Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗaya tayi zaku dawo?”. Nutsatstsiyar muryar Abah ta daki cikin kunnensa. Idanunsa ya sake lumshewa ya buɗe da ƙyar, cikin ƙoƙarin ganin muryarsa ta kuma samun nutsuwa yay ɗan gyaran maƙoshi kafin ƙasa-ƙasa ya ce, “Gamu nan in sha ALLAHU Abah”.      Shiru Abah yay sautin shaƙaƙƙiyar muryar ta AA na dakar masa zuciya. Dan duk wanda ya sanshi ya jisa a yanzu zai fahimci akwai lauje cikin naɗi. Amma kasancewarsa dattijon arziƙi sai cewa yay, “Okay kuyi sauri Oum ɗinku nason kwanciya” daga haka ya yanke kiran. Idanu AA ya sake lumshewa ya buɗe a karo na barkatai, shi kansa ganin ƙarfe nawa sai da yaji zuciyarsa ta girgiza. Harga ALLAH bai san sun jima haka ba, dan sai yake ganin ma kamar basu wuce minti talatin da fitowar ba. A karo na farko ya maida birkitattun idanunsa kan Maanal dake a duƙufe har yanzu. Lallausar fatar bayanta da hasken fitilar titin ta hasko ya zubama idanu, sai farar b ɗin jikinta datai matuƙar dacewa da fatar gata fes babu wani alamar datti a tare da ita. Numfashi ya sake ja a fisge, kafin cike da kasala ya kai hannu kan zip ɗin zai ja mata shi saman. Zaram ta miƙe zaune sosai idanunta share-share da hawaye. Shi dariya ma taso bashi ganin yanda ta wani zazzaro masa idanun alamar gargaɗi. Ƙasan zuciyarsa kuwa sai yaji kamar yana jin nauyinta shima musamman da wani gefe na zuciyar keta maimaita masa kalmar (Bestynka ce fa! Amma ka rufe ido ka aikata mata wannan abin kunyar har kana neman sakin layi) kauda tunanin yay gefe murmushin gefen baki na neman suɓuce masa. Amma sai ya daure a tausashe ya ce, “Yi haƙuri zip ɗin zan rufe miki, idan kuma kina son Abanki ya gane to a barshi a hakan kawai kinga na huta sai yace mu wuce sashen mu kawai ya salllama”. Ai da gudun tsiya ta duƙe alamar ya rufe matan. Yanzu kam saida ya murmusa kaɗan, kafin ya kai hannun yaja zip ɗin, yazo dai-dai jikin b ɗin ta ya dakata, hook ɗin yay ƙoƙarin maida mata dan duk ya ciresu saura ɗaya jal ya rage masa. Rumtse idanu kawai Maanal tayi da ƙarfin tsiya harya kammala ya ƙarasa ja mata zip ɗin.      “Oya wanke fuska mu wuce, idan kuma a samu hotel anan kusa muƙarasa to”.     A baima gama rufe baki ba ta ɓalle murfin motar, batare data kallesa ba ta warce goran ruwan hannunsa ta juya ta fara wanke fuskanta. Murmushi ya saki, tare da kai hannu ya shafa lallausar sumar kansa dake lashe kuɗaɗe da shima bai san adadi ba. Koda ta gama bata kallesa ba, ta yarda goran a ƙasa ta maida murfin ta rufo, sai kuma ta matsa jikin murfin ta maƙure. Komai baice mata ba, sai handkacheff ɗinsa mai ƙamshi ya miƙa mata kawai. Ɗan kallonsa tayi, suka ko haɗa ido. Da sauri ta janye nata tana fisgar handky ɗin kawai. Nanma murmushi yay yayima motar key suka cigaba da tafiya. Sai dai yanzu gudu yake sosai saɓanin ɗazun. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu a gaban ƙaton gate ɗin gidansu...               Koda suka nufi sashen Oum salaf-salaf Maanal ke tafiya kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Gani take kamar tana shiga kowa zai gane abinda ya faru a tsakaninsu. Musamman ma Abah da Oum. Ɗan tsayawa AA yayi, ita kuma kanta a ƙasa tunanin da take yi ya ɗauke dukkan hankalinta har tazo gab da shi bata sani ba. Sai da ta bugu da bayansa sannan ta ɗago da sauri, tayi baya kuma zata faɗi. Saurin juyowa yay tare da riƙota a lokaci guda, cike da kulawa ya jinginata da jikin bango. Muryarsa a sanyaye saboda halin da yake ciki ya riƙe fuskarta, ɗayan hannunta kuma a cikin nashi yana kallon fuskar ya ce, “Tunanin mi kikeyi ne haka?”