Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba, amma dai zuciyarsa ta riƙe abun matuƙa..........✍️ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖3️⃣ ______________ ........Mamy kam a inda tabar su Fawzan anan ta samesu, sai dai yanzu Nibras ta ƙaru.       Ɗan tsurama Nibras ɗin datai mata wani iri idanu tayi, sai kuma cikin tausasawa ta furta, “Nibras baki da lafiya ne?”.        Kallon Nibras ɗin Fawzan da Babban Yaya suma duk sukayi saboda jin furicin Mamyn. Cikin damuwa Fawzan ya ce, “Mamy gara kam ki tambayeta ke, dan tun jiya nima nake fama da ita amma sai tace ba komai gajiyar biki ce wai.”            Cikin jinjina kai Mamyn tace, “Itama gajiyar bikin akwaita ɗin ai, dama sai a hankali zata saki kowa duk da ga wani na tunkarowa kuma dai. Kinga kije ki samu ki gasa jikinki da ruwa mai zafi sosai sai kisha pracitemol ki kwanta abinki kiji. ALLAH ya ƙara sauƙi”.       Ji Nibras tai kamar ta zageta, amma sai ta daure ta jinjina mata kai kawai da faɗin, “To Mamy”. Daga haka ta juya ta fita zuciyarta na mata zafi da ƙuna matuƙa. Tazo ne dan taga fuskar AA ko zataji sassaucin abinda ke cizon zuciyarta, amma Mamyn ta wani korota. Ba komai zata dawo ne, dan in har yau Fawzan anan  zai kwana ALLAH sai dai su kwana tare a sashen AA ɗin. Koba komai ta rage raɗaɗin kishin dake dafa mata zuciya. Sau ƙin ma har yanzu ko sau ɗaya bataga Maanal a sashen nashi ba..        Fitar Nibras ya saka Mamy ma yunƙurin tafiya, amma sai Babban Yaya ya dakatar da ita cikin ladabi. Tsayawa tai tana kallonsu su duka. Fawzan ya ce, “Mamy dan ALLAH magana zamuyi ne”.       Wani irin sanyi mai silalar da kuzari ne ya shiga bin jijiyiyin jininta yana gauraye jikin ta. Yayinda wani farin ciki ke cika zuciyarta tamkar kumfar omo a cikin ƙaton bahon wanki. Yau itace yaranta ke faɗa mata suna son yin magana da itane iya su kaɗai babu matar can a tsakkiyarsu. Ya rabba, ita kam mizatace da UBANGIJI yau. A zahiri kam sai ta dake babu wani alamun komai a fiskarta ta dawo ta zauna. Babban Yaya ne ya fuskanceta da ƙyau cikin nutsuwarsa.      “Mamy akan Ajwaad ne dama muke son dan ALLAH kisa baki a tsakanin rikicin Abah da Oum. Dan ALLAH ki taushi Abah akan ya bari Maanal ta tare a ɗakinta gobe idan ALLAH ya kaimu, dan gani yake kamar Oum ta kasa fahimtarsa ne saboda soyayyarmu ta rufe idonta, Auta na buƙatar matarsa a kusa da shi ya fahimci Oum dan ALLAH”.       Sosai kalmar soyayyar nan ta daki zuciyar Mamy, dan saida ta maimaitata a zuciya yafi sau uku. A fili kam sai ta sake raunana fuskar tata ta ce, “Oh dama wani abune ke faruwa? Ai ni na zata dan bashi da lafiya ne kawai bata tare ɗin ba. Yau gajiya tasa sau ɗaya kawai muka haɗu da Oum ɗin. Amma gaskiya ai Abahn naku ya faɗa, Mamanku ta cika rigima akan al'amarinku.....”     Cikin ƴar dariya Fawzan ya ce, “Kai Mamy kema haka zaki ce”.         “Ai gaskiya ne Fawzan, ita idan kaga tana fushi a gidan nan abu ya shafi ɗayanku ne. Karku damu zan sameshi muyi magana in sha ALLAHU. Itama zuwa da safe zan zauna da ita. Ni bara naje na ɗan kwanta nima kamar Nibras ɗin gaɓɓaina duk ciwo suke min”.      