ya taba kaita kwanaki dake da swimming pool, dan tasan can din ma sharr ne da hasken tamkar rana. Shigarta wajen ya sakata lumshe idanu saboda busowar wata niimtacciyar iska mai kanshin furanni a cikin hancinta, murmushi tayi, zuciyarta na sake zumudin karasawa gaban ruwan. Sai dai me tana daga kafa dole ta koma ta tsaya cak, sakamakon saukar muryar Mamy cikin kunneta. Magana take a kausashe, cike kuma da bada umarni. Kai kawai Maanal ta girgiza cike da takaici zata juya dan bama ta bukatar jin bakaken maganganun da Mamyn ke fada akan Oum, amma mi sai taji Muryar AA a bazata yana fadin, "Amma Mamy yanzu bakya ganin hakan zai zama wani abu daban idan nace yarinyar nan ta dakata da zuwa Company na. A yanzu fa Maanal matata ce, a ganina ta wuce dukkan wata alfarma kuma sai iko ma da take da shi akan komai na. Kerna fa gashi fada kike kullum akan Abah. dan na tabbata da ace baku hada miji da Oum ba amintarku har abada bazata taba rawa balle har kukai ga wannan matakin.
Duk da dai daga bangarenki ne aka samu rashin fahimtar, dan har zuciya wlhy Mamy kina a zuciyar Oum da girma da daraja. Ni dai Mamy bazan gaji da baki hakuri da fada miki gaskiya akan wannan al'amarin ba. Dan ALLAH ki ajiye makamanki akan Oum, bana son lokaci yakai kurewar da wani a gidan nan zai ji wani abu akan hakan, musamman sauran yan uwana da Abah. Sannan batun aurena da Maanal kiyi hakuri, hakan wani hukuncine na UBANGIJI dake rubutacce a kaddararmu, kodan yanda abubuwa suka faru a baya, da yanda suke a yanzu yakamata mu fahimci al'amarin nan fa mai girma ne.....
"
"Hakane ubana".
Mamy ta fada cike da hasala da gatse kuma. Murmushi AA yayi na tsantsar damuwa.
Sai kuma ya dan kalleta da idanunsa da suka kade sosai. "Kiyi hakuri idan kalamaina sunyi nauyi da yawa Mamy, har abada ni mai biyayya ne a gareku ku duka ukun nan. Sannan zan bama kowanneku kariya daga cutarwar dan uwansa.....
"
"Kai ka sani kuma wannan. Na baka kafin nan kafin fara azumi kazo min da cikakken bayani akan ma'anar Maawad kamar yanda na fada maka, tare da dukkanin takardun kadarorin ka...
"Mamy ki gafarceni, wlhy ban san yanda zan iya tunkarar Oum na amshi abubuwan nan a hannunta ba".
Mamy ta fada cike da hasala da gatse kuma. Murmushi AA yayi na tsantsar damuwa.
Sai kuma ya dan kalleta da idanunsa da suka kade sosai. "Kiyi hakuri idan kalamaina sunyi nauyi da yawa Mamy, har abada ni mai biyayya ne a gareku ku duka ukun nan. Sannan zan bama kowanneku kariya daga cutarwar dan uwansa.....
"
"Kai ka sani kuma wannan. Na baka kafin nan kafin fara azumi kazo min da cikakken bayani akan ma'anar Maawad kamar yanda na fada maka, tare da dukkanin takardun kadarorin ka...
"Mamy ki gafarceni, wlhy ban san yanda zan iya tunkarar Oum na amshi abubuwan nan a hannunta ba"."Okay haka kace? Toni zan tunkareta na
amsa tunda ba uwata bace ba ai".
"Mamy Please...."
Ko kallonsa batai ba ta wuce fuuu. Ja baya Maanal tai ta labe a dan lungun da akai adon wajen. Dan bata bukatar Mamyn ta ganta.
Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata, matukar tausayin AA na ratsa mata bargon jiki. Kenan shi Mamy ta bayyana masa ainhinta, tana kuma amfani da damar tana tursasa masa yin abubuwa dan tasan yanda Oum keda muhimmanci a garesa. Murmushi ta saki mai matukar ciwo, sai kuma da sauri ta share hawayenta ta bar jikin bangon tamkar yanzu ne take shigowa saboda jin karar taku alamar shine zai fito. Bayyanarta ya sashi tsayawa cak, itama sai ta tsaya din tana kallonsa, dan duk yanda taso basarwa ta kasa hakan. Tausayinsa ne ke neman fin karfin zuciyarta.
AA da ganin Maanal din ya sashi jin shock wani irin tsinkewa zuciyarsa tayi, addu'a yake ALLAH yasa yarinyar nan bataji tattaunawarsa da Mamy ba. Dan bazai taba son hakan ta kasance ba sam. Cikin son basarwa ya shiga hadiye nannauyan abinda ke tsaye a makoshinsa ya daidaita fuskarsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a hankali har zuwa gabanta.
Kayan hannunta ya dan zubama ido, kafin ya janye ya maida kan fuskarta. Cikin tausasa murya da kankanceta ya furta, "Daga ina?".
"Sama".
Ta bashi amsa.
Murmushi yayi a karo na farko, tare da lumshe idanunsa ya sake budewa a kanta. "Bakin nan dai bazai daina ma mutane bakar magana ba ashe?".
Samun kanta tai da dan sakar masa murmushin itama sai kuma ta kauda kanta gefe tana mai labe bakin kadan. Shima murmushin ya sake saki dan nata murmushin wani sanyi ya saukar masa a zuciya. A hankali kuwa ya saki ajiyar zuciyar tare da matsowa gab da ita.
Matsawa tayi baya tana mai waro masa idanun kadan, irin na (lafiya dai?) shima sai ya bita.
Danganewa tayi da bango, hakan sai ya bashi damar dafe bangon da hannu daya ya mata rumfa da jikinsa. Gaba daya ta jita kamar a keji, ga wani irin watsal-watsal da zuciyarta ke mata, sassanyan kamshin turarensa kuwa na saukar mata da kasalar jiki da gabbai. Shima din wani irin haurawa yaji jininsa nayi a saman kai, a hankali muryarsa cike da taushi da nauyi ya furta, "Bestie, please give me a hug mana".
Sosai zuciyarta ta harba, duk yanda taso daurewa ta kasa, idannunta ta dago slowly ta sauke akansa, shima kallon nata yake, sai taga kamar idanunsa na kyallin hawaye, duk da tasan wannan normal ne a garesa, dan in har ma yana cikin farin ciki sosai idanun na fari tas-tas zakaga tamkar kuma an bisu da mai ne.
Amma na wannan yanayin babu abinda take hangowa a cikinsu sai tsagwaron damuwa da bacin rai.
To bazawarin Huznah dai kazo da bidia, runguma kuma? Wannan ai cin amanar Abah ne Gaskiya
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣5️⃣
______________
........Samun kanta tai da sakar masa sassanyan murmushi, tare da buɗe hannayenta a hankali alamar bashi damar daya buƙata.
Idan yace zuciyarsa bata nema tarwatsewa ba a wannan gaɓar yayi ƙarya, amma wannan ba lokacin tunani ko nazari bane. Duk da ya mata tsaho sosai cike da jin illahirin jinin jikinsa na narkewa ya wani irin shigewa jikin nata ya rungumeta tsam har sai da ta ɗan rumtse idannunta. Sosai tausayinsa ya shiga marmashe mata illahirin zuciya, dan kasancewar kanta kwance a ƙirjinsa tana iya jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, ga hucin numfashinsa na sauka a kunnenta da zafi-zafi. Sun kai tsahon mintuna biyar a haka, ita harma ta fara jin ƙafafunta sun mata nauyi. Sai taji shima kamar ya mata nauyin. Muryarta na wani irin komawa sanyi ƙalau ta ce, “You're sleepy?”.
