Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wata ƴar kanta ƙarama an ajiye dispenser da coffee machine sai kofuna a cikin glass kanta ɗin na shan shayi dana shan ruwa. Office ɗin a cikin jerin officers na Designers Directors yake. Daga floor ɗin nasu kuma sai nasu oga kwata-kwata dake a floor ɗin ƙarshe. A tsakaninsu ma ba sai ka hau lifter ba su steps ne kawai.      Sallama AS yay mata bayan sake tayata murnar sabon office duk da a waccan ranar duk sun mata. Karan farko tai guntun murmushi tare da amsa masa. Yana fita ta sakama ƙofar key, sai kuma ta jingina a jikinta tana murmushi. Wannan fa shine DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE. Tayi wata biyar kacal matsayin Junior watch designer yau gata a wanan matsayin. ALLAH kaine abin godiya, kai ke maida bawa sarki, kai ke badawa ga wanda kaso a lokacin da kaso. Kai ke sauya al'amura daga wautar tsarinmu zuwa ƙyaƙyƙyawan ikonka. Ya rabbi ka cigaba da jagorantar rayuwata bisa ikonka ba wayona ko dabarata ko tsarina ba...       Takawa ta cigaba da yi cikin office ɗin a nutse har zuwa kujerar zamanta mai laushi da ƙyau tanata sheƙi na sabunta. Sai da tai addu'a sannan ta zauna, ta lumshe idanunta tare da yin wani kalar juyi tana dariya ƙasa-ƙasa. Sai kuma ta tura kujerar jikin desk ɗin sosai ta ɗauka wayarta. Sai da ta duba taga Didi Shahidah da Amaal da Ammie duk a online sannan ta shiga group ɗinsu tai video call. Babu ko ɓata lokaci duk suka shiga yin joining. Sun san da zaman office su duka, amma basu taɓa ganinsa ba. Aiko ta shiga nuna musu komai daki-daki. Sai da aka gama murna sannan Ammie ke tuhumarta miyyasa ta dawo aiki haka da wuri, kwana tara fa kenan.        A shagwaɓe ta ce, “Ammie su Oum ne fa sukace na dawo”.      “Shi Ajwaad ɗin fa?”. Shiru tai ta kasa cewa komai. Ammie ta ce, “Humm. Maanal nidai zan baki shawara kibi mijinki, abinda ya faru ya riga ya faru, kar kiga Aban Fadeel nata baki kariyar nan kice kin samu damar bijirewa kema. Bance kada kibi umarninsa ba, amma ki ƙyautata alaƙarki da mijinki kinji”.      Sosai idanun Maanal suka cika da ƙwalla. Muryarta na rawa ta ce, “Amma Ammie shike nan komai da yay min yasha ruwa? Har yanzu fa babu wata nadama a tattare da shi. Ganin komai yake tamkar ma dolene a tsakanina da shi. Idan shi dake namiji bai sauke girman kansa ba Ammie sai ni na zubar da kaina a garesa?.”        “Ni bance ki zubar da kanki ba. Amma ki kula da duk abinda zai dinga kasancewa a tsakanin ku. Maanal kawai kinƙi yarda ne, amma Ajwaad ya jima da yin nadama, sannan yana sonki fiye da zaton kowa. Bafa dole sai namiji ya buɗe baki yace ma mace yana sonta bane zata yarda. Irin su Ajwaad a aikace suke nunawa musamman idan akai dubi da yanayin shaƙuwarku”.      Baki sosai Maanal ta tura gaba, “Ammie kawai dai baya laifi ne a wajenki”.          “Oh haka kikace? Shike nan nayi shiru. ALLAH ya daidaitaku cikin sauƙi. Ni bara naje gidan Nene zanje ALLAH ya sanya albarka. Sai a sake riƙe gaskiya a kumayi aiki tuƙuru”.      Kai ta jinjina tare da faɗin, “In sha ALLAHU Ammie”.      