Godiya sukai mata da sai da safe. Fitarta babu jimawa Oum ta shigo itama. Su duka miƙewa sukai sukai kanta ganin har yanzu fiskarta a cinkushe, ga idannunta kamar wadda tayi kuka. Take suma duk fuskokinsu suka sauya. Murya a rauanne Babban Yaya ya ce, “Oumna Please ki cire damuwar nan, kin san fa Abah wani lokacin dan kawai ya kunnaki ne bawai abinda ke ransa kenan ba.”        “Amma Fadeel ya tausaya masa mana, kwance fa yake baida lafiya. Shin ALLAH ma ba muna masa laifi ba ya kuma gafarta mana saboda rahamarsa”.     “Hakane Oum shima zai huce”. Cewar Fawzan yana mata murmushi da kama hannunta ya sumbata. Haka sukaita lallashinta har sai da tayi murmushin itama. Kafin su nufi bedroom ɗin AA ɗin. Ganinsa zaune a bakin gado yasa ta ƙarasa shiga ciki da sauri, kusa da shi ta zauna tana mai riƙo hannunsa daya dafe kansa da shi, dan yaji duk zancen Mamy da su Babban Yaya. Mamakin Mamy da halinta ke sake raunana masa zuciya, amma yana mata fatan shiriya kafin lokaci ya ƙure mata. Yasan duk abin nan fa Abah keyi daga cikin shirinta ne, zai kuma bama kowa mamaki in sha ALLAHU cikin sauƙi.           “Auta yaya akayi? Kanne har yanzu dai?”.     Karan farko ya kalla Oum ya sakar mata murmushin ƙarfin hali, sai kuma ya kwantar da kansa a saman kafaɗarta. “Ya daina Oum”.       Ya faɗa acan ƙan maƙoshi.     “To Alhamdullah, ALLAH ya ƙara lafiya baby na kaji, yanzu mi kake son ci?”.        “Oum tea kawai”.    “To ba damuwa bara Fawzan ya haɗa maka”.    Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya kalla Babban Yaya da Fawzan. Murmushi yay musu kaɗan, suma dake kallonsa suka maida masa murtani suna tambayarsa yaya jikin nasa. A samman laɓɓa yace da sauƙi. Daga haka Fawzan ya fita haɗa masa shayin. Kallon Oum ya ɗanyi, har ya janye idanun sai kuma ya tsira mata su, kafin tai ƙoƙarin dai-daita fiskarta har ya furta, “Oum kinyi kuka”.      “Kukan lafiya Auta ”. Ta faɗa tana ɗan harararsa cikin yanayin son basarwa. Ina bai gamsu ba, cikin rashin kuzari ya zamo ƙasan lallausan carpet ɗin gaban gadon ya zauna yana mai zuba mata idanunsa dake a shanye. Zatayi magana ya girgiza mata kai, “Oum Please ki daina damuwa, nasan a kaina ne ko? Dan ALLAH ki bari naji sauƙi fa, ki tambayi babban Yaya ma”. Ya ƙare maganar yana kallon babban yaya a raunane.     Cike da tabbatarwa babban Yaya ya jinjina kansa shima yana kaiwa zaune kusa da Oum ɗin, Fawzan ma yazo ya miƙama AA kofin tea ɗin daya haɗa masa suka zagayeta kowa na mata nashi daddaɗan kalamin, idan ka gansu abin sha'awa da birgewa sojojin yaƴanta zagaye da ita, basu barta ba har sai da fiskarta ta washe da fara'a kamar yanda suke so. Shima AA sai ƙoƙarin ƙarfafa kansa yake yanda hankalinta zai ƙara kwanciya. Ganin dare yayi Oum da babban Yaya suka baro sashen suna ƙara tattaunawa aka bar Fawzan da zai kwana da shi. Bayan wucewar tasu ne Fawzan ya zayyanema AA komai dake faruwa ana rikicin da Abah keyi akan tarewar Maanal kamar yanda ta buƙaci ji. Murmushi AA yayi mai faɗin da har ya saka Fawzan zuba masa idanu baki buɗe.           “Oh abin ma kai nishaɗi ya baka kenan?”.    Cewar Fawzan cike da mamaki. Murmushin AA ya sake saki a karo na biyu, sai kuma a hankali ya jingina da fuskar gadon yana kai hannu ya ɗan shafo gashi kumatunsa. “To yaya Fawzan in bai sakani nishaɗi ba kuka kake son nayi, banda ma abin Oum minene abin ɗaga hankali anan, ta bar masa ƴarsa mana”.       Dariya Yaya Fawzan yayi da faɗin, “Oh hakama zakace? ALLAH yasa ya jika, kaga idan sati ɗaya yay niyyar horaka sai ya maida shi wata uku kadai san halin Abah”.       Murmushi kawai AA yayi kaɗan batare daya sake cewa komai ba. Fawzan kuwa ya tasashi gaba da tsogumi... __________★       Washe gari da safe Alhamdullah Oum ta tashi da sauƙin damuwa ba kamar jiya ba. Dan tunda ta kira Mah-mah a ɗazun da asuba ta sanar mata sai Mah-mah ɗin ta tausheta da mata nasiha akan ta sakama Abah ɗin ido, ta bashi damarsa matsayin mahaifi dan ko yaya shima bazai yi abinda zai cutama Ajwaad ɗin ba ai, sannan kuma tunda a gida ɗaya suke ai babu wani abun ɗaga hankali in dai yaran yanzu ne masu ƙarancin kunya, shi da kansa ma zaice ya ɗauki matarsa basai ta ɓatama kanta rai ba. Ji tai zuciyarta ta rage jin haushin Abah ɗin, ta kuma ɗau alwashin daidaita komai a tsakanin AA ɗin da Maanal ta yanda Abahn da kansa zai tattarasu ya kora sashen nasu batare da alwashin nasa ya cika ba.        Yau ɗin yanda Manaal take ta faman sinne-sinnen kai ya saka Oum kamata ta duddungure da faɗin, “Wai Auta ni kike son maidawa surukarki a gidan nan, jiya na saka miki ido ne kawai naga iya gudunki, to kar naji karna gani. Maza tashi muje kitchen ki haɗama mijinki abinci yau kije ki duba jikinsa dai kada mu take doka”.     Murmushi Maanal tayi tana ɓoye fuskarta a jikin Oum ɗin, itako Oum na mata dariya. Atare da Oum suka shirya abinci mai sauƙi ma AA ɗin har kala uku, sai wanda suma zasu ci, dan yauma Abah a sashen Mamy zai karya. Suna kammalawa Oum tace taje tai wanka, yayi da masu aiki keta faman kimtsa sashen kamar yanda suka saba. Ba wata kwalliya Maanal tayi ba, ta dai gyara fuskarta ta ɗan saka kwalli da lipsgloss, sai tai simple ɗaurinta daya zauna mata ɗan kwantaccen gashinta ya ɗan fito ta gaban goshi kaɗan. Tana ƙoƙarin saka turare kiran Amaal ya shigo mata. Ɗagawa tai cike da shagwaɓa dan haushinsu take ji a Kano sunce zasu dawo amma sukai mata wayo. Dariya Amaal ɗin taita mata, sannan ta kwantar mata da hankali akan ai next week in sha ALLAHU suna nan tafe da sauran kayanta, dan Daddy yace sai zuwa ƙarshen sati za'a kai kayan gararsu ita da Huznah. Duk da dai Oum tace a ɗan saurara akwai sauran biki da zasu yi anan Abujan shiyyasa ma bata tare ba. Sosai ita Maanal ma abin ya bata mamaki, yanzu duk wancan kaikawon da akasha na Kano bai kuma isa ba. A fili kam sai suka cigaba da maganar su da Amaal. Tana