Maimakon bata amsa sai ya girgiza mata kai kawai. Sai kuma ya miƙe tsaye sosai ya ɗagota itama daga ƙirjin nashi ta tsaya da ƙafafunta. Fuskarta ya kafe da sassanyan kallo, ita sai ma ya bata kunya. A hankali ta risinar da idanunta ta koma kallon yatsun ƙafarsa dake fes-fes cikin tattaunsan baƙin takalmin daya sanya. Hannu yasa ya ɗago fuskar tata ta hanyar kamo haɓarta cikin hannunsa. Maimakon ta kallesan kamar yanda yake buƙata sai ta lumshe idanun nata. Murmushi ya saki kaɗan, cike da son tsokanarta ya ɗan ranƙwafo ya dai-daita fuskar tasu numfashinsu na sauka a fuskokin juna. Cike da shauƙin yanayin nasu ya furta, “Besty!”.
Kasa amsawa tayi, dan gaba ɗaya jinta take kamar ta nutse a cikin ƙasa. Shima fahimtar bazata amsa ɗin ba sai ya sake sakin murmushi irin mai maƙalewa a gefen bakin nan. Cikin maida muryar tasa ƙasa-ƙasa sosai tamkar mai raɗa ya ce, “An bani Hug saura kis....”
Ai baima kai ga ƙarasawa ba ta waro idanunta gaba ɗaya warrr a kansa. Sai dai kasancewarsu gab da juna ya sata maidawa kuma da sauri ta lumshe tare da janye jikinta baya tabar wajen da sauri. Dariya sosai ta bashi, amma sai baiyi ba ya saki ɗan murmushi yana miƙewa tsaye da ƙyau ya zuba duka hannayensa a cikin aljihun farin jeans ɗin wandonsa ya bita da kallo. Sai da ta zauna batare da ko waiwayensa tayi ba ta buɗe novel ɗinta ta sanya eyeglasses a idonta sannan ya shiga takawa a hankali zuwa inda taken..
★ Ya jima tsaye a inda ta barshi yana kallonta, kafin ya tako shima a inda taken. Kujerar dake facing ɗinta ya zauna, batare da yace mata komai ba ya zuba mata idanunsa kawai hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa. Yanda ya zuba mata idanun nasa masu kaifi ya sakata daburcewa ta daina fahimtar abinda ma ta fara karantawa. Amma a zahiri bazaka taɓa tunanin a rikicen take ba dan ta maze ƙwarai da gaske kamar bata san da shi a wajen ba. Dai-dai nan kiran Oum ya shigo wayarsa. Kasancewar ringing ɗinta na musamman ne ya saka shi dakatawa daga faɗar abinda yay niyya ma Maanal. Wayar ya ciro daga aljihu yana gyara zamansa da ƙyau. Sai dai idanun nasa har yanzu a kanta tamkar ya samu television ɗin kallo.
Cike da tsokana ya furta, “Assalamu alaikum uwargidan Abah har a ALJANNA”.
Murmushi Oum tayi daga can. Cike da jin shauƙin ƙaunar Autan nata tace, “ALLAH to ya tabbatar Autan Oum ɗinsa, sannan tare da ku Bestyn bestynsa.”
Murmushi AA yayi mai faɗi, sai kuma ya ɗan saci kallon Maanal a miskilensa ya furta, “Shike nan dai Oumna kin rama 1-1 kawai.”
Dariya sosai Oum tayi, sai kuma ta ce, “Dama zance kazo kaci abinci gamu nan zuwa tare da Abahn ku zaici abincin tare damu”.
“I'm so happy, Oum! gamu nan”. Daga haka ya yanke batare da Oum ta fahimci inda (gamu nan) ɗinsa ta dosa ba. Yana ajiye wayar ya zare book ɗin Maanal tare da ɗaukar kwalin popcorn ɗin nata da goran ruwan ya ce, “Oya let's go Oum na kira”.
