Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗaya sai tai mutuwar tsaye kawai, harya gama zare handbag ɗin ya koma tsaye sosai hannunsa a cikin nata. Batare daya kalleta ba can ƙasan maƙoshi ya furta, “Let's go”.        Ƙin motsawa tayi, dan haka ya waiwayo yana kallonta. Da wani salon ƙanƙance idanu tamkar ya manta a inda suke tsaye, muryarsa acan ƙurya ya furta, “Ko goyo kike so?”. Yay maganar da ɗan takowa gabanta kamar zai duƙa ɗin ta hau bayansa. Ai a zabure ta riƙo hannunsa jikinta har yana ɗan rawa. Hakama muryarta na rawa ta ce, “Ya ilahi mi kake yi haka?”.           Karo na farko ya saki wani shegen murmushi da ita kanta sai da zuciyarta ta motsa. Girarsa ɗaya a ɗage yana wani wara mata fararen idanunsa masu ƙyalli a cikin nata. Sai taji tsigar jikinta na tashi. Da sauri ta ɗauke kanta. Shima bai sake magana ba yaja hannun nata. Dole ta bishi yanzu kam suka fara tafiyar a jere. A nutse suke ɗaga ƙafafunsu su ajiye kuma a tare. Hakan yasa ƴan gulma sake nutsuwa a kallon nasu, harda masu ɗaukar hoto a kaikaice. Sarai AA na lure da komai, amma da yake gwani ne a iya basarwa da kama kai yayi tamkar ma bai san da wasu halittu a harabar Companyn ba bayan shi da ita. Ita ko kunya da nadamar ƙin saurin shigewarta tuni duk ta baibayeta.          Securitys ɗin ƙofar kansu sunyi kasare suna kallon abin mamaki, yau boss riƙe da handbag ɗin mace. Macen da kowa yake cikin ɗunbin mamakin aurensu. Dan tunda akai bikin a companyn gulmar kenan. Burin kowa wannan ranar da zasu dawo kan aiki, dan kowa jima yake kamar bai taɓa ganin Maanal ɗin ba. Cikin sauri suka shiga miƙa gaisuwa ganin suna neman gota su. Tare da yi ma boss murnar aure da jajanta masa yaya jiki. A mamakinsu ya amsa harda ɗan murmushinsa. Duk da dama can ba wai yana wulaƙanta kowa bane, amma ganin murmushin boss haka arhar banza ai sai mai rabo.      To a cikin ma suna shiga kowa yay tsit, waɗanda ke leƙensu ta windows da musu video duk sun koma mazauninsu da gudu. Gaba ɗaya Maanal ji take kamar ta zura da gudu, dan gaba ɗaya attention ɗin kowa ya dawo kansu ne. Ta gefe ido take kallon ganin yanda duk suka miƙe a tare cike da girmamawa, shima sai yaja ya tsaya. Da ɗaɗɗaya suka shiga miƙo gaisuwa. Hannu ya dinga ɗaga musu fuskarsa da sakewa amma ba murmushi yake ba. A mamakinta sai itama suka shiga gaisheta. Karo na farko ta ɗan ɗago ta dubesu, ba wani yawane da su ba dan ba'a gama zuwa ba. Nan kuma iya waɗanda ke a ƙasa ne, mafi yawansu ma cleaners. Guntun murmushi kawai tai musu.       Fahimtar a takure take yasa AA ɗan kallonta tare da matsa hannunta dake a cikin nashi. Dubansa ta ɗanyi, a saman lips ya furta mata, “Muje”. Yanzu kam bata musaba ta bishi, dan hakan zaifi mata sauƙi ita kam. Duk da dai a ranta bata son binsa office ɗinsa department ɗinsu take son wucewa. Suna shiga elevator ta wani sauke ajiyar zuciya tare da janye hannunta dake a cikin nasa. Dariya ma shi kam ta bashi, dan haka ya taɓe baki da faɗin, “Matsoraciya, nine kika raina kawai”.        