Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamar yanda taji iyayenta na faɗa makircin Oum ne kawai. Bata sami nutsuwa ba har sai da sukai waya da Mamy da Saheeba da suka kwantar mata da hankali da tabbatar mata aure na nan babu fashi. ALLAH dai ya kaimu bayan sallar da sati guda za'ai ma ba biyu ba.. Sannan a gidan zatai azumi kuma...         Hakan ya ɗan sakata jin sanyi da sassauci a cikin ranta. Harta ɗan saki jiki ta cigaba da harkokinta musamman a media. Harda su tsara write-up ta turama ƙawayenta da abokan arziƙinta cewar biki sai bayan sallah saboda har yanzu ango babu lafiya..... ___________★        WASHE GARI.   Safiyar yau Litinin har Oum ta fidda ran Abah zai bar Maanal ɗin ganin tun jiyan baice mata komai ba. Haka shima AA ɗin baima saka ran komawar Maanal ɗin yau ba. Kawai dai ya tashi da nasa shirin ne. Bayan sallar asuba daga massallaci Abah sashen Oum ya nufa. Kasancewar yasan yanzu ita da Maanal ne a ɗakin ba kai tsaye yake shiga ba. Dan haka yay sallama bayan yin knocking a ƙofar bedroom ɗin sannan ya koma falo ya zauna. Babu jimawa kuwa sai ga Oum ta fito daga ɗakin sanye cikin dogon hijjabin sallarta. Tunda ta doso shi ya zuba mata idanunsa da suke a narke. Itako sarai data san halin kayanta da gejin da yake kawai na haƙuri da rashinta a kusa da shi sai ta basar kamar bata fahimci magiyar da yake mata da idanun nasa ba. Ɗan nesa da shi ta zauna, sai kuma ta ɗan zamo a kujerar kaɗan cike da neman magana ta ce, “Yaya Aliy ina kwana” (haka take kiransa lokacin ƙuruciya). Hararta yay da faɗin, “A'a baba Aliy ba yaya ba. Saboda kina son a faranta ran ɗanki zaki ce dani wani yayan gulma”.      Ƙaramar dariya Oum tayi, amma batace komai ba. Shima fuskarsa da murmushi ya ce, “Kun tashi lafiya?”.      “Alhamdullahi”. Ta bashi amsa. Kansa ya jinjina cike da gamsuwa. Kafin ya cigaba da faɗin, “Akan maganar ki ce ta jiya. Na bada dama Maanal ta koma aiki, amma da sharaɗin driver zai dinga kaita ba ɗanki ba. Dan bana son wata alaƙa ta haɗasu. Ki kuma gargaɗesa babu ruwansa da yarinyata a office balle ya takurata, na saka securityn da zan san duk motsinsa akan hakan, idan ya karya min doka kuma zan ƙara yawan kwanakin suspension ɗin”.     Murmushi Oum tayi a karo na farko. Hakama AA da yazo sashen sai dai yana hawowa stairs ɗin yaji muryar Abah dan haka ya dakata. Idanunsa ya lumshe, tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Ayya Abah koba security ba. Badai ka yarda taje ba, ai sai abinda ka gani kawai Aban Maanal”. Daga haka ya juya ya koma abinsa domin yin shirin office ɗin....       Oum ma bayan tafiyar Abah ɗaki ta koma tace Maanal tai shirin office Abah ya bari. Duk da zama waje ɗayan dama ya isheta sai taji gabanta ya faɗi. Na farko dai tana jin kunya da tunanin yanda zata kalla ƴan company a yanzu. Dan tasan dai sun gama sanin ita ɗin matar ogansu ce a yanzu. Na biyu yaya rayuwarta a companyn zata kasance a yanzu kuma tsakaninta da mai kamfanin. Tunda a gida ya rasa kowace dama a kanta acan da babu idanun Abah kuma fa?.....        “Ko baki son komawa ne Baby?”. Oum ya katse mata tunani. Ƙasa tai da kan nata tana ƙaƙaro murmushi. Sai kuma ƙasa-ƙasa ta ce, “A'a Oum. Kawai dai ina jin nauyin ƴan kamfani ne”.       Dariya sosai Oum ta sanya da faɗin, “Oh oh! Har yanzu dai Babyna na nan da wautarta. Ina ruwanki da su bayan yanzu ke oga ce. Matar oga ai oga ce ko. Tsakaninki da su sai girmamawa ai. Dan haka ki kwantar da hankalinki ki riƙe girmanki, ki ƙara ƙwazo da himma akan aikinki. Kiyi abinda ya dace na rike martaba da girmanki domin kare mutincinki dana mijinki. ALLAH yay miki albarka”.      Cikin jinjina kai Maanal ta ce, “Amin”...      Wanka ta shiga, Oum kuma ta fita zuwa kitchen haɗa musu breakfast dan tasan Auta baya wasa da fita akan lokaci, duk da Abah ya kafa dokar ba tare zasu tafi ba tana son Maanal ɗin ta koyi yanayin fitar tashi tunda na ɗan lokaci ne zasu koma fita a taren.. Zuwa bakwai ta kammala komai daya kamata. Ta fito fes da ita cikin Abaya maroon color datai mata matuƙar ƙyau da haska chocolate color skin ɗinta data sha gyaran aure ta sake kwanciya luff-luff. Ga wani ni'imtaccen sassanyan ƙamshi dake tashi a jikinta. Sam batayi wani kwalliya ba a fuskar, iya hoda ce sama-sama sai kwalli da ɗan lips-gloss kaɗan. Dan ko taje girarta ma batai ba. A dining ta zauna kamar yanda Oum ta bata umarni, ta ajiye ƙaramar handbag ɗinta saman table ɗin dining ɗin itama. Dai-dai nan shima AA ya shigo, tun kafin su ganshi mayataccen ƙamshinsa daya gama manne jikinsa da komai nasa ya iso hancinansu. Yayi matuƙar ƙyau cikin Maroon suit shima sai long sleeve shirt fara tas. Harga ALLAH sai da zuciyar Maanal ta ɗan motsa. Amma sai ta dake abinta tama fara ƙoƙarin zuba abincin a ranta tana ƙunƙunin (wayace ya sake airin kayanta)        “Auta har an fito?”.    Oum ta faɗa dai-dai isowar AA dining ɗin. Kansa ya jinjina mata, tare da kamo hannunta ya sumbata yana mai ɗan bata side hug. Sai kuma a ƙasa-ƙasa ya furta, “Barka da safiya my everything”.       Murmushi Oum ta sake masa, tana mai amsawa da, “Ka tashi lafiya ya ƙarfin jikin?”.         “Alhamdullahi Oumna, ai ɗanki ya warke sarai in sha ALLAHU ”.     “Masha ALLAH haka muke fata ai Auta”.        A hankali Maanal data ƙi sake kallon inda yake duk da zuciyarta na cike da zumuɗi da maradin hakan ta ce, “Ina kwana”.     Batare daya kalleta ba shima ya ce, “Lafiya”. Daga haka ya kalla Oum a ɗan shagwaɓe ya ce, “Oum yunwa zata cinye hanji na”.       Ƙaramar dariya tayi tana kallon Maanal, itama Maanal ɗin dai-dai ta ɗago ta hararesa. Dan itace ke faɗar haka idan tana jin yunwa. Gira ɗaya ya ɗage mata irin (Ni ɗin kike harara?) sai ta sake murguɗa masa baki sannan ta ɗauke kanta. Ita dai Oum wurin tai ƙoƙarin bar musu tana faɗin, “Bestynka ta zuba maka abincin zanje nayi wanka ne”.           Kamar Maanal zatai kuka tabi Oum da kallo. Sai dai batace komai ba. Sai da ta shige sannan ta ɗauke idanun nata. Tsohon minti ɗaya kafin tace, “Me zaka ci?”