Komai bata kawo a ranta ba ta miƙe kawai. A jere suka fito duk da ba wata hira suke ba. Sai da sukazo fitowa ne cike da neman magana ya gwargwaɗa mata magana a kunne. Da sauri tai gaba zata barsa saboda kunya, yayinda murmushi ya ɗan ƙawata fuskarta batare data shirya hakan ba. Shima murmushin yake yi dan haka kawai murmushin nata ya saka shi jin nishaɗi. Ai cak Abah da Oum dake fitowa daga sashensa suka tsaya. Galala Abah ya saki baki yana binsu da kallo, yayinda Oum ta gimtse dariyar dake neman suɓuce mata da ƙyar. Suna tsaye kamar gumaka AA da Maanal suka shige sashen Oum batare da su sun ma farga da su ba. Gyaran murya Oum tayi kaɗan, hakan ne yasa Abah maido da idanunsa kanta, harrarta yayi. Daƙyar ya iya gimtse dariyar tayi gaba tana faɗin, “let's go tunda gasu can.” bata jira cewarsa ba tai gaba tana murmushin data kasa riƙewa. Suna zuwa ƙofar sashen Oum Maanal ta zame tai hanyar baya ta kitchen ita adole bata son a gansu tare da AA. Bata san wanda take gudun su gansun ba sun riga sun gansu. Samun su Inte na haɗa abincin da zasu kai dining sai kawai ta shiga tayasu.
AA kam daya shige shi kaɗai dariya ma ta bashi. A ransa yace (Magulmaciya, kina so kina kaiwa kasuwa). Fawzan kawai ya samu a falon yana kallo. Zama yay kusa da shi. Fawzan ya dubesa da ƙyau, sai kuma ya ɗan matsa da fuskarsa yana shinshina shi. Harararsa AA ɗin yayi, ciki-ciki ya ce, “Miye?”. Da ƙyar Fawzan ya gimtse dariyar dake cinsa, cikin ɗaure fuska shima kamar yanda AA ɗin yayi ya ce, “Yada tsarguwa haka Malam, ka bari na gama tantancewa mana. Naji ne kana ƙamshi kamar na turaren Lilly.”
Irin ɗan waro idon nan AA ɗin yayi, ya ce, “Kai yaya Fawzan ido ka koma samin?”.
“Oh da mikake tunani? Kasan dai bazan bari aci amanar Abah ba. Kuma zanma ƙanwata garkuwa”.
Rasa ma abin cewa AA yay, sai kawai ya zubama Ya Fawzan ɗin ƙasaitattun idanunsa. Sosai Fawzan ya kwashe da dariya, dan yasan ya gama kaishi maƙura kenan. Ai idan kaga Auta ya rasa abin faɗa to yakai maƙura kenan...
A haka Oum da Abah suka shigo suka samesu. Gaishesu sukayi, suka amsa Oum na faɗin, “A'a ina Baby na kuma?”.
Fawzan ne ya bata amsa da, “Ai tunda na shigo ban gantaba Oum, maybe tana sama ko?”.
Kai Oum ta jinjina tana jiran AA ya bada amsa, amma ya basar abinsa tamkarma baijisu ba. Sosai shima Abah ke satar kallon AA ta gefen ido ransa fal mamakin, dai-dai nan Maanal da su Inte suka fito a kitchen. Dariya taso kama Oum, amma ta danne da ƙyar idonta akan Maanal ta ce, “Oh ashe kina kitchen Auta”.
Kai Maanal ɗin ta jinjina tana murmushi da satar kallon AA daketa latsa waya kanshi kwance a kafaɗar Fawzan hankalinsa kwance like baima san mike faruwa ba. Juyawa tai tana gaida Abah dayay Zuru yana kallonsu su duka. A ransa ko faɗi yake (Aiko zakuci ƙaniyarku ku duka) a zahiri kam amsawa yay cike da kulawa. Daga haka suka ɗunguma dining cin abinci.....