Ammie na fita Amaal da Shahidah da suke sauraren faɗan Ammie suka shiga tsarama Maanal abubuwa. Dan suma dai suna goyon bayan kada Maanal ta sake tayi sake har sai ya kwantar da nashi kan. A cewarsu ita Ammie bata san halin mazan zamanin nan ba ZUMA NE SAI DA WUTA. Balle ma irin su AA miskilai ga giyar kuɗi na hura su.        Kiran wayar da akai ya saka Maanal tuna a office take, haka suma su Shahidahn duk suna wajen aiki. Ai babu shiri sukai sallama akan idan sun koma gida ayi zaman. Wayar ta ɗaga, Director Mustapha ne. Bayan sun gaisa yake sanar mata akwai meeting nasu na designers zuwa 12 inji HOD. Yanda yake mata magana da girmamawa sai ma abin ya bata dariya. Itafa su rufa mata asiri suna oganninta bai kamata suna mata haka ba. Maganar aiki daban da matsayin da suke kallonta da shi yanzu. Dan haka ta ɗauki aniyar yin maganar a wajen meeting ɗin in sha ALLAHU.        Ganin akwai sauran lokaci ta fara duba ayyukanta na baya, wanda ta fara bata ƙarasa ba da wanda zatama gyara. Sosai take aikinta a nutse, cike kuma da shauƙi. Akwai aikin da suka fara fa Yaqub, basu kuma kammala ba, tana ganin kafin aje wajen meeting ɗin kuma ya kamata su kammala shi. Kan waya ta ɗauka bayan ta duba cote ɗin department ɗinsu tai kira. Bayan an ɗaga tare da gaisheta batare da tasan wanene ba ta buƙaci ganin Yaqub a office ɗinta, ba kuma tare da jiran amsa ba ta ajiye..           Cike da gulma daga can Zaharadeen ya ce, “Matar boss ce fa da kanta.”       Kusan su duka idanu suka waro, Yaqub ne kawai yay kamar ma bai jisu ba. Zaharadeen ya cigaba da faɗin, “Yaqub kai take nema, dan ALLAH idan kaje ka nema mana damar ganinta, dan ya kamata muje mu miƙa gaisuwa mu taya murna muyi ALLAH yasa alkairi ko ALLAH zaisa ta manta da abinda ya faru baya”.      Miƙewa Yaqub yayi yana mai girgiza kansa. A fili ya furta, “Oh ko kunya ku bakuji ba yanzu ko ita da kanta tace kuzo sai kuje dan neman kusanci da ita”.        “Da gudu ma kuwa. Ko tunani ka kai kaɗai zakaci arziƙin?”.    Cewar Ema.. Murmushin takaici Yaqub ya saki, batare da yace komai ba ya nufi hanyar fita abinsa ɗauke da folder ɗin daya haɗa drawing pappers ɗin daya san zata nema a wajensa. Yana gama ficewa Jameel ya ce, “Ɗan baƙin ciki, idan fa bamuyi da gaske ba guy ɗin nan sai ya kankane komai ta yanda ko kallonmu bazata ringa yi ba balle ta tuna munrayi tare anan matsayin abokan aikinta. ALLAH dai yasa ta manta da abinda ya faru baya. Ni damuwata ma randa ta kamamu muna gulmarta ni da Teemo da Hafiz”.        Caaa kowa yay yana faɗar albarkacin bakinsa. Sai dai duk suna cikin fatan ALLAH yasa Maanal ta yafe musu sudai. Daga haka suka ɗora da gulmar ashe Maanal ɗin tasan abinda ta taka akwai alaƙa tsakaninta da boss shiyyasa take musu girman kai. Gashi nan cikin ƙanƙanin lokaci tazo ta samesu ta kuma shallake abinta matsayin ogarsu. Kai kai wannan al'amari da taɓa zuciya yake..........