Kallonsa tai baki a tunzure ta ce, “Waye matsoraciyan?”.         Kamar wasu masu faɗan yara ya juyo yana riƙe ƙugu idanunsa ware a kanta ya ce, “Ke mana”.           Itama juyowar tai tana matsowa gab da shi idannunta cikin nasa da yanayin harara hannayen nata a ƙugu kamar yanda sukeyi a da in suna faɗa ta ce, “Niba matsoraciya bace sai dai idan kai”.      Matsawa shima yay ƙoƙarin yi gabanta sosai idanunsa a cikin nata. Baya ta shiga ja yana binta har suka dangane da bangon elevator ɗin. Sai da ya tabbatar ya matse mata ko'ina ta yanda ko numfashinta a sarƙe yake fita sannan ya ɗaura hannunsa ɗaya a bangon shima ya sake mata rumfa, still dai idanun nasa na'a cikin nata da take mar-mar da su na alamar tsoro amma a zahiri a dakenta take. Ranƙwafawa yay a kanta da ƙyau tsahonsu ya dai-daita, kafin ya sake matsar da fuskarsa gab-gab da tata tamkar zai haɗe bakinsu waje guda. Gaba ɗaya sai Maanal ta rikice, fuskarta tai ƙoƙarin maidawa gefe cikin in-ina da sarƙewar harshe ta ce, “Wa....w. wai miye haka kake yi?”.           Cikin son ƙoƙarin hanata janye idanunta a cikin nasa tamkar mai raɗa ya furta, “Kulawa da ƴar Abah mana.” ya ƙare maganar yana hura mata iskar bakinsa akan idanu.       Baki ta ɗan tura tana ƙoƙarin tureshi da yin mar-mar da idanun saboda iskar da yake hura musu, “To ni nace maka ina so?”.            “Ai basai kin faɗa ba, Abanki ma haka yake so naga”.        Kasa cemasa komai tayi, ga idanuwanta sun fara tara ƙwalla. Dai-dai nan ƙofar elevator ɗin ta rabe biyu ta buɗe kanta. Daburcewa Manaal tayi ganin mutane har kusan uku tsaye saboda itace ke facing ƙofar, shi kuma ya juya musu baya. Ai babu shiri takai hannu gefen cinyarsa ta mintsina cikin rawar murya da raɗa ta ce, “Mutane fa”.       Idanu ya ɗan lumshe dan har yanzu hannunta na'a jikinsa taƙi sakin mintsinin data masa sai ma sake matsewa take sosai. Kaɗan ya waiwayo kansa ya kalla ƙofar elevator ɗin. Sai kuma yay wani kalan luuu da idanun cike da basarwa ya miƙe tsaye da ƙyau. Maɓallin rigar suit ɗinsa ya shiga sakawa tare da kallon hannunta dake a jikinsa har yanzu. Silently ya ce, “Sai fatan ya cire ne Besty”.       Da sauri ta janye hannun nata, sai kuma ta yunƙura zata fice ya cafko hannunta. Cike da takunsa na nutsuwa da ƙasaita tamkar komai bai faru ba ma ya fito, su HOD dake wajen suka shiga musu barka da dawowa cikin girmamawa. “Thanks you”. Kawai ya faɗa a taƙaice ya jata suka bar wajen kanta a ƙasa ita dai.        Sai da suka ɓace a wajen gaba ɗaya Director Steven ya kalla HOD da CFO fuska da murmushi ya ce, “Uhm dama haka boss yake”.      Dariya HOD ya sanya, tare da faɗin, “Ai irinsu daman yan babu sauƙi ne ina gaya maka. Ai kowa ya shirya, dan sai an mana ƙurmus a companyn nan da soyayya”.       