Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 12
ta fara tunanin rayuwata daki daki.... Duk me ya jawo waɗan na abubuwan haka da suke ta faruwa da ita har haka? Shin wai wacece ma Aysha'n kanta dan haka ta faɗa duniyar tunanin rayuwarta tun daga farkon fari.... A take tunaninta ya daka tsalle yayi baya daga inda ta fara sanin ko wa ce ce itaaaa.... *SOME YEARS BACK* Ban san da me zan fara muku ba ko nace ta ina ya kamata ace mun fara? Amma kafin haka. Da farko dai Ni! Sunana A'ISHA MUSTAPHA WAZEEE. Iyayena haifaffun garin Bauchi ne wanda kasuwanci ya kai shi Kano da zama tun yana matashinsa, Anan ya haɗu da matar sa ta farko wato Mama uwar gidan sa kenan kafin shekara uku da aurensu ya haɗu da Mahaifiyata ƴar asalin garin Kanon dabo ya aura itama...... *BY AMMEY LAYLERH ✍️☑️* _Mu haɗe a page na gaba kawai don jin cikkaken tarihin rayuwar Aysha mustapha wazeer da kuma irin gwagwarmayar Rayuwar da aka sha fama da ita kafin hakan....._ _Idan kun shirya bin alƙalamin AMMEY LAYLERH ✍️ to ni me muku maraba lale ceeee dan haka go ahead kai tsaye mu nausa cikin asalin labarin ɗin kai tsaye 💃💃💃💃._ _Hajiya wllh karki bari ayi tafiyar nan babu ke domin kuwa ta musamman ce be ɗauke da salo salo babi ² bi da bi na irin ƙalubalen data ringa fuskanta In da In Sha ALLAHU yanzu ne hasalin labarin ɗin ze soma🤸🤸🤸💃_ 08104493215 🌏𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐🪐 𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚🤦 ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Official Mirrah💐 ♡ Page 5&6 ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *_𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭_* Best kayan kwalam 09025859622 or 09163353050 *END OF DISCUSSION PACKAGE* Now available in- candies package stop in and stock up on a sweet piece of summer! 🍬🍔🧆 𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭: ce ta shirya tsafff domin kawo muku. Samosa Spring rolls Filled doughnut Glazed doughnut Puff puff Shawarma Cupcake Birthday cake Bento cake Egg roll Milk cake Candy's Alewar madara Gullisuwa Tsami gaye Coconut laddo Milky gireba Albishir Mandula Sayen daya ko sari muna aikawa ko ina cikin aminci muna karɓar order bikin suna ko aure Location zamfara state ,gusau What's no :-09025859622 or 09163353050 Hajiya karki bari wannan garaɓasa ta wuceki domin taken mu shi ne 𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝘿𝙀𝙇𝙄𝙂𝙃𝙏 Koda kuɗinka seda Rabonka... Se kun zo ♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Aurensu da Mahaifiyata Khadijah da shekaru biyar ALLAH ya sake haɗasa da Baba Ladiyo ƴar asalin garin Katsina. Mama data kasance uwar gida tana da yara da bakwai cif. Yaya Khaleel shi ne babban ɗa a gidan kafff ɗan kuma Mama na farko, se Aunty juwairiyya, Yaya Sulaiman, Aunty Na'ima, Se Khariyya da Anum da suka kasance twins ne se Autarta Mufeedah. Se Ummanmu data kasance me yara biyar a gidan. Aunty Fa'izah ita ce babba a ɗakin mu kafin ni me bi ta wato A'isha, se ƙanwata Bilkisu, Maryam,da Khairat. Haka muka kasance ƴaƴan Ummanmu kuma daga kan Khairat haihuwar ya tsaya mata wacce take me shekaru goma sha biyu cifff