.        Wata irin kunyarsa take ji shima, dan haka tana ɗan ɗago idonta ta kallai ta maida su ta risinar, shiko nashi yawo kawai suke akan ƙyaƙyƙyawar fiskarta. Kanta kawai ta girgiza masa tana ƙoƙarin janye hannunta dake a cikin nasa yaƙi bata damar hakan. Hawayen da take riƙewane suka ziraro, ya waro lumsassun nasa sosai. “Ya arrahaman, miye abin kukan kuma?”.       Cikin rawar murya ta ce, “Yanzu idan Oum da Abah suka gane fa”.      Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, a ransa yana faɗin, (Ashefa na manta yarinyar nan ɗanya ce, rinton aji yasata gama makaranta da wuri) a fili kam sai ya shafa fiskarta tare da faɗin, “Sai dai in kece kika so su gane”.     Kallonsa ta ɗago tayi sosai a karo na farko, ya jinjina mata kansa yana ɗan laɓe baki da murmushin gefen baki a tare. Sai kuma ya shafa kanta cike da lallashi da tsokana ya rankwafa yana mai kai bakinsa saitin kunnenta da raɗa ya ce, “To ko mu tafi sashen mu kawai ki kwana acan, da asuba na miki alƙawarinkin rakoki da wuri kafin kowa ya tashi”.      Tamkar wadda ya zaburar, ta sa hannayenta duka biyu a ƙitjinsa ta tura shi baya. Matsawar yayi yana dariya, ita ko ta kwasa da ɗan gudu cikin sashen Oum. Ko ganin Abah dake bayansu ma batayi ba sam. A falon kuwa akwai Oum, Mamy, Nibras, Saheeba da Fawzan harda babban Yaya a yanzu na zaune suna hira sai kawai ganinta sukai kamar walƙiya ta wuce hanyar upstairs. Da sauri Oum ta ce, “Munga idi Baby waya biyoki haka?”.      “Oum fitsari-fitsari” ta faɗa batare data waiwayo ba. Dan tasan wannan dabararce kawai zata rabata da jin kunya. Saboda babu wanda zai kalleta bai fahimci wani abu ba a fuskar ta da lips ɗinta da yasha wahala a hannun wancan mutumin. Dariya Fawzan da Babban Yaya suka saki a lokaci guda, dan abinda Maanal ɗin tayi ya tuna musu da baya ne. Haka take yi idan suka dawo makaranta, sai ta riƙe fitsari tun daga can, mota na tsayawa ta fita a guje zuwa ciki tana faɗin, “Fitsari-fitsari”. Sai da Ammie ta zaneta wataran aka samu lafiya ta daina abin nan. Oum ma dai dariyar tayi, dan itama dai abinda yazo mata a rai kenan. Mamy da su Saheeba kam wani irin takaici ne ya ƙullesu, da kallon abinda Maanal ɗin tayi matsayin wani sabon bariki.... A waje kam, AA na gama dariyarsa dake fita a hankali ya juyo da nufin shigewa shima sukai ido huɗu da Abah daya harɗe hannaye a ƙirji ya tsaresa da idanu. Da sauri AA ya juya yana rumtse idanu da kai hannu ya shafa kansa, haƙoransa damtse da lips ɗinsa. A zuciyarsa faɗi yake (Ajwaad kaga takanka, tsohon nan ba raga maka zai yi ba....) katsewa zancen zucin nasa yay saboda taɓashi da akayi, juyowa yay kansa a ƙasa hannunsa a cikin sumar kansa, sai kuma ya ɗan buɗe ido ɗaya ya ɗan kalla Abahn. Abah da dariya ke cinsa a rai ya gimtse da ƙyar ya wani sake tsatsatsaresa da idanun. Sai AA ɗin cayay, “La Abah kai ne?”.      “A'a bani bane aljani ne”. Abah ya bashi amsa cike da gatse. Bayansa AA ya koma ya tungumesa, ya tabbatar hakan shine rufun asirinsa dan wlhy tsaf Abah zai gane halin da yake ciki, musamman idanunsa da suka kaɗe. Cike da shagwaɓa ya kwantar da kansa a kafaɗar Aban yana faɗin, “Kaga ko Abah ALLAH ban lura time ya tafi haka ba. Na tuba! Na tuba! Na tuba!!”