dai baiwar ALLAH Oum har cikin zuciyarta ne, hasalima takan manta da cewar ba itace ta ɗauka cikin su AA tai naƙudarsu ba saboda yanda ta sakankance matuƙa).........✍️
_Dangin Mamy ina gaisuwa 🙄🥱🏃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖5️⃣
______________
5
......Sun tattauna sosai kafin su yanke shawarar yayar ta tunkari Abah da batun bikin cikin hikima. Hakan kuwa sukayi, bayan sallar la'asar Abah ya dawo gida Mamyn tai mata rakkiya har sashensa. Bayan sun gaisa cikin mutunta juna dan akwai ƴar kunyar surukuta a tsakaninsu duk da kuwa Abah ya girmeta sosai, amma yana kawaice mata saboda dattako. Cike da kissa tana murmushi take faɗin, “Kukam kamar a kanku aka fara aurar da auta, yanzu bayan shagalin Kanon bazaku barmu mu huta ba wani satin kunce zakuyi wancan kuma?”.
Cikin danne takaici da ƙyar Mamy ta ƙaƙaro murmushi tana ɗan laɓe baki, “Ai jikinsu ne zai gaya musu dan nikam dai nayi na ALLAH da naje muku Kanon ma. Amma da zaku tausayama kanku da kun barshi ku haɗe duka”.
Cikin rashin damuwa Abah yay ƴar dariya shima da faɗin, “Ai ku kwantar da hankalinku bikin ma Saturday ɗin dama da wahala ya yiwu. Dama yau nake son zama daku akan zancen dan yau da safe Baba ya kirani, ya kuma tabbatar min zuwa gobe shima zai samu mutanen gidan naku dan bammayi zaton Aunty Babba zatazo ɗin ba”. Ya ƙare maganar yana kallon Aunty Babba datai wani irin ɗagowa tana kallonsa.
Wani irin harmutsawa zuciyar Mamy tayi, da ƙyar Aunty Babba ta iya saita yanayinta cike da dakiya ta ce, “Lafiya dai ko Aban Fadeel? (Dan haka take kiransa)”.
“No lafiya Lau, Baba ne yace a ɗan dakata Ajwaad ɗin ya ƙara samun lafiya sosai, dan yaron nan ya bugu sosai dan ma ALLAH ya bashi ƙarfin hali ne. Ga kuma mutane sunyi ƙoƙari na zuwa wancan ɗin, ga azumi yana gabato mu kwana goma sha kawai ya rage, sai yace a bari kawai bayan salla idan muna da rabon kaiwa sai ayi. Amma nima naso ayin kawai a huta, damma uwarsa taƙi bani haɗin kai amma ina son horasa akan yarinyar nan ita kanta, idan son samuna ne kada ta tare yanzu har sai bayan sallar itama da kansa ya magantu ya faɗa mana dalilin ƙin amsar aurenta da yay har yana neman kashe kansa, amma nasan da wahala ta bari duk da dai jiya da yau naga ta daure ana son aga gudun ruwana, kuma zasusha mamaki ita da ɗan nata dan na shirya musu sosai....”
Gaba ɗaya takaici ma ya hana Mamy magana, jitake kamar ta falle fuskar Abah ɗin da mari ta huta daga ita har yayar tata. Amma dai suka danne da ƙyar suna ƙawata fuskarsu da murmushi kaɗan. Da ƙyar Aunty Babba ta ce, “Uhhm kaima kasan dai bazata bari ka horashin ba Aban Fadeel, amma kuma hakan shine dai-dai, ya kamata yasan muhimmancin yarinyar, kar yaga an bashi a ɓagas ya ɗauka arha ya samu ”.
“Ato kema dai ƙya faɗa Aunty, amma bazata yarda ba, shekaran jiya fa kuka ta sanya min ma wai ina son na maida masa ciwo baya. Tunda dai anyi ya wuce a haƙura mana. Kai ban san irin son da Fateema kema yaranta ba wlhy.”
