Dangin miji, Su Yaya Amar ne kawai suka tare a dakin Hajia Yaya, sunce su suna Auren da ita, haka suka dunga shan hira da ita, dayake ita akwai son jikoki,
Washe gari Asuba ta gari Hajia Kilishi ta kamo Hanya, haka Daddy UK shida Matarshi da ya Aura A can, Hajiya Kilishi kuwa ita da Talban ta, karfe goma ya musu a Zaria nan da nan gida ya cika, lbr ya karade gidan fulani kowa yasha Mamaki, haka Kilishi ta dunga lallaba Mama kamar zata mai data ciki, Ummimi na Zuwa taje da gudu ta rungumeta, Dallah dagani da kika mana gudun Hijira, Toni ba ta kanki nakeyi ba yanzu ta kan ya'ta nakeyi, Aka kwashe da dariya turo baki tayi Momy tace kinji zo Baby na ni ban dena yayinki ba, "yauwa Momy na, can suka ga An fara shigowa da kayayyaki na alfarma Kama daga abun ci da Abun sha, da akwatinan kaya Kala Kala, wata Balarabiyan matane ta shigo rike da wata yarinya irin su daya da Ummimi, tana Zuwa ta tsaya tana kallon duka yan dakin aiko da sauri ta karasa kusa da Mama ta rungumeta tana fadin MashaAllah, Alhmdulillah yau kukan mijina ya kare, Mun gode Allah, kowa ka kallah a gurin farin ciki fal ranshi, bayan an natsa Daddy UK ko yaki sakin Mama tunda ya rungumeta a jikinshi, daka ganshi kasan ya tsufa sosai sai dai jin dadi ya boye tsufan nashi, ita sai jin kunya takeyi, tana yin motsi kowa zai taso yace mata lpy, Aiko Aunty mu taga karyar Arziki da gata da takeyi ma Mama gori, kunya duk ya isheta, ta rasa yanda zatayi don Daddy UK Akwati guda aka bata na tsaraba da ita da yaranta,
Bayan kwana biyu komai ya lafa aka kira taro Hajia Yaya da Hajia Kilishi, Bayan an zauna ne, suka gabatar da abunda yake ransu Maganar sa ranar Ummimi, da Mubarak, nan aka sa ranar sati biyu, Yaya Ameen ne ya mike yace nima fa na samu mata kawai aje kano a tanbayo mun Auren nan a hada duka ayi rana daya, "iyye mare kunya Kilishi ne tace haka waye matar to, ai da gudu RALEEYAT ta tashi ta gudu don taga Alama YAYA Ameen ba kunya gareshi ba, dariya gaba daya akayi, "Yaya Umar ne yace "ai gunda layi ya dunga matsawa ko a bamu guri muma, "iyyeh gidan ku Umari nace, ta wurgoshi da pillow data kishin gida dashi, kaucewa yayi yana dariya Hajia Kilishi ai gskya na fada ko Jafar? "Eh mana Aboki to munji kai Habibu da Habibu da Jibrin da Yahaya da Ahmadu kundai ji yaron ku yana son kuje ku nema mai Aure, "Eh Hajia ai yau Zamu tafi, toni Anata Maganar Aure banji kunyi na yarana bane, inata kawaici naga kun share, "suwa kenan,? "Su Zahra da Amar mana, "ok ai duk tare za, ayi da nasu Mubarak din Hankalinki ya kwanta yanzu koh? "Sosai ma nan taro ya watse,
"Madam ya kamata a dunga kulani mana don Allah bakya ganin su Zahra ne da Yaya Ameen yanda suke shan luv Amma ni sunan an Amince mun din ne amma anki bani daman in nuna irin Soyayyan da ke raina, "Naji zan baka dama, Amma da a sharadi har sai kace ka yafe ma Billy sannan ka nuna ma yayanta mahimmancinta a garesu, ka dunga kaisu gurinta su saba da ita kafin ku koma, "haba baby wannan sharadin yayi tsanani da yawa, gskya bazan iya ba, to shikenan juyawa tayi ta tafi ta barshi a gurin a tsaye, da sauri Billy ta juya ta labe tana share hawaye lallai Ummimi ta cika yar halas duk irin muguntar dasukayi mata Amma ita kokari take ta nema mata yafiya take yi, Abunda ta kasa ita, wayyo rayuwa, niko nace Billy kadan ma kika gani,