ajiye wayar mai aikin Oum ta shigo tai kiranta, mayafi ta ɗauka ta sanya, dan haka kawai taji tana jin kunyar fita a haka matuƙa. Tayi ƙyau sosai, duk wanda ya ganta kuma yaga amarya, dan ƙamshinta daban ne, ga ƙunshinta raɗam yanata ɗaukar ido daga baƙin har jan, fatar jikinta kam da tasha gyara ba'a magana, sai wani irin glowing take a idanun mai kallo kamar ka lasheta. Ita kanta Oum kallonta kawai take tana murmushi, ta jima bataga ma'auratan da suka dace da juna ba irin Maanal da Autanta, sai dai ai musu fatan zama lafiya mai ɗorewa kuma. ALLAH ya kawo zuri'a masu albarka..........✍️ 🏃Da suwa zamuje sashen AA ɗin ne?.         *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣ ______________ .......Basket ɗin da aka shirya masa kayan abincin Maanal ta ɗauka, kai kace wani anguwa zasu je ba cikin gidan ba. Sun fito gwanin sha'awa daka gansu kaga uwa da ɗiya ba uwar miji da matar ɗa ba. Oum tasan Mamy na sashen Abah dan haka bama tace Maanal taje ta gaida su ba, shiru ma gidan alamar kowa na sashensa, sai ma'aikata dake ta ƙoƙarin kimtsa ko'ina, sunta gaishesu har suka isa sashen AA. Haka kawai Maanal ke jin kamar tace bazataje ba, amma bazata iyama Oum musu ba duk tsanani. Kai tsaye Oum ta shige dan tasan bazasu sami kowa a falon ƙasan ba, Maanal dai  biye da ita zuciyarta na mata wani nauyi. Dan kana shiga da sallamar sabon fenti dana sabbin kaya zaka fara cin karo. Tabbas dole ne mai kallo ya furta Masha ALLAH, dan kuwa dai Daddy yayi matuƙar ƙoƙari, daga Maanal ɗin har Huznah ya zuba musu dukiya. Duk da asace Maanal ke kallon komai sai da taji hawaye sun cika mata ido sosai, wata irin ƙaunar Daddy da Ammie na ratsata, falon ƙasa ma kenan, bata san yaya kitchen yake ba, kuma su Didi sun sanar mata daga saman har ƙasa Daddy ya cika mata su da kaya. Zuciyar Maanal bata ƙarasa fashewa ba sai da suka hawo upstairs ɗin, ya subahannallah komai yaji, a hakan ma nan ba'a kammala aikin ba dan ga manyan kwalaye nan a ajiye gefe an tule, zama sukai a cikin kujerun dan su an riga an shiryasu, dai-dai nan Fawzan ya shigo shima da alama yaje sashensa ne.       Cike da tsokana yace, “Inyee kaga Lilly amaryar Auta”.        Da sauri Maanal ta ɗan waro masa idanu, sai kuma ta ɓata fuska. Dariya Fawzan yake yi, Oum dake tayashi ta ce, “Ni ban taɓa ganin yaya irinka ba Fawzan, anya kuwa bazan turaka hutu Kano ba ka bar min yara su shaƙata”.     Dariya sosai Fawzan yake yi, ya kai zaune kusa da Oum ɗin yana gaisheta, itama Maanal ɗin sai ta gaisheshi. Oum ce kawai ta tambayi yaya jikin Autan nata, Maanal kam kunya ta hanata yin hakan. Fawzan ya ce, “Da sauƙi sosai Oum, dan tare mukaje massallaci ma da asuba yau. Ku shiga mana ai ya tashi”.        