Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
san na miye ba itama. Kawai dai ta tsinta kanta a cikin nishaɗin yin hakanne....      Kusan ƙarfe goma takarda ta iso mata daga office ɗin HOD. Bata komai bace sai ta tafiyarsu. Komai an kammala, sannan iya su da zasuyi tafiyar an basu hutun zuwa aiki gobe, idan ma daga yau mutum zai wuce gidan duk an basu dama amma sai zuwa break bayan anyi zama da su, suyi shiri kawai dan jibi in sha ALLAHU ƙarfe biyar na yamma jirginsu zai ɗaga. Ajiyar zuciya kawai ta sauke a hankali, zata ƙarasa ayyukanta kawai yau ɗin ita kam bazata tafi yau ba. Ƙarfe sha biyu suka shiga meeting. Sai a lokacin taga sauran wanda zasu yi tafiyar da su. Ashe harda cikin manyan ma. Dan akwai CFO, sai CMO, WCD da sauransu..... Sunyi nisa a meeting ɗin kafin CEO ya shigo shida Assistant ɗinsa. Bayan sun zauna ya nema afuwar jikinrinsa, acewarsa yana da baƙi ne. Maanal na ɗagowa suka haɗa ido. Da sauri ta janye nata. AS ne yay musu bayanin abinda zasuje yi, dan kowa da fanin sa, tare da karanto musu dokokin tafiyar. Zasu yi kwana goma ne, kenan zasu dawo azumi nada kwanaki takwas, dan yau saura kwana huɗu a fara. Daga ƙarshe yace kowa zaiga alert na kuɗi a cikin account ɗinsa domin shirin tafiyar. Bayan komawa ya zauna AA ya dubesu a dakensa, idonsa ne ya sauka akan Maanal a karo na barkatai, sai dai yanzu ita ba kallonsa take ba, tana magana ne da Yaqub ƙasa-ƙasa, da'alana akwai bayanin da yake mata da bata gane ba a maganar AS. Shima janye nasan yayi yanayinsa na canjawa sannan ya fara musu nasa jawabin mai cike da gargaɗin daya saka Maanal ɗagowa ta dubesa, harara ya sakar mata a kaikaice, wani gefen kuma nasiha ce. Ya rufe da addu'a daga haka meeting ɗin ya tashi. A tare Maanal da Yaqub dake mata sallama suka fito, sai kawai jitai an riƙo hannunta, juyowa tai da sauri, sukayi ido huɗu kuwa da mai gayya da aiki. Wani banzan kallo yay mata, sannan ya zubama Yaqub wani kallon gargaɗi daya sakashi barin wajen da sauri....... __________★ اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ. Allahummak finihim bima shi'ita. _Ya ALLAH! Ka isar mini su da abin da Ka so._ _________★ AIRPORT           Cike da farin cikin dawowarsa ƙasar haihuwarsa bayan dogon hutun daya sha na watanni uku yake fitowa a jirgin. Yayi fresh da shi dan ma tsufa ya cinye komai. Ƙarfarsa na gama sauka bisa ƙasa idonsa ya sauka kan amaryarsa, gefe kaɗan Oler ne da Rabilu sai sauran yaransa dai na siyasa. Sen... Bukar Kaugama yay wani murmushin jin daɗi mai cike da ma'anoni. Dan kuwa abu biyu ke ɗawainiya da shi, farin cikin dawowa ƙasarsa a gaɓar da zai mallaki ƴar shilar amaryarsa Maanal, da kuma kewar ƙasarsa ta haihuwa. Babu kunya amaryarsa tazo ta rungumesa tana masa barka da dawowa cike da farin ciki.       