Haka akaje aka nemama Yaya Ameen Auren Raleeyat inda duk aka sa rana daya dana su Ummimi, nan su Momy suka fara shirin komawa sbda Biki, Kilishi ta dage sai da Mama zasu tafi ita da Daddy UK, su daddy suka haba su barta mana bayan bikin su Ummimi sai taje duk dangi su ganta, da kyar suka yarda,
Haka suka shirya suka dunguma sai Yola Yaya Mubarak duk da haka Basu daidaita da Ummimi ba,
To nima nace bari inbi ayari inje Yo, la daga nan na in biya gidan su sis Adama, ๐๐
KUCIGABA da bin yar mutan Zazzau โ๏ธโ๏ธโ๏ธ
Share
Vote
Comment โ๏ธโ๏ธโ๏ธ
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: ________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*๐ฆ{Arewa ginshiฦin al'ummah}๐ฆ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com๐๐๐๐๐๐
GIDAN GADO
๐๐๐๐๐๐
(LOVERS AND WEDDING)
WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
๐น๐นEPISODE SIXTY TWO&THREE๐น๐น
Sadaukarwa ga duk wata mai suna Zainab, Takwarallenas duk ku fito na baku kyautan page guda I love Zainab๐๐๐.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
"Amincin Allah ya tabbata gareki My sweet Baby, "tare da kai lafiya kira cikin dare Haka? "Haba laifine don Mutum yayi kewar Matar shi, "Oh har na zama ma matar taka kenan? "Eh mana kin Zama ko kin Manta na biya Sadaki ne daurawa ya rage,? "Uhmm ina jin sleep sai da safe, haba Baby na please ki tsaya muyi mgna Naji na yafema sautin zanzo jibi zanzo da Yaran sai ki kaisu gurinta, Amma ni ban son ma ganinta, "Da gaske Masoyi, da gske mana bashi ne dai kawai bukatarki ba, duk yanda kikeso haka za, ayi ranki ya dade, "thank You Hubby muuuaaah๐kit ta kashe wayanta tana dariya, shiko daskarewa yayi da wayar a hannun shi, Imagine yau Nusaibat ne ta mai kiss aiko duk randa suka hadu sai ta mai, juyi yayi ya fada gado, ya rungume phone din shi kawai yana tuno sautin fitan Kiss dinta yana imagine yanda zatayi da lips dinta, kawai ji yakeyi kaman ya ganta a jikinshi ne ya rungumeta, "wai kai Mallam na shigo inata magana kamun shiru, sai wani Murmushi kakeyi, "kai Besty bakayi ba, kazo ka katseni ina cikin shaukina, har ka gama ba filawan ruwa kenan, ka wani zauna gaban yarinya kana ta wani shirme ko kunya, shiyasa na tashi na baku guri, "hhhh sannu mister Big naga kaima yanxu ka gama naka wayan da yarinyar ai duk daya muke da kai, kaga Zahra ta ma ta ba Baby two Months fa, "To sai mene Dallah Mallam ni Kara gaba ka barni in gama tunanin Baby na, kar kuma ka Kara cemata Baby ka kira ta da sunan ta Ni ne kawai da Momy dasu Daddy muke da right din cemata Baby, "to kishin ya motsa kenan kadai san kanwata ce kabini a hankali ko in fasa baka, "to sai mene nima in fasa baka kanwata Zahra, "kai wlh baka isa ba, dariya duka sukayi suka tafa, "kaji Besty ka kwana kawai gobe in Allah ya kaimu ka rakani Zaria, "Ni Allah ya kyauta in rakaka tadi gurin tsohuwan budurwata da