.     Yanzu kam kasa daurewa Abah yay saida ya murmusa. Amma kasancewar AA na bayansa ba gani yay ba. Fuskar ya maida ya himtse a dake ya ce, “Ai na faɗa maka daman saina ƙara kwanakin suspension idan ka daɗe min da yarinya”.          A sanyaye AA ya ce, “Abah holdup ne fa a hanyar”.     “Na aljanu ko? Yo in ba na aljanu ba a daren nan wane huldup ne zai taru. Kaji tsoron ALLAH Ajwaad”.        Ƙaramar dariya yanzu kam AA ɗin yayi da faɗin, “To Abah kawai abar kaza mana cikin gashinta. Kawai kayi murna mun dawo bamu ɓata ba ma”.      Rankwashi Abah ya kai masa bisa kai, da sauri ya sakesa ya shige sashen Oum yana dariya. Shima Aban dariya yake yi da girgiza kansa. Wani irin farin ciki na ratsa masa zuciya. Rabon da yaga Ajwaad a irin wannan yanayin na farin cikin da har zai dinga wasa da dariya kai tsaye an ɗauki shekaru masu yawa. Ko tsokanarsa sukai sai dai yay guntun murmushi kawai yay shiru. Amma yau jiba yanda yake zuba masa surutu da shagwaɓa kai tsaye. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya nufi sashensa yana mai jerama UBANGIJI kirari da godiya.........✍️ _Abah namu, anya! Anya kuwa🥱. Bara dai nayi shiru😂👍_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣9️⃣ ______________ *_LADIES COLLECTION AND MORE_* 08169307477 SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai? To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane, MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah, LADY'S COLLECTION AND MORE ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻 Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Less Hijabs Supplements Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko 08169307477 Address bayan gidan drugs katsina State Kayan mu masu inganci ne sosae Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯 *********** ________________ ......Su babban Yaya na dariyar Maanal AA ya shigo. Duk kallonsa sukai, musamman Mamy dake masa kallon ƙurulla, hakama Nibras ji take kamar taje ta rungumeshi ta fashe da kuka saboda kishin Maanal dake ruruwa a zuciyarta. Gashi yanda lips ɗinsa suka wani ƙara zama pink duk sai taji ta tsargu, zuciyarta ta shiga wassafa mata abinda ya faru. Cike da basarwa AA ya kai zaune. A nutsensa kamar bashi ya gama yima Abah shagwaɓa ba ya ce, “Ikon rabbu, miya saku nishaɗi haka?”.       “Bestynka mana” cewar Fawzan, sai kuma ya shiga bashi labarin abinda tayi. Wani ɗan murmushi ya saki tare da girgiza kansa. Ba ƙaramin dukan zuciyar Mamy da Nibras murmushin nasa yayi ba. Amma sai ya katse yanayin nasu da faɗin, “Mamy mun kai”. Batare daya kalleta ba. Dan yasan tana nan tana tuhumarsa da ido.          Kafin ta amsa masa Fawzan ya dawo kusa da shi neman tsokana, sai dai yana zama ƙamshin sassanyan turaren Maanal daya manne a jikin AA ya shiga hancinsa, idanu ya waro tare da sake matsawa yana shinshina shi. Cike da raɗa Fawzan ya ce, “Ehem-ehem malam yau dai babu zancen dojewa ALLAH ƙamshin turaren Lilly kake yi?”.      Harararsa AA yayi, shima ƙasa-ƙasa ya ce, “Yaya Fawzan ka rage gulma wlhy, mutum da matarsa dan anji ƙamshinta a jikinsa sai mi?”.     Sosai Fawzan ya saki baki da hanci yana kallonsa, shima AA ɗin kallon nasa yake da wani irin salon ɗage gira sama irin na (Eh ɗin nan). Jinjina kai Fawzan yayi, a hankali yace, “Ashe za'a bajeta a gaban Abah gobe. Dole a ƙara maka kwanaki sai after babbar salla”.        