Shiru Aunty Babba tai masa dan maganarsa ta ƙarshe sake sukar mata zuciya take, ita ko Mamy ma sai ta miƙe abinta. Shima kiran wayarsa da akayi ne ya sashi miƙewa ya fita. Da kallo suka bishi, yana fita Mamy ta miƙe a fusace har idannunta na tara ƙwalla tana faɗin, “Ashe da rigima kuwa a gidan nan Aunty......”
Da sauri Aunty Babba ta rufe mata baki, sai kuma ta kama hannunta suka fice ta baya zuwa sashenta.....
__________★
Har dare Oum bata san yayar Mamy na gidan ba. Sai kusan takwas su AA sun dawo massallaci, shi kaɗai ya wuce sashen Oum. Babban Yaya da Fawzan kowa sashensa ya wuce. Abah kuwa sun barsa a waje yana gaisawa da maƙwafcinsu. Kai tsaye upstairs AA ya haura, dan ƙasan masu aiki na gyarawa kasancewar anan suka tashi. Shiru falon babu kowa sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka saka ke tashi. Cikin yanayinsa na wanda yasha faman jiyya ya kai kwance a doguwar kujera, a haka ya jawo remote ɗin tv dana ac ya kunna, yana cikin searching channel Oum ta fito daga bedroom. Zama tayi tana ɗan matse fuska da faɗin, “Auta kun dawo?”.
Remote ɗin tvn ya ajiye tare da juyowa ya kalleta. Maganar da yay yinƙurin yi ya haɗiye tare da tashi zaune idanunsa akanta. Fahimtar kamar ya gane yanayin da take ciki ya sata saurin gyara fuskarta, cikin murmushi ta ce, “Lafiya? Ya naga ka tashi?”.
“Oum muje asibiti”. Ya faɗa cikin sanyi da damuwa maimakon amsa tambayar datai masa. Murmushi ta sake saki tana gyara ƙafafunta, “Asibiti kuma? Ni lafiyata ƙalau”.
Idanunsa da suka ɗan kaɗe ya tsurama ƙafafunta, sai kuma ya zamo ƙasan lallausan carpet ɗin falon ya zauna gab da ita. Ƙafafun nata ya kamo ya ɗora a saman jikinsa. Duk sun ɗanyi fushi kuwa, cikin sauri ya ɗago yana kallonta. “Oum dan ALLAH ki tashi muje asibiti, see your leg! fa”.
Murmushi sosai Oum tayi da faɗin, “Oh oh! Look, there's nothing wrong, my dear. I'm okay fa. Kawai dan kwana biyu ban ɗan motsa bane ba. Sannan yau na manta bansha magani na da yamma ba sai yanzu na tuna nasha bayan idar da salla. Ina mai tabbatar maka zata sauka yanzun nan”.
Sam bawai zuciyarsa ta gamsu bane, amma bazai iya jayayya da ita ba. Sai kawai ya shiga mammatsa mata ƙafafun. Idanu kawai Oum ta zuba masa tana murmushi, dan tasan yayi shiru ne kawai badan ya gamsu ba. Cikin son kwaranye masa damuwar data bayyana akan fuskarsa ta ce, “Auta ya kamata kaci abinci fa, sai kasha maganinka, doctor yace 8 amma gashi har ta shige baka nema ba.”
Fuskarsa a narke sosai ya ce, “Oum bana jin cin komai fa, zan sha maganin a haka kawai”.
“A'a bazai yiwu ba, bara na haɗa maka ko tea to.”
Da sauri ya maida ƙafafunta da take neman janyewa a jikinsa. “No Oum zan haɗa da kaina zauna ki huta. Naji sauƙi fa sosai”.
“Haka ake so ai my baby ALLAH ya ƙara afuwa, amma wannan jikin naka da sauran ƙarfinsa. Bara kawai na kira Inte ta haɗa maka”.