kamun kwace, "Kut da gudu ya bishi sukayo waje, da Daddy suka kusa bugewa ya kaucemusu "kai ku zo nan, karisowa sukayi Yaya Mubarak nata wani ciccin magani shi kuma Amar nata mishi Dariya, gamu Daddy, "waiku yaushe zaku girma ne iyeh, Ana shirin Auran ku kuke wannan shirmen,? "Daddy wlh wannan dan rainin wayon ne bai son zaman lpy, kudai fita idona in an girma a san an girma ko wlh a fasa Auren sai Next year, "kai Daddy wlh mun bari wasa ne fa, murmushi Daddy yayi ya shige gida abunshi, su kuma suka koma part din su,
Washe da safe Mamy ne da Zahra a kitchen suke hada break fast, "Momy to wai yaushe zanje Zaria ne, Nifa ina son ganin Bloody, "to in banda abunki shekaran jiya fa muka dawo, in kinyi hkr gida daya zaku zauna fa, "da gaske Mamy? "Sosai ma kuwa, Naji dadi wlh"to Nidai kwashe Abincin kije ki jera kan dining, "to Mamy na,
Bayan sun kammala ne Zahra ta shige daki don yin wanka, kafin su zauna cin abinci,
Kowa ya sauko cin abinci sai Zahra da take can take kal kalan kwalliyanta na fama, sai da Mamy ta kira ta sannan ta sauko, tun da ta sauko Yaya Amar ke satar kallonta, kowa yanata cin abinci shi, tana isowa taja kujerar da yake facing din Yaya Amar, gaida kowa tayi sannan ta fara zuba abinci, turo kafanshi yayi ta kasa ya takata, da sauri ta dago duka hada ido, kashe mata ido yayi, wani murmushi tayi mai, mai sanyaya Zuciya, lumshe ido tayi, Uhmmm murmushi Daddy yayi yana nuna ma Mamy Su Zahra da ido murmushi itama tayi tana karkada kai, Daddy ya fara tashi Sai Mamy itama ta bishi, "to Marasu kunya Mamy suna kallon ku kunata rashin kunya, sunkuyar da kai Zahra, tayi shiko yaya Amar ko a jikin shi, shima Yaya Mubarak din tashi yayi ya Basu guri, kaman yana jira kuwa ya dawo kusa da ita, "Haba my Kalby bakya son cin abinci da yawa fa, nikuma ina son inga kinyi katuwa fa, "Uhmm Hayaty inafa ci, "Nidai kawo in baki, haka ya karba dunga bata, tanaci suna hiran su, sai shagwaba take mai yanata lallashinta, har sai data koshi, suka dawo main Falo suka zauna, sunata hira,
Can Yaya Mubarak ya fito rataye da jaka, "kai Yaya Mubarak ina zuwa? "Zanje Gidan kilishi ne in dauki su Anwar da Iman Zaria zani, "lah da gske bari in baka Sakon da Momy ta bani na gurinta kace Momy zata kirata tayi mata bayani, ok yi sauri, don ban son shigan dare, "to, tana zuwa ta dauko ta bashi,
"Waye mai Sallama,? Oyoyo Daddy, Tsohuwa kizo Daddy mune yazo, "to fitowa tayi a,a Maigida za, aje ganomin kishiyar tawa ce, sosa keya yayi, "eh wlh Daddy ya fadamiki zan tafi dasu Anwar ko, "eh ga kayansu can ma nasa an hada musu, to godiya mukeyi, ku fito mu tafi koh, "Daddy damu zaka, zaka kaimu gurin New Momy ne, Eh my Yarana, to Amma Daddy ni ina son ganin Old Momy mu, Iman ne tace haka, shiru yayi ya rasa mai zai cemata, eh zamu ganta a can ko Daddy Anwar ne yace haka, samun kansu yayi da Amsawa da Eh, Kama hanyar fita sukayi, kilishi ta fito, "au yarana tafiya ba sallama? Dawowa sukayi da sauri duka suka rungumeta suka mata kiss a goshi, suka mata Bye suka tafi,
*************************
ZARIA