sa'ar Amaan ce don kusan lokaci ɗaya muka haihu nida ummana.... Se Baba Ladiyo me yara takwas a gidan kuma itace har yanzun take kan haihu wacce ita ce ta karshe amma kuma duk ta su yawan yaya. Ƴaƴan ta duka maza ne bakwai cifff de macenta guda ɗaya itace kuma babbar yarta Hajara....Kowa yasan gidan Alhaji Mustapha wazeer yasan gidane da yake tarin iyalai, wanda yake zaune da Rufin ashirin ALLAH domin kuwa Bappa'n sanannen ɗan kasuwa ne sosai kuma manomi. Duka yaran gidan mun taso cikin wani irin tarbiyya da kulawa iyaye uwa da uba. Domin munfi ƙarfin komai na Rayuwar yau da gobe. Mahaifinmu ba mutum bane me duhun kai domin kuwa kafff cikin yaransa mata babu wacce batayi makarantar gaba da Sakandire. Domin a cewar sa a dai wannan Rayuwar ilimi shi ne gaba da komai kuma wannan ɗin haka yake komai na Duniyar tafe yake da ilimin boko dana arabi.... Tun Ina ƙanƙanuwar yarinya kowa yasan tsohon buri nane zama ƴar jarida (Journalist). Kwarai a duniya babban burinane na naga na zama ɗaya daga cikin shahararrun ƴan jarida..... Ko dan farkar da ƴan uwana mata yawancin kusa kuran da suke aikata game da aibanta macen da take haifar ƴaƴa mata. Kamar yanda dangin Bappa'n mu dama kishiyoyinta ke mata habaicin bata da Ɗa Namiji duka yaranta matane dan haka wahala kawai ta haifa. Se dai sammm hakan bai taɓa damun Ummanmu ba sema wani bin takanyi Murmushi ne kawai ta kawar da kanta gefe bata taɓa tanka musu. Amma hakan ba shi ke nufin gobe ma ba zasu yada mata habaicin ƴaƴan mata gayyar hawala bane. Wai a cewarsu idan duk akai rashin dace basu sama gidan Rufin asiri ba to kamar ka se da akuyar kane ta dawo kuma tana ci maka danga. Wannan abu na ƙona raina da sauran ƴan uwana barin ma Aunty fa'iza data kasance ita ce masifaffiyar ɗakinmu ita da Bilkisu duk wanda ya musu duk girman sa basa ƙyaleshi tun Ummanmu na dukansu harta tazo ta dena ta zubawa Sarautar ALLAH kawai Ido. To ata nan ma se Umman ta samu wani ɗan rangwamen tun da matan Bappa'n sukanji tsoron mata abu kamar baya kafin ƙarfin mu ya kawo. A tawa fahimtar da abinda shekaran jiyanka ta zo maka dashi da kuma abinda yau ɗin ka zata zo maka da shi zan iya cewa duk ƙaddararka ita ke jagorantar komai tun daga lokacin shaƙar numfashin ka na farko har zuwa samun tsahon rai ga kowanne halitta a cikin Rayuwar ko wanne bawa. Ta wani fannin kuwa idan aka duba A zahirin rayuwa ni ɗin ba kowa bace face wacce ƙaddara da kuma ƙalubalen Rayuwa suka jima da lulluɓe babina.... *MAFARI* Na taso cikin wani irin kwarin gwiwa da kuma jajircewa a kan komai nasa gaba nawa. Wannan shi ne dalilin daya sanya na kammala Secondary School ɗina cikin haƙuri da juriyar Rayuwar har ALLAH yasa na kammala secondary. Daga nan na shiga University a jami'ar Ado Bayero. Cikin Aminci na UBANGIJI komai nasa gaba da sauƙi yake zuwar min yayin da na zurfafa kaina sosai akan aikin Journalist nawa da har outing aka fara fita damu da ake zaɓar masu jajircewa da naci sosái akan abin. Lokacin ƴaƴata fa'iza ta kammala karatun nata harma anyi bikinta anan cikin garin Kanon, Ganin irin yanda kowa ke yina makaranta kuma tana yayina yasa hankalin mutane fara dawowa kaina