.        Shiru kamar bazai amsata ba hankalinsa akan waya. Kamar wadda taji haushi ta ɗago manyan idannunta ta zuba masa. Kaifin idanun nata da tasirinsu a garesa ya sashi kasa jurewa shima ya ɗago lumsassun nasa  ya zubasu cikin natan. Bata iya ta janye nata ba suka shiga ma juna kallo mai taushi da kassarasa kuzarin jiki. Lips ɗinta ta sake motsawa a hankali batare data raba idanun nasu ba ta ce, “Nace mi kake so?”.        Cikin kasala da tausasawa kamar baya so shima ya motsa lips ɗin nasa ƙasa-ƙasa ya furta, “Ke!”...........✍️ _Ehemm-eheem nace ba, 1+1 nawa kenan? An bamu assignment ne a makarantar islamiyyar mu ne ni kuma ban gane lussahin ba😌😣, shine nace bara na tambayeku🫣🏃🏃🏃🏃🏃🏃._ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣ ______________ .......Daburcewa taso yi, ta kuma rasa yanda zata fassara amsar ta shi. Cikin suɓutar baki ta ce, “Ban gane ni ba!”.       Wani ɗan iskan gajiyayyen murmushi ya saki a iya lips ɗinsa. Kafin ya sake narke idanunsa dake sarƙafe da nata har yanzu. “Kince mezan ci? Me nake so? Nace KE!”. Ya faɗi (ke) ɗin da wani kalar sanyin murya yana ɗan waro fararen oily idanunsa da ƙyau cikin natan. Ai babu shiri ta janye nata zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Sai taji gaba ɗaya ma jikinta na neman fara rawa. Shi ko tsaf ya fahimci halin data shiga, dan haka ya saki murmushi cike da ƙeta. A ransa kuwa rayawa yake (Ba Abanki yace bazai bani ba sai na horu. Kafin na gama horuwar kema sai kin horu yarinya) a fili kam harɗe hannayensa yay a ƙirji kawai ya zuba mata ido. Ita dai ta miskile tana haɗa masa abincin a gabansa. Can ƙasan ranta luguden daka kawai zuciyarta keyi, jitake kamar ta zura da gudu, amma bazata yarda ta zubar da kanta a garesa ba...         “Ehheem! Ehemm!!”.     Gyaran muryar Fawzan ta maido AA daya zubama Maanal idanu a hayyacinsa. Janye idanun yay luuu ya maida kansa, Fawzan ya ɗage gira yana murmushi. Shima sai AA ɗin ya ɗage masa tasa girar irin (Miye?) ɗin nan. Dariya Fawzan ya sanya, tare da jan kujera kusa da AA ya zauna. Maanal data ɗan rage ɗaure fuskar da tayi ta ce, “Good morning Yaya F”.         “Morning Ƙanwar Yaya F, Baby Oum, Autar Abah, sannan kuma Bastyn Besty”.      Duk yanda taso dannewa bai yiwu gareta ba sai da ta saki murmushi tana turama AA duk abinda ta zuba masa, sai dai bata yarda ta kallesa ba. Sai ma hankalinta data maida kan Fawzan ta ce, “Yaya miza'a zuba maka?”.       “Ai duk abinda kika san yayi daɗi zuba min kawai Lilly.”    Murmushi Maanal ɗin tai tana jinjina kai. Sai da ta kammala zuba masa sannan ta koma cin nata. Suna gab da kammalawa Oum ta fito, duk da Maanal dama ba wani tana ci sosai bane ba. Oum na fitowa ma ta miƙe kamar wadda ke akan ƙaya. Cike da tsokana Fawzan ya hau yima Oum kirari, kafin ya gaidata. Itako tana dariya abinta cike da farin ciki. Sai ga babban yaya da su Naufal dake cikin shirin makaranta. Saheeba biye da su. Suma Oum ɗin suka shiga gaidawa cike da girmamawa, yaran kuma sukaje suka rungumeta. Itama Nibras ta shigo cikin shirin aiki, da alama ta makara ne. Idonta akan AA ta gaida Oum cike da ladabi, hakama babban Yaya sannan ta juya tana gaida AA ɗin daya juya yana magana da Naufal. A taƙaice ya amsa mata batare daya juyo ba. Maanal dake karantar yanayin kowa musamman Saheeba da tunda suka shigo taga ta mata wani irin kallo ta ɗauke kai a taƙaice ta ce, “Auntys barkanku da safiya”.        