Ummimi ne ta dage a kitchen tana hadama Everlasting dinta girki, ita da Mami, sai zuba takeyi, "kai Mami kin isheni fa, "kai Aunty ke wai baza, ayi hira dake ba sai kice Mutum ya cika surutu, "kedin ne ai Mami disturber ne ke, "uhmm to wai haka zaki je ki dunga ma Yaya Mubarak din wannan zaman kuramen, tab akwai aiki, ni wlh aunty ma kamar baki je wata kasa karatu ba, baki wani waye ba, wlh ki tsaya wani fulatanci wata tazo ta kwace miki shi, dama ga shi dan gayu, wlh koni don ke aunty nace Amma kwace shi a gurinki bazai wani wuya ba shifa Aunty Namiji dan kulawane da tattali in baki kula dashi bakya tattalin shi gani zaiyi kaman baki sonshi, don haka wlh aunty ki canza hali Nidai shawara nake baki, "tabdijam Mami duk ina kika san haka, lallai zan gayama Hajia Yaya Aure kikeso irin wannan maganar ta manyance da kikeyi, ko wata uwar matar bazatayi haka, "kai aunty daga bada shawara kinga ma tafiyata na fasa tayaki girkin Sorry my kanwass rikota tayi, zomu karasa, sun kammala komai sun kai dakin Yaya Ameen tunda anan dama yake sauka, shi ma Yaya Ameen yaje kano ba filawa ruwa๐, bayan sun kammala taje tayi wanka Mami ta yi mata Make up, "kai Aunty na kin ganki ne kamar wata sarauniyar kyau, dole yaya Mubarak ya ban kudin kwalliyan nan,"Allah dai ya shiryeki my kanwass "Ameen Aunty na, yanzu sai jiran Ango koh, "yau da dauki Kulan can kije sashin su Billy ki kaimata, kema dai kin san ban zuwa sashin nan fa Aunty sai dai in kira miki Mufeeda ko Hauwah su kaimata, "Haba my kanwass ke ba yafiyane a rayuwarki koni da, aka ma abun na yafe balle ke, Billy tana cikin damuwa duk gidan nan kun bi kun tsaneta bafa ita ta aikata abun ba Mahaifiyarta tayi, meyasa bazakuyi mata uzuri ba? "Aunty kenan na tabbata da, ace ke kikayi ma su Billy haka bazasu yafemiki ba, Amma shikenan ya wuce kawo in kaimqta,
Shiganta sashin kenan ta ganta ta zauna tayi tagumi, sai da ta matsa kusa da ita ta mata magana sannan ta jita, "Aunty Billy gashi inji aunty mu, "kice mata ngd Allah yasa ka da Alheri ya Kara zumunci, "Ameen.
Karfe hudu na Yamma yayi ma su Mubarak a Zaria, suna shigowa Su Anwar sukayi sashin Mama kasancewar Basu mance gidan ba, shi kuma Yaya Mubarak ya shiga Masallacin kofar gidan su yayi sallah,
Yana shiga dakin wani kanshi dadi ya bigeshi dakin yasha gyara kasancewar Yaya Ameen akwai tsafta, zama yayi ya ciro wayan shi ya tura mata text Baby ina jiranki I eager to see you, habiby eat d Food I am coming, no kawai ni kizo ina jiranki ganinki yafi cin abinci Muhimmanci, to ganinan cold ur mind dear,
Mami ne ta shigo hade da sallama, Amsawa yayi tare da dago kai yana mata murmushi kanwata Barka, "yauwa Yaya brka da zuwa ya hanya yasu Mamy da su Kilishi da Aunty Zahra duk suna lpy, "lpy lau suna gaisheku, yauwa bari in kiramaka Aunty nawa, ok to