Fuska ya yamutsa, dan shi fa baya son masu aiki su masa abinda zaici. Bawai dan basu da tsafta bane ko yana ƙyanƙyamin su, a'a kaf ma'aikatan gidansu da iliminsu da kuma tsaftarsu. Kawai shi abinci idan bana Oum ba baya so sai idan ta ƙure. Dan ko abincin Mamy yakan daɗe baici ba a gidan balle masu aiki, su Saheeba kam ai da wahala su girka abinci ya cisa, shi kallon ma basu iya yake musu ba. Oum data fahimci baya so sai tai murmushi. Dai-dai nan Maanal ta fito daga bedroom ɗin Oum hannunta riƙe da novel, sai waya manne a kunneta tana magana da Didinta Shahidah. Sam hankalinta bai kai kan AA ba sai Oum dake zaune a kujera, sai da tazo gab da su fuskata ƙawace da murmushi daya ƙara mata ƙyawu sosai tana faɗin, “Kai Didi to ga Oum ɗin” sannan idanunta suka sauka akansa, ai da gudun tsiya ta janyesu tana haɗiye murmushin nata. Shima nasa idanun daya ɗan zuba mata ya janye, dai-dai nan Oum takai wayar data amsa a hannunta kunnenta. Ƙoƙarin juyawa tabar falon tayi, Oum ta riƙo hannunta tana mata alamar ta tsaya. Sai kuma ta ɗan janye wayar a kunnenta a hankali tace, “Haɗama mijinki tea”. Maida wayar tai ta cigaba da amsa gaisuwar Shahidah tana murmushi.
Manaal dai ta kasa motsawa, dan haka kawai furicin Oum ɗin ya ratsa mata jiki da ƙyau. Kalmar *Mijinki* ɗin nan da Oum ya ambata sai taji ta mata nauyi sosai a ƙirji. Juyowar da Oum tayi taɗan kalleta ya sata ajiye novel ɗin hannun nata ta nufi hanyar stairs cikin sanyin jiki tamkar wadda aka saluɓema kuzari. Ƙasa-ƙasa ya bita da kallo, sai kuma a hankali ya ɗan lumshe idanun nasa yana mai sakin ajiyar zuciya acan ƙasan maƙoshinsa ya cigaba da matsama Oum ƙafafun nata.
Sarai Oum na lure da su da yanayin da suka shiga. Amma sai ta basar ta cigaba da wayarta da Shahidah...
Kusan mintinan goma sha sai ga Maanal ta dawo. Ta samu har yanzu Oum na waya, yayinda shi kuma ke riƙe da novel ɗinta kansa a ƙafar Oum dai-dai gwiwa ya ɗan kwantar daga zaunen da yake. Murmushi Oum tai mata da nuna mata gaban AA ɗin alamar ta ajiye madaidaicin tiren dake a hannunta anan. Kanta ta gyaɗa, tare da kaiwa duƙe gabansa ta ajiye tray ɗin a hankali. Sai a lokacin ya ɗago idanunsa ya ɗan kalleta. Fuska taɗan ɓata tana kallon littafinta dake hannunsa, sai kuma tai masa yuuu da idanun irin na jin haushin dake nuni da wayace ka ɗauka min novel?. Laɓɓansa da ciwo ya sakasu sake komawa pink sosai ya wani ɗan laɓe mata, tare da ɗage gira kaɗan irin na (An ɗauka ɗin nan) sai hakan ya sake tunzurata ta miƙa hannu zata warce novel ɗin. Janyewa yay yana mai ɗan zaro idanu waje na mamakinta. Harara ta sake dalla masa ta ɗauke kanta.
Shayin ta shiga haɗa masa, tasan baya shan suger sosai tun zamanin ƙuruciya, dan ko sanda yay tashen shan chocolate baya shan mai suger sam dan baya shiri da shi sam. Gwara-gwara ma zuma ita kam yana masifar so, shine ma ya koya mata sonta itama. Amma dan neman magana yanzu saita ɗibo har huɗu kasancewar mai ƴaƴa ne zata afka masa. Ai baima san ya cafke hannunta ba yana ɗan waro idanunsa da faɗin, “Oum kinganta ko? Zata saka min suger”.