✍️ _😀 ALLAH ya shirya yan gulma a duk inda suke🤣😂_        *_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_* *09032345899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* Chapter: 13 ......A office din Maanal kuwa sai da taima Yaqub magana sannan ya dan saki jiki suka karasa aikin a dan gurguje saboda lokacin meeting dinsu yayi. A tare da shi suka fita a office din. Hakan yay dai-dai kuma da sakkowar AA daga sama, da'alama daga office ya fito. Bayansa CFO ce da Bussines Director. Da alama suma wani abun zasuyi mai muhimmanci, dan elevator suke kokarin nufa. Wani irin zuba musu ido AA yayi dan guntun sakewar dake fuskarsa na bacewa. A ransa ko ayyanawa yake, (Yarinyar nan bazata fita sabgar yaron nan ba ko?). A zahiri kam yanda ya wani dauke kai sai ka rantse baima gansu ba. Amma ita Maanal tana gannin kallon banzar daya watsa mata na fisha ta kasan idon. Amma itama sai ta wani basar kamar bata gansu ba ta nufi hanyar conference room tana cigaba da wayarta. Dan magana take da Amrah data kirata suna fitowa. Shi dai Yaqub dan matsawa yay ya gaishesu. CFO ce kawai ta amsa da Bussines Director. Boss yi yay kamar baiji ba ta shige elevator. Kasancewar shi Yaqub ba kallonsu yake ba bai san yaya boss din yake ba. Sai da suka shige kofar ta rufe sannan shima ya nufi conference room din..... Rafeeq na zune Nuwaira a jikinsa tana masa hira amma shi hankalinsa na wani tunani daban. Maganar zuwan Najma Abuja ce keta masa kai-kawo a rai. Kodai zai yi amfani da wannan damar ya sata tai masa wani aiki. Wani gefe na zuciyarsa kuma na farin ciki da fatan tabbatuwar abinda yake hasashe a tsakanin Najma din da Fawzan. Dan auren wani karin GARKUWA ne ga aunty Babba bayan na AA da Maanal. Tun jiya yake son yin waya da Maanal, dan yana son su tattauna wasu abubuwa masu muhimmanci sai dai bai san a yanda zata kalli al'amarin ba. Sannan alakarsa da ita kafin aure zai iya saka AA yaji wani abu a ransa idan yaga kiran duk da yasan har abada Ajwaad bazai kawo mummunan abu a garesu ba, amma yana da kyau ya kiyaye. To amma a yanzu batun Najma sai ya zaburar da shi, a ganinsa hakan wata hanya ce mai sauki da sakon da yake so zai isa ga Maanal din dan ita kawai yake so a wannan gabar tasan hakan saboda ya yarda da ita dari bisa dari, ya kuma gamsu da tarbiyyarta da soyayyar da takema yar uwarsa, soyayya ce irin ta da da mahaifi..... "Babie!" Nuwaira ta kirashi a cikin kunne cike da shagwaba. Kallonta yay da sauri, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da sakar mata murmushi ya sake jawota jikinsa. Hancinta ya kama ya dan ja. "Kefa yarinyar nan shagwababbiya ce. Minene kuma?" Baki ta dan tura masa. "Bakai ne ka tafi tunani ba inata kiranka bama ka jina. Minene ke damunka wai? Ina lure da kai tun jiya baka da sukuni" Sake lakace mata hanci yayi. Tare da fadin, "Tunaninki nake fa". Tai murmushi mai kayatarwa. Duk da tasan ba hakan bane cike da farin ciki tace, "Godiya nake Babie. ALLAH ya kara mana farin ciki da kwanciyar hankali", "Amin my angel, harma da soyayyar juna" Ya fada yana kankameta a cikin jikinsa. Wata irin soyayyarta na ratsa jini da bargonsa. A tabbas har randa aka daura masa aure da ita zuciyarsa Maanal take so, amma ganin halin da suka samu AA ya sake sakashi daukar damarar yaki da zuciyarsa akan sadaukarwarsa. Dan ya sake tabbatar da AA ya fisa bukatar Maanal. Shine kuma ya cancanci samunta din. Koda ya shigo ya samu Nuwaira a dakinsa matsayin mallakinsa baiyi wani yunkuri ko tunanin zasu sami juna ta sauki ba, sai dai