ya zaman kowa so yake ya ƙulla abota dani koda kuwa ace iyata maganar fatar baki ce. Se dai ina da wani irin kamun kan da ma kowa nake shiga cikin Rayuwarsa ba. Wanda wasu mutane daban suka ma hakan wata iriyar fassara da cewa baƙin hali ke gareni. Naji hakan kuma ina kan jin hakan se na toshe kunnuwana tun da dai ni har zuciyana nasan hakan ba haka yake ba. Domin ni! Wata irin Mutum ce meson kowa ya barni nayi Rayuwana Ni kaɗai na ba tare da kowa ya shigo cikinta ba. Ana haka ALLAH ya haɗani da Masoya na gaskiya na kuma Amana Ameenah Abubakar da Jameelah Sani. Waɗan nan sune suka zame Rayuwata acikin school ɗin har lokacin da muka kai mataki na ƙarshe wanda a shi ne makarantar ta ware wasu jajirtattu Sosái daga cikin mu da muje Abuja domin tace iriyar fikirar da muke da ta fannin aikin namu... Tun farkon haɗuwa na da Ameenah da kuma Jameelah Makarantar ta bamu matsayin *SELFISHNESS ASSOCIATION AWARD* saboda naci da kuma jajircewarmu akan duk abinda mukasa gaba se mun cimma Nasara.... *ROYAL KINDNESS* Shi ne suna na biyu da Duniya ke ƙiranmu dashi. For sure tabbas mune kuma muka sanyawa kanmu wannan sunan na *Royal kindness* ɗin. Zuwanmu Abuja shi ne mabuɗin ƙaddara ta ta farko domin kuwa a wannan tafiyar ne ALLAH ya haɗani da Hameed Ahmad.... *MABUƊIN KOMAI* Sosai naji tsoro da kuma fargaban hawa jirgin lokacin da muke dap da shi ga don kuwa wannan shi ne karo na farko da shiga jirgin. Sedai na danne tsoron hakan da kuma shanye kayana ba tare dana bari ko abokan tafiyana sun lura da hakan ba, _wata sabuwa_ na faɗi a raina ganin kuma ni aka bama setin window. Dan haka kammm wannan karon Sosái tsoro na ya bayyana muraran, Amma se su Ameenah suka kwantar min da hankalin babu abinda zai faru gashi kuma duk an rarrabamu ne kowa wuri daban. Ahankali nakai zaune ina ƙanƙame jikina wuri guda zuciya na na min wani irin Mahaukacin bugu bana wasa ba. Wani kalan toshe kunnuwana tare da Runtse idanuna nayi loƙacin da jirgin ya fara landing na tashi. A wani kalan hankali da slow jirgin ya fara tashi wanda hakan harya sani jin zuciyana ya sama nutsuwa sedai ban farka daga hakan ma jirgin ya wani kalan zura a guje tamkar wanda aka zabura. Hakan ne yay sanadiyyar daya sani wawurar hannun wanda ke kusa dani ina wani irin damƙar hannunsa da mugun kyaun da idan har ba ALLAH ne ya tsare ba tsabb zan iya masa rauni... Ganin hakan da nai ne ya sanya wannan matashin dawo da hankalin sa kachokamm akaina yana Runtse idanunsa da karfi Sosái sakamon jin yadda tsigogin jikinsa suka tashi sakamakon wani azabar ciwon da yaji hannunsa ya ɗauka lokacin da nake sake nutsa faratan hannuna cikin fatar bayan hannunsa.... A kuma lokacin ne jirgin ya daidai ta wanda ya sani dawowa nutsuwana wanda se a lokacin nake lura da irin yanda har lokacin hannune ke riƙe da nashi idanunsa Lumshe. Saurin sakin hannunsan nayi wanda hakan ya sashi buɗe idanunsa da suke a Lumshe yana sauƙe kyakykyawan idonsa a kaina. inda ya bi da kallo nima nabi se na kalla yanda na masa rauni Sosái har jini na fita ba da yawa ba kaɗan amma. Saurin fiddo ido waje nayi tare da faɗin. "Amm don ALLAH kayi haƙuri wllh sammm bana sane