Babu yanda suka iya daga Saheebar har Nibras ɗin dole suka amsa. Sai dai kowanne da kalar zafin da yake jin Maanal ɗin a ransa. Yayinda shigar tata ta saka zuciyarsu sosuwa. Duk da bawani kwalliya tayi ba, babu kuma wani ƙyale-ƙyale a tare da ita kamar nasu. Amma tayi matuƙar yin ƙyau mai sanyi. Ga ƙamshinta na fita a nutse babu wata hayaniya. Tunda kuma tai musu kallo ɗaya ta watsar da su a tasu fahimtar. Yanzu kuma ta jefesu da gaisuwar raini. Oho ita bama tasan sunayi ba. Tama maida hankalinta ga babban yaya suna magana...      Shigowar Abah ta saka kowa maida hankalinsa kansa. Sai Mamy dake biye da shi riƙe da briefcase ɗinsa. Sosai Abah dake kallon zuria'ar tasa farin cikin ya mamaye ransa. A ransa rayawa yake (Nanfa duk mallakina ne, zuri'ata ce. Idan kuma ALLAH yaba Fawzan haihuwa da Ajwaad shima Fadeel aka ƙaro masa sai mu sake yawa). Mamy kam zuciyarta ce ta sosu da ganin wahalarta zagaye da kishiyarta. Tayi-tayi ta hana wannan zaman safen a sashen Oum tarasa yanda zatayi. Dan ita inma sun shiga gaisheta sama-sama ne, amma Oum kuwa anan ma suke breakfast wasu ranakun koda matansu sun girka sai su ƙi cin nasu sai sun zo nan musamman Fawzan da matarsa ke malalaciya..... Tunaninta ne ya katse saboda gaisuwar da Maanal ke mata. Amsawa tai fiskarta da murmushi, sai kuma ta tsargu da yanayin shigar Maanal ɗin. Ta ɗan saci kallon AA dake tsaye kusa da Maanal gab batare da suma sun farga da yanda suke ba. Dan ya miƙe ne zai amshi number a hannun Babban Yaya, kasancewar Maanal ɗin na tsaye a wajen suna magana da babban Yayan kuma sai tsaiwar tasu ta kasance gab-da-gab. Itama daba kallonsa take ba sam hankalinta bai kai da kasancewar kusancinsu ba duk da mayataccen ƙamshinsa ya addabi hancinta. Hirama Naufal ke mata tanata murmushi. Itama dai Nibras hankalinta akan AA da kasancewar Maanal ɗin a kusa da shi yake. Zuciyarta na mata zafi da jin kishin hakan. Ganin Maanal bata tare a sashenta ba ita kaɗai tasan a farin cikin da take ciki. Dan yanda take farin cikin har sai da Fawzan yay mamaki ma ya tambayeta. Amma sai tace da shi babu komai...       Gaba ɗayansu abin sha'awa a tare suka fito wajen da gwarazan motocin mazajen gidan suke duk a wanke. Dan tun jiya Bola ya wanke su fes kasancewar aikinsa kenan. Yara aka fara sakawa a motar su ta makaranta, sannan Baban yaya ya shiga tasa. Abah ya shiga shima tasa driver a gaba yace Maanal ta shigo kusa da shi. Murmushi AA yay a kaikaice kawai ya shiga shima inda nasa drivern ya buɗe masa. Shima Fawzan ya shige tasa hakama Nibras da taji wani kalar daɗi ganin Maanal tare da Abah zata tafi ba AA ba. Cike da mamaki Mamy take kallon motar Abah, dan bata san da komawar Maanal office ba. Sai da duk motocin suka gama ficewa maigadi ya maida gate ya rufe sannan Mamy ta kalla Oum dake murmushi.          “Wai nikam ƴarki badai aiki aka koma ba?”.      Ƴar dariya Oum tayi, ta ce, “Ai na manta muyi maganar jiya. Da ƙyar muka samu mijinki ya yarda, shine aka kafa mana dokar bazata bi Auta ba nace munji”.        Dariyar yaƙe Mamy tayi, a ƙasan ranta tana faɗin (munafuka abinda kika ƙullo kenan jiya dama. Ba komai zan yi maganinku) a fili kam sai cewa tai, “Ai ina bayansa yay maganinku keda ɗan naki”.        “Oh na manta ƴar adawa ce kefa. Nayi nan”. Cewar Oum tana barin wajen. Dariya Mamy tayi kawai, sai da Oum tai nisa da wajen ta gimtse fuska da rakata da harara. Sai kuma suka kalla juna ita da Saheeba dake cike fam da takaici itama. Dan ita sai yau da taga Maanal da ƙyau fiye da ko yaushe taji zuciyarta ta sake girgizuwa. Maanal ba fara bace ba, amma irin Black beauty ɗin nan ce da ALLAH yayma wani kalar sassanyan ƙyawun fuska dana jiki dana fata. Ga idanu masha ALLAH. Ba namiji ba ko mata da yawa sun sha yaba ƙyawun halittar Maanal, a hakanma tana da ƙoƙarin sututurta jikinta ne. Dan bata shigar banza, ko ɗinki bazaka taɓa ganinta da matsatstse ba sam. Gata ƴar ƙwalisa dan tasan sirrin kula da jiki matuƙa. Rashin yawan fara'arta a yanzu kansa irinsu Saheebar shakkarta, dan sai suga kamar ta cika girman kai ne, ita kuma sam a gareta ba haka bane. Maganar ce kawai yanzu bata cika son yi ba ne..... __________★         ZARIA   “Mom please ki barni naje. ALLAH acan nake son yin azumi nidai”.          Harara Hajiya Majdiya ta wurga mata. “Ni kinji nace karkije ne Najma? Ni nace ki kira Mah-mah ki sanar mata, tunda ita tace kije mata azumi kika kuma amsa. Sai yanzu ne zakice kin fasa Abuja zakije. Kina gani kuma tunda muka dawo Rufaidah kullum cikin kira take akan yaushe zaki koma. Ita kanta Mah-mah ɗin jiya muna waya sai da tace yaushe zaki taho.”         Sosai hawaye suka cika idanun Najma. Haushin kanta ya kamata. Miyasa ma ta amsa ma kakar tata zataje can ne. Wayar da sukai ɗazun da Yaya Fawzan ta sake dawo mata. Yanda yake roƙonta akan tazo Abuja tai azumi inba haka ba kullum zai kasance a hanyar Zaria ne. Kuma tasan sunyi alƙawarin ɓoye komai har sai nan da bayan salla Babba ta kammala exam ɗinta... Kamar wadda tunanin nata ya zaburar da ita tai saurin kallon Mom ɗinta.       “Mom na yarda zan kira Mah-mah ɗin, har ma da Aunty Rufaidah ɗin”.     “Sai ki haɗa da Babanki ma. Tunda shima kin san Kano kika gaya masa, kuma ya tsani magana biyu.”        “Mom dan ALLAH ki taimaka min ke ki sanar masa”.     “Wa? Ni? A'a kema kin san ganganne wlhy. Babu abinda ya shafeni. Kinga tashi ki ƙarasa min aiki malama kafin yarana su dawo school da yunwa”.      