kuma labarin ya canja saboda karfin tasirin nasihar iyayensu a garesu, gashi shi kuma yana a cikin wani hali na bukatar abokiyar rayuwa. Cikin kudirin samawa kansa sauki kawai ya yarda ya tunkareta, sai dai a lokacin da komai ya kankama sai labarin ya canja, dan tamkar ya shiga sabuwar duniya ne da zazzafar soyayyarta. Na biyu hakurinta da biyayyarta, Nuwaira bata da kwaramniya, ga saukin kai da kyakkyawar fahimta. A dan kwanakin da suka samu tare ya fahimci hakan sai soyayyarta ta kara tasirantuwa a zuciyarsa. Dan haka yake baje kolin amarcinsa yanda ya kamata, itako tana nuna juriya da dattako.. Daukarta yay cak ya nufi bedroom. Zizzilewa ta farayi cikin dariya tana fadin, "My R please Aunty Rufaidah fa zanje na taya aiki a kitchen" "A nan ma ai aikin zakiyi, yama fi na Aunty Rufaidah lada". ". Ya fada yana tura kai cikin dakin da sumbatar goshinta.. Tattaunawa ce sosai ta kasance a zaman meeting din na su Maanal. Domin abubuwane masu muhimmanci da suke son kawowa na gyara a matsayinsu na artists din companyn. Daga karshe Director Mustapha ya sanar dasu batun da za'aje kasar Chaina a kansa. Wadda tun kwanaki CEO ya gabatar, ya kuma bada damar kowanne bangare su bada mutane biyu da zasu samu horaswar ta kwanaki goma kacal in sha ALLAHU. To zuwa yanzu kowane department na kokarin kai nasu, dan haka suma ya kamata sukai nasu din. Dan haka adan nazari da su manyan sukayi cikin satin daya gabata, da ayyukan kowa da suka duba da kwazonsa sun yanke wadanda suke ganin sun cancanci zuwa. Aifa nan kowa ya shiga gyara zama da fatan ya kasance shine. Duk da kuwa wasu a cikinsu an taba zuwa dasu wasu kasashen akan irin hakan. Dan ba sabon abu bane duk bayan wata shida Company na irin wannan zuwa karo sanin kai da kai din dan karuwar ilimi ga ma'aikatansu. Director Steven ne ya mike yay bayanin wadanda suka samu wannan dama. Wato Maanal Habib Giro da Yaqub Nuhu. Tuni fuskokin su Zaharadeen sun canja, ko tafin da akayi ma da kyar suka tafa. Maanal da Yaqub suka nuna farin cikinsu. Duk da ita dai Maanal bata so haka ba. Musamman data tuna maganar da AA ya taba mata akan tafiyar. Sai dai tana fatan ALLAH yasa bada shi za'ai ba. Suna tasowa a meeting din yay dai-dai da lokacin break. Ransu Zaharadeen a bace suka wuce. Kowa naji a ransa akwai makirci a wannan tsarin. Dan a ganinsu kawai an zabi Maanal ne dan tana matar boss a yanzu, ita kuma ta zabi Yaqub saboda suna tare. To aiko lallai zasusha mamaki, dan ko zasuyi amfani da wannan damar akan Yaqub game da alakarsa da Maanal din sai yabar Companyn nan da kafafunsa. Ai sun san dai boss ba mahaukaci bane ba zuciyarsa ba dutse bace zaiji kishi... Salla kowa yay kokarin zuwa gabatarwa. Bayan an idar masu tafiya cin, abinci suka tafi, masu komawa office suka koma. Harda Maanal kuwa a masu komawar, duk da yau batazo da abincin nata ba. Hankalinta kwance ta fito daga elevator tana danna waya fuskarta da murmushi dan kuwa charting take da su Aneesa. Dai-dai ta danna zata ma Zeezah vn aka zare wayar a hannunta, da sauri ta dago idanunta, sai ko cikin na AA dake kallon wayar alamar karanta charting din yake. Hannu takai zata amshe wayar, ya janye