Cikin irin nasu salon na manyan ƙasa ya wani ɗan bubbuga bayanta da ɗan mata ƙaramin kiss a gefen fuska sannan ya janyeta daga jikin nasa ya riƙe mata hannu. Sai lokacin su Rabilu sukayo wajensa suma. Fuskokinsu da farin ciki suke masa barka da zuwa. Shi ko yana amsa musu da kulawa. Basu wani ɓata lokaci ba suka ɗunguma inda jerarrun motocin da sukazo tarbarsa suke. Aka buɗe masa wadda tafi kowacce daukar ido shi da amaryarsa suka shige. Motocin na fitowa a airport ɗin tawagar uwargidansa na isowa itama tarbar tasa. Sunata sauri ganin sun makara, sai dai kuma basu dace ɗin ba. Drivern ta daya lura da motocin ne ya ce, “Ranki ya daɗe ai kamar ha Excellency ɗin ma can fa har sun fito”. Da sauri ta kalla motocin itama, tabbas kuwa motocin gidansu ne, sai dai motar da ta tabbatar yana a ciki tasan tana a gidan amaryarsa ne ajiye. A take ranta ya ɓaci matuƙa. Cikin fushi da jin zafin kishi tace, “Mubi bayansu”.      Babu musu yay reverse, hakama drivern daya ɗakko yaranta shima, sai ma'aikatan gidanta, motar ƙawayenta ce ƙarshe, dan kuwa shiri tai na musamman akan dawowar tasa yau tare da shirya masa wani ƙwarya-ƙwaryar liyafa dan ranar tayi dai-dai fa Anaversary ɗin aurensu. Motocin su amarya na gama shiga maigadi zai maida gate ya rufe na uwargida suka iso. Dole ya dakata dan aguje suke. Fuskar Sen... Bukar da murmushi ya fito a motar, dan amaryar tasa ce ke zuba masa iskanci a motar, shiko ya narke mata. Da ƙyar ma ta bari suka fito. Sai dai me yana gama fitowa Uwargida ran gida na tsayawa a gabansa kamar wadda aka jeho. Hamshaƙiyar mace data amsa mace, dan kuwa sune manyan mata. Amma (iyayi na mutum nan yace bai son ƙiba🙄, shima kuma fa ƙaton gaske ne🥱). Yanda uwargidan ke kallonsa cikin ido dole ya ƙaƙaro murmushi tare da ɗan rungumota yana faɗin, “A'a ku kuma maimakon airport nan kuka yo?”.        Itama a maimakon bashi amsa ɗagowa kawai tayi daga jikinsa, sai kuma ta kama hannunsa a dake ta ce, “Muje ko! Ga mutane a waje na jiranmu”.      Gaba ɗaya daburcewa sen.. Bukar ya nema yi, dan kowaccensu da shirinta take an kai sunansa wajen teacher na zaure, ya kalla amarya ya kalla uwargida. Kowacce ta haɗe fuska abinta kamar dai a film. A ransa faɗi yake (wadda duk zata ɗaukeni gaba ɗaya daga hannunku ta kusa zuwa ai tula-tulan banza). Amaryar ƴar tsiyace ya sani, ita kuma uwargidan bata da yawan magana amma itama fa ba daga baya ba tasan ta inda take dafa shi duk rashin mutuncin da yake musu musamman ma ita da babu kalar da bata gani ba. Fuuu amaryar ta shige ciki ita mai zuciya, a zatonta ai zai biyota kamar yanda yake mata idan su kaɗai ne musamman ludayinta na akan dawo, (bata san yanzu akwai Manaal ba😂), wannan ya bama uwargida dama ta jashi suka wuce...... _________★ اَللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ اْلأَحْزَابَ، اَللَّهُمَّ اهْزِمْهُمْ وَزَلْزِلَهُمْ. Allahumma! Munzila-l-kitabi, sar'a-l-hisabi! Ihzimi-l-ahzaba. Allahumma ihzimhum wa alzihlum. _Ya ALLAH! Mai saukar da littafi, Mai gaggawan sakamako! Ka karya kungiyoyin abokan gaba. Ya ALLAH! Ka karya su, ka girgiza su._ ________★      Idan Maanal tace yanda taga fuskar AA hankalinta bai tashi ba ƙarya tayi, ita shaida ce tun suna ƙanana ya tsani yaga tana kula wani, ko ƴan uwansa su Fawzan dan baida yanda zai yi ne kawai. Addu'a ta shiga karantowa a zuciyarta