum da doguwar hijabata har ƙasa fuskana sanye cikin liƙab, tun da ta fito ya kureta da ita shi kaɗai ne yasan kalan baiwawwakin da yake kalla tattare da ita. Gata tsaka tsaki, gata kyakkyawa ta gaban kwatance, ga wasu ƴan filic ɗin luscious lips nata Perfect material kawai With Full option cki da waje gata very sound and nice person to be fined and finished. A Hankali ya sauƙe ting glas na car ɗin tare da mata hong, Ina sane dashi dan dan a ƙalla ya kusa 3 Months Kullum se yazo nan ya tsaya, duk yacce zekai ga nacinsa ko kallar inda yake banyi. Tafiya ya fara da motan su kuma ƴan wahalar nashi suna can tsaitsaye zagaye da sauran motocinsa wajen bishiyar setlite ɗin deke wajen gidan jaridar namu. Seda yayi daidaita dani kana ya ziro kansa ta cikin motar ya furta. "Pls TASHA dama ɗaya takkk nake nema daga gareki plsssssss" Ya faɗi yana Kallonta ta cikin Motar, yi nay tamkar bansan yanayi ba, kan motar ya ɗan buga tare da Parking car ɗin ya ziro fararen zaratan sawayen sa, yana bayyanuwa baki ɗaya kan diga digansa tsaye gaban ta. Sanyin iskar daya kaɗo da ƙamshinsa ne suka doki hancinta, wanda dole suka sanya ta lumshe idanunta kana ta ware ta kalli inda yake ya wani tsare ta da mayun idanunsa. Tun da ga kan kyakkyawar soft fatar jikin san nan me murjajjen jiki ta bi da kallo, har zuwa kan ƙaƙƙarfan siffarsa da cikakken zatinsa da suka gama nuna kansa da kansa ta jikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na combat Reva net ɗin dake jikinsa. Har zuwa kan wani haɗaɗɗen luxury Rolex watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa. Zuwa Baƙar sumar da baƙaƙen kayan dake jikinsa suka haɗu suka sake haskaka farar fatarsa tarrrr tamkar fitowar rana a farkon wuni. Shade ɗin daya toshe idansa dashi ya zare take kyawawan kwayar idanunsa dake da wani irin shape mai matuqar fusgar hankali, suka sarƙe da nata wanda suke cike da wani irin kwarjini mai tarin yawa, ganin irin kallon da take binsa da shi ne ya sanya ASAAD zare nose mark dake face nashi dan ya bata damar ƙare masa kallon da kyau... Ta re da furta. "Me ya sa a koda yaushe kike son tilasta ma kanki da zuciyarki cusa mata ƙin abinda shi ne yafi dacewa da ita TASHA???..... *BY AMMEY LAYLERH ✍️* °༺ 🌏𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐🪐*࿐ 𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚🤦 https://whatsapp.com/channel/0029Vb4EHwq6LwHgpTokZA3D ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Official Mirrah💐 ♡ Page 19&20 *End of Last free Page's end🤗* # SingleAndThriving # HeartToHeart # UsAgainstTheWorld # LoveWithoutLimits # HiddenHeart # GlowingAfterGoodbye # Heartbroken # CryItOut # LoveHurts # Heartbroken ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* ★★ ♡♡♡♡♡♡ Wani kalan murmushi me ciwo nayi tare da soma takawa domin sammm a yanzun ba aure ba ne gabana, kallonsa nayi yadda yake sake tunkaro ni ya sanya ni saurin buɗar bakina ina me furta. "Ka dakata kada ma kace zaka ɓata ma kanka lokaci, domin a tsarin lissafina na yanzun samm babu aure a cikin sa, kuma koda ace ALLAH ya kadarta zanyi auren a karo na biyu, to kuwa da tabbas bazan taɓa zaɓar ASAAD JUNERD ba. Domin ni da shi ba abu ɗaya bane, duk da nasan cewan komai na rayuwa na tafiya ne tsakanin jerarrun abubuwan da aka ma laƙani da sunan ƙaddara. Wata kuma takan zo a siffar hargitsattsun layukan da sai an tsallake iyakoki masu zurfi da kuiya kafin a cimmasu. Kaɗan a cikin mutane ke taka matakin nasara da ƙaramar gwagwarmaya, da yawa kuma a cikin mutaka zaga cikin duniya se ALLAH ya haɗa ka da wacce kake SO ASAAD...... Saurin taryan