jikinsa batare daya daina karanta hirar tasu ba. Kamar zata saki kuka ta ce, , "Amma dai haka babu kyau ALLAH" Bai tanka mata ba bai kuma daina karantawar ba, sai ma fara tafiya da yayi, binsa tayi tana jinta duk a rude, dan tsokanarta su Aneesan keyi a kansa. Acewarsu har an gama cin amarcin ne ta dawo aiki. Amasar data tura musu cewar (Ai ba sai an gama a gida ba zasu cigaba da ci a office) yasa suka tasata gaba da shakiyanci irin na kawaye. Itako tana bama kowa amsa dai-dai shi. Dan tafi sakewa tai musu surutu a charting fiye da zahiri. Son amsar wayar yasa Maanal bata ankara ba har sun shigo office dinsa. Sai da yakai zaune a rukunin kujerun ta kara kai hannu zata fige wayar batare daya daina abinda yake ba ya saka mata kafa ta fado jikinsa sannan. Da sauri ta kalla inda take, aiko dai a cinyarsa take dare-dare babu karya. Mikewa tai yunkurin yi, yasa hannunsa ya sake rungumota da kyau, tare da saka idanunsa cikin tsakkiyar nata da wani salon dage gira sama. "Bake kika ce za'aci amarcin a office ba! Miye na pretending kuma amarsu ta ango?" Yanda yay maganar kamar mai rada ya saka tsigar jikinta tashi, ga kunya na neman halakata tamkar ba tana tare da Bestyn ta dake goyata a bayansa ba ko bayan kekensa, wanda suke cin abinci a kwano daya. Wanda yasha yimata wanka da mata tsarki, wanda yasha wanke mata underwears harda masu jini a jiki batare da kyankyami ba. Wanda y..." Knocking kofar da akai ne ya katse mata tunani, bama tasan ta daka tsalle ta mike daga jikin nasa ba gaba daya. Bai hanata ba, amma ya kamo hannunta ya zaunar a gefensa gab, kafin ya danna remote kofar ta bude a hankali ta hanyar rabewa biyu. Kallo daya AS yay musu ya dukar da kansa. A haka ya karaso gabansu ya ajiye basket din hannunsa yana fadin, "Sir gashi in ji driver". '. Bai jira amsarsa ba ya juya ya fice, kofar ta koma a hankali ta rufe kanta. Ajiyar zuciya Maanal da kanta ke kasa ta saki. Kallonta yayi, ganin ta kauda kai gefe ya dan labe baki,sai kuma ya gyara zama ya fara fiddo kulolin da ke cikin basket din wanda babu tantama yasan na gidansu ne, kuma tabbas daga Oum suke. Sai da ya gama bude komai kamshin abincin ya bulale office din sannan ya juya yana kallon Maanal dake satar kallon sa shi da abincin ta gefen ido. "Mrs Darma aikin kine wannan! Tashi ki bani abinci". Kallonsa ta juyo tayi, ya dage mata gira daya. Cike da neman magana ya furta, "Kin san dai anan babu Aban naki ai balle kice bazaki yi ba". Sosai ta tura baki gaba. Batare da tace komai ba ta matsa kadan bakin kujerar ta dauka plate ta fara hada masa abincin. Idanu kawai ya zuba mata, ransa fes da kasancewarsu a hakan. Sai yanayin ke tuna masa wani lokaci acan baya daya shude. Murmushi ne ya shiga kawata fuskarsa dan tamkar a yanzu ne komai ke faruwa. Harta kammala bai farga ba, sai da ta dan bubbuga spoon a plate din sannan. Cike da basarwa ya hadiye murmushinsa, batare daya ce komai ba ya gyara zama abinsa ya hau cin abincin bayan ya dauka wani spoon din ya kara alamar nata. "Nifa na koshi". "Dura kike so kenan? Garama kici da arziki". Tasan zai aikata kuwa. Dan haka ta dauka spoon din kawai itama. Jujjuya abincin kawai take amma