Murmushi Oum tai da faɗin, “Alhamdullahi”. Sai kuma ta juya ta kalla Maanal da kanta ke'a ƙasa. Cike da kulawa ta ce, “Auta tashi ki shiga masa da abincin gamu nan zuwa”. Kai kawai Maanal ta iya ɗaga mata, sai dai ji take kamar tace ma Oum ɗin a'a amma babu dama. Haka ta ɗauka basket ɗin kanta a ƙasa, Fawzan ne yay mata nuni da ɗakin yana tsokanarta, ita dai yau babu bakin maida murtani sai Oum ke kare mata. Sai da tai ɗan jimm a tsaye kafin tai knocking da yatsanta ɗaya kamar mai jin tsoro, tabbas badan bazata taɓa iya musu da Oum ba komi za'ai bazata je inda yake ba, duk da kuwa har cikin ranta tana jin damuwa da rashin lafiyar tasa. Jin shiru ta sake yin knocking ɗin, sai kawai jitai daga falo Fawzan nace mata ai ta shiga kawai ba lallai yajita ba. Nan ma jitai kamar ta saki hawaye, amma haka ta danne kamar mai tsoron shiga wuta ta tura ƙofar ɗakin a hankali. Sai da ta ɗan rumtse idannunta taja numfashi kafin ta saka ƙafarta a hankali lips ɗinta na motsawa alamar sallama. Bata kalla cikin ɗakin ba ta maida ƙofar ta rufe, yayinda wani sassanyan ƙamshi ya daki hancinta, ɗan sanyin acn da aka saka kaɗan yay wani shiga jikinta. Sosai ta saki ajiyar zuciya a cikin ƙirjinta. Sai kuma ta shiga bin ɗakin da kallo jin alamar kamar babu mutum, babu kowa kam, sai dai gadon babu gyara alamar yanzu aka tashi a kansa, ɗakin ya tsaru matuƙa, ga komai dai-dai misali babu wani tarkace, duk da safiya ce babu yawan haske a ɗakin, dan labulayen duk a sake suke, fitulun kuma a kashe sai mara haske sosai kalar blue. Hakan ya saka launin ɗakin sake zama mai ɗaukar hankali. Nanma ajiyar zuciya ta sauke, sai kuma ta cigaba da takawa a hankali kamar mai sanɗa da nufin ajiyewa ta fice abinta tunda ALLAH tasota baya ɗakin, sai dai kuma da'alama shirin nata zai bi ruwa, dan tana gab da isa tsakkiyar ƙaton bedroom ɗin ƙofar bathroom dake daga can cikin closet ɗinsa da zaka iya hangowa ta cikin ɗakin ta buɗe, harga ALLAH da farko tsorata tayi dan haka ta kalla wajen, sai dai kuma da gudu ta ɗauke idanun nata zuciyarta na wani kalar bugawa saboda saukarsu a kansa. Ba ƙaramin jin ta gama rikicewa tayi ba, dan daga shi sai ƙaramin towel daya ɗaura a ƙugunsa, buɗaɗɗen jikinsa jiƙe da raɓar ruwa alamar wanka yayi, dan hatta sumar kansa a jiƙe take itama dai da alama wanketan yayi. Shima dai cak ɗin ta tsaya, dan ganin nata ya saka shi jin shock na rashin zato dan tunda suka dawo bai gata ba, duk ciwon nan bata shigo dubashi ba. Kamar zai ɗauke kai dan jin haushi. Sai dai ganin yanda tai tsammm kanta a ƙasa ya sakashi sakin wani shegen murmushin gefen baki yana ɗan yin luuu da idanun nasa kamar zai lumshesu. Ƙaramin towel ya cira dake rataye a jikin wani ƙyaƙyƙyawan hanger dake gab da ƙofar bayin, dan an tsara su ne a wajen kala-kala ta cikin closet ɗin gwanin birgewa. Saman kansa ya kai towel ɗin kafin ya fara takowa harya fito daga closet ɗin gaba ɗaya.         