ita dai, dan yanda ya damƙi hannun nata ma ji take kamar ta fasa kuka. Suna shiga office ɗinsa a kusan tsakkiya ya sakar mata hannu, batare dako kallonta ya sakeyi ba ya wuce kujerarsa ya zauna. Aikinsa ya cigaba da yi tamkar yama manta da ita. Itama tun tana basarwar harta koma satar kallonsa, tama kai ta zuba masa idanun kai tsaye. Kusan mintuna ashirin taji ƙafafunta na neman sagewa, zuciyarta kuma nata angizata akan taje kawai ta bashi haƙuri, dan itama abinda yay ɗin ya sake fargar da ita alaƙarta da Yaqub fa dole ne ta tsaya a iya matsayin daya dace, ba kamar ada da suka ɗan fara ba kodan darajar aure da kare mutuncin wanda yake a matsayin mijin nata kuma ogansu a ma'aikatar gaba ɗaya. Sai kuma nasihar Ammie da Nene da ma Oum take mata faman kai-kawo a rai, basuce ta wulaƙanta kanta ba, amma sun gargaɗeta ta sauke nauyin dake kanta musamman a gaɓar data san abu kuskurenta ne. Gyarawar tata shima zaisaka ya gyara nasa kura-kuran su gina ƙyaƙyƙyawar rayuwar aure mai nagarta, dan ita wannan rayuwar tasu ta yanzu tana da banbanci da wadda sukai a baya ta ƙuruciya musamman ga ita dake ƙarama sosai, tunda ko acan bayan tasan nagaba yay gaba, kawai dai ita dashi haɗuwar jini ce bawai abotar kai da kai ba. A hankali ta fara takawa zuwa inda yake tamkar mai koyan tafiya, maimakon zama a visitors chair kai tsaye inda yake zaune ta zagaya. Kusa da shi kaɗan taja ta tsaya, hakan datai ya saka ziciyar AA ƙara gudu a ƙirjinsa, dama can bawani aiki yake yi ba, dan ji yay bama ya fahimtar komai. A yasan shima yana da kishi mai karfi a kanta, dan haka yake so ta gane kuma ta kiyaye, duk da kuwa sanin hakan a gareta game da shi ba sabon abu bane ba ai, amma ya fahimci kamar ta manta ne....        “AA!”.   Ta kirashi da sunan da abakinta ya fara jinsa, ga shi nan kuma ya bisa dan wasu da yawa a yanzu bama su iya tantance ainahin sunansa sai AA Darma kawai. Duk da harbawar da zuciyarsa ta shiga yi a ƙirjinsa saboda tasirin kiran sunan nasa da tai bai kalleta ba, aikinsa kawai yake kamar gaske.           “Besty fushi fa ba ƙyau!”.     Ta faɗa tana leƙa fuskarsa cike da shagwaɓa. Nan ma tamkar dutse haka yay mata shiru. To itama fa zuciyar tata ta fara hawa, dan haka tai shiru kawai tana kallonsa. Tsahon mintuna uku taga ba kulatan zai yi ba kawai saita nufi barin wajen. Karan farko ya ɗago ido ya bita da kallo, itako ta wuce fuuuu alamar dai itama ta hau sama. Shima ai yasan yanda ya tsani yay magana ai masa shiru haka itama ta tsani ɗabi'ar. Har ita zai nunama zuciya da kishi, ita jiya ba ɗaukarta yay ya kaita wajen budurwarsa ba dan wulaƙanci, amma mitace masa, sai shi dan kawai ya ganta da abokin aikinta, to shike nan kuma bazata dinga mutunci da mutane ba'a Companyn?.       Tana gama fita yay wani irin watsar da file ɗin hannunsa akan desk ɗin, sai kuma ya buga shi ya juya kujerar ya kalla bangon wajen daya kasance glass....     