numfashina yayi ta hanyar furta. "Duk abin da kake so ka shirya yin gwagwarmaya don samun sa da gumi da wahala da aiki da tunani da addu'a da kuma tsawon lokaci. Kuma ko yanzun Alhmadulillah Ala kullu halin, wannan ba wayona ba ne, ba kuma dabarata ba ce, iko ne daga Allah. Ko anan kin sake nuna min ke ɗin dole duk inda akaje aka dawo aka gwabza gwagwarmaya da kwamalaca keɗin your mine *TASHA* ke tawace" Ya furta a sadda yake tsaiwa gabana idanunsa ya Lumshe tare da ɗan ranƙwafowa kasancewar ya fini tsayi nesa ba kusa ba. "Zaki bani dama ɗaya takkk *TASHAH* zan killace ki Anan tsawon rayuwata!!!" Ya faɗi yana nuna setin heart náshi. Jin nayi shiru tare kuma da kawar da kaina ne ya sanya shi buɗe idaniyarsa duka a kaina tare da furta. "Ki amsa ni please I'm just worried *TASHAHHH*" _Oh ALLAH na faɗi a raina ina jin wani irin takaicin sa a cikin zuciyata , Ba wa ni kaina ba shi kanshi nasan ya lura da yanda fuskata ta canza, amma duk da haka be hakura ba gashi a titi muke ALLAH ma yaso daga gefin titin muke. Saurin tsallaka ɗayan gefen titin naje ban ankara ba se wata babbar mota na gani gabana ta taho da wani bala'in mugun gudu. "TASHAAAA!!!" Haka ƙirarn sunan nawa da yay ne ya sanya ni tsaiwa chakkk tsaƙiyar titin ina rumtse idanuna, haɗi d adda'a wa yarana ALLAH yasa su gama da duniyar lafiya domin ko ba tantama nasan ni yau tawa ta rigada data ƙare. Cikin zafin nama se gashi ya isa gabanta tare da janyo ta ta dawo jikinsa. Ni kuwa jin yadda aka janyoni ne ya sanya ni tura shi da hannayena duka biyu. Domin nasan shi ne ba kowa ba, Amma madadin na ji ya matsa sema ji nay da nayi ya sake tsayuwa chakkk yana haɗeni da jikinsa, Kafin kuma Ahankali ya zare hannunshi daga kan waist nawa yana rabani da jikinsa tare da tsayar dani akan ƙafafuna, idonsa kan fuskana yana kallon yanda nake a ƙanƙame har lokacin idanuna gam gam cike da tsoro,yana kallar yanda pink lips nawa ke wani irin shaking da yasa dimples nawa na lomawa, ata sanadiyyan yayewar da liƙab nawa yayi. Ahankali ya shiga motsa lips nashi cikin daddaɗar muryansa ya furta. *"TASHAAAA"* Ashe tun a lokacin daya bayyana gabana ya kawar damu daga motar, wanda tsananin tsoron da nake cike ne ya sanya ban ma san lokacin da akayi hakan ba. Wani shegen murmushin gefen baki ya yi yana zuba mata fararen idanuwarsa. "Zaka bani hanya ko kuwa sena ɗauke fuskarka da mari sannn?." Ta yi maganar babu ko alamar tsoro ko ladama a cikin face nata. "Za ki iya duk abinda zakiyi tasha, Amma wllh babu inda zan matsa idan har yau baki amsa soyayya taba a karo na biyu..... Ya ƙarasa maganar tamkar wani zararre. _ꨄ Cike titin yake da motoci wanda ba komai ne ya haddasa hakan ba sai wani uban shegen go slow da wata shegiyar Black car ɗin da AJ MAJEED ɗin ke ciki. Yayi crossing ɗinta akan titin yadda ta rufe titin completely duk glasses dinta tinted ne. dan haka ba'a hangar wanda yake cikin motar,mutane sai hayaniya suke. Wanda kallo ɗaya zaka ma motar kasan cewan ba ɗan ƙaramin Kuɗi aka narka wajen siyar motar ba. gurin ya cunkushe mutane sai hayaniya suke yi, wanda basu san asalin abinda ya haddasa go slow ɗin ba. "YA RABB!" Ta faɗa tana wani irin fesar da iska ta cikin bakinta me zafi. Zuciyanta ma mata wani irin suya sosái da wannan cin mutuncin da AJ MAJEED ɗin ya mata, shi fa ba ƙaramin Mutum bane, shekaru sun fara ja masa duk da kasancewan idan ka kalleshi a ido baifi ka bashi irin 30 year's ɗin nan ba, amma kuma a zahiri ya na gaskiya ma ya rufawa 40 year's baya. Wani shegen takaicin sane ya sake ƙume ta dan haka ma bata san sanda zuciyanta ya ingiza ta