Bedroom slippers ne a ƙafarsa masu taushi, duk da ba ƙara sautin takun nasa ke badawa ba sai take jin sa ita har tsakkiyar kanta, karo na farko a rayuwarta da taji wani mashahurin tsoron kasancewarsu su biyu kacal a waje, da ace zata iya da ɓacewa kawai zatai a ɗakin ta huta. Amma babu damar hakan gareta tunda ita ba aljana bace. Yana isowa gab da ita batama san wani ƙarfi yazo mata ba tai saurin juya masa baya tana sake ƙarfin rumtse idannunta hannayenta biyu data riƙe basket ɗin na ƙara damƙe shi da ƙyau. Cak ya tsaya shima dariya na neman cika masa zuciya, dan yanda ta juya ɗin da saurinta sai ka ɗauka wani kumurcin maciji ta gani ko zaki. Da ƙyar ya iya danne dariyar dake cinsa a rai ya matsa jikinta sosai, tsabar neman magana sai ya zagayo da hannayensa ta gefe da gefenta ya ɗaura akan nata hannayen dake riƙe da basket ɗin, badan ya riƙe hannun nata da ƙyau ba da sai basket ɗin yayi faɗuwar da abincin zai tarwatse a wajen. Yanda ta takure jikinta waje guda ya sake bashi damar manne jikinsa da bayanta sosai tare da duƙo kansa saman kafaɗarta yana busa mata numfashinsa a saman dokin wuya da cikin kunne, sannu a hankali ya sake matsar da fuskarsa jikin tata idanunsa a lumshe, kwantaccen gashin kumatunsa dake da damshin ruwa na gogar gefen fuskar tata. Da sauri ta zame hannunta dake riƙe da basket ya koma nasa hannun gaba ɗaya. Karo na farko ya saki ɗan murmushi mai sautin da har taji, har yanzu kuma idanun nasa a lumshen suke yana shaƙar ni'imtaccen ƙamshinta. Cikin matuƙar raɗar da koda wani ne a kusa da su da wahala yaji miya faɗa a hankali can ƙasan maƙoshi ya furta, “Good morning Bestie”.            Tsabar yanda maganar tashi taima Manaal shigar zuruff bama tasan ta zabura ba tana ƙoƙarin tureshi, dolensa ya bata damar fita a jikin nasa, dan duk ta daburce har tana neman kaɓe basket ɗin abincin hannun nasa. Hanyar fita ta nufa da sassarfa, muryarta na rawa, harshenta na sarƙewa ta furta, “Su Oum na falo”. Kafin yay wani yunƙuri harta fice. Kansa kawai ya girgiza yana mai sakin murmushin da har sai da haƙwaransa suka bayyana, a ransa kam ayyanawa yake (Zamu haɗe ne ai yarinya).        😂Tace maka ita ba yarinya bace yanzu kana sake maidata baya🏃       ★ Sarai Oum ta lura da yanda Manaal ta dawo kamar wadda aka biyo, sai dai batai magana ba har sai da Manaal ɗin ta sanar musu cewar ya tashi. A dai-dai nan ma kiransa ya shigo wayar Oum ɗin. Basu ji abinda ya faɗa ba, Oum tadai miƙe tana murmushi tace su shiga.      Fawzan ne ya fara shiga, Oum biye da shi, itace ƙarshen shiga dan maƙalewa tayi a bayan Oum. Sosai Oum ta nuna farin cikin ganin yanda jikinsa yay sauƙi yau sosai fiye da kullum, shima ganin fara'a a fuskarta sai zuciyarsa ta masa sanyi. Fawzan kam ya tasashi gaba da tsokana shi da Maanal data zauna a cikin yanayin takura, dan tun haɗa idon farko da tayi da AA ta ɗauke kanta bata sake kallon sashen da yake ba. Yanzu ma da Fawzan ɗin ke tsokanarsu kanta a ƙasa sai Oum ke kare musu. A dai-dai nan Saheeba da Nibras sukai sallama. Kafin a basu iznin shigowa Naufal da Anum sun shigo. Kai tsaye yaran inda AA yake suka nufa cike da farin cikin ganinsa a zaune, shima fuskarsa da ɗan sakewa ya ɗaga Anum ya zaunar a jikinsa, Naufal kuma ya zauna a kusa da shi.         