Manaal na shiga office ɗinta kayanta ta tattara tsaf tai fitowar ta. Duk inda ta gitta gaisheta akeyi, ita sai suka ma ƙara bata haushi. ALLAH ya sota sanda ta fito harabar kamfanin duk ana ciki, sai securitys ne kawai ke ɗan kai-kawo. Suma duk wanda ta gitta sai ya gaisheta, drivern AA dake cikinsu yana hira yana hangota ya taso da sauri, gaisheta yay, tare da faɗin bara ya ɗakko mota. Amma sai sai tace da fa shi karya damu su Abah na jiranta a waje. Jin tace Abah ya sashi dakatawa, haka ta fita a ƙafa a kamfanin.         Tun fitiwarta harabar kamfanin sosai idon AA ya sauka a kanta, har maganarta da drivern sa da gaisuwar da securitys suke mata duk ya gani, kawai dai baya jin mi suke faɗa ne. Ji yay zuciyarsa ta ƙara hasala. Da ga zaunen da yake bazai iya ganinta ba yanzu saboda ta fita a kamfanin, dan haka ya miƙe tare da matsawa jikin gilashin. Sai ko ya hangota ta tsaida wata taxi ta shiga. Idan AA yace zuwa yanzu zuciyarsa batai kumburar da take neman fashewa ba yayi ƙarya. Shi yarinyar nan zata wulaƙanta da mutuncinsa a garin nan tana matarsa ta shiga taxi, shi zatama laifi ta fishi zuciya kuma. (Amma ai ta zo lallashinka kaƙi kulata) Wani sashe na zuciyarsa ta faɗa. Ji yay kamar ya kaima zuciyar naushi, amma dai ya daure, wajen ya bari gaba ɗaya, sai ma ya koma rukunin kujeru ya zauna, dan yasan ko aikin yace zai cigaba shirme kawai zaita tafkawa.........✍️ حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ. Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel. _ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro._ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣1️⃣ ______________ .........Maanal dai ta isa gida lafiya abinta, ALLAH ya sota a wallet ɗinta akwai kuɗi, haka ta cire ta biya shi tai ciki. A ƙasan maƙoshi AA dake bibiyarta ta hanyar GPS tracker ya sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya kife wayar a saman desk ya kwantar da kansa da bayansa jikin kujerar da yake ya lumshe idanunsa. Maanal na shiga Nuratu da Hajiya Turai na fitowa a mota, da alama zuwansu kenan. Idon Maanal ne ya sauka akan ƙaton akwatin da Bola ke fitarwa a booth. Tayi niyyar wucewarta, sai zuciyarta ta gargaɗeta da hakan kodan Hajiya Turai dake babbar mace. Dan zata iya sa'a da Ammiensu koma ta girmeta. Duk da ta lura da kallon banzar da Nuratu ke mata saita watsar da ita, kaɗan taɗan matsa kusa da su ta gaida Hajiya Turai dake kallonta itama irin kallon ƙasan idon nan na ƙurulla. Bata kuma jira jin a yanda ta amsa mata ba tai gaba abinta. Daga Nuratun har Hajiya Turai binta sukai da kallo, tsakin da Nurry taja yasa Hajiya Turai faɗin, “Ko itace Maanal ɗin?”.      Baki Nurry ta taɓe, a gadarance ta ce, “Waifa Momy itace, shegiya baƙar banza, tana tafiya tana murguɗama mutane ɗuwawu dan asan tana da su ko”.        Hajiya Turai dake bin Maanal ɗin da kallo har yanzu ta ce, “Yoni Baby yarinyar nan ma nada muhimmanci kuwa a gidan nan? Kamar fa daga wajen aiki take a ƙafa alamar taxi ce ta ajiye ta, ace duk motocin gidan Darma ace surukar gidan na hawa taxi kuma matar AA duk dukiyarsa”.        “To Momy dama ba aikin asiri bane yasa ta shigo gidan, tunda ya riga ya gama da ita tun a titi wace soyayya zata gani kuma. Ba dai na shigo gidan ba, sauran asirin ma dan ubansa zan ƙarasa karyashi ne. Ana gama bikinmu zata ware dan sai ta sha ƙi baƙin cikin shagalin da za'a sha kafin na sa ya saketa.”      Sosai Hajiya Turai ta sanya dariya. Tamkar wasu ƙawaye ta bata hannu suka tafa. Daga hakan suma suka nufi sashen Mamy cike da nishaɗi...   Oho Maanal ma bata san sunai ba, tana shiga sashen Oum sama ta wuce abinta. Ta samu Oum da baƙuwa. Maanal ta gaishe da matar ƙyaƙyƙyawa da ita. Itako cike da kulawa take tambayar Oum, “Hajiya Fateema ko ɗiyar tamu ce?”.     Murmushi Oum tayi, ta ce, “Itace Hajiya Shuwa”.       “Kai Masha ALLAH, yarinya dirarriya ƙyaƙyƙyawa haka ga nutsuwa. A ruwan idon autanki bai tafi a banza ba ashe, ashe yasan miya taka, ɗaya yake son tsamowa a cikin dubu, to ALLAH ya sanya albarka a cikin auren nasu”.      Oum dake ta murmushi ta ce, “Amin ya rabbi”. Sai kuma ta kalla Maanal dake nufar hanyar bedroom. “Baby wai har kun tashi ne? Ina Bestyn naki?”.       Cikin danne komai Maanal taima Oum bayanin su an basu damar zuwa suyi shiri ne saboda tafiyar jibi. Oum ta ce, “Tofa tafiyar ta tashi ke kenan?”.     Manaal ta ce, “Eh Oum.” daga haka ta shige ta barsu. Hajiya Shuwa da gaba ɗaya Maanal ɗin ta ƙara birgeta ta ce, “Kai masha ALLAH, jiba yanda ta saki jiki dake kamar ba surukai ba, haka naso mu rayu da Amisha amma ƙawayen banza sukai mata huɗubar tsiya. Shiyasa yanzu nace masa aure zai ƙara, dan na gaji da ɓacin rai wlhy Hajiya Fateema. Wani lokacin idan aka juya min kan yaron nan ko kallo ban isheshi ba, shiyyasa kikaga nai tafiyar nan marocco ko sallama ban miki ba. Shi ma kansa bai san na tafi ba sai bayan kwana uku”.       “Kiyi haƙuri Hajiya Shuwa jarabawa ce, kowa da irin tasa kuma. Amma Amisha ta bama kowa mamaki, dan nidai ina ganinta shiru-shirun nan banyi zaton haka a gareta ba. Ni kaina yanzu saboda tasan yanda muke dake bata shigowa gidan nan, har mukaci bikin nan muka tsare bata leƙo ba, shima Ameer ɗin Fawzan yace baije mana ɗaurin aure ba, shine ma ya haɗasu faɗa shine yake cemasa ai dama Amisha tace ba sonsu muke ba, nice ke zugaki kina wulaƙanta masa mata. Nace ma Fawzan ya barsa baya cikin hayyacinsa ne kawai”.        Kwafa Hajiya Shuwa tayi, ranta na sake mata zafi da halin da ɗan nata yake ɗaya tilo namiji. Su Hajiya Shuwa sune makwaftan su Oum ta hannun damar su, asalinta ƴar marocco ce girman Libya, daga can mijinta Alhaji Mubarak KT ya aurota, yara biyu suka haifa kacal a duniya, Ameer shine babba, bayan haihwarsa ma ta jima bata sake ba harta haƙura ma sai ga ciki. Sunyi farin ciki sosai ita da mijinta, ALLAH ya sauketa lafiya ta haifi mace ƙyaƙyƙyawa itama suka saka mata Ameerah, bayan haihuwar Ameera bata sake ba kuma, yarinyar nada shekara goma a duniya ALLAH yayma Alhaji Mubarak rasuwa sakamakon bugawar zuciya na dare ɗaya daya samu. Shi ɗin babban ɗan gwagwarmaya ne kuma ɗan siyasa ta wani gefen, duk da dai bai saki jiki a siyasar ba gaba ɗaya. Yana kuma kasuwanci sosai. Ya tafi ya barta da yaran su biyu, ita ga cigaba da kulawa da rayuwarsu