Sosai Najma ta zunɓura baki tana miƙewa. Kitchen ta nufa dan ɗaura girki. Tana girkin tana neman mafita. Dan bata san yanda zata tunkari babansu ba kasancewarsa mutum mai zafi. Dama da gyar ta samu ya barta zuwa Kanon dan shi kam bai son yaransa suyi nesa da shi ko yaya. Harta kammala tana faman ƙullawa da kwancenwa. Sai da ta fara zuwa ta sanar da Mom ta gama sannan ta nufi ɗakinsu. Miss call har biyu ta samu daga Ya Fawzan. Ta ɗan waro idannunta waje. Kiransa ta shiga yi, sai dai harta tsinke bai ɗaga ba. Tana ƙoƙarin yin na biyu kiransa ya shigo mata. Cike da shauƙi tai masa sallama. Daga can yay ɗan murmushi da faɗin, “Uhm-uhm wannan ƙanwa tawa dai bata jin magana”.        Sosai ta sake kwantar da murya, “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri, ina kitchen ne Mom ta sani girki”.      “Ba damuwa na haƙura ai Mom ce”.      “Yauwa Yayana. Dama fa yanzu zan kiraka. ALLAH akwai matsala......” tsaf ta zayyane masa yanda sukai da mamanta. Murmushi yayi kawai, “Kinga karki damu, ni zan kira Grandma ɗin da kaina. Sannan ki shirya zanzo Zarian na ɗaukeki in sha ALLAHU ”.      Cikin waro idanu kamar yana gabanta ta ce, “Baba fa?”.        “Shima ki barni da shi”.     “Yauwa yaya Fawzan shiyyasa nake sonka”.        “Da gaske?”. Ya faɗa da wani irin shauƙi. Ai da sauri ta yanke kiran fahimtar katoɓarar da tayi. Ita kuma kawai irin tayi maganar normal ne bada wata manufa ba. Duk kiran da yay mata ƙin sake ɗauka tayi kuwa. Shi kuma daga can yayta murmushi. Tabbas kasancewarsa da Najma na bashi farin ciki, duk da kulawar da yake samu a gareta iya ta kalaman baki ce ta ɗara masa Nibras. Shi kaɗai yasan irin haƙurin da yake akan rayuwa da Nibras. Amma yana addu'ar Najma ta zama sanadin sharuwar hawayensa......     Itama dai Najma cike take da wani irin shauƙi, dan har tsakkiyar rai jin son Fawzan take yi. Kafin yanzu soyayya take masa na ƴan uwantaka kawai, amma lokaci ɗaya da bayyana mata manufarsa sai taji al'amarin ya zarce hakan. Yaya Fawzan shine irin mijin da take ma kanta fata. Wato mutum mai sauƙin kai. Gashi ƙyaƙyƙyawa ga nutsuwa da dattako. Sai dai kuma wani gefe na zuciyarta na jin shakkar matarsa. Duk da a zahiri Nibras ɗin ba wata masifaffiya bace, sai dai irin matan nan ne marasa sakewa da mutane.... Shigowar kira a wayarta ne ya katse mata tunani, a zatonta Ya Fawzan ɗin ne ya sake kira, amma sai taga Uncle Rafeeq. Idanu ta waro sosai, tare da ɗagawa da sauri.       “Lah Uncle R kai ne?”.   “A'a bani bane”. Rafeeq ya bata amsa cikin gatse. Da sauri tace, “I'm sorry Uncle mamaki nayi ne. Ina yini? Ya Aunty Nuwaira”.        “Lafiya Lau muke. Miya samu wayar Aunty inata kira a kashe?”. “Nah-nah ce ya shiga da ita bayi ɗazun da safe ta tsunbula a ruwa, shine aka sakata cikin shinkafa”.       “Tofa ALLAH ya kiyaye to, jeki kai mata taki”.    “Okay Uncle. Amma dan ALLAH kafin na kai mata na roƙeka wani abu”.             “Banda kuɗi nayi brock”.        “Kai Uncle nifa ba kuɗi nake nufi ba”.     “To ina jinki”. “Uncle kaga so nake naje Abuja nai azumi, sai aka samu matsala nariga na faɗama Baba Kano zanzo tun kwanaki, yanzu idan nace masa na canja bazai yarda ba, zai ma iya cewa duka a fasa......”