A nutse suke cin abincin, yayinda Oum da Abah ke ɗan hira Fawzan kuma da Maanal. AA kam hankalinsa nakan waya komi yake oho masa. Abincin ma bawani ya maida hankali bane a cinsa. Wayar Oum ta zare daga hannun nasa, yako kalleta a shagwaɓe. Harararsa tayi tare da nuna masa abinci tana faɗin, “Ni tunda ka tashi ciwon nan kake neman maida abinci abokin gabarka Auta. Oya maza yanzu naga plate ɗin nan, in ba haka ba ɗura zan maka”.
Dariya Fawzan yayi, Maanal ma ta kasa riƙe nata murmushin saboda ganin yanda AA ɗin yay da fuska. A dai-dai nan Mamy ta shigo sashen da sallama. Gaisheta Fawzan yayi bayan duk sun amsa mata sallama, tare da faɗin, “Naje sashen yaran nan sukace kina wanka”.
Cikin danne takaici Mamy ta ce, “Eh sun faɗa min”. Ledar hannunta ta ajiye a gaban AA da tunda ta shigo ya maida hankalinsa ga cin abincinsa. Maanal kam sai satar kallon Mamyn take bayan ta gaisheta itama. Ajiye ledar ya saka AA ɗagowa ya kalleta a karo na farko, hakama su Abah kallon ledar suke. Murmushi ta ƙawata fuskarta da shi, tare da juyawa tana kallon Oum. “Bara na aiki ɗanki gidan Aunty tunda dai yaji sauƙi, na manta shaf har drivers ɗin gidan sun tafi gashi da sassafe zasu wuce lagos”.
Fuskar Oum babu wani damuwa ta ce, “Eh ya kamata kam a kai mata su a daren nan. Auta sai ka maida hankali ka gama ko kar dare yayi, duk da dai kai ba tsoron fitar daren kake ba”.
Kansa kawai ya jinjina batare da yayi magana ba. Dan shi yasan babu wani saƙo. Mamyn ce ta kafa masa sharaɗin zuwa yaga Nuratu ya kuma bata kayan da zata bashi yace inji shi wai Ramadan basket. Zama Mamyn tayi suka cigaba da hira da Oum da Abah, sai kawai AA ɗin ya miƙe badan ya kammala cin abincin ba, dan zuciyarsa gaba ɗaya jinta yake a ƙuntace, amma miƙewar da zai yi suka haɗa ido da Maanal sai wata dabara ta faɗo masa. Guntun murmushin iya shege yayi, cike da shagwaɓa ya dubi Abah. “Abah dan ALLAH ka bani aron ƴarka ta rakani tsoro nake ji”.
Atare gaba ɗayansu suka ɗago suna kallonsa, ya sake narke fuska kamar zai yi kuka. “ALLAH Abah da gaske nake”. Ai kasa daurewa Fawzan da Oum sukai suka sanya dariya. Abah kansa da ƙyar yake iya danne tasa dake neman kufcewa. Maanal kam baki da hanci tama saki tana kallonsa, yayinda Mamy ta cika tayi fam fa takaici har hakan ya kasa ɓoyuwa a fuskarta. Cikin dariya Oum ta ce, “Please Abansu a taimaka mana, ai bazasu daɗe ba yanzu zasu dawo”. Fawzan ma yace, “Abah ayi haƙuri ta rakashi kada yay mana kuka ko kura ta cinyeshi a hanya dan tsoro. Kasan Besty da Besty duk tsanani tare suke zuwa aika”.
Kai Abah ya girgiza, tare da faɗin, “ALLAH ya shiryeka Ajwaad. Jiba yanda ka wani ɓata fuska like zakama mutane kuka. Shike nan kuje, amma ina nan ina jiran dawowarku, idan kuka daɗe kwanakin zan ƙara”.
“Thanks You sweet Abah”.
AA ya faɗa a hankali. Nan ma kan Aban ya girgiza kawai, yayinda Oum ke faɗin, “Baby tashi ku tafi kinji”.