ta gagara kai lauma ko daya, baice mata komai ba. face dibowa ya nufi bakinta da shi. Yanda yay wani kicin-kicin da fuska babu alamar wasa yasa ta amsa din. "Gulmammiya dama abinda kike so kenan" Ya fada yana dungure mata kai tamkar ba shine yay maganar ba. Ita sai abin ma ya bata dariya, amma bata dara din ba ta dai yi murmushi dan ya tuna mata baya. Idan ya lallabata taki cin abinci musamman in tana fushi da shi sai ya diba ya bata a baki tare da dungure mata kai sannan yace mata gulmammiya. Murmushin nata ba karamin daukar hankalinsa yay ba, amma yasan yana yin magana zata birkice masa, dan haka yay shiru ya cigaba da cin abinsa yana diba yana bata kuma. A mamakinsu sai gashi su ci sosai abinsu. Sun kammala kenan tana gyara wajen kiran waya ya shigo masa, AS ne ya sanar masa ma'aikata fa sun taru domin masa murnar aure. Amsa ya basa da cewar suna zuwa. Daga haka ya yanke kiran. "Oya let's go mutane na jiranmu". Da mamaki Maanal ta bishi da kallo dan ya nufi inda rigar suit dinsa take, "Wai mi?". Ta fada cikin sigar tambaya. Batare daya kalleta ba yace, "Zasu tayamu murnar aure ne". Kasa sake cemasa komai tayi, ta karasa tattare komai kawai ta maida a basket din sannan ta mike, veil dinta ta gyagygyara tare da daukar wayarta a inda ya ajiye sannan ta nufi kofa inda yake tsaye yana jiranta.......Chapter: 14 .HUZNAH Sosai gabban jikinta ke mata ciwo, duk yanda take tunanin iya daurewa hakan ya gagara. Kuka kam taci harta godema UBANGIJI. Zagi babu kalar wanda Sageer bai sha ba a wajenta. Gashi bata sake jin motsinsa ba a gidan sai bayan magrib. Tana zaune wujiga-wujiga har yanzu bata gyara jikinta balle sauke nauyin sallolon dake a kanta ya shigo dakin. Kallo daya yay mata ya dauke kansa, batare da damuwa da hararar da take binsa da shi ba ya wuce bathroom din dakin. Ruwa mai dumi ya tanada sannan ya fito, batare da Huznah data cusa kanta a kafafunta tana sabon kuka na takaicin ganinsa ta ankara ba taji kawai an ciccibeta.Mutsu-mutsu ta farayi na son sauka, amma da yake karfi ba daya ba ko gezau ya shige bayin da ita. Tana kai masa duka da komai da fisge-fisge ya taimaka mata. Sai da ya tabbatar ruwan ya ratsa mata jiki ta samu yar nutsuwar da yake bukatar ganinta a ciki sannan ya fito a binsa muryarsa babu alamar wasa ya bata umarnin yin wanka tare da gargadinta mintuna biyar ya bata tazo tai sallolin data tarama kanta. Idan kuma ba hakaba zata sha mamaki. Haka kawai taji wata masifaffiyar shakkarsa, babu bata lokaci ta gabatar da duk abinda ya sanyata ta fito tana dingisa kafa daure da towel. Duk da ta bashi dariya da tausayi duk sai ya danne, fuskarsa babu fara'a ya mika mata riga da hijjab, komai batace ba ta dauka ta sanya ta fara gabatar da salla. Sai da yaga har tayi raka'a biyun farko sannan ya fita domin zuwa massallaci shima....... Karfe biyar Abah ya kirata yace ta fito su wuce. Lokacin tashi yayi, amma akwai aikin da take yi, sai dai bazata iya cema Aban haka ba, sai kawai ta tattara aikin da abinda duk zata bukata ta tafi da su bayan ta kashe wutar office din ta fice. Kai tsaye inda AS ya nuna mata zata dinga ajiye key dan masu shara da safe su gani ta ajiye. Batare