naji maka ciwo don ALLAH kayi haƙuri" nayi maganar ina zaro plaster na rufe masa ciwon. Idanunsa ya sake ja yana lumshe su kafin har zuwa lokacin dana gama filasce masa ciwon kana ya buɗe idonsa a kaina daidai da sanda nake sake ce masa. "Ina jin tsoron tashin jirgin ne, tsoron nema yasa bansan na aikata hakan ba kayi haƙuri plsss" Idanunsa Masu wani kalan jan hankalin me kallonsu ya kalleni dasu tare da jansu baya luuu kamar ze Lumshe su sedai be kai ga lumshewarba ba kuma ya buɗe yana bina da wani mayen murmushin da ya daki har tsaƙiyar zuciyana. Wanda yasa har ni kaina bansan loƙacin dana sakar masa da nawa murmushin ba ina jin yanda zuciyana kuma ke lafawa tare da jin mutumin yana ratsa ko ina na jikina ilahirinsa... Daga haka na koma ina kwantar da kaina jikin kujerar da nake a har bansan sanda bacci yay awon gaba dani ba. Se ji nan a wani kalan hankali cikin nutsatstsiyar murya yana faɗin... "Hiey Beauty!!!.. mun ƙara so..... Dake bana da nauyin bacci firgigit na farka ina sake komawa nutsuwana ganin yadda yake a kaina yana tashin nawa, Ja baya yayi ni kuma ina yin hamma tare da miƙewa tsaye ina sabar handbag nawa Ina gyara mayafin dake jikina me ɗan girma.... Se dai taku ɗaya nayi ana biyun naji an riƙe mayafin nawa. Wani kyakykyawan murmushi ya sakar min yana me furta.... "BEAUTY tafiya babu notice haka? Ko kina son zuciyana ya buga ne a ta dalilin rashin sake jin koda muryanki ne bare kallonki Uhm?" Wani irin daskarewa naji gaba ɗaya jinin jikina nayi gaɓoɓina na ɗaukar wani kalan sanyi sosai. Numfashi na shaƙa jin kamar bana shaƙar shi da kyau se kuma nayi saurin zare mayafina ina ɓacema ganinsa... Wata lafiyayyar mota ce tazo ɗaukar mu daga babban gidan jaridar Abuja. Yayin da shi kuma ya shiga napep domin don ba'a san da zuwan nashi ba kuma dama can baison ma kowa yasan ya shigo Abuja'n... Wani lafiyayyeyan masauƙi me kyau aka sauƙe inda har mu gama 2weeks namu muna gidan ne. Dake duk a gajiye ake ka nace a gajiye nake kuma basa ban ba zubewa kawai kan gadon dake mazaunin nawa nayi ko wanka ban sama arziƙin yiba wani kalan wahalallen bacci yazo ya sake awon gaba dani, ban farka ba se bayan sallar la'asar dan haka koda na farka da wanka na fara kafin a kawomin lafiyayyen abinci me rai da lafiya naci dan su tuni harma sun manta da sunci tunda su ba wannan bane karonsu na farkon hawa jirgin. Kowacce a cikin su ƴar masu kuɗi ce sosai dan duk sunfimu kuɗi sedai muma ɗin Alhamdulillh kawai zamuce... Daga nan kai tsaye aka fita damu domin soma gudanar da aikin tacewa da kuma kwarewar tamu domin aka irin rawar da zamu taka da kuma irin mutanen da zamu jawo hankalin su a iyaka 2weeks kawai.. Tun da na farka Idanuwan sa kawai kemin gizau samm na kasa mantasu kamar yanda naso sharewa. Sema tsinta na da zakai ni kaɗai ina yawan sakin murmushin da bansan kona mine ba. Kowa akace ya tsara abinda zai jawo hankalin al'umma kansa dan haka na koma baya Ameenah da Jameelah suka fara gabatar da nasu dama sauran mutane kafin ni.... A lokacin da kumnuwane ke maƙale da Microphone ɗin idanuna Lumshe suke ina amsar bugun da zuciyana kemin akan mutumin da ko sunansa ban sani