har girma, duk da dai sanda ma ya rasu Ameer har ya shiga University yana first year ɗinsa. Ameera ce ke primary 4. Tasha wahala da dangin mijinta dan dukiyar ƴaƴanta komawa tai tsole musu ido, acewarsu ai ɗan uwansu ne ya tara, bazai yiwu ya aurota daga wata ƙasa ba daga sama tazo ta mamaye komai, aiko suka ƙulla mata akan ta basu yara su cigaba da riƙewa da dukiyar ita kuma ta koma ƙasar ta. Hankalinta ya tashi, dan babu wanda take tausayi irin Ameera. Nanfa ta shiga faɗi tashin ganin hakan bata kasance ba, tana neman taimakon abokan mijinta, amma mi, kowa sai ya nuna sai in ga amince zata auresa zai yi hakan, wasu ma da iskanci suke zuwa mata. A cikin wannan kai-kawon nata ne suka haɗu da Ambassador Aliyu Darma, ta dalilin nashi abokin shima da ya kasance abokin mijin Hajiya Shuwa. Shima dai yayi mata maganar banza ne, ta fito ranta a ɓace shine sukaci karo da Abah da yaji komai dan yay ƙoƙarin shiga office ɗin ne yaji kalaman abokin nasa sai ya tsaya, amsar da Hajiya Shuwa ta bashi yay matuƙar birgesa, data fito kuma ya ganta mace mai kamala da nutsuwa. Baice mata komai ba a lokacin ta wuce ya shige, bai kuma nunama abokin nashi yasan komai ba shima. Sai da ya dawo gida ya sanarma Oum komai, hankalinta ya tashi baiwar ALLAH harda kukanta. Itace ta ƙarfafa Abah suka shirya taimakon Hajiya Shuwa, washe gari taje har gida ta sameta, zuwa ranar kuma Hajiya Shuwa ta sallama ma dan Oum ta sameta tana haɗa kayanta, tana shirya nasu Ameera domin danƙama dangin uban nasu kamar yanda suka buƙata. “ALLAH sarki na ALLAH baya ƙarewa duk rintsi”____wannan itace kalmar da Hajiya Shuwa ta faɗa bayan Oum ta gama mata bayanin abinda ya kawota, daga haka ta rungume Oum tana kuka...      Wannan shine sanadin tarayyar su, Abah ya tsaya mata akan komai har sai da aka mata tsakani da dangin Alhaji Mubarak, aiko sai akaita gulma ai sonta Abahn keyi, dan har Mamy ma ba sonta take ba ta kuma tsargu da hakan, musamman data roƙa Abah ya sayi filinsu dake a kusa da su dan lokacin su suna a zone 4 ne. Da farko Aban yaƙi, gudun kar ace ta basu ne shiyyasa suka taimaketa, sai da taita roƙonsa da tabbatar musu zamansu a kusa zai zamar mata garkuwane sannan ya amince. Ƙaton filine amma sai da Abah ya ƙara da wani a bayansu shine ya gina wannan babban gidan suka zama makwaftan juna. Anta jira aga Abah ya aure Hajiya Shuwa amma akaji tsit har ma shekaru suka ja. Ameera ita ta ɗan ragema Oum kewar Maanal a lokacin, har ALLAH yasa ta wuce karatu waje ita, yanzu haka tana can, amma tana gab da dawowa ƙasar haihuwarsa. Amisha ƴar ƙanwar Hajiya Shuwa ce, auren zuminci ne ita da Ameer, duk da kuwa su sukaga juna suka gina soyayyar su ba iyayen suka haɗasu ba. Farkon auren kowa nata yabon Amisha musamman data kasance da suffar mutane masu shiru-shiru da haƙuri, sai da tafiya tai tafiya sai komai ya canja, yanzu Amisha aya take gasama Hajiya Shuwa a hannu, har takai wataran idan ta juye kan Ameer ɗin sai ya manta da Hajiya Shuwa na a gidan ma tare da su gaba ɗaya. Sai ta dage da addu'a sai abin ya sassauta. Watanni kusan bakwai kenan abubuwa suka rikice a tsakaninsu shine kawai ta tattara ta wuce marocco sai jiya ne take dawowa, bata nan akai bikin su AA ɗin, sai bayan wucewarsu aiki ta shigo shine suketa hira da Oum ɗin dan ƙawaye ne sosai...       