Oum data basar da su kamar bata san mima suke yi ba ta kallesu, cikin shagwaɓa Maanal data ƙwace hannunta daga riƙon da yay mata ta ce, “Oum nima fa novel ɗina ya ɗauka min”.
Ita Oum ma sai suka nema sakata dariya, dan idanun Maanal har sun fara ƙyalli alamar taruwar ƙwalla. Ta fahimci sufa idan suna a gabanta mantawa ma suke yanzu bada bane sun girma. Dai-dai nan Mamy da yayarta sukai sallama batare da Oum ta raba faɗan ba. Kusan a tare Oum da Maanal suka amsa sallamar, sai dai ita Maanal a hankali. AA kuwa a maƙoshi ya amsa yana kai tea ɗinsa ɗaya ɗauka baki. Yayinda yaƙi yarda ya kalla su Mamy da tun shigowarsu ita nata idanun ke'a kansu a kaikaice. Dan ba ƙaramin dukan zuciyarta ganinsu a taren yayi ba, ga yanayin zaman nasu kusa-kusa dan tray ɗin nan ne kawai ya rabasu sai ƙafar Oum ɗaya dake kusa da AA gab, ɗayar kuma kusa da Maanal. Manaal ɗin ce ta fara ƙoƙarin gaishesu, yayinda shi kuma ya ɗan basar da farko, sai Oum dake sallama da Ammie. Da ƙyar Mamy ta danne zuciyarta ta amsa gaisuwar Maanal ɗin, yayarta kuwa dan makirci tuni ta washe haƙwara tana tsokanar AA da Maanal. Wai autoci sunzo sun saka babarsu a gaba.
Ƴar dariya Oum tayi da faɗin, “Aunty harda ke kema bazaku bar min yara su huta ba? Saukar yaushe haka babu labari?”.
Kafin Aunty ta bada amsa AA ya gaisheta. Amsawa tai da kulawa tana jajanta masa jiki. Kansa kawai ya jinjina mata yana bin Maanal data miƙe da kallon ƙasan ido. Hakama Mamy da yayarta a kaikaice Maanal ɗin suke kallo, kowa kuma da abinda yake kissimawa zuciyarsa akan yarinyar. Yayinda Oum kam hankalinta ke akan AA ne kawai. Babu jimawa Maanal ta dawo, ƙaramin tray data saka ruwa da lemo da kofi akai ta ajiye a gaban Auntyn Mamy. Itako sai ta shiga saka mata albarka cike d makirci. Harda faɗin, “Eh lallai na ƙara yarda autar Hajiya Fateema ta girma”.
Kunya ce ta kama Maanal, dan haka ta sulale zata bar wajen, yayinda Oum ke dariya Mamy na tayata da murmushin yaƙe. AA kam novel yake karantawa hankali kwance yana shan tea ɗinsa. Oum ce ta tsaida Maanal ganin ta nufi hanyar ɗaki. “Auta dawo kici abinci, nasanki daga wannan shigar zaki iya neman wajen kwanciya”.
Kan Maanal a ƙasa ta ce, “Oum bana jin yunwa ALLAH. Sannan ba kwanciya zanyi ba yanzu zan dawo”.
Kai Oum ta jinjina mata, ita kuma ta shige tana istigafari akan ƙaryar da taima Oum, dan harga ALLAH batai niyyar dawowa ba sam...