gareshi ba. Marfin car ɗin kawai ta kama tana buɗe wa tare da yowa woje dashi, idnaunta taff da ƙwalla ta ɗauke kyakkyawar face nashi da wani shegen kalan bahagon mari. Tare da furta. "Duk meye hakan? Wai kai a tunaninka da kayi hakan kayi zaton zaka sama soyayyata ne ASAAD? To wllh banji zan soka Bama sema ƙara tsanarka da nayi I hate you ASAAD! And na tsake tsanar da ban taɓa kowa kalan taba!! I hate you ASAAD JUNERD MAJEED...... Daga nan ta jefar da hannunsa idanunta ko gani bayyi ta soma tafiya tana jin tamkar akan gajimare take. Wata farar mota ce tasha gabanta wani kyakykyawan matashin saurayi sosái yana leƙo kanshi ta window'n motar tare da furta. "A gaskiya kin burgeni Hajiya, da za'a bani wannan damar nima dana biyo sahu ALLAH ya ba mai Rabo Sa'a, domin da gani keɗin ta mai tsananin Rabon c..... Gummmm yayi da bakinsa sakamon buge bakinsa da Hameed yay,Wanda Ashe shima yana daga jerin wanda motar ta tarema hanya. Se famar wani huci yake tamkar kububuwa, "Idan ka sake kuskuren yima Matana magana wllh sena rufe ka" ya furta don se lokacin yake sanin ita ce ma ashe. Kallonta yayi tare da furta, "Ya miki dai-dai ashe dama irin abinda kike aikatawa kenan? Shi yasa kika tashi hankalin ki har seda kike kashe AURENA dake kanki, don ki fita maza na miki irin haka kenan. To wallahi ko kiso ko kada ki so ayau ɗin nan ba sai gobe ba sena meda AURENA dake kank....... Bammmm haka yaji anyi sama da nasa bakin shima. "Se dai ka sani ka zo a MUMMUNAN LOKACI, domin kuwa tun da har kayi kuskuren Rabuwa da ita, to la sani ta zama ba taka ba har Ƙarshen Abada, dama channnn ALLAH ya riga da ya gama tsara cewan TASHA ta wace tun daga farko. Ka sani rabon yaranka dake tattare da ita ne ya sanya ta aure ka, kuma ta gama zazzage maka kayan ka SO dan haka yanzu wannan lokacin nawa ne karka ce zakayi kuskuren kutsa kanka cikin soyayyata!!!....." Haka yaji sauƙar kalaman AJ MAJEED ɗin tamkar wanda ya watsa masa garwashin wuta a cikin zuciyarsa. Su dukansu kafin su ankare tuni harta faɗa cikin wani keke napep yayi gaba da ita. Worning me tsauri AJ MAJEED ɗin ya dokama Hameed ɗin yana faɗawa cikin lafiyayyar motarsa, tarin gurds nashi na take masa baya ciki kuwa harda driver'nsa da yace ya fita sanda zaije wurin Aysha'n. _ꨄ Me napep ɗin na sauƙeta ko gidan bata kai ga shiga ba taji gabanta ya faɗi ganin Bappa'n ta tsaye tare da samarin gidan wajen su biyar, tare da wasu mazan anguwar kuma duk hankalinsu kamar ba'a kwance ba, don haka tayi saurin Isa gare su ko me napep ɗin ma bata sallama ba, yaya Habu ne ta biyashi. Tana zuwa ta tsaya gaban Bappa'n ta ta furta. "Na shiga Uku Bappah meke shirin sake faruwa kuma dani me zafi haka?" Tayi maganar domin irin kallon da taga Bappa'nta ke binta dashi me kama dana tsananin tausayinta. "A'ISHA ki shige ciki duk kan wani tsanani yana tare da sauƙi muddin bawa ze jure ma hakan!" Yana faɗa mata wannan maganar ta san shikenan wani iftila'in ya sake faruwa da ita kenan. Don haka idanunta ko gani baiyi ta faɗa cikin gidan. Wani kalan sagewa taji ƙafafunta sunyi don ganin mutanen gidan tsugunne a bakin parlour'n Ummanta, gefe guda ga Amaan nan tare da little Aysha idanunsu jajur. Da wata kalan sassarfar ta isa ga AYSHA data taso tayo kanta da gudu. Rungume yarinyar tayi tana jin yanda ƙirjinta keyin kamar ze ɓalle, "Mamy Áshman!, Áshman babú ya tafi babu mota ta kaɗe shi tabi ta kansa ko shur....... Tsittt tayi sakamakon jin da tayi mamy'n nata ta janye ta a jikinta da ƙarfin gaske, wani zaman ƴan ɓori tayi wata zuba na tsatstsafo mata. Kafin ta fasa wata ƙara me

Chapter 11 of 12