Yanzun ma ƙasa-ƙasa shima AA ya ce, “Yo a bajetan mana, zuwa babbar sallar kun fara jiyyarta dan ta fara laulayi kuwa, kunga sai ku bari sai ta haihu ku bani”. Daga haka ya miƙe cike da basarwa tamkar bashi ya faɗa ba. Fawzan daya saki baki yana kallonsa ya kwashe da dariya da faɗin, “Kai wannan yaro tantiri ne kai, ALLAH sai na tona”.     Gwalo AA daya nufi hanyar fita ya juyo yayma Fawzan, kafin yace, “Oum! Mamy! Babban yaya good night”. Ya fice a binsa. Cikin ɗaga murya Fawzan yace, “Muma da bakace mana good night ɗin ba lafiya lau zamu kwana, kuma gobe sai na fasa ƙwai a gaban Abah”.       Wani kalar ƙululun takaici ne ya kume Mamy, dan kallon da takema Fawzan da AA ta gefen ido tsaf ta fahimci abinda suke tattaunawa da juna ta hanyar motsin bakinsu. Gittawar AA a yanzu kuma sarai ta ji ƙamshin turaren Maanal itama. Hakama Nibras data sanya musu ido. Saheeba dai tsarguwa kawai tayi, shiko babban yaya da Oum dariya ma suke musu dan Fawzan da Ajwaad tamkar tom and jarry haka suke. Komansu irin na asalin sako-da-sako ne basa ragama juna. Ta wani gefen kuma kamar wasu abokai.. Fitar AA ɗin ta saka hirar tashi gaba ɗaya, dan dama dai rashin dawowarsu yasa hirar tsaho haka da sha biyu ta wuce...        Lokacin da Oum ta shiga ɗaki samu tai Maanal harta kwanta. Murmushi kawai tayi itama ta shiga kimtsawa domin tafiya wajen mijinta. Taje zuba kayanta a laundry basket taji ƙamshin turaren AA matuƙa a wajen, kayan cikin basket ɗin ta kalla, kayan Maanal ne data cire yanzu. Kasa daurewa Oum tai ta ɗakko doguwar rigar takai hancinta. Itace kuwa ke ƙamshin na gasken gaske. Kai Oum ta girgiza dariya na suɓuce mata, sai yanzu ta fahimci dalilin gudun Maanal da ƙin tsayawa a wajensu da wannan kwanciyar saurin. Ƙasa-ƙasa ta ce, (Wannan nake jiye maka Abansu, karka bashi matarsa dai a juri zuwa rafi) daga haka ta ajiye rigar ta ƙarasa shirinta ta tafi wajen mijinta... _________★   Sille ya jima akan titin bayan wucewar motar AA. Dan abinda ya gani na faruwa daga nesan da bayansu da yake kasancewar gilashin motar a sauke yake kaɗan ya sashi canja shawara. Waya ya fiddo ya shiga yi musu video. Dan wata shegiyar waya ce dashi mai ƙarfin camara ta yanda yake iya zooming abu mai nisa sosai. Yako yi nasarar ɗaukar komai yanda ya kamata, daga ƙarshe ya adana videon a wayar tasa yana murmushin cin nasara. Dan yaci alwashin sai videon nan ya zame masa kadarar tatsar mutane da yawa kuɗaɗe kafin yasa ai masa editing ɗinsa ya bazashi a media ta yanda sai ya kunyata rayuwar AA da Maanal dan zai canjama al'amarin siga ne ta koma matsayin kafin aurensu ne hakan ta faru. Sauran alwashinsa kuma zai biyo baya dan baya yafiya ba kuma ya canja tsarinsa akan maida murtani saboda sabon idea.....      Hummm wannan Sille! Wannan Sille wai mike damunka ne🙄🥺. ________★      Murmushin da Oum keta faman yi ne ya saka Abah dake binta da kallo faɗin, “Wai shi wannan murmushin na miye?”.         “To Gadanga miye a murmushi ko dai ka tsargu ne?”.   “Tsarguwar ma sai nayi, dan nasan halinki sarai”.    Dariya Oum ta sakeyi, sai kuma takai zaune a kusa da shi tana faɗin, “Abansu ka fahimci a yanayin da Ajwaad da Maanal suka shigo kuwa?”.      Kansa ya girgiza alamar (a'a) Cikin ɗan waro idanu Oum tace, “Gadanga kaji tsoron ALLAH”.      