Da kai kawai ya amsa gaisuwar da Saheeba da Nibras sukai masa. Ba haka Nibras taso ba, amma har ranta taji daɗin ganin jikinsa da sauƙi sosai yau ɗin. Wani gefe na zuciyarta kuma najin zafin ganin Maanal a tare da shi, gashi data kallesa sai taga idanunsa akan Maanal ɗin suke, ita kuma ƴar ranin hankalin sai wani latse-latsen waya take yi ita adole ga mai aji. Oho ita Maanal bama tasan tanai ba, hasali ma jinta take duk a takure, da Oum zata barta ma da tuni ta wuce abinta ta koma sashenta ita kam..... ________★   A lokacin da anan ahalin gidan ke sashen AA a ɓangaren Mamy tana can tana waya da babbar yayarsu akan batun auren AA ɗin da Nuratu da sukaji su Abah sunyi shiru sunƙi cewa komai ga shi har yau laraba, a yanda tsarin nasu yake kuma daga gobe alhamis ya kamata ace biki ya fara musamman tasu ɓangarensu, amma sunji ɗif babu wani bayani. Shine tai kiran Mamy ɗin dan jin mike faruwa. Bayanin da Mamyn ke mata rai ɓace yasa tace yau zatazo Abujan dan tana Kano. Da wannan sukai sallama.        Zama Mamy tai tana mai dafe kanta. Eh lallai taci nasara akan Abah na hana Maanal tarewa a sashen AA, sai dai tana jin fargaba akan tunkararsa da batun bikin nan kuma. Musamman idan akai dubi da halin da AA ɗin ke'a ciki na ciwo. To amma kuma itama fatanta ai ayi bikin ne. Numfashi mai nauyi ta sauke sosai, tana mai tattara batun gefe ta jingine har isowar yayar tata dai, dan gara su tunkari Abahn tare zatafi samun ƙwarin gwiwa....        Kusan ƙarfe uku na rana kuwa yayar Mamy ta iso gidan. A lokacin kusan kowa yana a sashensa, dan hatta AA yana sashen Oum, daga sallar azhar daya samu iya fita yau shi da sauran yan uwansa suka wuce sashen Oum ɗin. Manaal dai na ɗakin tunda taji motsinsu taƙi fitowa, sai ma tayi kwanciyarta barcin dole, daga baya na gaskiyar ya ɗauketa.       Mamy da kanta ta fito ta tarbi ƴar uwarta, kai tsaye kuma sashenta suka wuce, suna dai-dai gifta window ɗin Oum dake kallon sashen Mamy ɗin sautin dariyar su Fawzan ta shiga kunnunwansu, kasa haƙuri sukai sai da suka leƙa. Aiko idanunsu suka gano musu zaratan mazajen ƴaƴan na Oum zagaye da ita tana bama AA abinci a baki, dai-dai kuma lokacin Babban Yaya shima ya buɗe nasa  baki wai ta bashi, shine suka saka sanya dariya, shima Fawzan yace bazai yarda ba ya je aka bashi. Kai da kaga fuskar Oum kasan cike take da farin ciki, haka suma su babban Yayan, farin cikin Oum ɗinsu ya saka fuskokinsu bayyana murmushi na musamman, musamman ma shi da AA da ba cika son yin dariya sukai ba sai sun so. Fuuuuu Mamy ta wuce sashenta zuciyarta na tafasa. Koda suka shiga ɗaki saita sakar ma yayarta kuka. Ita kanta yayar tata wata irin masifa take ji na tafaso mata daga ƙirjinta, amma dole ta danne ta shiga lallashin Mamyn da nuna mata kuka fa ba shine mafita ba. Dole suzo susan abinyi dan al'amarin na Oum fa na neman zame musu ɗan zane. Dan tabbas ta rigada ta gama mallake zukatan yaran nan da salon makirci (kamar yanda suke fassara soyayyar Oum ɗin akan su AA. Sai dai kuma wannan nasu mummunan zaton ne kawai, dan ita

Chapter 2 of 15