Ta dade a tsaye a kofa ta kasa shiga, tun dazu yake jin Alamunta da kanshin turarenta kuma ya tabbatar itace shi yazaiyi da kunyar nan ne don yaga Alama kunyarta bazata barta ta nuna mai Soyayyar ba, tasowa yayi ya budo labule a hankali ita kuma lokacin ta kulle idonta ita kuma Mami tana kokarin turota dai dai shikuma ya fito, kawai sai ji tayi an turata ta fada jikin Mutum, ai da gudu Mami ta juya tana dariya, shi kuma tana fadawa jikin shi ya rungume ta kamar wani zai kwace mai ita, a tare su ka saki ajiyar zuciya, da sauri ya jata suka shige dakin itako Kara rufe idonta tayi gam tana ta mutsu mutsun ya saketa yaki, dago kanta yayi ya kura mata ido ba, abunda yafi daukan hkalinshi irin cute Lips nata, da Zara zaran eye lashish nata, lip din yaji janvaki a hankali ya kai bakin shi kan nata ya bata lights kiss, sannan ya saketa komawa yayi ya zauna ya jawota ya zaunar da ita kusa dashi, muryan shi can kasa yace mata I love you too Baby ur my life, my life without you is empty like Bread without sugar, pleasssseee ki soni ko rabin yanda nake sonki ne, Baby na๐"I love you too hubby Nusaibatu tana sonka fiye da tunaninka, kaine Namijin data fara so a duniyar Soyayyan ta, please na baka Amanar zuciyata Karka ci Amanar ta, "na karba Baby na Allah ya barmu tare, "Ameen mijina, to sauko kaci abinci haka ya sauko ta dunga bashi abinci suna hiran love, Sister Nafeesat kizo ki dau course๐,
Bayan ya gama suka shiga cikin gida suka hadu dasu Anwar wai su akai su gurin Daddy su, rike musu Hannu sukayi suka ci gaba da shiga gidan suna zuwa dai dai sashin su Billy, Ummimi ta waske dole haka Mubarak ya bita sashin ba kowa, Amma fes fes tunda dama Billy bata da kazanta, dakin Umman su suka shiga suka ganta kwance a kujera da sauri ta tashi tazo ta rungume Ummimi ta fashe da kuka, Don Allah kiyafemun Ummimi ki tayani rokon Mubarak ya yafe mun "haba Yar uwa ni na dade da yafemiki, don Allah ki yafema Ummata ma, nida Mubarak duka mun yafe muku Allah ya bayyana Umman taku, Ameeen ga kuma yaranki na kawo miki su kwana a gurinki, kudi Mubarak ya ciro ya mika ma Ummimi yace ta bata, in suna bukatar wani Abu ta siya musu, "yauwa my Yarana ga Momy ku kuje gurinta koh, "mu bama sonta tunda bata damu da muba kuma ta tafi ta barmu, "kar in karajin kunce haka oya kuje ku gaidata is ur Mom kunji yan albrka, da kyar suka yarda sukaje gurinta,
A haka har sukayi kwana biyu ba laifi yanzu sun dan saki jiki da ita, Amma ba kamar yanda suka saba da Ummimi da Mami ba, yau ne zasu koma, Ummimi ne da Mami suka rakoshi bakin titi inda ya ajiye motarshi, bayan sun shiga Motar ya fito har sun juya, "Habibaty juyowa tayi ya kariso gurinta da sauri, ya bata fake kiss a forehead dinta ya juya ya tada mota ya tafi yana dago mata hannu, Murmushi tayi ta shafa gurin da hannunta tayi ma hannu ta kiss kwashewa da dariya Mami tayi, aiko da gudu ta bita, ita shap ta mance da ita a gurin, Banza yar sa, ido ai halinku daya da Jafar din,
Kwanci tashi ba wuya har gobene Daura Aure, sai dai Kilishi tayi mana kwafsi tace in an Daura akai mata Amare gidanta ne, har Amaryar Yaya Ameen din, sai daga baya za, ayi duk wani celebrate sbda wasu dalilai, nata nima dai ban san komeye ba, Amma zan dage sai na jiyo muku dalilin da yasa kilishi zata mana haka, inda muka ci burin chashewa dinnan nida su sister Adama da Nafeesat da duk yaan gidan Gado Fans, to muna jira.