Baƙi da aka kira Hajiya Shuwa a waya cewar tayi ya sata tafiya gida, sai lokacin Maanal ta fito falon, tayi wanka abinta fes sai ƙamshi take. Takardar da aka basu a wajen aiki ta bama Oum ɗin, tare da zama gefenta ta ɗaura kanta a kafaɗarta. Shafa kan nata Oum tayi tana murmushi, cike da kulawa ta ce, “Ko azumin ya fara duka?”.       Shaf Maanal ta manta da ƙaryar azuminta, ta kalla Oum tana dariya. “Lah Oum ƙarya fa nayi dama babu wani azumi ɗazun ban son karyawa ne kawai”.        Idanu Oum ta zaro waje, sai kuma ta dungure kan Maanal ɗin tana dariya itama. “ALLAH ya shirya kin Baby na to da har yanzu bata canja hali ba”. Dariya itama Maanal tayi, tare da ɓoye fiskarta a jikin Oum ɗin. Itama Oum na cigaba da dariyarta ta ce, “To aiko tare zamu shiga kitchen yanzun nan idan munyi sallar zuhur”.          Haka ɗin kuwa akai, bayan Oum ta kammala duba takardun ta riƙe a hannunta akan zata nunama Abah, duk da dama ta masa bayani akan tafiyar amma bai ce mata komai ba. Salla suka je sukayi, koda suka fito kai tsaye kitchen suka nufa, sun fara aikin kenan Mamy da Hajiya Turai da Nurry suka shigo sashen. Oum ce kawai ta fita suka gaisa, basu wani jima ba Hajiya Turai tace bara ta wuce tunda taga Oum ɗin aiki suke itama zataje wani waje ne. Godiya Oum tai mata, sunzo zasu fita Maanal ta fito ta gaishesu. Tana kallon hararrata da Nurry take bata kula ba ta koma kitchen ɗin abunta. Sai da zasu fita Mamy ke faɗin, “Lafiya ƴarki ta dawo aiki da wuri haka yau?”.       “Lafiya Lau, daga office ɗin ne aka basu damar zuwa suyi shirin tafiya ne”.       Sai Mamy ta rasa ina zata kamo zancen tafiya kuma. Amma bata nema ba'asi ba dan tana son su fita su ƙarasa zancensu da suke da Hajiya Turai. Ba kuma tason ma Hajiya Turai ta fahimci bata san da zancen da Oum ɗin keyi ba dan yanzu ta gama cika mata baki akan batun dawowar Maanal a taxi. Ta nuna itace ta kafa sharaɗin sai dai Maanal ta hau taxi amma ba motocin gidan ba, shiyyasa sukaga hakan. (Mamy an iya ƙayya🤣🙏)     Tsulum Nuratu taja ta tsaya tana faɗin, “Momy bye nima zan zauna taya Oum girki, bara naje wajen sis.. Manaal ɗin”. Daga haka ta juya ciki ta nufi kitchen tabar su Oum na murmushi. Duk da dai abinda Nuratun tayi ya bama Mamy takaici, amma sai ta danne... Maanal na cikin aikinta ita da su Inte dake musu ƴan yanke-yanke a work table Nurry ɗin ta shigo. Ko kallon inda take Maanal batai ba, sai su Inte ne ke gaisheta a girmamame, itako tana amsa musu a yamutse. Sun riga sun san halinta shiyyasa basu wani damu ba. Dai-dai nan Oum ta dawo, dan haka Nuratu ta nufi wajen Maanal cike da makirci tana faɗin, “Sis.. Maanal mizan tayaki da shi?”.         Wani shegen murmushi kawai Maanal ta saki tana kallon Nurry ɗin a tsakkiyar ido, a zuciyarta faɗi take, (Yarinya ai indai makirci

Chapter 11 of 15