se muryansa kawai dake min kai da komo tare da waɗan nan Idanuwan masu kama da jansu ake akan maganaɗisun kyau da haske... Dan baka wani murmushin me kyau da jan hankali na saki tare da buɗe karamin bakina me kama da gidan tsutsa na furta.... "Hieyyyhhhh!!!! Hello Barkanmu da farkon fara saduwa da masoyanmu a wannan sabon wurin da muka tsinci kanmu ayau, Barkanmu da lokaci Ni *AYSHA MUSTAPHA WAZEER* nake ma Masoyana barkan da yinin wannan Rana. Me cike da ababen tarihin da bazasu taɓa shuɗewa ba har gaban abada abadan kuwa.. A kowacce Rana mun saba tattaunawa akan batutuwa masu ban sha'awa duk dai a cikin WANNAN shirin namu me suna BARKANMU da WAR HAKA... Yau kun san akan me ne zamu tattauna? Akan tafiya! Kwarai Rayuwa wata tafiya ce domin a yayin da kake cikin tafiyar nan taka zaka haɗu da mutane da yawa haka zalika zaka iya Rabuwa da mutane da yawa.. Wasu kuma su zamo abin tunawa amma muna samun ɗaya zuwa biyu waɗan da ba zamu iya mantawa dasu ba!, Waɗan da idan muka tuna su fuskokinmu dukan wanzar da wani murmushi, Wasu kuma yayin da muka tunasu se muji zuciyoyin mu sun raunana ga Rashin su..." Daidai da lokacin da Hameed ke zaune kan doguwar plastic chairs ɗin dake balcony na gidan daya sauƙa Ipad nashi riƙe a hannunsa yana kallar ta. Wani kalan Lumshe idanunsa yayi yana irin fesar da numfashin nan, idanunsa masu kama dana mashaya ba can na zube a kanta. Har zuwa sanda take motso Lips nata kafin a natse kuma ta buɗe idanu yayin da fuskanta me ɗauke da Murmushin ke ci gaba da faɗin.. "Dan haka idan da akwai wata wanda kuke kewa akan sanin inda suke, ko kuma sanin halinda suke ciki wanda hakan ke matuƙar damunku zaku iya tuntuɓarmu a kafafen sadarwa ko lambobin mu masu kamar haka 081........... Kafin nan masu sauraren mu Ku sha ƙata da wannan waƙar... Na sakar musu waƙar Hamisu Breaker ta *SO DAƊI * tsabar daɗin da wakar kemin har wani lumshe idanuna nake domin kuwa dama cann ina masifar son waƙar. Daga nan wasan namu ya ƙare sedai tun kamin mubar wurin yarin jama'a suka dinga turo da saƙonninsu wasu kuma ƙira. Se da mukay Sallar Magrib kana mukabar gidan jaridar daga nan muka nufi masauƙi. *RANA TA BIYU, SANADIN FARUWA DA KULLUWAR KOMAI* A rana ta biyu daya kasance juma'a yi ce babbar rana yau kam tun sha ɗaya saura aka zo aka ɗauke mu sakamakon ƙira da messages na jama'a daya hanasu sakat. Se dai A Maimakon jiya dana kasance ni ce ta ƙarshe se ya zaman yau kuma Ni ce ata farko sakamon masu test mess ɗin da kowa AYSHA MUSTAPHA WAZEER yake ambato da muradin sake ji..... Sosai na sake dedata nutsuwa na domin kuwa kwana nayi mafarki da tunanin bawan ALLAH'n da ko sunan shi ban sani ba. Hannuna ɗaya nakai ina ɗan shafar gefen ƙeyata tare da ware idanuna da suke a ɗan kumbure like irin ina jin ba baccin nan, kamar jiya yauma dai a television ne ake haska mu kai tsaye dan haka yau dana fito da shirina tsafff na ɗan zare eye glasses ɗin dake idanuna tare da fuskantar dubban jama'ar dake gareni tare da ɗaga hannuwana biyu sama ina me furta.... "ASSALAMU ALYKUM WARAGHMATULLAHIE WABARAKATU!!, MAY ALLAH TURN ALL YOUR IN SHA ALLAH INTO ALHAMDULILLH!!!" Se kuma naja numfashi