Taro yayi taro sai da akaje Kano aka dauro na Yaya Ameen aka wuto da Amarya Zaria sannan aka Daura nasu Yaya Mubarak karfe sha dayan safe, inda gaba daya kusfa ya dauka ba masaka tsinke inda dubban mutane suka shaida daurin Auren Mubarak da Nusaibatu, Akan sadaki dubu dari biyu, duk da su Baffa Yahaya sun so a rage sadakin sunce yayi yawa Daddy yace su sukayi niyar haka, Ana gamawa aka buga Yola akace a Daura nasu Zahra,
Karfe biyu suka Kama hanyar yola, Amma Amare su a jirgi zasuje, kaduna suka wuce don already dama anyi booking na jirgi, ciki harda Hajia Yaya da Guggo tsohuwa sai Yola.
Nima na bisu aka koroni akace sai dai inje in I yan Daura aure a mota niko nace sai jirgi zan hau ko a fasa, aiko Hajia Yaya tace sai dai in fasa, ni kuwa na fasa, dama wayar dauko rahotan chaji ya kusa karewa, innayi chaji na bi Su Mama dazasu tafi jibiโ๏ธโ๏ธโ๏ธ
Share
Commmment
Vote
Please โ๏ธโ๏ธโ๏ธ
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: ๐๐๐๐๐๐
*GIDAN GADO*
๐๐๐๐๐๐
*(WALIMA&DINNER)*
*WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.*
*๐น๐นEPISODE SIXTY SIX&SEVEN๐น๐น*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*๐ฆ{Arewa ginshiฦin al'ummah}๐ฆ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*Alhmdulillah ngd da Addu'oi ku Hussaini yaji sauki har yana magana ma.*
_*Ina kuke Masoyana ga Sabon Novel dinan da zai zo muku nan ba da dadewa ba mai suna ๐๐WAZAN AURA? ๐๐ tausayi da ban al ajabi da yarda da kaddara duk a cikin Sabon Novel Dina mai suna๐๐WAZAN AURA๐๐ kudai kawai karku bari a baku labari ku cigaba da bibiyan yar mutan zazzau.*_
"Wai an kusa gama kunshin kuwa? "Eh saura dama ita daya ta rage a gama to ga mai make up ta iso, ina son ayi a fara waliman nan da wuri ne sbda bama son African time, ke Baby taso kiyi wanka gashinan an hada miki a toilet tunda ke angama miki, to Momy.
Kai Masha Allah din Allah ku tayani gani wai Su Nusaibat ne haka ko an canxo Sune, kuzo kuga Amare inda suka hade a cikin wani golden Abaya sun hadu iya haduwa, sun zauna gurin da aka tanada domin Amare Malama juwairiyya ce tazo ta gwangwaje musu wa'azi mai ratsa jiki akan aure Amare sun sha nasihohi sosai, Anci ansha can na hango yan gidan gado fans sun ci ankon hijaban Su milky colour sunsha kyau, sister Adama naga tana ta ribibin Amso musu take away da ake raba gurin takwaranta Aunty Adama a,a Su sister Adama Amara kirjin biki, a karbo har da nawa karki manta dani๐. Taro ya watse tubarkalla ansha selpie can na hango takwara ta dage sai sunyi selpie da Amare, kai su daughter kibi a sannu kema zaki shiga pic din kai Banga Maman Ahmad bane da sister Nafeesat ko mota ta Makale muku a hanyane๐ to nima dai bari na matsa kusa duk da ba tsawo gareni ba Anya za,a hangoni kuwa๐kai sisters kumin karo karon tsawon ku mana nima ko a hangoni a selpie nan, haka aka gama WALIMA lpy aka tashi sai kuma gobe in Allah ya kaimu zamuje mu kwaso shoki, dole in nemo heels shoes domin a hangoni da kyau, ๐gurin Dinner din nan to sai dai matsalan banda mayafin sawa Amma tunda garin su sister Adama ne ta Aramun nata, ๐.