Dariya suka sake sanyawa a karo na biyu, banda CFO da zuciyarta ke mata zafi da raɗaɗi saboda kishi. Tsahon lokaci take jin son AA a ranta duk da ta girmesa a shekaru, sai dai tana matuƙar ƙoƙarin dannewa ta yanda kowa bai taɓa fahimtaba a companyn. Shi kansa ta fahimci kamewarta ya sashi bata amanna kai tsaye, dan duk wadda zata nuna masa tana sonshi in har tana a kusa da shi duk iya aikinta sai ya canja mata waje. Hakan data fahimta yasa ita tazo da sabon tsarin kame kanta. Ita ɗin bazawarace, mijinta rasuwa yayi shekaru biyar kenan, bata taɓa haihuwa ba. Bata sake wani auren ba kuma har yanzu. Tun randa akai musu interview a companyn ta ɗaura idanunta akan CEO taji duk duniya shi kaɗai take so. Ƙyaƙyƙyawace itama ta gaske, gidansu kuma gidan kuɗi ne ƙwarai da gaske, tayi karatu mai zurfi, ko aikin nan tana yinsa ne dan ra'ayi kawai bawai dan buƙatar albashi ba, duk da dai AA mutum ne mai ƙoƙarin kamantawa ma'aikatansa albashi mai tsoka dako gwamnati albarka musamman daya kasance ƙasar tamu zalunci yayi gaba ba'a wadata ma'aikatan da albashi mai ƙyau..........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ _* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣ ______________ ........Cike da farin cikin aikar da Mamy tai mata ta fito, dan dama hanyar da zata fita a gidan take nema sai kuma ga mafita ta samu cikin sauƙi. Abinda ya ƙara mata daɗi da Mamyn tace ta hau taxi tunda drivers ɗin gidan duk sun fita. Ɗaya ya tafi kai yara makaranta, ɗaya ya tafi da Abah ɗayan AA. Ita kuma tana buƙatar akai mata saƙon ne yanzun nan. Ba komai Haule ta fahimta akan Mamy ba, amma ta daɗe da gane wasu abubuwanta a gidan musamman akan fuska biyu ga Oum, kawai dai ba abinda ya shafeta bane shiyyasa bata gaɓa ɗaɗara kanta da ƙasa ba. Sai dai duk wani aiken Mamy ita take sakawa, ta yarda da ita ɗari bisa ɗari. Tasan kuma hakan nada nasaba da kasancewar Maman Nuratu ce ta kawota gidan. Sai dai abinda Mamyn bata sani ba Maman Nuratun ta kawota ne dan tai mata aiki a gidan, yayinda ita kuma Maman Nuratu bata san Sille takema aiki ba a kansu su duka da AA. Can gaban wani tsohon Company Haule tace mai taxi ya sauketa. Ta zaro kuɗinsa ta basa sannan ta tura kai ciki babu ko ɗar. Kai kawai mai taxi ɗin ya girgiza zuciyarsa na sosuwa da ganin yanda yaran mu na hausawa suka lalata kansu. Kowa yasan wajen nan maɓoyar ƴan daba ce da manyan ƙasa  ke amfani da su wajen ta'addanci, shiyyasa ko anzo an kama su basa wuce ranar ake sakinsu su dawo. Ya tabbatar yarinyar nan kodai kayan shaye-shaye zata saya ko kuma mu'amular banza. Shi dai yaja taxi ɗinsa yay gaba.         Tunda Haule ta shigo cikin tsohon companyn sosai yaran Sille dake zaune daba-daba wasu na shaye-shaye, wasu na wanki, kai kowa dai na hidimar gabansa tamkar wanda suka samu gida suketa gaisheta dan kowa a cikinsu yasan yarinyar oga ce. Ita ko cike da jin kai take amsa musu harta dangane da idan ɗakin Sille yake. Bacher ce ta langa-langa, daga ciki kuma katako, sai dai an fenteshi tsaf ta yanda bazaka taɓa yarda katako bane ba. Ɗakin babbane sosai, akwai gado a ciki da kujeru set guda, sai freight da television harda speakers harda AC. Ƙasan ɗakin