Murmushi kawai yayi baice komai ba. Oum ta ɓata fuska. “To ALLAH ina gaya maka idan baka bama Auta matarsa ba za'a haifi ɗa mara ido, kadai gani da idonka sau biyu”.            “A haifi ma mara kunne, ai nasan dai duk rashin kunyarsa bazaiyi abinda kike tsoron ba. Fateema da kike ganina sarai nasan abinda nake yi, dan haka ki daina damun kanki ina kan ra'ayina. Saboda ni nasan dalilina nayin komai”.     Shiru kawai Oum tai tana kallonsa, sai kuma ta kai kwance cike da haushi. Baki kawai Abah ya taɓe ya cigaba da duba littafin hannunsa daya kasance na addu'oi....       ★Washe gari Abah ya tashi da uzirin fita da wuri, dan haka ya bada umarnin driver yakai Maanal wajen aiki. Yauma kamar jiya bayan sun kammala breakfast da Maanal bataci ba tace azumi take kowa ya shiga motarsa. Driver ya buɗema Maanal mota itama. Oum batace komai ba dan a gabanta Abah ya sanarma driver ɗin. AA ma yi yay kamar baiga komai ba ya shiga tashi motar nasa drivern ya jasa. Sai da suka fito ko street ɗin basu gama bari ba ya saka drivern sa tsaida na Abah. Fitowa drivern yay yazo saitin inda AA ɗin yake zaune yana faman duba wasu takardu. Batare daya kalla drivern ba sai gilashin daya ɗan sauke a dakensa ya ce, “Buɗe mata ta dawo nan”.     Daburcewa sosai drivern yayi, dan ba ƙaramin gargaɗi Abah ya masa ba akan hakan kasancewar yasan AA ɗin zai iya aikatawa. Cikin tashin hankali driver yace, “Ranka ya daɗe Alhaji fa yace...”      Wani banzan kallo da AA ɗin ya ɗago ya watsa masa ya saka shi kasa ƙarasa faɗa, sai ma duƙar da kansa da yay ƙasa da sauri. Shi kam dai sun sakashi a tsaka mi wuya. Kusan minti ɗaya AA ya ajiye takardun hannun nasa ya ɓalle murfin motar ya fito. Yayi ƙyau matuƙa cikin baby pink color ɗin suit, fuskar nan babu walwala sai kwarjinin kamala dana ibada ke fita. Maanal da haushin tsayawar tasu ya kumeta taja tsaki tana ƙoƙarin ƙarasa abinda take a laptop ta fito kawai taji an buɗe side ɗin da taken, ɗagowa tai cike da masifa dan son ganin wanene suka haɗa ido da AA da yay kicin-kicin da fuska. Itama dai tayi ƙyau sosai cikin lass da akaima doguwar riga, ta kafa ɗaurin zarah buhari sai veil ɗinta da yay dai-dai da tsarin shigar tata. Tana ƙoƙarin rufe laptop ɗin kawai ya duƙo cikin motar a kanta, kafin ta samu damar magana ya ɗagata cak ya fito da ita. Idan tace al'amarin AA bai fara girgiza tunaninta ba ma ai tayi ƙarya, yanzu banda ikkanci a titin ALLAH zai ɗakkota a mota da safen nan mutane nata kai-kawo. Koma tace a anguwarsu data tabbatar ko wani bai sanshi ba wani ya sanshi duk da ana rayuwa ne irinta ba ruwan wani da wani ɗin nan a anguwar. Da sauri kuwa nasa drivern ya fito ya buɗe masa ɗayan side ɗin da yaga ya zagaya, a ransa kuwa dariyar halin ogan nasa yake, yayinda suka matuƙar birgesa duk da yanata wani sinne kai. Ajiyeta AA ɗin yayi ya gyara mata rigarta ya rufe ƙofar, ita kam ai tamayi sumar zaune ne ko mi zatace oho. Dan sam tama kasa masa magana dan al'ajabi. Shigowarsa wajen da yake zaune hannunsa riƙe da tarkacenta da drivern Abah ya kwaso mata ya sata kallonsa ta gefen ido, sai wani ɓaɓɓata fuska yake kamar ba shine daren jiya ya gama aikata mata abin kunya ba. Aikinsa ya cigaba da yi batare daya sake kallonta ba yana cema drivern sa, “Muje” a daƙile.      