*************************
"Eh Mamy ina ta jiran su juwairiyya har anyi WALIMA an tashi Basu zo ba ok sun kamo hanya harda Yaya Bilal da Muniba to sai sun iso, "nima yanzu na gama waya dasu Mama tace mun jirgin karfe biyar din safe zasu taso harda Mami da Yaya Umar da Yaya Jafar, "ok Allah ya kawosu lpy Ameeen suka Amsa Basu suka kwanta sai karfe goma sha daya Bayan sun gama turaren jiki,
Asuba ta gari Hajia Kilishi tazo ta tashesu Sumy artist aka kira don suyima duk wanda suka zo bikin Make up, aiko ranar sai dasu Yaya Mubarak suka ga Amaren su, sai dasu ka gigita ganinsu, sbda Kara cika da kyau da suka karayi, Yaya Amar kasa hkr yayi jan Zahra yayi can boys quarters ya gama uhmmm Nidai bakuji a bakina ba, ba ruwana๐kar sister Adama tace nayi rashin kunya, to suma dai ta fanni su Yaya Mubarak hakan ta kasance niko nace in kunyi hkr anjima Ana gama Dinner Kilishi zata kawo muku Amare,
Well come Queen palace hotel yola haka naga an rubuta a saman gurin suna bada wani light mai kyau,
Biki yayi biki mu a can muka kwana rawa rawa, kidane ke tashi na mawakin nan mai tashe Hamisu breaker ne ke ta wakarshi ta jarumar mata, mutane sun fara zuwa Ana sauke su a hadaddun motoci, can na hango su Mami ita da juwairiyya da Muniba kannin Raleeyat sun cakare sun ci ado kamar ka sace su ka gudu, gefen Mami na kalla sai na hango cingum nata wato Yaya Jafar a gefenta can na hango yaya Umar nata dama dama da Juwairiyya nace kodai kodai๐. Tun Daga kofar shiga gurin aka zuba wasu filawoyi masu kyau, wata hadaddiyar Motane ta parker inda ta jawo hankalin duk wanda ke gurin tuni Mc ya canza kidan I am fall in love, wasu hadaddun yarane guda biyu suka fara fitowa Daga Motar kaman yan larabawa,,,,, sorry sai kunji ni anjima kuyi hkr da wannan one love.
KUCIGABA da bin yar mutan zazzau
Share
Vote
Comment
Please โ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธ
[6/29, 08:41] +234 803 742 0816: ________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*๐ฆ{Arewa ginshiฦin al'ummah}๐ฆ*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com๐๐๐๐๐๐
GIDAN GADO
๐๐๐๐๐๐
(KILISHI HOUSE)
WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
๐น๐นEPISODE SIXTY FOUR&FIVE๐น๐น
Sadaukarwa ga kannina yan biyu Hassan da Hussainikilishiini Allah ya baka lpy ya tashi kafadunka Ameen ya Allah.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
*************************
Sun isa Yola lafiya kasan cewar a jirgine karfe biyar na yamma sun isa, direct Motocin gidan Hajia Kilishi ya zo daukansu can suka wuce,
Bayan sun isa sunje sun tarar da Zahra a can gidan ita ma an kaita bayan sunci Abinci sun huta, daki daya aka ware ma Amare wannan umarnin kilishi ne, "Sittynerh buri ya cika an Auri Yaya Mubarak, ๐harda wata ta fara ciwon so, "Naji din naga wata ma hakane ta gama jan ajin Ana so Ana kaiwa kasuwa, ita dai Raleeyat dariya ta musu Nidai bana cewa komai nasan ina cewa yanzu za, a gwasaleni, dariya gaba daya suka kwashe dashi ai ke yanzu Auntyn mu ce, slmar da akayi shi ya katsemusu hiran da sukeyi, Aunty Adama ne ta shigo ita da wasu mata su biyu shuwa, Arab ne matan "yauwa ga Amaren nan yanzu yau zaku fara aiki ko sai gobe, "ai Hajiya tun yau ya kamata a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 12