ina dakatawa tare da ci gaba da faɗin.. "I wish for you. Happiness deep down within, serenity with each sunrise success in each facet of your life close and caring friends love that never ends... Special memories of all the yesterdays A bright to day with much to be thankful for A psth that leads to beautiful tomorrow's. Dreams that do their best to came true and appreciation of all the wonderful things about you.. May you have a fantabulous and Mubarak jumuaah.... In Sha ALLAH Ameen 👏.." Daga nan na dakata ina haɗe hannayena biyu alamar ALLAH ya amsa. Kana naci gaba da fara bayani na cikin yarena harshen Hausa na fara da cewa... "Barkanmu da wannan lokaci masoya!, a wannan karon ma dai kuna tare da Ƙaunarku Sister AYSHA MUSTAPHA WAZEER A yau ma dai zamu yi shiri ne akan daidaito. A koda yaushe mun saba tunani akan mutanen da muke matuƙar SO Sosái,Muna so mu ga sun zo garemu koda sau ɗaya ne ba zato ba tsammani kuma se suzo, wannan shi ne daidaituwar muradi!!!"..... Daga nan na ɗan daga ta tare da rufe hannuwana da buɗe wa ina me sake furta. "Kafin nan bara bu ɗan leƙa ɓangaren Rayuwa!!!. A Rayuwa babu abinda ke tafiya kara zube, dole ne ka zama mai Haƙuri da tsare tsare masu kyau da kuma hangen nesa domin ribatar damammakin Rayuwa ta yadda ya dace...Ko kun san meke jagorantar ko wacce iriyar Rayuwa ƴan uwana, abokaina iyayena ƙannaina yayyaina????.... Se kuma ɗan yi shiru tare da sake fuskantar su da kyau kana na furta.... "Haƙuri da jurema duk tarin ƙalubalen daya fuskantoka me tafe da ƙaddara me zafi ko akasinta... A kowacce Rayuwa Haƙuri shi ne mataki na farko dake fara gina Rayuwar kowanne bawa, Idan akace kayi haƙuri bawai ana nufin ka gaza bane, A ahhh sema wata daraja ko martabar da Ubangiji yama... Ko haka kawai zaka kalla mutum yana cikin tafiya kace mar *YI HAƘURI?* Kun ga kuwa kenan dole akwai dalilin daya sanya ake baka shi dai wannan haƙurin domin kuwa shi ne mataki na farko wajen gina Rayuwar kowanne bawa Inji*ALLAH (S.W.T)* dan haka nake me son jawo hankalin iyayena mata da kuma ƙannaina kai harma da yayyaina maza da mata duk wannan abin namu ne... Domin Idan ka yi rayuwarka da tsari, to ba ka buƙatar gaggawa abin da ake yi da gaggawa yawanci ba ya haifar da ɗa mai ido. Ka yi aiki tukuru wajen neman abin da zai amfaneka a duniya da lahira, sannan kuma ka yi addu'a, duk wani abu mai kyau sai an wahala ake samu.. ....Kafin nan amma bara na bamu wata shawara kyauta.... Mu zama mutane masu Amana da juriya da haƙuri domin kuwa anan ina son mu dena ɗaukar ko wanne irin abu da zafi, don wata tafiyar bata sauri bace ze zamana idan ka ɗauki ko menene da zafi karshen sa baya taɓa yin kyau right?... Gashi kuma dai daga ƙarshen duk mutuwa zamuyi ayyukan mu ne zasu samar mana da rayuwa bayan mun mutu, Haka Ayyukan kwarai zasu zaba maka rayuwa mai daɗi akasin haka shima zai kasance akasin haka mu huta lafiya taku *ƘAUNARKU AYSHA MUSTAPHA WAZEER* Ke muku fatan Alkhairi 👏 da gamawa da duniya lafiya zamu da kata anan domin kuwa lokaci zaiyi halinsa, Rabbighfir warham wa anta khairur rahimeen (My Lord, forgive and have are the best of the merciful)👏👏👏👏" Daga