Hira ta ɓarke sosai a tsakanin Oum da su Mamy, sai dai ita hankalinta ya rabu biyu da rashin dawowar Maanal falon, sam bata son yarinyar ta takura kanta. Dan ta fahimci har yanzu Maanal ɗin bata gama dawowa Maanal ɗinta ta baya ba. Ba komai ta saki jiki ba kamar yanda suke a da, yanzu ma wata kunya take neman ƙirƙira a tsakaninsu ne, shiyyasa take ta ƙoƙarin ganin ta kauda mata da yanayin. AA ma dai har yanzu yana zaune yana saurarensu, sai dai a zahiri zaka ɗauka gaba ɗaya hankalinsa akan novel ɗin da yama Maanal kwace yake. Sai dai sam ba haka bane ba, mamakin su kawai ke nuƙurƙusar masa zuciya da ruhi, dan su duka biyun ya musu farin sanin da harda wanda basu bayyana a gabansa ba. Haka yake, mutum ne shi mai tsartar tsiya, ALLAH ya azurtashi da saurin gane halayyar mutane a ƙanƙanin lokaci balle su. Kuma wannan halin nasa tun yana yaro yake tare da abinsa, miskilancin sa da rashin yawan magana yasa ba'a fahimtar hakan kai tsaye, sai Oum ɗinsa data gama masa sanin in and out. Duk da hankalinsa nakan su Mamy ya fahimci hankalin Oum kuma a rarrabe yake. Ganin yanda take faman kallon hanyar bedroom ɗinta yasa shi ajiye novel ɗin hannunsa ya ɗauka kofin daya gama shan tea yanzu ya haɗa wani shayin, cike da kulawa ya kalla Oum.
“Oum bara na kai mata wannan naga duk kin damu”.
Murmushi tai masa tana mai jinjina kanta, sai kuma ta shiga sanya masa albarka. Shi dai ya wuce yana amsawa fuskarsa da ɗan murmushi. Daga Mamy har yayarta da kallon takaici kuwa suka bisa, suna ganin Oum ta juyo garesu suka basar.......✍️
_Mun tafi kai tea. Saura kuma aci amanar Abah🙄🏃🏃🤣🤤_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_*
🅿️➖6️⃣
______________
.........Babu knocking babu komai ya tura ƙofar ya shiga, tana zaune a gaban mirror tana shafa mai daga ita sai towel. Cikin yanayinta na rashin gaggawa ta juyo duk da kuwa tsoro taji, amma miskilancinta ya ɓoye hakan akan fuskarta. Shima dai saukar idanunsa a kan nata ya saka zuciyarsa motsawa, duk da jarumtar da yake nunawa a kanta da danne yanayinsa da tsiya-tsiya saboda miskilancin nasa shima da iya taku, a yanzu kam zuciyar ƴan maza da gangar jiki duk sai da suka motsa da ƙarfin ikon ALLAH. Da ƙyar ya iya lumshe idanunsa ganin taja hijjab ta saka a yanayin ko'in kula da shi. Busashen yawun daya haɗiya na samun sassauci daga kasalar dake neman zagwanye ɗan ƙarfin daya fara samu a yau ya saka Adam's apple ɗinsa motsawa sosai a cikin wuyansa. Cikin tasa dakiyar da basarwar shima ya cigaba da takowa cikin ɗakin, a gabanta saman mirror ɗin ya ajiye kofin shayin, batare daya sake kallonta ba ya ɗan jingina bayansa a mirror tare da harɗe hannayensa a ƙirjinsa.
“Kinsan bazaki dawo ba miyyasa kikama Oum ƙarya?”.
Shiru tai babu alamar zata tanka masa, hakan ya sashi karkatowa ya kalleta, dan abune daya san tafi kowa sanin ya tsana, wato yin magana a masa banza. A kausashe ganin tana neman miƙewa ma ya ce, “Ni nake miki magana kina min banza?”.
A halayya irin ta AA babu abinda Maanal bata sani ba, kai sai dai ma ta bama wani labari. Dan ko Oum badan ita uwace ba zatace akwai abubuwa da yawa data fita sani game da shi. A yanda yay maganar kawai ta fahimci ya hau zuciyar tasa, dan haka itama a ɗan tunzure ta juyo tana kallonsa cikin ido. Girarta ɗaya a ɗage ta ce, “Kai da ka shigo ka min sallama ne balle neman izini? Ko an gaya maka dabba ce a ɗakin!”. Ta ƙare maganar da balla masa harara ta murguɗa baki. Yanda kasan robbot haka ya tsaya hana kallonta kawai harta ƙarasa cikin closet ɗin Oum. Da wani irin salo ya shiga girgiza kansa irin na ɓacin ran nan yana cizon lips, a ransa kam rayawa yake (Wato yarinyar nan duk randa na tashi gyara mata zama zata banbance akwai tazarar shekaru a tsakaninmu masu yawa ƙwarai da gaske.) a zahiri kam closet ɗin ya nufa shima. Sam Maanal bata san da isowarsa wajen ba hankalinta na'a zaɓar kayan barci da zata saka. Dan tun shekaran jiya Oum ta saka Inte mai aikinta ta shirya kayan Maanal ɗin cikin closet ɗin ta tunda babu ranar komawarta nata sashen. Sama taka kawai taji nutsatstsiyar muryarsa mai cike da zurfi da fitar isa a cikin kunenta.