Ji Maanal tayi kamar ta nutse dan kunya. Duk da kuwa a shekarun baya hakan ba komai bane a tsakaninsu. Dan ko tana gidansu aka aikesa zaije yace tazo ta rakashi kida cikin anguwa ne. Haka itama idan aka aiketa ko yana gida agaban su Abah ɗin zatazo tace masa (Besty zoka rakani aika) amma sai yau gashi tana jin hakan kamar sabon abu. Sarai AA na lure da mugun kallon da Mamy ke masa, amma ya fuske abinsa, sai ma nufar sama da yay ganin Maanal na niyyar warware ƙaramin veil ɗin kanta alamar da shi zatama fita take nufi. Da kallo duk suka bisa, Fawzan kuwa na masa tsokanar daya saba da kirari. Babu jimawa ya dawo da mayafin da yafi na kan nata da ke kamar na yara dan na Abaya ne. Wanda ya miƙa mata ɗin ta kalla, sai kuma ta ɗan tura baki gaba. Wancan ta cire ta amshi na hannun nata ta sanya, zata nufi saman itama ta maida Oum tace ta kawo kuje kawai kar dare yayi. Oum ɗin ta ba, shi kuma ya ɗauka ledar Mamy da takaici ke neman bombing mata zuciya suka fice..........✍️
_Abah da kasan kura kaba ajiyar nama da baka bayar ba😂🥱_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖1️⃣6️⃣
______________
.......Wata Nurse da Sageer ya kira anan anguwarsu na tsaka da duba Huznah kiran Hajiya Basariyya ya shigo wayarta. Kasancewar yana a kusa da ita shi ya kai hannu ya ɗauka dan ita ana mata ƙarin ruwa ne. Shine ya fara yin sallama, dan haka Hajiya Basariyya tai ɗib daga ƙoƙarin maganar da tai niyyar yi. Da ƙyar ta iya amsa masa gaisuwar da yake mata. Kafin ya ƙara cewa wani abu ta yanke kiran. Murmushi kawai yayi baice komai ba. A ransa kam dariyar ƙeta yake da faɗin (Mama ai sai kuma haƙuri, ƙiyayya ta ƙare tunda ruwa ya gauraya da jini). A zahiri kam murmushi yayi kawai....
Wani irin malolon baƙin ciki ne ya sake tokare zuciyar Hajiya Basariyya. Dan ita kam abin ya zame mata goma da goma. Tana yaƙin ganin ta koma ɗakinta kafin Hajiya Yaya ta koma, Daddy kuma ya saki Asiya a randa ta koma dan alwashine sai tayi maganin Asiya a wannan gaɓar ga kuma batun Huznah da shima suketa faɗi tashin ganin wannan auren ya rabe tazo ta auri AA sun fiddo waccan shegiyar agolan daga ciki mai ƙwacen saurayi. Ita kuma sakaran tayi sakaci wannan matsiyacin ya kwace ɗan mutuncin. Zaune takai a bakin gadon ɗakin da take zaune a gidan yayanta, ɗakin da saida akai uban rikici matansa suka bari ta zauna duk da kuwa ɗakin baƙi ne. Kayayyakin data amso a Zaria tare da Maman Yaseerah take bi da kallo. Haɗi ne sosai tayoma mutane guda biyar. Daddy, Asiya, Hajiya Yaya, sai mijin Huznah da AA. Kuma duk ana son ta aiwatar da su daga nan zuwa gobe, shiyyasa ma tai kiran Huznah dan taji yaya za'ai nata ya iso a goben itama ta aiwatar, ko Sageer na yawo da ubansa ko sai ya saketa da hannunsa. Dan sunan maganin KANWA UWAR GAMI. Amma shine tantirin ya ɗauka mata waya.. Bumm!! Bumm!!! Bumm!!! Bugun ƙofar ɗakin da take aka shiga yi da masifar ƙarfi, a zabure ta miƙe tana yayimar kayan ta tura ƙasan gado, kafin ta mirza idonta ta nufi ƙofa kamar mai barci. Dan bata raba ɗayan biyu yayanta ne matansa sunkai ƙararta saboda yau ta zagesu tas wai suna saka mata nama biyu a abinci, duk naman dake gidan saboda an rainata ace biyu ne kawai kasonta...