Yanda ya basar ya cigaba da aikinsa itama sai ta basar ta cigaba da nata aikin. Har suka iso Company wani magana bai shiga tsakaninsu ba. Kai babu ma wanda ya kula ɗan uwansa. Koda motar ta tsaya kuma kasancewar tana tattara kayanta shine ya fara fita. Tayi zaton zai yi tafiyarsa ne. Amma sai a mamakinta ya zagayo ta inda take ya buɗe mata. Koda ta fito kuma sai ya saka hannu ya amshi kayan hannunta harda handbag ɗin kamar jiya. Ya kuma kama hannunta da ɗayan hannunnsa. Nashi kayan kuwa sai drivern sa daya bisu da kallo yana murmushi ne ya tattara yabi bayansa da su.      Yau ma cike da gulma wanda suka iso ke binsu da kallo suna kuma gaishesu da girmamawa. Yayinda wasu ke gwada son amsar kayan hannun AA ɗin amma sai ya girgiza kai kawai alamar (a'a). Kamar dai jiya harda masu leƙensu ta windows dan gulma. Suna shigowa kuma kowa ya nutsu aka shiga miƙa musu gaisuwa... Yau dai kai tsaye office ɗinta suka nufa. An gyara komai fes an saka air freshener masu daɗi, shine ya kunna wutar office ɗin dake a kashe, har saman desk ɗinta kuma yaje ya ajiye kayan hannun nasa batare daya kalleta ba ya nufi hanyar fita, ita dai tana tsaye tana kallon ikon ALLAH. Har yaje ƙofar sai kuma ya dawo gabanta yaja ya tsaya. Cike da gargaɗi fuskarsa a tamke murya a dake ya ce, “Daga yau wannan ya zama first and last da zaki bishi in har ba tare da Abah ba. Azumin mi kikeyi kuma”.      Yanzun kam kallonsa tai cike da mamaki, sai kuma ta tura baki gaba ta ce, “Na nafila mana”.         “To sai kisan yanda zakiyi da shi tunda baki sanar min ba.” ya ƙare maganar da dalla mata harara ya juya zai fita..........✍️ _Oh oh AA rigima azumin ne kuma sai an sanar maka munga idi🏃🏃🤣_ *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU....💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_My TikTok account 👇_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram👇🏻_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_ *_BOOK 2_* 🅿️➖2️⃣0️⃣ ______________ *_LADIES COLLECTION AND MORE_* 08169307477 SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai? To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane, MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah, LADY'S COLLECTION AND MORE ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻 Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Less Hijabs Supplements Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko 08169307477 Address bayan gidan drugs katsina State Kayan mu masu inganci ne sosae Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯 *********** _______________ 20 WANNAN SAƘONKU NE😊 LA'ILAHA ILLA-ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAZZALUMIN!! ......A tunzure Maanal data cika tai fam da wannan mulkin mallaka ta ce, “Kamar ya nasan yanda zanyi da shi? Yanzu ibadar ce kuma dan zan yi sai na sanar maka?”.         Sai da ya buɗe ƙofar sannan ya waiwayo ya kalleta, cike da izza ya furta, “Ya rage naki”. Daga haka yay ficewarsa. Harara ta rakashi da ita. Sai kuma tama ƙofar gwalo dan shi dai ai ya riga ya fice abinsa. Kujerar zamanta ta nufa ta zauna tana ƴar dariyar ƙeta. Dama babu wani azumi da takeyi, tayi hakan ne dan gujema halinsa na salon tattaɓata daya ɗauka. Handbag ɗinta ta buɗe ta ciro ƙyaƙyawan bottle mai kama da cup ɗin nan na zamani dake cike da tea, sai gasashshen bread a ƴar bowl data sanyo batare da ko sanin Oum ba. Dan Inte tasa ta haɗa mata su. Hankalinta kwance ta fara aikinta tana karyawa. Sai zabga murmushi take da bata

Chapter 10 of 15