kuwa tils ne tsaf. Zaune yake a kujera ya wani barbaje gabansa kwalaben giya ne har uku, sai dai ba giyar yake sha ba taba ce a hannunsa kunnesa maƙale da waya alamar magana yake, daka gansa kuwa kaga Sillen na gasken gaske, dan sirrine sosai tamkar zai karye ko in iska mai nauyi zata iya yin gaba da shi. Tunda ta shigo ya zuba mata ido, tana ƙarasowa gabansa yasa ƙafa ya taɗota ta faɗa a kansa, matseta yay a jikinsa tare da manna mata kan tabar hannunsa a damtsen hannunta. Ƴar ƙara tai da ƙanƙame jikinta saboda zafin wuta, sai yay murmushi da yarda tabar a ƙasa ya shiga shafa mata wajen da har ya ɗashe dan ya ƙonata. A haka ya kammala wayar, ana yankewa daga can bai wani tsaya komai ba yay wurgi da ita gefe ya ɗauka Haule cak ya nufi gadon ɗakin da ita.....        Sai da suka gama masha'arsu sannan ta miƙe a ɗan rikice tana faɗin, “Baby bara na wuce. Aikana matar can tayi gidan su Nuratu nakai saƙo”. Ta miƙa masa wayarta tana cigaba fa faɗin, “Gashi na ɗakko maka yau da safe, dan ita da shi duk sun koma aiki”.        Kamar yanda bai tanka mata ba tun ɗazun yanzu ma batare daya ce komai ba ya amsa wayar daga kwancan da yake. A zabure yay wani kalar tashi zaune yana waro idanu waje. Sai kuma ya nufi drawer ɗin dake a ɗakin ƙarama ya buɗe, kayan ciki ya shiga watsowa a ƙasa har ya samu damar ganin abinda yake nema. Ita dai Haule tsoratama tayi da yanayin nashi, da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa. Juyowa yay inda take idonsa akan wani hoto daya ɗakko. “K duba min nan ko idona ne? Data cikin hoton nan da wannan duk mutum ɗaya ne?”. Karo na farko kenan dayay mata magana cikin buɗaɗɗiyar muryarsa mara daɗin saurare da tafi gangar jikinsa girma. Amsar wayar tata tayi da hoton ta zuba musu ido itama. Sai kuma ta ɗago tana kallonsa. “Baby tabbas wannan duk mutum ɗaya ce, kawai dai anan bata ƙarasa kaiwa mace bane ba. Dama kasan matar AA ɗin?”.         Bai tanka mata ba, sai wani irin naushi daya kaima bangon katakon ɗakin yana faɗin, “Yanzu ne yaƙin na gaske zai fara”..      Sakare Haule tai tana kallonsa. Sai dai ko kallon inda take bai sake yi ba ya nufi bayin dake ɗakin ɗan ƙarami na wanka, wanda shima dai ɗin na langa-langa ɗin ne.. Wanka yake yana dariya sosai kamar mahaukaci sabon kamu. Jinsa yake a wani irin nishaɗi mai girman gaske daya daɗe baiji a zuciyarsa ba. Ajwaad ya auri Maanal fa? Eh lallai yanzu ne za'ai wasa mai zafin gaske tsakaninsa da shi. Tabbatacen alwashine wannan a garesa sai ya nakasta Ajwaad da Maanal. Dole ne yayi RAMUWAR GAYYA DA TAFI GAYYA zafi. Shine fa Sillen karan gero mai wuyar tsagewa, idan kai nasarar tsagewar baka yanke ba kai mai nasara ne. Uban daba yake a yanzu mai kujerar ƙarfin iko. Ajwaad! Maanal! Ku jira sakamako....     Ya kwashe da wata shegiyar dariya yana kaiwa bangon langa-langan duka har sai da Haule dake shirin tafiya ma ta firgita. Hakama yaransa dake can ta waje duk sai da suka kallo ɗakin da mamakin minene ya saka ogan nasu nishaɗi haka ne?...      _Tofa, mike faruwa ne? Wanene kuma Sille? Miyake nufi da yanzu ne wasan zai fara? Menene tsakaninsa da AA ko nace Darma Family da har ya shafi Maanal yake ajiyar hotonta?. Hummm kumuje zuwa kudai cakwakiya ce ta gaske fa🏃🏃🏃😀._ ___________★        Suna ƙarasa shiga cikin office ɗin Maanal ta ƙwace hannunta daga cikin na AA. Babu musu shima ya saketa. Bai kuma ce komai ba ya nufi kujerarsa. Ko'ina a tsaftace yake ƙal a office ɗin. Ga wani ƙamshi mai kwantar da zuciya na tashi. Files ɗin dake a table ɗin nashi tule yabi da kallo, sai dai an ajiyesu a tsare dan kowa yasan shi ya tsani ganin waje rakwacam ba tsafta. Hannu ya kai a hankali ya kunna computer ɗin saman desk ɗin, kafin ya ɗago idanunsa ya zuba akan Maanal dake a tsaye har yanzu. Kallonsa take yi itama, sai dai yana ɗagowa ta kauda kanta. Baki yaɗan taɓe, sai kuma ya ɗauka kan waya ya danna 1 tare da kaiwa kunnensa. Dai-dai an ɗauka. A taƙaice ya furta, “Zo ciki”. Bai jira amsa ba ya yanke kiran. Maanal ya kalla fisha ya ɗauke idanunsa, ciki-ciki ya ce, “Malam sit”.      Harararsa ta ɗanyi, sai kuma taje ta zauna dan bata son wanda taji yace yazo ya shigo ya ganta a tsayen kodan nasihar da Oum da Abah sukai mata na darajta kanta ga ma'aikatan companyn. Bawai tazama mai girman kai ko wulakanta kowa ba. A'a ta mutunta kanta da kame kanta yanda ya dace dai matsayinta na matar ogansu. Inba haka ba mutane da yawa zasu fara amfani da ita a yanzu domin cimmasa a ciki da wajen companyn. Hakama mata dake ƙulafucinsa a ciki da waje zasuji shakkar nunata koda da zunɗene balle isa gabanta.       AS ne ya shigo bakinsa da sallama bayan yayi knocking AA ɗin ya bashi damar shigowa ciki. Batare daya kalleta ba saboda girmamawa ya wuce sum-sum kamar munafuki inda boss yake. Hankalin AA a computer shima, batare daya ɗago ba ya ce, “Daban kiraka ba bazakazo kamin bayanin abinda ya dace ba kenan Haneef?”.            “Ayi haƙuri sir, naga kana tare da Auntynmu ne shiyyasa. Amma ai min afuwa”.      Komai AA bai sake cemasa ba. Sai tulin documents ɗin dake zube ya kalla. Matsowa AS yayi kusa da shi domin fahimtar abinda yake nufi. Cike da nutsuwarsa ya shiga masa bayani yanda ya kamata. Shi kuma yayi shiru yana saurarensa. Hakama Maanal dake latse-latse a waya kunnenta na kansu ne tsaf. Fin minti ashirin kafin su gama magana da AS ya fita. Dan haka ta ɗago ta kalla sashen da yake zaune. Ganin zai fara aikinsa kamar ya manta da ita yasa ta miƙe. Wayarta ta saka a handbag ɗinta sannan ta nufesa, batare data ƙarasa inda yake ba ta ce, “Nifa zan tafi”.      Yi yay kamar baijita ba tsawon sakanni kafin ya ɗago ya kalleta. Ganin yanda ya kafeta da idanu yasata ɗauke nata tana sake tsuke fuska. Shima janye nasan yay ya maida ga aikinsa yana faɗin, “Nace miki na gama dake ne?”.          “Amma kasan fa aiki nazo ko. Kuma Abah yace ka fita harkata”.     “Hakane Aunty Maanal yi haƙuri ƴar gidan Abah”. A yanda yay maganar tasa ta ɗan hararesa. Dan irin gatsen da yake mata kenan ko ada can idan tace yay abu kota takura masa idan yace bazaiyi ba sai ya dinga kiranta da Aunty...... Takaici ya saka Maanal ɗauke hankalinta daga gareshi gaba ɗaya. Tsohon mintuna arba'in yanata aikinsa kamar ma ya manta da ita akai knocking ƙofar. Sai da ya kalla sashen da Maanal take sannan ya bada izinin shigowa. AS ne ya shigo yanzun ma. Batare daya kalletaba yanzu ma yay mata sannu. Maimakon amsawa saita samu kanta da harararsa, dan haushin ogansa ya shafe sa shima. Shi dai da yake ba kallonta yake ba baima san tanayi ba. Cikin girmamawa ya ƙarasa gab da AA, murya a ƙasa yake masa bayani like ba'a son taji komai. Sai ta sake tunzura. AA ya jinjinama AS kansa, tare da faɗin, “Shike nan kuje ka kaita, su kuma su bari after break na ɗan rage aiki”.       “Okay sir”. AS ya faɗa yana nufar inda Maanal take. Kansa a ƙasa ya ce, “Aunty bismillah”.        Miƙewa tayi batare da tace komai ba, sai dai ta kalla inda AA yake zaune cikin yanayin harara. Sai ko akai sa'a shima ita ɗin yake kallo. Gira ɗaya ya ɗage mata, sai kuma ya kashe ido ɗaya cike da neman rigima da son tunzurata. Aiko fuska ta yamutse tare da janye nata fuuu tabi bayan AS bayan ta zuba masa harara. Rakata yay da idanu har ta fice gaba ɗaya. Guntun murmushi yayi yana mai lumshe idanunsa ganin yanda take cika da batsewa. A kan lips ya furta, “Ƴar gatan Abanta kenan” yay wani murmushin shaƙiyanci yana datse lip da haƙori.........✍️ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣2️⃣ ______________ ........ KANO    Ganin yanda ya shareta kwana biyu bai sake gwada son kwana ɗakin ba yasa yau ta saki jiki, balle ma daya shirya ya fita wajen aiki. Su uku ne kawai a gidan, ita sai ƙannensa biyu ƴammata da suka zo mata wai yini. Dan yana fita babu jimawa suka zo. Sune suka mata gyaran gidan tsaf da tsohon kwana biyu bai samu shara ba. Dama dai yaran anguwa dake ɗan shigo mata take ritsawa su mata. Ko kuma baƙin da sukazo ganin gida idan taga ƴan tagajan-tagajan ne sai ta saka su. Wasu ma danginsu ne, amma da yake su dama ƴan gidansu an musu shaidar girman kai da raina mutane bata jin ko nauyi take cewa su mata aiki koda sun girmeta. Su kuma da shegen kwaɗayi da neman gindin zama sai suyi ɗin kuwa.         Ƙannen nasa ma sai faman yamutse-yamutse take musu. Sajeeda sarkin zuciya har tace su tafi kawai, da ƙyar Khadijah ta lallaɓata. Aikin ma kinyi tayi sai Khadijan ce tayi mafi yawa a ciki. Huznah dai ana bedroom an ɓararraje ana barci, dan daga charting ta ɓingire a wajen. Ana idar da sallar Azhar Sageer ya dawo gidan. Yaji daɗin ganin babu kowa sai ƙannensa, ga kuma mutuniyar tasa na sharar barci. Hankalinsa kwance ya kaɗa su Sajeeda gida, yaje kuma ya kulle ƙofar gidan sannan ya koma ciki. Hajiya Huznah anji daɗin fanka barci yay daɗi sai taji hannu na yawo a jikinta. A firgice ta farko sukai ido huɗu kuwa da Sageer. Wani irin ɓacin rai ne ya sata yunƙurawa a masife, sai dai gogan yariga ya mata ɗaurin huhun goro