Tana gama buɗe ƙofar wani kakkauran mari ya ratsa mata kumatu. Da bala'in sauri da rawar jiki ta dafe fuskar da hannaye biyu gaba ɗaya. Bai dubi girman shekarunta ba ya sake wanketa dana biyu. Shi dama mutum ne mai zafi sosai. Ai yanzu kam ihu ta ƙwala dan azaba ta koma cikin ɗakin a guje. Bayanta yabi, ta maƙure jikin bango tana hawayen azaba a matuƙar gigice. Cikin wata irin tsawa mai kaɗa hanji ya ce, “Ina kukaje yau dan ubanki?”.
Hawaye na ziraro mata ta ce, “Babu inda naje fa yaya, matanka sun haɗani dakai saboda su munafukai ne. Wankin kai da kitso fa naje kuma na gaya maka ka bani kuɗin da kanka”.
“To mara mutunci, aiba maraina wayon naki bane ba ni da idona na ganki tare da Alhaji Usman a Zaria. Ko zakice min kitson acan akeyi?”.
Sosai jikinta ya fara rawa na haƙiƙa kam yanzu, zuciyarta kamar zata faɗo cikin in-ina tace, “Yaya Zaria kuma?..”
“Oh ƙarya nai miki kenan? Wlhy Basariyya ki shiga hankalinki a gidan nan. Wato har yanzu baki daina biye-biyen bokayeba ko? Shike nan karki fasa ki cigaba da yi, ki kuma haɗa inaki-inaki gobe kawu na Katsina zaizo ku tafi tare. Ki koma can wajensa dan ni bazan iya ba...”
Wani irin gigitaccen ihu ta sanya tana roƙonsa ya taimaketa bazata iya zama gidan kawun nasu ba. Ko kallonta baiyi ba ya fice abinsa. Tashin hankali matuƙa Hajiya Basariyya ta shiga a wannan dare. Dan wlhy bazata iya zama gidan kawu Manu ba. A ƙauye yake bama cikin birnin katsinar ba, ita wlhy ko ruwan gidan bata iya sha idan sukaje gaisheshi na yini ɗaya saboda kiwon dabbobinsa na tsiya. Gashi masifaffe hakama matarsa, kuma su duka ƴan uwansu ne dan auren zuminci ne shida matar tasa. Tun babansu na da rai ake fama da shi ya baro ƙauyen amma yaƙi. Mahaifinsu kansa tsoronsa yake ji balle su, dan mutum ne azababbe na bugawa a kalanda, ga tsauri dan komai na gidansa da doka akeyinsa. Kuka sosai taci, daga ƙarshe ta yanke shawarar yin asubanci ta gudu. ALLAH gara ta koma gidan mijinta duk ma bala'in da za'ai ayi bazata fito ba koda Daddy zai daketa kuwa. Kayanta ta shiga haɗawa, tsaf ta kammala ta ajiye komai a ƙofar ɗakin, sauran kuma ta ajiyesu akan daga baya zata turo su Madeena yaranta su ɗaukar mata. Ko barcin kirki kuwa batayi ba, huɗu na bugawa zabar ta miƙe dama ba wani barcin kirki tai ba, a gurguje ta shiga bayi ta kimtsa ta fito, ta saɓi jakarta tana murmushin nasara, sai dai tana murɗa handle ɗin ƙofar taji gam, hakan na nufin an kulleta ta baya kenan. Ai jitai gaba ɗaya ta wani irin gigicewa, bama tasan ta zube a wajen ba ta fashe da kukan takaici, dan ta tabbatar yayanta ne ya rufeta tun fitar jiyan da yayi.......
🤣🥱Ba abun faɗa
_________★
Sun fito a jere Maanal na faɗin, “Kai dai ka canja hali ALLAH”. Cikin ƙunƙuni take maganar, amma hakan bai hana AA ɗin jinta ba saboda ƙarfin ji da ALLAH ya bashi. Murmushi yay kawai, sai kuma ƙasa-ƙasa shima yace, “Inba tsoro
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 15