nan kuma sauran suka ci gaba sallar zuhr shiya fitar da mu. Kana muka dawo muka ɗora daga inda muka tsaya har dap da zallar la'asar.... Sallamar mu akai se kuma ALLAH ya kaimu gobe. Directly Motar dake aikin kaiwa da komawa damu ce tazo ɗaukar mu, Sedai muna dap da isa ga motar wata farar bugaggiyar Bugatti Veyron ta iso har dap da inda muke tsaye itama... Kafin a hankali a wani irin mirza ƙofar motar bugun numfashi na ya bayyana kan diga digansa tsaye gaban mu ko na ce gabana. Wani irin dokawar da seda na dafe ƙirjina zuciyata tayi ganin mutumin da banyi zata ko tsammanin gani ba tsaye gabana... Amma kuma sena fuske abuna ina kaicema ganinsa da nufin in kai ga shiga motar da ƴan uwana suka rigada suka shiga, Se dai ya tare hakan ta hanyar sanya hannunsa ɗaya ya rabani da shiga motar ta hanyar dafa motar da yay. Wani kyakykyawan murmushi ne ya wanzu samar fuskarsa tare da kallonsa da idanunsan da sune abu na farko da suka fara vilibian nawa.. "Zan wuce!" Na faɗi cikin dakewa da tsare gida domin karyay saurin rantoni. "Zaki wuce ɗin amma idan kin sallameni ba" kallonsa nai da sauri jin wai idan na sallameshi to ni kuma me yay min da zan sallameshi?. Na tambayi zuciyana a bayyane kuwa sena ɗan kalleshi tare da furta. "Ohhhh So Sorry ya hannunka?" Na faɗi irin se yanzun nan na gano shi. "Ba wannan bane tsarin yay maganan yana sauƙe min tsadaddar wayarsa kan hannuna yana cewa insa may number na. Ɗan wara idanuna nayi tare da cewa.. "NUM???.... Ya ƙarasa min da cewa "BER....... Leƙowar Ameenatou tana furta cewa "Royal bleu waikam zamar me kikeyi ne waje ko yanayin wurin ne ya miki dad..... Se kuma tay shiru, shi kuma ya ɗaga kai ya na kallonta wannan shi ya bani damar saurin sunkuwaya ina shigewa cikin car ɗin ina manta cewan wayansa na riƙe a hannunsa jikina na karkarwa Sosái.... Shi kuwa wani irin janye idanunsa baya yayi yana me furta.... "ASHNOORRR....... *BY AMMEY LAYLERH ✍️☑️💪* _TO shin ya kukaji da yanda salon Ya fara, karfa ku manta wannan shi ne farkon lamarin tafiyar da muka farata a baybaye yanzun ne hasalin komai ze bayyana_ _Shin kun shirya bin alƙalamin AMMEY LAYLERH ✍️ don jin yadda labarinta zai soma?_ _Salon tafiyar akwai ɗaukar hankali nake ga 🤗 🤗 mafaka da damar ki ɗaya ce shi ne ki mallaki naki tun kan lokacin ya ƙure miki ƴar uwa..._ _Ina me sanar miki cewa idan baki taɓa Karanta ire-iren littatafan AMMEY LAYLERH ba to maza ƴar uwa hanzarta ki taho domin kuwa wannan tafiyar tasha banban da kowacce iriyar tafiya..._ _To albishrinku ga wata sabuwar tafiyar ta samu mai cike da tarin rikita rikita kalubale me tafiya da ƙaddara, da ma abubuwan da baku zata ba_ 08104493215 🌏𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍𝙈𝙐🪐 𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚🤦 ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Official Mirrah💐 ♡ Page 7&8 ✯ *🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION💫* (J.W.A) ♡ _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* *_𝐌𝐚𝐫𝐲𝐚𝐦_𝐝𝐞𝐥𝐢𝐠𝐡𝐭_* Best kayan kwalam 09025859622 or 09163353050 *END OF DISCUSSION PACKAGE* Now available in- candies package stop in and stock up

Chapter 3 of 12