.......✍️        _Mu haɗe a Maawad da wanda suka shirya🏃🏃🏃🏃😲_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖🔟 ______________ ........“To ke wace gulmar ta saki canjawar, bayan naji Mah-mah da Aunty Rufaidah na maganar zuwan naki ma”.        Baki taɗan tura gaba, sai kuma cike da shagwaɓa ta ce, “Ni Abuja nake so yanzu Uncle please, idan akai salla su kuma basai nazo musu ba. Kaga nayi ma Ya Fa... Uhm uhm Aunty Maanal alƙawari itama”. Tai saurin waskewa jin katoɓarar da ta nema yi. Jimm Rafeeq yayi yana nazarin sunan data so fara ambata. Sai kuma tunaninsa ya ɗan koma baya akan ganinsu daya dinga yi a bikin nan tare da Fawzan. Tabbas ya zargi akwai wani abu kam, sai dai rashin hujja ya sashi sakin zancen tun a lokaci.....       “Uncle Please mana...” Ta katse masa tunani. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke. Tare da faɗin, “Ba ruwana, kije ke ki samesa ba babbanki bane”.     Sosai ta sanya masa kukan shagwaɓa. Dan haka yace yaji zai yi tunani ta kaima mamanta wayar....       Badan taso ba ta fita kai wayar, tana addu'a a ranta ALLAH ya ɗaurata akansa, dan tasan yanama Baban nata magana zai amince......     _________★        Kusan a tare motar Abah data AA suka iso MAWAAD COMPANY. Maanal dake murmushin hirar da Abah ke mata tabi ko'ina da kallo. Komai yana a yanda ta sanshi. Sai da Abah ya ƙara mata nasiha na karta sakarma AA fuska da Addu'a sosai sannan ya barta ta fito. Hango AA tsaye jikin motarsa yana waya yasata tsayawa har sai da motar su Abah ta fita. Numfashi ta sauke a hankali, wata irin ƙauna ta ɗa da mahaifi na sake mamaye zuciyarta akan dattijon arziƙi Abah. Tabbas alkairin Abah a gareta mai yawa ne, da baki bazai iya musaltashi ba ma. Jinsa take a ranta shi da Oum matuƙa gaya a matsayin mutane masu muhimmancin gaske. Wani murmushi mai sanyi ya ɗan suɓuce mata hawaye na taruwa mata a cikin ido tunawa da nasihar Oum ita kuma. Ita fa dariya Abah da Oum ɗin ke bata ma a kwana biyun nan, Abah na nuna mata ta hora AA, Oum na lallashinta ta yafe masa komai ya wuce su koma kamar da can baya da suke.....        Tunaninta ne ya katse jin an riƙo hannunta da wani tattausan abu da ta tabbatar hannu ne shima. Sai kuma ƙamshin turarensa yay mata irin shigar zuruff ɗin nan ya wuce har tsakkiyar brain ɗinta yabar maƙaƙinsa a maƙoshinta. Cikin ɗan motsawar zuciya ta waiwayo, sai ko idanunta a cikin nasa daya wani tsatstsareta da su. Ƙwacewa numfashinta ya nema yi, ta fisgoshi da ƙarfi tana mai saurin juyawa ta kalla harabar Companyn. Sosai ma'aikatansu ke shigowa ciki, wasu a abin hawa wasu a ƙafa. Da yawansu idanunsu a kansu suke, duk da dai sai wani sinne kawuna suke wanda ta tabbatar na munafuncine kawai. Ƙoƙarin sake juyawa garesa ta sakeyi, dai-dai ya kawo ɗayan hannunsa zai zare handbag ɗinta a ɗayan hannunta. Hucin numfashinsa ya wani irin sauka mata a fuska. Gaba

Chapter 5 of 15