da jikinsa. Ƙarfi kuma ba ɗaya ba, dan ko motsin arziƙi bata iya tayi ba, tana ji tana gani kuma ya shiga yin yanda yaso da ita batare daya nuna damuwa da hawayen da take ba. Cikin sauƙi da nuna mata mazanfa maza ne yay kiɗinsa yay rawarsa tare da more sadakinsa. Itako tana faman kuka da zaginsa, zagi kuma na rashin mutunci. Nunawa yay bai damu ba, dan ta ceci kanta data kawo mutuncinta, harga ALLAH bai kumayi tsammanin hakan ba daga gareta, musamman idan yay dubi da wayewar yan gudansu ta tsiya. Sai dai kuma mahaifinsu mutumin kirki ne, dan tsaye yake akan tarbiyyarsu babu wasa. Hakama Yazeed yana nasa ƙoƙari kasancewarsa babba kuma namiji. Yaso taimaka mata amma taƙi yarda, dan haka yay ficewarsa yabar mata ɗakin ransa fes.          Kuka bana wasa ba Huznah taci, daga ƙarshe tai kiran wayar Hajiya Basariyya. A lokacin Hajiya Basariyya na zaria tare da ƙawarta cikin wani ƙauye wajen wani malaminsu. Sosai gabanta ya faɗi jin yanda Huznah ke kuka. A rikice tace, “Ke dan ubanki minene zakisa zuciyata ta buga”.      Kasa magana Huznah tayi, sai da ta sake jan wani ƙugin kukan sannan ta ce, “Ummy fyaɗe yamin”.        “Fyaɗe kamar ya?”.   “Wlhy Ummy fyaɗe, ina barci a ɗaki kawai yazo ya haike min, nayi duk yanda zanyi na ƙwaci kaina amma na kasa. Kuma da yake shi tsinanne ne ya fita yana min dariya. Wlhy ji nake kamar na kashe shi Ummi, gashi nan ko tashi na kasa yi wata irin azaba nake ji a jikina”.      Jagwab Hajiya Basariyya ta kai zaune, kafin ta ce, “Amma dai wannan yaro anyi matsiyaci ɗan iska. Munafiki sum-sum da shi. Wlhy Huznah kin cucemu kin cuci kanki. Yanzu duk faɗi tashin da nake na ganin kin baro wannan kurkukun gidan kin koma inda daula take ki huta muma ahalinki mu huta shine kikai saken da matsiyacin yaron nan ya ƙwace abinda shine kimar taki. Yanzu ubanmi zaki kaima AA Darma ɗin to?”.      Kuka sosai Huznah ta sake fashewa da shi mai ƙarfi ma kuwa tana faɗin, “Na shiga uku Ummi, wlhy ina sonshi, bazan iya haƙurin rasashi shi ba. Ki taimakeni ALLAH ba laifina bane ba, kullum rufe masa ƙofa nake kamar yanda Aunty tace nayi shine munafikin ya dawo da rana azzalumi dan ya cutar dani. Ummi dan ALLAH ki taimakeni kada na rasashi.....” kuka ya sarƙeta. Kasa magana Hajiya Basariyya tayi, sai Maman Yaseerah ce ta amshi wayar...... _________★             Mamaki ne sosai ya kama Maanal ganin inda AS ya kawota. Wato sabon Office da aka bata kafin tafiyarta hutu, ita sam tama manta da batunsa. Office ne madaidaici da aka ƙawata aka kuma haɗa mata komai daya kamata da zata iya buƙata. Kujerar zamanta da desk mai ɗauke da computer guda ɗaya, sai visitors chairs dake gaban desk ɗin. Ta gefen damarta haɗaɗɗiyar kanta ce ta show glass da aka shirya kayan buƙata irin wanda mai zane zai buƙata...., Hatta da pensul gasu nan tari-tari kamar a shagon sai dawa. Sai daga ɗan gaba yan kujeru guda biyu suma da visitors zasu iya zama ko ita idan tana bukatar hutawa, daga bayansu akwai fright da

Chapter 6 of 15