da tabi takan AA ba ta fice abinta ta samu su Abah. Cike da girmamawa ta gaisheshi sannan ta shiga driver ya maida kofar da dama shine ya bude mata ya rufe. Fuskar Abah da murmushi ya danka mata tsarabar da yayo mata, dan shi fa har yanzu kallonta yake tamkar su Naufal a gabansa. Cike da jin dadi tai godiya ranta fal farin ciki... Sam AA bai san da tafiyar Maanal ba. Aiki ya masa yawa harya shiga over time din nasa na tsiya. Kiran magrib ya sashi kallon kawataccen agogon dake a office din. Dan tsai yay cikin tunanin Maanal data fado masa a rai. Sai kuma ya dauka waya yay kiran AS dan yasan tunda bai shigo masa sallama ba shima yana nan bai wuce ba. llai kuwa hakanne. Yana dauka daga can AA din ya furta, "Zo mana". Ya yanke kiran. Babu jimawa sosai AS ya shigo, sai da ya masa sannu da aiki kafin yace, "Gani sir". Batare da AA ya dago daga abinda yake ba ya ce, "Besty fa?". Sam AS bai gane kan zancen ba, dan haka ya ce, "Sir Besty kuma?" Karan farko AA ya dago ido ya kallesa, sai kuma ya dafe goshi ya dan murza. Cike da basar da subutar bakin nasa ya furta, "Maanal". "Oh l'm sorry Sir, ai inaga tun five ta tashi". Jimmm AA din yayi, sai kuma ya jinjina kansa batare da ya sake cewa komai ba yay masa nuni yaje. AS na gama fita AA yaja numfashi ya fesar, sai dai a zahiri baice komai ba. Saima mikewa da yay ya nufi bedroom yay alwala. Koda ya fito tattara dukkan abinda zai bukata yay a cikin briefcase dinsa, dan dolensa yay aiki a gida kam daren yau. Yana fitowa AS ya amshi kayan hannun nasa ya hada da nashi shima, a tare suka sauka kasa. Sai da suka fara salla a massallaci su yan tsiraru dan akwai irinsa yan over time sannan suka nufi gida shi da drivern sa, AS ma tashi motar ya shiga ya nufi nasu gidan..... Lokacin da AA ya isa gida tuni Maanal ta jima da hutawa. Dan har taya Oum girki tayi kasancewar rigimar Abah ta tilasta mata komawa kan duty. Bayan sun kammala ne suka nufi daki yin salla. Ana idarwa tai zaman yin karatun Alkur'ani Oum kuma na lazimi har akai ishai sannan suka fito. Sashen Abah Oum ta tafi, hakan yasa Maanal zama ta shiga duniyar tunanin nata na fama. Gaba daya kwanakin nan hankalinta ba'a jikinta yake ba. Dan al'amarin su Mamy yayi matukar jijjiga mata zuciya. Dauriya kawai take tana danne komai dan kar kowa ya fahimta musamman AA da Oum. Hatta a office yau dauriya kawai take da karfin hali. Dan tasan idan kowa bai fahimci halin da take ciki ba shi zai fahimta. Shiyyasa ma ta toshe duk wata hanyar kasantuwarsu a waje guda a gidan kafin yau, yayinda shi kuma ta fahimci yana fushi da ita akan hakan duk da dai yanda suka kasance yau a office kamar ya huce... Bayan wucewar Oum zaman shurun ya isheta, gashi tana son yin waya da Didi Shahidah. Tasan kuma dole ta nemi inda zata kawaice idanun mutane kodan abinda zasu tattauna. Fitar Oum zuwa sashen Abahn ya bata damar daukar novel dinta da glasses ta yafa karamin veil a kanta batare data daura dan kwalin atafar doguwar rigarta ba ta dauka ruwa da popcorn dake ajiye a dining. Compound ta fito, sai da ta gama bin koina dake kwanyar da hasken security light da kallo sannan ta nufi hanyar inda AA

Chapter 7 of 15