“Amma kin san zan iya dirje bakinki a ɗakin nan har sai yayi jini batare da sanin kowa ba ko? Bar ganin Abahnki ya tsaya miki tsaf zan koya miki yanda akema miji magana cikin tausasawa da ladabi nabar masa ke na ƙara gaba har sai kin HAIHU zan dawooo....” yanda ya ƙare zancen cikin ƙasan maƙoshi da busa mata numfashinsa akan dokin wuya zuwa cikin kunne ya sata kasa daurewa ta saki kayan a ƙasa tare da juyowa gaba ɗayanta dan sam batayi zaton a kusa yake da ita gab-gab ba. Aiko sai kawai gata a jikinsa gaba ɗayanta. Daburcewa tayi, wajen mutsu-mutsun janyewa ta ruƙunƙumesa gaba ɗaya saboda motsa jikinsa da yayi ya ƙure duk space ɗin dake a tsakaninsu suka mannu da katakon wadrob ɗin bayanta. Bata da zaɓin daya wuce yimasa zobe da hannayenta saboda shiga ɗimuwa. Gashi ta motsa gabas da yamma kudu da arewa babu ko ɗan ɗigon space ɗin barin jikin nasa balle fita. Mayataccen ƙamshin turarensa kam ya gama gauraye ilahirin hijjabin Oum data saka zuwa hancinta har ya ratsa fatar jikinta.
AA kam ɗan duniya, tunda ta shige jikin nashi yay wata kalar tsaiwar sojan badakkare kawai ya lumshe oily idanunsa masu hasken tsiya kamar an watsa madara a ciki ya wani kalar tura lips ɗinsa cikin baki ya matse yana sauke numfashi a hankali. Sai da ya tabbatar ɗumin jikinta ya gama ratsa nasa gangar jikin har ƙofofin gargasar jikinsa na bubbuɗewa, wata ƴar zufa ta taru masa a goshi sannan ya ɗan ja jikinsa baya gudun kar'a tafka abun kunya a ɗakin tsohuwa. Dan yasan kansa ƙwarai-ƙwarai da gaske, ALLAH ya azurtashi da ƙarfin buƙata, sai dai ya masa rahama da jarumta da dauriyar iya shanye yanayinsa koda ta ƙarfi ne. Sam bai shirya yin kowanne kalar yunƙuri a gareta ba a yanzu, ya ɗauka ɗammarar bama Abah damar horashin daya ɗauki alwashin yi, itama zai bata damar manta bayan data riƙe a ranta, itama Mamyn zai bata dama akan nata yunƙurin, daga haka sai ya fara dama tashi damar a yanda yake fata da tsarawa da kansu zasu bashi ita da gudun tsiya.
Tunanin da yay zurfi a ciki yasa bai ankara har Maanal ta surare daga wajen ba, sai da ya motsa ƙafarsa yaji ya taka kayan data yadda sannan ya farga da hakan. Juyawa yay kaɗan ya dubeta, zaune take a bakin gado ta dafe kanta da duka hannayenta. Fuskarta a duƙe take shiyyasa bazai iya sanin a wane hali take ba. (Ga tsiwa ga tsoro) Ya ayyana a ransa yana mai duƙawa ya ɗauka kayan data ciro ɗin, tare da rufe closet ɗin. Inda take ya iso, batare da yace komai ba ya ajiye mata kayan a gefenta ya wuce abinsa. A tunaninsa su Mamy sun jima da barin sashen, amma sai ya samu a yanzu ma harda Abah, da alama kuma magana suke mai muhimmanci. Sai dai fitowarsa ta sakasu ɗagowa duk suka zuba masa ido amma banda Oum. Sosai ya karanci kallon tuhuma da zargi a idanun Abah. Yayinda Mamy da yayarta suke masa na takaici da ɓacin rai. To yaya lafiyar kura... Dama, ai sai ya wani fiske abinsa yama shiga gaida Abahn. Abah yasan wanene ɗan nasa da halayyarsa, dan haka shima sai ya basar ya amsa masa tare da tambayar jikinsa. Ya amsa cewar da sauƙi, daga haka ya nufi hanyar fita abinsa dan fahimtar zaman nasu iya nasu ne...
Sarai Oum ta lura da kallon da Abah yabi AA ɗin, dan haka ta sake cuskule fuska tamau. Murmushi kawai Abah ya saki ya basar shima, a ƙasan ransa mamakin Fatemansa na sake mamayesa. Tama kwantar da hankalinta bazai mata magana ba. Amma yasan matakin da zai ɗauka. Dan yanzu kam ya sake aminta da zancen Kamila ƙwarai da gaske......
________★
Maanal tana tabbatar ta daina jin motsin su Mamy a falo ta miƙe ta fito ɗaukar ruwan sha. Ganin Oum ta nufi hanyar stairs kamar mai tafiya da ƙyar tai saurin nufarta da faɗin, “Oum!” a raunane. Tsayawa tayi tare da juyowa, ganin Maanal ya sata sakin murmushi. “Oh kinji sun tafi shine kika fito daga ɓuyan? Auta sokike dai ki maidamu surukanki a gidan nan ta ƙarfi da yaji ko?”.
Kai Maanal ta duƙar tana murmushi. “A'a Oum nayi wanka ne, naga kuma zakuyi magana shiyyasa”.
“Za'aima Oum wayo kenan”.
Murmushi Maanal tayi tana rufe fiskarta da tafukan hannayenta. Oum ma dai dariya tayi. Sai kuma ta ce, “Kinga bara na bama su Inte wayar nan su kaima Aunty ta manta da ita”.
Da sauri Maanal tace, “Kawo nakai musu Oum”. Babu musu ta bata, dan itama tasan bazata iya sauka ƙasan ba ƙarfin hali ne kawai irin nata. Gittata da Maanal tayi yasa taji ƙamshin turaren AA sosai a hancinta fiye da sama-sama da take ji. Hakan ya sake tabbatar mata a jikin Maanal ɗin ne. Murmushi tayi sosai, a ranta tace, (Ai nasan za'a rina. Irin hakan nake gudarma Abanku amma ya kasa fahimta).
Koda Maanal ta nufi ɗakin masu aiki samu tayi har sun kwanta. Sai kawai ta maida musu ƙofar ta rufe a hankali. Ta kitchen tabi ta fita dan zai fi mata sauri. Gidan fayau yake da haske dan tako ina akwai security light kwanyar, kanta tsaye ta shige sashen Mamyn, babu kowa a ƙasa sai Haule dake a kitchen, jin motsin Maanal ya sata leƙo. Murmushi ta sakarma Maanal, tare da fitowa gaba ɗaya cikin girmamawa ta ce, “Aunty Amarya barka da dare”. Guntun murmushi Maanal tayi mata da miskilar fiskarta dan sunan da Haulen ta kirata da shi ya mata wani iri, musamman daya kasance Haule zata girmeta, dan zasuyi sa'anni da Amaal. Cikin yanayin rashin sakewarta tace, “Mamy fa?”.
Upstairs Haule ta nuna mata. “Suna sama”. Kai kawai Maanal ta jinjina mata ta nufi hanyar, bayan ta buɗe ƙofar ta shiga ta maida ta rufe, dan tsarin sashen irin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 15